Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, 27 May 2016

AMINAN***JUNA 221---250

adsense here aminan-juna.jpg

[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNAEXTREME HAUSA WRITERSNa Xarah~B~B
241-2455 MONTH LTR

Abubuwa da dama sun faru daga cikin su har exams d'in second semister da su Amrah sukayi kuma "Alhamdulillah" result d'in su yayi kyau duk da basu cikin walwala hakan baisa sukayi wasa da karatun su ba.


B'angaren Farouk kuwa damuwa da tunani sun hana mashi maida hankali ga karatun shi hakan yasa da result d'insu ya fito point d'in shi yayi LOW sosai, dalilin haka kuwa aka kori FAROUK daga Skul duk da magiyar da yayi tayi amma basu saurare shi ba, hakan ba k'aramin tada hankalin Farouk yayi ba ya k'ara shiga damuwa fiye da ta da. Bayan ya koma gida tun yana 6oyewa iyayen shi har dai ya yanke shawarar fad'a masu, fad'a sosai yasha dalilin haka kuwa hawan jinin mahaifiyar shi ta tashi, tsine mashi kad'ai ne Abban shi baiyi ba.


Kwance take tana waya da Futha cikin kwanciyar hankali domin kuwa ba k'aramar kulawa Futha da ya Affan ke ba Zarah ba, shiyasa yanzu damuwar ta d'aya ce shine Aminiyar ta tasan bata yaudare ta ba.


"ya kamata kinatsu kicire duk wata damuwa a ranki, haba Amrah sai ka ce Farouk shine autan maza dubi fa yadda kika koma sai kace wadda tayi shekaru tana jinya" Mum ta fad'a, "wlh Mum na kasa manta abunda Zarah tamani ne, kuma gashi idan nakira Farouk wayar shi bata zuwa" "to kiyi hak'uri mana ki koya ma kanki cire son shi a ranki, kiba wasu dama su zo mana" Mum ta fad'a tare da janyo hannuwan y'ar ta ta a ranta kuwa tana mai tausaya mata..... Urs Zarah~B~B.


246-250Haka rayuwa ta kasan cewa Farouk dan kuwa yanxu komai ya had'e mashi, ga rashin karatu gashi bayada wata sana'ar yi, mahaifiyar shi ba lfy Abban shi kuwa har yanzu fushi yake da shi duk abun duniya ya dame shi.
BAYAN SHEKARA UKU.Wani saurayi da budurwa na hango zaune a balcony wanda daka gansu kasan masoyane dan kuwa firar su sukeyi cikin jin dad'i da farin ciki, a hankali na fara takuwa dan ganin suwaye wad'annan masoya dan kuwa sunyi matuk'ar birgeni, kafin na k'araso naji murya na fad'in " haba dai MY DEAR kaima kasan bazan iya rayuwa ba kai ba" idona na k'ara murzawa dan k'ara tabbatar da abunda idona ya ganan man, wazan gani ? AMRAH ce da MUSTY sai soyayyar so sukeyi abun gwanin ban sha'awa.


Zaune suke a parlour ita da umman ta suna fira, ummah tace " Zarah wai yaushe ne Affan yace zai turo dan nama kawon ki mgn da wuri?" "Eh ummah daman cewa yayi da munk'are Skul zai turo ayi mgn amma bai fad'a mani ko yaushe ne ba" "ok Allah ya taimaka yasa adace ya kuma yi maku albarka" ummah ta fad'a, zarah ta ansa da "amin" wayar Zarah ta d'au ruri ganin ya Affan ne ke kiranta yasata mik'ewa tana murmushi tare da fad'in ummah ina zuwa ta wuce d'akinta

Da shigar ta ta fad'a kan gado, waya sukeyi mai cike da kulawa had'e da so da k'auna, anan ta shaida mashi yanda sukayi da Ummah yace "ai dama ni ke kawai nake jira, a shirye nake ko gobe ma, amma dai zan fad'awa Ammi, sai in kira ki idan mun yi maganar". "Ok sai na jika"a haka har sukayi sallama tare da tsinke wayar.......Urs
Zarah~B~B.
EXTREME HAUSA WRITERS.Fatima~Bello~Bala.
[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNAEXTREME HAUSA WRITERSNa Xarah~B~B
221-225Yau ta kama SUNDAY ranar dasu Ya Affan zasu koma Katsina, bayan sun shirya ne Futha tace "dan Allah akai ta gidan su Zarah suyi bankwana", Ammi tace "bayan wanda kukayi jiya?" Futha a shagwa'bance tace "wayyo Ammi", "bari Affan ya kai ki amma kar ki dad'e tunda kinga tafiya zakuyi" inji mumy, "yauwa Mumy na tanx alot" Futha ta fada tana mai jin dadi.

Ya Affan yaji dad'i sosai dan ko bakomai yana son ya 'kara ganin Zarah, cikin 'kagara yace " kisame ni a mota" ya fita waje, bayan shi tabi suka wuce gidan su Zarah.


Zaune suke a parlour ita da umman ta, ba laifi yanzu Zarah ta rage damuwa da yawa duk da rashin shirin su da aminiyar ta ba 'karamin ta'bata yakeyi ba amma a haka ta fawwalawa Allah komai har lokacin da Allah zaisa Amrah ta gane bata yaudare ta ba.

"Assalamu Alaikum" "wa'alaikun salam" Zarah ta fad'a tare da mi'kewa, "Laah my Futha ashe bakuwuce ba?" "Eh cewa nayi sai na'kara zuwa na ganki kafin mu wace", "Allah sarki my Futha tnx alot 4 ur caring" "bakomai my Zarah you deserve more". Bayan sun gaisa da ummah Futha taja Zarah sukaje waje gurin ya Affan sun jima suna fira abun gwanin ban sha'awa kamar kada su rabu sukeji, wayar Futha ce ta d'au ruri ganin number da ke kiran ta yasa ta saurin d'aga wa "Hello Ammi", banji abinda aka fad'a ba a d'ayan 'ban garan sai naji tace "ammi gamunan kan hanya mun kusa 'karasowa" sa'annan ta katse wayar. Cikin rashin son tafiyar tace "Ya Affan muje Ammi ta kirani tana fad'a wai mun zo munyi zaman mu", Ya Affan yace "ok mu tafi". Kud'i masu yawa Ya Affan yaba Zarah duk da da'kyar ta kar'ba har saida Futha tasa baki, sukayi sallama tare da shaida mata "daya samu lokaci zai zo kuma dan Allah ki 'kara rage damuwar nan", "insha Allah yaya nagode sosai" Zarah ta fad'a, haka suka rabu suna kewar junan su........Urs Zarah~B~B.

226-230Suna isa basu 'bata lokaci ba suka wuce da yake daman sun shirya komai nasu, Amrah kam kin fitowa ma tayi suyi bankwana sai da Ammi ta same ta a Room d'in ta tamata nasiha sosai akan ta fawwalawa Allah al'amarin ta tayi ha'kuri ta rage wannan damuwar aranta "to" kawai ta iya cewa Ammi, sa'annan Ammi ta fito suka wuce, itakam Futha batama shigaba dan tasan ko ta shiga bazata saurare ta ba.


Har gate Mum da Dad suka raka su tare damasu Allah ya kiyaye hanya suka kama hanyar katsina.


Farouk ne zaune 'kar'kashin wata bishiya yayi tagumi sai hawayen dake ambaliya a fuskar shi, duk wanda ya ga Farouk yasan ya sauya sosai dan ni da farko dana ganshi ban gane shi ba saida na'kara dubawa da kyau sa'annan na gane ashe Farouk ne, Musty ne naga ya doso inda Farouk yake zaune, bayan ya zauna ya kalli abokin nashi yace "a ganina kanada hanyar magance wannan matsalar taka, saboda har yanzu kanada chance kaje ka fad'a masu gaskiya tare da ro'kon gafarar su, ko ka samu sau'kin abunda kakeji aranka, saboda wallahi alhaki bazai ta'ba barin ka ba",, "uhm Musty kenan, me zan fada' masu ni yanzu? burina d'aya naga sundawo Skul saboda rashin ganin Zarah ba 'karamin cutarwa ce a gareni ba. {Jama'a kuji Farouk fa, shi baisan idan da abinda Zarah ta tsana ba to shine amma shi wai har son ganin ta yake yi, hmmmm duniya ina zaki damu?, Allah kasa muda ce ya kuma yi mana karshen kwarai Ameen Ameen }. Ganin Farouk yayi nisa baya jin kira yasa musty yanke shawarar 'kyaleshi tunda bayajin shawara ko ya bashi...... Urs Zarah~B~B.

231-235TWO DAYS LTR


Su Amrah ankoma makaranta sai dai yanzu ba tare suke zuwa da Zarah ba, ita Zarah keke napep take shiga ta kaita bus stop, tashiga bus ta 'karasa cikin Skul idan ma ta gama lectures haka take biyo Skul bus, kud'in da ya Affan ya bata da sune take maneji sai kuma abunda ba'a rasaba dayake Ummah na y'ar sana'arta kuma Alhamdulillah.


Haka dai rayuwar su ke tafiya ko wanen su baya cikin walwala sosai bama kamar Amrah da idan ta kira wayar Farouk bata samu sai idan ta kira Musty yakan kwantar mata da hankali sosai.

Duk wata hanya da Farouk yabi dan yaga Zarah amma abin ya faskara dan kuwa Zarah na hango shi zata canza hanya.


Yau takama Friday kuma ranar result d'in su Amrah ya fito, wajen duba result d'in ne Zarah da Amrah suka had'u, fuskar Zarah da'uke da annuri take kallon Amrah da alaman tana son yi mata magana, sai dai me? wata harara Amrah ta bankama Zarah had'e da tsaki, abunda Zarah tafi tsana a rayuwar ta kenan tsaki. Tuni hawaye suka wanke mata fuska a ranta kuwa tana tunanin irin zaman da sukayi da Aminiyar ta mai cike da so da kauna amma gashi lokaci d'aya FAROUK ya ruguza masu rayuwa, wata tsanar Farouk taji ta 'kara shiga a ranta...... Urs Zarah~B~B.

236-240Koda ta dawo daga duniyar tunanin da ta lula Amrah har ta duba ta wuce abinta, cikin rashin kuzari ta isa inda ake duba result d'in, ganin sakamakon tane yasa ta washe baki tare da fad'in "Alhamdulillah!" cikin hanzari ta maida kallon ta gana Amrah, ganin duk sunci, result d'in yayi kyau sosai yasa ta 'kara fad'in "ALHAMDULILLAH".

Da fara'ar ta tashiga cikin gida kan cinyar Ummah ta fad'a,,, "aaaaaaaaa karki karyani, lafiya Kuwa Zarah?" ummah ta fad'a, "lafiya 'kalau ummah, albishirinki" "goro fari tass" inji ummah, Zarah tace" ummah result d'in mu ya fito kuma mun samu point d'in da ake so nida Amrah" " MASHA ALLAH kai naji dad'i sosai Allah ya taimaka" Zarah ta ansa da "amin ummah na". Ummah tace " tou kin had'u da Amrah?" " Eh mun had'u amma sai bayan tawuce na duba nata da yake kinsan idan mutum yasan ADM NUMBER d"inka zai iya dubawa", " tou Allah ya taimaka yasa adace "amin ummah" "tashi kije kici abinci" "a'a ummah sai nayi wanka zan ci", Zarah ta fad'a tare da yin room d'inta....... Urs Zarah~B~B
EXTREME HAUSA WRITERS adsense 2 here
Share:

1 comment:

  1. Abubakar Ibrahim4 June 2016 at 16:11

    Godiya muke Allah ya kara basira

    ReplyDelete

please after reading drop down your comment here!...

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact form

Name

Email *

Message *