Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Sunday, 19 July 2015

WACE CE*****ITA? 51

adsense here computerimages1.jpg

WACE CE ITA..?? littafina 3 kashina 51
by
Abba~Gana

Duk sukayi tseet principal taja su ZZ aka Basu
punishment mai tsanani dama ansha kawo
qararsu gaskiya sunji jiki ba kadan ba ga duka
ga uban aikinda aka sakasu, duk sun kamawa
iffaat mutunci sunqi mata magana, aka tashi
suka kama hanyarsu itama tayi banxa dasu.
Gobe sukazo nan ma gaba sukeyi sun shirya
mata sharri da zataci duka amma bata saniba
tazo ta musu magana sukayi banza da ita har ta
juya sai Zumar tace ke banza ce wallahi, jiya
shine kika gudu kika barmu, mufa duk wani
hanyar dojewa mun koya miki amma ke baki
koya mana komaiba kalli Dan Allah jiya yanda
aka lallasamu, ta nuna mata hannunta dayasha
bulaloli.
iffaat tayi dariya son ranta sannan ta Basu
haquri suka fara tambayar ta ya akayi daga
saman bishiya ta wuce clss? Harda baba sajeen
aka saka yahau bishiya amma baki ba labarin ki
tayi dariya sosai lallai bakusan iffaatu Yar
mamaba nan ta Basu details yanda tayi sunata
mamaki lallai wannan yarinyar mayyace, kuma
hartashiga class malamin bai gantaba......
Sun shirya mata sharri ZZ kenan sun hada mata
gadar zare sukace sujee baya, sunje baya kuma
an hana xuwa wajen da yake iffat bata taba
zuwa gurin ba, kuma batasan an hana zuwa
gurinba suka turata sukace suna zuwa, har ta
shiga sai kawai ta hango bishiyar mangoro ya
nuna tayi murmushi haba Ashe dadi suka turota
tasha tuni ta haye bishiya ta fara tsinko mango
tana saman bishiya kawai sai taji maganar su
da wani malami wallahi tananan kullum nan
take zuwa mun gaya mata an hana zuwa tace
ba ruwanta. yanxu ma mungaya mata zamu
fada muku tace sai dai a kasheta, kaji mugayen
qawaye....
Iffaat tanajin haka tayi tsanda daga saman
bishiyar tahau garu ta dira a toilet, ta barsu a
gurin, taje da gudu ta kira principal tace tana
bayi taji maganar mata da maxa a bayan skull
principal taje da sajeen koda akaje aka gansu
duk sun cire hijabi suna Neman ta wai ko ta hau
bishiya coz ta gaya musu ta iya hawa bishiya ko
wace irikuwa.
jikinsu ya fara rawa ganin principal tana zuwa ta
fara yiwa Malaminda yake tare dasu fada mi
yaxo yi da yayan mutane anan bayan an hana
zuwa anan tasa aka tafi da su ZZ office.. iffaat
tayi wata dariya ta musu gwalo aranta tace
wallahi saidai Ku wahala duk case dn dana shiga
a duniya zan iya fitardakaina yanxu ya rage naku
ta kakkabe hunnu ta qara gaba.....
Muje zuwa. adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *