Friday, November 6, 2015
IDAN BAKI DAWO MIN DA ABINDA KIKA DAUKABA NA SAKEKI
IDAN BAKI DAWO MIN DA ABINDA KIKA DAUKABA
NA SAKEKI'
Tambaya ???
Assalamu alaikum Malam mutum ne matarsa ta
dauki abinsa, sai yace kodai ta dawo da abin data
dauka ko kuma ya saketa, ita kuma zafin wannan
maganar da yayi, sai tace bazata dawo da abin ba,
sai yace ya saketa, sai tace masa saki nawa, sai
yace konawa takeso, sai tayi shiru ba tace komai
ba, sai yayi maza ya shedama mahaifinta abinda
yafaru, da cewa yasata, ta maido da abin data
dauka domin ya warware kalamin da yayi, daga
qarshe ta maido da abin.
Malam matsalar anan shine matar tace ya saketa
amma shi yace bai sake tava Allah ya san zuciyar
shi, idan harta dawo mashi da wannan abun ,toya
warware kalamin sakin da yayi.
Matar ta tsayu akan sakine amma shi yace ba
sakine bane.
Mallam don Allah menene gaskiyar wannan
lamari ?
Allah yasaka da alkhairi.
(Daga Salisu Mahmoud).
AMSA:
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
Abin da yake daidai shine sakine, saboda niyya
bata da tasiri a saki, ana amfani ne da furuci
ma'ana (Abin da miji ya furta).
Sannan ya rataya sakin da wani abu, kuma abin ya
tabbata, daga baya kuma yazo ya furta, don haka
ta saku.
Allah shine mafi sani. adsense 2 here
Burodin ayaba
Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.
Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.
MAJNOON hausa love novels
Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more
Assalamu.alaikum malam wata matane take kuntata ma mijinta amma iyayensa suna ganin kamar laifin sane suna fushi dashi ganin haka sai ya kirata ya sanarda ita idan tabar wannan hali ya yafe mata amma taki bari saboda da taga mahaifansa na fushi dashi shin fushin nasu zai samu wannan mai gida?
ReplyDeletewlks mallam za,a kokarta a amsa [email protected],
ReplyDelete