Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, July 18, 2015

WACE CE ITA? 32

adsense here .: WACE CE ITA..?? 32
Na ABBA GANA
Sun qarasa gidansu iffaat goggo tagansu ba
zata duk da batasansuba amma ta gane farhan
goggo harda tuntube Dan tsabar rudewa, baki
kuwa har kunne tasan cewa zata samu alkhairi
zuwansu, ta musu shinfida aka kawo musu fura
sabuwa aka siyo nono aka xuba a cikin furar sun
kwashi damu lafiyayye farahnax hadda santi da
yake goggo ba qazama bace su iffaat ne dai
ragajabul, mutane sai zuwa kallon su akeyi,
iffaat dai bata gaida farahnax ba, ke ko kallon
gefenta batayiba, iffaat tace wa farhaan yazo ta
kaishi yaga gari, yakuwa biyota sun zaga garin
tana nuna mai guraren da tayi hatsabibanci
sunata dariya ko ina kallonsu akeyi wasu suna
gulma ana cewa ta lalace, har yanzu ba miji
amma ba halin magana yanxu mutum yaji ba
daidaiba ba Wanda zai iya tunkararta da zancen
rashin miji, dasu dijee aka zaga garin duk gunda
ya masa kyau sai ya tsaya ya dauki photo har
sukaje bakin ruwa, suka shiga kwale kwale yayi
hotuna sosai, qarshe yayi photo da iffaat bakin
ruwa, hotunan sunyi kyau sosai iffaat tayi haske
yanxu cox kullum sai sunyi wanka tanason ta
zama yar gayuuu....
Bayan sun dawo gida umma tace miyasa bamu
tafi da farahnax ba, iffaat tayi sauri tace au
dama tare akazo da ita?? Ni banma gantaba sai
yanxu. Taci gaba umma kinsan farahnax ta
tsaneni har na baro birni batamin magana,
shiyasa nima na fita harkarta, kowa sharhin nata
ya bashi dariya. duk suka kwashe da dariya, nan
dai aka shiryasu sundaina fada,
Su umma suna son a basu iffaat taci gaba da
musu aiki, koda ba aiki takeyiba yanxu kamar
yarsu take Dan Allah yasakawa umma qaunar
yarinyar, dama ga iffaat akwai shiga rai, ran
iffaat baiso tafiyaba amma idan ta tuna abinda
goggo tace mata sai taji gara ma tabar garin
wataqila birni ta samu miji tayi Aure,
Sun tafi akan nanda sati daya za'a aiko a tafi da
iffaat
Sun ma goggo alkhairi sai washe baki takeyi,
itakam yayan kishiya sun mata rana, koda bata
haihuba ta moresu.
**
Bayan Sati daya akaxo daukar iffaat ta buga
qafa a qasa akan ita sam baxatajeba sai anyi
bikin qawayenta dijee da rukayya, goggo tasata
daki, ta mata huduba,
Yanxu idan kika zauna har bikin su wallahi
gulmarki kawai zasu riqayi ace har qawayenki
sunyi Aure ke bakiyiba kinga ba dadi haka, gara
kije birni abin ki, ki raqayin gayu kamar yar
yarinyar nan danaga sunxo da ita har ki sami
miji Dan gayu irinki kiyi aurenki a birni, idan
kuma zama zakiyi bakin mutane yakamaki to
shike nan. Maganar goggo ta shigeta , gara birni
da qauye, ta hada kayanta taje tayi sallama da
su dijee ransu baisoba tana babbar qawa ayi
bikinsu batanan amma ba yanda ta iya itama
taso ayi da ita, amma goggo ta hore mata
kunne...... adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *