Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, 22 April 2016

SAUYIN RAYUWA 11__15

adsense here

sauyin-rayuwa.jpg

[9:10PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page11 na BABY ZAHRA cikin murna da zumudin yau iyayen masoyin ta zasu zo tambayar auren ta aketa sheka mata kwalliya, girke girke babu irin wanda ba ayi ba sae shiga da fita akeyi tsakanin palourn baki da dakin fulani da kitchen, shirye shirye ya kan kama angama komai yazamana bakin kawai ake jira, kade kade ake tayi da buse busen algaita cen zuwa jumawa sae gasu nan sun iso motaci biyu kawai suka zo dashi na alfarma, mota daya drivern sune da abban abuja da abban jajere dayar motar kuwa muktar ke janta sae yayan mamar su da kuma kanin baban su iyayen su kenan, tun daga bakin gate suka san sunzo gidan alfarma dogarai aka turo suka tare su izuwa masaukin su, abinci aka hau jero musu shi kala kala kuyangu ne suka shigo suka hau zuzzuba musu suna gama zubawa sukayi gaba saida suka ci suka sha kusan awa daya da rabi kafin sarki yashigo da tawagar sa, suka zauna gaisuwa suka fara mikawa sarki, sannan daga bisani suka soma zancen auren da waziri aketa zancen, har maganar sun takai ga maganar sadaki, #500,000,00 naira dubu dari biyar aka bayar na sadaki, an tsaida magana akan nan da wata biyu za ayi bikin, sallama sukayi na alfarma sannan daga bisani suka tashi suka dau hanyar jajere BABY ZAHRA [9:10PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page 12 na BABY ZAHRA Cen yamma suka isa cikin garin jajere, suna zaune bayan sun gama cin abinci, abban abuja yake cewa to ni dai gobe idan Allah yakaimu zan wuce abuja amma kai muktar ina ga zan barka anan saboda kusamu Ku sasanta atsakanin ku ku fahimci juna sosae, kan muktar akasa baice komai ba, abba yaci gaba da magana inyaso koda sati daya ne sai kayi kadawo saboda kazo afara shirye, too kawai ya iya cewa abban na sa, yata shi yayi cikin gida Washe gari da sassafiya abba ya dau hanya shida drivern sa, akabar muktar a garin jajere, bakin kogi ya nufa don shi ba inda yake burgeshi a garin irin bakin ruwan, tun daga nesa ya hango su sunata tadi bai fahimci su Waye a gurin ba har sai da ya kusan to su, yana matsowa sai ya fahimci ashe kaisa ce da saurayinta ga kuma kawarta ma danata saurayin a gefe, ji yayi wani abu ya sokeshi acikin ransa domin kuwa muktar mutum ne mai matukar kishi, don kuwa ko zahra ce kanwar sa yakanyi kishi akanta idan yaga wani a tsaye da ita balle kuma kaisan da jiya jiya aka gama magar auren su da ita, domin kuwa ko banza matar shi zata dawo nan ba da dadewa ba, afusace ya iso inda suke, tana ganin sa gabantane yayi mummunar faduwa, tafara dan sose sose narashin gsky, tsawa yasake mata ke wannan kuma waye shiru tayi bata ce mai komai ba, saida yasake nanatawa bada ke nake magana ba, cikin inda inda tace sunan shi IRO, shi karan kansa iron yaji tsoro ba kadan ba, ido kawai yayiwa iron ya fahimci akwai wani abu, yadubi kaisa yace to kaisa ni kam bari in karasa sai anjima ko, batama iya amsa masa ba yayi gaba cikin tsawa yace kidauki ruwanki kibar nan kafin in saka miki hannu, da sauri ta dau abin ruwar ta tabar gun da gudu ko takan rakiya bata biba ta nufi gida cikin sauri, fasa zaman da zaiyin yayi yajuya ya koma gida, saboda ransa ya baci, abban jajere yagani kishingide acikin zauran, yadan samu gefe ya zauna, abban jajere ne yace yaya dai yaron abba, kan shi akasa yace abba daman kaisa tana hira ne, abban jajere yace hira kuma wani irin hira? Muktar yace ina nufin hira fa da saurayi, abba yace kaisan? Muktar yace eh, da karfi ya kwadawa kaisa kira da gudu tafito donjin yanda abban nata yakirata cikin kakkauran murya, tana shigowa zauran ganin ya muktar datayi zaune agun bakaramin fadar mata da gaba yayi ba, itama ta naimi gu ta zauna tace abba gani, yace kaisa ashe bakyajin magana ban sani ba wulli wulli tayi da ido saboda tasan me tayi, abba ne yace bana hanaki hira da wannan yaron ba, shiru tayi , yace to bari ingaya miki wani abu kinga wannan ya nuna muktar yace daga yau shene MINJIN KI!!! Kamar saukar aradu taji maganan, da sauri tace MIJINA kuma abba, ce mata yayi eh mijin ki ne shi, ko kina da jaaa ne, shiru tayi , yace tambayarki fa nakeyi, a'a kawai ta iya ce masa. BABY ZAHRA [9:10PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page 13 na BABY ZAHRA * Acen abuja kuwa bayan abba yaci abinci ya huta yana kishingide a palourn kasa, hjiy hafsat ce a hannun daman sa, hjy rukayya a hannun hagun sa, yajuya ya kalle su dukkan su, sannan yace munje munyi wa muktar tambayar aure fa, da sauri momy takatse shi da cewa tambayar nasreen in akaje akayi, ehhh kawai yace mata, fadada murmushin ta tayi cikin jin dadi, tace amma gsky alhj kun shammaceni dama ashe tambayar auren sa kukaje, ae dana bada tsaraba mai tsoka ankaiwa surukata, kallon ta kawai abba yayi ya kauda kai (bansan inda wannan matar zata kai son abin duniya ba) yafadi a ransa, sannan yace ai har sadakin ta mun bayar, an kuma tsaida rana nan da wata biyu, wani dan guda momy ta sake cikin jin dadi tace kaiii amma alhj naji dadi ba kadan ba, kace muna da shagalin biki a gidan nan babu kakkautawa, abba yace mata ehhh, amma fa su biyu ne zai aura, kamar saukar aradu taji da sauri tace su BIYU kuma Kamar ya alhj bangane ba, murmushi abban yayi yace ohh daman yaron naki bai gaya miki emmata biyu yake nema ba, emmata biyu kuma alhj, kuma kayarda kanema masa su dukka biyu, abba yace to yazanyi tunda yace dukka yana so, momy ce tace to nidai baitaba min tadin dayar ba, to ita dayar a ina take? Ita inma duk acen in suke, Momy tace ita kuma er gidan wanene ita, yace ba er gidan kowa bace hasalima ba acikin jalingon suke da zama ba, momy tace ban gane ba BABY ZAHRA [9:10PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page 14 na BABY ZAHRA Abba yace ehh ba a jalingo suke ba, acikin jajere suke kuma ba kowa bace face KAISA, ba momy ba har hjy Rukayya ta razana domin bata taba tsammanin hakan daga gurin muktar ba, momy ce ta katsemata tunani da cewa KAISA kuma amma dai ba kaisan da nasani ba, abba ne yace to wacce kenan, ko kinsan wata kaisa bayan wannan in, innalillahi wa inna ilaihirraji un!!! Abinda momy ta fadi kenan, tashi zaune abba yayi yace mata lafiya, tace yanzu yaron nan yarasa wanda zai auro kuma sai kaisa, sai da ta fadi maganar kuma sai tatuna dangar takar da ke tsakanin abba da kaisa, nan take sai taji kunya, afusace abba yamike tsaye yace bangane me kike nufi ba kina nufin ita kaisan ba mace bace kome, to ingayamiki ki iya da bakin ki, kuma aure tsakanin kaisa da muktar kamar anyi shi, idan kuma kika sa wasa ita wanda kike son ma sai in hana auren ta, sosae abba yake fadan domin ranshi yabaci da maganar da momy tafada, idonshi yakada yayi jaaa, hakuri kawai suke ta bashi, fuuuu yayi wucewar sa ciki, gsky momy itama bataji dadin abinda tayi ba, amma tayaya za ayi dan da ta haifa acikin tane wai yarasa wanda zai aura sai er kauye gsky da sake, ita azaton ta tadauka azuciyarta take furta maganar ashe yafito fili, hjy rukkaya ce tace mata to inbanda ke hajiya ae kuwa kaisa ba bakauyiya bace tunda itama tayi bokon nan de diploma ne fa da ita, cikin tsawa momy tace dallah cen rufe min baki ke me kika sani game da 'da, har zaki wani cewai tayi diploma, diploman banza diploman hofi, cikin sauri hjy rukkaya tace too Allah yabaki hakuri ni bada wata nufi nafada ba, tayi wucewar ta dakinta , tabar momy agun sae babbami take ita daya BABY ZAHRA [9:10PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page 15 na BABY ZAHRA Tana shiga daki tadau wayarta numbern muktar tane mo ta danna kira, sai dai amma kash tayi tayi yaki shiga ba network tsaki kawai taja ta cillar da wayar kan gado, tane mi guri ta zauna a baki gado takama kai ta hau tunani, ni da nake son dana idan zaiyi aure ya auro wacce dukiyar ubanta ya ninka namu, shine zai kama ya nemo min wata jaka to wai meye nufin muktar akan wai zai aure su su biyu, kai gsky da sake, shi kuma muktar in zai zo yasame ni agidan nan zanji dalili. Garine ya waye sosae misalin karfe 11am waya suke tayi da nasreen akan ta turo drivern ta zaizo ya dauki muktar don shi bazai iya shiga motar kasuwa ba kuma yana son zuwa saboda zaiyi mata zancen kaisa yaji me zata ce, sallama sukayi akan bari yatashi yayi wanka kar drivern ya iso, lekowa yayi tsakar gidan yana neman dan aike, kicibus kuwa sukayi da kaisa, yace kee zonan rai bace yayi maganan, tajuyo cikin nutsuwa tazo gaban sa ta tsaya tace mai ina kwana yaya, yace inda ban kwana ba zakigan nine, shiru tayi tana sauraron taji yau kuma ta ina masifar zata tashi, suna nan tsaye kusan minti biyar ahaka, cen kasan ranshi ji yake kamar yarufeta da duka, sannan yace mata kiwuce ki kawomin ruwan wanka kuma ruwan zafi nake so, too kawai ta ce mai tayi cikin gida, babu ruwan zafi sai da ta daura masa ta jira yayi zafi kafin ta juye masa abokati ta sirka mai dan dai dai wanka, sannan ta dakko ta kawo mai, da sallama ta shige cikin dakin, ko amsawa baiyi ba ya hauta da fada sai yanzu kikaga damar kawo min ruwan, cikin nutsuwa tace a'a wlhy yaya ba ruwan zafin ne shine na daura maka wani sae da najira yayi zafi kafin nakawo maka yace to meyasa bakizo kincemin babu ruwan zafi ba zaki kama kisa inyi lattin zuwa gurin matata uwar 'y'yana, ayya yaya kayi hakuri wlhy bansan gunta zakaje ba don Allah inkaje kace mata wata kanwarka tana mata gaisuwa, yace mata to naji jeki, hankalinta a kwance ta fuce a dakin, shikuwa muktar ba haka yaso ba, yaso ace taji haushin abinda ya gaya mata amma kuma sai ta gwada masa bata damuba, mitsww tsaki yayi yadau bokatin ruwan sa ya wuce cikin bayan gidan sa, kasancewar bayan gidan a dakin yake BABY ZAHRA

adsense 2 here
Share:

3 comments:

please after reading drop down your comment here!...

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *