Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, January 15, 2016

NA DAINA SO!! 39 & 40

adsense here na-daina-so.jpg

NA DAINA SO 39



Muhd-Abba~Gana


take tattara tufafinsa wadanda suka yi datti ta wanke masa ta tuna irin yadda take tarairayar mijinta irin yadda take ji da shi kamar tsoka daya a miya amma kuma......... sauri tayi ta dafe gefen kanta sakamakon ciwon da ya soma yi to amma ba yadda zata yi ta hana tunane-tunane kutsawa cikin kwakwalwarta tun bayan yin bikinsu da watanni shida yusuf ya hadu da wata irin rashin lafiya mai zafin gaske kusan duk wani abu da mairamu ta mallaka sai da ya kare a hanyar nema wa yusuf magani akwai wata gona da ta gada daga wajen mahaifinta mutumin da bata taba gani ba saboda ya rasu ne kafin a haifeta har gonar sai da ta sayar don ganin mjinta yusuf ya samu lafiya sannan kusan komai ita take yi masa sakamakon tsamarin da rashin lafiyar tayi sai dai a kwantar a tayar daga karshe dai ya warke daga cikin kashi uku na kudin gonar kashi daya ya tafi a kudin magunguna kashi daya kuma ya salwanta a kudin abinci da kayan cefene yayin da kuma taba shi kashi daya ya ja jari mairamu bani da kalmomin da zan iya amfani da su wadanda zasu iya biyyana hakikanin irin farin cikin da nake yi da Allah ya bani ke a matsayin mata abin da kawai na sani shine ina daya daga cikin wadanda sukayi dacen samun mace ta gari kuma ina yi miki godiya a bisa kokarin da kikeyi min Allah ya saka miki da alkairi shin mai kike so a waje nâ?


Muhd-Abba~Gana





www.abbagana.pun.bz

NA DAINA SO 40






Muhd-Abba~Gana





kayi min alkawarin cewa har abada zaka rike amanata wannan ne kawai burinki? kwarai kuwa na sha yi miki alkawari kuma ina mai kara jaddada miki cewa you are the one and only one' i love you more (kalmar wani i love u karyane injini) shi duk ire iren wadannan kalam da yusuf ya sha fada mata kanzon kurege ne? mai yasa zai yi mata haka ? kudin da ta bashi da shi yayi kasuwanci har kasuwancin nasa ya bunkasa ya yanke shawarar zai je birni ya nemi wani aiki sannan ya ci gaba da bunkasa jarinsa watakila da yaje jarin nasa ya bunkasa watakila a cikin jarinne har ya samu ya auri surayya daga bisani sai data nemi wannan mujallar ta karanta a boye duk da ta san cewa yin hakan ba karamin karin takaici da bakin ciki ba ne a gare ta abin dayafi dugunzuma tunaninta lokacin da dan jarida ya tambayi yusuf cewa shin ya taba yin aure? ban taba yin aure ba!! kuma ba zan kara yi ba! surayyace kadai matata ta haddace maganar daya fada furuci mafi tayar da hankali a shekara shin hakan na nufin yusuf ya manta dani? mairamu ta tambayi kanta a karo na barkatai bata tsammani hawaye a idanunta sai dai hawayen jini..... wanda yace namiji uba ne to tabbas zai mutu maraya.............namiji ba dan goyo bane .........maza kwandon zawo........maza tabarmar kashi.......maza mayaudara .......maza maha'inta!!! ( wallahhi bandan)





Muhd-Abba~Gana





www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *