Wednesday, April 27, 2016
SAUYIN RAYUWA 71 (KARSHE)
SAUYIN RAYUWA. page 71 na BABY ZAHRA HAIFA,ARIF, nd AFREEN, sun tashi cikin gata da jin dadin rayuwa, iyayen su suna mugun son su, ba a gwada musu ban banci kullum suna tare suna wasa, a hakan muktar yasake gina musu wata gidar babba falat uku ne acikin gidan nashi da na nasreen dana kaisa, rayuwa sukeyi cikin jin dadi, idan nasreen zataje hutu ta kan kwashe yaran ne dukka ta tafi da su, haka itama kaisan.
Viser yayi musu dukkan su, sukatafi London daga nan suka biya Egypt, sai da suka kama yawon shakatawar sune sannan suka tsaya a makka sukayi aikin hajji sannan suka juyo ta gida, dukkan su kowa ta dawo da nata tsarabar da muktar yabasu na wata bibbiyu, suna dawowa suka cigaba da rainon cikin su...........bayan wata bakwai ne kowa ta haifo danta, inda kaisa ta haifi Hajara mai sunan fulani, nasreen kuma ta haifi mai sunan mai martaba.....muktar yabude musu manya manyan shaguna na sayar da atamfofi da lesuna, ga kuma na jakkuna da takalmi, ko wacce da nata......zaman lafiya da jin dadi ga kwanciyar hankali ba irin wanda basayi agidan su sun sami SAUYIN RAYUWA bana kadan ba.......to ni kuma bari in huta anan, sai dai ince muku TAMMAT BI HAMDILLAH
Sai mun hadu a sabuwar littafina mai suna WATA RAYUWA insha Allahu.
Nice naku akullum FATIMA ZAHRA YAKUB wanda akafi sani da BABY ZAHRA
SADAKARWA
Na sa daukar da wannan littafin ma group ina
DUNIYAR LITTATTAFAN HAUSA
DA KUMA
GAREKU MATAN KASAITA
Ina mika gaisuwata ga dukkan mutanen group in
GODIYA TA MUSAMMAN
Ga duk masoya na masu karanta littafina
INA MIKA GAISUWA TA
Ga dukkan online writer's, Allah yakara mana basira gaba daya Amin thumma amin
ALHAMDULILLAH. adsense 2 here
Burodin ayaba
Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.
Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.
MAJNOON hausa love novels
Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more
mun gode allah yakara basira amin
ReplyDeleteSANNU DA KOKAREEE.
ReplyDeletetnk yhu
ReplyDeleteGodiya mai tarin yawa
ReplyDeleteMungode littafeen yayidadi
ReplyDeleteAllah ya kara basira
ReplyDeletesannu dakokari mungode s/s
ReplyDeleteTnks
ReplyDeletemungode
ReplyDeleteTanks Sister
ReplyDeleteSannu Da Kokari, Allah Ya Kara Basira. Jazakallahu Khairan!
ReplyDelete