Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, April 30, 2016

WAYE SANADI 1??

adsense here waye-sanadi.jpg

WAYE SANADI?

1


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz

Misalin karfe sha biyu na ranar lahadi mama ta nufi gidan alhaji mukhtar dake unguwar dorayi.Dan Allah malam ina son ganin mai gida hajiya zuwanki wajen nan uku yana kin fitowa ni gaskiya na gaji da zuwa kiranshi dan Allah.dana ka taimaka min wallahi in dai bai fito ba daga yau bazan kara zuwa ba yayi cikin gidan yana shiga can ya dawo kinyi sa'a yana zuwa to na gode nafi minti goma kan ya fito har nayi tunanin tafiya na hango fitowarsa yana cikin yana batsuwa ya karaso wajen.yau kuma da me kika zo? bbu abin da naxo maka dashi sai alkairi Alhaji ka dubi girman Allah ka tausayawa rayuwata rakiya kuma ka tuna kaunar da ka kewa rakiya har kai mata mugun sakamako kinfa malama ya isheki ni da kuke so ku cuceni ku batan suna ku zubar min da mutunci sannan ku raina hankali magajiya kar ki dauke ni wanda bai san me yake ba in baki sani ba ki sani in kuma kin manta in tuna miki ni din cikakken likita ne wanda yasan meye ke na riga na saki yarki ba aure a tsakaninmu sannan kizo min da batun tana da ciki har na tsawon wata uku yau duka rabuwarmu wata biyu ya akayi ciki a jikinta har na wata daya ban san dashi ba? to wallahi magaji yau shine maganata dake ta karshe duk ranar da kika kara zuwa nan gidan sai nasa police sun kameki maza ki fice daga nan yar ku taje tayi abin kunya ana so a likan daman can na aura bisa tsatsayi yanzu kuma Allah ya rabamu,kuke neman doran masifa ya juya ciki hajiya kiyi hakuri in har kuna da gaskiya komai daren dadewa zata bayyana na gode ta juya zata tafi ya zaro naira dari ya bata.WANE NE DR MUKHTAR?
Dr mukhtar isah, haifaffen garin kano ne cikin unguwar yakasai su hudu mahaifinsu suka haifa binta da lamratu sai kuma sadiya sannan shi dan auta dukan su sunyi aure har ma sun aurar da ya'yansu sun sami jikoki shi ka daine Allah bai bashi haihuwa ba Allah ya zuba masa son yaya yayi aure aure da dama duk dan ya samu haihuwa amma shiru yana zaune a dorayi da matansa biyu,hajiya zuwaira da hajiya saratu yana yawan karbar yayan yan uwansa ya rike amma rikon baya zuwa ko ina saboda makircin matansa ana cikin haka ya hadu da rakiya bafula ta nace suna zaune a fanshekara,a salinsu yan gongola ne rakiya yarinya kyakkyawa dr mukhtar ya nuna mata ra'ayinsa nasan ya aureta ka ba a sha wata wahala ba, ta amince nan da nan magana ta kankama har takai batun aure sai dai tun shigarta gidan bata taba farin ciki ba koda na minti daya ba,


MUHD*ABBA*GANA


Abbagana hausa novels @ facebook. adsense 2 here
Share:

22 comments:

  1. Allah ya biya muna jiran karashi

    ReplyDelete
  2. A Dadi Anayi Sai Gaskiya Godea Marar Adadi.

    ReplyDelete
  3. Allah kara basira

    ReplyDelete
  4. Allah ya biya

    ReplyDelete
  5. more grease to your elbow

    ReplyDelete
  6. gsky litafin yayi dadi wlh Allah yakara budi da basira

    ReplyDelete
  7. Allah ya kara basira

    ReplyDelete
  8. Bilkisu AbdullahiMay 3, 2016 at 11:54 AM

    Allah ya kara basira

    ReplyDelete
  9. godiya mai yawa

    ReplyDelete
  10. ALLAH YABIYA MUHAMMAD ABBA GANA

    ReplyDelete
  11. littafin yana da dadi

    ReplyDelete
  12. agsky muna karuwa da kai Allah yakara bsr

    ReplyDelete
  13. gaskiya litaffanka suyi kuma ina jidadi su sannu da kokarin ni sabon shigane don waye sanadi shine farko litaffin ka da nafara karantawa

    ReplyDelete
  14. gaskiya litaffanka suyi kuma suna bada ma ana

    ReplyDelete
  15. Allah ya kara basira

    ReplyDelete

please after reading drop down your comment here!...

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *