Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, July 18, 2015

WACE CE ITA?3

adsense here WACE CE ITA..?? 3 Na Abba gana Ta wuce abinta koda taje gida ta rasa yanda zatayi ta shiga Gidan ta fara labe labe. Ubanme kikeyi anan ??muryar babanta taji ya mata tsawa saida hanjin cikinta suka juya duk duniya babanta kawai take tsoro ta fara kame kame, bakomai baba sannu da zuwa. To wuce gida munafukar banza ya tasa qeyarta suka shiga. Malam ina ka tsintomin ippatu? wallahi tun qarfe biyu na aiketa Dan nasan halinta batadawoba sai yanxu, kaga har na qare tuwo! Dan ubanki ina kikaje? Ta fashe da kuka wallahi baba sai bayan la'asar ta aikeni ko minti uku banyiba na dawo. LA ilaha illallahu Muhammadu rasulillahi... Ihhatu "haka take kiranta Dan bata iya sunan ba" kina nufin qarya zan miki? Kinma saba bani kayana ta qwace manjanta da daddawarta, baba ya juyo ya kalleta ina kika samu kifi sai qarnin kifi kikeyi. Ta fuske kamar gaske gidan su kulu mai daddawa suka sammini.! Na dauka kin qara tsokano bello mai kifine. Aah wallahi baba.!! Idan ta tashi zama ta Allah sai ki rantse da Allah ba ita bace take taqdiranci a hanyaba kamar wata waliyiya har ma dai gaban babanta..... ******************* Ippatu yarinyace yar kimanin shekara 11 duk yanda zan muku bayanin ta idan dai ba ta muku taqdiranci nata kungani da idonkuba ba zaku gane WACE CE ITA ba, Sabida batada kunya, batada tsoro ba tada ladabi ba tada mantuwa ba yafiya haka take wata hargitsatsiyar yarinya da ita. Gata qazama taqin qarawa, batasan tsabtaba ko kadan haka batasan wankaba bare wanki farace Amma yanxu tafi zainb khalifa baqi, haqoranta Dan rashin wankewa har sunyi tsatsa daga sama, daga qasa kuwa kamar an kwaba laka an shafa mata idonta kuwa gasu Manya Manya Amma sunyi jaa kamar na sister khade qafar nan kuwa duk tayi wani iri Allah ne ya tsareta qafar bata Faso da tuni ta farfashe Dan su dijee tuni qafafunsu sun yayyage da Faso, bata yawo da takalmi, a cewarta takalmi basa barinta gudu. Mahaifiyarta sun rabu da mahaifinta tun tanada shekara 6 tanada yayye guda biyu maza duk mamansu daya, suna gurin mamansu, itama babansu yaje gun mamar ne akan dai ta bashi yayanshi, ta hana, dazai dawo ippatu ta maqalemasa ya dauketa ba da son ran mamarba, tana zaune gun kishiyar mamanta gwagwo rabi, gwagwo batason ippatu ko kadan ita kuwa ippatu ba abinda ya dameta harkar gabanta take bata damu da asotaba kuma gwagwo rabi duk abinda zata mata saita rama cox bata mantuwa bata yafiya.! Shiyasa hankalinta kwance bata tsoron kowa duk qauyensu sai babanta kuma bata ragawa kowa duk qauyen nan. An sakata makarantar boko har uku ana korota sabida uban yara da takeci, a makarantar allo ma Dan yana maqocinsune da tini ya korota ippatu kenan.... adsense 2 here
Share:

1 comment:

please after reading drop down your comment here!...

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *