Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, May 27, 2016

AMINAN***JUNA 271---280 (END)

adsense here aminan-juna.jpg

AMINNAN JUNA

END



EXTREME HAUSA WRITERS


Na Xarah~B~B


271-275


Sosai maganganun Farouk sun d'aurewa Amrah kai, itakam Zarah batayi mamaki ba sai dai ya bata tausayi sosai ta yanda taga ya dage yana kuka sosai kamar 'karamin yaro, wannan dalilin ne yasa itama ta kama kukan. Amrah kuwa sai ta ringa tuno irin wula'kanci da cin fuska da tayiwa Zarah, a ranta tana tunanin "shin da wane ido zan kalli Zarah yanzu? Zata amince dani muci gaba da AMINTAKA kamar yanda muke da?", kanta ta gyad'a a zahiri tace "nooo! Bazata amince ba, kuma koni ce hakan zanyi".
Da 'karfi ta fasa kuka tace "ka cuce ni Farouk! Kaci amanar AMINNAN JUNA, ka raba mu'amala ta data AMINIYATA wadda nafi so a rayuwata".

Farouk ya dafe kai yama rasa abnda zaice, Zarah ce tace "Farouk indai da gaske ka shiryu tou na yafe maka, Allah ma muna masa laifi mu ro'ke shi gafara kuma ya yafe mana barin tana ni baiwa wacce ba kowan kowa ba, ina maka fatan shiryuwa ta har abada, masu irin halinka ma Allah ya shirye su". Tayi shiru saboda kuka da yake shirin cin 'karfin ta.

Goge hawaye yayi yace "nagode Zarah da kika yafe man, yanxu kam nawan ko mutuwa nayi banda ha'k'kin ki", ya juya ga Amrah yace "ki taimake ni Amrah, nasan ni mai laifi ne, amma ina so ki sani wallahi nayi nadama, dan Allah ki yafe mani muci gaba da rayuwar mu kamar da".

Saurin d'ago kanta tayi tace "its too late Farouk, na yafe maka duk abnda ka mn, kuma kaima ina so ka taya ni ro'kon AMINIYATA data yafe mn, amma bazamu ta'ba zama kamar da ni da kaiba domin kuwa yanzu haka akwai baikon wani a kaina, kuma Idan kaji ko waye baza kayi marmarin zuwa ko bikin mu ba". Da sauri Zarah tace "Amrah ashe kema auren zakiyi?",
Murmushin ya'ke tayi tace "aure zanyi Zarah yau saura sati biyu ma, kuma ba kowa zan aura ba face MUSTAPHA UMAR wanda kuka fi sani da MUSTY".
Ido mud'e Farouk yace "Musty?".........Urs Zarah~B~B

276-280

"MUSTY dai wanda ka sani, babban abokin ka" Amrah ta bashi ansa cikin halin ko in kula, Zarah tace "ashe rana d'aya za'ayi nau da naki",
Amrah tace "ehh haka naji wurin Momy wai zaki auri Yaa Affan".

Farouk yace "Allah sarki! Rayuwa kenan, (a novel by Amrah and Nafee Ankah) dama Musty yace mn har ya gama Msc d'inshi har zayyi aure, ashe kece zai aura",
"Ehh nice" ta bashi ansa a ta'kaice. (Farouk bai wani damu ba saboda dama baya son Amrah, yafi damuwa da jin zarah za tayi aure, amma itama d'in da yasan baida yanda zayyi dole ya cire damuwar a ranshi). Da murmushi yace "tou Allah ya nuna mana, insha Allahu zan hallara kuwa za'ayi komai dani", nam ya hau ro'kon Zarah akan ta yafewa Amrah, cikin 'kan'kanin lokaci suka daidaita kansu, suka koma tamkar yanda suke da.
A ranar kowa yasan AMINNAN JUNA sun shirya har mutanen Katsina.

Bayan kwana goma.
Shirye shiryen biki ne ya kankama a duka gidajen. Amrah da zarah kuwa had'e zaman su sukayi a gidan wata Aunt d'in Amrah da gidan ta yake a kusa da unguwarsu. Futha ma tazo tare suke ta shiri, Mom ita ce ke shirya yaranta biyu da nagartattun kayan mata. Musty da Farouk ma dai tare suke shirinsu. Amrah ta ro'kawa Farouk Dad d'inta ya bashi manager na wani company'nshi dake cikin garin Sokoto, ya shiryu sosai ya zama nitsattsen mutum.
Yau ta kama Thursday (kamu day), amare na hango sun sha kyau sanye da lace iri d'aya kamar tagwaye, a bayan su Futha ce da wata friend d'in Amrah suka kama masu bayan rigunan su (flower girls).
Ranar Friday aka d'aura aure. 'Daurin auren daya tara manyan mutane sosai. A ranar akayi dinner 'kayatatta, duka iyaye sun hallara, amare sunsha wedding gown fara, angwaye kuwa suits suka saka black and white, babu wanda basu burge ba. Washe gari aka d'auki amare aka kaisu gidajen su, Amrah anan cikin Sokoto aka ajeta, Zarah kuwa har Katsina aka kaita.
Tuni soyayya mai 'karfi ta shiga tsakanin Farouk da Futha, sai mu masu fatan alkhairi tare da zuri'a mai albarka.

TAMMAT BI HAMDULILLAH

Duka duka anan na kawo 'karshen wannan dogon labarin nawa, kurakuren dake ciki Allah ya yafe mn, fatan alkhairi ga masoyana baki d'aya.

Note:
Wannan labarin ya koyar damu abubuwa da dama, cikin su akwai;
1) Soyayya ba dan Allah ba, ana so mutun yaso mutun dan Allah, kar kaso mutun saboda abn hannunshi, duk wanda yayi haka tou daga 'karshe akwai dana sani.
2) yanke hukunci cikin fushi. Anfi so mutun ya tabbatar da laifin wani kafin ya zartar da hukunci, daga 'karshe akwai dana sani.
3) muhimmancin Amintaka, ana so duk wanda yake da amini ko aminiya tou ya kasnace akwai yarda a tsakaninsu, kar su bari wani yana shiga tsakaninsu. Da sauran su.



Sadaukarwa ga:Na sadaukar da wannan book ga IYAYENA da kuma MASOYANA a duk inda suke,,,, Allah ka gafar tawa mahaifina ya mashi rahama, yasa aljanna ce makumar sa da shi da duk musulmai "Ameen ya rabbi"




Jinjina ga:Gareki my princess Amrah, u mean alot 2 me my dear, i dnt knw hw to even tnx u my Luvly and caring Frnd, lyf wld be no fun wizout u, luv u so much .


Godiya ga:Godiya ta musammam gareku

'YAN Group d'ina


XARAH~B~BFANS.


SMART LADIES
SADIYA ND ZARAH~B~B NOVELS.
AMRAH ND RABI'AT NOVELS
AMRAH'S KITCHEN
KHADIJAH CANDY NOVELS
HOUSE OF NOVEL na kdeey
WORLD OF HAUSA NOVELS.
Dama Sauran wad'anda ban ambata ba ina mek'a gaisuwa ta gare ku.

GAISUWAR KU TA DABAN CE

EXTREME HAUSA WRITERS
WISDOM HAUSA WRITERS
Nagode kwarai da kulawar ku agareni Allah ya bar zaman tare



Kunfi kuwa son wannan book, nagode kwarai da kulawar ku


〰Sadiya~Jegal
〰Miss Moriki{Qawata}
〰Deejah Luv
〰Aisha~'Dayyabu



Taku gaisuwar ta musammance

My Khadijah Candy
My Rabi'at sk msh
My Beelert Zango
My Raehan{Reporter}
My Basmah{Habeebaty}
My Kdeey
My Futha
My Sadeeya Afka
My Kausar Luv
Zarah{my besty}
Meesha lolo
Fidodo
My Munay
Halima Haima
My Sisi Aisha Ya'u Kurah
Sisinah Hauwa Jabo
My Asea B Aleeyu
Zee Xuciya
Teemerh lolo
My Afrah
Hafsat Usman Gusau
Ummu Ammar

Dama wad'anda ban Fad'a ba duk ina gaida ku


LUV U ALL MY CWT CWT FANS



ZARAH~B~B KE MAKU FATAN ALKHAIRI. adsense 2 here
Share:

8 comments:

please after reading drop down your comment here!...

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *