Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Tuesday, December 13, 2016

waye sanadi?? 81

adsense here

💘WAYE SANADI?💘 8⃣1⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.cf "Alh. Nasiru nine mahaifin su Rukayya yaran da ka shigar court kana tuhumarsu kan Batan 'yarka Safiyya, mun zo ne muyi magana ta fahimtar juna sbaoda bai kamata a ce da kimarmu da mutuncinmu mun je gaban aikali kan wata matsalar da mu a gamnmu in mun zauna mun fiiskanci juna za mu iya maganinta. Don haka muka zo mu yi magana ta fahimtar juna za mu yi kokarin shawo kan matsalar ba saimu je ga zuwa court." Ya dan tsaya ya sauke numfashi. Alh. Ibrahim ya karBa, "Na san ba za ka rasa sanin fuskokinmu ba, kuma bai kamata da kimarmu a idon jama'a a ce mun je gaban court muna karar junanmu ba, gara mu hadu mu yi maganin matsalar da kanmu."Alh. Nasiru ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya ce, "Duk abin da ku ka fada haka ne, to amma a inda matsalar take shi ne har yanzu ba ku fadi inda matsalar take ba, kuna ta maganar mu fuskanci juna. In har maganar fuskantar juna ce nima ina son haka, tunda tun farko ni na so mu fuskanci juna mu yimagana cikin mutunci, amma hakan bai samu ba, ranar da na ga hotunan Safiyya a jarida ana cigiyarta na tashi da kaina na je wajen 'yarka Rukayya ta yi min bayanin ya aka yi Safiyya ta Bata, amma kwata-kwata ta kasa yi min magana saboda borin kunya.'Yarku ta munafince ni, zuwana biyu Lagos nemanta, kuma wajensu nake zuwa ita da daya kawar ta Sadiya bayan zuwa kullum cikin waya nake na tambaye su sun ganta, ko sun ji labarinta. Amma sai su ce min suma kullum cikin nemanta suke rana tsaka kuma na ga suna cigiyarta abun ya yi min ciwo. Kuna ganin sun yi daidai? Ya yi shiru yana kallonsu."Gaskiya ba su yi daidai ba, kuma mu ka ga ba mu san an yi haka ba. Sai da muka ce ya kamata a zo gidansu Safiyya a gaya rnusu Batanta, sannan take gaya mana wai tun kafun su tafi Lagos ta bar gida ta ce kuma ba za ta taba komawa ba. Wallahi Alhaji Nasiru tana gaya mana haka muka hau ta da fadan me yasa mu ba ta gaya mana ba. Kan Alh. Nasiru ya yi saurin katse shi da cewa, 'Wannan duk ba maganar da za a dauka ba ce, ni din nan a yanzu cikin zargi nake a kan Batan Safiyya, mahaifiyarta ce take zargina da SANADIN Batan Safiyya, don haka ni yanzu ba zan iya ce muku komai ba."Alh. Mukhtar ya ce, "Mu ma ba so muke ka ce mana komai ba, ilia muna so ka janye karar da ka kai zuwa court bai kamata a ce mun hau court ba kan matsalar da ina ganin za mu iya maganinta ba tare da mun yi wa kan rnu tirere a gaban dumbin dubatar alumma ba."'Ni kaina zan so hakan, to amma ba nine matsalar ba mahaifiyar Safiyya ce matsala. Safiyya amana ce a gare ni, don haka ya zama dole na tsaya tsayin daka na taimake ta a kowanne hali take.""Mu kanmu za mu iya taimakon Safiyya, Rukayya tana son Safiyya na yi imanin ba za ta taba cutarta ba, har ma Sadiyya. Don haka muke so kai yi wa mahaifiyarta magana ta yarda a janye karar, sai mu fuskanci maganar nemanta ba wai mu zauna bata lokacinmu a court ba."Zan yi wa mahaifiyarta maganar da muka yi da ku in har ta amince a janye zan so hakan."Shi kenan Alhaji Nasiru mun gode da karbar da ka yi mana, kuma mun ji dadin sauraronmu da ka yi." Har bakin darareriyar motar su ya rakosu,Tana zaune a falon ta rafka uban tagumi ga Hassan a gabanta yana jan kayan jikinta, amma kwata-kwata hankalinta baya wajensa ya tafi ga tunanin NANA SAFIYYA ruwan ranta. Ya shigo tare da yin sallama har ya Karaso gabanta ya dau Hassan.Rukkayya! Rukkayya!!" Ya kira sunanta.Ta dago a firgice ta gan shi a tsaye, cikin tausayin halin da take ciki ya ce, "Don Allah Rukayya ki bar tunani kar wani ciwo ya kama ki, insha Allahu Safiyya ta kusa dawowa gare mu."Ta daure zuciyarta suka gaisa."Ina Hussaini ne?"A takaice ta ba shi amsa da cewa "Sun shiga gidan Malam tare da Baba."Bayan ya zauna yake gaya mata zuwan su Alhaji Mukhtar. Ta dago tana kallonsa idonta cike da ruwan hawaye ta ce, "Meyasa ba ka tambaye su cewar 'yar tasu ta gaya musu inda ta kai Safiyya. Hawayen da suke cikin idonta suka gangaro zuwa dakalin fuskarta."Ki bar kukan nan Rukayya.""Duk ranar da ka ga na daina hawayen nan to ranar da na ga Safiyya ne, ranar hawayen zai bar idona. In har kana son farin cikina to ka zama SANADIN dawowar Safiyya gare ni, bana so mu yi wani sulhu gara mu je gaban alkalin.""Shi kenan Rukayya yadda ki ke so xa a yi, ko da sun dawo ba zan Kara sauraran su ba, kawai ma hadu a court, sai yanzu ma na kula da rainin hankaiin da suka yi mana 'ya'yansu munafukai ne na karshe, zuwana na karshe can Lagos yaran nan suka hadu har kuka suke ya zama ni nake ba su baki ina lallashin su."Umma ta ce, "Ban yi tunanin haka daga wajen yaran ba, ina musu kallon masu hakali da nutsuwa, ina jin dadin haduwarsu."'Hum, daman ba ka yabon dan kuturu sai ya girma da yatsu."Ita Rukayya tana ganina ta rude kwata-kwala ta kasa magana."Haka Sadiyar ma har yanxu ban ganta ba, don ko lokaicin da na raka yaron alkali ya kai musu sammace babanta ne ya leKo tun farko na fi jin haushin Sadiyar Ha ce ranar da na je rnakarantarsu nemanta ta ce ba ta nan rabon da su hadu tun ranar Jumma'a, kuma alhalin suna tare wai amma yaran nan suka rainan hankali." "Ni kaina farkon ganina da yaran nan bana tunanin haka daga gare su a fuskarsu akwai alama ta nutsuwa har ma da hankali, ashe a zuciyarsu ba haka ba ne."Har Baba ta dawo yana gidan. BAYAN KWANA BIYU Su Alh. Mukhlar suka dawo gidan Alh. Nasiru don jin inda maganarsu ta kwana. Tunda suka tura kiran sa suka ga canji da ya jima bai fito ba, har sun fara tunanin Kara tura kiransa suka hango tahowarsa yana waya. Har ya karaso bai gama wayar ba, yana karasowa kai tsaye ya shiga falon saukar baki suka bi shi a baya.Bayan sun gaisa shiru ya biyo baya na yan wasu sakanni. Alh. nasir ya katse shirun da cewa 'Kamar yanda na gaya muku cewar zan je na gayawa mahaifiyar Safiyya zuwanku da yadda muka yi da ku, to na je na kuma gaya mata." Ya dan yi shiru yana kallon Alh. ibrahim.Shirun da ya yi ne yasa Alh. Mukhtar dagowa shi ma yana kalonsa, shiru babu wanda ya yi magana. Alh. Ibrahim ya ce,."To ya ku ka yi da ita rnahaifiyar Safiyyar?"Ya dan yi jini yana saka abin da zai fada, ya dan sauke marayan numfashi tare da daga hannunsa ya (dora akansa yana shafa gashin kansa. Sannan ya fara magana."Gaskiya Alh. Ibrahim mahaifiyarta ta ki amincewa mu yi sulhu na yi duk iya yina taki yarda ita tana tunanin su suka batar da Safiyya, kuma ko ni kaina ina tunanin haka, ina ganin abin da zai fi ku je ku kara tambayar yaranku su fadi inda suka boye ta, ni zan yi d'awainiyar. zuwa taho da ita. Ina ganin haka zai fi zama alkhairi a gare mu, in har suka fadi inda suka bar ta, ni kuma na yi muku alkawarin gobe zan yi waya a janye karar."Alh. Mukhtar ya dago cikin fushi ya ce, "Na gane nufinka ka fito ka ce ba a janye karar'ya'yanmu daga court ba kana magana kamar ta yara, waye ya gaya maka su suka boye yar matarka? Idan kana da shaidar hakan ka fadan mu kuma in har ka ba mu cikakkiyar shaidar da ta nuna su suka boye 'yarka mun yarda ka kai kararmu kowacce court da ke duniya don yanke mana hukunci. Mun zo maka da sul...."Kan ya karasa ya katse shi da cewa, 'Tabbas ina da shaidar da zan tabbatar da haka, kuma ku kanku kun san 'ya'yanku ba su da gaskiya, don haka ku ke neman sulhu cikin gida ba tare da mun je gaban court ba. Bara na gaya muku gaskiya ko da babarta ta yarda a janyc kararku a court ni ba zan yarda ba."Alh. Ibrahim ya tari numfashinsa da cewa, 'Mu daman haka muke so mu ji daga wajenku, Allah yana bayan mai gaskiya." Ya mike. "Kawu taho mu tafi."Yana fadar haka ya fita daga falon. Alh. Mukhtar ya mike jikinsa a sanyaye har ya kai bakin kofa ya juyo yana kallon Alh. Nasiru ya dan yi murmushi sannan ya ce.'Alh. Nasiru ba mu yi tsammanin haka daga wajenka ba, amma babu komai."Yana fadar haka ya fita daga falon.Tunda suka sbiga mota babu wanda ya yi magana kowa da abin da yake sakawa a ransa, har suka karaso gida a gate Alh. Mukhtar ya sauke Alh. Ibrahim.Tana zaune a falo tana karatun Alkur'ani ya shigo."Abba sannu da zuwa."Bai amsa mata ba ya hau sama. Jikinta a sanyaye ta mike tana shiga daki ta ji kiransa ta fito da sauri. Yana zaune a falo har Hajiya, ta karasa gabansa ta zauna muryarta na rawa ta ce, "Ga ni Abba."Ya dago fuska a hade cikin tsawa ya ce, "Ki gayan gaskiya ina ki ka kai Safiyya?"Wata irin dagowa na yi ina kallonsa, ita kanta Hajiya dagowa tayi. "Abba ban gane nufin k aba yayi saurin katse ni da cewa, "Tun muna mu biyu da ke ki gayan gaskiya me ya faru da Safiyya?" 'Wallahi Dady ban san me ya faru da ita ba, mun fita da Sadiyya muka dawo ba mu ganta ba sai yanzu da na dawo na ga wasikar da ta yi min cikin Jakarta."Ina maganar ina kuka; Ya juyo wajen Hajiya Hassana ya ce, "Me ki ka sani dangane da Batan Safiyya ki gayan tsakaninki da Allah Cikin rnarnaki Hajiya ta ce, "Alhaji wani abun ne ya faru ka ke wannan tambayar?""Babu abin da ya faru ina so na san gaskiyar inda yarinyar mutane take, kar mu yi wahalar banza a court a zo a tsananta bincike a kama mu da laifi saboda na fuskanci iyayenta suna ganin kamar ku ku ka boye ta, ko ku ka batar da ita. Don haka nake so na ji gaskiyar abin da ya faru da ita."Na dago ina hawaye na ce, "Wallahi Abba iya gaskiyata na gaya maka, a ranar da za ta bata sai da muka yi fada muka shirya a lokacin kuma duk akan ta ce ba za ta koma Kano ba, muka yi fadan bayan mun shirya muka fita da sadiya shine dawowarmu muka tarar bata nan bayan na dawo ne na duba jakata shine na tarar da wasikanta da sauri yace yanzu ina wasikar? yana wajen hajiya ya juyo wajenta kan yayi magana ta mike bata fi min ti biyu ba ta dawo dauke da farar takarda mai dauke da rubutun nana safiyya bayan ya gama karantawa, ya dago kansa yana murmushi ko wanan takarda ta ishe mu shaida in ya ishe shida in yaso alhaji nasir yaje can ya nemo WAYE SANADIN batan yarsa kan ya karasa salim ya shigo bayan sun gaisa da abba ya ce ke kuma sarkin daukar magana me ya saki kuka ko kina tsoron haduwarku da manta sabo (alkali) ne? ya dan yi murmushi maganin kwashe-kwashen kawaye kenen kallo daya zakayi masa kasan yana cikin tsantsar farin ciki, ***** ***** ***** ***** ***** shi daya cikin mota sai faman murmushi yake ji yake kamar anyi masa bushara da gidan aljanna ya karya kan motarsa ya shigo layin gidan mallam kalil tun daga kofar gida ya hango manyan motoci ya karasa ya yi fakin. ya shigo tare da sallama malam kalil yana ganin shigowarsa ya hau murmushi ya karasa har kasa gabansa ya zube bayan ya gaishe shi ya juyo wajen mutanen da suke gaban kakansa tsoho mai ran karfe kaki ka mutu araba mana gado ko sai kaga jikokin imran naka ne? 🅰bbagana hausa novels @ facebook. adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *