Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, February 19, 2016

BANA KAUNARKA!!! 25

adsense here bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 25 MUHD-ABBA~GANA 09039016969 -------------------------------------------- ina shiga na kankame ta ina kuka hannu ta daga da kyar ta shafa kaina wahida ba dai abin sa sukai miki ko? a daran yaya shahid dani muka kai anty wani babban asibiti kudi basu yi wata-wata ba suka shiga da ita emergency likitoci sunyi nasarar cire mata bulet din ina zaune na hada kaina da gwiwa ya shigo taso mu tafi yace min na mike na bishi muna isa muka tarar su abba mom atu baba rabiu duk sun zo har anyiwa daddyn wanka kukan da nake yine yasa abba yayi min magana tashi ki koma daki ina kallo shahid na kwararawa mahaifinsa addu'a waya naiwa haidar cewa maza ya taho gida bbu lafiya kan kice meye wannan gidan ya cika da mutane tashin hankali, haidar ya iso ya tadda ana shirin fita da mahaifinsa daga dakinsa lokaci daya ya birkice da kyar aka shawo kansa yaiwa mahifin nasu addua,amma sumansa uku koda za,a dauke shi kukan kura yai ya rike makarar ya dinga duka masu rike da ita,shahid shi ya dauki haidar yasa shi a daki ya kulle sannan aka samu damar fita da mahaifin nasa a asibiti kuwa sunce basa bukatar dan jinya sai dai anti da kanta ta roki a bata wahida saboda haka wahida ce a gurinta.bayan sati daya ba laifin jikin antin yana sauki ranar shahid da haidar abba da baba rabiu anty ta soma yi musu magiya hadda kukanta su fada mata gaskiya ina mijinta yana raye ko kuma ya rasu kukanta ya daga hankalinmu ainun,haidar yace anty sai dai hakuri amma maganar gaskiya daddy ya rasu yaune kwanansa bakwai gaskiya ta girgiza domin bbu wanda ya ankara sai ganinta akai wanwar a kasa ta fadi tuni jini ya balle haidar ne ya kira likita,likitoci sukai hanzarin dauke ta wani likita ne ya dinga fada kun gani kun wargaza mana aiki shi yasa muka fada muku bamu.....kan ya karasar bom boy ne cikin fushi ya dakatar dashi ya dinga yiwa likitan bala'i da kyar abba ya ja shi suka tafi.tsakad dare ina zaune kan abin sallah tace wahida ban ruwa insha na mike na dauko robar swan na tsiyayo a cup na dago kanta na bata tasha sosai har tace ya ishe ta na maida ita ba kwantar tace sannu wahida nace yauwa wahida Allah yai miki albarka ubangiji Allah ya raba ki da sharrin makiyanki amin,wahida ki taimaka ki bawa dan uwanki ishassun hadin kai shahid yana tsananin sonki anty ba wai bana sonsa bane ina son karatu ne to wahida Allah ya taimaka ameen,ta koma ta kwata ina jin ta tana ta jero kalmar shahada koda inda saboda yace na saba jin irin wannan saboda koda yaushe sannan duk irin baccin da anty take yi muddin akayi kiran sallah ta kan ce in taimaka mata tayi alwala tai sallah yau ma ina zaune har akayi sallar asuba sai dai nayi mamakin yadda har aka idar anti na bacci komawa nai na kishingida bacci ne ya soma daukata sallamae abbana naji shi da ya shahid. Abbagana hausa novels @ facebook. www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Share:

2 comments:

please after reading drop down your comment here!...

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *