Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, April 27, 2016

SIRRIN ZAMA DA MIJI 9

adsense here sirrin-zama-da-miji.jpg

SIRRIN ZAMA DA MIJI

{KASHINA 9}

(IYA MAGANA)


BY

MUHD*ABBA*GANA
09039016969

yana daga cikin ladubban zamantakewa wadanda yake amta mace ta kiyaye shine ta iya magana a lokacin da take hira da mijinta ma'ana ya kamata tun farkon ta sani cewa ita fa macece kuma Allah madaukakin sarki ya san ya nutsuwarta a wajen mijinta don haka yana da kyau maganarta ta zama mai farantawa maigidanta. yana da kyau mace ta zama mai tausasa muryarta a lokacin da take hira da mijinta wato ta zama kamar wata karamar yarinya mai nuna shagwaba wannan shi zai dada sa mijinta ya yarda da ita kuma harta kallo idan zaki kalli mijinki to ya kasance kallone na girmamawa da mutuntawa kuma ya zama kallone da zai tabbatarwa mijin cewa kina kaunarsa kuma kin yarda dashi har a cikin zuciyarki, kuma yana da kyau ko a fagen tafiya kada mace ta zama kamar namiji musamman idan tana a gaban mijinta don haka ya kamata tafiyarta ta zama a bisa tsari da kuma nutsuwa amma idan tafiyarta ta zama ta hauka wato irin ta masu jin karfi to wannan zai iya rage kimarta a cikin zuciyar mijinta. haka kuma yana da kyau a musulunce mace tayi shagwaba a gurin mijinta domin nana aisha (RTA) ta kasance yar lelen manzon Allah (SAW) hasalima an samu lokacin data cewa manzon Allah (SAW) sai ya dauketa haka kuma yazo a cikin wani hadisi cewa manzon Allah (SAW) yana yin tseren gudu shida matarsa wato sayyidatu Aysha (RTA) don haka wannan yana nuna mana muhimmancin kyautata mu'amalla a tsakanin mace da mijinta domin a samu jin dadi nutsuwa da kwanciyar hankali sabanin yanda harkar aure take gudana a tsakanin al'ummar wannan zamani wanda zaka mafi akasarin jama'a wato ma'auratan sun saki ka'idojin zamantakewa shi yasa ake ta fuskantar matsaloli a tsakaninsu wannan yasa saika ga hartakai suga rabuwa wanda shine mafi zama abin ki a gurin Allah (SWT) a cikin harkar aure.mafi akasarin abinda ya sa ma aurata suke samun matsaloli a cikin harkar aure shine son zuciya da suke sa a gabansu wato ya zama an daina binciken abinda Allah yace ko abinda manzon Allah (SAW) yace sai ya zama su kuma mata sun maida aure kamar wata hanyar neman wadata da kuma arziki wato kamar kasuwanci tun a farkon neman auren ba a tausassawa mai neman sai a dinga dora masa abubuwa daban daban tun yana ganin kimar matar har ma ya daina ganin girmanta dana iyayenta, kuma sai a zo ayi auren shi kuma idan ya kalli wahalar daya sha kafin ayi auren shi yasa ba zai ji tausayin matar ba. kuma a karshe dai ita ma sai tace mijin ba zai juyata ba to haka dai lamarin zai ci gaba da kasancewa a tsakaninsu a karshe sai kaga an rabu domin kuma tun daga farkon auren an sabawa koyarwan manzon Allah. zan cigaba gobe insha Allah. adsense 2 here
Share:

4 comments:

please after reading drop down your comment here!...

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *