Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, 18 July 2015

AURE KOH ZAMAN GIDA? 2

adsense here ♥♥♥AURE KO ZAMAN GIDA♥♥♥••••••••
•••••••PART 2••••••••••••••••••
…Munci munsha mun hole anan na fahinci
zainab
tanada balaeen saurin sabo kuma akwai tsiwa
da
wasan rainin hankali, Nandanan muka saba da
ita
amma naga tafi maida hankali gurina ko dan
taga
nafi hankaline ohoo..?
Watannmu uku da sanin zainab duk ansanmu a
gidanta tana zuwa gidanmu sosai,Ranar munje
gidanta, Nan nanemi ta bamu labarinta daga
farko
tayi gardama daga baya mitayi tunani ta amince
naso inyi shishigi intambayeta amma sunyi
rayuwa
a iran ko amma sai nafasa nace bari in barta
kawai
maji daga baya...
Tun safee nazo inji gulma nikadai nazo saboda
nasan idan nazo da zeenah khalifa to labarin
bazaimun dadiba, Nayi sa'a tagama aikinta
gaskiya
zainab tanada kazar kazar batada son jiki ko
kadan,
Takawomin fresh milk nashanye, Ta gyara zama
ta
fara bani labari kamar haka.........
Sunana zainab Abdullahi mahaifiyata gurin hai
huwata Allah yamata cikawa, Mahaifina mutum
ne
mara kulawa sosai, Sam bai damu da tarbiyarmu
ba
baidamu da chin muba bai damu da shanmuba,
Gamu mu mu shida ne a gidan ni kadai nake
agun
mamata data rasu sauran biyar din duk yayan
kishiyar mamanmune maza uku mata biyu,Agurin
kishiyar mamata na girma, kishiyar mamata
mutumce wacce batayi dan Allah idan kikayi
mata
zatamiki idan baki mataba to bazatayi
mikiba,Amma
bata cutar da kai sai ka cutar da ita, Tana
dauramin
tallan kayan miya ranar da nasiyar to zamuji
dadi
idan kuwa yayi kwantai to bamu ba abinci sam
saboda da dan ribar da take samune take bamu
abincin safe dana rana, Nadare kuwa baba yake
bayarwa, Bata ta6a dukanaba kuma bata cika
yimin
fadaba amma tanacin uban yayanta sosai nice
babba agidan, Banta6a sanin hanyar makarantar
bokoba balle ta addini har nakai shekara goma
sha
daya bana karatu sai yawon talla, Ina sha'awar
boko
sosai inada wata qawa wacce muke yawon talla
tare da ita amina s bawa, Ita tana dan boko ta
bani
littafinta daya tafara koyamin A B C D.... Ina
ganewa
sosai saboda inada hazaqa duk ranarda muka
saida
kayan miya da wuri to ranar zamu zauna muyi
boko
wasa wasa har nafi amina iya karatu sai tafara
jin
haushi saboda musun da nake mata akan
wannan
haka yake tace a'a ba haka yakeba, Haka yake
tadaina koyamin komai ataqaice duk wata
takardar
qosai ta unguwarmu idan nagani sai nakaranta
na
iya hada kalmomin english inkaranta amma
bansan
ma'anarsuba ke intaqaita miki abba duk wani
karatun
indai karantawane ina iyayi da rubutawa.....
Akwai wata rana na fito tallan wara saboda
yanzu
nadaina tallan kayan miya wara nake talla yafi
kasuwa ina tafiya naga wata qatuwar mota baqa
baka ganin waye aciki,Anyi parking dinta a gefen
hanya, Kusan wata daya Kullum sainaga
motarnan
wani yaro yace wai mai motan yace ki kawo
wara
na kalli motan lokacin iya tunanina nasan mai
Wannan qatuwar mota bazai ci waraba, Nace
bazanje, Shegiya matsiyaciya arziki yana kiranki
kina gudu kar kije miya dameni wannan mutumin
duka yake siya yace kikai masallaci....
kukasance tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA
part 3 adsense 2 here
Share:

1 comment:

please after reading drop down your comment here!...

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *