Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, 27 May 2016

WAYE SANADI??? 21---24

adsense here waye-sanadi.jpg

WAYE SANADI?

21


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz


ihun data ji na saki ne ya sata katshe maganar "dole ne sai na gode masa wallahi in dai sai nayi masa ne kar ya ban ni kawai ki mai dani dangin babana,tunda ke bakya kaunata ina maganar ina hada kayana "ki mai dani dangin babana, ita ce kalmar da take yawan yi mata ciwo a cikin kunnenta ganin zan fita daga dakin yasa tayi saurin rike hannuwana "nana yanzu ban isa nayi miki fada ba to tunda haka ne nayi miki alkawarin duk abinda zaki bazan kara yi miki fada ba kiyi hakuri ki zauna tana fadan haka ta fita, washe gari karfe tara da rabi na shirya cikin farar doguwar riga me adon duwatsu tayi min kyau sosai takalmina milk colour high hills na jawo durowa na dau glass dina fari siriri na dora nace yau dai bara na dau wayata. na fita dakin umma na fada cewa zan tafi makaranta gashi inji daddy ya shigo kina barci dubu biyu ta mikon na juya na fita kai tsaye wayen motata na nufa sai daukar ido takeyi me kyau 2007 fara sol maryam na hanga tana jiran direba na shiga na bata wuta na tafi nayiwa maryam bye bye wata uwar harara ta zabgan nayi mata murmushi na fita jina nake cikin nishadi mara misaltuwa in da muka saba daukar sadiya nan na tsaya na san tana hanyar fitowa. waya tace naji tayi kara alamun shigowar message ne suka shigo har guda uku, nana me yasamu wayar taki tsawon kwanaki a kashe dayan kuma akace: nana duk inda kika shiga cikin duniyar nan ba zaki guje min ba mutum baya gujewa kaddararsa muna tare har abada wani kuma yace; ni nasan muna tare gara ki tsaya ki fahimce ni duk inda kika shiga imran mai nemo kine. ganin sadiya a sanyaye na bude na fito zuciyata cike da tunani baki ta saki tana kallona har na karasa "meye haka kin wani saki baki sai kuda ya fada miki sufy kice yau ke kike jan motar to ko ban dace ba no wallahi ban taba ganin macen da take jan mota tayi mata kyau ba sai ke gaskiya kin dade fitowa fa darajarmu a B.U.K kinga kinzo mu tafi lokaci yana tafiya muna shiga kira ya shigo wayata sufy kina jin calling "sady lamarin wannan me kiran nawa yana bani tsoro ban gane ba "wrong number yayi ta kirana nafa gaya masa wrong ya kira amma kullum sai ya kira har kiran sunana yake abinda matukar mamaki kuma yana tsoratani".


Abbagana hausa novels @ facebook.
WAYE SANADI?

22


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz


kin ga message din shi bayan ta gama dubawa ta dago tana girgiza kai gaskiya shawarata kawai karki kara gayawa mutumin nan magana inkina son kanki da arziki dai anyo ko mutum ne kibi a hankali dan ya rabu dake duk lokacin daya kiraki ki daga kuma kar kice zaki masa rashin kunya "sadiya wallahi har tsoron wayar nake ni kawai yarda ita zanyi na huta ke waya gaya miki in kin yar kin huta a yani duk inda kika shiga kuna tare kawai kawai ki dau shawarar dana baki shikenan sadiya na gode tunda muka shiga makaranta ake kallonmu duk inda muka shiga nuna mu ake har mukayi parking muka fito sufy kallo ya dawo kanmu duba ki ga mutumin naki na juya ina kallon ina ta nunan saifu na hange shi zaune da abokinsa duk suna kallonmu muna hada ido ya sakarmin murmushi ya dagan hannu fuska na hade hannuna biyu nayi masa umbola naja hannunta muka tafi muna shiga class sakon m.yusuf ne ya same mu na same shi a office sadiya zaki raka ni gaskiya kawata bbu inda zani kawai kije ki dawo bani wayarki nayi game ban koyi sallama ba na shiga in da kai tsaye nace "gani" nana safiyyya mukhtar ki zauna mana ina da abinyi to nana ina maganar mu ta kwana ban dau maganarka a bakin komai ba tunda ba ita ce a gabana ba ina na riga haba ka amsa bana sonka dan ba soyayya nazo yi ba nana saffiya nima bance muyi soyayya ba aure nake so muyi sannan ina sonki please ki taimaka ki karbi soyayyata kanan......... kan ya karasa nayi ficewata sadiya na tarar akan mota na har kin fito? to kwana zanyi wallahi sadiya zan rufe idona na zabgawa malamin nan rashin mutunci,ki dai bi a sannu tun dazu nake kiran number taki shiga sai yanzu......"Assalamu alaikum sunana sadiya dawa nake magana ke baki san dawa kike magana ba gaskiya ban sani ba a a towa kike nema? ina neman wanda yake kiran kawata nana safiyya inji meye nufin shi a kanta sannan imran salis,ni dan nigeria ne karatu ne ya kaini america zan kira momyna kira wrong number bazan boye miki ba ina son kawarki taki tsayawa muyi magana ta fahimta kullum sai fada sai zagi ki taimaka ki shawo kanta".gaskiya ka dau babban aiki dan kuwa bauddaden hali gareta musamman akan maza amma ya akayi kasan sunanta??


Abbagana hausa novels @ facebook.

WAYE SANADI?

23


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz

ran da muke waya da ita kanta kashe naji wata ta ambaci sunanta shine naji nana safiyya bata da kawa ni daya ce kawarta nace maka wani irin hali gareta? ita fa yanzu.ta daukeka a matsayin aljani kafa bata tsoro sosai" yauwa sadiya naji dadin wannan labarin kuma zan so ace kin boye mata cewa baki sanni ba karki nuna mata kin yi waya dani kuma dan Allah kici gaba da tsoratar da ita kanni aljanine sannan ina so ki dinga gayan wani abu daya faru akanta wanda kike ganin zata kara tabbatarwa ni aljanine shikenan imran zan yi maka kokarin okey na gode sadiya nafi wata uku ban ji wayar aljani nan ba wanda a wannan lokacin shekara ta biyu a makaranta yau muna zaune da sadiya da kuma sabuwar kawarmu mai suna rukayya wanda nake kira da momy waya ta tayi kara nasa hannu na dauka na shiga uku sadiya aljani ya dawo waye kuma aljani? inji rukayya to kinga ki nutsu ki daga to sadiya ya zance kiyi masa sallama hannu na yana rawa na daga cikin shakewar murya nace salamu alaikum kamar na fashe da kuka ya amsa wa alaikissalamu wata zazzakar muryace ta amsa nana saffiya ya gida ya karatu nasan yanxu kina makaranta ko? sufy kinyi shiru kimin magana Dan Allah ka gayan waye kai kana tayar min da hankali "sunana imran kuma gaskiya ni aljanine kar kuma kice zaki ji tsorona zan dinga kiranki karki tunanin kubuta daga tarkona yana fadan haka ya katse, sadiya naga ta kaina kuna jin maganar da yake fadan wai kr meye haka kiyi abinda nace miki dan ku rabu lafiya ko class ban koma ba nayo gida lafiyar ki nana? umma kaina ke ciwo Allah ya sauwake to kije ki kwanta na shigo miki da abincinki ina shiga na kwanta ina ta tunani naji wayata tana kara cikin dauri na daga nayi sallama. ke baki iya gaisuwa ba ya fada cikin wata katuwar murya kayi hakuri yanzu zan gaisheka daman ke bakya gaida kowa koh hantar cikina ta kada waye ya gaya maka? kina tunanin waye ya gayan ko? karki manta ni fa aljanine karkiyi mamakin ganina zabura nayi na mike ina kallon dakina dan Allah yanzu kana ganina?


Abbagana hausa novels @ facebook.

WAYE SANADI?

24


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz


au kin dauka wasa bara na tabbatar kiga shaida da gudu na kara bakin kofa dan Allah kayi hakuri barrister ki nutsu to na nutsu in kina so mu shirya duk safiya ki dinga gaida ummanki da mijinta da kuma abokiyar zamanta kin ji, naji wallahi zan dinga gaishesu to ki tashi kiyi sallah,nima yanzu zan tafi makka zanyi sallah ban san lokacin da bakina ya furta a hirgi zaka? wane jirgi minti biyar zan isa in kuma zaki mu tafi,zubewa nayi ina bashi hakuri dan Allah kayi hakuri yanzu zanyi sallata to da kin idar kije kiyiwa umma aiki ina kallonki kan nayi magana ya katse wayar da sauri na mike nayi toilet ina idar da sallah na mike na fito umma in kina da aiki ki kawo nayi miki cikin mamaki ta dago kai tana kallona umma kinyi shiru zuba min ido tayi"nana ban da aiki ke da kanki yake ciwo na gama komai kije ki kwanta ki huta kamar na saka kuka na juyo na dawo dakina nasan yanzu yana kallona kuma gashi naje tace bata da aiki haka na yini ranan daidai da wanka ma kasa shiga nayi ina tsoron karya ganni ni gashi fitsari ya cikan mara tunda na dawo nake son na kasa tsungunawa nayi, wata zuciyar tace naje toilet din umma nayi imran kinje yana ganinki haka hawaye ya shiga bin fuskata wayata na dauka na kira sadiya sufy ya gida? sadiya ki taimaka min duk motsin da zan aljanin nan yana gani na me kuma ya faru? fitsari ya cika min mara na kasa zuwa yace yana ganina kan tayi magana kudina ya kare wayar na cilla kan gado tana fadawa aka kira da sani na dauka ina tunanin sadiya ce number shi na gani nan da nan jikina ya hau rawa hannu na yana rawa na dauka sufy kije kiyi abinda zakiyi a bandaki zan rufe idona ba zan ganki ba kuma ina ganin bugawa da kikawa sadiya sannan karki kara kirana da aljani ki kirani da imrana sunan da mahaifina yayi min hudu ba dashi dakyar na iya cewa to karki kashe wayar jeki da ita da gudu na mike nayi toilet dan Allah ka rufe idonka zan tsunguna"bara naje london na kai sako kan kiyi amma karki katse min waya minti uku zan dawo cikim murna nace to na gode. washe gari muna zuwa school na fada jikin sadiya hannuna ta kama muka fito cikin motata muka koma har da momina "sufy wai lafiyarki kuwa???


Abbagana hausa novels @ facebook. adsense 2 here
Share:

6 comments:

 1. Baantaba jindadin littafinnanba kamaryau

  ReplyDelete
 2. muna godiya da yawa pls adinga yi kullum.

  ReplyDelete
 3. Ummu Amaturrahaman3 June 2016 at 07:36

  Gabadai Gabadai Direban Jirgin Sama Fasinja Suna Jira Jirgi Yatashi Muna Godiaaa.

  ReplyDelete
 4. Abubakar Ibrahim3 June 2016 at 13:50

  Gara a gyara mata zama

  ReplyDelete
 5. tnxxx Allah yakara basira abba

  ReplyDelete
 6. muhammad abba gana20 July 2016 at 07:26

  @ummukulsum, ameeen

  ReplyDelete

please after reading drop down your comment here!...

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *