Wednesday, July 22, 2015
WACE CE******ITA? 64
WACE CE ITA..?
64
by
Abba~Gana
No ka tafi Yaya ni baxanjeba ya rarrasheta har
ta amince suka shirya suka fita. Sunje wani park
ne suna shan ice cream, hakan ya faranta mata
rai matuqa suna sha suna tadi a hankali yy amin
yake nuna mata illar abinda takeson tayi, suna
tsaka da magana tana yan kalle kalle charab ta
hango wani abu wacce ta hango ba shakka itace
ba qarya budurwar farhaan ce ramcy, tayi
murmushi su ramcy ananan da yake Yy baisan
taba tana kallon ta har ta shige ba'ayi minti
goma sai kuma ta hango farhaan, wani rasss taji
ko shakka babu tare suke da farhaan amma da
yake shi mai wayone a hankali yake takunsa, wai
farhaan wane irin jarababben mutum ne?
Tayi tsaki, yy amin yace miya faru kuma? Ta
kalleshi idonta sun kada sunyi jaa ba komai! Ya
ba komai, ta dago mai idonta da har sun zama
qanana tace ba komai yy, sukaci gaba da
tadinsu amma Sam bata tare da yy amin
tanachan tana tunanin farhaan, kusan 30mnt
Basu fitoba ta kasa haquri ta miqe tsaye, ina
zaki kuma? Y tace ina zuwa yaya ya kalleta,
yanxu zan dawo Yy, ta wuce da sauri ta shiga
Ashe cikin gurin hotel ne ta fara dubawa duk ta
zagaye gurin bata gansuba, sai taje gun
reception ta tambayi farhaan mutumin yace
mata yanada baquwa wani rass taji, tace ai na
na sani shi yace nazo na karbi saqo yayanane,
ya kalleta sosai sai ya gaya mata number
dakinsa wani dumm dummm dummmm takeji,
ana mata zagaye a zuciya ta isa gofar dakin tayi
jimm ta daure ta bubbuga saida ta buga uku
sannan aka bude, ramcy ce ta bude qofar iffaat ji
tayi kamar ta shaqeta ta mutu ramcy bata gane
iffaat ba Sam.! ta watsa mata harara, tace lfy
iffaat ta daure tace yy farhaan yace naxo na
karbi saqo na kaiwa umma, tanajin haka sai ta
saki fuska, okay bari na kirashi, ta kwala mai
kira yazo yana zuwa ya ganta.........
Tofa.muhd Abba Gana adsense 2 here
Burodin ayaba
Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.
Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.
MAJNOON hausa love novels
Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more