Monday, July 20, 2015
WACE CE*****ITA? 53
WACE CE ITA..?? 53
Na ABBA-GANA
*****
An saka ranar auren Yy farhaan da Yy Suhaila
18/12 daidai da ranar brdy din muhd abba gana.
Tunda aka saka ranar auren iffaat sukuni ya
qara kubce mata saidai ta fuske takeyi tayi
harka amma tana azabtuwa matuqa, ta fadawa
ZZ suka bata shawara taci gaba da haquri
kawai..
Lokaci sai matsowa yakeyi ita dai mama ta rasa
gane sirrin zuciyar iffaat farko ta gano cewa
tanason farhaan ne musamman lokacin da ta
suma, nan zatoñta ya zama gaskiya, sai kuma
yanxu komai ya tsaya mata yanda iffaat ta
chanxa gaba daya duk wani Abu da take da wa
suhaila batayinsa yanxu, hakan yana basu
mamaki sai kawai suce ta qara girmane....
An fara shirye shiryen biki su iffaat da farahnax
sune qirjin biki dama farahnax ta hada auren, shi
farhaan irin ya nuna yanason suhaila irin
soyayyar shan minti sai kawai farahnax taje ta
fadawa su umma, kuma Suhaila ce keson
farhaan sosai shi ba wani sonta yakeba, amma
ganin iyayensa sunshige gaba yasa ya sallama
ko banxa Suhaila kyakyawace kuma tana daga
cikin matan da yake so dalilin da yasa ya
amince da ita kenan. amma bai taba sontaba
daidai da rana daya..
hasalima mafi yawar da sukeyi ita take kiran shi
kuma ita Suhailar tasan ba wani sonta yakeyiba
haka take son kayanta. Allah sarki Suhaila tana
bala'en burgeni cox ba ruwanta abinda na
fahimta farhaan ya sace zuciyar Suhaila da iffaat
ne amma iffaat ta barwa Allah tasan ba yanda
za'ayi ya aureta bayan ma ya rainta gata
qanwar matarshi...
haka dai akayi komai cikin jin dadi auren ya
qayatar anyi komai cikin jin dadi da arxiki naira
taci ubanta...
An kai amarya dakin mijinta,
Hmmm Daren dai iffaat ba'ayi bacci ba gaskiya
na jinjinawa iffaat matuqa cox tayi jarrumta ba
kadan ba nidai jabo idan nice wallahi sai nayi
ciwo, Ashe Banida labari hadda iffaat anyi
zazzabin daurewa kawai takeyi, ta bani tausayi
matuqa kowa sai yace gajiya ce da kuma kewar
Yar uwarta har mama Dan yanxu mama ta gane
ba komai zatonta ba gaskiya bane,..... adsense 2 here
Burodin ayaba
Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.
Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.
MAJNOON hausa love novels
Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more
niko na ce hmmm
ReplyDelete