Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Thursday, September 24, 2015

KALLO***DAYA-5

adsense here kallo-daya.jpg

KALLO DAYA
5


WANENE HYDAR?
Asalin sunanshi Aliyu hydar dana farko a gurin alhaji Mahmud Ahmad mai naira babanshi hamshaken mai kudi neh yana sana'ar shigoda motoci daga kasashen ketare ya mallake kamfanoni samada ashirin shi kanshi baisan iya adaden dukiyarshi ba mutum ne mai kyakkyawar xuciya,taimakon talakawa, da kuma marayu, Sabanin matarshi hajiya halima macece mai tsananin jidakai,izza, da kyamar talaka ta tsane talakawa batason kowa ya rabesu wannan kenan 'yan asalin garin kanone dukansu zamane ya kawosu a kaduna babban dansu hydar, hydar yaro ne dan kimanin shekara 30 dogone mai cikar zati da kamala farine tas yanada manyan idanuwa dara dara masu rikita 'yan mata ko yaushe a lumshe kamar maijin bacci yanada dogon karan hanci da lips masu kyau pink yanada kwantacchiyar suma mai kyau tamkar larabawan Ethiopia ,idan yayi murmushi kumatunsa sukan lotsa saidai hydar miskili ne na karshe da wuya kaga murmushinshi akwai tsare gida hydar kenan akwai farin jinin 'yan mata amma ko kallo basu isheshi bah hydar kenan yaro ga kudi ga kyau uwa uba ilmi yayi karatunshi a oxford uni dake london tun yana karami yake shaawar aikin soja gashi yanxu har yakai matsayin captin duk da karancin shekarunshi.kanwarshi daya mai suna munira kawar hanadi yayinda jafar da hydar suke aminan juna duk da halinsu ba daya bah kasancewar shi jafar akwai shi da surutu da barkwanci sabanin hydar.wanñan kenan .
09039016969 adsense 2 here
Share:

1 comment:

please after reading drop down your comment here!...

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *