Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, July 20, 2015

WACE CE******ITA? 57

adsense here computerimages1.jpg

WACE CE ITA..?? 57
Na ABBA-GANA
Bata tsaya ba taci gaba da chin uban hafsa
farhaan ya kasa aikata komai kunya ta isheshe
dagyar hafsa ta samu ta miqe tayi bayan
farhaan da gudu tana kuka, tabbas hafsa ta
gane iffaat Dan kuwa itace ta qona mata qafa
shekara wajen Shida da suka wuce, iffaat ji take
kamar ta hada da farhaan din ta musu lilis
amma bazata iya dukan farhaan ba, tsanar sa ta
rufe mata ido ta tausayawa yayarta da take
tareda fasiqi irin sa tagodewa Allah da bata
aureshiba, da saidai suyi kashin kai a gidan Dan
bazata dauki wannan iskancinba ta dakawa
hafsa tsawa tabar gidannan hafsa ta kasa fitowa
bayan farhaan ta qara mata tsawa wallahi idan
naxo sai na kakkaryaki, inbanda hafsa batada
gaskiya ai ko qanwar hafsa iffaat bazata iya
fada da itaba bare hafsa mai Shekara wajen 30,
zata kakkarya iffaat. amma tunda batada
gaskiya dole ta boye farhaan kuwa ya rungume
hannuwa yana kallon ikon Allah kunya ta isheshi
da nadamar abinda ya aikata, tayi cikin hafsa
da qarfi hafsa ta riqe farhaan da qarfi wani baqin
cikine ya qara tasomata yanda taga tana
rungume farhaan ta baya uhum su kishi manya
tayi cikinta da qarfi ta janyo gashin da tayi qara
da qarfi ta wurgata a kan fridge farhaan ya
dakawa iffaat tsawa akan miye haka ta juyo
tamai kallo keep quiet ina zuwa gunka kaima..!!!
tama hafsa gargadi kamin ta lissafa biyar tabar
gidannan hafsa dagyar ta miqe ta kwashi
kayanta a hannu taji jiki tana gudu tana tunanin
wai wannan WACE CE ITA?? House girl ce haka
kyakyawa kuma ta mata haka gaban farhaan.
Anya kuwa?? Bayan ta kori hafsa ta juyo ta kalli
farhaan ido cikin ido tana tunanin balbala masa
masifa ji take kamar zuciyarta ta fito Dan baqin
ciki aranta tace wai ita kenan inaga matarsa da
sukasan juna idan taga haka sai hade rai ta
mutu.! Ya dago ido ya mata wani kallo ta
mayataccun sexy eyes dinsa tuni ta manta
abinda takeson ta masa sai ya bata tausayi tayi
tsaki.....
Har zata fita dakin sai kuma ta daure ta dawo ta
gyara ko ina ta tattara sauran kayan hafsa data
bari ta miqa masa tace ga kanan tsohuwar
karuwarka nan idan ka bita ka kai mata.. ta juyo
kenan ya janyo mata gashi da qarfin bala'ee
saida tayi wata qara.... adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *