Sunday, July 19, 2015
WATA BUDURWA DA TAKE SHAN AZABA A QABARINTA. [06:30
Akwai Wata Budurwa da ALLAH Madaukakin Sarki
Ya 'Dauki Ranta, Aka Kaita Maqabarta Aka
Binneta.
Bayan An Dawo Daga Makabarta Sai Daya daga
Cikin Mutanen Da Suka Je Binnenta Akwai Wani
Mutum Ashe Yacire Zoben Hannunsa Ya Sanya a
Aljihun Gaban Rigarsa.
Sai Ya Je Yasami Limamin Unguwarsu Yace
Masa:
Mallam Ka Ji Abinda Yafaru Na Bar Zobe Na a
Gaban Aljihuna Kuma Ina Tunanin Yafada Kabarin
Nan, Kuma An Binne Dashi aciki.
Yanzu Yaya Za'ayi ???
Sai Malamin Yaje Yasami Iyayen Yarinyar Yace
Musu Ga Abinda Ke Faruwa Kuma Babu Kyau a
Binne Mutum Da Wani Kayan Ado.
Nan Take Aka Amince Akan za'aje a Ciro Zoben.
Zuwansu Keda Wuya Suna Bude Ramin, Sai
Sukaga Wasu Bakaken Kunami Dayawa a Cikin
Ramin Suna Harbinta.
Limamin Daya Dawo Sai Yafadawa Iyayen
yarinyar Abinda yake Faruwa.
Ya Tambaye Su Shin Akwai Wani Hali Da Take
Dashi Mara Kyau Ne ???
Sai suka Ce A'a.
Aka Tambayi Qawayenta Suma Sukace A'a.
Sai Malamin Ya Tambayi Mahaifiyarta, Shin Tana
Sallah Kuwa ???
Sai Tace Eh! Tanayi Amma Matsalarta 'Daya
Itace;
Idan Tana KALLO Ko CHATTING Ba Tayin Sallar
Akan Lokaci harsai lokacinta yakusan fita.
Sai Malamin Yace:
"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN"
To Wannan Kunamin Sunayi Mata Azabane
Saboda Rashin Sallar Da takeyi Akan Lokaci.
Don ALLAH Mu Qara Kula Da Sallah Domin Itace
Za'a Farayi Mana Screening Ranar Qiyama.
Mudinga yinta Akan Lokaci, kada kallo ko
chatting yadinga yaudararmu.
Musami Nutsuwa Yayin Da muke yin ita Sallar
kada mudinga yin gaggawa.
Muyi Sallah Kamar Sallar yin Bankwana da
duniya.
A gaskiya kam yanzu muna cikin matsala.
ALLAH Ya Yafe Mana Kura-Kurenmu Manyansu
Da Kananunsu. adsense 2 here
Burodin ayaba
Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.
Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.
MAJNOON hausa love novels
Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more
hasbunallahu Allah ka kare mu dukka
ReplyDeleteameen, kodai keh ma halin ki kenan?
ReplyDeleteeh toh wasu lokuta
ReplyDeletetoh sai a kiyaye
ReplyDeleteHasbunallahu Waniimal Wakil Allah yakare mu Maza da Mata kuma ya shiryar damu bisa Sunnar Maaiki(S.A.W)
ReplyDeleteameen thunma
ReplyDeleteameen
ReplyDeleteAllah yakaremu daga azabansa.
ReplyDeleteameen
ReplyDeletenakaranta wannan labarin a daidai lokacin da yar uwata tai kwana biyu da rasuwa amma in akwai abinda zanmata shaida dashi agaban Allah shina nutsuwar sallah da kuma yinta akan lokaci Allah yagafar ta musu mukuma ya shiryemu
ReplyDeleteIna lil lahi waa ina ilahi rajun allah kai kasan yanda zakayi da bawanka, allah kabawa wana baiwai sauki rayuwa akabareta, kayafe mata zunubata mukuma en uwa dan allah mu kulla da ibadumu allah kasa mudace amin
ReplyDeletekai amman wannan labarin yakamata yazaburar damu mukara maida hankali gurin ibadarmu musamman sallah ya allah kaji tausayinmu
ReplyDeleteAmeen
ReplyDelete