Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Thursday, 9 February 2017

ALHINI complete

adsense here [10/16, 8:01 PM] ‪+234 816 616 9254‬: *_ALHINI_* ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_* 1to2 ```Page``` kuka take kamar zata cire ranta, idanunta sun kad'a sunyi jawur saboda tsananin kuka, fuskarta tayi face-face da hawaye, zaune take cikin d'akin kan tabarmar kaba, jikinta wata atamface Riga da zani, simple da ganin atamfar kasan tad'an kwana biyu saboda farin data d'an yi Alamar kod'ewa, sai wani madai-daicin hijabi data sanya, shima dai dagani kasan ba sabo bane, amma kuma wankakke ne, duk kayan jikinta basu tare da datti. "Haba laraba kiyi ha'kuri ki daina kukan nan, sabi'u dai yariga ya mutu kuma kinsan kukannan naki baze dawo dashiba, Addu'a kawai yanzu yake bu'kata daga gareki, ta dafa kafad'arta kiyi hakuri dan Allah ki daina kukan nan. Sai lokacin Balaraba ta kalli wacce keta faman rarrashinta tace "Haba indo dole inyi kuka, kukan nan danike shi kad'ai ze ragemin rad'adi da ba'kin cikin danake tartare dashi, (tacigaba da kukanta,) Indo tana matu'kar tausayama halin da 'kawarta take ciki, itama wasu guntayen hawaye ta zubar sannnan ta'kara matsaowa kusa da 'kawarta ta dafa kafadarta da hannu guda, gudan hannun kuma tana goge mata hawayen dake kwarara daga idonta, tace "Tabbass nasan rabuwa da masoyi akwai ciwo, baranta kuma rabuwa ta har abada, Amma dole kiyi ha'kuri ki d'auki wannan a matsayin jarabawa ce daga ubangiji. Laraba ta fashe da wani sabon kuka, tace indo bazaki ta6a gane halin ba'kin cikin danake cikiba, ki duba kiga irin soyayyar da muka shimfid'a nida Iro acikin 'kauyennan muna burge Kowa, amma lokaci guda ana saura sati d'aya bikinmu yaje wanki rafi yafad'a ruwa sai dai gawarsa aka fiddo, tafashe da wani sabon kuka, indo ma kukan take, amma hakan be hanata rarrashin 'kawar tata ba. Cikin sheshshekar kuka tacigaba da cewa "yanzu kuma :yau an wayi gari sabi'u shima ya mutu kamar yanda Iro ya mutu, wannan wane irin iftila'i ne yafad'amin. Assalamu Alaikum, inna ce tashigo da sallama, indo ta amsa mata sannan tashigo d'akin, ta cire ijabinta ta rataye kan 'kyauren d'akin sannan takai dubanta ga Balaraba wacce taketa faman kuka indo kuma na rarrashinta wacce itama kallo d'aya zakayimata Kazan kukan tayi. Indo takai dubanta ga inna dake shirin zama kan kujera tace "lnna har kun dawo? "Har na dawo indo ay anriga anrufoshi sai dai muyi mashi addu'ar samun rahamar ubangiji, sabi'u kam yayi mutuwar ban mamaki, duk da ba mamaki cikin lamarin ubangiji, amma mutane da dama sunce lafiya lao ya kwanta, kawai aka wayi gari ya mutu, wasu siraran hawaye suka zubo daga idon inna dan tana tausayama tilon yarta, wacce tayi rashin masoyi a karo na biyu. Laraba ta fashe da wani irin kuka, ta taso daga inda take tafad'a jikin inna tana kuka, "shikenan inna yanzu narasa sabi'u wayyo nashiga ukku, sabi'u miyasa kamin haka saida kabari na sha'ku dakai sannan zaka tafi ka barni, innalillahi,wa'inna,ilaihirraji'un, ta fad'a kawai sai ji sukayi tayi shiru ba Alamar numfashi tattare da ita, duka jikinta ya saki Nan inna tashiga wani irin rud'ani tana girgizata tana kiran sunanta, "fatima..... Fatima innnalillahi nashiga ukku, Indo dake tsaye hankalinta duk ya tashi tarasa inda zata sa kanta da gudu tafita daga gidan tana neman taimako. "Dan Allah Hashim ka taima mani kada ta mutu, wanda takira da hashim yace "wacece zata mutu, bata bashi amsaba tacigaba da kuka tana cewa ka taimakeni, mutuwa zatayi, dan Allah, da gudu takoma cikin gidan. Har yanzu laraba na rungume jikin inna ba Alamar numfashi tattare da ita, inna kuma sai kuka take tana kiran sunanta. Da gudu hashimu yanufi gidan me gari ya aro baro, Kofar gida ya ajiye baron, sannan yashigo gidan da taimakon, indo da lnna aka dora Laraba kan baron, Hashim ne ke tura baron da gudu. Lnna da indo suna biye dashi hankalinsu tashe suka nufi 'karamar asibitin dake 'kauyen. Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 8:02 PM] ‪+234 816 616 9254‬: *_ALHINI_* ```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_* 3to4```Page``` Sannu Laraba sannnu kinji, kallo kawai take bin mutanen dake gurin dashi, idanunta suka ciko da hawaye, Inna tasa gefen mayafinta tana goge mata. Sai da musalin 'karfe biyar na yamma aka sallamesu daga asibiti, bayan 'karin ruwan da aka sanya mata ya 'Kare, Indo kuwa duk abinnan tana tare dasu sai gab da magrib inna ta umarceta data koma gida kada anemeta, haka ta wuce tana me tausayama halin da 'kawarta ta tsinci kanta. Hashim kuwa tinda akaje asibitin yaketa hidima da Laraba dan kusan duk kud'in da aka kashe shine yabiya, yana mutu'kar tausaya ma Laraba, Shima sai lokacin yabar gidan yanama Laraba fatan samun lafiya, inna kuwa godiya kawai take mashi dan ya taimakesu ba kad'anba, dan in baccin shi da batasan inda zata samu kud'in da zata biya na magani da 'karin ruwan da akayima Laraba ba. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *_BAYAN SATI BIYU_* Zaune take kan guntuwar tabarmar da aka shimfid'a kan shararren gidansu na 'kasa, ta tasa kwanon abinci gabanta, ita bata ciba kuma bata maida ta rufe ba, ta zubama abincin ido tana kallo, wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta, tasa hannu ta goge. "Yanzu Laraba bazaki cire damuwarnan daga cikin ranki ba, kiyi ha'kuri ki d'auki kaddara, kin riga kinsan dukkan me rai mamacine, muma nan mutuwa jiranta muke ko yau ko gobe ko jibi koma yanzu, Dan Allah kisama ranki ruwan sanyi. Wasu siraran hawaye suka zubo daga idanunta tace na ha'kura inna.... Na ha'kura..... Ki tayani da addu'a Allah yayemin damuwar dake tattare dani. Inna ta tausayama Laraba har cikin ranta, tace "Allah yaye maki Laraba, Allah sa maki 'ha'kuri da dangana. Tace Ameen tare da share hawayen dasuka zubo daga idanunta. Da 'kyar inna ta rarrasheta taci abincin, Wanda taci be wuce loma hud'uba, dan ma lnna ta matsa mata ta d'ora da fura rabin cup, sannan taji d'an 'karfi-'karfi. Da sallama ya shigo gidan, ya dur'kusa har 'kasa ya gaida inna, cikin far'a ta Amsa "Hashim kaine sannu da zuwa, ta d'auko wata guntuwar tabarma ta shimfid'a mashi ya zauna, tunda ya shigo idanunshi na 'kan Laraba wacce duk tabi ta rame ta fita hayyacinta, Saida ta lura da yanda yake kallonta sannan tace mashi "ina wuni, ya amsa da "Lafiya lao Laraba ya jikin naki? "Da sauki, "Allah 'kara sauki, tace "Ameen. Sannan ta tashi tanufi randa ta ebi ruwa cikin wani madai-daicin bokiti tashiga kewaye dan tawatsama jikinta taji sanyi. Tunda ta tashi yake binta da kallo, cikin zuciyarshi yana cewa _"Na dad'e ina son Laraba dan dai wasu sun rigani ne yasa na ha'kura, amma yanzu bazanyi sake da wannan damar ta wuceniba, 'kila dama rabonace shiyasa Allah ya kashe lro da Sabi'u_. Inna ce ta katse mashi tunani "Hashim ya mutanen gidan naku?, yayi saurin dawowa daga dogon tunanin dayake yace "suna lafiya sunce agaisheku, daga gurin aike nake nace bari in biyo inga jikin Laraba, inna taji dad'i har cikin ranta yanda Hashim ke nuna kulawa ga 'yarta, tace "jiki Alhmdlh, yace "Allah 'kara sau'ki tace Ameen. Nan dai suka 'dan ta6a fira kafin yayi mata sallama, ya ajiye wata ba'kar leda yace "ga wannan aba Laraba, inna tace "a'a Hashim hada hidima kuma, yace "ba kome inna Allah sauwa'ke nina wuce, tace to Angode Allah bada lada, yace Ameen. Bayan fitarsa ne, Indo tashigo, lokacin Laraba tagama wanka tana shafa mai, inna na Nuna mata abinda Hashim ya kawo mata, balangu ne lafiyayye hanta tafi yawa aciki, sai 'kananan robar yourghut guda ukku,. Bayan inna tafita waje, Indo ta kalli Laraba tace, "gsky Laraba Hashim yanada wata manufa acikin ransa dangane dake, dan ni nasan ba a banza yake maki wannan hidimar ba, Laraba ta kalleta cike da nuna rashin sanin inda maganarta ta dosa, tace "Ban ganeba wace manufa kuma? Indo tayi murmushi tace "gani nake kamar 'Hashim sonki yake.. . Wani mummuman Fad'uwar gaba Laraba taji, dan yanzu ko kad'an bataso taji an anbaci kalmar wani na sonta. Tace Dan Allah indo mubar wannan maganar Hashim ba sona yakeba, inajin kawai dai yana tausayi na ne, amma babu wata soyayya dayakemin, murmushi kawai indo tayi, dan bata so suna kace-nace da 'kawar tata. Ranar dai indo ta d'ebema Laraba kewa dan fira suka sha sosai, har fita sukayi suka d'an zaga gari, Tinda suka fita mutane ketayima Laraba ta'axiyya, indo ce ke amsawa dan bata son abinda ze daga hankalin 'kawar ta. Sai bayan la'asar indo taraka Laraba har 'kofar gidansu saida taga shigewarta sannan itama ta wuce gidansu. Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 8:10 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [20/08 12:47 pm] πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 5⃣to6⃣```Page``` πŸ–ŠKwanaki sun ja lokaci na tafiya, yau an wayi gari sabi,u nada wata ukku da sati biyu da rasuwa, Alhmdulillahi Laraba ta saki jikinta, ba kamar da ba, kuma jikinta ya goge yayi sumut, 6angaren Hashim kuwa kullum soyayyar Laraba 'kara ha66aka take acikin zuciyarsa, har yakai da yakasa sukuni, hakan yasa ya yanke shawarar zuwa gidan yayarsa, ya fad'a mata halin dayake ciki, kuma ya ro'keta taje gidansu Laraba ta gabatar dashi amatsayin me neman Laraba da Aure. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Laraba ce tafito cikin shirinta, atamfa ce jikinta d'inkin doguwar riga, kalar ruwan 'kasa duk da atamfar ba sabuwa bace amma ta masifar yimata kyau, abinka ga farar mace, kowane kaya tasa kyau yakeyimata, wani 'karamin hijab ta sanya shima 'kalar ruwan 'kasa tayi kyau abinta, duk da ta taso 'kauye bazaka kalleta ka kirata 'yar 'kauyeba, saboda bata irin shigar nan da 'yan 'kauye keyi na zani daban riga daban, ita tanasa kayanta complete, sannan kuma bata fiye sa gyale ba, yawanci kullum zaka ganta da hijab d'inta, gata da nutsuwa da kamun kai, shiyasa duk mutanen 'kauyen take burgesu. Kitchen ta iske mahaifiyarta tana faman girka masu abincin rana, tace "Inna zan d'an fita, Inna ta kalleta tace "ina kuma zaki Laraba,? "Inna inaso zanje gidansu indo ne naji kwana biyu ban gantaba, To shikenan Laraba kije Allah kiyaye hanya, tace "Ameen, sannan ta fice daga gidan. Inna kuwa har cikin ranta taji dad'in yanda d'iyarta ta saki jiki, dan rabon datace zata fita tun da rasuwar masoyinta sabi'u. Cikin nutsuwa take tafiyarta, kanta sadde dan batason yawan kallon da mutane suke mata. Dai-dai santar dazata sadata da gidan su indo ne taji kamar ana kiranta, waigowa tayi dan ganin me kiranta, Cikin nutsuwa ya iso inda take fuskarsa d'auke da murmushi, yace "Laraba kina lafiya, tace "Lafiya lao Haruna, ya'kara fad'ad'a murmushinsa yace "Laraba ashe kina ganuwa, itama mumushin tayi tace wace ni ince bani ganuwa, yace ay naga tun rasuwar sabi'u rabon da inganki sai yau tace kaidai bari Haruna, wallhi fitar ce yanzu kwata-kwata tayimin wahala yauma dan naga kwana biyu banga mutumniyarba shiyasa nace bari inzo inga ko lafiya, Haruna yayi murmushi yace "gaskiya ne 'kara da kika fito, nikau wallahi 'kawancenku yana birgeni keda lndo, duk 'kauyennan ba Wanda besanku tare ba. Murmushi kawai tayi tace "Haruna kenan, yace "Allah kuwa, duk 'kauyennan kuna burge mutane da dama kuma gashi kunsha bam-bam da 'yan matan 'kauyen, gurin nutsuwa da kamun kai. Tace "to mungode da wannan yabo damuka samu daga gareku, ni zan wuce kaga rana na 'karayi baniso in wuce azahar ban koma gida ba, Yace "to Amma idan bazaki damuba inaso zamuyi wata magana dake, tace "ina sauraronka Amma Allah sa bazata d'auki lokaci ba. Yace "inshaAllahu bazata d'auki lokaciba duk da bansan yanda zaki ji ba indan kikaji maganar dazan fad'a, bejira tafad'i wani abuba ya'kara gyara tsayuwarsa yace "watako Laraba a gaskiya na dad'e ina Sonki cikin zuciyata, ganin sabi'u yarigani ne kuma gashi har maganarsa takai ga iyaye yasa na ha'kura ban bayyana kainaba, amma yanzu tunda ta Allah ta kasance shine nace bari nazo da 'ko'kon barata ko Allah zesa a ki 'kar6eni in maye gurbin sabi'u a cikin zuciyarki. Tunda ya furta kalmar so, Laraba taji gabanta yayi wani mummunan fad'uwa, da kyar ta tattaro nutsuwarta, batare da ta kallesa ba tace "naji duka bayaninka amma inso kabani likaci inyi shawara. Yace "nabaki kwana biyu ko wace shawara kika Yanke zanji, tace "Allah kaimu yace "Ameen. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Da sallama tashiga gidansu lndo, innar indo ta iske tsakar gida tana wanke-wanke, ta dur'kusa har 'kasa ta gaisheta, "inna ina wuni, cikin fara'a ta amsa "lafiya lao Laraba yau kece a gidan namu, tayi murmushi tace "nice inna, indo nanan kuwa? "Tananan da yanzu ma take cemin zata gidanku, ki isa mana. Cike da murna indo ta tarbeta, 'kawata sannu da zuwa, wlh shirinnan da kika ga inayi gidanku zani, Laraba tace "sai kuma gani nazo, lndo tayi dariya tace "ay naji dad'in zuwanki, dama jiya Hashim yazo gidannan yabani sa'ko gurinki, Laraba cikin halin rashin damuwa da maganar da lndo zata fad'a mata tace sa'ko kuma, lndo tace kwarai ko, dan abinda na dad'e ina gaya maki ne ya tabbata, Hashim dai yace inmi'ka 'ko'kon bararsa gareki, yace wlh ba wasa yakeba sonki yake, kuma baza'a d'auki lokaciba yakeso ayi aurenku. Laraba tayi murmushi tace "yanzu ma kan hanya Haruna yatsareni da surutu waishi a dole yana sona, lndo tayi murmushi tace "inkon Allah, to yanzu yazamuyi kenan? Laraba tace "yafa zamuyi addu'a zamuyi Allah za6amin abinda yafi Alkhairi, indo tace hakane Allah shige mana gaba, Laraba ta amsa da "Ameen. Ranar gidansu indo Laraba ta wuni, sai bayan la'asar takoma gida. Zaune ta iske innarta cikin inuwar bedi tana hutawa, d'aki tawuce tacire hijabinta sannan tadawo ta zauna kusa da innar, tace inna sannu da hutawa, tace "yauwa har kin dawo, tace nadawo innna. Inna ta kallata tace bayan tafiyarki, saratu yayar Hashim tazo gidannan, wai Hashim ya turota yana sonki idan anbashi dama kuma kin amice Aurenki zeyi, cike da kunya Laraba ta sadda kanta 'kasa ta gayama inna yanda sukayi da lndo, sannan kuma ta gayamata shima Haruna yana sonta, inna tace "to dukansu dai basuda makusa amma ni aganina Hashim kamar zefi, kuma idan kikayi la'akari da hidimar daya dad'e yanayimaki idan kika gujeshi yanzu kamar munyi butulci ne. Laraba tace "inna nidai duk Wanda kika za6amin shine za6ina, fatana kawai kitayani addu'a Allah za6amin abinda yafi Alkhairi. Inna tace "Ameen. πŸ–ŠZee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:10 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [20/08 6:36 pm] πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 7⃣to8⃣```Page``` πŸ–Š Soyayya me 'karfi ta 'kulle tsakanin Laraba da Hashim duk 'kauyen mutane sun gama sanin Hashim ne ze Auri Laraba. Haruna kuwa hakuri Laraba tabashi akan soyayyar daya nema daga gareta, bata za6e Shiba, A ranshi yaji ba dad'i amma sai ya nuna bedamuba, yayi mata fatan Alkhairi. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Inna na zaune gidin bedi tana tsintar wake wanda zasuyi sanwar rana, tajiyo sallamar mal Lawal, Wanda ya kasance 'kanine ga mahaifin Laraba, da fara'a inna ta amsa sallamar "a'a mal Lawal ne sannu da zuwa, jiki na 'kyarma taje ta d'auko tabarma ta shimfid'a mashi. Mal Lawal mutum ne d'an bala'i bayada mutunci ko kad'an shiyasa lnna ke binsa ahankali dan tasan duk garin Laraba batada mahaifin daya wuceshi, Yayinda shikuma yake amfani da wannan damar yanayimasu yanda yaga dama. Laraba ma masifar tsoronsa takeyi, hakan yasa tanajin shigowarsa gabanta yayi mummunan fad'uwa dan tasan akwai abinda yakawo shi, Zuwa tayi har gabansa ta dur'kusa ta gaisheshi, cike da gadara da nuna isa ya amsa, sannan ta mi'ke taje ta d'auki tukunyar 'kasar data kasance ta ebar ruwansu, ta yafo gyalenta tazo gaban inna tace "inna zanje d'ibar ruwa, inna ta kalleta, tariga tasan dalilinta na son tafita, saboda haka bata hanataba, tace to Allah bada sa'a tace "Ameen sannan tafice. Kamar jiran fitarta yakeyi, ya maida hankalinsa ga inna yafara magana cikin bala'i da d'aga murya, "Hinde dama gurinki nazo, watako banida daraja a idonku dan baku d'aukeni bakin komeba keda d'iyarki, shine har yarinyar nan tana soyayya da wani ba'a sanar daniba dan an d'aukeni mahaukaci Wanda besan abinda yakeyiba. Tunda yafara masifarsa lnna bata d'aga kai ta kalleshiba, saida yagama, sannan tace "Allah baka ha'kuri, dama wallahi yau nayi niyyar inzo dakaina har gida ingaya maka. Ya tari numfashinta cikin masifa, yace "sai kuma gani nazo, to duk da bakison sanyani cikin Al'amarinki baki isa ki rabani da Laraba ba, saboda Laraba batada Uban da ya wuceni duk fad'in 'kauyennan. "To duk da baki tura shi Hashimun gurinaba yaje ya sameni munyi magana, kuma yatura magabatanshi mun tsaida maganar aurenshi da Laraba nan da sati ukku idan Allah ya kaimu. Inna tace "Allah kaimu Allah sa muna raye, ta tashi tashige d'aki tana matsar kwalla, kusan duk randa mal Lawal yazo gidan sai inna ta zubar da hawaye. Nan yagama zamanshi yanata zazzaga masifa marar dalili, ta inda yake shiga ba tanan yake fitaba, lnna kuwa tana d'aki tana jinshi har yagaji ya'karama rigarsa iska. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Zaune suke kan wani dutse 'kafafunsu na cikin ruwa, da Alama sunajin dad'in yanayin gurin, Hashim ya kalli Laraba yace "Am Laraba na manta ban sanar dakeba, jiya baffanki yasameni yace intura magabata na, yanzu haka kafin infito nabaro su baba bala sun tafi, Wata irin kunya takamata tasa hannu tarufe fuskarta, tace "kace munkusa zama miji da mata, Hashim yayi dariya yace "Allah dai yacika mana burinmu, wlh Laraba dan bakisan yanda nake sonkiba, ina maki 'kaunar da duk cikin masoyanki babu wanda yata6a yimaki makamanciyarta, Wani lokaci nakan zauna inta tainani, inga kamar baffanki baze bani keba, sai inji gabana yayi wani mummunan fad'i. Laraba ta kalleshi cike da tausayawa, dan ko ita tagama yadda da son da Hashim yake mata bana wasa bane tace "ka kwantar da hankalinka masoyina indai muna raye inshaAllahu bakada wata mata bayan ni. Cike da jin dad'in kalamanta Hashim yace "Allah sa tace "Ameen. Haka ta Ebi ruwan Hashim d'in ya d'aukar mata suka kama hanyar gida suna tafiya suna tad'i cike dajin dad'i. Saida suka kawo gab da gidansu Laraba sannan yami'ka mata tukunyar ya tsaya nan saida yaga shigarta sannan ya wuce. Da sllama tashiga gidan, inna tayi saurin 'kar6ar ruwan dake kanta, tace "Laraba kindawo, Kallo d'aya tayima innar tata tasan tana cikin 6acin rai, tasan arina _(wai ansaci zanin mahaukaciya)_ muddin ldan baffa Lawal yazo gidan to dole sai inna ta zubar da hawaye. Bata ko tambayi inna dalilin 6acin ranta ba, tashiga rarraahinta tana bata ha'kuri. Inna ta kalleta cike da tausayawa tace "Laraba 'kanin mahaifinki yazo, ko ban fad'aba kin riga kinsan halinsa, yace ya sanya bikinki da Hashim nan da sati ukku, ina ro'konki da dan Allah kada ki d'aga hankalinki ki zamo me biyayya sai kiga an zauna lafiya. Laraba bataji komeba dangane da abinda mahaifiyarta ta fad'a mata sai cewa tayi "inna kitayani Addu'a Allah za6a min abinda yafi zama Alkhairi a rayuwata, inna ta share wasu guntayen hawaye tace, tashi kiyi wanka ga abincinki can gindin bushiya, cikin langa, ba musu ta ebi ruwa cikin bokiti tafad'a kewaye, inna kuma tacigaba da matsar kwallar tausayin yarta. πŸ–ŠZee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:10 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [21/08 8:18 am] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 9⃣toπŸ”Ÿ```Page``` πŸ–ŠRanaku suna wucewa lokaci na tafiya, yau saura kwana hud'u d'aurin Auren Laraba da masoyinta Hashim Hidima sosai 6angarorin guda biyu sukeyi, lnnar Laraba kuwa bata wani damu ba game da abubuwan da ake bu'kata gurin biki, saboda dama tanada kome ta tanada, sai d'an abinda ba'a rasaba, 6angaren Laraba kuwa yau sun fita gayya itada 'kawarta indo, sun gayyato 'kawayensu da dama wad'anda mafi yawansu sunada aure, marassa auren basuda yawa, wasu ma harda 'ya'yansu. A gajiye suka dawo, gidansu indo suka sauka, lnnar indo tayi masu sannu, Sannnan suka wuce d'aki suka cire mayafansu suka fito suka d'aura alwala suka gabatar da sallar la'asar sannan lndo ta d'auko masu abinci suka fara ci, dambun masara ne yaji zogale, sai 'kamshin man gyad'a ke tashi, Sun kammala indo ta d'ebo masu ruwa me sanyi a tulu suka sha, sannan suka cigaba da tattauna yanda shirin bikin ze kasance, sun shirya taron 'kawayen amarya ana gobe d'aurin Aure. Sai gab da magrib suka fito indo zatayima Laraba rakiya ta tafi gida, suka gamu da ilu saurayin lndo, Laraba ce tafara gaidashi, ya amsa cike da fara'a, Sannan lndo ta gaidashi cike da jin kunyarsa, ya amsa sannan ya maida dubansa ga Laraba cikin tsokana yake magana "Amarya baki laifi,.... Laraba tayi saurin tarbarsa "kada dai ka ida wannan magana dan ba yanda za'ayi mutum yakashe d'an masu gida ace beyi laifi ba, kai ko kazar masu gida marya takashe sai tayi laifi barantana d'a. Suduka sukasa dariya, ilu yace yanzufa nan da kwana hud'u kinzama marya, tayi dariya tace kai kuma nan da wata d'aya kazama ango, yace "inshaAllah ga kuma amaryata, ya nuna indo ya wani kashe mata ido, cike da jin kunya indo taja hannun Laraba tace zomuje dan Allah yamma na'karayi, haka suka wuce suka barshi cike daso da 'kaunar indon sa. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Yau Yakama Alhamis, kuma daren d'aurin auren indo, Yau ne kuma suke taro da 'kawayenta, sun taru gidan wata mata nan makwabciyarsu, anata shewa, Kowa kagani cikin farin ciki, abin Alhamdulillah. Indo ce tafito cikin shigar sabuwar atamfa riga da zani d'inkin yayimata kyau, duk da simple ne d'inkin amma ya'kara fito da kyawunta, Kafarta tasha 'kunshin Jan lalli, tayi kyau tafito amarya sak _(amma a 'kauyensu)_😜 Sun zauna Kowa na yaba kyawu irinna Laraba, wata daga cikin 'kawayensu me suna hansai tace "gaskiya Laraba kinada kyau, inama ace yayana ne ze aureki ki ri'ka haifo masa kyawawan 'ya'ya masu Kama dake. Murmushi kawai Laraba tayi mata dan tasaba jin haka 'kawayenta da dama sunaso ta auri yayyensu. Hansai ta matso kusa da Laraba ta rad'a mata a kunne, wallahi yaya habu ya d'ad'e yana sonki, abinda yasa be furta maki ba dan yaga lokacin bashida 'kud'i, tun bayan rasuwar masoyinki na farko, yanzu kuma yadawo daga birni yayi kud'i, amma sai yadawo da rashin sa'a ya iske saura sati d'aurin aurenki. Wani mummunan fad'uwar gaba Laraba taji lokacin da hansai ta tuna mata da rasuwar saurayinta, sai lokacin ta tuna da samari biyu nefa aka saka masu rana sai ana gab da d'aura masu aure suka mutu. Wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta tasa gefen mayafinta ta goge, cikin ranta tace _(Ya Allah kada ka kashe Hashim Allah sa muna da rabon kasancewa inuwa d'aya nida shi)_ Ganin Laraba na hawaye yasa hansai tayi shiru da maganar datake tace "dan Allah kiyi ha'kuri idan maganata ta 6ata maki rai, bata jira jin abinda Laraba zatace ba ta tashi ta koma cikin 'kawaye aka cigaba da labari, amma tana yawan satar kallon Laraba dan ganin yanda lokaci d'aya hankalinta ya tashi. Indo tafito da biskit da cingam wanda suka kulla cikin ba'kar leda tashiga rarrabawa, saida ta tabbatar da Kowa ya samu sannan takoma kusa da Laraba ta zauna, tin tana cikin rabon kaya ta lura da 'yanda 'kawar tata take cikin wani irin yanayi. Sai gab da magrib 'kawayen amarya Kowa ya watse, lokacin lndo da Laraba suka wuce gidan su Laraba. Gidan cike yake da 'yan'uwa da abokan arzi'ki, anata hidima, nan suka gaisheda mutanen dake tsakar gidan sannan, suka wuce d'aki. Suna shiga Laraba ta cire mayafinta ta zauna da6as kan tabarmar dake shimfid'e tsakar d'akin jikinta ba 'karfi ko kad'an, Indo ta kalleta tace "Laraba na lura dake tun d'azu baki cikin nutsuwarki, wai me ke damunki? Wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanunta tace, "lndo jikina duk ya mutu, hankalina yakai 'kololuwa gurin tashi, gani nake Hashim mutuwa zeyi kamar yanda, lro da sabi'u suka mutu... ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi. Indo tace ki daina wannan tinanin acikin ranki, dan Allah ki daina kuka inshaAllah Hashim baze mutuba, ay mutum baya mutuwa sai kwananshi sun 'kare, suma da suka mutu dama Allah ya 'kaddaro hakan ne garesu. Nan lndo tarin'ka rarrashinta, sai bayan isha'i sannan tabar gidan cike da tausayin halin da 'kawarta take ciki. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Rana bata 'karya sai dai uwar d'iya taji kunya``` 'Daruruwan mutane sun taru 'kofar gidansu Laraba domin halartar d'aurin Aurenta. Yayinda itakuma a ranar ta tashi sukuku, jikinta ba 'karfi ko kad'an, matar 'kanin babanta ce mal Lawal ta matsa mata tayi wanka ta shirya cikin wata koriyar atamfa, riga da zani sannan tayi mayafi da kalar zanin atamfar, A 'kofar gida kuma yan'daurin aure sungama taruwa dangin ango kawai ake jira a d'aura aure, amma shuru basu ba labarinsu, Mal Lawal yagama 'kulewa shiru kawai yayi, jira yake dangin angon suzo sai ya sauke masu ta cikinsa snnan a d'aura auren. Bayan kamar minti talatin mal Lawal yanata cika yana batsewa, sai ya hango ml bala tare da wasu mutane guda biyu suna tinkaro su. Cike da bala'i mal Lawal ya mi'ke dan ya saukema mal bala ta cikinsa, sai mal bala yafad'a mashi wata magana wacce ni kaina bansan meya fad'a ba, sai ji nayi ya rafka uban salati, nan mutane suka taso suna tambayarsa "meya faru?. Cikin gida kuwa mata sunata tsegumin an'ki d'aura aure an shanyasu, jira suke a d'aura atafi da amarya gidan mal Lawal daga can za'a d'auketa akaita gidan miji. Baba salame ce wata makwabciyarsu tashigo gidan hankali tashe, bako sallama, da sauri mutane sukayo kanta ana tambayarta "meya faru? Sai ta fashe da wani irin kuka, wata magana tafad'a masu bansan me tafad'aba saboda cikin muryar kuka tayi maganar sai jinayi suduka sun d'auki salati. *To fah πŸ€” nifa ansani aduhu😱 miye ake fad'a wanda yake tada hankalin mutane πŸ˜­πŸ™†πŸ»* _ku biyo zee mmn khady dan jin cigaban labari_ _08166169254_ πŸ–ŠZee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:10 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [21/08 12:15 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 1⃣1⃣to1⃣2⃣ πŸ–Š zaune take d'aki tasha lulli6in zanin atamfa, wani mummunan fad'uwar gaba taji, kawai sai jitayi hawaye suna gangarowa daga idonta, suna diga bisa jikinta. Hayaniya tajiyo a tsakar gidan, a tunaninta an d'aura auren ne amma koda ta 'kara saurarawa sai taji sa6anin haka *_Dukkan me rai mamacine, Allah ji'kan hashim_* Wata uwar 'kara ta saki tare da fashewa da wani irin kuka, wanda yajawo hankalin mutane zuwa gareta, Lokaci guda tanemi numfashinta ta rasa, ta fad'i 'kasa sumammiya, nan fa aka shiga tsananin tashin hankali, inna tayi saurin tallafota tana kuka, tana kiran sunanta, da sauri aka d'ebo ruwa aka yayyafa mata sannan numfashinta ya dawo, amma duk da haka batasan inda kanta yakeba. A ranar dai anga tashin hankali, mutanen dasuka taru d'aurin Auren Hashim sune sukayi jana'izarsa, Bayan an kaishi makwancinsa aka dawo aka cigaba da zaman makoki, mutane kowa na Al'ajabin yanda mutuwar Hashim ta kasance, dan kuwa ranar saida abokaninsa duka suka taru, yashiga wanka bayan yafito ya shirya cikin farar shaddarsa, har sun fito zasu tafi, yace masu kanshi na ciwo zeje chemist ya siyo magani. Har wani cikin abokanin yace bari yaje ya siyo mashi, amma sai yace ya barshi kawai zeje da kanshi, haka yatafi yabar abokaninsa suna jiran dawowarsa su wuce gurin d'aurin auren, Sun kai kimanin minti arba'in suna jiransa amma shiru,saboda haka suka Yanke shaawarar binsa. Innalillahi'wa,inna,ilaihirraji'un suka furta, lokacin da suka hango Hashim kwace cikin ciyayi, ga jini duk ya 6ata farar shaddar dake jikinsa, amma ba Alamar rauni jikin sa. "To ta ina ya samu wannna jinin? Tambayar dasuka rika yima Kansu kenan wacce basuda amsarta. Nan suka d'aukeshi suka nufi gida hankali tashe, Kafin kace miye labari yagama baje gari, abunka da 'karamin gari duk inda kanufa maganar akeyi, dan wasu har sun fara yima abun wata mummunar fassara, *_°Bayan sati biyu_*° 6angaren Laraba kuwa tun rasuwar Hashim batasan inda kanta yakeba sai yau tadawo hayyacinta, abin mamaki batayi maganr mutuwar Hashim ba, kawai tacigaba da hidimominta, Wanka tayi ta shirya cikin, sabuwar atamfarta d'aya daga cikin wacce aka kawomata na lefen aurenta, da aka maida gidansu Hashim suka 'ki kar6a, Kwalliya tayi sosai, tayi gwanin kyau abunka ga 'kya'kyawa duk yanda tayi kwalliya yimata kyau take, duk da tana tashin 'kauye, gyale ta dauko ta rataya kafad'arta tazo gaban inna tace inna zanje gidansu lndo, inna ta d'ago idanunta ta kalleta cike da damuwa, da mamakin yanda halayyar Laraba ta canja bayan rasuwar Hashim, tace "haka zaki fita Laraba yakamata ki sanya hijab d'inki, ta turo baki tace ni gaskiya inna bazansa hijab ba kamar wata me takaba, lnna ta girgiza kai cike da takaici da kuma mamakin abinda ke damun 'yarta wanda har zatayimata magana tace ba hakaba, wanda da ba halinta bane. Koda taga Inna batada niyyar mata magana kawai sai tasa kai tafice, tace "saina dawo, cike da takaici inna ta matse kwallan dasuka taru idonta tace "Allah maidoki lafiya. Tafiya take hankalinta kwance abinta, ga gyalenta rataye a kafad'a gashi ta wani kashe d'aurin d'an kwali, Kan hanya kuwa duk wanda yagamu da ita cikin wannan yanayin sai yayi mamaki, kafin kice me mutane sun fara tsorata da Al'amarinta. A zaure ta iske indo da saurayita ilu suna zance, Wanda yau yarage saura sati d'aya bikinsu, dama suna cikin tattaunawa ne akan maganar Larabar ne, inda ilu ke garagad'in indo a kan ta rabu da laraba indai har tanason su shirya, sai gata tashigo, ta kalli ilu cikin sakin fuska tace ango kasha 'kamshi,... Wani irin fad'uwar gaba ilu yaji lokacin daya jad'a ido da Laraba , saboda haka jiki na kyarma yayima lndo sallama yabar gidan. Cike da mamaki lndo ta kalli Laraba, tace "kawata yau kece da wannan shigar abinda ban ta6a gani kinyi ba, Laraba tayi dariya tace "lndo kenan yo kuma kullum haka zanta yawo da hijabi kamar me takaba, ay nan gaba ma ko gyalen barin sawa zanyi. Cike da mamaki indo tace "to Allah ya 'kyauta, sannan suka wuce cikin gidan. Innar indo na zaune tana shan iska taji shihowarsu, Laraba ta gaisheta, wani mummunan fad'uwar gaba taji da ganin Laraba, dan taji rad'e-rad'in da akeyi agari, *aiko dole tasan yanda zatayi taraba 'yarta da Laraba tun kafin suma ta kashesu. Indo ce ta lura da yanda mahaifiyarta tashiga dogon tunani tace "inna Laraba na gaisheki ko bakijiba ne? Firgigit tadawo daga dogon tinanin datake ta washe baki tana ya'ke tace lafiya lao. πŸ–ŠZee Elkaseem Mmn khadyπŸ’‹ [10/16, 8:10 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [21/08 4:53 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 1⃣3⃣to1⃣4⃣ ```Bayan kwana sha ukku``` Yau ake taron 'kawaye na lndo, gobe kuma d'aurin aurenta, 'kawayenta ne cike ma'kil da gida anata shewa, Kowa kagani cikin farin ciki, hansai ta kalli lndo tace "waini indo ina Laraba naga tunda nazo ban gantaba, lndo tayi murmushi tace "tun d'azu muna tare ta koma gidane ta shirya, amma nasan tana gab da dawowa, hansai tace Allah sarki, sai ta tashi ta goya d'anta tace "to amarya ni zan wuce sai kuma gobe idan Allah ya kaimu, lndo tace "kai hansai tun yanzu bazaki bari Laraba ta dawo tabaki biskit d'in ba? Hansai tayi dariya tace a'a ba kome wlh ay zan dawo gobe, kafin tarufe Baki suka jiyo sallamar Laraba, aiko ko kallon inda take Hansai batayiba tasa kai tafice daga gidan, Can sai wasu gun-gun 'kawayensu suka taso suma sun kai su goma suka ce "muma dai mun wuce, cike da mamaki lndo ta kallesu "tun yanzu baku bari ajima, tare suka had'a baki suka ce "a'a akwai inda zamu ne, suka sa kai suka fice, in takaita maku labari shigowar Laraba gidan saida yasa duk mutanen dake gidan suka tafi. Indo tasan dalilin tafiyarsu, har ga Allah bataji dad'iba amma ba yanda zatayi, ta dad'e da sanin mummunan zaton da mutanen 'kauyen keyima Laraba, wasu guntayen hawaye suka zubo daga idonta tasa hannu ta goge batare da Laraba ta kula da halin datake ciki ba. Ranar dai haka suka gama yinin, abin ba dad'i. Laraba kanta ta fahimci yanda mutanen garin ke gudunta, a zuciyarta tace _"me nayima mutane suke guduna_ *_Innalillahiwainnailaihirraji'un_* Tafad'a tare da goge wasu zafafan hawaye. Washe gari aka d'aura auren lndo da ilu, da dare aka kai amarya, Ranar Laraba taga tashin hankali, dan 'kiri-'kiri mutane suke nuna tsana da tsangwama da 'kyama gami da tsoro agareta. Hakan yasata barin gidan bikin batare da ta shirya ba, lndo ta tausayama 'kawarta, cike da tausayi take mata addu'a Allah ka yayemata abinda ke faruwa da ita. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Kiyi ha'kuri kinji Laraba, inshaAllah kome ze wuce, kiri'ka addu'a kinji Allah yaye maki matsalar dake tattare dake, wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanunta tasa hannu ta goge "yanzu shikenan inna babu ni babu maganar Aure duk namijin dayace ze aureni da lokaci ya gabato sai a wayi gari ya mutu, gashi nazama abin tsoro cikin mutane duk inda naje sai afara barin gurin, ta'kara fashewa da wani sabon kuka. Inna har cikin ranata take tausayama d'iyarta, itama hawayen take, tace "kiyi ha'kuri Laraba ki d'auki wannan matsayin kaddara, inshaAllah wata rana kome ze zama labari. Nan lnna tayita rarrashinta tana kwantar mata da hankali, Harta samu tayi shiru tace "tashi ki d'au tukunya ki d'ebo ruwa kiyi wanka, ba musu ta tashi ta dauki 'yar 'karamar tukunya tanufi rafi, bako gyale jikinta barantana hijab wanda har ta manta yanda ake sanyashi, inna tayi fad'an harta gaji ta 'kyaleta Haruna ta hango zaune cikin gonarshi shida wani abokinshi suna cin gyad'a me 6awo, suna fira, abokin nashi ne yafara hangota ta doso inda suke, cikin dabara ya tashi yacema Haruna "ina zuwa bari in d'an zagaya can wlh jiya naci wata tafasa tad'an 6atamin ciki. Haruna yace "Allah sauwa'ke, ya mi'ka mashi ruwa, ya amsa yawuce, yayi nesa kad'an ya hango Laraba ta iso inda Haruna yake zaune tanayimashi magana, a fili yace "Allah nagodema da Laraba bata riskeni gurin can ba, da sauri ya 'kara gaba yayi cikin gari yana tinanin yanda abokinshi ze rabu da Laraba *Mayya* la'kanin da mutanen 'kauyen suka fara kiranta dashi kenan dan su acewarsu mayya ce shiyasa duk wanda yace yana sonta take cinye kurwarshi ya mutu. Da fara'a take magana "Haruna dama ina nemanka, cike da tsoro ya kalleta, duk illahirin jikinsa kyarma yake amma bakinsa yakasa furta kome, Bata kula da halin dayake cikiba tacigaba da magana, "waini Haruna ya maganar soyayyarmu, tunda Allah besa anyi da Hashim ba mizai hana ka dawo a d'aura mana aure. Sai lokacin yasamu yayi magana cike da tsoro bakinsa na 'kyarma yace "Laraba dan Allah kiyi ha'kuri ni wallahi tuni nafasa yin Aure, bazanyi Aureba kwata-kwata..... Cike da mamaki Laraba ta 'kara matsowa inda yake tace bazakayi aureba fa kace Haruna, nice fa Laraba ka manta irin soyayyar da kace kanayi mani, a da, Yace "a da ba amma yanzu na daina soyayya kiyi ha'kuri, Laraba ta'kara matsowa kusa dashi yana matsawa "Haruna nice Laraba baka ganeni ba ne? Cike da tsoro yace "na...na..ganeki mana, haba sai lokacin yasamu ya ranta a na kare πŸƒπŸ» Mamakine tare da takaici da ba'kin ciki suka rufe Laraba ta dur'kusa nan tana kuka. _Allah sarki laraba na tausaya maki_ πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:10 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [22/08 7:26 am] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 1⃣5⃣to1⃣6⃣ πŸ–ŠZaune suke sun buga uban tagumi, Laraba na zubar da hawaye itama lnna hawayen take zubarwa dan taji yanda ake maganar Laraba a 'kauyen mutane suna kiranta *mayya* tasa hannu ta goge hawayen dake idonta, abinda yafaru da ita jiyane yashiga dawo mata a kwalwa, shikenan yanzu abin Laraba har inna yake shafa, dan jiya akayi bikin wani d'an Aminiyarta, wacce a da matar taso ace d'anta Laraba ya aura amma Allah be nufaba, lnnar Laraba batada aminiya wacce ta wuceta, amma har aka fara biki ba'a gayyacetaba, saboda haka tace bari taje tayi mata Allah sanya Alkhairi, Haka ta shirya ta nufi gidan, tana isa zauren gida, magan-ganun dataji anayi gidanne yasa hantar cikinta juyawa, Muryar mata taji daban-daban suna magana "wah ay Laraba ta fiddo maitar ta fili, yanzu fa mutum ukku ta kashe 'kauyennan kinsan kuwa maitarta takai inda takai, can wata mata ta kar6e zancen "ay ance gado tayi gurin mahaifiyarta, dan ance ita ta kashe mahaifin Larabar, muryar wata matar taji tana cewa "to mudai uwar biki Allah sa baki gayyato mamu suba, dan nasan bakida Aminiya kamarta, can sai tajiyo muryar amiyar tata tana cewa "a da ba, amma banda yanzu dan ban gaji da rayuwaba inaso inga auren auta ta har inga jikokina, suduka sukasa shewa "heyyyyyy, wata tsagerar mata takama hanci ta rangad'a guda "ayyuririiii,......... Innar Laraba najin haka wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta, zuciyarta tayimata nauyi, kanta yayi wata irin Sarawa, take ciwon kai me tsanani ya saukar mata jitake kamar kanta ze rabe, haka ta dafe kanta tanufi gida cike da takaici da ba'kin cikin magan-ganun data ji, dan gidan bikin da bata shiga ba kenan, Kan hanya ma duk wanda tayima magana sai taga ya matsa da Alamar tsoro tattare dashi baze ko amsa maganar ba, Wasu kau dasun hangota suke rugawa, abin ya matu'kar d'aure mata kai. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Yanzu kai habu larabar kake so, kana ganin yanda mutane ke gudunta, amma kai karasa wacce zaka za6a sai ita, kuma kariga ka gama sanin *mayya* ce, habu ya kalli abokinsa cike da takicin kalmar mayya daya furta ga Laraba yace "eh ni ina sonta koda zata ri'ka yankan naman jikina tana ci d'anye 'karewar maita zan aureta, abokin nashi yace to "Allah raka taki gona, nidai kaga tafiyata, kuma muddin kasani idan kana tare da Laraba to abotarmu ta 'Kare, habu yayi wani guntun murmushi mai d'auke da takaici yace, Allah had'a kowa da rabonsa, rabuwar habu kenan da abokinsa. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Zaune suke sunyi tagumi duniya tayi masu zafi itada innarta, dan fitama wahala take masu kullum suna gida basuda aiki sai tinani sai kuka, Rabon kau da wani mutum yashigo gidansu har sun manta, Itako Laraba da gidan lndo kad'ai take zuwa taji d'an dad'i-dad'i shima yanzu yaushe rabon dataje, tun ranar dataje ilu yayimata wula'kanci yace kada ta 'kara zuwar mashi gida idan kuma bata dainaba hukuma zata rabashi da ita, Suna cikin wannan yanayin sukaji an bankad'o kyauren gidan kad'an yarage a karyashi, mal Lawal ne yafara magana cikin bala'i da masifa, watau kin koyama d'iya maita tana kashe mutanen gari, to wallahi ba maitaba ko uban maita ke gareki dole Laraba ta fito da miji inyimata aure, dan bazan yarda tana yawo agari ana zagina a matsayin mahaifinta na gaza aurar da itaba. Tunda yafara magana basu cemashi 'kala ba, saida yagama bala'i sannan ya kalli Laraba yace "waye kuma yanzu kike so wanda tsautsayi ke shirin afka mawa, Cikin kuka da bakin ciki tace "dama Haruna ne tin kafin rasuwar Hashim yake sona, mal Lawal yace "to bari yanzu inje in samu Haruna idan da gaske yake ya turo iyayenshi dan bazaki 'kara sati biyu a gidannan ba, sadaki kawai ze kawo a d'aura aure, haka yafita gidan yanata bal-balin bala'i, inna dai bata cemashi ci kanka ba illah kuka datakeyi. Haruna Zaune shida abokinsa suna fira, mal Lawal ya iso gurinsu, suka gaidashi ya amsa, sannan yace Haruna gurinka nazo kan maganar Laraba, wani irin fad'uwar gaba Haruna yaji, jin an ambaci sunan Laraba, mal Lawal be jira abinda Haruna ze fad'aba yaci gaba da magana, "tace kaine wanda ta tsaida shine nace ka turo magabatanka bamu bukatar kome daga gareka sadaki kawai zaka kawo nan da sati d'aya a d'aura maku aure. Haruna Wanda tinda mal Lawal yafara maganar jikinsa ke rawa kamar mazari yace "a'a ni maganar soyayayya bata ta6a had'ani da Laraba ba, kuma bani sonta, inaji ba dai ni harunan take nufiba A fusace mal Lawal yabar gurin da niyyar yaje gida yaci mutuncin Laraba da mahaifiyarta. Tinda mal Lawal yabar gurin jikin Haruna ke 'kyarma, ya kalli abokinshi yace kanafa jin wannan mutumin, abokin nashi yayi dariya yace "watako yarinyar nan tasaka a zuciyarta tagama kwad'aituwa da kai walh saika tashi tsaye, Kazo muje gidan kakata 'yar me ganye tana bada maganin mayu, Malam abaka kasha kayi wanka. Ba musu Haruna yace mutafi, Sun isa gidan 'yar me ganye anba Haruna maganin daze ri'ka ji'kawa yana wanka dashi sannan aka bashi tazargade yari'ka haya'ki, matar tace indai yana amfani da wannan badai maye ba, ko sarkin mayu sai dai yaganshi ya 'kyale. πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:10 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [22/08 6:41 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 1⃣7⃣to1⃣8⃣ πŸ–Š "lna 'yar iskar yarinyar nan take, dan ubanki kinsan babu soyayya tsakaninki da Haruna kika turani gurinshi, naje naji kunya, to bari kiji in gaya maki tunda dai kinzamar ma mutane bala'i kin zamar masu 'karfen 'kafa to zan aurar dake ga duk wanda naga dama,sannan ya juya gurin inna wacce tunda yafara fad'anshi ta kauda kanta gefe tana zubar da hawayen takaici, shin wai dame zasuji da tsana da tsangwama da tsoro da 'kazafin da 'yan garin kemasu koda masifa da bala'in mal Lawal. Yaci gaba da magana, cikin d'aga murya "Kara Ku yanke shawara tun kafin nan da kwana biyu idan kuma ba hakaba zan yanke duk hukuncin da naga dama, yasa kai yafice yanata kumfar baki. Yana Fita Laraba ta taso tafad'a jikin innarta ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi, itama lnnar kuka take amma duk da haka rarrashin 'yar tata takeyi. *```Bayan kwana Hud'u```* Inna ce ke rarrashin 'yarta wacce duk yinin yau kuka take, ko ruwa takasa sama cikinta saboda tsananin damuwa, tariga tagama sanin sunan da ake kiranta dashi a 'kauyen na *Mayya* "Kiyi ha'kuri Laraba duk tsanani yana tare da sau'ki, in Allah ya yarda duk masu gudunki sai sun dawo suna binki, kedai kiri'ka addu'a Allah yayi maki maganin matsakarki. Suna cikin wannan ne sukaji an bankad'o 'kyauren gidan, suduka suka maida hankalinsu ga 'kofar ganin 'kyauren sukayi 'kasa ya karye, kasancewar dama na langa-langa ne bayada wani 'kwari. Mal Lawal ne yabi ta kan 'kyauren yashigo gidan a sukwane, Laraba na jikin inna ta 'kan-'kameta duk tsoro yakamata gani take yau baffa Lawal dukan ta zeyi. Kudi ya watso jikinta yace "ga sadaki nan na d'aura aurenki da habu, yayan hansai, idan kin cika ke mayyace yau kada ya kwana da rai, tinda sauran kafin a d'aura kike kashesu, to wannan karan an d'aura kuma 'kurwarsa kur kuci kanku, *Mayu*. Wani irin kuka Laraba ta 'kara fashewa dashi, ta 'kara shigewa jikin innarta Wanda shi kad'aine yanzu take ra6a taji sanyi tace. "Shikenan inna bamuda Kowa bamuda Wanda zamu ra6a muji dad'i, abin takaici da ba'kin ciki wai hada baffa Lawal ake kirana *Mayya* to waye ma baze kirani da *mayya* ba tinda 'kanin mahaifina ma yakirani haka. Bayan magrib mal Lawal da kansa yazo ya tafi da Laraba tana kuka tana kome ya kaita gidan miji, basu iske kowa gidan ba amma duk wani Abu na Al'ada na tarbar amarya an kawo an aje masu, Haka baffa lawal ya ajeta yabar gidan, tunda Allah ya halicceta bata ta6a ganin irin wannan auren da akayimata ba, gashi dai ankawota gidan miji amma ba kowa sai ita kad'ai cikin gida kamar *Mayya* _(sunan da mutanen 'kauyen ke kiranta dashi)_ Ta fad'a kan soson katifar da aka kawota dashi wanda ko zanin kirki bayadashi, ta fashe da wani irin kuka, baiwar Allah Laraba tana cikin tashin hankali, duk tabi ta rame, ta kod'e idanun nan nata sunyi zuru-zuru, hancin ya 'kara tsawo sai wani uban 'kashin wuya daya fito yayi mata 'kwaro-'kwaro. A 6angaren habu kuwa yariga yasan an kawo amarya, yaje gun 'yan uwanshi yaro'kesu akan suje gidan ayi d'an shagalin bikin da akeyi bayan an kawo Amarya amma sukace "ina ay basu gaji da rayuwaba tukun, waye ze kai kanshi ga halaka. Indo kuwa taso zuwa bikin 'kawarta kuma aminiyarta, amma ilu ya bad'e ido toka yace bazataba, 'karshe data isheshi da magiya sai cewa yayi idan ta'kara maganar zuwa bikin Laraba to bakin aurenta, hakan yasa ta ha'kura badan ranta yaso ba. Bayan habu yagama fama da 'yan uwanshi akan suje gidanshi sun'ki sai yatafi gidan 'kanwarsa hansai, da sallama yashiga gidan, ta amsa sannan ta gaisheshi ya amsa, nan yake tambayarta "Hansai ya ban ganki gurin bikin ba, lafiya kuwa? Hansai ta yamutsa fuska tace lafiya lau, kaina ne yake d'an yimani ciwo, cike da tausayi yace eyyah Allah sauwa'ke tace Ameen. Yace Amma naga kamar kin d'anji sauki, kozaki daure ki le'ka gidan kai amaryar, Cikin firgici Hansai ta kalli yayanta tace "wah ni Yaya habu, idan ka ganni lahira kaini akayi, wallahi bazani gidan *mayya* ba. Cikin 6acin rai habu ya d'auke hansai da mari yace "idan bazakiba ki zauna, amma kada ki kuma kiran matata da *Mayya* yasa kai yafice ranshi a 6ace. Me zai faru yana fita daga gidan Laraba yagani tanayimashi murmushi, ta 'karso gurinshi tace masoyina nagaji da jira ne gida ni 'kad'ai shine na biyoka... cike Da mamaki yace "ya akayi kikasan ina nan, murmushi kawai tayi Mashi ta kama hannunshi suka nufi gida. πŸ–ŠZee Elkaseem Mmn Khady πŸ’‹ [10/16, 8:10 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [23/08 5:48 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 1⃣9⃣to2⃣0⃣ πŸ–Š Tafiya suke Laraba na ri'ke da hannun angonta Habu, sai da sukayi nisa da gari sun shiga gonaki, baka ganin kome sai duhun daji da kukan tsuntsaye, kasancewar akwai 'yar tazara tsakanin gidan Hansai da gidan Laraba, sun shiga cikin duhun ciyayi, Habu ya waigo ya kalli Laraba yace "Amma Laraba nayi mamakin yanda kika san ina gidan Hansai, kodai wani ya gaya maki ina nan? Shuru yaji tayi batada niyyar amsa mashi tambayar da yayi mata, hakan yasa ya juyo ya kalleta, suna had'a ido da ita gabanshi yayi mummunan fad'uwa dan ganin ta yayi ta d'ad'd'aure fuska yanda kasan tunda Allah ya halicceta bata ta6a dariya ba, ga fuskar tata tayi duhu, ba alamar haske tattare da ita, kamar ba larabar da yasaniba, kya'kyawar yarinya fara tas fatar ta kamar ka ta6a jini yafito, amma lokaci guda ta sauya takoma ba'ka, ga fuskar ba Alamun fara'a tattare da ita. Lokaci guda jikinsa yafara 'kyarma kamar mazari, yakasa matsawa daga inda yake, sai da 'kyar yasamu ya iya daga baki yace La....la....Lara...ba, miya sa kika biyoni, miyasa zaki tsoratar dani...... Kafin ya rufe bakinsa yaji ta gagga6e da wata irin mahaukaciyar dariya tace, "Tambaya kake yanda akayi nasan inda kake, to ayni ba sai na tambaya ba, tunvdaga ranar daka furta kalmar so gareni nake biye dakai, kuma kasani sai nazama ajalinka..... Hhhhhhhhhhhhhhhhh, ta 'kara gagga6ewa da wata nahaukaciyar dariya karo na biyu. Habu kuwa banda 'kyarma ba abinda yake, yariga yagama sad'aukar da rayuwarsa, dan yasan 'karshen rayuwarsa ne yazo, kwata-kwata kasa yin wata addu'a yayi dan tsananin tsoro, sun kai kimanin minti ashirin tsaye gurin Laraba, tana tsoratar da Habu. Sai zuwa can Allah yabashi ikon furta kalmar *lnnalillahiwa,inna'ilaihirraji'un* sannan yasamu 'kafar guduwa daga gurin, Gudu yake iyakar 'karfinsa, domin yau ya tabbatar ma kanshi maganar da mutane ke fad'a suna cewa Laraba *mayya* ce, a zuciyarshi yana cewa koma miye Nina jawoma kaina, dama ance _(Wanda beji bari ba yaji hoho)_.😱 Lokaci guda yahad'a wani uban gumi, ga tsabar tsoro ga kuma uban gudun dayasha, da kyar yashiga gida ya maida 'kyaure yarufe, yana maida numfashi. 'Daki yanufa yana nishi yana goge uwar zufar data rufeshi kamar wanda aka watsama ruwa, Mutuwar tsaye yayi dan wani babban tashin hankalin daya tarar a gidan, yasan dai yabaro Laraba a daji, amma kuma yanzu gata ya tarar da ita kwance kan 'yar katifarta tana kuka. Jin alamun shigowar mutum yasa Laraba tashi daga kwancen datake, ta d'ago da manyan idanunta wanda suka kad'a sukayi jawur saboda tsabar kukan data sha. Cike da mamaki Habu ke kallonta, a zuciyarshi yace "to wai miye ke shirin faruwa dani ne, kodai ba Laraba bace wacce nabaro a daji. Ganin bashida niyyar ida 'karasowa cikin d'akin yasa Laraba tayi magana "Sannu da zuwa, tafad'a cikin zazza'kar muryarta mai sanyin sauraro. "Yauwa yafad'a zuciyarsa na dukan ukku-ukku, "bari inje in dawo nayi mantuwa a gida, cike da tsoro Laraba tace "miye kuma ka manta, nifa wallahi tsoro nakeji ni d'aya gida, a zuciyarsa yace _"Ai kece abin tsoron laraba, ke yakamata aji tsoro bake zakiji tsoron wani abu ba_ "Tinanin me kakeyine, ta tambayeshi dan ganin ya tsaya a gun bayada niyyar tafiya, Yayi saurin dai-daita nutsuwarsa yace "a'a zanje bari intafi bazan dad'eba zan dawo, sannan yasa kai yafice, cike da tsoro yafita daga gidan, zuciyarshi cike da tunani kala-kala. Tafiya yake bekoyi nisa da gidan ba amma wani mugun abun tsoro daya gani shine yakusa sanya numfashinshi ya d'auke, dan Laraba yagani gabanshi, ta kashe d'an kwali ta ri'ke 'kugu tana jijjiga jiki, suna had'a ido ta gagga6e da wata mahaukaciyar dariya, sannan kuma ta d'aure fuska kamar bata ta6a dariyaba. Tace "Habu kana gan-ganci da rayuwarka, inaso kafin nan da safiya ka gaggauta yankema kanka hukuncin daze fitar dakai. πŸƒπŸ»Da gudu yayi baya yakama hanyar gidanshi, tashin hankali wanda ba'a samashi rana 😳 Laraba ya iske a tsakar gida tafito daga kewaye hannuta ri'ke da buta. Wata irin gigitattar 'kara yasaki nan take yafad'i 'kasa kanshi yabugu da wani dutsi dake tsakar gidan, aiko kan yafashe jini yafara zuba. _Innalillahiwa'inna,ilaihirraji'un_ Laraba tashiga furtawa, tanufi inda Habu yake kwance tana jijjigashi tana kiran sunanshi amma ba alamar numfashi tattare dashi. πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:10 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [24/08 2:03 pm] Zee Elkaseem: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 2⃣1⃣to2⃣2⃣ πŸ–Š "wayyo nashiga ukku dan Allah habu katashi kada ka mutu, idan kamutu nasan bazan 'kara shan ruwa garinnan ba, dan Allah ka taimakeni, Laraba ce ke fad'in haka cikin muryar kuka, Yayinda habu yake kwance har yanzu besan inda kanshi yakeba, ga kuma inda kanshi yabugu har yanzu zubar da jini yake, "Ya salam laraba tafad'a "Lallai rayuwata tana cikin had'ari ya Allah ka fitar dani, wasu sabbin hawaye suka gangaro kan kumatunta. Lokaci guda jikinta ya mutu li'kis kamar wacce akayima duka Ta tashi da sauri tanufi d'aki ta dauko wani tsohon zani cikin zannuwanta ta yaga ta d'aurema Habu kanshi inda jini ke zuba, cikin ikon Allah kuwa sai jinin ya tsaya, amma har yanzu ba Alamar numfashi tattare dashi, Sai lokacin dabarar ta yayyafa mashi ruwa ya fad'o mata a arai, da sauri tanufi randa ta d'ebo ruwa me sanyi ta yayyafa mashi, a firgice ya tashi yana "cewa "dan Allah kiyi ha'kuri Laraba kada ki kasheni, Laraba ni me 'kaunarki ne bekamata ki sakamin da sharri ba. Wata irin 'kara Laraba tayi, cikin wata gur6atacciyar magana take cewa, Habu bazan ta6a raga makaba, babu ragi ba ragowa tsakanina dakai, nariga na gaya maka kafin gari ya waye ka nemama kanka mafita, Cike da tsoro da firgici habu ya kalli Laraba, yaga fuskarnan tata ba Alamar sassuci, tabbass idan yaci gaba da zama da ita ze iya rasa rayuwarsa, hakan yasa ya yanke shwarar rabuwa da ita. "Laraba"yakira sunanta, Jiki a sanyaye ta juyo ta kalleshi, yace "kije na sakeki *Saki ukku* Daga yau babu ni babu ke, "Hhhhhhhhhhhhhh, wata irin mahaukaciyar dariya sukaji ta gauraye gidan, har tsawon minti biyar sannan dariyar ta lafa, wata irin murya sukaji wacce basu San daga inda take fitowaba ana cewa, "Yaro kayi ta barka, ashe kana son rayuwarka, aka sake bushewa da wata dariya, sannan sukaji d'if kamar anyi ruwa an d'auke. Wani matsanauncin tsoro Yakama Laraba dan jin wani sabon Al'amari, da gudu tanufi habu wanda shima jikinsa mazari kawai yake saboda tsananin tsoro tafd'a jikinsa ta 'kan'kameshi. Cike da tsoro habu ya finciketa daga jikinsa, yajata kiiiiii, ya turata waje yace "kije nace nasakeki *Saki ukku* ya maida 'Kofa ya rufe. Laraba ta shiga bugun 'kyauren gidan, tana cewa "Dan Allah habu ka taimakeni ka barni in kwana gobe sai intafi, haka ta rin'ka magiya amma bataji Habu yayi maganaba, hakan yasa ta kalli gabas ta kalli yamma kudu da arewa, ba Alamar haske, garin yayi duhu dind'um bakajin kome sai kukan tsintsaye, take wani mugun tsoro ya dira a zuciyarta. [24/08 2:38 pm] Zee Elkaseem: Wani irin haske ta hango daga nesa yana nufo inda take, tin tana kallonsa nesa da ita har yazo gab da ita, Wani irin matsanancin tsoro ya'kara kamata, Wata irin 'kara ta fasa sannan ta ranta a na kareπŸƒπŸ» °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Inna na kwance d'aki, kan guntuwar tabarmarta sai juyi take bacci ya gagari idonta, ba abinda take sai tinanin kowane hali 'yarta take ciki, Wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta, tasa hannu ta goge, Lokacin kuma taji Uciyarta tayimata nauyi kamar an d'ora mata wani katon dutse, lokaci guda taji yun'kurin amai, aiko tatashi zaune tafara amai, babban tashin hankalin da inna tagani duk yun'kurin datayi maimakon taga aman abida taci, jini ne take amayowa hadda gundarinsa, Cikin 'kan-kanin lokaci ta galaibaita tafita hayyacinta, Da gudu Laraba tashigo gidan, wata irin 'kara tasaki dan ganin halin da inna take ciki, sauri ta 'karaso gareta, takamata tana kuka tana kiran sunanata, inna....inna...inna... Da 'kyar inna ta iya d'aga ido ta kalleta tace "Laraba nasan tawa ta 'kare amma bazan gusheba inamaki addu'ar Allah fiddaki daga mawuyacin halin da kike ciki. Fad'uwa tayi rai yayi halinsa, ```Allahu akbar inna tarigamu gidan gaskiya``` Wata uwar 'kara Laraba tasaki, dan ganin inna ba Alamar numfashi tattare da ita, Wani irin duhu taga ya gufta mata, kokacin kuma kanta yayi wata irin sarawa, jiri ya ibeta ta fad'i kasa sumammiya,.... πŸ–ŠZee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:10 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [24/08 7:45 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 2⃣3⃣to2⃣4⃣ πŸ–Šwashe gari tunda asuba Habu yanufi gidan iyayenshi, yana isa innarshi taganshi da uban rauni a kai, ga jikinshi jage-jage da jini, dan be canja kayaba haka ya kwana, wani uban salati ta buga tace "Habu lafiya meya faru dakai, ina Larabar,? Lokaci d'aya ta jero mashi wad'annan tambayoyin, Habu bayaso ya fad'i gaskiyar Al'amarin abinda yafaru dashi saboda besan wani halin fad'in ze jefa laraba ba, saboda haka shiru yayima innar tashi. Innar taga bayada niyyar bata amsar tambayoyin datayi mashi, kawai saita d'ora hannu a kai tafashe da kuka, wanda yin hakan ya jawo da hankalin mutanen gidan garesu, duk akayo d'akinta ana tambayarta lafiya meya faru, dayake gidan irin gidan yawa ne, Ganin habu dasukayi zaune ga jini duk ya 6ata jikinsa yasa suka ba kansu amsa, tabbass koba tambaya sun san larabace ta tasarma kasheshi Allah beyiba dayake yanada sauran shan ruwa. Wata mata cikin mutanen dake tsai-tsaye Bakin 'kofar d'akin tace "ina kabaro amaryar angon Laraba? cike da takaici habu ya kallesu yace "Laraba na gidansu na saketa, Wani uban salati matan suka d'auka lokaci guda, sukace "yo habu ya akayi haka tafaru? Be basu amsaba illah fita dayayi yabar gidan dan bayaso ana can-cana maganar. Wata tsohuwar mata ta kalli innar Habu tace "Wallahi atika kinyi ta barka, dan wannan maganin da 'yar me ganye tabada tace ki binne a gidan, amma da badan haka ba da yanzu habu sai dai wani bashiba. Innar habu tayi murmushin takaici tace "Hmmm Wanda beji bari ba ay yaji hoho, cikin gidanan waye be ba Habu shawarar kada ya auri Laraba ba amma yakafe, ay dama me rabon shan duka bayajin kwa6a, bata jiran me sauran matan zasu fad'aba tashige d'aki tana matsar kwalla. Ganin haka yasa kowace takama gabanta, suna fad'in albarkacin bakinsu, Abinka ga matan 'kauye kad'an suke jira su 'kara, kafin kace me labari ya bud'e gari. Mutanen gari anata yayatawa, Laraba takusa kashe Habu Allah ya taimakeshi ya saketa. Aiko labari yakaima mal Lawal, a fusace yanufi gidansu Laraba da niyyar yaci masu mutunci itada uwarta wacce ke d'aure mata gindi tana kashe mutane. Bako sallama ya bankad'a 'kyauren gidan yashiga, Laraba yagani ta had'a kai da gwiwa tana kuka, gefe kuma ga innarta kwance cikin jini. "Ke.....ya daka mata tsawa, da sauri ta d'ago da fuskarta ta kalleshi, saitaji wata dama-dama a ranta, tunda tariga tasan inna tamutu, kuma batasan wa zata gaya mawaba, tunda mutane yanzu da sun ganta guduwa suke. Da sauri ta taso tazo gabanshi ta dur'kusa, yanzu kam idonta ba hawaye ko kad'an dan tayi kuka har hawayenta sun 'kafe, tace "dan Allah baffa Lawal ka taimakeni inna ta mutu, tun jiya da dare, ban san yazanyiba, shiyasa ban fitaba dan nasan duk inda na nufa ba wanda ze saurareni, Wata irin dariya mal Lawal yayi sannan ya kalli Laraba yace, "watako maitar taki har takai ga uwar data haifeki, to wallahi ki shiga hankalinki, danni idan kikace zaki cinyeni sai inci ubanki, 'yar iska kawai, yakai mata wani hauri har saida ta fad'i, sannan yafita yabar gidan. Zuwa yayi yasanar da mutane, innar Laraba ta mutu, amma kowa sai yace Allah ji'kanta, da ance suzo ayimata sutura akaita makwancinta sai kaga mutum yafara zame-zame Alamar dai baya zuwa. Haka akayita fama da muatanen Gari, karshe dai saida me gari yasa Baki, yasa liman da wasu tsirarun mutane akaje akayima innar Laraba wanka akayimata sutura aka kaita makwancinta, Kuka kau Laraba yanzu ta daina na hawaye, sai dai na zuci, dan zuciyarta tariga tagama soyewa, tasaba da ba'kin ciki da takaici. *_BAYAN KWANA BAKWAI_* Yanzu Laraba ita kad'ai ke kwana gidansu babu me ra6arta, ga yunwa dan ba wanda kebata koda sauran abinci, idan kuma tafita dan tasiyo abinda zataci dataje shago sai muatane sukama gudu, haka zata dawo gida takama kuka, abin dai gwanin ban tausayi, duk ta rame ta kod'e idanun nan sun kara fitowa sunyi zuru-zuru, ga wani ciwon ciki datake fama dashi sakamakon yunwar datake fama da ita, Ruwa kawai take banka ma cikinta koda yaushe, to yanzu ma idan tasha ruwan sai ya 'kulle mata ciki tayita amai, Yau dai tagaji da bala'in datake ciki, saboda haka tayi niyyar zuwa gidan baffa Lawal dan ya taimaka mata. πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:11 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [25/08 7:08 am] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 2⃣5⃣to2⃣6⃣ πŸ–Š Baffa Lawal ne cikin gonarshi yanata noma, yanayi yana 'yar wa'ka irin ta mutanen 'kauye, abin yayi masa dad'i har gyad'a kai yakeyi, zuwa can kuma sai yatashi yanufi inda ya ajiye kayansa ya fiddo da wata 'yar madai-daiciyar radio, yasanya sabbin batura ya 'kunna, ya kuwa yi sa'a gidan redio an sanyo wa'kar d'an kwairo, aiko sai ya rataye redion jikin bedi yana ji yana aikinsa, Befi minti shidda da kunna red'ion ba sai yaji d'if redion ta d'auke, ya d'ago kansa ya duba bega kowaba, yaje ya ta6a redion sai yaji kashe take, nan ya sake kunnawa ya maida yarataye ya juya ze cigaba da aykinsa sai yaji an 'kara kashewa, yana juyowa wa ze gani, Laraba ce tsaye jikin bedin tana yimashi wani mugun kallo, Cike da masifa da bala'i baffa Lawal ya tunkarota na niyyar ya wanka mata mari, amma kafin yayi wani Abu sai jin saukar mari yayi, a fuskar shi. Cike da tsoro yakai dubansa ga Laraba, wacce tana dai tsaye inda take ko motsi batayiba, wani wawan mari aka 'kara d'aukeshi dashi, lokaci guda kuma aka rufeshi da duka ta ko'ina, Laraba dai na tsaye har yanzu bata motsa ba, Haka akayita jibgar mal Lawal saida ya daku sannan aka 'kyaleshi, wata irin mahaukaciyar dariya Laraba ta she'ke da it'a sannan ta 6ace, mal Lawal yashiga rud'ani, hankalinsa yayi matu'kar tashi, jikinsa yakama 6ari, aiko da sauri ya tattare 'yan kayanshi yanufi gida, Ganin ya shigo hajaran-majaran yasa matarshi tamabyarshi, "mal lafiya, meya faru naga ka dawo tun 'yanzu gashi ko azahar batayiba, Mal Lawal bayaso yafad'i gaskiyar Al'amari dan kada mutane suyi Mashi dariya, sai cewa yayi "gajiya nayi kuma jikina ba dad'i d'an dafamin ruwan d'umi inyi wanka, cike da mamaki matar tace "ruwan dumi kuma malam πŸ€”, kaida idan kadawo daga gona kake son ka watsa ruwan sanyi amma yau ruwan d'umi kake nema, Aiko nan yarufeta da bala'i "keni banison shashanci, Idan zaki dafamin ki dafamin, idan kuma bazaki dafaba ni in tashi in dafa da kai......... Be ida rufe bakiba, Laraba tashigo gidan da sallama, mal Lawal naganinta jikinsa yafara kyarma, yace "la......la....la...raba miya kawoki nan? Ba yanzu kikaje gona kika sameni, Cike da ladabi Laraba ta dur'kusa har 'kasa tace "wallahi baffa banje gonarkaba, ni yanzuma daga gida nake, dan Allah baffa ka taimakamin da abinci yunwa nakeji, Cike da tsoro baffa Lawal yace "bamu dafa ba, ki koma idan mun dafa zan kawo maki har gida, jiki ba 'kwari Laraba tanufi hanyar fita daga gidan, matar baffa Lawal ce taji wani irin tausayinta yakamata, ta kirata taje d'akinta ta d'auko mata wata tsantsamar fura tace anshi kisha ko wannan ce kafin ayi abincin akawo maki, jiki na 'kyarma Laraba ta kar6a ta kafa kai ta shanye sannan ta ajiye kwaryar tace "nagode, sannan tabar gidan zuciyarta cunkushe da ba'kin ciki da takaici. Laraba kuwa daga gidan baffa lawal maimakin tayi hanyar gida saita yanki hanya tayita tafiya cikin daji, saida tayi nisa da Gari, wani wawakeken rami ta iske gabanta, nan ta tsaya tana kallon fad'in ramin da zurfinsa, take wasu zafafan hawaye suka wankemata fuska, a fili ta furta "'kara in mutu da rayuwar ba'kin cikin danake ciki, lokacin kuma taji kanta ya sara,idanunta sun rufe, bata ganin kome, nan ta fad'i war-was gata gab da ramin, dan motsi kad"an zatayi ta ida afkawa ciki. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Tafiya yake cikin had'ad'd'iyar motarshi 'kirar Camry mai ruwan sumunti, tu'ki yake cikin kwanciyar hankali, cikin motar kuwa ba abunda ke tashi sai sanyin a,c daya had'e da kamshin freshener, sai kuma 'kirar'ar sheik Abdurrahama sudais dake tashi, Tafiya yake amma zuciyarshi na raya mashi abubuwa da dama, game da 'kauyen kwata-kwata babu titi ko d'aya sai dai mutum yayita bi cikin jar 'kasa da burji, Kamar ance yakai dubansa gurin, lnnalillahi yafad'a yayin da ya hango mutum kwance 'kasa, gab da wani wawakeken rami, da sauri yayi fakin din motarshi yafito, addu'a yafarayi kafin yakai hannunshi gareta, saida ya tabbatar da sauran numfashi jikinta sannan ya kinkimeta ya sata bayan motar shi, Juya akalar motar yayi yakama hanyar komawa cikin gari, tafiyar awa ukku ta dadashi da garinshi, asibiti ya wuce kai tsaye, da sauri aka amshi Laraba aka shiga wani d'aki da ita domin duba lafiyarta. Awon farko aka gano yunwace ke neman halaka ta, nan aka d'aura mata drip, sannan akayimata Allaurai, bata farka ba amma likitan ya tabbatar mashi da lafiya lau babu wata matsala zata iya tashi koda wane lokaci, saboda haka asamo mata abinda zataci, dan tana tattare da yunwa kuma tana bu'katar abinci mai kyau. πŸ–ŠZee Elkaseem Mmn khadyπŸ’‹ [10/16, 8:11 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [25/08 8:21 am] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 2⃣7⃣to2⃣8⃣ πŸ–ŠMotarshi yanufa a zuciyarshi yana tausayama halin da yarinyar take ciki, mintina da basu wuce sha ukku ba suka sadashi da gidan iyayenshi, wani 'katon gida ne had'adden gaske, bakin get yayi horn me gadi ya bud'e mashi get yashiga da motarshi, gurin ajiye motoci ya ajiye motarshi, motocine gurin kusan guda shidda, sai lokacin nagane ashe wacce naganshi ciki batada kyau, dan manya- manyan moticine masu tsadar gaake ajiye gurin, wannan yafita da itane dan yasan yanayin garin da zaya. Hanyar da zata sadashi da ainafin cikin gidan yanufa, kai tsaye falon hajiyarsa yanufa. Wata dattijuwar mata ce zaune cikin falon, cikin shiga ta Alfarma, idonta sanye cikin wani siririn farin glass, wanda da alama medical ne, hannunta ru'ke da Al Qur'anic, tana nazari, gefe kuma wata 'kya'kyawar yarinyace wacce bata wuce shekara sha biyarba, ita kuma ta maida hankalinta gun kallon TV, tashar sunnah tv take kallo. Sallamar yayan nata yasa tayi saurin kai dubanta gareshi tare da amsa sallamar, tace "lah Yaya Mukhtar, ya akayi ka dawo yanzu, ko baka kai da tafiya bane, yace "naje mana, amma ban kai ga isaba wata 'yar matsala ta maidoni, tace matsala kuma Yaya, Tame? "To tambai, wannan tamaboyoyi haka, kamar wata 'yar jarida, tace "hm Yaya Mukhtar ai ko banzama 'yar jaridaba kasan abinda nake burin zama, Yasan kullum burinta be wuce na tazama lawyer ba, murmushi yayi yace "Allah taimaka, inaso ki shiga kitchen keda Uwani me aiki ku dafamin abinci, jallouf d'in wake da shinkafa zakiyi, ayi amfani da hanta gurin girkin, dan bani bu'katar wani kalan nama, sannan a dafamin ruwan zafi ahad'a kayan tea, zatayi magana yayi saurin tarbarata "banison tambaya kiyi sauri ina jiranki yanzu, haka Jidda tanufi kitchen a zuciyarta tana tinanin me Yaya zayayi da abinci yanzu kuma harda kayan tea. Sai da yagama da Jidda sannan yanufi inda mahaifiyarsa take, wacce duk abinda suke shida Jidda tana jinsu, itama zuciyarta cike take da tambayoyi da dama gareshi. Cike da ladabi ya isa gurin hajiyar tashi, yasamu guri ya zaune kusa da 'kafafunta, yace "Hajiya barka da hutawa, cike da fara'a ta kalleshi tare da rufe Qur'anic dake hannunta tace "yauwa, kafin tayi wata magana yace "nasan zakiyi mamakin ganina yanzu, wata yar matsalace ta maidoni, nan ya kwashe yanda ya tsinci Laraba ya gaya mata, take tausayin yarinyar yakamata, kuma tayi alwashin taimakamata. Saida sukayi sallar magrib sannan suka nufi asibiti, Mukhtar ne ke driving, sai Jidda dake zaune gefensa duk ta isheshi da surutu, sai Uwani me aike dake bayan motar, Jidda ta kalli yayan nata tace, wallahi yaya har na 'kagara inga yarinyar nan, wallahi ta matu'kar bani tausayi, ko ina iyayenta suka barta, har yunwa na neman halakata, kai wallahi mutanen 'kauye basuda hankali, wai sai mutum yayi zaune da yunwa har sai tayi mashi lahani, Mukhtar dai jinta kawai yake tanata zuba, be cemata uffan ba har suka iso asibitin, Parking d'in motarsa yayi inda aka tanada dan ajiye motoci sannan suka nufi cikin asibitin uwani na d'auke da kwandon da aka jero kayan abincin ciki. Sun shiga d'akin da Laraba take, zaune suka isketa, tayi zuru da alama tafad'a kogin tinani, saida sukayi mata sallama sannan ta dawo hayyacinta, binsu kawai tayi da kallo dan su duka ba wanda tasani, jidda ce tafara magana, tace "Yaya wannan itace yarinyar daka tsinta d'in, kai Amma ky'k'kyawa da ita, amma gaskiya mutanen 'kauye basuda wayo da har sukayi sakaci da wannan 'kya'k'kyawar yarinyar... Wata uwar harara yayan nata ya daka mata, hakan yasa tayi saurin jan bakinta tayi shuru, Sannan ya maida kallonshi ga uwani yace "Uwani gatanan ki bata abincin, Uwani da tunda suka shigo take kallon Laraba, tana yaba irin kyawun da Allah ya zuba mata, tace "to amma yakamata ta d'an watsa ruwa taji dad'i kafin taci wani abu, sai dai kuma babu kayan da zata canja idan tayi wanakan, jidda tayi saurin cewa "yaya muje gida in d'auko mata cikin kayana, Mukhtar ya gyad'a kai yace barshi kawai bari inje in siyo mata, ya kalli uwani yace a taimaka mata tayi wankan kafin indawo, sannan yafice daga d'akin. Bayan fitarshi uwani tahad'ama Laraba ruwan d'umi ta kaita kewaye, ta gwada mata yanda zatayi, dayake Laraba yarinyace mai nutsuwa batayi wani karanbani ba, yanda aka gwada mata haka tayi, ta dade tana wanke jikinta da sabulu mai 'kamshi, wanda rabon datayi wanka da ruwa ma har ta manta, sai da ta tabbatar da tayi fess sannan tafito daga kewayen. Bata dade da fitowaba mukhatar yashigo da wata 'katuwar Leda a hannunsa, ya mi'kama Uwani, sannan yafita daga d'akin yabasu guri dan suji dad'in aiwatar da kome. Jidda ce tayi saurin zazzage kayan tana dubawa, kayane kusan kala takwas duk na kanti, wasu riga da siket wasu kuma dogayen riguna, Wata doguwar riga jidda ta d'auko, kalar sararin samaniya daga gaban rigar anyi mata kwalliya da duwatsu dark blue tace wannan zaki sanya, Laraba dai binsu kawai take da ido, dan ita har yanzu batasan a ina take ba, ba musu ta 'kar6i rigar ta sanya sannan jidda ta d'aura mata d'an kwalin rigar, wani irin kyau tayi duk da ba wata kwalliya bace a fuskarta, jidda kasa yin shiru tayi tace "kinga yanda kikayi kyau, wai miye ma sunanki, sai lokacin karaba ta iya bud'a Bak tace "sunana Laraba, jidda tayi murmushi tace wallahi na d'auka larabci zanji kinyi, dan kwata-kwata kinfi kama da jinsin larabawa, to amma miye asalin sunanki dan Laraba ba suna bane... Mukhatar ne yashigo da sallama, yakai dubansa ga Laraba, wani dum yaji gabansa ya fad'i dan bacin yasan uwani da jidda suna d'akin da sai yace wannan ba yarinyar daya tsinta bace, saboda wani masifaffen kyau datayi mashi. Tambaya yayi taci abincin kuwa, Uwani tace "jira nake agama shirin sai in zuba mata abincin, wata harara yayima jidda dan yasan kicifin tane, mutumin da beda lafiya har wani shiri za'ayimashi. Da kanshi ya had'a tea mai kauri Wanda yaji madara da Milo ya mi'ka mata. Ba musu ta 'kar6a ta kafa kai ta shanye, dayake tanada bu'kata dama, sannan aka zuba mata jallouf d'in wake da shinkafa wanda yaji kayan lambu da hanta, nan ma taci amma kad'an kasancewar tean data sha yacika mata ciki. πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khadyπŸ’‹ [10/16, 8:11 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [26/08 12:13 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 2⃣9⃣to3⃣0⃣ πŸ–Šsai bayan sallar isha'i sukayi niyyar barin asibitin bayan sun yanke cewa Uwani zata zauna gurin Laraba, aiko itama jidda kafewa tayi dole sai an barta ta kwana gurin Laraba, saida mukhtar yayimata fad'a sannan suka tafi, ranta yayi matau'kar 6aci dan an hanata kwana gurin Laraba, Haka suka tafi tanata zum6ura baki ita a dole fushi take, dan ko surutun data sabayima yayan nata yau batayiba tunda ya 6ata ranta, Yana lura da ita yanda taketa cika tana batsewa, amma sai yayi kamar besan tanayiba, A haka suka iso gida, bakin get sukayi horn me gadi ya bud'e masu get suka Shiga, gurin ajiye motoci yayi parking d'in motarsa, kafin ya gama gyara parking tafito daga mortar tanufi cikin gida da gudu, tana zuwa falo bata taradda Hajiya ba, saboda haka bedroom d'inta ta wuce kai tsaye, zaune ta isketa kan abin sallah tana tasbihi, fad'awa tayi jikinta tana kuka, Cike da mamaki Hajiya ke tambayarta "lafiya jidda meya faru, meya saki kuka ina yayan naki,? Kafin ta bata amsa sai gashi yashigo, cikin ladabi yake gaisheda hajiyarsa, sannan yace "Hajiya bafa wani abune yafaruba, kawai dan nace bazata kwana asibiti bane shine take fushi, Murmushi Hajiya tayi tace "haba Jidda yaza'a barki ki kwana, asibiti ayba gurin zaman yaro bane, kibari idan Allah ya kaimu gobe tunda ba school sai mu tafi tare nima zanje in gano yarinyar, Haka Hajiya tayita rarrashinta har tasamu ta saki ranta, tayi murmushi tace "Hajiya bakiga yarinyar ba wlh kya'k'kyawa da ita, ni naji dad'i nasamu 'kawa, Hajiya tayi murnushi tace daga ganin sarkin fawa sai miya tayi za'ki, daga ganin yarinya sai kice kinyi 'kawa, Mudai iyakarmu taimako, kuma data samu lafiya ta warware zamu maidata ga iyayenta, nasan yanzu duk inda iyayenta suke suna can hankalinsu ba kwance ba, Jidda tayi saurin tashi daga kwancen datake kan cinyar Hajiya tace "dan Allah Hajiya kada a maidata, inasonta inaso tazama 'kawata, Hajiya bata cemata komeba sai murmushi kawai tayi, *(Yaro man kaza)* sai lokacin Mukhtar yayi magana yace "kedai baki gajiya da shirme, ke yanzu kinaso arabaki da Hajiya wasu su ri'keki, ta turo baki tace to ayni hajiyata na sona bazata barni da yunwa ba,har in kusa mutuwa wasu su tsinceni, harara yayi mata sannan yafita yabar d'akin. 'Dakinsa yanufa kai tsaye zuciyarshi cike da tausayin Laraba, shi kanshi yanda jidda tafad'a hakane bayason rabuwa da Laraba, dan tsakanin wannan d'an lokacin wani irin abu yakeji dangane da ita, Da wannan tinanin yafad'a toilet ya she'ka wanka, sannan yafito ya canja kaya, jallabiya yasa me gajeren hannu sannan yanufi babban falo, can ya iske Hajiya da jidda kan dining suna niyyar cin abinci, shima kujera d'aya yajawo ya zauna kusa da hajiyarsa, jidda ce ta zuba mashi tuwon shinkafa da miyar Alayyahu, sai 'kamshin curry ke tashi, Haka suka ci abincin kowanensu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, bayan sun 'karasa suka kora da kunun aya me sanyi, sannan suka ta6a fira Sai gurin 'karfe goma sannan, sukayi bankwana, mukhtar ya wuce d'akinsa, jidda kuwa d'akin Hajiya tanufa, Hajiya ta kalleta tace "kika biyoni nan d'akin naki kuma fa? Cikin shagwa6a tace "Hajiya ki barni in kwana anan idan aka sallamo Laraba ta dawo nan gidan sai mu koma d'akin nida ita kinga nasamu abokiyar fira, murmushi Hajiya tayimata sannan ta canja kaya zuwa kayan bacci, itama jidda kayan baccin ta sanya sannan suka haye katafaren gadon wanda yasha wani lallausan bedsheed, sukayi addu'a suka shafe jikinsu. Mukhtar kuwa koda ya koma d'aki tinanin Laraba ya zauna a kwa'kwalwarsa, cikin zuciyarshi yari'ka ro'kon Allah sa iyayenta su yarda ta zauna tare dasu, dan shima har ga Allah baya son rabuwa da ita, yarinya 'kya'k'kyawa amma dayake 'kauye ta taso sukayi sakaci da rayuwarta har tana neman halaka. Da wannan tinanin bacci yayi awon gaba dashi bayan yayi addu'a Ayatul kursiyyu da qula'uzzai ya shafe jikinsa. _```Waye Mukhtar```_? Mukhtar Abass shine asalin sunanshi, haifaffen d'an garin katsina ne, a wata unguwa me suna 'yan,shuni. Mahaifinshi Alh Abass, mutum ne mai ilimin addini, kuma yana aiki dashi, dan duk wani abu daya shafi addini yana fidda dukiyarshi yayi hidima da ita, shiyasa kullum Allah ke 'kara bud'a mashi, kuma dama yana dukiya me yawa ga kuma taimakon na 'kasa dashi da miskinai, ga fidda zakka duk shekara kamar yanda Allah ya hukuta. sunyi auren saurayi da budurwa da matarshi wato Hajiya Zainab, bayan aurensu da shekara ukku Allah yabasu haihuwa inda suka haifi namiji aka sanya mashi suna Aliyu, har Aliyu ya shekara bakwai Hajiya Zainab bata kuma haihuwa ba, wata rana an taso su Aliyu makaranta yafito bakin titi yana jiran driver yazo d'aukarsu wata mota ta bankeshi, kafin akaishi asibiti rai yayi halinsa, Hajiya Zainab da Alh Abass sunyi kukan rashin d'ansu, 'karshe suka ha'kura suka fawwalama Allah lamuransu, kuma daga lokacin Hajiya Zainab bata kuma samun cikiba sai bayan shekara biyu tasamu cikin mukhtar, bayan an haifeshi ne da shekara bakwai aka haifi jidda, wanda daga ita hajiya Zainab bata kuma haihuwaba. Jidda nada shekara ukku Allah yayima mahaifinsu Alh abass rasuwa bayan yayi fama da gajeruwar rashin lafiya, Bayan rasuwar Alh Abass da shekara d'aya 'yan'uwan Hajiya zainab sunso takoma garesu amma sai tace sam bazata komaba zata zauna ta ri'ke yaranta dan bataso ta dorama wani nauyinsu. Haka Hajiya Zainab tacigaba da kula da karatun yaranta da tarbiyarsu, amma haka be hana 'yan,uwan Alh Abass taimakonsuba, dayake mahaufinsu mutum ne mai taimakon 'yan,uwa. lokacin da muke yanzu, mukhatar yazama cikakken d'an kasuwa, dan sana'ar babansa kenan kafin ya rasu, hakan yasa mukhtar karantar business, ga kuma kiyo da suke a gidan gonarsu da mahaifinsu ya bar masu gado, lokcin da mukhatar ya tsinci laraba gidan gonar tasu yanufa, sai Allah ya had'ashi da ita. Jidda kuwa yanzu take junior secondary, j.s.s 3 bana zasu zana jarabawa. *_WANNAN SHINE TAKAITACCEN TARIHIN MUKHTAR_* πŸ–ŠZee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:11 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [26/08 9:30 pm] πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 3⃣1⃣to3⃣2⃣ πŸ–Š Haka Uwani tacigaba da kula da Laraba, yayinda mukhatar kullum sai yayi zuwa yakai shidda asibitin, dan bayaso anemi wani abu baya nan, hajiyar Mukhtar kuwa sau ukku tana zuwa ganin Laraba, jidda kuwa 'yar rigimar kullum nan take yini, kuma sai anyi daga da ita gun komawa gida, dan kullum kafewa take sai ta kwana, Satin Laraba d'aya asibitin taji sauki sosai, ta'kara fari tayi wani fresh, dan har 'yar 'kiba tayi, tana samun kulawa sosai daga malaman asibitin zuwa ga mukhtar sai kuma Uwani me aiki itama tana bakin 'ko'karinta. Yau Likitan dake dubata yazo round nan ya duba jikin uwani ya tabbatar da kome normal, sannan yarubuta masu sallama. Mukhtar ne ya d'aukesu a mota, jidda ce gaban mota kusa da yayanta, yau dai farin ciki fal a zuciyarta, dama kullum addu'a take a sallamo Laraba 'kawarta ta dawo gidansu da zama, uwani da Laraba kuwa bayan motar suke sunata sauraren jidda da keta zuba uban surutu. Dai-dai get d'in gidan sukayi horn me gadi ya bud'e masu get suka shiga, Tunda sukazo Laraba kebin gidan da kallo, saboda tsananin 'kyawunsa, cikin zuciyarta tace _"Anya ba mafarki nake ba, dan bani tinanin akwai irin wad'annan gidajen nan duniyar da muke_ Niko nace *Hmm Laraba kenan sai ma kin shiga gidan zaki tabbatar da ba irin duniyar da kk sani bace, (wani hanin ga Allah baiwa ne)* Jidda ce takama hannun Laraba sukayi cikin gida, wani irin tsoro yakama Laraba dan ganin 'kawatuwar falon, kai lallai dama ashe akwai masu irin wannan jin dad'in a duniya, haka kawai take fad'a a zuciyarta. Cike da murna da sakin fuska Hajiya ta tarbesu tanayimasu sannu da zuwa, jidda kuwa murna yau gurinta bakin har ya'ki rufewa, da kanta ta zaunar da Laraba kan kujera tace "Zauna 'kawata ki huta kafin anjima kiyi wanka, Laraba dai kallon mutanen kawai take, duk abinda sukace shi take yi, tazama tamkar ra'kumi da akala, Bayan sallar azahar suka zauna kan dining suna cin abinci, jidda ce ta matsama Laraba ta zauna suci, amma ita duk d'arare take ba kamar idan da mukhtar gurinta dan wani irin kwarjini yake mata. Bayan sun kammala ne jidda ta kama hannun Laraba tace 'kawata zo muje ciki kiyi wanka ki canja kaya, ba musu Laraba tabita zuwa d'akinta, Toilet taje ta had'a mata ruwan wanka, tare da zuba mata turarurrukan wanka masu 'kamshi gaske, sannan tazo ta kama hanunta ta kaita har toilet ta gwada mata yanda zatayi, sannan ta jawo mata 'kyauren tafito tana jiran ta. Laraba ta dad'e tana dirje jikinta a kewaye, kafin tafito d'aure da zanin atamafa jikinta, dan 'kin yarda tayi da d'aura tawul, dan bata ma san yanda zata d'aura shiba. Jidda tace "harkin fito, ta kamo hannunta zo inyimaki kwalliya irinna larabawa, laraba tayi murmushi tace " Hmm jidda kenan'har wata kwalliyar larabawa akeyi, jidda tayi dariya tace kedai bari kigani idan nayimaki ke kanki sai kin kasa gane kanki, murmushi kawai Laraba tayimata, dan abun jidda har mamaki yake bata yanda take nan-nan da ita, tun batayi mata magana har tad'an fara sakin jiki tana maida mata amsa idan tayimata. Haka jidda ta zaunar da Laraba gaban mirror tafara d'and'asa mata kwalliya, make-up tayi mata sosai, fuskar nan tafito ta larabawan sak yanda jidda ke fad'a, dan ba 'karamin kyau Laraba tayiba, dan koda ta kalli fuskarta a madubi kasa sheda kanta tayi, in baccin ma jikinka jikinka ne da Laraba tace ba fuskarta bace a madubin. Jidda kanta tsayawa tayi tana kallon kyawun da Allah yayima Laraba, kasa yin shuru tayi tace _"tsarki ya tabbata ga ubanjin daya halitta wannan 'kya'k'kyawar sura_, juwowa Laraba tayi dan ganin wace kya'k'kyawar sura ce jidda ke fad'i amma bataga kowaba sai jiddar hakan yasa ta tabbatar da ita jidda take. Murmushi tayi tace, kai jidda wallahi baki gajiya da zaualaya, yanzu nice kikema wannan zuzutawar, bayan nasan kin fini kyau nesa ba kusa b....... Jidda tayi saurin sa hannu ta rufe bakin Laraba tace, bari kada kiyi sa6o, inani ina had'a kaina dake, Wadrope d'inta tanufa ta d'auko ma Laraba wasu riga da zani na less cikin kayanta, tace "amshi ki saka wannan nasan zeyi maki 'kyau. Laraba ta gyad'a kai tace "jidda da kinbar kayanki na sanya cikin wanda Yaya Mukhtar ya siyomin, tunda akwai ma wanda ban sanyaba har yanzu, Jidda ta harareta cikin wasa tace banison haka, ay nice nace ki sanya idan kuma bazaki sanyaba to ki gayamin, bata jira me Laraba zata fad'aba tashige toilet domin itama ta watsa ruwa. Haka laraba ta rin'ka juya less d'in a hannunta tana yaba kyawunsa, dan ko a mafarki bata ta6a tunanin zata sa irin wannan kayanba, Allah mai yi yanda yaso da bawanshi, wasu siraran hawaye suka zubo daga idonta dan tunowa datayi da Innarta, tasa hannu tayi saurin gogewa dan kada jidda tafito taga tana kuka ta isheta da tambaya, dan tagama karantar halin jidda ahegen surutu gareta, ga kuma tambayar tsiya kamar tamabai...... πŸ–ŠZee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:11 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [27/08 8:02 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 3⃣3⃣to3⃣4⃣ πŸ–ŠBayan sun kammala shirinsu tsaf, Laraba ta sanya less d'in da jidda tabata ta Sanya, aiko less d'in yayi masifar yimata kyau ya zauna d'as ajikinta, itama jidda less ta sanya tayi kyau sosai, ta kalli Laraba tace kin san wani abu,? Laraba ta gyad'a kai Alamar a'a, Jidda tace wannan kwalliyar gurin Yaya kawai yakamata muje yaga yanda kikayi kyau, 'kilama idan ya ganki baze ganekiba, Laraba tayi murmushi tace, "sai dai idan wata fuska na canja, to sannan na yarda baze ganeniba, amma fuskar da yayi kusan sati biyu yana tare da ita yaushe dan yau d'aya kinyi min kwlliya kice baze ganeniba. Jidda ta kyal'kyale da dariya tace "lnda ba 'kasa nan ake gardamar kokowa, inaji ai yayan yana gidan ba inda yaje saboda haka muje araba gardama, Laraba ta zaro ido tayi dariya tace "kefa dad'ina dake jidda baki gajiya da shirme, to idan munje muce masa me? Jidda tayi dariya tace kedai kibar komi a hannuna, yau zaki tabbatar ma kanki tsananin kyawun da kikayi idan ni baki yarda da maganata ba, bata jira me laraba zata fad'a ba ta kama hannunta tace "zo muje, laraba ba yanda zatayi da jidda haka yasa tabita kawai, cike da mamakin shirme irinna jidda.. A falo suka iske Hajiya tana hutawa, suduka suka iso gareta suka rissana sukace "barka da hutawa, ta kai dubanta garesu, wani irin fad'uwar gaba Hajiya taji dan ganin wani irin kyau da Laraba tayi mata, cikin zuciyarta tace *Allah sarkin halitta lallai Allah ya ajiye kyau tattare da Laraba ga nutsuwa da sanin ya kamata* Cikin fara'a Hajiya ta amsa "yauwa 'yan matana, wannan kwalliya haka, kamar 'ya'yan saraki, murmushi laraba tayi cike da jin kunya, Jidda kuwa dariya tayi tace "Allah Hajiya laraba tafi 'ya'yan sarki kyau, murmushi kawai Hajiya tayi masu, Jidda takama hannun Laraba, suka nufi hanyar fita daga falon, Hajiya tace "ina zaku haka,? Jidda tace zamu gurin Yaya ne, Hajiya tace to 'yan gidan Yaya, idan kunje kuce ina nemansa yanzu, kutaho tare, tare suka had'a baki suka amsa da "to. A lambun gidan suka tarar dashi, yana zaune kan wasu fararen kujeru, gabanshi kuma wani 'karamin table ne d'auke da laptop d'insa yana danne-danne, gefe kuma fresh milk ne da cup d'in glass, besan isowarsu ba saboda haka jidda tace ma Laraba "kawata ki tsaya bayan wannan flower so nike inba Yaya mamaki, laraba tace "wane irin mamaki zaki bashi kuma? Jidda tayi saurin rufe mata baki tare da jan hannunta ta turata bayan wata flower, sannan ta isa ga yayanta wanda hankalinshi na kan computer shi, bema san sun zo gurin ba. Sallama jidda tayi mashi, d'ago kanshi yayi yakai dubanshi gareta sannan ya amsa sallamar, murmushi yaga tanayi, saboda haka yasan akwai magana tattare da ita, hakan yasa ya tambayeta "ya dai 'kanwata? Ta 'kara fad'ad'a murmushin dake fuskarta tace Hajiya ce ta aikoni gurinka, amma kafin in gaya maka sa'kon inaso in baka *surprise* yayi murmushi yace mamakin me za'a bani kuma? Tace kaidai ko miye zakagani amma ka rufe idonka tukun. Yasaba da shirmen 'kanwarsa saboda haka beyi musuba yasa hannu ya rufe idonsa, yana jiran yaga yau kuma da wane shirman tazo mashi. Tana ganin yarufe idonshi tayi saurin zuwa inda ta 6oye Laraba ta kamo hannunta suka nufi inda Mukhtar yake zaune. Laraba nagani haka tarin'ka bin jidda kamar ra'kumi da akala, saida sukaje gaban mukhtar sannan tace "Yaya bude idonka, Ahankali ya sauke hannuwanshi daga idonshi ya saukesu kan laraba, kallonta yacigaba dayi, cikin zuciyarshi yace *tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci wannan 'kya'k'kyawar yarinya, lallai Allah ya ajiye kyau a nan* . Laraba ta kula da yanda mukhtar ya tsareta da ido hakan yasa taji duk ta tsargu, takama hannun jidda tana janta Alamar tazo su tafi, dariya jidda tayi, wacce ta dawo da mukhtar daga dogon tinanin dayake, tace "Yaya dama hajiyace tace kazo yanzu tana nemanka. Basu jiran amsarshiba suka wuce cikin gida, Jidda na dariyar yanda yayanta ya tsare Laraba da ido, Ita kuwa Laraba bata ji da'din hakan ba amma bata nuna ma jidda taji haushi ba ko kadan. _*Kuyi ha'kuri da wannan πŸ‘†πŸ» yau ina busy be*_ 3⃣5⃣to3⃣6⃣ very πŸ”œ πŸ–ŠZee Elkaseem Mmn KhadyπŸ’‹ [10/16, 8:11 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [28/08 12:50 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 3⃣5⃣to3⃣6⃣ πŸ–Š Laraba na ri'ke da hannun jidda suka shigo falon, suka samu guri suka zauna, basufi minti biyar da zama ba sai ga yayan su yashigo, cike da ladabi ya zauna kan kujerar dake facing d'in Laraba ya zuba mata idanunshi masu tsananin kwarjini yana kallonta, itako ta lura da yanda yake kallonta hakan yasa duk ta daburce. Hajiyace tayi gyaran murya tare da 'kara gyara zamanta tace "am mukhtar abinda yasa nace akira mani kai shine kan maganar Laraba, Wata irin fad'uwar gaba laraba taji dan jin maganar da Hajiya tayi, a zuciyarta tace _"shikenan nasan lokacin barina gidannan yayi, dan nasan muddin suka San Matsala ta bazasu kuma zama daniba_. Hajiyace ta maidota daga dogon tinanin datake, tace "Laraba, laraba ta d'ago fuskarta ta kalli Hajiya, sannan t sadda kanta 'kasa tana kallon kafet d'in dake malale tsakiyar falon. Hajiya tacigaba da magana "kamar yanda kika Sani mun taimakeki kuma Alhmdulillahi kin samu lafiya kin warware, kuma nasan bazaki rasa sanin inda 'yan,uwanki da iyayenki sukeba, saboda haka inaso ki sanar damu ke wacece? Kuma miye ya jefaki cikin mawuyacin halin da shi mukhtar ya tsinceki a ciki? Saboda munaso mu maidake gurin iyayenki. Shiru Laraba tayi takasa ko motsi dan jin tambayoyin da hajiyar ta jero mata lokaci guda, wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanunta, batada niyyar d'ago fuskarta, saida Hajiya tayi mata magana karo na biyu tace "laraba ke muke sauraro. Laraba ta d'ago da fuskarta wacce tayi sharkaf da hawaye, ganin haka yasa hankulansu tashi su duka, cike da damuwa jidda ke rarrashin Laraba tasa hannu tana goge mata hawaye "kiyi ha'kuri 'kawata ki gayama Hajiya abinda ta tambayeki, ni nasan hajiyata mai tausayice zata taimaka maki a kan abinda kike Neman taimako, inshaAllahu. Haka jidda tayita rarrashinta da kalamai masu taushi, hartayi shuru sannan ta goge hawayenta tafara basu Labarinta, kamar haka: _*Sunana Fatima amma amfi kirana da laraba kamar yanda kuka Sani, mahaifiyata yar Asalin 'kasar camaron ce, sun h'ad'u da babana ne lokacin yana zuwa fatauci can 'kasar.*_ _*Mahaifina kuma d'an nan cikin garin karsina ne a wani 'kauye dake 'karamar hukumar malumfashi me suna 'kurungafa' Allah yayima mahaifina rasuwa tin ina 'yar shekara ukku a duniya, kamar yanda naji mahaifiyata tana fad'a,*_ _*Haka yasa muka taso cikin wahala nida mahaifiyata, kasancewar batada kowa a nan 'kasar shikuma babana su biyu ne gurin iyayensu daga shi sai 'kaninsa baffa Lawal, baffa Lawal mutum ne wanda bashida taisayi ko kad'an hakan yasa baya taimaka mamu da koda ruwan sha,*_ _*Haka mukacigaba da rayuwa nida mahaifiyata, yau da dad'i gobe babu har nakai shekara shidda lokacin kuma mahaifiyata tasakani makarantar bokon dake 'kauyenmu, bayan na kammala aji shidda ne samarin 'kauyen sukayo ca Kowa nason Neman aurena, lokacin inada shekaru sha ukku a duniya*_ _*An tsaida wani saurayi matsayin wanda baffa lawal ya amince dashi, dan baffa Lawal Isa da ta'kama ba wanda bayayi mamu amma kuma idan neman taimakone sai ya nuna be sanmu ba, ana gab da bikinane Allah yayima mahaifiyata rasuwa, Al'amarin daya sakani cikin mayuwacin hali, dan bayan rasuwarta da sati biyu saurayin dazan aura ya aiko a maida mashi duk wani abu daya kawo gidanmu yafasa aurena, nan fa tashin hankalina ya 'karu.*_ _*Baffa Lawal da kanshi yazo har gida yacimani mutunci, yana cewa ai nasan abinda nayimashi yace yafasa aurena, saboda haka tsinke baze barmin ba cikin kayan da yaron ya kawo, inaji ina gani ya tattare kome yasa kai yabar gidan, haka na zauna na had'e kai da gwiwa ina kuka ni 'kad'ai cikin gida babu me rarrashina, dan dama tunda mahaifiyata ta mutu yazamana ni d'aya ke kwana gidan, tun ina jin tsoro har zuciyata ta saba*_ *_Ban fuskanci babbar matsalaba sai da na wayi gari banida abinda zanci, yunwa tayimani mugun kamu wanda har wani matsanancin ciwon ciki ya kamani, hakan yasa na lalla6a naje gidan baffa Lawal ko ze taimakamin amma sai yayimin korar kare, lokacinne na 'kudiri niyyar kashe kaina ta hanyar fad'awa wani 'katon rami dake nesa kad'an da 'kauyenmu, dan lokacin na 'kwammace mutuwa da halin da nike ciki, ga ba'kin cikin rayuwa ga ALHININ rabo da iyayena....._* Wannna shine labarina, laraba ta fad'a tana goge hawaye, Jidda ma kuka take saboda tusayin larabar, "Lallai laraba kinsha gwagwarmaya, Allah Sarki, ta fad'a tana sharar kwalla. 3⃣7⃣to3⃣8⃣ very πŸ”œπŸ’ƒπŸ» πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:11 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [28/08 5:07 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 3⃣7⃣to3⃣8⃣ πŸ–Š Haka jidda takama hannun Laraba suka wuce d'aki, tashiga rarrashinta "kiyi ha'kuri Laraba ki d'auki rayuwar da kikayi a baya amtsayin jarabawa, kuma kiri'ka yima iyayenki Addu'a Allah kai haske kabarinsu, kuma ina me tabbatar maki bazamu gujekiba, zaki zauna damu har 'karshen rayuwarki inshaAllah, Laraba tasa hannu ta goge hawayen dasuka zubo a kumatunta tace "ko yanzu nabar gidannan nasan kunyi min hallacin da 'kanin mahaifina yakasa yimin wanda shi kad'ai yarage a dangina, nagode Allah saka maku da Alkhairi. Jidda tace ba kome laraba ki d'aukeni a matsayin 'yar'uwarki Hajiya kuma a matsayin mahaifiyarki Yaya mukhtar kuma a matsayin yayanki, inshaAllah bazaki 'kara fuskantar Matsala a rayuwarki ba. Haka jidda tayita rarrashin Laraba har zuciyarta tayi sanyi, ta goge hawayenta, Nan jidda tacigaba da bata labarai kala-kala tun tana jinta kawai harta biye mata ta saki jiki tana dariya kamar ba itaba. A falo kuwa Hajiya ta kalli mukhtar jiki a sanyaye tace "kaji abinda yarinyar nan tafad'a ya ka gani, Mukhtar Wanda shima duk illahirin jikinsa yayi sanyi dan jin labarin Laraba, yace Hajiya kawai abinda ya kamata shine mu ri'keta ta zauna gurinmu muga abinda Allah zeyi. Hajiya tace hakane, zatacigaba da zama gurinmu kuma zaka samo mata form a islamiyyar su jidda suri'ka zuwa tare. Sannan idan su jidda zasuyi Exam ayi 'ko'kari asakata ciki, tafara daga s.s.1 tunda kaga yanzu takai kimanin shekaru sha hud'u baze yiyu asata j.s one ba tayi girma, sai asamo Wanda zeri'ka mata lesson a gida kafin sufara karatun. Cike da jin dad'i mukhtar ya amsa ma Hajiya, zuciyarshi cike da farin ciki, dan ko kad'an dama bayaso ayi maganar maida Laraba garinsu. Jidda Kuwa dataji hukuncin da Hajiya ta yanke na zaman Laraba gidansu murna tashigayi hada tsalle. Laraba kuwa cikin ranta tana tsoron ranar da zasu gane gaskiyar labarinta data 6oye masu, dan tasan muddin suka gane to zasuyimata korar kare. _```BAYAN SHEKARA UKKU```_ Wasu kyawawan yan mata na hango su biyu tsaye bakin titi kusa da school d'insu sanye suke cikin uniform d'insu rigar chek pink, sai wando brown, sai 'yar karamar abayar da bata ko rufe hannuwansu ba, kafafunsu sanye cikin brown sandals sai farar safa computer, sunyi kyau sosai kamar 'ya'yan larabawa. Wata ba'kar mota 'kirar 4matic tayi parking gabansu, sannan matashin dake cikin motar ya sauke glass d'in motar yakai dubansa ga 'yan matan, da gudu 'yan matan wad'anda basu wuce shekara sha bakwai ba suka nufi motar suka shige, kowace baki ya'ki rufewa saboda farin ciki. Sun fara tafiya a motar jidda dake gaba, kusa da yayan nata ta juyo ta kalli Laraba ta kashe mata ido, murmushi kawai Laraba tayi mata dan tasan jidda da surutun tsiya, yanzu haka akwai abida takeson fad'a... Bata gama tunanin datakeba, ta tsinkayi muryar jidda tana cewa "Yaya bakayi mana congratution ba yau munyi graduated, ya juyo ya kalleta yace tun nan a mota zanmiki congrat d'in, to ke bari inyimaki amma Fatimana sai munje gida zan mata, yafad'a yana kallon Laraba yakashe mata ido, itako wata irin kunya ke kamata idan yakirata fatimarsa, jidda kuwa cewa tayi eh na yarda ayimin anan, ya juyo ya kalleta yace "lna tayaki murna 'kanwata, yanzu saura musha biki keda Usman, cike da jin kunya jidda tarufe idonta, daga lokacin bata 'kara magana ba, dan wata irin kunyace takamata, Usman shine saurayin datake masifar so kuma shine Wanda zata aura, dan maganar harta kai ga iyaye, dama makaranta kawai ake jira ta kammala. Laraba kuwa na kula da ita, saboda haka tari'ka kallonta ta madubin motar tana mata dariya 😜 itakuma girgiza kai tayi, Alamar zasu had'e........ Haka suka Isa gida cike da farin ciki, bakin get sukayi horn megadi yabud'e masu get suka shige, sukayi parking, da gudu suka nufi cikin gida suna kiran Hajiya, Hajiya na bedroom tajiyo haniyarsu da sauri tafito tana masu sannu da zuwa, nan suka zauna anata labarin makaranta, Hajiya tayimasu congrat, sukaji dad'i har cikin ransu. Sai lokacin mukhtar yashigo fuskarshi d'auke da fara'a yasamu guri ya zauna, lokacin kuma Hajiya takoma d'akinta dan cigaba da aikin datake, Tasowa yayi yazo gaban laraba, ya du'ko inda take zaune har numfashinsu na gauraya dana juna, hannu yasa aljihu yaciro wata had'ad'iyar waya mai kyan gaske, kirar tecno H³ yami'ka mata, tare da cewa *"Congratulation on your graduation Fatima na* cike da jin kunya ta amsa tace *Thank you very much, My Brother*. Duk abinnan jidda na zaune tana kallonsu, a zuciyarta tagama yarda yayanta son laraba yakeyi. juyawa yayi yanufi hanyar barin falon, da sauri jidda dake zaune tana jiran ami'ko mata tata wayar tayi saurin kamo hannunshi, cikin shagwa6a tace "Yaya nifa, cike da zaulaya yace "kikace iyimaki murna tun a mota, kuma nayi maki. Cikin shagwa6a tace ay ba cewa nayi kada kabani phone ba, dariya yayi sannan ya fiddo wayar itama ya mi'ka mata iri d'aya data Laraba. Da gudu tanufi inda laraba take tana tsalle,...... 3⃣9⃣to4⃣0⃣ Very πŸ”œ πŸ’ƒπŸ» πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:11 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [29/08 7:32 am] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 3⃣9⃣to4⃣0⃣ πŸ–Šmaganar Auren jidda da Usman d'inta ta kankama, dan har ansa ranar biki wata hud'u, jidda kuwa dad'i har cikin zuciyarta, amma takaicinta d'aya yanda Laraba bata kula maza ko kad'an, dan akwai wani abokin Usman daya nuna yana sonta kamar zeyi zauci amma ta bad'e ido toka ta nuna ita bata soyayya, tome hakan ke nufi? Amma ko badad'e ay dole tayi aure tunda tsarin gidansu ne mace bata wucewa gaba da karatu daga secondry, barantana tace karatun tasa gaba. _```Bayan kwana biyu```_ Yaune Hajiya ta tara 'ya'yan nata tana masu magana, kamar haka "Alhmdlh ke jidda banda ke cikin wannan fad'an da zanyi, ta maida kallonta ga Laraba tace "Fatima saboda me bakison ki fidda miji kiyi aure? Bata jira abinda laraba zata fad'aba tacigaba da magana "ita mace duk yanda take jin dad'i gidan iyayenta to gidan mijinta yafishi, kome duk Kyan mace da dukiyarta ko mulkinta darajarta shine d'akin mijinta. Haka Hajiya taketayi masu nasiha, suduka sunyi kasa'ke suna sauraronta, shikuwa mukhtar tsoro yake acikin zuciyarshi kada Fatimarsa tafad'i wani namiji tace shine wanda ta tsaida a matsayin miji, bayan shekarun daya d'auka yana fama da dakon soyaryyarta a zuciyarsa. Hajiya tayi gyaran murya tacigaba da cewa "kodayake ga yayanku nan shima tun yaushe nake fama dashi akan ya fiddo mata yayi aure amma yayi biris da maganar, amma 'kila so yake insamo wata koda 'yar Almajirace in had'ashi da ita, jidda ta kyalkyale da dariya, tace "kai Hajiya Yaya yafi 'karfin Almajira, itama hajiyar dariya take tace to kada ya fiddo matar kusha mamaki daga ke har shi, Sai lokacin mukhatar ya d'ago da idonshi wanda suka kad'a zuwa ja, ya kalli hajiyarshi cike da jin kunya yace "Hajiya ayni na dad'e da samun matar da zan aura, sai kuma ya sadda kanshi 'kasa yana shafa kanshi da Alamar kunya tattare dashi, Hajiya tace "uhum ina saurarenka wace mai sa'ar ce wannan, shiru yayi yakasa furta kome. Jidda tace Allah Hajiya nasan ko wacece, Hajiya ta harareta "ke banison shirme ina sauraronka, "dama...hm..dama ba wata bace sai Fatima, cike da jin kunya yake maganar. Jidda tace dama nasan wlh Hajiya Yaya ya dad'e yana son Laraba, Hajiya tace "to uwar surutu wai waya sanyo bakinki cikin maganar nan, tayi saurin sa hannu tarufe bakinta πŸ™Š. Cike da farin ciki fuskarta kuma d'auke da fara'a tace kai amma naji dad'in wannan abu, ta kalli laraba wacce tunda mukhatar ya furta Kalmar so gareta duk illahirin jikinta kyarma yake. Haka Hajiya tagama dasu ta sallamesu, tawuce d'akinta, Shima Mukhtar d'akinsa ya wuce zuciyarshi cike da farin ciki. 6angaren laraba kuwa tun lokacin da Mukhtar ya furta Kalmar so gareta tayi sukuku, kamar marar lafiya, jidda na kula da halin datake ciki takan tambayeta ko lafiya, sai ta 'ka'karo murmushin 'karfin hali tace mata ba kome, itakuma jidda sai tacigaba da tsokanarta tana cewa amaryar yayanmu, Laraba sai dai tayimata murmushi amma ita kad'ai tasan abinda takeji a zuciyarta, dama ranar data dad'e tana gudun zuwanta kenan, dan dama ta dad'e da lura da take-taken mukhtar na sonta, amma ba kome dole ta samarma kanta mafita, bawai son mukhtar ne batayiba, dan ko itace ta d'aurema butulci gindi a duniya bekamata tace bata son mukhtar ba, matsalarta d'aya shine abinda yabarota daga 'kauyensu, mutum nawa suka mutu dalilin aurenta, tabbas tasan idan mukhtar yadage akan aurenta shima 'karshen rayuwarsa yazo, wasu irin hawaye masu rad'd'i suka zubo daga idonta tasa hannu ta goge, duk abinnan bata yarda ta nuna damuwarta fili dan kada mutanen gidan su gane. _```Bayan wata d'aya```_ Soyayya me 'karfi ta 'kulle tsakanin mukhatar da Laraba, wacce a yanzu ta canja suna takoma sunanta na Asali wato *Fatima* Ranar ne kuma Hajiya takira Laraba tace mata, yakamata ki bada address d'in baffa Lawal saboda za'a tura magabatan mukhatar suje neman aure. Laraba cike da damuwa da far gaba tace "Hajiya kibari da safe zan bada yanzu kaina yana min ciwo, Hajiya ta tausaya mata tace "eyyah Allah sauwa'ke to kisha magani kafin ki kwanta kinji, tace "to, sannan tanufi d'akinsu zuciyarta cike da tunani kala-kala, *gaskiya bekamata ta sakama mutanen nan da sharri ba, yanda suka d'auketa amatsayin 'ya suka ri'keta suka nema mata gata wanda ko a mafarki batayi tunanin samun irinsaba, gaskiya dole tasamoma kanta mafita* Haka ta isa d'akin ta iske jidda tana chat da Usman d'inta tana dariya ita kad'ai kamar mahaukaciya, laraba ta kalleta batayimata magana ba ta haye gadon tayi kwanciyarta. Jidda ta kaimata duka, "ke yau baki chat da yayana, nasan yana online yana jiran zuwanki, Fatima tayi wani d'an guntun tsaki ta 'kara gyara kwanciyarta tace "kaina ne yakemin ciwo nasha magani bacci zanyi, cike da tausayawa jidda ta dafa kanta tace "Allah sauwa'ke, itama sai taji chat d'in yafita ranta haka sukayi sallama da Usman yanata magiyar kada ta tafi ta barshi, tace "kayi ha'kuri sister d'inace ba lafiya bazanji dad'in yin chat d'ina, yace "Allah sauwake sukayi sallama. Itama jidda kwanciya tayi bayan tayi addu'a tashafe jikinta, sannan tayima Fatima addu'ar dan ta lura da lokacin data kwanta batayi addu'ar ba. Duk abinnan Laraba na jinta dan ba bacci tayiba, tunanine kala-kala cikin zuciyarta. Jidda bata dad'e da kwanciyaba bacci yayi awon gaba da ita, haka laraba tayita juyi kan gado bacci ya gagari idanunta, wayarta ta d'auko ta duba 'karfe 1:58 am na dare, a zuciyarta tace yanzu ne yakamata in samoma kaina mafita, dan muddin nasan idan nabari mutanen nan sukaje 'kauyenmu sunan dana 6oye masu nawa na *mayya* zai bayyana. Saboda haka ahnakali ta tashi cikin sand'a ta d'auko site bag d'inta ta bud'e wadrope ta d'auki kaya kala 2 sannan ta cire rigar baccin jikinta ta Sanya wata doguwar riga ta atamfa sannan tasa wando legis daga ciki, sannan ta Sanya wata 'yar 'karamar hijab, ta d'au takalminta a hannu, ta lalla6a tayi sa'ar barin gidan batare da Kowa ya gantaba kokuma yaji motsinta. Bakin titi ta tsaya ta 'karema unguwar kallo bakajin kome sai kukan maguna da karnuka, da tsintsaye, haka ta yanki hanya tacigaba ta tafiya, zuciyarta cike da tsoro....... 4⃣1⃣to4⃣2⃣ Very πŸ”œπŸ’ƒπŸ» πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:11 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [31/08 8:21 am] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 4⃣1⃣to4⃣2⃣ πŸ–Š Tafiya take batare da tasan inda zata dosa ba, ta d'anyi nisa kad'an da gidan zuciyarta cike da tsoro, sai tajiyo Alamar tafiyar mutane bayanta suna tafiya suna magan-ganu wanda bata iya jiyo abinda suke cewa, saboda suna d'an nesa kad'an da ita, hakan yasa zuciyarta kara tsorata, tayi maza ta 'kara sauri cikin sa'a tayi karo da wani gida da aka fara ginawa amma ba'a karasaba, aiko tayi saurin shigewa ciki dan ta 6uya, da sauri ta shige wani guri a cikin gidan wanda da Alama d'aki ne amma ba'a karasaba dan ko rufi ba'ayiba, gidan dai kamar kango ne dan duk illahirin gidan ba 'kofar da aka sanyama 'kyaure, sai uwayen karikitai da Shara a cikinsa. Tana cikin kangon gidan data 6uya 'kirjinta na dukan tara², sai ji tayi wad'annan mutanen data 6uya dominsu sun iso gurin, jitayi sun tsaya bakin 'kofar kangon gidan data 6uya suna magana, muryar guda taji yace "gaskiya nifa na gaji da abinda mutuminnan yake samu muna aykatawa, kawai hakanan yasa muri'ka kawo mashi 'ya'yan mutane yana 6ata Masu rayuwa. Gudan yayi dariya, cikin wata muguwar murya marar dad'in sauraro yace "nikam bazan ta6a barin wannan sana'ar danikeba, dan in baccin ita ina zamu ri'ka samun 'kudin da muma zamuji dad'in rayuwarmu, haba baba, kazo muje kawai mucigaba da neman abinda ya fiddo mu, gudan yace to yanzu ina zamu nufa? Kasan dai yanzu duk wata d'iya mace indai tanada mutunci to tana gidan iyayenta, gudan ya gagga6e da wata irin dariya yace "yo dama duk wacce muka kama yanzu ay bata mutunci bace, dama mu irin 'yan iskan nan muke nema masu yawon dare, idan sunsha sun bugu mukuma sai muyi awon gaba dasu, suduka sukasa dariya marar dad'in sauraoro. Duk abinda suke Fatima na La6e cikin wannan gidan tana jinsu in banda kyarma ba abinda take, lokaci guda ta had'a wani uban gumi, dan tariga ta fahimci inda zancensu ya dosa, A gida kuwa da misalin 'karfe ukku da minti sha shidda na dare jidda ta farka zata shiga toilet sai taga bataga Fatima ba, hakan yasa tayi tunanain ko tana toilet d'in ta dad'e tana jiran fitowarta amma kusan minti goma shiru saboda haka saukowa tayi daga kan gadon da niyyar ta duba toilet d'in. Abinda idanunta yafara karo dashi shine ya d'aga mata hankali, kayan baccin Fatima yadde a 'kasa, bata tsaya d'auka ba ta tura 'kofar kewayen, nan ma ba Laraba, cikin tashin hankali tayo baya sai tayi karo da wadrop bud'e tayi sauri dubawa cikin wadrop d'in saitaga kaya yamutse da Alama an d'auki wani abu aciki, nan tashiga matsanancin tashin hankali lokacin data ta6a kofar fita daga d'akin tajita bud'e. Cikin tsananin tashin hankali tanufi d'akin hajiyarta ta sanar da'ita abinda ke faruwa, Mukhtar ma an tasoshi an fad'a mashi halin da ake ciki, cikin tashin hankali yafito, haka suka shiga duba ko'ina na gidan Amma ba Alamar Fatima, an tambayi me gadi yace shikam bega fitar Kowa a gidan ba. Lokacin idan hankalinsu yayi dubu tashe yake, mukhtar d'akinsa yanufa ya d'auko key d'in motarsa yacema Hajiya "Zan fita in duba ko Allah zesa in ganta. Lokacin itakuma jidda ta d'auko wayarta dan ta lura duk inda Fatima take ta tafi da waya dan ta duba bata gantaba, lokacin ta lalubo sunan sister Fatima, sunan data sanyama Laraba kenan ta danna mata kira. Dadai lokacin da wad'annan mutanen guda biyu suka tashi daga 'kofar kangon gidan da Fatima ke la6e a ciki guda na cewa "baba yakamata fa mu'kara gaba ko mun samu, ya duba agogon hannunshi yace 'karfe ukku da rabi kada gari ya waye mamu anan, kasan oga mayen mata ne duk ranar dabamu samo mashiba bamuda jin dad'i, d'ayan wanda tun farko yace yagaji da sana'ar yace "waallahi ni abin na oga yana bani mamaki, ga yan mata nan karuwai masu Neman mazan da kansu meyasa baya ri'ka d'aukosu yabiya bukatarsa yabiyasu 'kud'insu hankalinshi kwance suma hankalinsu kwance, gudan yace "kai dai banzane baka ta6a ganewa, ai a cewar oga duk macen data kai kanta ga naminiji batada wani fa'ida yafison wacce za'a d'auko Mashi ya mata fyad'e, yafi jin dad'in hakan dan duk wacce aka kawo tana tirjewa yasan ba 'yar iska bace, ko ka manta lokacin damuka kawo mashi wata yarinya tanata ihu tana zillewa, ta d'auka yankata za'ayi koda tagane ba yankata za'ayiba, tagane manufarsa kawai sai tace "dakasan wannan ne da baka sa nayi wahalar hawayena ba, kawai mallam bissmillah, yana ganin haka yace afita da ita, wallahi beyi amfani da itaba, dan ya lura sana'arta ce. Zasu tafi kenan wayar fatima tashiga ruri lokacin, kiran jidda ya shigo, cikin tsananin tsoro da kad'uwa ta sa hannu ta danne wayar, harta tsinke bata d'aukaba sai kuma aka 'kara kira karo na biyu, tayi ko'karin takashe wayar baki d'aya amma sai ta kasa saboda tsananin rud'ewa. Da sauri wad'annan mazan suka shigo cikin kangon gida suna dubawa dan jin waya nata ringing, lokacin kuwa Fatima tagama sadaukar da rayuwarta, cikin sa'a kuwa suka ganta basuyi wata-wata ba suka sungumeta, guda ya d'orata kan kafad'arsa tanata ihu tana dukansa tana yagunsa, hadama cizo amma ko a jikinsa, ganin zata tona masu asiri yasa gudan ya fiddo wani salatif ya toshe mata baki. Tafiya marar nisa ta sadasu da inda suka ajiye motarsu wata bakar Hummer jeef mai ba'kin glass suka jefata ciki, sannan sukaja motar, tafiya mai nisa sukayi wacce fatimar batasan inda sukeba, bata iya ganin kome, saboda duhun dare ga kuma ba'kin glass d'in motar. Bakin wani 'katon gida wanda zamu iya kira aljannar duniya saboda 'kyawunsa, sukayi horn me gadi ya bud'e masu get suka shiga, wani had'adden bedroom suka jefata kan gado sannna suka kware salatif d'inda ke bakinta, saboda tsananin azaba saida tafasa 'kara. Haka suka fita suka barta sukaja 'kofar, itakuma banda kuka ba abinda takeyi. 'Karar bud'e d'akin yasa ta d'ago kanta wani 'katon mutum tagani, dogo ne fari me dogon hanci da manyan idanuwa, ga bakinshi ma barakallahu babbane, ga 'kiba dake gareshi kamar basamude. Tsayawa yayi ya 'karema Fatima kallo, sannan ya matso yana lasar baki kamar tsohon maye, yace "kai amma yau nayi dace tunda ake kawomin 'yan mata ba'a ta6a kawomin 'kya'kyawa kamarkiba, yasa hannu ya cire hijabin dake jikinta, ganin surar jikinta yasashi 'kara rikicewa dan rigar datasa tad'an kameta, ga kanta ba d'an kwali, yayi dariya yace amma kinada ala'ka da india ko? Wannan 'kya'kyawan gashi haka, yakai hannu yana shafa kanta, itakuma kuka kawai take takasa ta6uka kome, a zuciyarta sai addu'a take Allah kada yaba wannan mutumin ikon aikata abinda yake nufi akanta. Haka yacigaba da shafata yana latsata, inbanda kuka ba abinda take, nan yashiga 'kokarin rabata da 'kayan jikinta, tasa hannu ta rirri'ke koda yaga zata kawo mashi gardama sai ya nunamata 'karfi lokaci guda ya rabata da rigarta, jikinta yarage daga ita sai bes, sai wando lagis data Sanya lokacin dazata fito, ganinta haka da bayyanar 'kya'ky'kawar surarta ya'kara rikitashi, ya fita hayyacinshi gaba d'aya ya rungomota jikinshi.... _*Ina barar addu'arku masoyana a duk inda kuke, shekaran jiya anyima babana theatre Emergency, amma yaji sauki, kutayani addu'a Allah 'kara Mashi lafiya da duk musulmi baki d'aya*_ πŸ‘πŸ»πŸ˜­ πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:12 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [03/09 4:10 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 _*ALHINI*_ 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _Written by_ _*Zee Mmn khady*_ 😘 4⃣3⃣to4⃣4⃣ πŸ–Š kuka Fatima tashiga yi ganin yana neman keta mata haddi, tana cewa "dan Allah kayi ha'kuri kada ka cuceni kada ka 6ata min rayuwa, tana fad'ar haka tana wani irin kuka me tsuma zuciyar me sauraro, amma mutuminnan ko ajikinsa, dan ko kad'an bata bashi tausayiba illah 'kara kwad'aituwa dayayi da ita. 'Ko'karin rabata da sauran kayan dasuka rage jikinta yakeyi, itakuma banda addu'a ba abinda takeyi, dan batada wani sauran kuzari tattare da ita. A 6angaren Mukhtar kuwa yasha yawo har kusan 'karfe biyar na asuba amma bega Alamar zega laraba ba, be 'kara shiga tsananin tashin hankaliba saida yafara jiyo kiraye-kirayen sallar asuba, haka yakoma gida zuciyarshi cike da takaici da ba'kin cikin rabuwa da masoyiyarshi. Yana shiga gidan a falo ya iske Hajiya da jidda sun buga uban tagumi, suna tunanin ko yaga fatimar,..... Ganin shigowarshi shi d'aya batare da laraba ba yasa jidda saurin tashi cikin muryar kuka tace "yaya baka gantaba? Innalillahi munshiga ukku, ta fashe da wani sabon kuka. Jiki sanyaye mukhatar yasamu guri ya zauna. Sai lokacin Hajiya ta kalleshi jiki a sanyaye tace "Mukhtar Yaya ba'a gantaba ko? Wata nannauyar ajiyar zuciya yayi sannan ya d'ago da idanunshi wad'anda suka kad'a sukayi ja saboda tsabar damuwa, yace "Hajiya Fatima ta su6ucemin shikenan Hajiya narasa Fatima, lokacin wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanunshi, yace "Hajiya me mukayima Fatima ta gujemu? Me tanema a gidannan tarasa?. Lokacin wani irin tausayin Mukhtar tashige hajiya, a zuciyarta tace tabbas mukhtar yana cikin halin damuwa, dan na lura da yanda ya gama dam'ka duk illahirin soyayyarshi ga Fatima, a Zahiri kuwa cewa tayi "inshaAllah duk inda Fatima take zata dawo garemu, kudai kucigaba da Addu'a Allah tsareta a duk inda take, Lokacin jidda ta fashe da wani sabon kuka tana cewa "ya Allah ka bayyanamin 'yar'uwata a duk inda take, Allah kareta da duk wani mugun abu. Sai da sukaji an kabbara sallah a masallacin kusa dasu sannan kowanensu yatashi yanufi sashensa dan gabatar da sallah, mukhtar kuwa koda yayi Alwala masallaci ya wuce zuciyarshi cunkushe da ba'kin ciki da takaicin halin daze tsinci kanshi inhar yarasa Fatima. A 6angaren laraba kuwa haka mutumin yari'ka jagulata amma har yanzu Allah be bashi ikon cimma burinshiba na keta mata haddi, Amma duk illahirin jikinta yagama jagulata, hannu yakai yana kokarin ida rabata da bes d'in jikinta wacce ita kad'ai tarage sai lagis d'inda tasa hannu ta rirri'ke lokacin dataji yana Neman rabata dashi, Wani irin 'karfi yazo mata a lokacin hannuwanta tasa duka biyun ta d'ora kan 'kirjin mutumin Wanda gaba d'aya yayimata rumfa dashi, ta turashi iya 'karfinta. Jiyayi kamar wasu 'katti goma sun angizashi, yayi baya,yafad'i 'kasa, lokacin kuma Fatima ta taso mashi hai'kan kamar wata tsohuwar damisa, lokaci guda duk wani haske na fuskarta ya dishe, idanunta suka canja launi zuwa ja, tayo kan mutumin hai'kan, a tsorace yatashi yafara ja da baya, dan ya masifar tsorata dan yanda take tunkaroshi. Saida ya dangane da bangon d'akin lokacin yashiga laluben 'kofa dan tsira da rayuwarshi, amma kafin yayi yun'kurin bud'e dakin yafita ta kaimashi wani wawan bugu da hannunta d'aya, wani irin duhu yaga ya gifta mashi, kanshi ya bugu da bangon d'akin, take yafashe jini yafara ambaliya, yana wanke mashi jiki, a tsorace yafasa wata uwar 'kara yana Neman taimako, da gudu yaranshi suka nufo d'akin dan jin ogansu yana neman taimako, suka shiga tura 'kofar amma ko kad'an ta'ki bud'ewa, da sauri guda yanufi wani d'aki ya d'auko wani makullin ya bud'e, da sauri suka nufi inda ogan nasu yake kwance yana maida numfashi sama-sama ga jini duk ya gama wanke mashi jikinshi, suka d'agoshi suna fad'in "oga lafiya meke faruwa? cikin dusashshiyar murya ya nuna Laraba, yace "ita....itac...itace... Nan kafin yagama fad'a masu yafad'i sumamme. A harzuke suka nufi Fatima wacce hankalinta yayi masifar tashi da ganin halin da mutumin dayayi niyyar yimata fyad'e yake ciki, dan ita bata San meya faru da itaba, tun lokacin da mutumin yanemi ida rabata da kayan jikinta. Amma me kafin su 'karaso gareta sai ji sukayi an d'aukesu da wasu mahaukatan marurruka, kowanensu ya dafe kunci yana duba d'an uwansa, kafin suyi wata magana aka rufesu da duka ta ko'ina, nan suka shiga ihu suna neman taimako, amma ba wanda ke jinsu, dan dama haka gidan yake ihunka banza ne, dan da haka ogansu ke samun damar keta haddin 'ya'yan mutane batare da anji koda ihunsuba. Saida suka daku sukayi li'kis sannan aka 'kyalesu, Fatima kuwa banda kuka ba abinda takeyi, dan ita kanta abin ya tsoratata yabata mamaki dan ganin yanda mutanen keshan jibga batare da su duka sunga me dukan nasu ba, Lokacin jikinta yashiga 'kyarma takama kuka tana 'yarfa hannuwa tana kiran innalillahi, Hanyar guduwa tashiga nema dan tsira da rayuwarta, lokacin idonta yakai kan 'kofa dake bud'e tun lokacinda yaran oga suka shigo dasukaji yana neman taimako. Bata tsaya d'aukar kayan taba tanufi 'kofar tashiga falon d'akin tari'ka shiga 'kofofi na gidan, tashiga nan tafita nan amma har yanzu Allah besa taga 'kofar da zata sadata da wajen gidan ba, 'karshe ma idan tashiga wata 'kofar sai taga ta 'kara maidota cikin gidan. Haka tayita zagayen gidan, har 'karfe bakwai da kimanin minti sha shidda na safe, lokacinne kuma oga ya farfad'o daga doguwar sumar dayayi, yayi saurin kai dubanshi gurin da laraba take amma be gantaba, cikin tsananin rud'ewa ya kai dubanshi ga yaranshi dake kwance suma basu san inda kansu yakeba, lokacin ya ta'kar'kara yatashi yakai masu duka, "kutashi kai dan uwarku ku tashi ina yarinyar nan take, a firgice suka kai dubansu ga ko'ina na d'akin basu gantaba. Cikin d'aga murya oga yake magana, kuyi sauri ku nemomin ita, kada ku kuskura tabar gidannan, da sauri suka tashi suka shiga zagaya gidan suna nemanta, dan sun tambayi me gadi yakuma tabbatar masu da bata fitaba, aiko suna cikin dubawa sukayi kici6is da ita a cikin wani korido, wata 'kara ta fasa tayi baya, kafin tayi wani yun'kuri har sun cafkota. Cikin gidan suka koma da ita, wannan karon wani d'akin suka kaita ba wanda suka fara ajiyeta da farko ba. Wata igiya suka sa suka d'ad'd'aureta, sannan sukaja 'kofar d'akin sukasa key suka kulle. Banda kuka ba abinda Fatima keyi, wannan karon tariga ta gama sadau'kar da rayuwarta, Bayan kamar awa d'aya da d'auretane, taji ana murd'a kofar, takai dubanta ga 'kofar dan ganin me shigowa. Oga ne yashigo cikin shigar ba'ka'ken jacket da wando sai wani ba'kin 'katon glass dake fuskarshi me suna no respect 😎. sai yaranshi guda biyu suma cikin 'kananan kaya suna take mashi baya. Bakin 'kofa yaran suka tsaya, kowane gefe guda yayinda sukasa 'kofar tsakiya, Shikum oga ya ida shigowa d'akin inda fatima take d'aure yanufa yashiga zagayata yana tafa hannuwa, itakuma sai binshi take da ido duk illahirin jikinta 'kyarma yake, Wani shu'umin murmushi yayi yace....... 4⃣5⃣to4⃣6⃣ Very πŸ”œπŸ’ƒπŸ» πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:12 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [04/09 3:57 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 _*ALHINI*_ 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _Written by_ _*Zee Mmn khady*_ 😘 4⃣7⃣to4⃣8⃣ πŸ–Š Cigaba yayi da kallonta, sannan yace "A gaskiya na kwad'aitu da kyakkyawar surar da Allah yayimaki, kuma iya tsawon rayuwata ban ta6a d'ora idona kan wata mace ba tabani sha'awa in kyaleta batare dana biya bu'katataba, amma ke sai gashi na kasa aiwatar da kome a kanki. "Ianso zan miki wasu 'yan tamaboyoyi yanzu, ki tabbatar da kin bani amsarsu iyakar gaskiyarki, hakan zesa in fiddaki daga gidannan da kaina batare da wani abu yafaru dakeba. Binshi kawai takeyi da ido, dan ita ahalin yanzu tariga ta sadaukar da rayuwarta, kuma yanzu take danasanin gudowa datayi daga hannun mutanen dasukayi mata halacci, yanzu batasan halin da guduwarta ya jefasu cikiba, tabbas ko ba'a fad'aba tasan idan hankalinsu yayi dubu yatashi, ba kamar masoyinta Mukhtar Wanda ya d'auki son duniya ya d'ora mata, a zuciyarta tace _(ya Allah ka fitar dani daga hannun wannan mugun mutumin, Allah ka maidani gurin masoyina abin 'kaunata Mukhtar)_. Wata uwar tsawa ya daka mata, wacce tayi saurin maidota daga duniyar tunanin data afka, yace "miye sunanki? Jiki na 'kyarma ta kalleshi idanunta na zubar da hawayen nadama tace "Sunana Fatima... Murmushi yayi sannan ya maiamaita sunan fatima koh? Ya'kara tambayarta, ta d'aga Mashi kai alamar eh. Yayi shuru na kimanin mintuna biyu sannan ya'kara jeho mata wata tambayar, "Fatima ke mutum ce ko Aljan? Tace "ni mutum ce. "Amma ke matsafiyace, Jiki na 'kyarma ta girgiza kai tace "Ni ba matsafiya bace ban ta6a tsafiba. Shuru yayi na wani d'an lokaci sannan yace "to fatima abinda yafaru jiya miye kikayi idan kince keba Aljana bace, cikin muryar kuka tace "minayi,? Wallahi banyi kome ba. Cikin takaici ya kalleta yatuno da irin 'karfin data nuna mashi jiya lokacin dayake 'ko'karin yimata fyade, da ciwon data jimashi, yashafa kanshi inda ta dokeshi gurin ya fashe, take wani irin mugun tsoronta ya dirar mashi a zuciya, ya maida kallonshi gareta yace "yanzu zaki iya gane gida? Kai kawai ta d'aga mashi alamar "eh badan tasa ran ze maidata gidan ba. Hannu yasa ya kwanceta daga d'aurin da sukayimata, sannan yace "zaki iya shiga toilet ki watsa ruwa ki canja kaya ni zan maidaki gidanku da kaina, dan barin irinki suna zuwa hannun masu irin halinmu babban had'arine. Be jira abunda zata fad'aba yafita daga d'akin yaranshi suka take mashi baya. Tana ganin yafita jiki na 'kyarma taje ta kulle d'akin hada sa key da sakata, sannan tafad'a toilet tahad'a ruwan d'umi tayi wanka, tad'an gasa jikinta dan duk illahirin jikin ciwo yake mata, sannan ta d'auro Alwala tafito tasa kayanta sannan ta d'ora hijab ta kabbara sallah, dan bata manta da batayi sallar asuba ba. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Zaune suke jugum-jugum kowanensu yabuga uban tagumi bakajin kome sai sheshekar kukan jidda, dan tunda aka tabbatar da 6atan fatima jidda ke kuka, idanunta sun kumbura ga matsanancin ciwon kai dake damunta sakamakon kukan datake ba 'ka'k'kautawa. Mukhtar ma kukan yake kamar mace, kokuma 'karamin yaro, sun tasa hajiya gaba, wacce itama duk illahirin jikinta mace yake, dan ta d'auki fatima kamar 'yar data Haifa da cikinta saboda haka dole taji 6atanta har cikin ranta, amma ganin yanda yaranta suka d'aga hankalinsu yasata daurewa tari'ka rarrashinsu. Suna cikin wannan zaman ne megadi yashigo da sallama, bayan Hajiya ta masa sallamar yace Hajiya sallama ake a waje, cikin damuwa Hajiya ke tambayarshi "wanene me sallamar, yace "eh to Hajiya gaskiya ban shedashiba amma yace maganace me mahimmaci ke tafe dashi idan da hali yanaso ayimashi iso yashigo, Hajiya tace "OK shigo dashi. Bayan fitar me gadi da kamar minti biyar saigashi yashigo, cikin shigar manyan kaya shaddace jikinsa, light blue, sai hularsa light blue, sai takalmi ba'ki, kallo d'aya zakayimashi ka gane mutum ne wanda naira ta zauna mawa... Bayan yasamu gu ya zauna yafara magana "ni sunana sadiq kuma ni d'an cikin garinnan ne, idan bazaku damuba inaso insan yara nawane a gidannan, ma'ana 'ya'ya nawa kuke dasu..... Wani 'kululun ba'kin ciki ya tsayama mukhtar a wuya, a fusace ya kalli mutumin yace "wannan wane irin rainin wayone zakazo kana mana tamabayar da bata shafekaba, Sadiq yabud'e baki zeyi magana kenan sukaji tafiyar mutum ana shigowa gidan, da sauri suka kai dubansu gurin.... Da gudu jidda ta tashi taje ta rungumeta tana kuka, tana cewa "sister ina kika shige kika barmu cikin tashin hankali, fatima kasa furta kome tayi sai hawaye datake zubarwa, cike da murna da fargaba Hajiya tazo takama hannun Laraba tashigo da ita falon, mukhtar kuwa kasa furta kome yayi, illah bin fatima da yayi da ido. Maganar Sadiq ce tadawo da hankalinsu gareshi, yayinda yake sanar dasu abinda yafaru tsakaninshi da Fatima, be 6oye masu kome ba ya sanar dasu gaskiyarshi, dan yariga ya tuba daga mummunar d'abi'ar dayake ta 6ata yaran mutane. Wani irin takaici da ba'kin ciki da kishi suka taru suke rufe Mukhtar dan jin labarin da Sadiq yafad'a saboda haka ido rufe ya tunkareshi kamar wani tsohon mayunwacin zakin daya kwana beciba....... 4⃣9⃣to5⃣0⃣ Very πŸ”œπŸ’ƒπŸ» πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:12 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [04/09 10:48 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 _*ALHINI*_ 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _Written by_ _*Zee Mmn khady*_ 😘 4⃣9⃣to5⃣0⃣ πŸ–Š A zuciye mukhtar yakaima Sadiq wani wawan naushi a fuska, take gancinsa yafara zubar da jini, cikin 'kankanin lokaci jini ya 6ata mashi tsadaddiyar shaddarsa wacce tasha d'inkin computer, ganin jinin dake zuba daga hancin Sadiq besa Mukhtar ya saurara mashi daga dukan dayake mashi ba, cigaba yayi da dukanshi ta ko'ina, sannan yacimashi kwala ya tadashi tsaye ya angizashi, cikin fushi da d'aga murya yace "kafita daga gidannan tun kafin inzama ajalinka, mugu azzalumi barin irinka cikin Al'umma had'arine. Duk abinnan da Mukhtar yayima Sadiq beyi 'ko'karin hanashiba, kuma be kare kanshi daga dukan dayayi mashiba, badan beda 'karfin daze ramaba, dan a girme sadiq yakai d'aya da rabin mukhtar, dan acewarshi duk abinda Mukhtar yayimashi ya can-canci hakan. Jidda ce taga abin na yayanta yayi yawa dan dukan sad'iq yake kamar baze barshi da rai ba, ta kalli Hajiya tace "dan Allah kihanashi kada ya kasheshi, Bata jira hajiyaba tanufi gurin tari'ke hannun mukhtar tana cewa "dan Allah yaya kayi ha'kuri ka 'kyaleshi tunda Allah be bashi ikon aiwatar da kome kan Fatimar ba. Ganin beda niyyar sauronta yasa ta kama hannunshi tari'ke tana bashi ha'kuri a zuciye ya hankad'ar da ita tafad'i zaune tafashe da wani irin kuka. Ganin abin na Mukhtar bana hankali bane yasa Hajiya tazo ta kamashi, tace "kai mukhatar ka daina dukanshi nace, be saurari hajiyaba sai 'ko'karin tura Sadiq waje yake, yana cewa "kafita kabar gidannan ban 'kaunar ganinka, wallahi idan ina ganinka zan iya illataka dan ban had'a fatimana da kowaba. A fusace Hajiya ta fincikoshi, cikin fushi take magana "wai kai Mukhtar wane irin mutum ne, yaushe kafara rainani da inama magana baka saurarena. Wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonshi, baya yayi yasamu guri ya zauna kan d'aya daga kujerun falon yana cika yana batsewa, jiyake dama Hajiya tabarshi da sai yakusa halaka sadiq. Fatima kuwa tunda suka shigo gidan taga halin data iskesu hankalinta yatashi, bata 'kara shiga wani tashin hankalinba saida taga yanda Mukhtar ke dukan Sadiq gashi harya fitar mai da jini amma be daina dukansaba. *_Innalillahi'wa,inna'ilaihirraji'un_* tashiga furtawa, tana kuka kamar zata cire ranta, jidda ce takamata tace "ki daina kuka fatima ki godema Allah daya tseratar dake da mutuncin ki, Cikin dusashshiyar murya Alamar tayi kuka tagaji tace "jidda dole inyi kuka, duk halin damuwar da kuka shiga nice na jefaku, sannan abinda mukhtar yayi yanzu duk saboda ni yakeyi, wayyo Allah na ina zani da Alhaki, nazama butulu, na guji mutanen dasukayimin hallaci a rayuwa, mutanen dasuka sharemin hawayen da 'kanin mahaifina yakasa sharemin, Zuwa tayi gaban Hajiya ta dur'kusa gwiwa biyu, tana kuka tace "dan Allah Hajiya Ku yafemin nasan nashiga rayuwarku na jefaku cikin damuwa. Cike da damuwa da tausayi Hajiya takama hannun fatima ta zaunar da ita kan kujera tana gogemata hawayen dake zuba Daga idonta. . Hajiya takai dubanta ga Mukhtar Wanda keta cika yana batsewa, tace "ba haka akeyiba kawai ka kama mutum kayita duka har ka jimasa ciwo, duk da abinda yafad'i yana aikatawa ai bekai ga aikatashi ga ita fatimar ba, Kuma tunda kaga yakawota har gida ina tunanin akwai dalilin sayasa yakawota. Sannan ta maida dubanta ga Sadiq tace ina jinka yaro, cike da nadama Sadiq yafara magana,cikin muryar tausayi da nadamar abubuwan daya aikata a baya. _ ```na kasance ni 'kadai iyayena suka haifa, kuma iyayen nawa sun kasance masu tarin dukiya, tun ina 'karami suke nunamin tsantsar so da 'kauna, hakan yasa natashi banajin magana ko kad'an kuma duk abinda naga dama shi nakeyi, tun ina secondary school nake 6ata yaran mutane, ta hanyar yimasu fyade idan sun'ki amincewa, a lokacin nama fi so inyi fyaden dan nafi jin dad'in hakan, kuma idan aka ganeni aka kawo 'karata babana sai yakama fad'a yace anjamin sharri dan ana ba'kin ciki da dukiyar da Allah yayi Mashi, kuma yabani shi amatsayin d'a d'aya tilo haka yake fatattakar mutane, wasu su fita suna kuka wasu kuma suje suna Allah ya isa, ana cikin wannan halinne mamana da babana sukayi tafiya, kan hanyarsu ta dawowa suakayi had'ari suduka suka mutu, nayi kukan rashin iyayena sosai, bayan kome ya lafa aka raba gado aka bani, kasancewar bani ganin Kowa da gashin arzi'ki yasa ba wanda yayi gigin cewa ze ri'kemin dukiyata, cikin dangin mamana, kona baba na, haka nacigaba da bushasha, har basamu yarana wad'anda sune ke d'aukomin 'yan mata ina keta masu haddi ta 'karfin tsiya``` Wasu hawaye masu zafi suka zubo daga idanunshi, yace amma sanadin zuwan fatima gareni yasa natuba na daina wannan mummunar d'abi'ar danikeyi, kuma inaso dan Allah fatima ki yafemin, yafad'a yana kallonta. Mukhtar be tausayama sadiq ba ko kad'an illah wani irin haushi daya 'kara bashi yace "dallah Malam kafita kabar gidannan munji duk bayaninka Allah shiryeka, bani son ganinka cikin gidannan kuma bani bu'katar jin muryar ka. Cikin fad'a Hajiya ke magana, dan mukhtar yafara 6ata mata rai tace "wai kai wane irin mutum ne, mutum yazo har gida yaro'ki yafiya amma kakama cimasa mutunci, ay inajin koda kafirine yazo neman gafara gareka zaka gafarta mashi kodan yasan musulunci akwai Alfarma acikinsa, barantana d'an uwanka musulmi, Allah yana son masu yafiya ga junansu, wai Mukhtar ina iliminka yake,? Kuma kafin wannan ma ay komiye fatima itace babbar mai laifi, da bata fitaba da duk haka be faruba. Sadiq yace "ni najin dad'in fitar tata dan tazama sanadin shiriyata, fatana shine tace ta yafemin, yafad'a yana zubar da hawaye... Cikin muryar kuka fatima take magana "tabbas kome yafaru nice na jawo, dan daban fitaba da hakan bata faruba, Ta kalli sadiq tace nayafema, Allah 'kara shiryaka, kuma naji dad'i dana zama sanadin shiriyarka. Tana gama fad'in haka Sadiq yami'ke yace nagode Hajiya sai anjimanku, yafice daga gidan. Fatima kuwa durkusawa tayi tsakiyar falon tana kuka, tana ro'kon Hajiya da jidda da mukhtar su yafemata, Mukhtar har cikin ranshi yakejin kukanta, baze iya juraba saboda haka barin d'akin yayi zuciyarshi na tafarfasa. 5⃣1⃣to5⃣2⃣ Very πŸ”œπŸ’ƒπŸ» *_'kya'k'kyawar gaisuwa ga 'kanwata, NASIBAT ELKASEEM_* _Love u my sister_😘 πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:12 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [06/09 3:22 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 _*ALHINI*_ 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _Written by_ _*Zee Mmn khady*_ 😘 5⃣1⃣to5⃣2⃣ πŸ–Š washe gari bayan kome ya lafa, da misalin 'karfe tara da rabi na safe, Zaune suke a general falo, bayan sun kammala kalacin safe, Kowa yayi shiru, amma akwai abinda yake sa'kawa cikin zuciyarshi, yayinda Fatima takan goge guntayen hawayen dakan zubo mata daga idanunta akai-akai. Mukhtar yana lura da halin datake ciki saboda haka hankalinshi duk yana gurinta, fatanshi Hajiya ta wuce d'akinta ya rarrashi fatimarsa ya kwantar mata da hankali, dan idan akwai abinda yafi tsana a duniya shine 6acin ran hajiyarsa sannan kuma yaga fatimarsa cikin damuwa. Hajiyace ta maido da kowanensu daga duniyar tunanin daya Lula, yayinda ta kalli Fatima tace "Fatima inaso ki nutsu ki kwantar da hankalinki ki fad'amin gaskiyar dalilin dayasa kikayi 'ko'karin guduwa daga hannunmu wanda hakan yajefamu cikin matsanancin tashin hankali. Shuru tayi na d'an wasu mintoci bakajin kome sai sheshshekar kukanta, sannan tafara magana cikin sarkewar murya tace "da farko inaso in ro'keku yafiya akan halin damuwar dana jefaku na 'ko'korin guduwa danayi, Bawai nayi hakan bane dan kun gaza da ri'kon da kukemaniba, ba kuma dan na raina hallacin da kukayimani bane, a'a nayi hakane saboda baniso in sakamaku da sharri akan Alkhairin da kukayimani. Sannan inaso Ku gafarceni akan 6oye maku wasu abubuwa da dama danayi dangane da labarina, yau inaso zan sanar daku kome bakin gaskiyata, dan baniso nazama sanadin rushewar farin cikinku. *_HAKA LARABA TA KWASHE LABARINTA KAF TA FA'DA MASU BATARE DATA 6OYE MASU KOME BA_* Bayan tagama basu labarinta ne tacigaba da cewa "muddin na yarda da auren mukhtar nasan shima 'karshen rayuwarsa yazo, nasan shima ze mutune kamar yanda maza ukku suka mutu sanadiyyar aurena, a 'kauyenmu' yayinda na hud'unsu yasha ba'kar azaba har yarabu dani ranar dana tare gidanshi, shima na tabbata kwanasa ne be 'kareba da yanzu shima sai labari. Jidda wacce tunda Fatima tafara bada labarinta take kuka tace "Fatima duk wanda yamutu kwanansa ne suka 'kare kuma inshaAllah yayana ze aureki kuma ze zauna dake ba abinda ze faru daku. Hajiyama saida ta goge guntayen hawaye dan tausayin da Fatima ta bata, tace ki kwantar da hankalinki Fatima ni nayi Al'kawarin zama dake kuma inshaAllah ko miye ze rabu dake, kuma aurenki da Mukhtar ba fashi muddin kuna son junanku. Wani sanyi Fatima taji har cikin ranta, dan son mukhtar ya dad'e da d'arsuwa a zuciyarta. Shima mukhtar haka yaji, Cike da farin ciki yace "Hajiya inaga Al'amarin Fatima kamar hada iska cikinsa, saboda haka inaso zan kaita gurin wani friend d'ina wanda shida babanshi sun 'kware gurin magance irin wannan matsalar ta hanyar amfani da ayoyin Allah da kuma magungunan musulunci wanda babu shirka a cikinsa. Cike da jin dad'in yanda d'anta keson taimako Hajiya tace "to Allah taimaka Allah sa a dace. Su duka suka amsa da Ameen. Sannan jidda takama hannun Fatima suka nufi d'akinsu, kai tsaye toilet suka shiga suka d'auro alwala suka kabbara sallar nafila da niyyar Allah yayema Fatima lalurar dake tattare da ita. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Washe gari da musalin 'karfe goma na safe sun fito cikin shiri, jidda da faima suna sanye da riga da wando na fakistan sannan suka d'ora hijabansu, sunyi kyau abinsu, Mukhtar kuma cikin shigar manyan kaya shadda ash colour sai ba'kin takalmi sai 'kamshin turarensa daya buge ko'ina, Har mota Hajiya tayi masu rakiya, suka shiga me gadi ya bud'e masu get suka d'au hanya. Mintuna talatin suka sadasu da gidan mal bature, shine mutumin daya 'kware gurin magance matsalar jinnu ko asiri ko sihiri, ta hanyar amfani da ayar Allah batare da an kauce hanya ba. Suna Isa Mukhtar yayima abokinshi waya me suna Usman ya sanar dashi isowarsu, Da far'a ya fito ya tarbesu, sannan yayimasu iso, Bayan sun shiga sun gaggaisa Mukhtar ya sanar dashi abinda ke tafe dasu, duk da dai kamar 'karin bayanine yake mashi dan sun riga sun gama maganar kome ta waya, har Usman d'in ya Sanar da babanshi zuwansu. Nan ya nunamashi Fatima matsayin wacce za'ayima maganin, Fatima wacce tunda sukazo kanta ke sadde 'kasa Usman yakira sunanta "Fatima, sai lokacin tad'ago ta kalleshi, suna had'a ido gabanta yayi mummnar fad'uwa wanda ita kanta batasan dalilin hakan ba. Cewa yayi su biyoshi zuwa gurin babnshi, haka suka bishi Fatima jikinta sai 6ari yake kamar wacce ake girgizawa.... 5⃣3⃣to5⃣4⃣ very πŸ”œπŸ’ƒπŸ» πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:12 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [06/09 7:00 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 _*ALHINI*_ 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _Written by_ _*Zee Mmn khady*_ 😘 5⃣3⃣to5⃣4⃣ πŸ–Š Bakin 'kofar d'akin Fatima ta toge ta'ki shiga, mukhtar ya kalleta yace "muje mana Fatima ko wani abu kk jira, banza tayi ta 'kyaleshi ta tsaya gurin batada niyyar matsawa ciki, saima 'kokarin komawa da baya take. Jidda da tayi gaba harta shiga inda malam yake saida ta waigo taga Fatima da mukhtar basu shigoba, dawowa tayi dan ganin ko lafiya, nan ta iske mukhatar na fama da ita akan ta shiga d'akin ta 'kiya. "Haba Fatima ki shigo mana' gurinfa maganinne mukazo nasan kinfi kowa son rabuwa da lalurar dake tattare dake, jidda tafad'a cikin rarrashi. Ganin Fatima batada niyyar tanka mata kuma batada niyyar shigowa yasa jidda kama hannunta da niyyar tashigo da ita. Saukar wani lafiyayyen mari jidda tayi a kumatunta, Wanda saida ta gigice saboda tsananin zafin marin, takai dubanta ga Fatima wacce ke cika tana batsewa tace "me nayimaki zaki mareni. Cikin wata gur6atacciyar murya Fatima tafara magana, wacce ko alama ba muryarta bace dan muryar tafi kama data maza, "an mareki d'in tafad'a tana wani irin huci, "ke har kin isa ki shigar dani gurin dabanyi niyyaba. Mukhtar naganin haka yasan ba Fatima bace, saboda haka ya kalli jidda yace "maza kiramin Usman ya taimakamin dan wannan abin nayine. Jiki na 'kyarma jidda tatafi kiran Usman, abin kamar jira tana fita kokowa ta kaure tsakanin Fatima da Mukhtar, dan niyyar guduwa tayi shikuma ya ri'keta. Saida Usman yazo da taimakonshi aka shiga da ita inda malam yake. Suna shiga tafasa wata uwar 'kara wacce duk illahirin mutanen dake gurin saida suka firgita, banda Malam wanda dama yasaba ganin irin haka. Fad'uwa tayi 'kasa bakinta na fitar da wani irin kumfa, Malam yataso ya tsaya gabanta yace "waye kai, ko wacece? Shiru Fatima tayi sai wani gurnani takeyi, Malam ya'kara magana karo na biyu nan ma shuru tayi, wani ruwa ya d'auko ya karanta wasu addu'oi yatofa aciki ya watsa mata, wata irin 'kara tasaki firgigi tatashi zata gudu kamar wacce aka watsama garwashin wuta, mallam ya daka mata tsawa yace "koma ki zauna, ba musu ta zauna tanata wani layi kamar wacce tasha ta bugu. Sannan yace ina jinka waye? Cikin muryar daba ta Fatima ba take magana tace "nine, hakan yasa Malam yagane namijine yace "Kaine wah? Yace "nine masoyinta. "Masoyinta kamar ya? "Me shirin aurenta "Me shirin aurenta kome shirin cutar da ita. "Niba cutarta zanyiba, dan na dad'e ina dakon soyayarta tun tana cikin tsumma nake tare da ita ina rainonta da niyyar idan ta girma in aureta. "Kasan dai babu aure tsakanin mutum da aljan saboda haka kayi gaggawar barin jikinta. "Bazan iyaba ina sonta. "Kafita da arzi'ki kokuma in fidda kai da tsiya. "Bazan fitaba ko zaka kasheni. Haka akayita daga tsakanin aljani da Malam, 'karshe dai mallam yayita karanto ayoyi yana tofa mata, tashiga birgima tana ihu, hakan besa mallam ya daina karanto ayoyin Allah yana tofa mata ba. . Kusan awa d'aya da rabi ana abu guda, sannan daga 'karshe Fatima ta fasa wata uwar 'kara tafad'i 'kasa war-was, Wani abin al'ajbi dai-dai wannan lokacin kuma wannan 'katon ramin wanda laraba tayi niyyar fad'awa a 'kauyensu lokacin da mukhtar ya tsinceta, yakama da wuta, Ashe dama nan ne mazaunin wannan Aljanin da yake jikin Fatima. Mallam ya kalkesu yace Alhmdulillahi kome ya wuce, babu sauran wani jinnu a jikinta zaku iya tafiya gida, cike da tsoro jidda ta kalli malam tace "mallam a haka zamu tafi da ita bata fa farfad'o ba, mallam yace "kada ku damu zata tashi wannan nannauyan baccin dole tayishi, ga wannan garin habbatussauda ne tar'ika amfani dashi tana zubawa a abinci ko cikin abinsha, kamar kunu ko koko, ko tea, sannan ya mi'ko wani maganin yace wannan 'kuma haya'kin shaid'anune, tarika turarashi kullum kafin ta kwanta, sannan ta ri'ke addu'oi da azkar da salatin annabi, Allah sauwa'ke, suduka suka amsa da "Ameen. Sun kar6i maganin sukayi godiya,mukhtar ya ajiyema mallam kud'i me tarin yawa yace "mallam ga sadaka, mallam yace Allah ya kar6a. Haka mukhtar da jidda suka kama Fatima wacce batasan inda kanta yakeba, suka sakata mota, Har gurin mota Usman yazo sukayi bankwana yaimasu Allah kiyaye tare dayima Fatima fatan samun lafiya me d'orewa. Tunda suka tafi a mota jidda ke faman kuka dan fatima ta masifar bata tausayi, Mukhtar kanshi 'karfin hali yake gurin driving dan duk illahirin jikinshi kyarma yake, haka suka iso gida bakin get sukayi horn megadi yabud'e masu get suka shige. Suna shiga jidda tabud'e motar tafita, cikin gida tayi tana kuka, Hajiya dake zaune falo tayi uban tagumi tana tunaninsu, tajiyo sallamar jidda, kafin tayi magana jidda tafad'a jikinta tana kuka, Cikin tashin hankali Hajiya ke tambayar jidda "ina fatimar meya faru da ita? Sallamar Mukhtar tajiyo, yashigo falon d'auke da fatima kamar wata jaririya, Shimfid'ar da ita yayi tsakiyar falon sannan yasamu guri ya zauna suka zubama sarautar Allah ido..... 5⃣5⃣to5⃣6⃣ Very πŸ”œπŸ’ƒπŸ» πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:12 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [07/09 9:30 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 _*ALHINI*_ 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _Written by_ _*Zee Mmn khady*_ 😘 5⃣5⃣to5⃣6⃣ πŸ–Š *_BAYAN WATA BIYU_* Fatima ta samu lafiya, kuma acikin 'yan kwanakinne soyayyarta da mukhtar tayi 'karfi wanda sukayi tsananin shakuwa, da so da 'kaunar juna. Wata rana suna zaune a falo su duka kamar yanda suka saba idan sun gama cin abinci, Hajiya ta kalli fatima tace "yakamata kibada izini aje 'kauyenku gurin baffa Lawal Neman aurenki, *'Rassss* Fatima taji gabanta yayi mummunar fad'uwa, lokaci guda tanemi nutsuwarta ta rasa dan ko kad'an bataso ayimataaganar 'kauyensu dan yariga yafitar mata arai, garin da aka 'kuntata mata aka muzantata, garin data wayi Gari yunwa da 'kishirwa sun kusa halakata saboda tsana da tsangwama da suka nuna mata. Hannu tasa ta goge hawayen dasuka 6ata mata fuska, Hajiya tace "ki saurareni fatima, kinsan indai mace na neman mutunci to anemi aurenta gun dangin mahaifinta, shiyasa kikaga na matsa akan aje gun baffa Lawal d'in.... Fatima ta fashe da wani sabon kuka tace "dan Allah Hajiya ki taimaka min ki barni kada inje 'kauyenmu, wallahi banison zuwa, ba yanzu bane lokacin dana yanke zanje 'kauyenmu, nayimaki Al'kawarin idan muna raye inshaAllah ba sai kinyimin maganar ba da kaina zan gayamaki zanje.... Jidda tayi karaf cikin fuskar tausayi tace "dan Allah Hajiya ki barta, idan lokacin yayi zataje da kanta. Cike da tausayi Mukhtar yace "Hajiya dan Allah kiyimata Alfarma ki barta duk lokacin data bu'kata sai taje.... Hajiya tayi murmushi tace "tayaro kyau take bata 'karko, idan kunce inbar fatima kada taje 'kauyensu waye ze zama wakilinta ranar Aurenta? Jidda tayi sauri tace "Hajiya ga 'yan'uwankinan, dan Allah su zama wakilanta. Fatima ta taso jiki sanyaye ta dur'kusa gaban Hajiya ta d'ora hannunta kan 'kafafunta tace "Hajiya kece uwata, kece ubana, kece dangina, nasan Hajiya zaki iya tsayamin akan kome, dan Allah kiyimin kome ba sainaje 'kauyeba, idan lokaci yayi zanje... Cike da tausayi Hajiya tace "to shikenan Allah shige mana gaba, suduka suka amsa da Ameen, jidda hada yin wani gajeren murmushi dan jin Hajiya ta Amince da bu'katar Fatima, dan ita a duniya tana masifar son abinda Fatima keso. *_BAYAN SATI BIYU_* Ansaka ranar Auren Laraba da mukhtar, lokaci d'aya aka sanya dana jidda, hakan yayi dai-dai da saura wata d'aya da sati daya ayi bikin. Wai kada kaga farin ciki tsakanin masoyan, jidda kuwa tafi kowa murna, dan tana masifar son kasancewar fatima amatsayin matar yayanta. Tun daga ranar da'aka saka biki hankali ya kwanta hidima ta kankama, Bayan sati biyu mukhtar yasa akayo ma amaren odar kayan d'aki kome da kome yasa sukayi Mashi list, Ankawo kaya abin gwanin ban burgewa, mukhtar kuwa angama 'kera mashi gidanshi a unguwar dutsin safe malali quaters, gidane nagani na fad'a dan ba 'karamin 'kerashi akayiba. Ana saura sati biyu biki aka kawo lefen jidda daga gidansu sahibinta Usman, akwati shidda nar'ke da kaya nagani na fad'a. Washe gari kuma mukhtar ya dam'kama Fatima nata lefen akwatina takwas, nar'ke da kayan arzi'ki, ranar saida Fatima ta zubar da hawaye na abu biyu, wani 6angaren farin ciki wani 6angaen kuma tana _*ALHININ*_ rashin mahaifiyarta lokacin dazatayi aure, tasan datana raye datafi kowa farin cikin kasancewar zuwan ranar. A 6angaren Hajiya kuwa hidima takeyi sosai dan duk wani Abu daya dace uwa tayima 'yarta lokacin aurenta Hajiya tayima jidda da Fatima, babu wani banbanci take had'e kome tanayimasu tare. Maman Ummi itace 'Kanwar Hajiya wacce sukafi sha'kuwa, saboda haka ita Hajiya tabarma 'kwangilar kome na gyaran amare. Ana saura sati d'aya bikin Maman Ummi tazo har gida tatafi da amare dan gyaresu. Gyara kuwa sosai amare sukasha, cikin kwana biyar, idan kagansu dole ka 'kara kallonsu dan wani masifaffen 'kyau dasukayi, jikinnan nasu har wani she'ki yakeyi, dan dilkar da Maman Ummi kemasu irin wacce ake yiwa larabawace daga 'kasar saudiyya, tataho da ita musamman saboda gyaran amaren, Dan Maman Ummi saudiyya take zaune saboda bikin kawai tazo, dan sune *Amara 'Kirjin biki*_{Littafin badi'at lbrahim}_ dan batada biki kamar na jidda *Autar Hajiya*_{Littafina daya gabata}_ Aiko sunsha gyara gurin Maman Ummi dan wani abun idan tashafe masu jikinsu dashi jin fatarsu suke kamar ta jarirai saboda laushi, 'kamshi kuwa ajikinsu kamar anyi 6arin turare. Gurin 6angaren kayan tsumi kuwa, ba'a magana, dan suma Maman Ummi tazo dasu daga 'kasar saudi, _*(Hmm ni su Maman Ummi mutanen saudia, kome na larabawa)*_😜 πŸ–ŠZee Elkaseem Mmn khadyπŸ’‹ [10/16, 8:12 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [08/09 9:37 am] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 _*ALHINI*_ 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _Written by_ _*Zee Mmn khady*_ 😘 5⃣7⃣to5⃣8⃣ *_RANA BATA 'KARYA SAI DAI UWAR 'DIYA TAJI KUNYA_* πŸ–Š Ni zee da inada dogon hanci dana rangad'a guda, amma ko yanzuma bata 6aciba dole ince πŸ‘ƒπŸ» Ayuuririri........ πŸ’ƒπŸ» Yau nahango dandazon dubban jama'a 'kofar gidan su jidda da mukhtar wad'anda suka halacci d'aurin auren Mukhtar da amaryarsa fatima (laraba) sai jidda da angonta Usman, kowanensu akan sadaki dubu sittin-sittin. Wai kada kaso kaga farin ciki gurin masoya aranar, mukhtar na hango ansha shadda hada uwar babbar riga, ga hula an d'ora, takalminnan nasa designer massaraci abin dai yabadada kala, kallo d'aya zakayima angwayen kagane suna cikin farin ciki, dan kowannensu bakin ya'ki rufuwa. Amare kuwa acikin gida Mmn Ummi tagama shiryasu cikin wani rantsatstsen material, kalar purple sai takalmin 'kafafunsu fari kowace da Jakarta fara, sai manyan mayafinsu fari da aka yafa musu, sunyi wani masifaffen 'kyau kamar yayan sarakuna, kome iri d'aya akayimasu musamman Hajiya tayi masu kaya kala shidda-shidda domin yin hidimar biki, dan suduka ba wacce tayi amfani da kayan lefenta. Da misalin 'karfe biyar na yamma Hajiya ta tara amaren a bedroom d'inta tana yimasu nasiha, ba abinda sukeyi sai kuka, jidda na kukan rabuwa da hajiyarta da kuma farin cikin kasancewa da masoyinta, yayinda Fatima kukanta ya kasu kashi ukku, wani 6angaren farin ciki wani 6angaren kukan rabuwa da Hajiya matar data zama tamkar uwa uba dangi agareta, sannan babban jigon yin kukanta shine *_ALHININ_* rabuwa da innarta, taso ace inna na raye a dai-dai wannan likacin itama taga Auren 'yarta tayi farin ciki, amma ina ba haka Allah ya 'kaddaraba... Ana cikin haka motar Alh mansir tayi parking a harabar gidansu jidda, Alh Mansir 'kani ne ga mahifinsu Mukhtar kuma shine ke shige masu gaba akan kome idan bu'katar hakan ta taso. Ganin shigowarsa yasa Ameeno saurin tashi daga zaman datayi kusa da Maman Ummi wacce keta bata labarin saudiyya, dama Ameenoo da Mmn Ummi 'kawayene, tun kafin Maman ummin tayi aure sukoma saudiyya itada me gidanta, Ameeno kuwa a gombe take aure amma duk da haka suna waya da Maman ummin. 'Dakin Hajiya tanufa ta iske ta tasa maren gaba tanayimasu nasiha, guri tasamu ta zauna itama ta d'ora da nata nasihar, dama Amino badai nasihaba, dan kan nan nata cike yake da wa'azi da nasihohi. Ahaka mutanen dake falon suka fara magana afito da amaren, jidda najin haka tafad'a jikin hajiyarta tana kuka, da 'kyar aka 6am6areta jikin Hajiya aka fita dasu kowace na sharar hawaye. Alh Mansir da kanshi yakai kowace gidanta, sauran mutane kuwa sai dai sukabi daga baya dan ganin gidajen amaren. Alhmdulillahi jidda ma gidanta ya had'u a unguwar layout aka kaita, fatima kuwa malali quaters mukhtar ya 'kyan'kyara masu 'kerarren gidansu. Bayan mutane sunje anga gidajen amaren anyimasu duk abinda yadace bayan sallar isha'i kowace takama gabanta, anbar amare su kad'ai a gidajensu. Fatima zaune tsakiyar gadonta ta had'e kai da gwiwa tana sharar hawaye wanda ita kanta ta kasa tantance na minene, farin ciki ko *_ALHINI_* A haka angon nata ya risketa, tanajin shigowarshi amma bata d'ago ta kalleshiba. Hawowa yayi kan gadon ya zauna gab da ita har jikinsu na gugar na juna, hannu yasa ya yaye lullu6in dake kanta, yasa hannu ya d'ago da 'kya'kyawar fuskarta wacce duk ta 6aci da hawaye, yace fatimana miye yasaki kuka, Baku far in ciki da kasancewa mallakina ne,? Shiru tayi mashi tacigaba da zubar da hawayenta wani na bin wani. Farin handkerchief ya fiddo daga Aljihunsa yasa yana goge mata hawayen dake zuba daga idonta, wani daddad'an 'kamshi dake jikin handkerchief ya doki hancinta batasan lokacin data saki wata ajiyar zuciyaba, "Plz fatimana ki dainamin asarar hawayenki, baniso, idan kuma kinaso nima kiga nawa hawayen to kicigaba da zubar danaki, kinriga kinsan damuwarki damuwatace, farin cikinki shine nawa, ki taimakeni ki daina kukannan. Haka yayita rarrashinta harya samu tayi shiru, sannan ya tashi ya nufi kitchen da kansa ya d'auko plate da duk wani abu dayasan zasu bu'kata. Dan'kara² kajine guda 2 ya baje musu da kanshi yari'ka yaga yana samata abaki, da tana d'an nonno'kewa tanajin kunya har dai tasaki jikinta taci, shima yaci sosai sannan yazuba musu lemu cikin glass cup suka sha sannan sukabi da ruwan roba, bayan sun kammala ne ya kalleta yace "kinyi sallah isha'i kuwa kai kawai ta iya d'aga mashi alamar eh dan duk illahirin jikinta 'kyarma yake sakamakon wani mayen kallo dataga mukhtar namata, yace "to sai ki tashi mu d'auro Alwala mu gabatar da sallar nafila domin nuna godiyarmu ga Allah daya cika mana burinmu, Nan fa ta daburce tarasa wacce amsa zata bashi dan tasan tana fashin sallah ne kuma bazata iya fad'a mashi ba. Tashi tayi tafad'a toilet tashe'ka wanka ta gyara jikinta, sannan tafito shima wankan yashiga, kafin yafito ta shafe jikinta da mayukan masu dad'in 'kamshi tare dayima jikinta 6arin turarruka masu 'kamshin gaske, sannan tanufi wadrope ta d'auko rigar baccinta tasaka tabi lafiyar gado. Mukhtar kuwa daya gama wanka sai ya d'auro alwala, yana fitowa yaganta kwance, beyimata magana ba saida ya d'auko wata jallabiya milk me gajeren hannu ya Sanya sannan yace "ki taso muyi sallar, shiru tayimashi tare da lumshe idanunta kamar bata jinsa, ganin tayimashi shiru yasa ya hawo kan gadon ya tallafo ta yace my fati kitashi muyi sallah, ahankali ta baud'e idonta tace nayifa sallah yace "eh kinfad'amin sallah nafila nake nufi, cike da jin kunya tace "uhm ina fashi ne, wani irin fad'uwar gaba yaji dan jin tace tana fashin sallah dan yau yayi niyyar suci amarcinsu, amma ba hali, haka ya kwantar da ita yaje ya kabbara sallah nafila raka'a biyu yayi sanan yayi addu'a yashafa, kafin yagama bacci me dad'i yayi awon gaba da ita. Yana kan prayer mat yajuyo ya kalleta baccinta take cikin kwanciyar hankali, ya 'kurama 'kya'k'kyawar fuskarta ido yayi wani 'kyawataccen murmushi, addu'a yayi ya shafe jikinsa sannan itama yayi addu'ar yashafe mata jiki, sannan ya kashe fitilar d'akin ya kunna masu ta gefen gado, sannan ya haye gadon ya rungumota jikinshi zuciyarshi cike da farinciki, a haka har bacci me nauyi yayi awon gaba dashi. A 6angaren jidda kuwa a ranar Usman ya more kud'in sadakinsa dan be d'aga mata 'kafaba, ba 'karamar hawala tasha ba, haka ya rin'ka raraahinta yana shimata Albarka, wani irin sonta ya'karaji cikin zuciyarshi dan yanda yasameta yaji dad'i sosai. πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn Khady πŸ’‹ [10/16, 8:12 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [08/09 9:40 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 _*ALHINI*_ 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _Written by_ _*Zee Mmn khady*_ 😘 5⃣9⃣to6⃣0⃣ *_BAYAN SATI BIYU_* πŸ–Š da misalin 'karfe biyu na rana fatima na hango kitchen tanata ha'kilon had'ama me gidanta abinci. Cikin awar da bata wuce d'aya da rabi ba tagama shirya kome kan dining, sannan tanufi d'akinta bayan tagyara kitchen d'in tsaf ta goge ko'ina kamar ba yanzu tagama girki ciki ba. Kai tsaye toilet tafad'a ta she'ka wanka, sannan ta d'auro Al'wala tafito ta kabbara sallar azahar, bayan ta kammala sallar gaban dressing mirror ta zauna tafara d'and'asa kwalliya, bayan tagama wadrope tanufa ta d'auko wasu riga da siket na atamfa ta Sanya, kayan kuwa sun zauna da6as jikinta kamar a jikin nata aka d'inkasu, sannan takashe d'aurin d'an kwali, turarruka ta feshe jikinta take 'kamshin jikinta ya gauraye da 'kamshin preshner dake d'akin da 'kamshin girkin datayi, yabada wani kalar 'kamshi me dad'in sha'ka. 'Karar tsayuwar motar angonta taji, da sauri tafito ta zauna falo tana jiran shigowarshi, dan yahanta zuwa tarboshi harabar gidan saboda me gadi na kallonta shikuma yana masifar kishinta. Da sallama yashigo falon, da sauri ta tashi ta tako zuwa gurinshi tana wani yanga tana karairaiya kamar wacce batasan taka 'kasa, rungumeshi tayi tare dayimashi 'kya'k'kyawan Sumba a kumatu tace "welcome my husband, yace welcome fatimana, nasameki lafiya, cikin zazza'kar muryarta tace "lafiya lao, kadawo lafiya yace "lafiya. Tace kafin kome muje ka watsa ruwa tukun, ba musu yabita zuwa toilet dinshi tahad'a mashi ruwan wanka sannan yashiga itakuma ta jawo mashi 'kyauren toilet d'in, sannan tazauna bakin gado tana jiran fitowarsa. Bayan ya fito ya sanya kaya marar nauyi sannan tayimashi jagora suka nufi dinning. Cike da jin dad'i da farin ciki suke cin abincin, har suka kammala, sukayima Allah godiya, Mukhtar ne yafara tashi daga dinning d'in yakoma kan kujera three seater ya kwanta, itakuma fatima tsayawa tayi tana tattare kayan dasukaci abinci. Bayan takai kuloli kitchen tadawo zata d'auki jug da cup's, sai taga wani had'ad'en zobe kan table d'in, dariya tayi sannan ta d'auki zoben tace nayi tsintuwa, mukhtar najin haka yatuno da zobenshi daya ajiye kan table din, da sauri yataso yace kibani ring dina, πŸ’ nasan dai shine kika gani, cike da tsokana tace bazan bayar ba, saika fad'amin wacece tabaka, cike da tsokana yace budurwata tabanishi kuma zoben Al'kawarine, bekamata ta ganni babu shi a hanuna ba, fatima ta yamutsa fuska tace "idan taganka babu shi ta tambayeka kace mata wacce tafita power a gurinka tarabaka dashi, matsowa yayi gab da table d'in yace "kibani abuna tun muna wasa da juna, cike da nishad'i ta 'kyal'kyale da dariya tace "bazan bayarba, yana kallo ta zirashi a yatsanta, aiko da sauri yanufota yana dariya yace "kkkkk kada ki Sanya........ Kafin yazo harta Sanya aiko ya nufota ze kar6a da gudu ta ruga tana dariya yabita haka suka rin'ka zagayen falon amma besamu ya dam'keta ba, bedroom tanufa dagudu yabita tana 'ko'karin turo 'kofar yayi saurin turawa yashiga, dariya takamayi tafad'a kan gado tana maida numfashi, shima kan gadon yafad'a kusa da ita yana maida numfashi, rungumota yayi jikinsa yace "waye nakama, dariya tayi tace baka kama kowaba, dariya yayimata yace zakiyi bayani zaki san ban kama kowaba, Nan fa wasa ya canja salo, a lokacin saida suka samu ladar aure, Saida sukaji amfara kiran sallar la'asar sannan suka dawo hayyacinsu, toilet suka nufa suka she'ka wanka sannan suka d'auro alwala, mukhtar yawuce masallaci, itakuma fatima Bakin gado ta zauna zuciyarta cike da farin cikin yanda mukhtar d'inta ke nuna mata tsantsar so da 'kauna. Wayarta ta lalubo ta 'kira jidda, ringing biyu ta d'auka "hellow sister ya kike, "lafiya lao sister ya amarci, to Alhmdlh zamuce, haka sukasha firarsu, kusan kullum dama sai sunyi waya akalla sau hud'u ko sau shidda. Bayan sunyi sallamane fatima ta tashi domin gabatar da sallar la'asar. Rayuwa me dad'i da so da 'kauna tsakanin masoyan abin gwanin birgewa, 6angaren jidda ma tana samun kulawa sosai daga gurin Usman d'inta. Fatima da jidda sukam sunyi dacen mazaje saidai suyima 'yan baya fatan samun mazaje kamar nasu. Sai dai lokaci zuwa lokaci fatima na kukan *_ALHININ_* Innarta, kuma tanason zuwa 'kauyensu amma lokacin data tsarama kanta na zuwa 'kauyen beyiba. πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:12 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [11/09 9:00 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 _*ALHINI*_ 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _Written by_ _*Zee Mmn khady*_ 😘 6⃣1⃣to6⃣2⃣ *_BAYAN SHEKARA 'DAYA_* πŸ–Š Fatimana......Fatimana.....tun daga falo yake kwalamata kira, amma yaji shiru, cike da mamaki ya nufi d'akinta dan yasan muddin tana lafiya to dataji tsayuwar motarshi take zowa bakin 'kofar falo tajira shigowarshi ta tarbeshi, amma yau sai yaga akasin haka, cike da fargaba yanufi d'akinta dan yimata Albishir Wanda yasan idan tajishi har 'kyauta sai tayimasa, dan kuwa so yake ya gayamata haihuwar jidda, dan kullum batada magana saita haihuwar jiddar, duk da itama tana fama da tsohon cikinta haihuwa ko yau ko gobe koma yanzu. Ringing d'in wayarta yajiyo bedroom d'inta hakan ya tabbatar mashi da tana ciki, dan haka da sauri yanufi d'akin. Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un ya furta tare da saurin 'karasawa ya tallafota ya had'ata da jikinshi yana fad'in "lafiya fatimana meya sameki, meya faru, cikin tsananin azabar rad'ad'in ciwon dake addabarta ta nuna mashi mararta, sannan ta dafe bayanta tana wash.... Can ciwon ya'kara tsinkulota tafara salati cikin wata wahalalliyar murya "wayyo yayana zan mutu ka taimakamin bayana ze 6alle 'kuguna, tana fad'i tana 'kara shigewa jikinsa tana kuka, cikin tsananin rud'ewa Mukhtar ke rarrashinta ga kuma wayarta gefe tanata ringing amma bebi kantaba, lalla6ata yayi ya kwantar da ita tare da fita domin yakira wata makwabciyarsu malamar asibiti, da sauri yashiga gidan sister safiyya ya sheda mata halin da Fatima take ciki, ba'afi minti gomaba suka shigo gidan tare,tana zowa tasa safa ta dubata taga ta kusa haihuwa, nan ta rubutama Mukhtar duk abubuwan da ake bu'kata. Da sauri yaje chemist d'in kusa dasu ya siyo, yana dawowa yabata kayan ba'afi mintuna 5 da dawowarsaba laraba tayi wani 'kwa'k'kwaran nishi me 'karfi tare da santalo sankad'ed'en yaronta. Sister safiyya tayi hamdala sannan ta gyara yaro tayima Fatima duk abinda ya dace, mukhtar kuwa dan tsananin murna bakinshi ya'ki rufewa nan ya fiddo yawa yakira Hajiya ya sanar da ita haihuwar Fatima, sannan yacigaba da 'kiran 'yan'uwa da abokan arzi'ki yana sanar dasu. Bayan sister safiyya ta taimakama Fatima tayi wanka ta gyarata itada baby. Fatima ta fito shar da ita kamar ba itabace wacce ta haihu sai buga uaban 'kamshi take itada baby, sister safiyya da kanta ta shiga kitchen tahad'oma Fatima tea me kauri Wanda yaji milo sosai takawomata tana zaune bakin gado, saida ta tabbatar data shanye duka sannan tabata magungunanta tasha sannan tafito da niyyar tafiya gida. A harabar gidan tagamu da mukhtar yana niyyar fitowa daga mota, da Alama wani wuri yaje amma bame nisaba saboda be dad'e da fitaba, ganinta yasashi saurin ida fitowa daga motar yace "ah sister har kin fito? Cikin fara'a da sakin fuska tace "harna fito Baban baby, zanje gidane kafin in 'kara zagayowa inga lafiyar baby da momynsa. Cike da jin dad'i mukhatar yayimata godiya sannan ta wuce, shikuma yashiga cikin gidan kai tsaye bedroom d'in fatima ya nufa da sallama yashiga. Zaune take gefen gado ta rungume babynta tanata murmushi abinta, da murmushin shima ya 'karaso yasa hannu ya 'kar6i baby yayimashi addu'a sannan yayimashi hud'uba kamar yanda addinin musulunci ya tanada,ya dad'e yana kallon babyn sannan ya maida dubanshi gareta yace "ammafa babyn nan dani yake kama,cikin shagwa6a tare da marairaice murya tace "Ba wani dani yake kama, cikin tsokana mukhtar yace "Ba wani ki duba kiga hancinsa irin nawane da manyan idanunsa, yafad'a yana kallonta cikin tsokana dan yasan kallo d'aya zakayima idanun yaron kasan irin na Fatima ne, bandasu amma duka face d'in mahaifinshi ya d'auko, Cikin murya kamar zatayi kuka tace "ka tambayi sister safiyya kaji tun tana mashi wanka tace dani yake kama...... Mukhatar ya 'kyal'kyale da dariya dan ganin yanda Fatima ta ha'kikance akan yaro yana kama da ita... Cikin nishad'i yacigaba da magana ammafa gaskiya sister safiyya tanada kirki, kiduba kiga yanda take hidima dake, fatima tace "hmm kaidai bari wallahi ni har kunyartama nakeji, yanzu abinda tayimin ko asibiti naje baza'a kula dani kamar hakaba........ Wayartace ta katse masu firar dasukeyi tahanyar yin ringing Alamar ana kira, da sauri ta tashi ta d'auko amma kafin ta danna OK har kiran ya tsinke, 18missed call tagani... Fiddo idan tayi waje tare da kallon Mukhtar tace "18 missed call, yace ki duba kigani nasan dai bewuce jidda, kinsan itama ta haihu.... Cikin zumud'i tace "dan Allah fa banda tsokana, yace "kirata kiji d'azu da Albishir d'in nazomaki saina taras kina labour shiyasa hankalina ya d'auke ban gaya makiba. Wayarta ta Shiga dubawa aiko 15missed call tagani na jidda sai 3 na Hajiya, Hajiya tafara Kira ta gaisheta, nan hajiyar ke nunamata cikin tsananin farin cikin datake na samun jikoki biyu Lokaci guda.... Nan Fatima ta ida tabbatar da maganar haihuwar jidda, saboda haka sunayin sallama da hajiya number jidda takira, lokacin itakuma jidda tanada labarin haihuwar larabar haka suka dad'e suna waya sunama juna barka sannan sukayi sallama. Itakuma jidda da asubane ta haihu tasamu baby girl, fatima kuma bayan azahar. _````ZEE```_ *Wishes u* ```HAPPY SALLAH``` *IN* _*ADVANCE*_ πŸ’ž```EID MUBARAK```πŸ’ž πŸ“note Inaba masu bin wannan Littafin ha'kuri akan jina da kukayi shuru kwana biyu, hakan yafarune saboda wasu 'yan hidimomi dasukasha kaina, gakuma hidimar sallah saboda haka kucigaba da ha'kuri zan ri'katurowa duk lokacin dana samu lokaci kafin agama hidimar sallah. Love u all πŸ’ƒπŸ» πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:13 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [17/09 8:34 am] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _Written by_ _*Zee Mmn khady*_ 😘 6⃣3⃣to6⃣4⃣ Haka 'yan uwa da abokan arziki sukayita zuwa gidan mukhatar da gidan jidda suna ganin baby, barakallahu. jidda Usman yayimata kaya nagani nafad'a, akwati ukku yacikama baby da kaya, jidda kuma akwati biyu sha'ke da kayanta, 6angaren mukhtar kuwa akwati set yacikama fatima da babynta, abin dai gwanin sha'awa anyi kome cikin tsari. Ranar kwana bakwai akayi suna, d'iyar wurin jidda aka samata suna Rahama, d'an gurin fatima kuwa sunan Mahaifin mukhtar aka sanyamashi, amma suna kiranshi sultan. Ba 'karamin abin arzi'ki fatima ta tara gun sunan ba, saboda 'yan'uwan mukhtar sunyi mata kara sosai, a ranar ma saida jidda ta zubar da hawayen *_ALHININ_* tunowa da mahaifiyarta, da kuma ganin duk taronnan da kuma abin arzikin data tara babu 'yan'uwanta ko d'aya. Yanzu gashi tayi aure har Allah ya azurtata da samun d'a amma ba rabon innarta taga wannan ranar, *(Allah sarki laraba haka Allah ya 'kaddara)* Haka akagama hidimar suna Kowa ya koma gidansa cike da farin ciki, washe garin suna hajiya tace Mukhtar ya maido fatima gida dan tayi wanka anan, haka Mukhtar ya maidota badan ranshi yasoba, yaso ace anbarta gidanta tayi wanka acan kullum yana kusa dasu itada babynsa, ya d'auko matar dazata ri'ka kula dasu amma Hajiya ta'ki amincewa da hakan, saboda haka dole ya tattarasu ya kaisu can badan ranshi yasoba sai dan bin umarnin mahaifiyarsa. Jidda kuwa dama Usman tunda aka gayamashi ya amince da tafiyarta gida wanka, saboda haka itama washe garin suna Usman da kanshi ya tattaro ya kawota gidan da kanshi. Haka Hajiya tacigaba da kula da 'ya'yanta da jikokinta, tare da taimakon jummai me aiki. _*BAYAN WATA BIYU*_ Hajiya na zaune falo ta tasa 'yan jikokinta gaba zuciyarta cike da farin ciki, yaran sai wutsil-wutsil suke da 'kafafunsu da hannuwa alamar suna cikin 'koshin lafiya. Jidda kuwa da fatima suna zaune gefe sunsha kwalliya kamar wasu sabbin amare, dan bazaka kallesu kace sun ta6a haihuwaba, kome nasu cif, jidda kwalliyar tata ta taron me gidanta ce dan yayimata waya yana zuwa, itakuma fatima dama tunda suka dawo gidan shima mukhtar ya dawo nan dan kwana kad'ai ke beyi anan. Da misalin 'karfe hud'u na yamma Usman ya iso gidansu jidda, Bayan yayimata waya ya sanar da ita zuwanshi tayimashi masauki a a falon ba'ki, bayan ta cikashi da kayan ciye-ciye da lashe-lashe, komawa tayi cikin gida ta d'auko rahama, a kafad'a ta sa6ota, tana taku Ahankali cikin nutsuwa harta iso gurinsa tasamu guri ta zauna gab dashi, 'kamshin turarensu ya gauraya dana juna, sannan ta gaidashi, bayan ya amsa suka cigaba da firarsu. Acikin firar nasu ne Usman yake cema jidda "A gaskiya jidda nayi rashinki kusa dani yaufa tsawon wata biyu kenan yakamata ace kin koma hakanan, jidda tayi murmushi tace nima nayi missing d'inka, usman yace "ban yarda da zancenkiba, jidda tayi saurin kai dubanta gareshi "baka yardaba fa kace, yace "kwarai ko dakinyi missing d'ina dakincema hajiya kinaso ki koma haka, domin ni gaskiya inajin kunyar fad'amata, jidda tayi murmushi tace "indai wannan ne kada ka damu kabani kwana biyu inshaAllah zan dawo cike da jin dad'i usman ya rungume jidda yana sumbatar ta, wani irin feeling sukaji suduka sakamakon rashin jin d'umin junansu dasukayi na tsawon lokaci. Baby rahama kuwa kwantar da ita jidda tayi kan kujera tanata sharar baccinta, Haka suka rin'ka romancing junansu, lokaci guda Usman ya rikice yafita hayyacinsa, idanunshi sun rufe yama manta da gidan surukai yake, sai da jidda taji yana 'ko'karin wuce gona da iri sannan tayi 'ko'karin saita nutsuwarta dan itama ta shiga wani irin yanayi, ta tureshi daga jikinta sannan ta tashi daga kujerar dayake ta koma nesa kad'an dashi tana maida numfashi, Shima kallonta kawai yake yakasa ta6uka kome idanunnan nashi sun kad'a sunyi ja, kusan mintuna ishirin suna haka sannan suka dawo hayyacinsu, ya kalli jidda cikin wata wahalalliyar murya yace "jidda zan tafi kinga magrib ta gabato amma zan shiga mu gaisa da hajiya tukun, tace "ba damuwa amma kasa ran dawowata nan da 2 days, yace "danafi kowa farin cikin hakan, tayi wani 'kawataccen murmushi tace kada ka damu abban rahama, wani irin dad'i yaji dan jin sunan data kirashi dashi, sannan yakai dubanshi ga 'kya'k'kywar babynsa rahama wacce ke baccinta cike da jin dad'i, yace "je kiyimin iso gun hajiyar. Haka ya shiga suka gaisa da hajiya, fatima da kanta tazo suka gaisa sannan ya d'auki sultan yana mashi wasa, jin anata kiraye-kirayen sallar magrib yasa ya mi'ke tare dayimasu sallama sannan ya wuce, jidda tarakashi har gurin motarshi saida taga tafiyarshi tana d'aga mashi hannu sannan tadawo cikin gida cike da tsananin so da 'kaunar mijinta. πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:13 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [17/09 7:30 pm] πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _Written by_ _*Zee Mmn khady*_ 😘 6⃣5⃣to6⃣6⃣ πŸ–Š Bayan sallar isha'i mukhatar ya shigo gidan a falo ya iskesu zazzaune suna shirin cin abinci, Shima zama yayi fatimace tayi serve kowa ta ajiye a gabanshi, bayan sun kammala cin abincinne Hajiya ta kalli mukhatar tace "d'azu mijin jidda yazo kuma ya nuna yana bu'katar matarshi saboda haka bazan tauye masu hakki ba na yanke shawara jibi zata koma gidanta kamar yanda itada mijin nata suka yanke, sannan ta maida dubanta ga fatima wacce keta faman rirriga sultan shikuma yanamata 'yar rigima tace "kema fatima sai ki shirya jibin kibi mijinki. Wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyar mukhatar dan jin Hajiya tabashi izinin tafiya da fatimarsa, Fatima kuwa gyara zama tayi lokacin tasamu sultan yayi bacci ta kwantar dashi, sannan ta kalli Hajiya tace "Hajiya Kafin inkoma ina Neman wata Alfarma, Hajiya ta maida dubanta gareta tace ina jinki Wasu irin hawaye masu zafi suka zubo kan kumatunta, tasa hannu ta goge sannan tace inaso dan Allah kafin inkoma inje 'kauyenmu..... Hajiya ta numfasa tace "to Alhamdulillahi naji dad'i da ya kasance yau da bakinki kika furta kinason zuwa, amma bazance komeba akan tafiyar ga mijinki nan kuyi shawara. Mukhtar yayi murmushi mai d'auke da damuwa dan ganin fatimarsa na zubar da hawaye, yace "Ba kome hajiya nima naji dad'i da hakan, amma tunda jibi ne aka sanya ranar komawar tasu sai ta shirya gobe muje garin nasu. Cike da jin dad'i laraba ta kalli mijinta tayi mashi wani 'kyawataccen murmushi, shima murmushin ya mayar mata. Jidda dake zaune tanajin duk abinda aka tattauna, bata tanka ba tashi tayi kawai tanufi bedroom wayarta ta d'auko tashiga laluben sunan Usman sannan ta danna mashi kira yana d'agawa tace "dan Allah abban rahama inaso gobe zamuje garinsu Fatima, Usman yace "me akeyi ne? Tace "zamuje mu gaidasu ne. Yace "ba damuwa, ki kularmin da kanku keda baby rahama Allah kiyaye hanya Tace "Ameen" Sannan ta tsinke kiran ta ajiye wayar ta dawo falo. Yanda tabarsu zaune haka ta tarar dasu gurin datake ta koma ta zauna sannan ta kalli Fatima tace "sister goben sai muje tare ingano garin naku nima. Wata irin harara Hajiya tayimata tace "da izinin wah zaki tafi? Ta kalli Hajiya tayi murmushi tace abban rahama ne yace inje, Hajiya tace "yaushe kukayi maganar ? Tace "yanzu fa nakiraahi a waya. Hajiya tace "to Allah kaimu goben kuma Allah kaiku lafiya ya maidoku lafiya. Sai lokacin mukhtar yayi magana yace "Amma gaskiya Hajiya abinda jidda keyi bata kyautawa yanzu dagajin tafiya harta sanar da mijinta zataje da son yawon tsiya kamar taci 'kafar kare. Jidda ta turo baki tace "ay dama tuni nake cema sister duk ranar dazata garinsu tare zamu tafi. Hajiya najinsu bata tanka masuba, tasan dai duk abin mukhtar tunda jidda ta 'kwallafa rai a tafiyar nan saitaje sai dai idan Allah ne be 'kaddara ba. _```WASHE GARI```_ misalin 'karfe tara na safe na hango fatima cikin wata shiga ta Alfarma wacce shigar tafi kama data 'ya'yan sarakuna. Dan wani tsadadden material ne purple jikinta me Ado da wasu kalan duwatsu masu haske, sai zanen farin flowar jikinsa, sannan wasu tsadaddun takalmi dake 'kafarta, material d'in d'inkin riga da zani pieces hakan ba 'karamin 'karamata girma yayiba, da kyau da kwarjini, wani babban farin mayafi ta yafa shikuma farine anyimashi ado da flower's purple sai adon duwatsu farare. Sultan na sa6e a kafad'arta shima anyimashi shiga ta Alfarma kayan jikinshi shima farine da purple sai fararen kyawawan takalmashi masu tsada. Jidda ma kwalliya tayi tagani ta fad'a dan itama ba daga bayaba gurin kyau, itakuma material d'in nata golden colour ne haka takalmi da mayafinta da jakar data rataya, baby rahama ma shigar golden d'in akayimata. Sai oga mukhatar shima yayi shiga ta Alfarma dan wata tsadaddiyar wagambari ya sanya ash colour sai hula itama kalar ruwan toka sai ba'kin takalmi, sai 'kamshin daddad'an turarensa dake tashi. Haka suka Shiga mota kirar Camry kalar ruwan toka me duhu, Hajiya na tsaye tanayimasu addu'ar zuwa lafiya da dawowa lafiya, Megadi ya bud'e masu get suka d'auki hanya, tafiya suke cikin nutsuwa da kwanciyar hankali dan mukhatar mutumne me nutsuwa saboda haka kome nashi cikin tsari yakeyinshi saboda haka tafiyar da bata wuce tsakanin awa ukku da rabi zuwa awa hud'uba ya sadasu da garin su laraba. πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:13 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [18/09 6:58 am] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _Written by_ _*Zee Mmn khady*_ 😘 6⃣6⃣to6⃣7⃣ πŸ–Š Suna isa 'kofar gidan baffa Lawal suka sauka bayan sunyi parking d'in motor d'insu suduka suka fito daga motar, Fatima ta kalli gabas da yamma kudu da arewa na garin, batasan lokacin da wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanunta ba, tasa gefen hankchief ta goge *Lallai wani hanin ga Allah baiwa ne* Fitowarsu daga mota yasa hankalin mutanen dake gurin yadawo garesu, Kowa kallonsu yake kamar basu ta6a ganin mutaneba. Dan yan yara wanda basuda hankali sosai har zuwa suke suna ta6a kayan jikinsu, tare da tatta6a motar dasukazo da ita. Gidan baffa Lawal suka shiga kai tsaye da sallama matar ta tarbesu tayi masu shimfid'ar sabuwar tabarma suka zazzauna amma bata gane ko mutum d'aya daga cikinsu ba. Baffa Lawal yana gonarsa yanata faman aiki labari ya iskeshi wai anga wata had'addiyar mota taxo gidanshi tare da wasu mata masu kyau, da wani namiji kuma anga sunshiga gidanshi. Aiko yanajin haka yayi saurin tattara yanashi-yanashi yanufi hanyar gida, da sauri yake tafiya kamar ze tashi sama, yana Isa 'kofar gidanshi yaga mota aiko stayawa yayi yana kallo cike da mamaki. Sannan ya 'karasa cikin gidan, laraba na ganinshi gabanta yayi mummunar fad'uwa, har gabansu yazo ya dur'kusa yana gaishesu, sukuma sai abin yabasu kunya cike da ladababi suka gaisheshi ya amsa sannan yace "bayin Allah ai ba nan bane gidan megari yanacan saman layi, amma tunda kunzo nan muje in rakaku aiba damuwa, yana magana jiki na 'kyarma sai wannan 6a6are yake yana washe ha'kora. Fatima tace ba gidan me gari zamuba nan mukazo, yanzu baffa Lawal baka ganeniba, Sai lokacin ya 'kuramata idanu kamar yana neman sanin wani abu tattare da ita, yace "kai yarinya banganekiba har yanzu, inaji ba nan bane gidan da kuke nema saboda ni banida 'yan'uwa birni. Kad'an yarage jidda tayi dariya dan ganin yanda baffa Lawal ya ha'kikance be gane laraba ba, Laraba kuwa goge hawayen dake idanunta tayi sannan tace *"baffa 'yarka ce laraba* 😳 mamaki yakamashi kuma tana fad'in itace laraba sai yaganeta, yace Laraba ina kika shiga shekara da shekaru mun d'auka kin mutu, matar baffa lawal ma tasowa tayi cikin mamaki tace "Laraba da kina raye Allah me iko, Baffa Lawal ya kalli su jidda da mukhtar yace wad'annan fa su waye? Fatima tace wannan shine mutumin daya taimakeni, ta nuna mukhtar kuma yanzu haka shine mijina, ga kuma d'an da Allah ya azurtamu dashi, ta mi'kama baffa lawal sultan, sannan ta nuna jidda wannan kuma 'kanwarsace lokaci d'aya akayi bikinmu itama ga d'iyarta, ta amshi rahama daga hannun jidda tami'kama matar baffa lawal. Cike da mamaki baffa Lawal ke kallon fatima yace "laraba haka kika koma, ikon Allah, Allah kenan me d'aukaka bawansa ta kowace hanya. Laraba dai in banda zubar da Hawaye ba abinda takeyi, Kusan awarsu guda gidan baffa Lawal laraba nabashi labarin irin taimakon da Hajiya da mukhtar yayimata, da kuma irin yanda suka ri'keta kamar 'yar cikinsu. Sannan mukhtar yaje but d'in motarshi yasa aka shigo da tsarabar da sukayomasu, buhun shinkafa katon d'in taliya dana makaroni da sabulun wanka dana wanki da sauran kayan abinci, Ahaka aka ri'ka shigowa da kayan baffa lawal kuwa banda godiya ba abinda yakeyi, saboda tsananin farin ciki besan lokacin da wasu hawaye suka zubo daga idonshiba, ya kalli laraba yace "Ashe dama akwai ranar dazanga aurenki har inga d'anki Allah Sarki Allah maki Albarka kinji laraba, Ashe hakanan mutane suke zarginki akan *maita* ashe Sharrin iska ne Allah dai ya'kara tsareki laraba, tana zubar da hawaye tace ameen baba. Bayan sun gama danan ne suka tashi, laraba tace "baffa zamu d'an shiga gari mu gaisa da jama'a. Cike da jin dad'i yace to laraba amma kafin kuje ko'ina ianso kuzo muje gidan me gari ki gaisheshi, mukhtar yace ba damuwa muje, haka suka d'unguma suka nufi gidan me gari kasancewar ba nisa tsakaninsu da gidan baffa lawal d'in shiyasa suka tafi a 'kafa, duk inda suka gifta kallonsu kawai ake kamar wasu taurari, baffa Lawal kuwa daya gaisa da mutane a hanya sai ya nuna masu laraba da mijinta da d'anta, haka shikuma Mukhtar ze fiddo dubu ya mi'kama wanda aka nunama larabar. Da haka suka isa gidan megari, baffa lawal yakwashe labarin da tafad'amashi duka yagayamasu sannan ya gwadamasu mukhtar a matsayin mijinta da kuma d'ansu sultan, sun d'an jima suna gaisawa da jama'a kafin suyi sallama tare da cika me gari da abin arzi'ki kafin kace me labarin zuwan laraba ya bud'e gari mutane sai zuwa ake ganinta duk wanda yazo sai mukhtar yabashi 'kud'i wani dubu wani d'ari biyar, yara kuwa me dari me d'ari biyu ranar garin duk wanda kagani bakinsa washe saboda murna. Baffa lawal kuwa daga nan gida yakoma yasa aka yanka zabbi akayima su laraba soye lafiyayye sannan aka dama masu fura wacce taji nono. Gidan indo 'kawar laraba suka nufa, kan hanyarsu ta zuwane suka gamu da habu yadawo daga gona yayo uwar ciyawa ya d'ora akai ga kuma hauya rataye akafad'arsa sai uban gumi yake had'awa, Fatima ta kalleahi tace habu, cike da mamaki ya d'ago ya kalleta dan jin wata 'yar gayu wacce batayi kama da 'yar 'kauyensuba ta ambaci sunashi, sauke ciyawar dake kanshi yayi ya'karema fatima kallo yace baiwar Allah daga ina kuma ina kika sanni? Fatima tayi murnyshi tace "habu nice laraba baka ganeniba, cike da mamaki habu yace laraba kece kika koma haka, dama wallahi abinda yasa nabaro Gona kenan inacan labari ya iskeni wai kindawo wanda ada mun dad'e da d'auka kin mutu. Laraba tayi murmushi tace "ina raye habu harma nayi aure, ta nuna mashi mukhtar wannan shine mijina, ga kuma kyautar da Allah yayimamu bayan Aurenmu ta nuna mashi sultan, sannan ta kalli Mukhtar tace wannan shine habu, mukhtar ya mi'kamashi hannu suka gaisa sannan ya d'auko 20k sannan sukayi sallama suka wuce, habu ya tsaya yana juya kud'in kafin daga bisani yanufi gida cike da farin ciki dan kobi takan ciyawarsa beyiba. πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:13 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [18/09 6:33 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _Written by_ _*Zee Mmn khady*_ 😘 6⃣8⃣to7⃣0⃣ πŸ–Š Sun isa gidan indo, da sallama suka shiga gidan sun isketa tana sharar tsakar gida da yaronta goye, d'agowa tayi daga duken datake takai dubanta ga fatima, kallo d'aya tayimata tace "laraba kece, cike da mamaki ta rungumeta tana zubar da hawaye, laraba tace nice indo, Indo tace Ku shigo, haka suka shiga d'akin indo tayimasu shimfid'ar tabarma suka zauna, nan suka gaisa, laraba taba indo labarinta kaf bayan barinta 'kauyen, lndo cike da mamaki tace "Allah kenan shike yanda yaso da bawansa, kinga kuwa yanda kika koma laraba, wallahi baccin sanin danamaki ba kad'an bane da bazan shedakiba, yanzu d'inma ba namijin 'ko'kari nayiba, dan yanzu kinfi kama da irin turawan damuke gani a talabijin, jidda tayi dariya, Haka sukasha firarsu sannan sukayima indo sallama bayan laraba tayimata 'kyautar kud'i me yawa sannan tace zata aiko da katon-katon d'in sabulun wanka dana wanki duk wata 'kawarsu dake garin abata sabulun wanka sin'ki guda saina wanki dozin, indo tashiga godiya, Suna gaf da fitowane ilu yayi sallama bayan indo ta amsa tanunamashi laraba, cike da mamaki yake kallonta, sannan yace "tabbas naji ana labari a gari laraba tazo da mijinta ance yanata rabon kud'i, indo tace kwarai dan nima ga abinda larabar tabani ta nunamashi dubu goma sha biyar, ilu ya zare ido dan tunda yake beta6a tinanin rike kud'i irin hakaba amma yau larabace ke bayar dasu kyauta. Tare sukayoma su laraba rakiya, a 'kofar gidan indo ta gaisa da Mukhtar shima ilu sun gaisa, Mukhtar yabashi kyautar dubu goma, wayyo dad'i kashe ilu ai fad'uwa yayi yana zuba uwar godiya. Daga nan asalin gidansu laraba suka wuce, sun shiga gidan ba abinda ya canja ga yanda tabarshi, d'aki tanufa duk kayanta Dana innarta sunanan, wani irin kuka tafashe dashi, jidda tashiga rarraahinta da 'kyar tasamu tayi shiru, kusan mintuna sha biyar suna cikin gidan sannan suka fita. Daga nan gidan baffa Lawal suka koma sun iske soyayyun zabbin da baffa Lawal yasa aka soyamasu da fura me rai da lafiya, sunsha sosai sannan suka ci naman, bayan sun kammala ne suka 'kara ta6a fira, saida sukayi sallar la'asar sannan saukayi haramar tafiya gida, har mota baffa Lawal yarakosu, kafin subar garin said a suka 'kara biyawa gidan indo suka sauke katon-katon din sabulu na wanka dana wanki wanda za'a rabama 'kawayenta. *********************************** Bayan sallar magrib suka iso gida,bayan sunyi horn megadi ya bud'e masu get, mukhtar yayi parking inda aka tanada dan ajiye motoci, su duka suka shige gida cike da gajiya tattare dasu, falo suka iske Hajiya ta tarbesu tana masu sannu da zuwa. . Washe gari da misalin 'karfe goma na safe Hauwa me 'kunshi tazo tayima jidda da fatima, kunshi, itace me 'kumshin Ameeno yanzuma itace ta turota tayimasu, kunshin ya zanu kamar wasu sabbin amare, bayan sallar azahar kuma sukaje gyaran kai, gyara sosai saukayima jikinsu Hajiya ma ta had'amasu duk wani abu datasan ze taimaka masu gurin gyara, Washe gari kafin la'asar sun gama kammala kome nasu, bayan sallar magrib Mukhtar yazo yatafi da fatimarsa, basu dad'e da tafiyaba Usman yazo ya d'auki jidda, To Alhamdulillahi kowace takoma d'akin mijinta, suncigaba da rayuwar soyayya da bawa junansu 'kyakkyawar kulawa. πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ [10/16, 8:13 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [18/09 9:00 pm] . πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _Written by_ _*Zee Mmn khady*_ 😘 _```THE END```_ 7⃣1⃣to8⃣0⃣ πŸ–Š Bayan wata biyu, yau yakama week end saboda haka Mukhtar baije ko inaba, dama duk weekend baya fita zama yakeyi tare da fatimarsa su ri'ka debema juna kewa, Yauma kamar kullum zaune yake kan kujera 3 seater sultan rungume ajikinsa yana bacci, fatima ce tafito daga bedroom d'auke da wata lallusar katifa me had'e da net ta yara ta ajiye sannan ta lalla6a ta kar6esa ta kwantar dashi, mukhtar na fad'in "kifabi ahankali kada kuma ki tasheshi kinsan dai rigimar dayayi kafin yayi baccin. Koda ta kwantar dashi beko motsaba dan dama rigimar ta baccin ce yayi, Koda tasamu ya kwanta tashi tayi tadawo inda Mukhtar yake zaune kan three seater ta kwanta tayi filo da cinyarsa shikuma yasa hannunsa kanta yana wasa da lallausan gashinta. Cikin nutsuwa da tausasa murya tafara magana "Abban sultan dama inaso muyi shawara dakai, ya tattara nutsuwarshi sannan ya maida duk wani hankalinshi gurinta yace inajinki, tace "inaso duk kud'in dake gareni zanyi amfani dasu a roshe gidanmu na 'kauye amaidashi ialamiyya wacce za'a ri'ka koyarda addini acikinta, shine nace bari insanar dakai hakan danayi yayi kuwa? Mukhtar ya numfasa har cikin ransa yaji dad'in wannan tunani na fatima dan d'an zuwan dasukayi 'kauyen ya fahimci yanda jahilci ke d'awainiya da mutanen garin. Yace kada ki damu indan wannan ne ni zan d'auki nauyin kome, kuma zanyi 'ko'kari insayi wani fili kusa da gidan sai ayi masallaci, kuma zamuyine da niyyar Allah kai ladar ga iayayenki, Wani irin farin ciki taji ya ziyarci zuciyarta batasan lokacin da wasu irin hawaye sukayo ambaliya daga idanuntaba, tace "nagode Abban sultan Allah sakama da gidan Aljanna. Haka kuwa akayi cikin satin Mukhtar yaje 'kauyensu laraba yasanarda baffa lawal shawarar dasuka yanke shida laraba, baffa Lawal yaji dad'i sosai sannan aka sanar dame gari, wani tsohon gida li'ke da gidansu laraba mukhtar yasiya aka had'e aka roshesu baki da'aya kasancewar gidajen manyane ansamu wadataccen fili. Ayki ya kakankama kasancewar nera ke magana, cikin wata d'aya aka kammala ginin islamiyya da 'katon masallaci me kyau duk 'kauyen babu kamarsa. Bayan ankammala da sati d'aya akayi walimar bud'e islamiyyar, Wanda laraba da kanta ta kaddamar da ita, su hajiya da jidda suma sun halarci walimar, laraba kuwa a ranar tayi kukan *ALHINI*Allah ya d'aukakata, ba rabon innarta taga wannan lokaci. , mutanen 'kauyen sunyi matu'kar farin ciki, Taro yatashi lafiya kowa yakoma gida duk garin bakajin maganar Kowa sai ta laraba. Cikin satin mutanen 'kauyen suka fara karatu a islamiyyar da suke kira _*LARABA ISLAMIYA*_ ```Alhamdulillahi``` πŸ‘πŸ» _*Anan nakawo 'karshen wannan littafi nawa me suna ALHINI, ina fatan me karatu ya nishad'antu kuma ya d'auki darussa dake cikin wannan littafi nawa*_ πŸ’ž _*Kyakkyawar gaisuwa ga masoyana a duk inda suke*_ πŸ’ž _*JINJINA GA GROUP'S*_ Nagarta writer's association. Wisdom Hausa writer's. Sahaf's novel. Deejer taheer group. Matan kwarai group. Presidential villa group. Mesha Luv fan's S.A.Azeez group. _*MY SpECIAL GROUP'S*_ πŸ’ž *Zee Mmn khady fan's & nvl* πŸ‘‰πŸ»πŸ‘©πŸ» *Ciwon ya mace group* _*Ina gaisuwa ga duk masu bin littafina, sai kunjini a sabon buk d'ina me suna*_ πŸ‘‡πŸ» πŸ’ƒπŸ» *_YARINYAR BABA_* πŸ’ƒπŸ» *Litattafan marubuciyar* πŸ’ž *Siyasa ko soyayya* 🌍 *Duniya juyi* πŸ‘πŸ» *Halin girma* 🏀 *Gidan ASALI* πŸ•Š *Autar Hajiya* πŸ‡ *Alhini* Love u all my fan's πŸ’‹πŸ’ƒπŸ» πŸ–Š Zee Elkaseem Mmn khady πŸ’‹ adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *