Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, 18 December 2015

KAUNA CE SILA***2***41-42-43-44 & 45

adsense here kauna-ce-sila.jpg

[12/2, 7:46 AM] Ábbä~Gåñā KAUNA CE SILA 41


MUHD-ABBA~GANA


NACE to Allah ya yarda akanan biyun nan na zama shiru shiru dan mutuwar marwan ta taba ni ba kadan ba haka dai muka je gaisuwarsa gidan su tare da asma,u Allah ka jikan musulmi,amin mutu war marwan ta kara sani naji hakuri da yaya shi ya dace dani dama ga yanayin da muke cikinyanxu ba wani shiri muke yiba ya rage yi min sako nima haka,wata safiya na fito sai na fara zuwa gurin su asma,u zanyi wani aiki bayan na fito sai naga wani D abokin nan nashi sai na gaishe shi sai yayi dariya yace jiya ai munyi waya da yayanki lokacin yana gidan Alhaji yaje zance sai naji wani abu amma na dake na ce masa E hakane kawai saina koma ciki kaina banji dadi ba nan da nan kuwa na fara rubuta masa sako na korafi jiya wato zance yake ko sai ya turo min sakon cewa dama yanzu kishi zai iya damuna ai shi ya dauka zuciyar da take dauke da jimami da rashin ganin irin yanda nake ciki bai kamata na tuna kishi ba ai kuwa ya fargar dani dan yanda nake da marwan bai kamata ace har na fara mantawa ba.

www.abbagana.pun.bz
[12/2, 8:01 AM] Ábbä~Gåñā KAUNA CE SILA 42


MUHD ABBA GANA


AI kuwa jikina yayi sanyi kuma naga rashin dacewar abin da nayi na kuma yi alkawarin zan yi kokari na rage nuna kishi na musamman a irin wannan lokacin bayan kamar wata uku zuwa hudu komai ya lafa mun koma kamar yanda muke amma bbu batun manta marwan sai ajizanci na dam adam wanda kusan ko yaushe muna masa addu,a da fatan Allah ya sa duk musulmi su cika da imani tafiya ce ta same ni zanje jos biki kuma nasan zanyi kamar sati daya ana gobe zan tafi ina gurin su yaya sai na cewa asma u ga amanar yaya na nan duk abin da yake so ki siya mishi idan na dawo kiyi min lissafi tayi dariya tace to ranki shi dade an gama nace mata kinga ganin wasa nake ko to da gaske nakeyi ita dai dariya tayi muka rabu nayi hanyar fida washegari muka dauki hanyar jos ban kunna wayar da muka saba tura sako ba dan bana so na fada masa nayi tafiya tunda bamu saba haka ba sai da naga muna shirin fita daga kano sai na kunna ai kuwa sai ga sakon gaisuwa naji dadi nan nima na tura masa da kuma godiya bamuyi sosai ba mukayi sallama lokacin da naje jos kusan kullum muna tare a waya wajan tura sako amma ban taba karmbanin fada masa bana kano ba shima kuma bai tambaya ba don nasan bai taba kawowa ba idan kuma ina san jin labarinsa sai na kira asma u mu sha hira nayi dariya nakuma ji dadi dan gaskiya babu irn hirar da take min dadi da kuma saka ni a nisahadi irin hirar shi wannan karan ma naji dadin zaman jos dan garin akwai dadi nafi kuma sakewa dan yanzu ina cikin nishadi da kuma shaukin so bani da aiki sai tunanin yaya da na samu kaina a ciki nishadi ko wani guri mai kyau sati daya naji na juyo kano ta dabo

www.abbagana.pun.bz
[12/3, 7:13 AM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 43


MUHD ABBA GANA

BAMU baron garin jos da wuri ba saboda haka bamu samu isowa da wuri ba sai wajen goman dare ina sauka na kira asma'u muna hira nace mata ya akayine? tace min ai dazu da yamma mutumin yace min yaje vocal amma bai ganki ba nan take naji wani farin ciki ya rufeni duk da nasan ba wai nemana yaje ba amma dai har ya lura bana nan jin hakan ne yasa kudiri niyyar gobe in Allah yaso ko ina yake sai naje ko da wucewa ne nayi ya ganni dan na fuskanci ida yayi kamar sati bai ganni ba zai zo ta gurinmu da safe ina fita a gurin mu na zauna ina gamawa na wuce gurin su ina zuwa wani takaici ban ganshi ba kai gashi nayi kyau sosai dan wata doguwar riga yar maroko na saka ta zamani wadda bata cika gari ba wasa-wasa har biyar saura ina ta raba ido ban ganshi ba ban ga asma'u ba sai nace bari dai na kira ta naji tana dauka tace kina ina ne? nace ina studio kefa? tace ina gidan hajiya gani dasu mutuminki ga DD ana rihasal ki taho dan Allah nace mata anya kuwa to nazo nace me? sai tace ke dai kizo mana to dama ni abinda nake jira kenan ba dai nasan nuna mata ne nan da nan na nemi abin hawa naje gidan ina kofar gate din na kirata nace ta fito bayan ta fito tace kai! kinyi kyau lallai kam nayi dariya nace tsokana ko tace a'a gaskiya dai nace mata nifa kunya nake ji to idan na shiga nace me ya kawo ni? tace kema dai wallahi sai kace wata bakuwa nace D ma yana ciki ko tace E mana,


www.abbagana.pun.bz
[12/3, 7:37 AM] Ábbä~Gåñā KAUNA CE SILA44


MUHD-ABBA~GANA

NACE nasan ma abin da zanyi muje kawai tana gaba ina biye da ita gabana sai faduwa yake a wani office muka same su yana dagowa muka hada ido dashi nayi sallama sai kuwa ya dauke kai yaci gaba da karanta wata jarida dana samu a hanunnshi ban kula shi ba nace wa D ina son printing na CD kawata ce zatayi aure nayi mata waka sai yace ki kawo zanyi miki nace to na fita harabar gidan a inda nan ake yi rihasal din na samu kujera na zauna sai kuwa kida ya fara tashi wa'yanda zasu yi suka fara fitowa wanda yaya na ciki asma,u ce mai yi musu amshi suyi waka amma kowa daya bayan daya zai yi tashi yaya ne ya fara tashi sai na dinga jin wani iri dan kamar dani yake a cikin amshi shinyar yana cewa "zahiri da badini na baki mallaki na wani iri na dinga jin kai ina ma yaya yana sona kamar yanda nake sonshi gaskiya duk duniya daba macen data fini dacewa dan yaya ya hadu ta ko ina wani irin kallo yayi min da ban taba ganin anyi wa wani irinshi ba ashe har ya gama ina ta tunani yazo ya wuce ta kusa dani ban dade ba bayan fitar shi nima na tafi haka dai muka ci gaba da bawa juna kulawa musamman ta hanyar turawa juna sakonni na caring wani abin mamaki yaya bai kara ce min ina sonki ba ko yace min I LOVE YOU amma muna hira sosai idan muka fara bama gamawa sai dare wataran ma muna tashi zamu dora a inda muka tsaya jiya watarana kamar misalin takwas saura na dare sai naji shigowar sako naji wani dadi dan na san nashine ai kuwa nashin ne sai dai abin daya rubuto min ne ya firgitani: IDAN ALLAH YASO SABUWAR SHEKARA MAI KAMAWA ZAN YI AURE.


www.abbagana.pun.bz
[12/3, 7:52 AM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 45


MUHD-ABBA~GANA


numfashina ne naji yana neman daukewa a take na karanta innalillahi wa inna ilaihi raji un kafin na samu ikon mayar masa da amsa, DAN ALLAH WA ZAKA AURA? KUMA YAUSHE ZAKA YI? ina tura masa naji wani hawaye mai dumi ya biyo kumatuna nace Allah ka zama gatana na goge na jawo filo kawai na kwanta dan ko tashi bana jin zan iya ai kuwa sai naji shigowar amsar sakona ; SUNANTA MARYAM A ABUJA TAKE, nan na tambayeshi iyayen ta masu kudine ko sai yace min shi kwadayayye ne ko nace ba haka nake nufi ba naji dai yace abuja ne kawai sai naji wata dariya ta zo min na tura masa sako: SHI KENAN ALLAH YA KAIMU YA SANYA ALKAIRI DAMA NIMA WANI MUKTAR YANA SONA ZANCE YA FITO MUYI AURE, sai yace min to kina sonshi ne sai nace a,a amma in har zaka yi aure nima ya kawai zanyi sai ya turo min haka: KIYI DAI ADDU'A DAN GUDUN DANA SANI ALLAH YA ZABA MIKI MAFI ALKAIRI
nace masa amin kawai na kashe wayata wani kuka ne yaxo min mai karfi ranar ni kaina naji tausayin kaina haka bacci ya saceni ina tashi da sassafe na fara kiran layin asma,u nace mata wallahi tashi duk dan da ya hana mamansa baci shima ba zaiyi ba muryar tada bacci tace me ya faru nace mata aure yaya zai yi tace kai mamaa gaskiya ba haka bane sai dai wasa yake miki nace maganar sa babu wasa asma,u ni dai kawai ki tambaye shi kiji sannan ni ku daina hada ni dashi tace kiyi hakuri ki daina kuka bara an jima zan kira shi nace mata sai anjima ban san yanda suka yi ba bata kira ni ba nima ban kira ta ba amma hankalina yana gurin ta ina ta so naji yaya suka yi ina fitowa ban dade ba Allah ya taimaka sai aka kirani gurin su ina zuwa muka hadu da ita tace dazu na kira wayar shi bai daga ba amma nasan yanzu zaki ganshi.


www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *