Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, 12 December 2015

KAUNA CE SILA***10----17

adsense here kauna-ce-sila.jpg

[9:39PM, 12/9/2015] My 1: KAUNA CE SILA 2***10

MUHD-ABBA~GANA

INA karantawa nayi murmushi ganin salisu bai hanani mayar masa da amsa ba "NI BANYI RAWA BA nan take ya kara turomin cewa me yasa nace masa haka ko wani ya bata min raine a gurin sunan sai kuwa ya turo min cewa mai ya faru na bashi labari lokacin kuma har mun shigo layin mu muna kokarin sauka ban samu bashi amsa ba har muka zo kofar gida sai naga har ya kara turo min wani cewa waye ya bata min rai ne nace masa salisu ne lokacin ina kokarin shiga gida ina shiga na cewa umma yau naga ikon Allah na fara bata labari sai tace min tashi kije ki cewa salisun ya zo ina son ganinshi tare muka shigo bayan sun gaisa ta fara masa nasiha tana nuna masa komai hakuri ake yi a sannu ake bin komai a karshe tace masa mun san yanda kake sonta itama bata taba fada min aibunka ba ai ni kuwa ina cikin ina ci gaba da text yanxu kuma cewa yayi ban labari bara na kira ki ba ce a'a bani minti ashirin zan kira ka yace to bara na yi sallah nace to sai naji muryar salisu yana fadawa umma wai shin abin da yake bata masa rai nafi ganin mutuncin wani da shi sannan wancan yafi shi iko da ni na san umma ta gane mai yake nufi amma sai tace ka yi hakuri mu bamu san kowa ba idan Allah ya yi kaine mijinta babu mai iya hanawa tunda tana sonka yace umma na gode tare muka fito sauri nake yi so kawai nake yi ya tafi kafin na raka shi na dawo har yaya ya kara yin text cewa ya idar nace ina zuwa wani yaro na bawa kudi ya siyo min kati ina sakawa na hau kira ai kuwa yana shiga ya dauka ko gaishe shi bai bari nayi ba ya fara tambayata wai me ya faruMUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz
[8:50PM, 12/10/2015] My 1: KAUNA CE SILA11


MUHD-ABBA~GANA


NAN kuwa na saki baki na fara zayyano masa abin da ya faru tun zuwan mu gidan suna har rabuwar mu da shi yayi dan shiru yace to wai shin wannan me yake so a yi masa ne? nace waya sani bai kara cewa komai ba yace ina zuwa bara na tayar da inji na ji an dauke wuta sai na ji ya kashe wayar na zauna ina jiran ya dawo ya kira ni shiru ina zaune wajen minti ashirin bai kira ba kawai sai na koma daki na fara cire kayan jikina ina shirin kwanciya na nufi bandaki dan watso ruwa ina dawowa naga miss call din shi ina kira naji har ya kashe wayarsa amma ba haka raina yaso ba haka dai na kwanta da tunani iri-iri da safe bakwai da rabi ina makaranta ban shiga aji ba ina zaune a bayan aji da handout a hannuna da alamu shirin karatu wajen takwas sai na kira layin shi sai naga ya katse na sake kira naga ya kara katswa ganinda ganga yake katsewa sai na shiga rudu sai kuma na fara yiwa kaina fada to me yasa nake kiranshi tanzu ai dai nasan yana da mata koh a kuma ai ba halina bane kiran mutumin da na san yana da aure in har yana gidansa kawai sai nayi tsaki naji hawaye ya zubo min daya zuciyar tace to ai kar dalilin abin da ya faru ya sa ya kyale ki tunda bai ce miki komai ba sai kawai na yi masa text SALAM DA FATAN KUN TASHI LAFIYA YI HAKURI NAGA JIYA NE BAKA CE MIN KOMAI BA NASAN DAI YA KARANTA AMMA BAICE KOMAI BA kawai na yi shiru can na kara tura mai DON ALLAH KAR WANNAN DALILI YASA KA RABU DANI WALLAHI DAN KULANANI DA KAKE YI NE YASA NAKE JIN DADI DON ALLAH KA JI TAUSAYINA KARKA BARNI,nan ma dai baice komai ba kuma nasan ya karanta kawai sai na shiga aji na zauna jiran malami haka na wuni ranar babu kuzari wani abin mamaki hankalina yafi tashi da yaki daga wayar akan abin da ya faru tsakanina da salisu don don bacin ran salisu bai daga min hankali ba har na bar studio babu kira ba text.

MUHD-ABBA~GANA

www.abbagana.pun.bz
[8:54PM, 12/10/2015] My 1: KAUNA CE SILA 12


MUHD-ABBA~GANA

WASHEGARI daga makaranta gida na wuce don bamu gama da wuri ba kuma ma dai bana jin dadi ko aikin bana ji zan iya ina zaune a gida salisu ya kira wayata ina dagawa ya fara magana kamar haka: haba mamaa yanzu ke dama haka kike meye dalilin ki na fadawa ahmad abin da ya faru tsakaninmu nayi shiru abin ya daure min kai au yaya fada masa yayi na fada masa,sai nayi kuka ai daga ni sai ke saboda haka ke za ki fada masa nace ni fa fada masa nayi don yayi maka nasiha sai yace ai ni yanzu ba zan aaiya rabaki da mutumin nan ba abin naku sai addu'a yanzu dai ina son ganinki idan kin fito nace yau ban fito ba yace to zamu hadu ai na riga shi kashe wayar nan take naji wani mugun bacin rai wato yaya ya nuna masa baya sona kenan in ban da haka yaza ayi na fada maka magana kai kuma ka kwasa ka fada masa nima dama ni nasan yaya ba sona yake yi ba nayi wani mugun tsaki na wullar da wayar gefe nayi fitcewata makota washegari ina makaranta sai marwan ya kira yace min ina makaranta ne nace eh yace yazo kusa da mu ne bara ya shigo nace masa sai ya shigo bayan kamar minti goma sai ga shi bayan mun gaisa na fara fada haba marwan yaya dan baya sona kuma daga fada masa abu sai ya fadawa salisu gaskiya ni ban ji dadi ba kuma bai kyauta min ba yace tsaya kiji sauran mamaa wallahi ahmad ya kira salisu ne dan yayi masa gargadi furucin da yake akan ki ce min yayi yaza a yi ya bari s cuceki kina matsayin mai kaunar sa,.


MUHD-ABBA~GANA

www.abbagana.pun.bz
[8:10PM, 12/11/2015] My 1: KAUNA CE SILA
2-16MUHD-ABBA~GANA
tace wai wasu ne naji suna zancen ki in har ana so a ga bacin ranki to a taba ahmad nayi dariya kawai tace to ko saurayin kine? na kuma yin dariya nace mata abin da kika hi haka ne amma ba saurayi na bane din nasna yan matansa shi maya san saurayin bane din nasna yan matansa shi ma ya san saurayi na ina fatan kin gamsu tace na gane wata rana ina gurin su yaya ina ciki su kuma suna waje sai wani ya shigo ana ce masa usman sai ya kalleni yace au ashe kina ciki ai tun dazun muna can mutumin muna ta shan hira sai nayi murmushi yace kin san matarshi ta haihu a firgice na juyo nace yaushe yace au bai isani ba dazu da safe ta haifi namiji ban san dalili ba naji wani bacin rai amma sai na tattaro dariya nace Allah ya raya ban dade sosai ba a gurin nayi gida wata zuciyar tana cewa ki masa barka wata tana cewa ai bai fada miki ba can wata zuciyar tace ai yasan dole zaki ji nan take dayar zuciyar ayi tasiri a kaina na ce meye nawa na bacin rai ma waya ta na jawo na fara yi masa taxt kamar haka: ALLAH YA RAYA AHMAD YASA HAFIZIN ALKUR'ANI NE abin da yasa na rubuta masa haka saboda nasan ba sunan da yake burin sakawa sai irin su nansa takwara zai yi wa kansa ai kuwa yana karantawa yayi min reply da AMEEN a bakin marwan naji baya gari sai na kara shi au baka gari yace eh nace yaushe zaka dawo yace kwana biyu zan yi ban yi niyayr zuwa barka ba sai dai na so ya zo idan mun hadu sai na masa barka .
MUHD-ABBA~GANA

www.abbagana.pun.bz
[8:19PM, 12/11/2015] My 1: KAUNA CE SILA
2--17MUHD-ABBA~GANA


siyayya sosai na yiwa yaro koni kayan sun birgeni sai na kira shi an ce wai yaushe zaka dawo sai yace zan dawo ai kafin muyi sallama sai cewa yayi baza kije ki ga dana ba ko sai nace zanje amma nayi mata barka ta waya muna makaranta husna ta kira ta sai ta bani yace okk nace amma zanje yace ya kamata kije nace insha Allah mukayi sallama da safe ina aji husna ta shigo nace mata ban yi niyyar zuwa barka ba amma yayana yace ba zani ba kenan zuwa yake so nayi kuma kinga tana gidan su sai tace ai yafai ki sanin tana can yace kije saboda hakas hiryawa kawai zakiyi muje mamaa gaskiya mutumin nan yana ji dake wallahi a mawaka ku mata nasan ba wadda zai ce taje ai naje gidan jiya da daddare nayi dariya nace haka dai kika ce mu bari gobe in mun bar makaranta da yamma sai muje tace Allah ya kaimu haka kuwa muka yi lokacin da muka shiga gida aka nuna mana dakin da zamu shiga bata ciki mun tarar da wata a dakin itama da alama harka taxo ita ma mun gaisa sai muka ji sallamar matar yaya husna tace au fita kikayi tace a'a ina can dakin na waje wani abokin babansa ne yazo barka sai ta miko min yaron muka haisa wani ikon Allah ina kallon yaron wata kmar yaron ta shiga raina wani abin mamaki kamar kaki yayi dan ba abin da ya raba su kamar har ta bacci ina cikin tunani naji muryar husna tace min ki gyara shi nace mata zoki gyara min shi kin san ban iya daukar yara ba kafin husta tayi magana matar yaya tace ba wanda zai gyara shi kar ku taba shi ai danta ne tasan yanda zata yi dashi.

MUHD-ABBA~GANA

www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Share:

1 comment:

please after reading drop down your comment here!...

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *