Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, January 1, 2016

NA DAINA SO!! 11 & 12

adsense here na-daina-so.jpg NA DAINA SO 11 Muhd-Abba~Gana shin hakan na nufin duk tsawon shekarun da aka shafe baya gudanar da rayuwarsa cikin walwala da jin dadi? miramu ta tambayi kanta ko dai al'amura sun sauya? ganin har karfe sha biyu rana bai iso ba yasa ta yin tunani ko sai wajen azahar zai iso tana da tabbacin cewa yanzu yana ciki mota akwai nisa sosai tsakanin kauyen da birni don sai an ratsa ta tsakanin wasu dajijjika kuwa hanyar akwai kwazazzabai don haka duk wanda ya bi ta hanyar dole ya gaji koda kuwa a cikin mota yake tafiya bayan da tayi wannan tunanin ne ta tanadarwa mijin nata ruwan wanka zama tayi a kan kujera ta ci gaba da jira tana mamakin irin tunanin da mijin nata keyi a halin yanzu ,WACE CE MARIYA?? an haifeta marainiya a cikin wani kauye mai suna kantafarfara mairamu ta taso a gaban mahaifiyarta wacce itama ta rasu sa ilin da take shekaru shida a duniya wata kanwar mahaifiyarta ce ta rike ta har ta girma a gabanta mallam nasiru malami ne mai almajirai shahararren mutun ne a fadin kauyen sunan matarsa dije mutane ne masu mutunci da girmama jama'a kusan kowa a kauyen yana kaunarsu sune suka rike mairamu cikin aminci da rashin nuna wariya a tsakaninta da sauran yayan ukun da suka haifa. NA DAINA SO! 12 Muhd-Abba~Gana wannan ne dalilin da yasa da yawa mutane ke zaton cewa su ne iyayenta na asali kabir shine babban da ga mallam nasir sai kuma kannensa mata guda biyu rukayya da zainabb rukkayya itace sa'ar mairamu don haka suka taso kawaye kuma aminan juna kusan komai tare suke gudanarwa saboda ko yaushe suna tare da ba don bambancin tsayi da kyaun fuska da mairamu tafi zainab ba to da babu abin da zai hana a kira su da suna tagwaye sun samu kyakkyawar tarbiyya irin ta addini islama kusan kowa na kaunarsu a duk fadin kauyen babu makarantar boko wannan ne dalilin daya sa basu samu ilimin zamani ba a lokacin da suka zama yan mata ne aka soma rububin su (kamar kayan gwanjo) kowa na burin ya samu mace ta gari musammanma mairamu domin Allah yayi mata farin jini fiye da yadda aka saba gani a kan sauran yan mata don ita har daga makwabtun kauyuka ake zuwa neman aurenta attajirai da yayan attajirai shahararrun manoma da mafarauta har izuwa kan yayan masu rike da sarautun gargajiya duk sun yi takara wajan neman aurenta amma ita mairamu tuntuni tayi nata zabin.....dogo ne siriri baki mai dan faffadan hanci baya ga kama a zahiri daya yi da mahaifinsa ya gado mahaifin nasa wajen kyawawan dabi'u musamman ta fuskar zamantakewa da jama'a. MUHD-ABBA~GANA www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Share:

1 comment:

please after reading drop down your comment here!...

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *