Tuesday, July 21, 2015
**MAI NEMAN MATA***
NAMIJI MAI NEMAN MATA ** A nan.ke matar
gidan nake kalubalanta,idan har Mijinki yana
neman wasu matan a waje to,to Wallahi ba ki iya
kissa ba,idan har kin iya kissa to da wahala ya
kula wasu Matan! Matakan da zaki bi sune,kullum
ki kasance cikin kwalliya da tsabta ,da
tarairaya,sannan aduk lokacin da yake a gida ki
dinga manne masa a jiki sannan hanyar da zaki
hana shi wannan dabi'ar shine,idan har mijinki ya
nemi ya kara Aure ki ka hana shi,to kina zaune zai
kawo miki tsarabar HIV/AIDS HAR BEDROOM DIN
KI,Wani namijin ba ya iya hakura da Mace
daya,wani Namijin kuma matar gidan ce,kazama
ba ta gyara jikinta,wata kuma bata iya jure
sha'awar maigidan to anan mijinki zai iya neman
Mata,wata kuma ta iya kissa,kwalliyar,da komai da
komai amma Mijinta manemin Mata ne,saboda
masifa kawai ,ba laifin matar gidan bane,to anan
sai ki dage da Addu'a,da ku biyo ni ref;Namiji A
Tafin Hannunki adsense 2 here
Burodin ayaba
Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.
Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.
MAJNOON hausa love novels
Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more