Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, July 18, 2015

WACE CE ITA? 7

adsense here WACE CE ITA..?? 7 Na abba gana Tashin hankali ni kaina Jabo na tausaya wayanda zasu dauki ippatu aiki gidansu kamin su korota nasan zataci ubansu.! Goggo kullum gori take mata har ta fara girgar dangi a gida, amma ba mashinshini bare a aurar da ita. Wazai kwasar ma kanshi jaraba. ippatu da yar birni ce da sai anyi haddadiyar mace dan komai Allah ya bata sak mamanta ta dauko fulani gaba da baya sai ta hada da da duhun babanta sai tayi Dan duhu farinta mai haske ne da duhu gata qirar kalangu ga gashinan kamar yakasheta amma ba gyara idan akayi kitson sallah qarama sai babbar sallah ake tsefeshi, tayi baqi Dan na tabbatar da tafi zainb khalifa baqi sabida tsabar rashin wanka, qafafu duk sun jeme haqora sunyi tsatsa da wata laka laka a ciki idonnan sunyi ja duk jikinta tabone sabida fadowa saman bishiya da akeyi a jijji ciwo, ko saman Garu da ake dirowa ko a na gudu a fadi a ji ciwo haka dai take masha Allah..... ******* Goggo tayi magana da altine akan tanason a kai ippatu birni aiki amma inaaaaaa altine taqi aminta Dan tasan halin ippatu sama da qasa, gaba da baya, altine taqi yarda har goggo ta gaji da zuwa gidanta neman alfarma ta haqura, ranar goggo taje suna maqotansu taga wata mata daga birni tana maganar a nemo mata yar aiki yarinya qarama mai qoqari da kuzari goggo batace komaiba, Dan tasan idan ma tayi magana anan mutane zasu fadi mugun halin ippatu. Saida aka watse matar na fita goggo ta faki ido ta bi bayanta, tajata gida tace tanada ya amma batason kowa yasan zata kaita aikine zatace takaita gun yar uwartane goggo tace yarinyar marainiyace, tanason ta dan riqa samun abinda zasu chi su rufawa kansu asiri, Amma batason kowa ya sani, hakadai goggo yayita tsara matar, ana haka saiga ippatu an dawo daga kogi tun safe dataje sai yanxu tayi shudi daya, Koda matar taga ippatu taga uban bokitin data dauko saman kanta chike da ruwa ta tabbatar da cewa ippatu Nada kuzari, kamar gaske ippatu ta gaida matar ta wuce abinta matar kuwa ta amince da ganin ippatu kuma tace baxata fadawa kowaba. Matar da yake gidan biki tayi sanarwar anata kawo mata yara yan mata amma Duk wacce aka aiko sai tace musu ai ta samu bata fadawa kowa cewa ippatu CE ta samuba har ta koma birni,.!! Bayan kusa sati uku da magana matar tazo ta tafi da ippatu birni ta mata dinki kala biyu Dan kar taje Gidan daga shigarta a koresu , aka hada da yan kayan sallarta. Ippatu tayi kukan rabuwa da qauyensu Dan batason zuwa aikin da za'akaita sun rabu da dijee da rukayya sunata kuka sai birni...... adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *