Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Sunday, January 17, 2016

NA DAINA SO!! 43 & 44

adsense here na-daina-so.jpg

NA DAINA SO! 43



Muhd-Abba~Gana


duk irin kokarin da mairamu keyi don ganin ta kawar da tunanin yusuf abu ya faskara tunaninsa ne abu na farko da take yi idan ta farka daga bacci kuma tunaninsa ne abu na karshe da take yi kafin bacci yaci nasarar sure ta ita da kanta ta gamsu cewar tana bukatar taimakon gaggawa tun kafin al,amarin ya kai ga wargaza kwakwalwa. by muhd abba gana

** ** **

a wani yammaci kabir ne da mairamu zaune a gefen kogi kan wasu duwatsu mairamu ina mai ba ki hakuri hakurin me? hakuri bisa laifin da nayi wanne laifi kayi? da tun da farko na goyi baya har yusuf ya zama mijinki wannan ai ba laifi kayi ba taimako na kayi na samu abin da nakeso laifi nayi mana tun da na san cewa yusuf ba mutumin kirki bane mai kake son cewa? sannin kanki ne cewa tare muka yi karatu da yusuf abin da kusan duk mutanen kauyen nan basu sani ba shine bai kammala karatun jami'a ba korarsa akayi....... saboda me? saboda wani laifi da yayi wanne laifi? sai da ya dan yi jim kafin ya bata amsa "wata budurwa ya yiwa ciki"


Muhd-Abba~Gana


NA DAINA SO! 44


Muhd-Abba~Gana


duk shiru sukayi kamar ruwa ya cinye su mairamu ce ta katse shirun ba kayi laifi ba yaya kabir don a lokacin ko da ace ka yi min wannan bayanin ba zan fasa aurar yusuf ba watakila ma naji haushinka mai yiwuwa nayi tunanin cewa ko bakin ciki kakeyi min saboda makahon so nakeyi wa yusuf kuma ba zan iya .....kasa karasa maganar tayi ina son ki saurari wata magana wacce magana? ki shirya gobe da safe muje kotu ayi me? a raba auren ki da yusuf raba aurena da yusuf zai dawo min da shekarun dana salwantar? raba aure na da yusuf zai kankare bakin cikin da ya kunsa min raba aure na da tusuf zai dawo min da farin cikin dana rasa a rayuwata? mene ne amfanin raba auren? saboda ki fuskanci sabuwar rayuwa ta hanyar sake yin wani aure? kwarai kuwa wallahii wallahi ba zan kara yin wani aure a rayuwata ba ki daina fadin haka to ai gaskiya ce wannan ba gaskiya bace to wane ne zai yarda ya aure ni? nine kai?? shakka-babu ko kina shakka a bisa irin so da nake yii miki?



Muhd-Abba~Gana


www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Share:

1 comment:

please after reading drop down your comment here!...

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *