Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Sunday, July 19, 2015

MUHIMMIYAR FADAKARWA GA MATA MASUYIN CIKIN SHEGE.

adsense here vampire2.jpg

img-20150520-133104.jpg

MUHIMMIYAR FADAKARWA GA MATA MASUYIN
CIKIN SHEGE.
Yin ZINA Babban Laifi ne, amma KISAN KAI ya
fishi laifi, duk Matar da ta yi ZINA, Kuma har
tasamu CIKI na ZINA, wannan laifi ne tsakanin ta
da Allah, kada ta KASHE Abin da ta haifa, idan
har ta haihu, ta yi wa abin da ta Haifa tarbiyya,
tayi "ISTIGFARI" Tsakaninta da Allah, ta yi Addu'a
ga abin da ta Haifa Allah Ya yi masa albarka,
domin shi ba shi da laifi, idan Allah Mai girma da
daukaka ya so, sai ya kar6i tuban ta, kuma ya
sanya abin da ta Haifa ya zama nagari.
Amma duk wanda yayi KISAN KAI da gangan.
Idan ba wata rahamar Allah ba, tozai dawwama a
WUTA, KASHE JINJIRI kamar KASHE BABBAN
MUTUM ne.
Saboda fadin Ubangiji inda yake cewa:
"WA MAN YAKTUL MU'UMINAN MUTA'AMMIDAN
FA JAZA'UHU JAHANNAMA".
Ma'ana
DUK WANDA YA KASHE RAI DA GANGAN
SAKAMAKONSA WUTAR JAHANNAMA.
ALLAH YA KARE MU, AMEEEEN
Hakama shan GIYA, Haka LUWADI, Haka CACA,
haka rantsuwar KARYA,
Duka wadannan laifuka ne tsakanin Bawa da
Ubangiji, idan Mutum ya TUBA Allah zai yafe
masa.
Amma hakkin tsakanin Mutum da Mutum, lallai
Mutum ya nemi GAFARA wajen Mutum Daya
zalunta, sannan Allah Ya yafe Masa.
KUMA BA'A SAMUN SHEGE A GIDA, IDAN MUTUM
YANA MATA 2 KO 3 KO 4 YA DAUKI KWANAN
WATA YA BAWA WATA, KOTA SAMU CIKI A
WANNAN SADUWAR BA SHEGE BANE, SAIDAI
KAWAI ACE YA ZALUNCI MAI WANNAN KWANAN.
SAI YA NEMI AFUWA TA YAFE MASA.
KUMA YIN ZINA DA MACE BAYA HANAWA A
AURETA, KODA TAYI CIKIN SHEGE TARE DA
WANDA YAYI NIYYA ZAI AURE TA, SUN AIKATA
ABIN DA ALLAH BAYA SO, YANZU KUMA ZA SUYI
WANDA ALLAH YAKE SO, SAI SU TUBA, TARIKE
DANTA TA GAJE SHI YA GAJE TA KO 'YAR,
AMMA SHIDAN BAZAI GAJI WANDA AKE ZATO
SHI YAYI MATA CIKIN BA, IDAN HAR ZA A YI
AURE, BAYAN HANKALI YA DAWO MUSU SAI TAYI
"ISTIBRA'I".
{WATO JINI UKU}
TANA DANA SANI MIYAGUN AYYUKAN DA TAYI
TANA ROKON ALLAH YA GAFARTA MATA,
TAZAMA CIKAKKIYAR BAZAWARA, SAI YASHIGA
CIKIN ZAWARAWA, KOTA AURE SHI, KOTA AURI
WANI".
TO MALAM IDAN CIKIN NA 6ARAYINE YAYA
KENAN ???
Amsa.
IDAN 6ARAYI SUKA SHIGA GIDA, HAR SUKAYI
ZINA DA MATAR GIDAN, TO LALLAI TAYI
"ISTIBRA'I KAFIN MIJINTA YA SADU DA ITA,
DOMIN MAI YIWUWA TA DAUKI CIKI, KUMA KADA
MIJIN YA SADU DA ITA, IDAN SHI MIJIN BAISAN
6ARAYI SUN SADU DA MATARSA BA, HARYA
SADU DA ITA, TO "ISTIBRA'I YA FADI, SAI A
BARWA ALLAH HUKUNCINSA.
ALLAH SHINE MASANI". adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *