Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, October 26, 2015

RAYUWAR***FAUZIYYA-30

adsense here rayuwar-fauziya.jpg

30RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (30). Fauzy karki
damu da yaddar ALLAH itama zata amince da
samun farin cikinki, kidena fidda rai da samun
farin ciki ko jindad'i ke dabance ALLAH
yanasonki kuma Mama ma zatasoki da yaddar
ALLAH, "Farouk ka amincewa maganata wllh
zuwa wajen Mama babu abinda zai haddasamin
sai tashin hankali da baqin ciki tare da bankwana
da kai, "Fauzyna kidena zubar da hawaye komai
ya wuce, na amince muje wajen Abban, don
ALLAH kidena tashin hankalinki kllm ina burin
naganki cikin farin ciki, haka muka dinga hira
cikin tarairaya da fahimtar juna. Farin ciki bazai
misaltuba cikin raina, haka nasanar da Aunty
Sadiya duk yadda mukai tayi murna sosai
tadinga bani hkr akan nadaure na koma wajen
Mama, kawai na amince mata da to amma badan
zan aikata ba, da yamma li'kis nai sallama da
Aunty Sadiya na tafi gidan Abba Tijjani cikin
tsananin farin ciki. Na sanar da Abba komai da
ya faru amma ban fad'a masa dalilin barina
gidan Fa'iza ba, kawai nafad'a masa nagaji km
Farouk yanaso yazo mutsaida maganar Aureyayi
farin ciki sosai da maganar Farouk amma yayi
takaici da baqin cikin halin ko inkula da Mama
take nunawa akaina, wanda har takai yau ta wayi
gari tana mai alfahari da salwantarki batare da
tasan inda zaki ba, Fauziyya tabbas bata kyauta
ba amma da kinyi hkr wata rana sai lbr, wllh
itace Mahaifiyarki baki da wata bayan ita, ina da
ikon Aurar da ke kota amince ko bata amince ba
amatsayina na wan Mahaifinki, amma bazanyi
hakan ba dole anemi amincewarta da sa
albarkarta, zanje wajenta bazanyi 'kasa
agwiwaba kuma insha ALLAHU zamu samu
nasara, ke tawace dolene nanema miki farin ciki
amma idan ta Haj. Khadija da sauran yaranne
idan nace nacire hannuna akansu ba wanda ya
isa yace sai na mayar, ki cigaba da addu'a
Fauziyya ALLAH yana tare da ke kuma shizai
dafa miki....... adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *