Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, 16 December 2015

KAUNA CE SILA****2***31-32-33-34 & 35

adsense here kauna-ce-sila.jpg

[3:01PM, 12/16/2015] abba gana: [11/27, 8:24 AM] Ábbä~Gåñā KAUNA CE SILA 31


MUHD-ABBA~GANA

HAKA dai abubuwa suka yi ta faruwa a yanzu kuwa ko nishadi nakeyi idan na tuno yaya ya nuna min muhimmancin matar nan sai naji bacin rai duk da bamu daina yiwa juna text din da mukeyi ba wataran ina shihowa daki sai naji waya ta na kara na dauka na saka a kunne ashe ita ce ban gane ba dan bani da ita sai naji tace mamaa kin san meye yau ga ahmad a gidana sai naji gabana ya fadi na kasa magana sai tace bara su tafi zan kira ki to kawai nace mata na rigatq kashe wayar ma ban bari ta kira ni ba dan muna gamawa nq kashe wayata zuciyata tana ta zafi kar dai zargina ya tabbata to amma ahmad yana da ilimi ita kuma matar aure ce to wai me yake shirin faruwa da nine da irin wadannan tunane-tunane na kwanta.wannan abu ya haifar da tsana mai karfi tata a zuciyata dan a zahiri bana san naga ko wace mace ta rabi yaya ballantana kuma naga yana baki wani girma haka dai mutunci da yake tsakaninmu ya fara ja baya dan yanzu ko a hanya bana ganin ta lambar ta ma na goge a wayata shi kuma mukaci gaba da mu'amala kamar yanda muka saba yakan yi min maganar ta wataran idan na nuna naji haushin sai ya bar zancen wataran dai har na gaji nake ce masa ai ni ba wani abu bane yake bani haushi me yasa take yawan damuna da zancen ka?

www.abbagana.pun.bz
[11/30, 7:57 AM] Ábbä~Gåñā KAUNA CE SILA 32


MUHD-ABBA~GANA


kuma watarana ma har ta taba ce min kana da qualities to meye nata sai yace ai na fada miki yar uwarmu ce sai nace masa a yanxu kuka gane ku yan uwane ai oho ko ma dai meye ni na fada mata ba abin dake tsakanina da kai sai yace to Allah ya kyauta watarana sai yayi min wani irin text ban gane me yake nufi ba kuma sakon ya bani tsoro dana bude shi ,KAMAR BOKA DA MALAM SUNA SHIGA AL'AMURANA nayi kokarin ya fahimtarr da ni abin da yake nufi amma ban gane ba dan a karshe ce min yayi ai boka yana iya yin sihiri ya kama mutum da izinin Allah dan shi yake bashi dama nace haka ne amma ka dinga addu'a yace to in Allah ya yarda amma kema ki dinga tayani nace masa dama ina yi amma yanzu zan kuma maida hankali yace to bayan mun gama text din ranar ya barni da tunane-tunane to meye yake nufi kar dai yace ni nake masa asiri sai wata zuciyar tace haba dai ai dake kike masa ba zai fada miki ba ka har yace ki dinga masa addu'a a fili kuwa cewa nayi to ai dai nasan ban taba ba ko addu'a Allah yasa ya soni ma ban taba ba da wannan na samu karfin gwiwa na kwanta ranar lahadi ne yau da na tashi dama ina da niyar zuwa kitso dan a ranar ne bana fita bayan na gama komai kamar karfe tara na safe na shirya na tafi gurin kitso sai na bar daya wayar da muke yin text da ita a gida tana caji na tafi da daya a hannu ban dawo ba sai sha biyu saura ina dawowa naga alamun anyi min text sai na fara dubawa ina budewa sai naga yaya ne kuma kamar ma guda biyu ne sai nayi sauri na rufe na fara rubuta masa sako kamar haka: tun kafin na karanta nashin DAN ALLAH YI HAKURI YANZU NA SHIGO GIDA NAGA SAKONKA BARA NA DUBA, farin cikina gaba daya yana tattare ne da ita bani da burin da yafi ta nan duniya nan da can dare da rana


www.abbagana.pun.bz
[11/30, 8:14 AM] Ábbä~Gåñā KAUNA CE SILA 33

MUHD-ABBA~GANA


SAFIYA maraice ita idaniya ke san gani zuciya kuma ta narke wajen shauki da mararin ta ko ina nake sai in zata ita ce hasken rana,ina gama karantawa na fara duba na biyun SUNAN TA IN NAJI AN AMBATA NAKAN GIGICE KAI HAR NA GEFENA KAN FUSKANCI NA FITA DAGA HAYYACINA NA TABBATAR BA BOKA KO MALAM TSAKANI NA DA ITA BARI DAI TSABAR KULA CE KAWAI DA TAKE BANI KYAWUN DABI'U DA ALLAH YA BATA BAYAN KYAWUN SURA MARA MISALIN KWATANTUWA INA MA AKAN IYA JIN RUGUGIN DA ZUCIYATA TAKE YI YAYIN TUNA TA DA AN TABBATAR DA SAURAN KIRIS DA NAI KIRANTA TA BAYYANA AMMA SANNU SANNU DAI, to fah! ganin wannan sakon na yaya ba karamin rudani yayi ba to shi kuwa da wa yake haka wace yar baiwa ce ta samu wannan gatan haka ai kuwa sai na tambayeshi zara koh? wannan wacce yar baiwa ce? sai yace min ai zara tuntuni bana jin ta har a zuciyata bayan tayi aure sai nace masa ina nufin koka samu wata wadda kake tsananin sone dan nasan duk macen da kake so kana mata lakabi da zara sai yace a,a wani littafi nake rubutawa sai nace oh amma da dadi sai yace min ya gode amma a gaskiya ba yarda nayi bana dai ji shine kawai haka na zauna ina ta maimaita karanta sakwannin nan nashi guda biyu amma ban fahimci inda sakon ya dosa ba haka na hakura wata rana ina gida da yamma na dawo ban dade ba sai naji wayata tana kara ina dubawa sai naga ashe wani yaron yaya ne ke kirana ina dagawa muka gaisa sai ya ce ya kano sai nace lafiya kai baka kanon kenan sai yace ai jiya muka taho kaduna nace au tare kuka tafi jiya naji ance ya tafi kaduna sai yace E ai a zoo road muka hadu bamu kadai ba sai da kuma muka bita wajen kofar gidan Alhaji ado kin san meye?

www.abbagana.pun.bz
[3:01PM, 12/16/2015] abba gana: [11/30, 8:44 AM] Ábbä~Gåñā KAUNA CE SILA 34
MUHD-ABBA~GANA
nace a,a yace dama da budurwa ya hajj gidan nace E mana sai yace muna mota ta fito ta daga masa hannu wata yarinya nace eh mana mukayi sallama dan bana san na nuna masa ban sani ba amma ban san me nake fada masa ba bayan na kashe wayar sai nace innalillahi ashe da kanwarta ta hada shi kenan tunda ai gidan baban hajiya aina ne kai ni kam na shiga uku ya Allah dan sunanka kyawawa casa'in da tara ka yaye min son mutumin nan,haka na tashi nayi sallar magariba ina jin kunci a raina ina addu'a ina kuka Allah kasan kaunar da nake yi wa wannan bawan naka Allah ka yaye min dan alfarmar ma'aiki dan gatanka ina nan zaune har lokacin sallar isha"i yayi bayan na idar na kasa cin abinci kawai sai na shiga daki na nemi katifa na kwanta kamar jira na ake ina kwanciya naji alamun shigowar sako a wayar da yake min nace to shi ne zai yi min kome ina budewa kuwa yaya ne jiya da yau banji daga gareki ba lafiya ina gama karantawa nace ji wani abu kuma kamar kar na bashi amsa amma sai na ga ba zan iya ba dan koba komai ina ganin mutuncinshi ba kadan ba kawai sai naga ina bashi amsa kamar haka: lafiya klau ya kaduna kun dawo ne yana gama karantawa sai ys kara turo min haka: waye ya fada miki na tafi kaduna sai nace masa labari naji ai har bye bye din da aka maka ma a kofar gidan Alhaji naji yana ganin haka sai ya turo min wani wai waye ya masa sai nace budurwarsa ta gidan mana sai yace shi dai bai san zancen ba to ya sunanta nace ina zan sani amma dai sunanta basma sai kuma yace wallahi Alhaji bashi da ya mai wannan sunan amma kekin san tane? nace a'a nifa kawai shi kenan.

www.abbagana.pun.bz
[11/30, 11:30 AM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 35


Muhd-Abba~Gana
wannan ,amari ba karamin daga min hankali yayi ba yanzu kuma na daina tunanin zakiyya basma ce a raina dan ni na yarda budurwarsa ce sai sai ban san waye zai min gamsasshen bayani ba tunda wanda ya kamata ya bani yace bai san zancen ba haka dai aka bani da tunani ni kadai haka dai muka ci gaba da mutunci tsakanin mu dan yanzu turawa juna sako kuwa yanzu bamu da lokacin yi dan a rana sai mu tura wa juna kwaya talatin zuwa arba in dan idan muka fara tun yamma sai karfe sha daya zuwa sha biyu zamuyi sallama wani lokacin kuma muna tashi da safe zamu dora da hirar mu sai dai yanzu baya min zancen su hajiya ko dan yaga da gaske idan yayi min hankalina yana tashine ban dai sani ba mutane kuwa yanzu ba a cewa komai dan kowa fada yake soyayya muke yi wai ma dan ban taba fadawa kowa komai ba dan ni ban ni ban yarda soyayya muke ba to haka ake yin soyyaya mutum bai taba cewa ina sonki ba duk irin sakonni da yake turo min to ba ma wannan ba kofa gidan mu fa bai sani ba ni dai nasan ba haka bane amma mutane kamar wani abu duk sun saka min ido don wani abu wasu ma har cemin suke yi ta ahmad wasu kuma amaryar ahmad wani lokacin idan naji nakan ce musu ni ba saurayi na bane muna dai mutinci idan kuma naga abin tsokana ne sai nayi musu shiru wani abin takaici ma wani lokacin sai na nufo inda suke zama sai naji ana cewa ga mamaa ta ahmad shi dai naga baya cewa komai nice ma nakan ce bana so to ganin halin yaya ahmad idan baya san abu ba shi da tsoron bayyanarwa ina ganin shi ya bada damar daya sa mutane da dama suke ganin kamar wata soyayya muke yi a boye watarana ina studio muna aiki sai naga ana kirana ashe abubakar ne shima mawaki ne babba ya kan yi aiki dani lokaci zuwa lokaci sai yace min nazo gurin su zamu yi aiki nace ganinan zuwa bayan na gama aiki zan tafi sai ya tsayar dani yace yana san zaiyi magana da ni mun zauna ya na fuskantata ina gefe sai ya fara magana" gaskiya mamaa na dade ina sonki kuma so bana wasa ko na yaudara ba ina tsoron bayyanawa ne dan nasan a masana antar nan bazaki taba rasa masu sonki ba ni kuma kishine dani amma yanxu na yanke hukunci ba zan iya shiru ba ina so na tambaye ki tsakaninki da Allah kina da saurayi a cikin mawakan mu? nace masa a a yace to kin tabs soyayya da wani tunda kika fara waka? sai nace masa eh na taba da salisu nayi masa kwatancen shi yace na gane shi amma ai shi ba waka yake ba nace E kayan kida ne dai dashi yace to yanzu me ya raba ku na dan y shiru nace mun dai samu matsala ne yace to shi kenan yanzu na tambayeki a duk mawakan hausa dawa kike tunanin zaki iya soyayya har ta kai ku ga yin aure sai nayi murmushi nace daga kai sai ahmad sai yace ahmad saurayinkine? nace a,a saiyace to muga wayarki sai na mika mai waya ta da kowa yake kirana da ita ban sam me ya gani ba sai ya ce kika ce ahmad ba saurayinki bane nace E sai naga ya jawo tashi wayar yana duba wata lamba ina dan lekawa sai naga ashe wannan layin da ake min text kwanaki cewa ana sona ashe layin yayane kai a take naji wani gumi ya keto min nace au wai layin shine wannan wallahi ban sani ba sai yace hmmmm har kin ji dadi ko?


www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *