Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, 16 December 2015

KAUNA CE SILA***2****21-22-23-24 & 25

adsense here kauna-ce-sila.jpg

[11/20, 8:36 AM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA21


MUHD-ABBA~GANA
SAI TACE E ina ma da kanne amma idar da sallar nan ki fada min ya akayi kika sanni haka ina jinta na tayar da sallah ta ina tayar da salla suma suka mike dan yin alwala na rigasu idarwa ina addu'a wasu kannen na makaranta suka shigo ina ta kokarin kar ta fadi sunana amma suna karasowa daya tace la yaya mamaa yaushe kika zo ina wuni ai kuwa zakiya ta juyo ban ma san ta idar ba sai naji tace a samu a addu'a mamaa nace ba sunana kenan ba sa'adiya sunana tayi dariya kawai ba mu kara cewa komai ba na fara gyara fuska ta dan shirin tafiya na tashi sai naji tace min to hajiya mamaa yanzu sai ina sai naji ta fara karantomin sunayen studios sai data ambaci wajen guda shida nace mata nifa ba waka nake ba gida zan tafi tace to bara mu tafi tare da muka fita gate ina so na gudu nayi tafiya to amma naga sai jana da hira take ta ce zo muje can mu dan zauna mu jira wannan kawata ta dauko abu a nex nace mata toh muka zauna ta fara yi min hira tace min ai dama nima wakar zan fara ahmad ne ya hanani wai sai mu tare a waka gara dai kar na fara nace Allah sarki ai yana sonki ai sai naga yayi dariya tace min haka ma watarana naje gurin kunshi naji wata tana ta yin karya wai ita ce zakiyyar da ahmad yayi ama waka nace lallai kuwa kina zaune ai da nice cewa zanyi karya ne gani nan tayi dariya tace kallonta kawai nayi sai nace mata yauwa wai dan Allah me ya hana ku yi aure ne sai tace Allah ne bai yi ba bayan yayi aure cewa yayi ai ba zan dade ba nima zai aureni to da gaba ma sai naji abin ya fara fitar min a rai amma dazu ma sai da ya kira niyace min mun shiga jarrabawar ne na ce masa yanxu zamu shiga yace Allah ya bada sa'a nace ameen"
www.abbagana.pun.bz
[11/20, 8:51 AM] Ábbä~Gåñā KAUNA CE SILA 22


MUHD-ABBA~GANA


NACE Allah sarki tace mu nan muna addu'a Allah yai mana zabi mafi alkairi nace mata amin kawarta ce ta karaso muka mike muka yi titi tare na ce mata bara na hau anan tace a'a dan Allah ki bari sai munje babban titi nace mata ba damuwa muje muna tafiya ita da kawarta suka dinga hirar yaya suna dariya dayar tace sai na tuna ranar da ya zo ya kwashe mu ya kaimu yahuza suya wai muna fitowa ya watsar da mu a gate ai babana bashi da dama nace ai shi ba ruwan shi ina ganin shi amma gaisuwa ce kawai take hada mu dashi ita ma ba sosai ba ban kuma cewa komai ba amma zuciya ta ta cika da tunani da kuma tambayoyi masu yawa a haka ta tsayar min da abin hawa na hau na bar su a nan na nufi zoo road lokacin da na zauna a studio duk sai naji raina ya baci ban san dalili ba na fara tunane tunane to ni yanzu da take min hirar shi da naga dama na nuna mata irin text din da muke yi fa tunda ko yanzu sakunan shi zasu iya kai dari a wayata kuma ai ko bana soyayya bane kawai nuna kulawa a ciki sannan ko zagina yake kudinsa yake kashewa ai wani mugun tsaki naja na zaro wayata wadda muke yin text da ita kawai na kashe dan haushinsa nake ji kuma wai sai na fara tunanin ko na bashi labari ko nayi shiru ina ta rabe-rabe zuciyarta dan ta gargadeni kar na fada tayi rinjaye a fili kuwa cewa nayi to idan na fada masa meye ribar ai dama nasan budurwar shi ce kuma zai ga na fiya korafi haka dai na hakura har muka bar gurin aiki haka kuma ban kunna waya taba.

www.abbagana.pun.bz
[11/23, 7:48 AM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 23


MUHD-ABBA~GANA


WASHEGARI ina fita nace bara na kunna ai na fara hucewa ina kunnawa sakon shi ya shigi ZAKIYYA TACE KUN HADU ina dubawa naji wani bacin rai wato ita har ta fada masa kenan nima sai na fara rubuta masa kamar haka TO DA TACE MAKA MUN HADU NICE MATA NAYI NA SANKA KOME sai ya kara turo min haka ba wani abu bane ta dai ce min kun gaisa haka dai muka yi tayi ina tura masa yana bani amsa amma fa ni da zafi nake tura masa a karshe dai kawai ya kira ni yace min wai meye haka ne? nace to ai gara na fada maka yanda mukayi da ita yace to ina jinki nan na zayyane masa yanda mukayi da ita sai naji yace ni dai ta kirani tace min mun hadu da budurwarka mun gaisa sai kuma jikina yayi sanyi amma ban daina jin haushina ba kawai na kashe wayata nace lallai budurwarsa fa yace, sai kuma wata zuciyar ta cemin to idan ita ta ce masa budurwarsa shi kika san amsar da ya bata nace hake ne fa kuma ba muyi text a kwana biyun nan ba amma ni dai ban daina tunanin shi ba ban dai yi masa text ba sai dai yanzu ina yawan zuwa gurin su wani lokacin idan na gama aiki sai in zauna muyi ta hira da asma'u sai daga baya na tafi gida kona koma gurin mu in lokacin tafiya bai yi ba mun ci gaba da yanda mukeyi da yaya dan yanxu abin ya fara yawa kusan kullum muna tare wajen tura sako ko ni na fara ko shi yanzu na zama aminiyar yaya domin baya shakkar fada min masoyansa haka makiyansa musamman yan harka irin ta mu wani ikon Allah duk mtumin daya fada min shi a take nima zanji na tsane shi mafi yawan lokuta ma wa'yanda baya shiri dasu ni dama ba shiga harkarsu nake yi ba,


www.abbagana.pun.bz
[11/23, 8:04 AM] Ábbä~Gåñā KAUNA CE SILA 24


MUHD-ABBA~GANA


A bangaren waka ta kuwa cigaban da na samu sai godiyar Allah don yanzu nima har nayi wakar data fara bin gari inda mukayi da matashin mawaki da yanxu da alamun tauraruwansa zata haska amma kuma ni da alamun yanzu wakar bata gaba na don nafi damuwa da al'amuran yaya kuma text din shins abinda nafi bawa muhimmanci fiye da komai ranar wata litinin da yamma na gama aikina a gurin su yaya na fito zan tafi gida lokacin sanyi ne amma nayi kyau ba laifi na fito sai muka hada da asma u tace min tafiya zakiyi bara na xo na rakaki bakin titi muna tsaye muna hira da ita a titi wadda duk hirar yaya ce ita ta matsa dole tana san sanin tsakaninmu domin taga ko zuwa nayi guri bamu cika magana ba to a ina muke murunci na bude baki zan magana daga kan da zanyi na hango yaya zai yi hanyar gurin su kai masha ALLAH gaskiya yayi kyau wata irin rigar sanyi baka ya dora akan kayan shi wani irin kallo yaya yayi min a take naji zan suma tab dama haka yaya ya iya wani irin kallo gaba na dai bai daina faduwa ba nace asma u sai da safe sai mun hadu gobe tace Allah ya kaimu haka na hau adaidaita domin ina jin kafata bazata iya daukata ba lokaci da naje gida daf magariba har nayi salla bani da kuzari na kuma rasa me take damuna wayara na dauka ina ta karanta sakonninshi ina jin wata irin kewa tare da nishadi gashi ina san ganin yaya amma bana iya yi masa magana kallon ma bako yaushe nake iyawa ba amma fa idan na gan shi ina jin dadi abin mamaki ranar kuwa baiyi min text ba nima kawai sai na hakura na kwanta haka daibabubuwa suka ci gaba da tafiya yin text din mu kullum ci gaba yake yi aikina ma haka na ci gaba da gudanar da shi haka sauran harkokin da mukeyi haka mutane basu daina sanya ido a kaina ba,


www.abbagana.pun.bz
[11/23, 8:38 AM] Ábbä~Gåñā KAUNA CE SILA 25


MUH'D-ABBA~GANA


WASU kuma yanzu da shi suke fakewa ko abu suke so nayi musu musamman amshi sai azo kusa da ni a yi ta yabon halinsa shi ko shi wanda yake so nayi masa aikin yayi ta nuna min suna mutunci da yaya ni dai haka nakan ji su amma kuma ina yi musu aikin da misalin karfe tara na dare a kwance nake ina ta yan tunane-tunane sai naji waya ta tayi kara alamar shigowar sako ba wayar da muke yin text da yaya ba tawa ta ainihi ina budewa naga wata sabuwar lamba dan bani da ita a wayata na fara karantawa NI WANI MUTUM NE DA ZUCIYA TA TA KAMU DA SONKI,NA RASA YA ZANYI NA GAYA MIKI AMMA DAN ALLAH KI TAIMAKA MIN DAGA MASOYINKI ina gamawa nayi banza da abin dana gani saboda nasan mu irin mu muna samun masu mana iri wannan nace aikin banza mutum bai sanka ba yace wai yana sonka ina ta fada kamar yana kusa da ni sai naji shigowar wani A FUSKARKI KAMAR AKWAI TAUSAYI DA SANIN CIWON SO DON HAKA KI DUBE NI INA JIRAN AMSA.dariya nayi nace ikon Allah ban kuma ji ina son bashi amsa ba alamar shigowar wani na kuma ji DON ALLAH KICE WANI ABU KO YES KO A'A kafin nayi tunank yin wani abu naji wani ya kara shigowa KIN BANI MAMAKI DA KIKA SHARENI BAN ZACE KI A HAKA BA,wayar tawa na kashe kawai nayi kwanciya ta dan bana san bashi amsa saboda ni ban san waye ba da safe ina tashi wajen takwas na safe sai ga sakon mutumin jiya na fara karantawa SALAM AN TASHI LAFIYA GOOD MORNING DAN ALLAH KO ZAGI NE KIYI NASAN KIN KULANI ganin zai takura min sai na yanke yi masa gargadi don ya daina kulani ga abin da na rubuta masa kamar haka: NI MATAR AURE CE KAYI HAKURI INA DA AURE.

www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Share:

1 comment:

please after reading drop down your comment here!...

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *