Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, April 3, 2017

AKAN SOCIAL MEDIA (YANAR GIZO)! COMPLETE

adsense here

[1/6, 6:20 PM] Kausar Luv💞: ```🕸AKAN SOCIAL MEDIA (YANAR GIZO)🕸``` ```©Kausar M Hassan``` Page 1 to 10. Bismillahi Rahmani Raheem! Masoyana Ina baku hakuri akan rashin zuwan littafin *MUGU BAI DA KAMA*. Wannan ya farune saboda bayanai da nake tattarawa akai. Kapin zuwanshi ina maku sallama da wannan takaitaccen littafin nawa mai suna Akan social media (yanar gizo) K'arar sakon daya shigo a wayantane yasata yin firgigit ta miqe dga zaune da take ta d'auki wayanta, sunan da tai saving dashi na "My one" ya fitah akai. Wani d'an karamin tsaki taja saboda wasu guntayen hawayen da suka zuba mata a fuska. Kanta ta kifah akan guiwowinta ta fara shiesiehkar kuka. Dea2 wannan lokacin wata yar matashiyar mata ta shigo gidan, baqa mai matsakaicin tsaye, mai kyau da itah. "Keko fadila mai yasa ki cikin wannan yanayin? Tun d'azun naketa rafka sallama gaki zaune kin kasa amsawa"? Hawayenta ta share ta d'aga idanunta ta dubietah, cikin muryar kuka mai d'auke da nadama ta furta "Farry ina cikin hatsarin ruwa, na shiga ukki na lalace" Zaunawa farry tai ta dubeta cike da d'umbin damuwa "Ke kuwa fadila mai yasa? Dan Allah ki deana fad'ar haka, kisani fa cewan komai na Allah ne, kuma duk abunda ya sameki Allah ya kamata ki miqawa ai" Hawayenta ta k'ara shareware, ta dubie farry "Farry na cuci kaina, naci amanar mijina da iyayena da kuma rayuwata gabad'aya" Hannunta farry ta kama "Look! Fadila idan bazaki fad'amin damuwarki ba billahil azim tafiyana zanyi" Idanunta ta saukar kasa tare da tashi tsaye ta juya bayanta "Farry, tun kapin inyi aure ina chatting da wani mai suna Adnan" Farry ta tari numfashinta "Adnan dai wanda nasani" "Eh shi farry, tun muna chatting a 2go, facebook, muka dawo whtsapp, hr muka fara imo dga nan sai video call farry" Dakatawa fadila tai tacigaba da cewa "Adnan ya kasance abokin firata a online idan banga adnan ba bana iya yin komai, ya kasance ya fara jan ra'ayina muna video call, haka adnan zaisani in cire kayana tas shima ya cire nashi muna video call, babu abunda muke fad'a inba maganganun batsa ba" Kuka yaci karfinta ta dakata ta cigaba da cewa "Farry, tun banyi aure ba gashi ynxn nayi aure har na shekara d'ayah, amma na kasa deanawa. Duk ranar da banyi video call da adnan ba, farry ji nake kamar zan mutu. D'aki nake shigiewa inyita kuka har garin Allah ya waye, gani da miji amma bana bari muna kwana a daki d'ayah, wayata ko ina security code ne da itah" Komawa tai ta zanah ta maida kallonta ga farry data saki baki take kallonta "Farry bazan iyaba, dan Allah ki taimakeni inaso in deana, dan Allah" Hannunta farry ta rike da itama d'in kukan takeyi "Fadila! Dan Allah kicemin mafarki nakeyi ne ba gaske neba" "Wallahi farida iyakar gskyr kenan, ki taimakeni dan Allah"... ************** "Rashida" D'agowa tai ta dubie mai kiran nata Cikin murya ta fitsara ta amsa da "Yes! Akuy damuwane"? D'an murmushi mai kiran nata yayi "Tun d'azun nake binki fa tundga makaranta kinsani kuma kin ganni amma kin fito kin kyaleni" Daria rasheeda ta kyalkyale dashi ta kalleshi tundaga sama har kasa "Chabb! Wallahi bazan aureka ba, kai bara kaji bana sonka ma, dubeka fa ko kyau bakada, yar motar nan ta hawa ma bakadashi. Ni mai kyau nakeso mai kud'i mai kuma motah ehe" Tsaki rashida taja masa ta wuce ta gabanshi ta shigie gida ta maida kopa ta kulle... ```®Kausar Luv💞``` [1/6, 6:21 PM] Kausar Luv💞: ```🕸AKAN SOCIAL MEDIA🕸 (YANAR GIZO)``` ```©Kausar M Hassan``` Page 11 to 20 Kai ya girgizah saurayin mai suna sani ya kama hanya ya wuce gida abunshi. *Fadila* Hannunta farry ta rike gam da jikinta ya hau rawa "Kinga ki kwantar da hnklinki dan Allah, ynxn ina sauri buh in shaa Allah zan dawo sea muyi magana, kada ki fad'awa kowa" Kai ta d'aga mata tare da share hawayenta, farry ta tashi ta fice dga gidan. Yayinda wayan fadila ya qara hawa ruri, again dai text msg ne dga adnan, hannu ta zura kamar ta d'auka kamar kada ta d'auka, jikinta ya hau rawa, tana d'auka yana kiranta a wayah. Ilaharin hnklinta gaba d'aya ya tashi saboda tsabar firgici, da sauri ta kifa wayan kasa ta juya bayanta ta cigaba da hawayenta. ******** Dea2 misalin karfe 2 na wannan rana, zaune take akan kujera wayarta na a hannunta tana cikin wani group mai suna "Girke2 da kwalliya" posting akai dea2 lokacin akan yanda mace zata rika gyara jikinta da kamshi kala2, da kuma wasu dabarun girki. Sallaman da tajine yasata d'aga idanuwanta ta duba mai yin sallaman Ganinshi da tai yasa ta d'an gyara zamanta tare da rufe datan wayanta ta maida kallonta gareshi "Sannu da zuwa mijina, abun alfaharina, awa d'aya idan nai banganka ba ji nake kamar anshare wasu shekaru masu tarin yawa" D'an murmushi ya sakar mata a fuska "Matata rabin raina kenan, kisani cewan kece mallakin zuciyata, dake nake alfahari a kodayaushe" Murmushi tai masa "Bara in kawo maka abunci" Tashi tai ta miqe zuwa kitchen yayinda ya d'auki wayanta ya shiga whtsapp d'inta ya fara dubawa, dae2 lokacin ta dawo ta ajiye masa abuncin akan carpet ta bud'e kolan ta fara zuba masa, towun shinkafa da miyan ganye. "Wato dama nan ake koya maku girki da kwalliya ko"? Murmushi tai masa "To kadea gani, groups d'inne ynxn kowanne da nashi fa'idah, ka manta na fad'amaka cewan har wani group ke garemu mai suna Matambayi baya 6ata? Gskya sunayin posting mai ma'ana kuma ynda kasan makaranta haka ake tafiyar dashi" Ido ya kanne matah "Kai salmana, nidea ngdewa dya had'ani da matar kirki, ynx dea a bani abunci inci sea inyi wanka dan ynxn sea kuma wata safiyar nida fitah" Murmushi salma tai "Yes sir angama" A wannan gida rayuwa suke cikin jin dad'i wal2 da kirkiza, basuda wata damuwa, saboda a cikinsu kowanne yana kula da hakkin d'an uwanshi a bisa gskya. ```Fadila``` Karfe 9pm dea agogo ya buga, fadila ce zaune a falonta tana kallon TV, ta baya taji an rungumeta sosai. Cikin sanyin murya ta furta "Haba zaid dan Allah, meye haka ne"? Murmushi yay "Fadila wea dan Allah halan ba auren soyayya mukai ba? Ki duba kigah yau shekara d'aya kenan da aurenmu amma kin kasa sakin jiki dani, a kullum kina d'aukata kamar wani baqo" Fuska ta d'an saki kad'an "Em am wallahi zaid ba haka bane, kawea bana jin dadin jikina ne" Da sauri ya juyu ta bayanta ya fuskanceta "Fadila mai ke damunki? Sannu kinji taso muje ki kwanta naga kamar jikinki da zafi" Wayarta ta d'auka zaid ya rika hannunta ya shiga da ita d'aki, ya kwantar da ita akan gado, bargo yasa ya rufeta, ya kashe mata wutar d'akin ya fitoh. Fitarsa baifi minti 10 ba ta tashi ta kunna light d'in d'akin sakamakon kiran da adnan ke matah. D'akin ta maida ta rufe da sakata. D'auka tai tare da zaunawa kan gado. Yana kallonta tana kallonshi. Adnan ya fara magana "Fadila! My one, talk to me plzz" Kallonshi tai "Adnan dan Allah ka fitah rayuwata ka kyaleni nifa ynx matar aure ce" Murmushi adnan yay "Fadila nasani mana, amma kema ai kinsan ina sonki sosai, dan Allah ki deana wannan maganar, ynxn dea inaso ne kimin kiss" Kallonshi ta karayi da hawayen dake zuba a fuskanta "Adnan plzzz dan Allah ka kyaleni" Fuskarshi wasai ta nuna alamun damuwa "Baby dan Allah ki deana kuka, idan kina kuka ji nake kamar jinina ne ke fitah dan Allah, look, zo inyi hugging d'inki" Kalamai adnan ya rika ratsawa fadila wanda har yasata ta kara aikata wannan aiki. ```Rashida``` Wayarta ce a hannunta, tayi zugum tana kallon group d'in da take ciki mai suna "Novels world" Typing ta d'anyi kad'an "Ummi Aisha muna jira pls a cigaba da sanadin gata" Bayan kamar minti 3 da faruwar haka sea gashi anyi posting page 30 to 35. D'an Murmushi tai ta rubuta "Tnx" ta aika ta gyara zamnta ta fara karantawa, bayan ta kammala wannan episode d'in tai murmushi, a cikin zuciyarta ta furta "Bazanyi aure ba sea mai kyau kamar Haydar d'in cikin littafin Khaleesat na maman shakur, gashi na kamu da soyayyar Anas (blue eyes) gashi ina son mai kud'i kamar barraq. Fuskarta ta yamutsie "Mtsww ya Allah ka cika min burina ta furta a fili, ta cigaba da chatting d'inta. ```salma``` Addu'ah sukai tare da kwantawa akan gado d'aya laqamie da juna. ```Rashida Salma Fadila``` Ya rayuwa zata cigaba da kasancewa a wad'an nan gidaje"? ```®Kausar Luv💞 [1/6, 6:21 PM] Kausar Luv💞: ```🕸AKAN SOCIL MEDIA🕸 (YANAR GIZO)``` ```©kausar M Hassan``` Page 21 to 30 Washe garin ranar da asuba, salma ce ta farka dga bacci, kasancewar yau sun d'an makara ne yasa ta tashi mijinta mai suna bilal "Yaa Bilal ka tashi zamu makara bamuyi sallah ba, tashi yay suka d'unguma zuwa toilet, yayinda sukai alwala suka dawo d'akin dmn yin sallar asuba. ```Rashida``` Tashi tai dga kwanciyar da tai, tai miqa dea2 lokacin an kammala sallar asuba, bayi ta shiga tai alwala ta fitoh tai sallah kapin nan ta koma bacci. ```Fadila``` Kayanta ta tattara gefe tana mai jin haushin kantah, ta tashi ta shiga toilet tai wanka har guda 2 kapin nan ta fitoh ta chnza kayan jikinta ta maida gabanta gabas tai sallan asuba, ta tsaya tana rokon Allah akan ya shiryata ya kuma sa ta daena wannan mummunar d'abi'ar. Dea2 lokacin zaid ya kwankwasa kopar d'akin, hannu tasa a fuskanta tai maza ta mike ta d'an kimtsa gadon kapin nan ta duso kopan ta bud'e. Kallonta ya tsaya yanayi akan kopar "Fadila y jikin? Hope dea ynxn kinji sauki ko"? Murmushi tai masa "Alhmdlh zaid naji sauki, ynxn dea muje in had'amana breakfast" Murmushi yay ya rungumeta "To ki bani hot kiss sea muje in taimaka maki" Matsawa tai tare da furta "Plzz zaid, ka barni mana" Murmushi yay "OK matar laushi, less feeling less emotional, muje" Haka suka kama hanya tana gaba yana bayanta har suka isa kitchen, tare da taimakawarshi ta kammala had'a masu breakfast d'in. ```Salma``` Kusan karfe bakwai na safe ta kammala had'a masu breakfast d'insu, indomie ta dafa masu, akasa ta dire farantin sukayi basmallah suka fara cin abuncin, suna fira irinta masoya wasa da daria. ```Rashida``` Bayan ta kammala karyawa ta shirya tsaf cikin uniform d'inta ta kama hanyar zuwa makarantar islamiyya kasancewar bana ta kammala secondary. Kasancewar dga gidansu zuwa makarantar akuy yar tazara. Ta kusa isa a mkrnta taji ana yimata horn, juyawan da zatai ta hangi wani santalelen saurayi a cikin mota, batasan sanda tai wata irin murmushi ba Saurayin saukowa yay dga motan "Yan mata sannu ko"? Fuska ta d'an gimtsie "Yauw, sannu" "Plz idan bazaki damuba ni sunana abdulmaleek, amma ana kirana da abdul, zanso ki bani lokacinki, dan wallahi kin burgeni kuma ni bada wasa nazo ba da maganar aure nake tafie" Kallonshi tai tare da k'arewa motarshi kallo "Tohm yxn dea kaga makaranta zan tafie" "Ba damuwa, mss...?? "Rashida" "Yauwa rashida, plzz ki bani number d'inki zuwa idan kin dawo sea muyi magana ko"? Fadamashi lambarta tayi shi kuwa ya d'au katuwar wayarshi fara tas ya fara rubutawa akai, bayan ya kammala yay saving ya danna kira. Vibration wayanta dake cikin jaka ya farayi "Yauwa ta shigo" Juyawa yay zuwa motanshi ya shiga "Zuwa karfe 1 zan kiraki nasan kin zama available, ki kula da kanki rash, I love u" Wucewa yay abunshi yayinda rashida tai tsaye tana jin kamar mafarki takeyi. "Yeeeeh! Abun kamar a novel wallahi, mai kyau mai kud'i yana son yar talakawah, yeeeee! Burina ya cika. Zan wataya inyi walkiya kan daula. Anya kuwa rashida rayuwar novel d'aya take data zahiri kuwah? Inji kausar. Zamu gani dea. ```®Kausar Luv💞``` [1/6, 6:21 PM] Kausar Luv💞: ```🕸AKAN SOCIAL MEDIA🕸 (YANAR GIZO)``` *Page 31 to 40* ```Rashida``` Karfe d'aya na rana, kira ya shigo a wayan rashida, murmushi tayi, ta d'auka tare da karawa a kunne "Assalamu alaikum" Abdul yay sallama "Amin alaika salam, gskya kam kana da cika alkawari" D'an murmushi yay "Gskyne amma kinsan abubuwa suna zuwa haka ai, yxn dea kimin misalin gidanku idan na tashi zuwa karfe 7 na dare zanzo in shaa Allah" Fari da ido tai kaman wanda ke ganinta ta fara yimasa bayani "Well! Nagane sea kinganni" Haka sukai sallama rashida dake zaune ta fitah wajen tsakar gidansu "Innah!!!" "Ke lapiya kike kwala min kira haka"? Ajiyan zuciya ta sauke "Inna kinsan na ta6a karanta maki labarin littafin martaba ta na ummi aisha ko"? Kai ta d'aga tare dayimata wani irin kallo "To inna abun kamar haka, yau na had'u da wani handsome, zuwa darema yace yana nan zuwa, shiyasa kiga inna na dage na iya abunci kala2 saboda tsaro" Murmushi innah tayi tare da cewa "Allah ya kyauta" ```Fadila``` Bayan tayi wanka tayi sallah ta d'an kishiengid'a kanta akan gefen kujerah. Ji tai gabad'aya batajin dad'in jikinta, wayanta ta d'auka kaman zatai kirah, sai kuma ta koma ta ajiye, bayan kmr minti 2 haka ta k'ara d'auka ta danna kiran number d'in adnan. Video call. Murmushi yay "Kyakyawa ykk? U miss me"? Kai ta d'aga masa "Yes! Adnan plz mai yasa bazaka fitah rayuwana ba"? Ido ya kanne mata "Ni adnan in rabu dake fadila kema kinsan abune wanda ba xai taba yuwu ba, just relax ki cigaba da kulamin da kanki kinji" Hawaye suka zuba mata a fuska "Adnan kasan cewa zamu mutu kuma zamu koma ga mahallicin mu, abunda muka aikata dashi Allah zai mana hisabi, mai yasa bazamu deana ba" Tsuke bakinshi yay "To dga yau kada ki kara kirana a waya, zan goge number d'inki a cikin wayana in koma gogeki a cikin zuciyata da kuma rayuwata" Jin kalamanshi da fadila tai yasata cikin tashin hankli, stammering ta fara yi, kapin ta bud'e baki ta bashi amsa ya kashe wayan tare dayin tsaki. Ido tabi wayan dashi da idanunta da suka chanza kala, take ta maida kiran nashi, har sau 3 kiran na shiga yana tsunkewa bai d'auka ba. Jikinta ya hau rawa gabad'aya ta fita hayyacinta, idanunta suka chnza kala saboda kukan data soma tana fad'in "Plzz adnan pick d call, plzzzzzzzz" Sea a karo na hud'u adnan ya d'aukie wayan "U see! Baxaki iya rayuwa badani ba my one, am in need of u, kina jina? Come on cire min hijab d'in nan, kinji"? Kallonshi tai, saboda maganar adnan kamar ta zama maganar iyayenta bazata iya kaucewa duk abunda yakeso ba. Kamar yanda yace haka ta aikata "Yauwa my one, kinsan fa ina sonki, fuskanki mai kyau, gaki chocolate colour, hancinki har kusan baki, ga manya ido, ga... Bai karasa ba taji sallama, da sauri ta katsie wayan ta maida dubanta ga matar dake cikin d'akin "Mother"! Ta furta a sanyaye "Nice fadila ba wata ba, mai yake faruwa ne haka"? Naga kamar kinyi kuka? Murmushi tai "Laa! Mother banyi kuka ba, ynxn dea zaunah, bara in kawo maki abunci" Tashi tai ta wuce kitchen ta zuba mata abunci a plate ta hadu mata da drinks ta dawo ta kawomatah ta ajiye, mother na saman kujera ita kuma fadila tana kasa. ```Salma``` Sallaman zaid da tajine yasata waigawa tare da sakin murmushi a fuskarta "Yaana barka da dawowa" "Yauwa matata, wlh nagaji sosai, bara inyi wanka in fitoh" "OK" Tashi bilal yay ya shiga toilet ya watsou ruwa ya fitoh ya chnza kayah zuwa d'an 3quarter black da farin riga karama ya feso turare ya dawo zuwa ga salma "Yaa bilal baxaka ci abunci bane"? Murmushi yay "Kinga wallahi dga office dana tashi sea na biya gidan hajiya shine fa ta bani towu naci" Murmushi salma tai "To shikenan sea mu barshi muci da dare ko"? "Haka za'ayi matata kizo gareni" Matsawa tai kusa dashi ta zaunah a kasa, bilal ya d'ora kanshi akan cinyarta yana wasa da hannunta "Ki bani labari" Wayarta ta d'auko "Kaga bara in karanta maka wannan" "Emhum ina jinki" "Yauwa! Wato wannan labarin ynxn akai mana posting d'inshi a group, wea wani mutum ne yanada mata, a kullum idan xata fitah sea tayi kwalliya ta kure adaka iya iko, ta bad'e jikinta da turare, to mijin yayi2 ta deana takie bari, kawea watarana suna tare da abokinshi sea ta wuce, abokin yace "Waiyh gskya kamshin turaren nan yayi" Mijin ya juya yace "Ubanwa yace ka kallie matata"? Sea shi abokin nashi yace "Wai dama matarka ce"? Mijin yace "A'a dan ubanka uwarka ce" Mijin tashi yay ya wuce gidah "Ke dan wanda y haifeki nagaji na sakeki" Matar sea ta fashe da kuka tana rokonsa arziki akan ya mayar da itah Fafur mijin yaki hakuri. To wea idan kaine ya zakayi"? Daria bilal yay "To ai shine dea2 amma shima ya kamata yayi hkuri ya kara bata dama" "Hkne yaana, amma itama ai bata kyauta ba, bai kyautu ba matar aure zata fita ta rika saka turare har wani namijin da ba nata ba yanajin kamshin turaren ta ba, haramun ne" "Sannan kamshin turare yana jawo sha'awah, dga sha'awa kuwa sai a afkawa zina, hakika yayana wasu matan auren suna keta haddin aure. Wasu a zahiri wasu kuma a social media" Hannunta bila ya kara kamawa "Data why nake alfahari dake, duk da kina amfani da yanar gizo baki chnza minba, kinada lokacina, kina kula da hakkina na aure, kigafa abokina yanada mata amma wlh yace idan ta kama wayar hannunta tofa baya gabanta batada lokacinshi, sea dea kawea chatting, kuma ko kad'an wayanta baya zuwa hannunshi" Murmushi salma tai "Allah ya kyauta dea, zan cigaba da baka labarin" Haka dea salma ta cigaba da baiwa bilal labarai a cikin whtsapp d'inta yana faman daria, wasu kuma labaran su maidau topic of discussion. Har shi da kanshi yake kar6an wayan yana karantawa ya shiga whtsapp d'inta yayi duk yanda yakeso abunshi, hankalin salma zaune zuciyarta kwance. Saboda bata bar yanar gizo ta lalata mata rayuwa ba, kowanne abu yanada nashi amfani yana kuma da rashin amfani. Mujeh zuwa dea akan yanar gizo. ***** Karfe 7pm abdul ya dira a kopar gidansu rashida yakirata a waya ya sanar da ita cewar yana kopa. Dama ta shirya tsaf abunta turare ta kara fesawa, ta kamo hanya cikin takun k'asaita ta fitoh wajen. Kallonta abudul yayi ya bud'a baki yace... ```®Kausar Luv💞``` [1/6, 6:22 PM] Kausar Luv💞: ```🕸AKAN SOCIAL MEDIA🕸 (YANAR GIZO)``` *Page 41 to 50* "Rashida kamar ynda na fada'maki ni aurenki nake son yi, kuma kapin inzo nan sea da nai bincike a kanki, saboda haka bana son a 6ata lokaci idan dai har kina sona" D'an murmushi tai wanda ya kara mata kyau. Rashida kenan, fara kyakyawar yarinya mai matsakaicin tsaye, ga tsabar shigar rai. "To yayi ba damuwa, zan fad'awa innah. Kasan cewa Allah yayiwa babana rasuwa" "Hakane rash, Allah ya jikanshi da rahama ynxn dea... Jin ana sallama ne yasa Abdul dakatawa "Yes! Malama lapiyah"? Bawan Allah sani ne rike da leda a hannunshi "Rashida gunki nazo" D'an murmushin yaki ta saki "Abeg malam tafi ka bani guri wallahi bana son haka" Ko kad'an sani bai nuna alamun damuwa a taredashi ba, juyawa yay abunshi yayinda abudl ke mamakin rashidah, gata dea mai ilimin addini amma tana wulakanta bayin Allah, kodayake ai baisan mai ya had'asu ba. Sun d'an jima suna fira kapin nan sukai sallama. ```Fadila``` Bayan ta kammala sallar isha ta shiga toilet tai wanka ta fitoh ta d'anyi simple make up ta koma kan kujera ta zaunah, wayarta ta d'auka ta shiga whtsapp d'inta ta fara duba msgs d'inta. Karo da number d'in adnan tai "My one"!! Ya rubuta har kusan hamsin, ga voice note ya ajiye mata kusan goma dukda basu jima dayin sallama a waya ba, voice note din ta bud'e ta fara saurara, wasu tayi murmushi wasu ta dubie kanta wasu kuma ta kyalkyale da daria, haka dea har ta kammala ta maida mashi da amsah. Bayan d'an lokaci sukai sallama akan anjima zai kirata suyi video call. Ba'a fi minti biyar da faruwar hakan ba, sai ga zaid ya shigo falon d'auke da sallamanshi. Kusa da ita yaje ya zauna ya kalleta "Em fadila dama inasone zanyi tafiya gobe idan Allah ya kaimu kuma zan d'auki kaman sati 2 ban dawo ba, saboda hka kinsan inda kud'i suke idan kinada buqatah, plzz kuma ina neman alfarma, zo kiji" Tashi yay yayi d'aki ita kuma ta tunzure baki ta kalleshi tare da watsa mashi harara tabi bayanshi. Babu ynda ta iya yau kam face ta baiwa zaid hakkinshi na aure, kapin nan ta koma d'ayan d'akin tai wanka, ta fitoh toilet d'in kenan d'aure da towel adnan ya kirata. Gashin kanta ta tattara guri d'aya kapin nan ta daukie wayan "Fadila"! Ya kira sunanta "Na'am adnan d'ina ya akai"? "Just kawea I feel lyk in kira sunanki saboda so da k'auna" Murmushi tai masa ta zaunah kan gefen gado "Adnan kenan kasan kuwa mijina gobe zayyi tafiya? Kuma har ta tsawon sati 2? Zaunen dayake ya tashi "Oya dan Allah kada kicemin wasane, kin kuwa ga da munsha shagalinmu son rai" D'an murmushi tai "Da matar auren"? Daria yay "Ke ynxn kina d'aukar kanki matar aure? Kodayake yhp u r, buh matata" Murmushi sukai dukansu tace "I love u" Adnan ya maida "I love u too" ```Salma``` Bilal ne kwance akan dogowar kujera dea2 misalin karfe tara na daren wannan rana. Salma ce ta fitoh dga d'aki rike da waya a hannunta "Yaa bilal duba kaga wata yr group dinmu ce ta haihu, yarinyar mai kyau ko"? Murmushi yay "Sosai tayi kyau plenty2, muma Allah ya bamu tamu mai albarka" "Amin yaa bilal, wannan itace sunanta zainab" "Allah ya raa zaynb" "Amin yaa bilal" Haka suka yita firansu abunsu wasa da daria har zuwa wani lokacin. ****** Washe garin ranar tunda safe zaid ya kama hanyar fitah dga gidah zuwa katsina, bayan fitarsa fadila da adnan suka fara wayah harta kai ga sunyi aikin b'arna. Akan yanar gizo. _1week letter_ ```Fadila``` Zaune take akan kujera ta d'ora kafarta d'aya akan d'ayah, tana girgizah ta. Hannun da tajine ya riketa yasata saurin juyawa, ido suka had'a, wanda yasata kyaftawa saboda ji take kaman a mafarki. Murya na rawa ta furta "Adnan"! Ni kaina kausar na razana jin wannan suna, to yama akai yazo gidan"? Murmushi ya sakar mata "Fadila gani nazo" Tashi tai ta fara jaa da baya shima yana binta har ya Kaita kan bango, had'e jikinshi da nata yayi wanda yasata sakin wata irin kara "Adnan plz stop it, bana so" Jikinta ya shiga laluba tare da kai mata sumba "Adnan!.. Kawea take iya furtawa. Dea2 wannan lokacin tajie sallama wanda wannan muryan ko a mafarki tajieta zata ganeta, ilahairin kafatarin hankalinta ya tashi, wanda yasata ture adnan, daya shiga wata duniyar ta daban. Kallon da ake matane yasata zubewa kasa kamar wadda ta mutu. Kad'an kenan dga cikin sharrin yanar gizo, domin wallahi zata iya kaimu wuta idan mukai aiki da ita ta hanya ba mai kyau ba, domin kuwa ko kad'an bazamu iya goge abunda muka aikata a ciki ba, koda kuwa ba wanda yasani dga mu sai kanmu tofa kada mu manta da ubangijin sammai da kassai shi yasan komai kuma yana ganin komai. ```Astagfirullah!!!``` ```®Kausar Luv💞``` [1/6, 6:22 PM] Kausar Luv💞: ```🕸AKAN SOCIAL MEDIA🕸 (YANAR GIZO)``` ```©kausar M Hassan``` *Page 51 to 60* Gam ya runtsie idanunshi yana jin wani irin azaba a tare dashi, zuciyanshi na kona matuqa, adnan kuwa rasa abunyi yayi wanda yasashi yin kamar zai gudu a d'akin. Kwanji zaid ya zage iya iko ya d'uma masa dundu, wanda yasa adnan zubewa k'asa. Dea2 wannan lokacin farry ta fad'o gidan. Ba karamin tashi hankalinta yayi ba ganin adnan da tai a gidan, gaba kad'an idanunta suka tsinkayo mata fadila kwance. Da gudu ta isa gareta "Fadila"!!! Ganin ko motsi batayi yasa farry runtumawa kitchen ta d'ebo ruwa a glass cup ta dawo ta fara yayyafawa fadila, har ya wannan lokacin adnan na hannun zaid, zaid yama rasa mai zaice dashi. Bayan kamar minti 10 haka, fadila ta farfadou, ganin zaid da taine yasata sauke kanta kasa tare da tashi tsaye ta fara jaa baya tana kokarin boyewa bayan farry. Cikin zafin rai da nuna zafin kunci da cikakken matsanacin 6acin rai ya furta "Fadila fito" Ganinshi da fadila tai a wannan yanayin da bata tab'a ba yasata fitowa take tana mai zubar da hawaye masu d'auke da nadama Hannun adnan zaid ya saki, da gudu adnan d'in ya kama hanya zai fitah. Zaid ya bud'a baki cikin tsananin bakin ciki yace "Ka dawo ka zaunah" Sim2 adnan ya dawo a falon a zaunah jiki na rawa ya sunkuyar da kanshi qasa, yayinda farry ta kama hannun fadila suka zaunah kan kujera 3seater, zaid ya zaunah kan one seater. Ya jima kapie da manyan idanunshi akansu kapin nan ya bud'a baki da idanunshi da suka cika da kwallah. "Fadila! Kinci amanata, Allah ya Isah! Kin yaudarene, banyafe maki ba" Kuka ta fashe dashi "Zaid dan Allah kayi hakuri ka saurareni kada ka yanke hukunci a cikin fushi, Allah yana son masu yafeya da kuma afuwa" Kwayoyin idanunshi ya saukar akanta "Ke! Har kin san Allah dama? Da aurenki kike bin maza? Kin kuwa san hukuncin da Allah yaywa mazinata a cikin alkur'ani? Musamman ma masu aure Fadila fad'amin yaushe wannan abun ya fara"? D'agowa tai ta dubie adnan kapin nan ta maida dubanta ga zaid "Zaid ban ta6a aikata.... Hannu ya d'aga mata "Ya Isah! Tambyrki nake" Hawayenta ta share "Adnan saurayina ne, tun banyi aure ba, har mukai aure, ina sex chat da video call dashi, har nai auren nan, zaid ka yarda dani wlh ban ta6a sanin wani d'a namiji a rayuwata ba inba kaiba" Le6enshi na kasa ya ciza kapin nan ya tashi tsaye ya matsa kusa da itah "Karya kike! Sex chat! Zina ne! Voice sex! Shima haka, uwa_uba video call da zakiyi tumb'ur kina kalaman batsa, wani katon banza yana kallonki, to duk wannan sunanshi ZINA" "Kai kuma" Ya juya ga adnan, hukuma zata rabani da kai, dan sai an biman hakkina, kai nama barka da Allah, Allah y isah! Tashi ka ficemin dga gidah" Cikin tsanain jin kunya adnan ya miqe yana mai baiwa kanshi magana da wa'azi da fad'a akan halin daya tsinci kanshi yana aikatawa Komawa zaid yayi ya zaunah chan kuma ya tashi yay kuryan d'aki yay kwance dirshan kan gado, hawaye suka cigaba da mai zarya. Farry ta maida dubanta ga fadila "Fadila bansan haka rayuwar da kike aikatawa tai zurfe ba, kinyi watsie da Allah, kinmanta cewa akuy ranar sakamko, kika manta da igiyar auren dake saman kanki, kika biyewa son ziciyarki kika aikata zinah" Hannunta tasa a baki "Farry plzz, ki saurareni bansan da zuwan adnan ba, kawea ganinshi nai" Farry ido ta zuba ma fadila "Allah y kyauta fadila, amma wlh kinci amanar kanki" Zaid dake d'aki ya fitoh waje rike da takarda a hannunshi, wajen fadila yaje ya tsuguna ya dubieta "Fadila, da mai Allah ya ragan? Kyau? Kud'i? Gida? Abun hawa? Ko kyau na banza na fiki, amma nasoki tsakani da Allah na kuma yarda dake, amma kikayi amfani da social media kika ci amanata" Fadila! Na sakeki, idan kinsamu miji kiyi aure domin bazan iya cigaba da zama dake ba, Allah yasani ina sonki! Amma kisani rayuwar yanar gizo ba rayuwa bace, ki koma ga Allah ki tubar mashi hakika Allah yana yafe zunuban bayinshi. ```Rashida``` Al'amarin auren rashida da abdul kuwa ya shiga cikin tsari, anyi abubuwa da dama kamar biyan sadaki da sauransu. An saka ranar auren nan da watan gobe, lefe aka had'u naji da gani kai da ganin wannan lefen kasan Abdul ya taka ya murza ya kuma zaunah tare da kwantawa luff a cikin daula. ```Salama``` Rayuwa suka cigaba dayi abunsu kamar ynda ya kamata. Ni kaina kausar ina alfahari da rayuwar salma. ®Kausar Luv💞 [1/6, 6:23 PM] Kausar Luv💞: ```🕸AKAN SOCIAL MEDIA🕸 (YANAR GIZO)``` ```©Kausar M Hassan``` *Page 61 to 70* ```Fadila``` Daga nan kuwa zaid d'akinshi ya shiga ya maida ya kulle da key, yayinda fadila taji duniya tayi mata zafi, ga aurenta ya mutu, shin mai zata fad'awa mamanta sanadin mutuwar aurenta"? Farry ce ta d'an dai2ta kanta ta kallie fadila "Fadila tashi muje gidah fadila, kadararki kenan" Idanunta da sukayi jajir ta d'aga ta dubie farry "Allah baya d'orawa bawansa abunda bazai iyaba, kisani cewa ni najawa kaina" Farry tace "Oya fadila deana kuka haka, tashi muje" Rik'ata farry tai, yayinda fadila ta kapie idanunta ko wani kyakyawan motsasu batayi, banda hawaye babu abunda ke sintiri akan kumatunta. A haka suka isa gidah. Farry na kaita falon mother, ta juya saboda batason had'a ido da mother, kasancewar mother bata falon. fitowanta kenan dga kuryar d'akinta taci karo da fadila. Kusa da itah taje ta zaunah "Fadila! Mai yake faruwa"? Fadila batace da mother komai ba, banda idanu babu abunda ta bita dashi Girgizata mother ta shiga yi tare da furta "Fadila kimin magana, dan Allah, 'yata fadila mai ya faru dakene"? Kusan minti 5 aka d'auka a haka kapin nan fadila ta fashe da kuka mai tsuma zuciya tare da rungume mamarta. Hankalin mamanta gaba'aya ya tashi "Fadila zaid ne"? To wallahi bara in kirashi sea ya fadamin abunda kikai masa da zaisamin ke kuka" Hannun mother fadila ta rike tare da girgizah kai, cikin muryan kuka ta hau furta "Mama!, zaid baida laipien komai hasalima nice na 6ata masa mama na cuci kaina da kaina, nabar dad'in duniya ya rud'eni na kuma manta da akuy ranar sakamako" Rungume juna sukai daga uwa har "ya duk kuka sukeyi. "😓😪 Rayuwa abin tausayi, fadila kin bani tausayi buh duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan daka, kad'an kenan dga sharrin social media. _3weeks letter_ Rashida ce zaune akan kujera tana chat sai ga kiran Abdul ya shigo a wayanta, Murmushi tai ta dauka tare da furta "Angona" "Amaryata ta kaina" Fira suka d'an fara sosai kapin nan aka kirashi hakuri ya baiwa rashida ya katsie wayan. "D'an karamin tsaki taja "Anya kuwa wea abdul yana sona, a novel ba'a haka mafi yawa gskya" Kasancewar aurensu yau saura kwana 6, ya kasance an fara shirye2 sosai na wannan buki. ```Salma``` Bilal ne zauneh a falo yayinda salam ta fitoh a guje dga kuryar d'akinta tai toilet. Amai ta suma kwarawa kapin nan bilal yazo ya rikata bayan d'an lokaci sukai asibit. Gwajin farko da akai masu aka tabbatar da cewa salma nada ciki, farin ciki da murna agun bilal abun sea wanda yagani. ****** Zaid ne zaune ya kifa kai da guiwa, yana tunanin duniyah, chaan kuma sea ya tashi ya harhad'a kayanshi ya fice a mota. 🤔ko ina zashi oho. ```Rashida``` Bayan ta kammala sallar Azahar ta d'aukie wayanta ta shiga facebook kasancewar akuy wani abokinta wanda suka shaku a facebook d'in ana kiranshi da Abdallah. A cikinsu babu mai number d'in wani, dan zasu share shekau kamar 3 haka tare suna chating, kasancewar da email adress rashida ta bud'e facebook d'in. Allah gwanin baiwa mai arawa bayi lokuta, kamar yanda aka sa ranar wannan auren haka Allah ya kaimu itah. Abdallah rashida tai pinging d'inshi dea2 ranar da ake d'aura mata aure ga abunda tace masa. "Abdallah dan Allah ka bani number d'inka na waya inaso zan kiraka" Kamar yanda ta buqata haka ya bata number d'in Saving tai tare dayin hidden number ta kirashi. Ringing 2 tai ya d'auka tare dayin sallama hadie da furta plz waye"? Sallaman ta amsa tace "Nice rashida wadda na karba number d'inka" "OK!! nagane, rashida ban kuwa ta6a jin voice naki ba sea yau" "Abdallah, wannan chat d'in da nai dakai shine chat d'ina na karshe tsakanina dakai, wannan wayan da zanyi dakai kuma itace zata zama ta farko kuma ta zama ta karshe tsakanina dakai, ina mai fad'amaka cewan yau ake d'aura min aure, kamin addu'ah akan Allah yabani zamaan lapiyah, kuma ga a halin rayuwa dan Allah idan na ta6a b'ata maka rai cikin sani ko rahshin shi a iya zaman da mukayi to pz ina neman gafara a gurinka" Kasa jurewa Abdllah yay "Rashida wallahi kinsani kuka, na tsani bankwana a rayuwana, I hate gud byes. Buh ina maki fatan Allah ya bada zaman lpy" Murmushi tai ta amsa da "amin abdllh" Haka sukai sallama da junah. akayi buki aka kammala cikin tsafta da walwala, komai na wannan bukin anyi shi cikin girma kamar yanda rashida ke tsammani. Misalin karfe 9 aka d'aukie amarya dga gidansu zuwa gidan mijinta dake nesa da unguwarsu. Amarya ta ango kenan. ®Kausar Luv💞 [1/6, 6:23 PM] Kausar Luv💞: ```🕸AKAN SOCIAL MEDIA🕸 (YANAR GIZO)``` ```©Kausar M Hassan``` *Page 71 to 80* Bayan an kaita addu'ah abdul yay masu kapin nan suka fara ciye2 da lashe, nan sukai sallah raka'ah 2 ya dafa kanta yay mata addu'ah. Dga nan ni kausar na baro masu d'akin. ```Fadila``` Fadila ce zaune ta had'e kai da guiwa kasancewar tun bayan faruwar wannan al'amari banda kuka babu abunda takeyi gashi mamanta tayi2 ta bari ayiwa zaid magana ta hana. Mamantace ta fito dga d'akinta ta kalleta "Fadila wea bazaki iya fadamin damuwarki ba? Bazakiyiwa kanki fad'a ba? Zaid babu zuwa babu aike? Hawayenta ta share "Mother ki barshi kawea ni na hakura dashi Allah ya za6amin abunda yafi zama alkhairi" "To amin, kinga ni zan fitah ki kula da kanki" Hanya ta kama ta fitah yayinda fadila ta d'auki wayanta ta danna number d'in adnan, kira 2 tai bai d'auka sai a na 3 kasancewar tun bayan faruwar wannan al'amarin bai kirata ba, kuma ko ta kirashi baya d'auka. "Wea fadila dan Allan lapiya kike ta damun rayuwata"? Mamaki kalaman adnan suka bata amma ta gimtsie ta cigaba da cewa "Adnan kusan wata d'aya kenan banji muryanka ba ka kuwa san ta yaya nake bacci? Dan Allan ka tausayimin kasanfa mijina ya sakeni" D'an murmushi yay "Taimakon mi? Kinga na godewa Allah dayaasa mijinki ya yafemin abunda nai masa sabida haka nina tuba har ga Allah" Idanunta ta lumshe ta cigaba da cewa "Adnan to mai zai hana idan na kammala iddana muyi aure tunda muna son junah"? Daria adnan yay mata iya iko kapin nan yace "Wallahi babu ni babu ke, chabb! Ke! kigama isakancinki a gari, a social media ba inda pic dinki bai shiga ba, na gama ganin komai naki sannan in aureki? Wallahu la ana wala ke, Allah shi kyauta, lemme warn you ma, dga yau kada ki koma kiran wayata saboda ma ke zan chnza number, bissalam akan social media aurenki ya mutu ni kuma bazan yarda in hadu da Allah a haka ba" Tsinke wayan yay, yayinda hawaye suka dinga kwararo mata a ido. Tana mai tuna lokacin data fara 2go bata san kowa ba, a chan ne ta fara sanin wani abu waishi sex chat. Haka ta dinga tunano rayuwa tana kuka har na tsawon wani lokaci. *2weeks letter* ```Rashida``` Rashida ce zaune akan kujera, wani yaro haka d'an matashi ya shigo gidan ya kawo cefane kasancewar tun bayan aurenta bata fara girki ba sea yau. Kayan cefane ne da su abarba, ayaba, lemo, mango da dai sauransu. Kar6a tai kasancewar lokacin misalin karfe 10 na safe ne. Kitchen ta shiga ta fara harhad'a girki, kala2. Abunci kusan kala 5 tayi, ta had'a lemon abarba da kwakwa, kankana da lemon mango ta jera aka dining table, dea2 lokacin misalin karfe 1. Toilet ta shiga ta watsu ruwa ta fito tai alwala tai sallah, bayan ta kammala ta tsantsara kwalliya ta shirya cikin English wears riga ruwan huda da bak'in wando tayi kyau sosai kamshi kawea ke tashi a d'akin. Tsaff ta zaunah a falo tana jiran dawowar abdul dga office kamar yanda ya shaida mata zai dawo. Ba'a d'auki minti 10 ba kuwa sea gashi ya shigo, kai tsaye wanka yay kapin nan ya dawo falon, hannunshi taja zuwa dining tare da bud'e masa jerin kolulin a gabansa. Ido ya zaro yana mai kallonta "Rashida wnnan wace irin haukace? Abeg in kawo kayan amfanin gidah domin su jima ana amfani dasu shine zaki banzartar, ynxn dan Allah duk ina zan kai wannan kayan abuncin? Yama zancishi lokaci d'ayah gskya bakida tattali ko kad'an wallahi" Hawaye ta sumayi yayinda abdul yabita da kallo "Ke meye na kuka? Ina maki magana kinamin kuka? Ki kalleni mana" Idanunta ta d'aga ta dubieshi "To ai nagani a novel ne" Ajiyan zuciya ya sauke tare da sakin kugunshi daya kama ya d'ora hannunshi kan kafad'unta "Rashida rayuwar novels daban rayuwar zahiri daban, abunda yasa suke sa haka su masu rubutun sboda abu idan ana kurarashi yafi dad'in saurara, ki deana tunanin rayuwar novel idan kina rayuwar aure, abunda zaki d'auka a ciki shine mai amfani, mai kyau. Ki watsar dana watsarwa" Har lokacin dayakeyin wannan maganar sheisheikar kuka rashida takeyi "Hank chief ya ciro a cikin aljihushi wanda yake da kamshi har na fitar hankali. Miqa mata yay tare da furta "Wipe ur tears" A hnkli ta karb'a ta goge hawayen nata. Abdul ya zaunah kan kujerar dining yace "Rash zaunah" Zaunawa tai shima ya matsa kusa da itah "Rash ida, zan soki dea2 yanda zuciyata zata iya d'auka haka zan kula dake dea2 ikona, amma ki duba rayuwar zahiri kinji"? Ynxn dea bani abuncin zan d'and'an kowanne. Murmushi tai ta mika masa cokali ya d'an dana kowanne tare da kurba lemukan "Em nice, gaskya yayi dad'i sosai nagode wipy ta" Murmushi tai itama suka rungume junah cikin farin ciki da kaunar juna. ```®Kausar Luv💞``` [1/6, 6:24 PM] Kausar Luv💞: ```🕸AKAN SOCIAL MEDIA🕸 (YANAR GIZO)``` ```©Kausar M Hassan``` *Page 81 to 90* ```Salma``` A wani group take chatting, nan suka had'u da wata masaniyar addini, a nan ne take sanar da ita cewa akuy hanyoyi na kula da baiwa "ya "ya tarbiyya tun kapin a haifesu" Jin wannan kalamai yasa salma tai pinging d'inta prvt, bayan sunyi sallama. Salma ke sanar mata cewan Tanada juna biyu kuma taji tayi wata magana gameda tarbiyyar yara tun suna ciki. Matar mai whtsapp name kamar haka "Aneeluv😘" Tace ``` "Eh salma kwarai dagaske wannan haka yake, kisani kowacce rayuwa tana farawane akan bagire mai kyau, idan bakiyi planning d'in rayuwa ba to tabbas kinyi planning na shirin failing a rayuwa, bazaki iya tab'a dowowa da jiya ba dan ta riga ta wuce sea dea zaki iya cimma gobe through planing. Daga lokacin da kika san cewa kina d'auke da juna 2 tofa kisani Allah amanace ya baki, na kula da abunda ke cikinki, ta hakkin kula da lapiyarshi, idan kina shaan music to yakamata ki deana ki rika sauraran karatun al'qur'ani a kowanne lokaci, ki rika yawaita nafila da karanta al_qur'anin ke da kanki, ki lizimci aikata duk wani aiki na alkhairi, abunda ke jikinki yanaji. Sannan a sakawa abunda aka haifa suna mai kyau mai kuma inganci wanda yakeda asali. "Ke kuma yawaita karanta wannan addu'ar Rabbi hablii minas shalihiin "My lord,grant me [a child] from among the righteous Sannan idan Allah yasa kika haihu, kina cikin jin ciwon nan kiyiwa yaronki addu'ah ta alkhairi domin kuwa a wannan lokacin Allah na amsar addu'arki ba tare da hijabi ba``` Aneeluv ta dea jima tana baiwa salma shawarwari sosai kapin nan sukai sallama kasancewar bilal ya dawo. Nuna mashi salma tai, ya kuma yaba ya jinjina sosai matuqa ga irin wannan nasiha ya kuma bata tabbacin cewar in shaa Allah zai kasance tare da ita domin baiwa "ya "yansu tarbiyya da kuma suna na gari.. ```Fadila``` Fadila ta rame ta bushe, yayinda zaid na samu labarin yana kasar Egypt a chaan ma har yayi sabon aure yamanta da rayuwar wata fadila. ```Rashida``` Soyayya suke zabgawa son rai, rashida ta dawo hanklinta sea a lokacin ta gane taiwa bawan Allah sani ba dea2 ba, alfarma ta rok'a a gurin Abdul, domin ya kaita gurin sani ta roka gafaranshi, dkyar ya yrda ya kaita, ta bashi hakuri yace "Babu komai shi ai ya hakura tun bayan tayi aure ya kuma yimata addu'ah sosai" Rashida ta dea gane cewar rayuwar novel daban rayuwar zahiri daban, so ta hankalta da wannan sosai... Ya labarin adnan?🤔🤔🤔 ```®Kausar Luv💞``` [1/6, 6:24 PM] Kausar Luv💞: ```🕸AKAN SOCIAL MEDIA🕸 (YANAR GIZO)``` ```©Kausar M Hassan``` *Page 91 to 100* A kwana a tashi babu wuya ga Allah, har fadila ta kammala iddah, tayi neman adnan ta rasah a kullum dashi take kwana dashi take tashi, gashi tana so ta rok'a gafarar zaid amma sam ta rasa contact dashi. Yau ranar ta kama monday, bayan tayi wanka ta shirya ta fitah kasancewar zatajie gidansu farry ne dan aurenta ya kusah. Akan hanyarta ta zuwa taci karo da adnan a kopar wani super market, tsayawa tai yana ganinta ya 6ata rai dubawan da zatai taganshi tare da wata mace cikin hijab shiga ta kamala. Matsawa tai kusa dashi cikin sanyin murya tace "Adnan"! Google glass d'in dake idonshi yacire ya dubeta, chaan ya maida dubanshi ga wadda suke tare "Ki shiga mota ina zuwa" Mota ta shiga yayinda adnan ya maida dubanshi gareta "Fadila bance ki fitah harkata ba? Kinga ni har nayi aure wannan matatace" Motarshi ya koma yaja tare da bad'awa fadilan kurah. Jikinta ta d'an kakka6e ta karasa gidansu farry. Itama dea farry nasiha taimata akan ta kyale adnan ta kuma nema gafara da yafiyar Allah. _9months letter_ ```Salma``` Allah ya baiwa salma haihuwa inda ta haifie "Yar ta wadda taci sunan marubuciyar aka rad'amata suna *Fateemakausar* yarinyar mai kyau da itah son kowa kin wanda ya rasa ```Rashida``` Cikinta ya kai wata 9 ana tsammanin haihuwa yau ko gobe, yayinda zamansu da abdul y zama abun jin dadi da kuma alfahari.. ```®kausar Luv💞``` [1/6, 6:24 PM] Kausar Luv💞: ```🕸AKAN SOCIAL MEDIA🕸 (YANAR GIZO)``` ```FINAL EPISODE ``` Bayan wata d'aya da faruwar hkn Allah y baiwa rashida haihuwa ta haipie yaro wanda yaci sunan salim. ```Fadila``` Haka tai hakuri ta sanarwa da mother abunda ya faru tsakaninta da zaid, saboda mother ta matsa mata akan zaid, mother kaman zatai hauka saboda bakin ciki, amma ba yanda ta iya face tai mata addu'ah. Ko bkomai uwa bazata kie yaronta ba. _2months letter_ Fadila ma tayi aure inda ta auri wani mai mata 2 takasance ta 3, ta kuma yi watsie da rayuwar bnzar data d'ibarwa kanta a social media Zaid kuwa yana Egypt zamanshi tare da matarshi, hka adnan shima y tuba. Ya yan uwana mu rika tubarwa Allah dmn Allah gafurun ne kuma rahiemun. ```Salma``` Baby kausar nata girma, yayinda salma da kuma bilal suke kula da ita sosai da sosai. A kullum bilal kuma a koda yaushe yana godewa Allah, da Anee. Da matarshi ta had'u da ita a social media dan ta wayar dasu abubuwa da dama da basu san dasu ba wanda gashi suna ganin ribar abun a halin ynxn. ```Rashida``` Kwance take tare da salim a gefenta. Abdul ya shigo, ta baya yay hugging d'inta "Matata nayi kewarki sosai wallahi" Kiss ta manna mashi a kumatu "Nima haka, kaga salim sea baccinshi yakeyi" D'an murmushi abdul yay "Nima nazo a kwantar dani, domin ynxn na kammala karanta wani littafi mai suna AKAN YANAR GIZO" Murmushi rashida tai "Haka yake kuma ai a wayana ka karanta nasani dan tun d'azun daka kar6a kaketa faman murmushi da daria, nasan kaji dadinshi, to ba wannan ba kada ka bari in baka labarin sabon littafin marubuciyar mai zuwa nan gaba wanda taiwa taken suna *MUGU BAI DA KAMA* Baban salim ko mugu yanada kama"? Kai abdul ya girgiza mata tare da furta "Inafa mugu yagan kama rashidah, zan kuwa gyara zama domin jin wannan labarin" Murmushi sukai a fukokinsu tare da rungume juna fuskokinsu cike da wal_wala da tsagwarun annuri ta tarin soyayya. ```******``` ```Praise is due to Allah, who has favoured us over many of his believing servants. My lord, enable me to be grateful for your favour which you have bestowed upon me and upon my parents and to work righteousness of which you will approve and righteous for me my offspring. Indeed, I have repented to you, and indeed, I am of the muslim. Creator of the heavens and earth, you are my protector in this world and in the hereafter. Cause me to die a muslim and join me wt the righteous. Our lord, guide us to the straight path. The path of those upon whom you bestowed favour, not of those who have evoked [your] anger or of those who are astray. Our Lord, let's not our heart deviate after you have guided us and grant us from yourself mercy. Indeed, you are the bestower Exalted is your lord, the lord of might, above what they describe. And peace upon the messengers. And praise to Allah, lord of the worlds..``` *ALHAMDULILLAH!!!!* Sadaukarwar novel d'in nan takiece *RASHIDA ABDULLAHI KARDAM* Whdr its whtsap! we chat! Facebook! IMO,keep, badoo, snap chat, e.t.c always remember that *"Kullun ula'ika anhu mas'ula"* As a woman kina d'aukan nude pics kina sending ma saurayinki, one ting da baki fahimata ba shine. shi dran yagani so zai nunawa wani, kuma shi da wuya ya aureki, saboda yasan bashi d'aya kika turawa ba, mutunci da daraja ta "ya mace shine d'akin mijinta, sunna itace abar takama, Allah ya bamu ikon tsarewa da kuma kare mutuncinmu amin.. +2347067465637 For any correction and comments. ```Sai mun had'u da JANNAT dake cikin MUGU BAI DA KAMA``` Love u❣ ENX FOR ALL THE LOVE AND SUPPORT.. *Happy eidil_ kabir in advance.*👌🏽 adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *