Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Sunday, 19 July 2015

WACE CE****ITA? 44

adsense here WACE CE ITA..??44
Na ABBA-GANA*****
****
Ranar da farhaaah yazo Nigeria goben aranar
aka hada mai tarba ta musamman a gidan su
iffaat, duk da cewa bata iya komaiba kuma har
yanxu bata taba shiga kitchen da sunan girkiba
amma ta nemo hutunan girki a internet, an hada
kayan komai da komai ana jiran Yy farhaan, tayi
kwalliyar da itakaitaa bansan ta iyataba kuma
batasan dalilin da yasa tayitaba, Suhaila ta
tsaya tana kallonta kinganki kuwa wallahi kamar
wata amarya, please kimin irin kwalliyanki, ta?
kuwa xauna gaban iffaat nidai Abba nace su
iffaat Masu haye hayen bishiya sune ake
kwalliya haka, ai yanxu kam taci uban Yar baqa
zainb khalifa da iya kwalliya iffaat ta dara tace
kina nufin kwalliyata tafi taki kyau? Sosai ma
kuwa nidai kimin tun basu qarasoba haka iffaat
ta tsinci kanta da gyashin yiwa yayar tata irin
kwalliyarta, ta nemi dalilin yin hakan ba dalili,
Suhaila har ta gaji da bibiyarta akan ta mata irin
kwalliyar ta iffaat ta nace akan bata iyaba itama
Sa'a tayi tama kanta.......
Guraren la'asar saigasu farhaan da farahnax sun
iso gidan ita Kuma tana dakin Yayanta tana
hada wasu kaya kamin baqin su Iso, dariyar
farahnax taji tana tambayar ina iffaat take, ta
hango farhaan, wani raaas taji zuciyata ta shiga
harbawa kuma batasan daliliba, farhaan guy ne
lafiyayye duk yanda namiji yake cikakke mai
lafiya to farhaah yana cikinsu dogo ne mai jiki
daidai shi yanada faffadan qirji haka yanada
sajee a fuskarshi wanda ya kwanta yayi luf a
fuskarshi, yana zuwa naga yy Suhaila taje ta
fada jikinsa ya rungumeta, iffat taji wani dum
dum dum...!!! wasu emergency hawayene suka
bulbulo daga fuskata, lokaci daya taji ta qara
tsanar Suhaila da farhaan, kee mi kikeyi anan ga
baqi chan tun dazu naji suna kwala miki kira,?
Ta waigo ba tare da tasan ko wayeba, idonta
sun Riga sun rufe, ta watsamai harara, miya
dameka da abin da nakeyi anan.!? Sokoko yayi
yana mamaki, iffaat kinsan wa yake magana
kuwa??
Tace a gadare nasani Yaya ameen ne yake
magana, kaiiii iffaat too lallai bakida kunya,
Ta kalleshi ido cike da hawaye tana kuka tace
Kaine bakada kunya, ni inada kunya Kaine kaine
Yaya, ta fada jikinsa tana dukan qirjinsa sai jin
yayi tayi deef tayi tana Neman faduwa qasa,
kamin kace kobo ta sumaaa..... adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *