Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Thursday, 1 June 2017

Lamarin duniya

adsense here

[9:54am, 8/5/2016] ☄DEENY☄SHOMAR☄: [4/11, 9:52 AM] Khadeeja Candy: BISMILAHI RAHAMANIN RAHIM 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 1⃣ Cike da gajiya ta shigo parlor kamar zata fadi Kana ganinta kasan jikinta babu karfi saida ta kawo kusa da hajiya shafa Sannan ta zube zaune kasan carpet Cikin kasalalliyar murya ta shiga mata magana hajiya na kare aikina Fuska a hade ta kalleta cikin isa tace tohm mie zan miki Kasa tayi da kanta dan ganin irin kallon da take mata tace daman gida zan wuce Dauke kanta tayi daga hararar da take mata tace to nidai yau abinci kadan nayi kiyi hakuri a gaida gida bata ce mata komaba ta tashi cike da damuwa ta nufi kofar fita Da sauri kdeey dake dining area ta kwala mata kira fatima a hankali ta juyo naam aunty kdeey Tana sude hannu tace zo ki dauki wannan abincin ni na koshi Karasawa tayi ta dauki plate din ta kalleta tace na gode Murmushi tayi tace ki hada dana yaya umar yana kitchen Kai kawai ta daga mata ta fice Tana shigowa gida jidda ta nufo.ta DA gudu tana fadin batula sannu da zuwa yauwa sannu ina umma DA yatsa Jidda ta Nuna mata ita " gata can" ta shiga kokarin karbar ledar dake hannunta sakar mata ledar tayi ta karasa karkashin bushiyar durumi inda umma take it kwance zauna tayi saman tabarma Tana sauke ajiyar zuciya Tasa hannu a hankali tana shafa fuskar umma tana murmushi Mutsawa ta farayi sannan ta bude ido suna hada ido ta tashi zaune da sauri tana gyara daurin dankwalinta " sannu batula kin dawo " "ae umma na dawo " juyawa tayi ta kalli jidda dake juye abincin dake cikin ledar a roba tace " ki karaso nan kuci da umma mana " " tohm bari na karasa " Bayan ta kare ta taso rike da abinci ta nufo gurin da suke zaunawa tayi tare da dire abincin gaban umma tana fadin " gashi kusa hannu muci ni yunwa nake ji Kuma ma abincin ba shida yawa " fatima tace " to ya za'aiyi yau hajiya bata baniba cewa tayi bata girka abinci da yawa ba wannan ma ragowar yayanta ne" kallon abincin umma tayi tana hadeye yawu tace " to kuci nidai naci abinci makota dazu " kallonta fatima tayi " haba umma wane irin makota kuma kufa na kawowa dan ni wlh naci acan " Kawar da fuska umma tayi tace " to ai saiki kara dan nasan baki koshiba " Fatima tace " dan Allah umma kici wlh ni naci a can wadda Kdeey ta raga sai nazo muku DA wannan Kuma kinji Na rantse ai " juyowa umma tayi ta zira hannunta cikin robar abincin Da sauri2 take cin abincin dan ba karamar yunwa takejiba Fatima dake kallonta idonta suka ciko da kwalla DA sauri ta kawarda fuskarta dan kar umma ta.gani tashi ta nufi daki ©Khadeeja Candy 🍭 [4/11, 9:58 AM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 2⃣ Washe gari fatima ta shirya cikin kudaddiyar atamfarta sai shafe2 fuska take da raggagin kayan kwaliyarta Tana karewa ta dauki hijab tasa ta nufo umman dake shan koko+kosai da malam rufa'i ya aiko mata tana fadin " ni zan tafi umma " jidda ta kalleta." bazaki kisha kokon ba "? Umma ta riko ta " zauna kisha kokon sannan kitafi kinma yi latti " turo baki tayi " ni wlh aikin nan ya fara isata ace mutum tun safe in yaje bazai dawo ba sai maraice kuma bako wani albashin kwarai ba kuma ba abincin kirki " Umma tace " kiyi hakuri nima ina nan ina nema kinga dana samu sai ki daina zauna kisha kokon " " a a umma kusha kawai ni can zan karya kinsan bason koko nakeyi ba " umma tace " ai dakin sha ko kadan ne karki fita baki karya ba " dukawa tayi tayi ludayi daya ta tashi " nikan na tafi " umma tace"to Allah ya tsare yayi miki albarka " murmushi tayi tace " amin umma sai na dawo " daga mata kai umma tayi, tafice Tana isa parlor ta fara wuce wa a dining area ta tararda su suna karyawa cikin ladabi ta isa gurin cikin girmama wa ta shiga gaisu hajiya shafa " hajiya ina kwana anty Kdeey yaya umar nabila an ashi tafiya "? Duk suka amsa Mata banda HAJIYA shafa Kdeey ta kalleta tace " kinyi kyau fatima " murmushi tayi "na gode " ta yunkura zata tashi Hajiya shafa ta watsa mata harara " kekeke zo ki kwashe plates din nan yar raini hankali kullum sai rana tayi falfal kike zuwa ke ishashiya ko "? Batace da ita komai ba dan tasan ko hakuri ta bata ba hakura zatayi ba, Tana cikin kwashe kwanukan nabila ta kalleta da fuskara kyankyami " waike baki da wasu kayan ne kusan koda yaushe kayan nan kike sawa "? yi tayi kamar bata jitaba ta dauki kayan zata wuce. Da sauri nabila ta fisgo mata hijab " ke badake nake magana ba kikayi banza dani yar iska kawai " Cikin daga murya ta kalleta tace " bani da su mana inda inada daban saka ba " hajiya shafa ta rike baki " lalala lailai wuyanki yayi kauri ihu kike mata kamar mai fada da warinki " Fatima kamr zatayi kuka tace "bakiji abunda tace.min bane kullum nazo gidan nan sai ta fadamin maganar dazata bata min rai " Hajiya tace "au nima rashin tarbiyar zaki nunamin ke nan to baza'a bata miki raiba diyar uban wace ke "? Shiru tayi dan bataji zata iya sake ce musu wani abunba Nabila tayi kwafa "yarinyar nan fa yar iskar karshe ce bari kiga nayi maganin ta " Tana tashi tsaye Kdeey ta riketa tana kallon Fatima tace " momi yi mata hakuri dan Allah fatima je kiyi aikinki " Juyawa tayi idonta cike da hawaye ta fice ©Khadeeja Candy 🍭 [4/11, 12:29 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆ Na Khadija Abubakar Alkali 3⃣ Tana cikin wanke2 kdeey ta kirata "fatima" " naam anty kdeey " ta tashi da sauri ta nufi balcony inda take zaune tana fadin." gani wani abu za aiyi miki " Nuna mata guri tayi kusa da ita tace "zauna a nan " Ba musu ta zauna gurin da ta nuna mata kdeey ta dauko bakar ledar dake hannunta tana shirin mika mata tace "tufafi ne zan baki amman fa sun miki yawa dan kisan nafiki girma " tana murmushi ta mika hannun zata karba "ae inaso haka nan " Yanje ledar kdeey tayi tace "to amman sai kin fada min mie kikayiwa ihu shekaranjiya da kika shiga dakin yy umar "? Fuskar shagwaba fatima tayi tace "nidai ba tun ranar nace miki babu komai ba " Kdeey ta hade fuska "Allah fatima in baki fada min ba batawa zanyi dake kuma kinga duk gidan nan ni kadai nake sonki ko kuma naki baki tufafina dama komai nawa" Shiru fatima tayi kanta a kasa tana ta wasa da hannayenta. Sai da taji kdeey tayi kwafa sannan ta dago ta kalleta kamar zata fasa kuka tace " in fa na fada kasheni zaiyi " Kdeey tayi murmushi tace "to ai ni kawai zaki fadawa kinga ni kuma bazan fadawa kowaba kinsan mufa kawayene " zatayi magana hajiya shafa ta fito rike da gayye tana fadin "khadija zo ki gyara min wannan gayyen zan dora girki " Tana kallon fatima ta hau ta da masifa "au baro aikin kikayi kika dawo nan kika zauna ko " jikinta na rawa ta tashi zata Kdeey ta rikota tana kallon hajiya shafa tace "momi ni na tsayarda ita " ta kalleta "dauki ledar ki tafi " washe hakura tayi cike da far'ah ta risina "anty na gode Allah ya biyaki " "amin zamuyi magana gobe je kiyi aikinki " Ta fada tana murmushi Kai fatima ta daga mata baki har kunne cikin tsawa hajiya shafa tace "uban mie nene aciki mie kika bata "? Kdeey tace "tufafi ne momi jeki fatima ciki gaba da aikinki " kamar nata jiran umarninta ta nufi gurin wanke2 ta da sauri ita kuma ta tashi ta nufi gurin hajiya shafa., ©Khadeeja Candy 🍭 [9:54am, 8/5/2016] ☄DEENY☄SHOMAR☄: [4/12, 5:47 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 4⃣ Yau cike da far'ah fatima ta shigo gida umma najin sallamarta ta fahimci cikin nishadi take dan da wake tayi sallama tun kamin ta karaso umma ke kallon ledar dake hannunta har ta zauna.kusa da ita saman tabarma umma ta kalleta fuskarta dauke da murmushi tace "yau batula wani abun ya samune ake far ah haka "? fari tayi da ido tana dariya ta shiga yage ledar les ne mai matukar kyau da daukar hankali.sai wata atamfa sky blue mai kyau babu wadda zai gansu yace an taba sanyasu sai dai wadda ya sani, umma tayo waje da ido tana fadin "duk na waye ne batula ina kika samo "? wantowa tayi jikin umma tana dariya tace "umma nawa ne "."waya baki batula "? "gurin aikina ne yar hajiya ta bani wlh umma tana da kirki sosai " "tohm Allah ya biya ta ya saka mata da alkhari haka akeson mutum ya zama ai mai taimakon na kasa dashi kinga kin samu na sawa ai ". tashi tayi zaune tana kallon umma tace "wane irin na samu na sawa kuma kinsan nifa ba sawa zanyi ba " umma tadan hade mata fuska "to wannan karon dai sai kinsa kaya mai kyau haka zaki ce ki saida " "to umma in ban saida ba nayi yaya kinga fa yamin girma kuma umma abinci fa zamu siya " umma ta sauke ajiyar zuciya tace "na sani fatima amman a zauna haka koda yaushe bakya sa suturar kwarai dubi fa rabin kayanki ki gani daga tsofafi sai yagagi "? "to umma ya zanyi haka Allah ya kaddaro muna ". kasa umma tayi da kanta fuskarta dauke da damuwa, fatima na ganin haka ta shiga kokarin kawar mata a tunanin "umma ga abinci fa yau tabani kuma da yawa ina jidda tazo muci " umma ta kalleta idonta cike da kwala ta shafa kanta tace "jidda tana ciki batula Allah ya muku albarka ya taimake ki kamar yadda kike taimakon mahaifinyarki ". murmushi tayi "amin umma jidda...! ". ta kwalawa jidda kira ©Khadeeja Candy 🍭 [4/12, 8:55 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 5⃣ Saida fatima tayi ta kiranta sannan ta taso ta nufo su tana murzar ido, Umma tace " wannan bachi dai jidda daga gani na yunwa ne tunda baki saba bachi rana ba " fatima tayi murmushi " to ai ga shinkafa nan sai muci yau ta zubo min da yawa " Ware ido jidda tayi tana shirin zaunawa " lahhh batula kayan waye ne haka mai kyau " " nawa ne gidan da nake aiki aka bani " Jidda tace " gaskiya suna da kyau kin samu tufafin sakawa kin huta da tsegumin yan umguwar nan " Umma ta kalleta " tsegumin kamar ya wani abun akace ne " jidda ta dan turo baki tace " ranar maman haruna da marwa suke cewa wai mugun halinmu ne ke binmu wai bama saka tufafin kwarai ko ambamu ba asan inda muke kaiwaba wai kamar mu mukafi kowa talauci " Fatima tace " nima haka ake cemin su hafsa da zara balle suwaiba wai ina mugun halin ban saka tufafin kwarai kamar yar almajirai har ma gurin aikina haka suke cewa " shiru umma tayi ta sunkuyar da kanta jin tayi wani kololo na bakin ciki ya taso mata A hankali fatima ta dafata " umma sa hannu muci abincin " jimmm tayi kamar bata ji mie fatima tace saida ta maimaita sanna sanya hannu suka faraci, Ana kare sallar magariba fatima ta dauki kayan tana fadin " jidda zo ki rakani gidansu maman Gaddafi nakai mata kayan nan ko zata tsiya " da sauri umma ta kalleta " a a batula kibar kayanki ki rika sawa " ,,,, ©Khadeeja Candy 🍭 [4/12, 11:19 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 6⃣ Risinawa fatima tayi ta dafa umma " dan Allah umma kibar wannan tunanin kibar beye mutane Allah dai yasani bada son ranmu muke haka ba " ajiyar zuciya umma ta sauke tace " mutane sunada gaskiya batula nima ina son ganinki cikin tufafin kwarai kamar ko wace ya ni ban siya miki ba batula bazai yiyu duk kuma aka bakiba mu siyar tun kina karama muke cikin wannan halin " Zaunawa tayi cikin yanayin damuwa tace " umma dukan tsanani yana tare da sauki kuma bayan wuya sai dadi umma miye anfanin saka tufafi maikyau babu abincin kwarai babu fa mai bamu inba Allah ba babu wadda ya kula da halin da muke ciki dan Allah umma kibarni nayi abunda nayi niya wata rana sai labari kuma in bamuyi haka ba ya zamuyi tunda kina gani ko makotanmu babu ruwansu damu " Umma ta nisa " hmm duniya kenan masu taimako sunyi karanci yanzu mokoci babu ruwansa da makoci sai muyini bamu ciba amman babu ruwan kowa da mu halin mutanen yanzu kenan batula tun mahaifinki nada rai burinsa kusamu karatu kusa rayuwa maikyau kamar kowa amman hakan bai samuba har yabar duniya saboda rashin kudi kibar zuwa makaranta amman babu wadda ya kula dubi yadda rayuwarki ta zama da kuruciyarki babu karatu sai ga aiki gidan da basu san darajar mutane ba ga kanwarki nan jidda ita babu karantu haka za......! Kukane yaci karfinta fatima ma kuka ta shiga yi tana ba umma hakuri " dan Allah umma kibar kukan nan kowa fa da irin rayuwar da Allah ya tsara masa wata kila haka Allah ya kaddaramana tamu rayuwar kuma Allah yana jarana bawa dan Allah umma muyi hakuri da abunda Allah ya kaddaro mana, " Haka tayi ta tallasarta har saida hankalinta yam kwanta sannan ta dauki kayan suka tafi,,,,, DEDICATED TO U kdeey 😘 ©Khadeeja Candy 🍭 [9:54am, 8/5/2016] ☄DEENY☄SHOMAR☄: [4/16, 7:18 AM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 1⃣1⃣ Tana shiga fatima ta saki jidda da sauri ta nufi dakin, dan ko kadan bata son jin kukan mahaifiyarta Zaune ta tararda ita ta hada hannu da kai tana aikin kuka Da fata fatima tayi " umma na daina ki daina kukan kinji "? Umma ta kalleta da jajayen idawanta ta shafa gefen fuskarta hawaye nabin fuskata kamar fanfo, Jidda na shigowa ta zauna gefen umma tana fadi " kingani ko umma mun daina dan Allah kiyi shiru " dakar ta iya tsagaita kukan suka fada jikinta suka rungume ta, Hannayenta ta daga sama " ya Allah ga yayana nan kafi ni sanin abunda ya dace dasu kafini sanin rayuwar da sukayi baya da wadda suke yanzu da wadda zasuyi a gaba ya Allah basu da gata sai naka babu mai taimakonsu sai kai Allah ya Allah ka dafa kafadarsu Allah suma su zama kamar yayan kowa Allah...." da kuka ta karasa addu'ar " Suma da kukan suka amsa da " amin " Bayan i'sha suna zaune gindin bushiya umma na gasawa fatima jiki da tuwon kasa, Akayi sallama duk suka amsa fatima ta daga kendir tana yadawa dajin kamar tasan mai sallama saida ta karasa tana shirin zaunawa sannan fatima ta ganeta. Nan da nan ta saki far ah Aunty Kdeey ina wuni" fuskarta dauke da murmushi ta amsa " lafiya kalau fatima " ta dubi umma " maman fatima ina wuni " umma ta dan saki fuska " lafiya kalau ya gida "? Kdeey tace " gida kalau dan Allah umma kuyi hakuri da abunda ya faru wlh bana nan saida na dawo ake fada min abunda ya faru " janyo hannayen fatima umma tayi ta shiga nuna mata " dubi yadda suka mata da jiki saboda bata da kowa saboda sun san babu abunda za'aiyi musu " kasa kdeey tayi da kana idonta suka cika da kwalla Can ta dago ta kalli fatima tace " kiyi hakuri fatima kinji komai mai wucewa ne " murmushin karfin hali fatima tayi " babu komai Aunty Kdeey ai ya wuce " Da fata Kdeey tayi suka dan taba fira da umma sannan ta ciro dubu 3 tana kokarin tashi ta ajesu gaban umma " gashi maman fatima asaye goro " umma tayi murmushi tace " to Allah ya biyaki ya saka miki da Alkairi " " amin maman fatima fatima muje ki rakani ko "? Fatima ta taso suka fito tare.,,, ©Khadeeja Candy 🍭 [4/16, 9:36 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 1⃣2⃣ Suna fita kdeey ta bude mota ta dauko wata katuwar leda ta mikawa fatima " karbi wannan nasan bakinki dason dadi ko " dariya fatima tayi ta karbi ledar tana mata godiya har ta juya kdeey ta kirata " fatima " ta juyo " naam Anty Kdeey " Saida ta dafata sannan tace " kici gaba da hakuri kinji shi LAMARIN-DUNIYA haka yake dole sai hakuri ba ke kadai kike cikin wannan halinba dan haka kiyi hakuri kinji "? Kai ta daga mata " na gode anty kdeey Allah ya saka da alkhari " " amin jeki gida umma na jiranki " " ok toh sai da safe Allah ya tsare " Tana shigowa cikin gida ta dire ledar gaban umma " umma kinga wai abunda ta siyo min " ta karasa maganar tana kokarin kwance ledar, Lemo da ayaba ne sai kankana da abarba da apple da yogurt 1lr jidda ta washe baki " kai gaskiya tana da kirki kamar tasan munajin kwadayi " umma ta sauke ajiyar zuciya tace " LAMARIN DUNIYA kenan wani ya kyautata maka wani ya musguna maka wani lokacin duniyar ta soka wani lokacin ta juya maka baya Allah ya biyata " " amin umma ai anty kdeey nada kirki saboda ita nake jin karfin zama gidan nan " cewar fatima Umma ta kalleta " yanzu kan ai batun aiki ya kau bake ba sake aiki a gidan nan " bata fuska fatima tayi " saboda mie umma nidai indan dan bugun nan ne dan Allah karki hanani "? Umma ta shiga cin ayabar tana fadin " batula na riga nasa araina bazaki kara xuwa aiki gidan nan ba har abada " "to umma kidina ba kinsan ankusa biya na fa ai kara nayi inyaso dana karbi kudin sai na daina zuwa " umma tace " a a vatula makukar ma bacin raina kike soba toh kibar maganar nan a yadda nace miki kibar mata kudin inma aikin kike so sai a nema miki wani guri " " amman umma inna daina aikin mie zamuci in muna son dan wani abu da mie zamu siya "? Jidda tace " lallai kan umma ai dakin barta taci gaba kamin a samu wani " harara umma ta watsa mata tace " bazata karaba Allah shine gatan mu shi zai mana magani amman aiki gidan hajiya shafa kan har abada " Fatima ta gutsura apple tace " shikenan umma Allah ya tsaya mana " ita da jidda sukace amin ©Khadeeja Candy 🍭 [4/16, 10:11 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 1⃣3⃣ Washe gari fatima na zaune gidin murhu ta tsurawa wuta ido, Kana ganinta kasan tunani takeyi. Dafata umma tayi " tunanin aikinki kike ko "? Tayi murmushi umma tace " wlh kinga damuwar nan taki batula duk tasa yau na tashi raina a bace jikin kuma ba dadi " Fatima tace " nima umma yau haka na tashi da rashin jin dadin kamar ki " umma tace " tunanin da kike ne batula " " a a umma ni ba tunanin aiki nakeba kawai ina tunanin wani abun ne daban " Kusa da ita umma ta zauna tace " wani abu kamar yaya "? " umma tunani nakeyi wai mie zai hana bazamu je gurin yan zakka da wakkafi ba mu fada musu matsalolin mu tunda ance suna taimakawa ko Allah zaisa su taimaka mana koda da abun sana'a ne "? Shiru umma tayi har na wani lokacin sannan tace " nima nayi wannan tunanin batula dan naji ance har suna daukar nauyin karatun yara marayu ko Allah zaisa au dauki nauyin naku karatun kuma ku dan samu koda kadan ne " fatima tace " to kingani ma umma dan Allah muje tunda kinga ni nabar aiki yanzu yan kudin da anty kdeey ta bamune in suka kare ya zamuyi can baya ma yaya abun yake balle yanzu " " to ai batula baki ta takiba ina tsoron karmuje bamu samo ba " zamuma samo umma tunda bamu mukafi kowa kansar talauci ba muje muma mu gwada sa armu " dariya umma tayi tace " to ai sai muje Allah ya bamu sa ar " murmushin jindadi fatima tayi tace " amin Umma amman gobe xamuje ko "? " gobe batula baiyi kusaba kodai jibi "? Jidda ta fito daki tana fadin " a a umma dan Allah muje gobe koma yau " fatima tace " munafuka kina jinmu Ashe ko"? Dariya tayi tace " wlh ina jinku jikinane babu dadi na kasa tasowa dan Allah umma muje gobe " umma tace " Allah ya kaimu amman rashin jindadin jikin nan duk haka muke ji Allah dai yasa na kafiya ne " Fatima tace " amin Umma na sa a ne zuwan da zamuyi " duk suka kwashe da dariya kamar babu abunda yake damunsu,,, ©Khadeeja Candy 🍭 [9:54am, 8/5/2016] ☄DEENY☄SHOMAR☄: [4/15, 7:07 AM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 7⃣ Da far ah ta shigo gida ita jidda tun kamin ta karaso ta tsaya bakin kofa ta kunna kendir, Saida sukayi sallama sannan suka shiga dakin umma na kwance rike da cirbi ta tashi zaune tana amsawa " amin waalaikissalma batula har kun dawo "? zaunawa tayi kusa da ita ta manna kendir din gefenta " ae umma na dawo gaskiya umma kayan nan masu kyau ne duba daya daya ta saye ko wanne " jidda tace " jikinta har yana rawa wai inta samu wasu ta kawo mata " Umma ta tabe baki tace " uhmm ai daga ganin kayan nan ba kanana bane tunda ma kikaga ta siya haka to sunfi hakan " jidda tace " lailaikan dan siyen wulakancine da ita " fatima tace " nidai ina ruwana badai ta siya ba " karbar ledar dake hannun jidda tayi tana fadin " umma kinga na siyo mana taliya da makkaroni nayi dan cefane" ta mika mata sauran kukin " karbi wannan ko kyasai wani abu" umma ta karbi kudin tana murmushi " Allah yayi muku albarka ya cika muku burinku ya jikan mahaifinku " duk suka amsa da " amin " tana kokarin tashi tace " bari naje na girka " da sauri fatima ta da fata " haba umma wani irin ki girka gani zaune nayi ga aiki wani gida balle namu nizan girka koma ki kwanta warki " ta karasa maganar tare da tashi Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar umma murmushi kawai tayi a zuciyarta sai yabawa fatima take da samata albarka. Washe gari fatima bata bar gidan ba saida ta gyara ko ina tayi diban ruwa ta girka abinci. Sannan ta nufi gurin aikinta ©Khadeeja Candy 🍭 [4/15, 8:50 AM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 8⃣ Hajiya shafa dake zaune tana kallon BBC dake labarun Nigeria taja tsaki " mtssss wlh nabila matsala ne dake bazaki iya tsayawa ki duba abu da kyau ba nan gurin na barsu mana " " Allah momi ban ganiba na duba fa sai in nabila ta dauke su dan ita kadaice gurin kwance " hajiya shafa tace " ahhab suna gurin ta jekice ta baki " Fatima na cikin bachi nabila ta kaimata wani mugun shiri. Saida ta zabura ta tashi tana murzar ido " naam wani abu za ayi miki "? Murguda mata baki tayi kamar wata warinta tace " momi tace ki bani kudi " fatima ta kalleta " wane kudi "? " kudin da momi ta aje nan mana " " bata baniba amman bari na duba miki " fatima ta shiga dauke kayan gurin tana dubawa, Saida ta kakkabe komai sannan ta dubi nabila tace " kingani basa gurin kila suna daki " nabila ta shiga kwalawa hajiya shafa kira " momi kinji wai bata dauka ba kuma basa gurin " Fitowa hajiya shafa tayi tana fadin " a a nan fa gurin na ajesu sai in ita ta dauke su " Nabila tace " ai bazai mata wuya ba tunda neman kudi take ido rufe " hajiya ta zare mata ido " bani kudi na dana aje nan gurin "? Nan da nan jikin fatima ya shiga rawa " wlh hajiya baki bani ba kuma ban dauka ba " nabila ta nuna ta da yatsa " karya kike ke kika dauke su barau niyar banza kawai " " ni wlh ba barauniya bace dan ban taba daukarwa wani2 abuba " nabila ta kama zaninta zata kwance fatima ta shiga kokuwa da ita " ni wlh ki sake min zane ban dauka muku kudi ba wlh ni bana sata " Nabila bata saurara mata ba saida ta maidata daga ita sai pant ta kure ta fadi kwance. Da sauri fatima ta tashi ta dauki zanenta ta daura tana kuka tace " yadda kika min Allah yayi miki kuma ban yafe kazafin satar da kika min ba Allah ya isar min azzaluma kawai " tana rufe baki taji saukar mari har biu a fusakarta Dafe kumatunta tayi ta fashe da kuka kamar karamar yarinya, Hajiya tace " yayi daidai kinji min yarinya da iskanci yar iskar banza wulakantacciya " hade bakinta tayi ta danne tana kallon hajiya hawaye nabin fuskarta. Hajiya tace " to ko raahin kunya zaki min dan kin saba yar marasa mutuncin " kasa fatima tayi da kanta tace " hajiya ki zageni amman karki zagar min iyaye" Salati hajiya shafa ta shigayi Umar dake kokarin fitowa parlor yace " lafiy momi mie ake yiwa salati da hayaniya haka "? ©Khadeeja Candy 🍭 [4/15, 9:33 AM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 9⃣ Nabila tace " fatima ce take ma momi rashin kunya har da Allah ya isa tayi min kuma fa kudi ta sata ", Da sauri fatima ta kalli umar tace " wlh yaya karya take ban daukar ma hajiya kudi " Umar ya hade fuska " inkinsan kin dauka fatima ki bada kawai kudin mie ne wai "? Hajiya ta fada masa Belt ya cire yana nadewa a hannun ja da baya fatima tayi tana girgixa masa kai dan tasan ita zai daka Ako yayi cikinta ya shiga dukanta da belt din babu kakkautawa hajiya batace kala ba ta juya ta shigewarta, Gidan duk ya cika da ihun fatima tun tana karewa inya daketa har takai bata iyawa Umar ko ya dage sai dukanta yake Saida yaga kukanta baya fita sannan ya kyaleta ya wuce dakinshi, Nabila tayi kwafa tace " ai shine maganinki gobe ki kara " ta juya ta nufi parlor fatima ta dade gurin kwance sai hawaye take har hajiya ta fito tana ganinta tace " to uwar kuka ai saiki tashi kiyi mana wake2 maraice ko"? Kallonta kawai fatima tayi idonta cike da kwalla Tsaki hajiya shafa taja ta wuce. Tana fita fatima ta dauki hijab dintta tasa ta fito cikin gidan tana hawaye Tana kaiwa gate mai gadin gidan ya kalleta yace " inata jin uhun ki fatima dukankine ake ko "? Batace dashi komaiba ta fashe da kuka mai ban tsausayi da sauri ya dafata " yi hakuri kinji sai hakuri lamarin gidn Allah ya bi miki hakkinki " daker ta iya cewa " amin " ta fice ©Khadeeja Candy 🍭 [4/15, 10:26 AM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 1⃣0⃣ Har ta isa gida hawaye take Jidda na ganinta tace " batula lafiya kika dawo yanzu mie kike yiwa kuka "? Faduwa tayi zaune wasu zafafan hawaye suka gangaro mata Umma rike da buta fito bandaki na ganin fatima ta saki butar ta karaso gurinta da sauri ta rikata cike da tsoro ta shiga tambayarta " batula lafiya mie ya faru wanine ya mutu mie kike yiwa kuka "? Fatima cikin kuka tace " umma maraici da talauci nake yiwa kuka " idanuwan umma cike da kwalla tace " mie akayi batula ki fada min mana "? Tana kokarin hade kukan da take tace " umma inda abbah bai rasuba da banje wani guri ga aikiba shine zai nemo ya bamu kuma koda bayan rasuwarsa da badan talauci ba daba basu wulakanta niba " Umma dake hawaye ta taba fuskarta inda taga kwancin jini tace " mie yasa fadin wannan maganar batula mie yasa zaki tuna min da babanku "? Tashi tayi tsaye ta cire hijab dinta ta shiga nunawa umma jikinta cikin kuka mai ban tausayi tace " umma dubi yadda suka min da jiki dubi irin dukan da suka min akan abunda bansan na aikata ba saboda banida gata saboda ni ba kowa bace saboda sun fini umma.umma suka cire min zane kan abunda banyi suka zage ni dan kawai ina talaka....." nan kuka yaci karfinta Da sauri jidda da umma suka rika hannunta suna duba jikinta ko ina kwanci jinine wani gurin ma har jini ya fito. Jidda da tun dazu hawaye take ta fashe da kuka ta rumgume fatima tana fadin " yi shiru batula Allah yan nan Allah ya isar miki " Umma tashi tayi tsaye ta rufe idonta daketa zubarda ruwan hawaye wani kololon bakinciki ya shiga mata yawo a zuciya Ta dade a haka sannan ta kalli fatima data rungume jidda suke aikin kuka Cikin muryar kuka umma tace " dan Allah batula kubar kukan nan har cikin raina nake jinshi " tana kaiwa nan ta nufi daki tana rufe baki saboda kukan da yaci karfinta.,,,, ©Khadeeja Candy 🍭 [9:54am, 8/5/2016] ☄DEENY☄SHOMAR☄: [4/18, 10:10 AM] Khadija A Alkali: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 1⃣9⃣ A hankali taji an dafata " malama lafiya kike kuka kuma a irin wannan gurin "? Kallonshi tayi tare da tashi tana fadin " ayi hakuri bansan ba a zama nan gurin ba " duk da ba haskene gurin sosai ba amman hakan bai hanashi ganin jan da idonta yayiba " a a so nake ki fada min mie kike yiwa kuka "? Tana share hawaye tace " ummata ne tayi hadari ta karye likita yace sai mun kawo kudi kuma bamuda su kuma yace zata ya mutuwa in bamu kawo da wuriba " Rungume hannayensa yayi " shine kike yiwa kuka "? Kai ta kada mishi " to kibar kuka kina son in taimaka miki "? Da sauri tace " ae dan Allah ka taimaka min " Hanya ya nuna mata ha hannu " to mutafi " ba musu ta nufi hanyar ya rufa mata baya. " bro's ina zuwa kuma "? Wata budurwa dake take front seat cikin wata hadadiyar mota take masa magana. Ta tare daya waigo ba ya daga mata hannu " bani 2hr sis " Da karfi tace " wht!!! "? Ta fito motar da sauri ta rufe Ta karaso gurinsu da gudu suka karasa fita parking space din tare Suna tafiya tana masa rada a kunne "bros wacece wannan kuma ina zamu "? Banza ya mata ta dakar masa kafada " haba bros mie yasa kake min haka ne "? Murmushi yayi " Rukaiya kin cika gulma dolene sai kisan wacece ita nima bansan wacece ba " " to kake binta mie zaka mata "? " in mukaje kya gani ai " Tsaki tayi ta leki fuskar fatima ta sake kallonshi. Shidai sai kokarin taushe dariyar dake son fito masa yake aranshi yana Allah ya shiryeki Rukaiya. Dakin da umma take fatima ta nufa dashi a bakin kofa ta tsaya ta nuna masa umma " gata can" ©Khadeeja Candy 🍭 [4/18, 11:01 AM] Khadija A Alkali: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 2⃣0⃣ Karasawa yayi kusa da ita Rukaiya na bayan shi hannu yasa ya dafa zuciyarta yasake dafa gefen wuyanta. Da sauri yakai hannunshi gurin hancinta Ya juya da dan gudu ya fita rukaiya ta rufa masa baya fatima dai sai kallosu take. Bai dadeba ya shigo da wasu likitoci 2 mace da namiji da nurses 3 nan da nan suka hau aikin dubata sai faman neman numfashinta suke. Su auna nan su auna can Can maccen ta kalleshi tace " I'm sorry lokaci yayi " hannunshi ya dora saman baki ya sauke ajiyar zuciya Fatima ta kalleshi ta kalleta " wai minene mie kuke nufi ne "? Dafa tayi tace " kiyi hakuri lokacinta yayi bazata tsaya ba " Fatima ta Girgirza kai " a a baki dai duba da kyau ba bazata mutuba ba yanzu ba inta mutu ni nayi yaya " haka ta nufi gurin umma ta kwanta jikinta hawaye suka fara bin fuskarsa tana Girgirza a hankali tace " umma tashi kinji ki tabbatar musu bda gaske bane jinki umma dan Allah koda hannunki ne ki motsa umma nice batula kinji umma nasan kina sona umma bazaki mutu yanzu ba "? Haka taketa surutanta kamar wata tababbeya tun tana Girgirza ta a hankali har takoma tanayi da karfi. Rikota yayi yace " kiyi hakuri ta riga ta rasu " tureshi tayi hawaye nabin fuskata kamar fanfo ta nunashi da yatsa " karka kara cemin ta rasu tunda bakai keda ranta ba ni ummata tana nan tare dani " juya tayi zata sake rika umma da sauri ya rikota zai fita dakin da ita. Aiko nan ta shiga kokuwa dashi duk ta cika dakin da ihu sai ummanta take kira har wasu nurses suka shigo jin irin kuwar da take duk wadda ya ganta yasan kokarin fita hayyacinta take. Rukaiya na tsaye gefe rike da baki sai kuka take ita da jidda,,,, ©Khadeeja Candy 🍭 [4/18, 11:51 AM] Khadija A Alkali: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 2⃣1⃣ Fita yayi da sauri bayan yasa wasu nurses sun rike masa ita. Bai dadeba ya shigo rike da allura hannunta ya kama ya soka mata ita. Tun kamin ya cire syringe tayi lagadam bachi yayi gaba da ita wani nurse ya mikawa syringe din sa hannu ya dauketa kamar wadda ya dakko jaririya da sauri sukace " sir we cn tke care of hr "? Ko kallonsu baiyiba yace " no need " ya fice Wani dakin ya nufa da ita ya sauketa saman gadon marasa lafiya Rukaiya na biye dashi kallonta kawai yayi yafice ita kuma taja kujera ta zauna tana hawaye. Yana fito yaga jidda tsaye bakin kofar tana kuka " itama ta mutu ko ni kadai na rage ko "? Wani irin tausayinta yaji ya kamashi dafata yayi yace " a a bata mutuba allurar bachi na mata dan ta samu natsuwa " kai ta daga mishi harta juya yace " ya sunnan yayarki "? Ta juyo cikin kuka tace " fatima ne sunanta " " ok tnks kibar kuka kinji " ba tace komai ba juya ta nufi gurinsu malam rufa'i da suka iso yanzu. Ya dade tsaye bakin kofar sannan ya tura kofar ya shiga. Kallon Rukaiya yayi dake kuka yace " sis kuka kikeyi "? " wlh yaya taban tausayi sosai " " a kawai tausayi kan but ya aka iya tunda haka Allah ya tsaro kowa bai wuce lokacin " " hakane bro Allah dai ysa mucika da imani " " amin sis shi muke fata " Wayarsa tayi ringing ya cirota a aljihu yayi picking " hello mummy " ya danyi shiru sannan yace " i knw mummy I'm rlly srry yanzu zaturo ta wlh wani dan abune ya tsayarda mu yanzu zata zo amman ni kan sai gobe " murmushi ya danyi yace " I'll mummy Tnks " ya kashe wayar Yana kallon Rukaiya tun kamin yayi magana tace " ni gaskiya bros bazani ba " fuskar shanu ya mata " to mai zakiyi a nan ba aiki kike ba ba jinya ba kawai ki kwana nan dan rainin hankali "? Nuna masa fatima tayi ya Girgirza kai yace " common sis wannan ba lokacin wasa bane tashi kije mummy na jiranki " tashi tayi kamar zata fasa kuka " to wazai kaini kuma bros kai mie zaka tsaya yi " " sis tana bukatar wadda zai zauna da ita ya kuma kwantar mata da hankali kije Dr. Ramla ta kaiki " kai kawai ta kada masa ta fice ©Khadeeja Candy 🍭 [9:54am, 8/5/2016] ☄DEENY☄SHOMAR☄: [4/19, 7:09 AM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 2⃣2⃣ Sai kusan asuba fatima ta farka tana bude ido ta fara ganin dishi2. Tayi kusan minti 5 ahaka sannan ta koma daidai, A hankali abun da ya faru ya fara dawo mata da sauri ta sauka saman gadon ta nufi kofa, Sai kuma ta tsaya ganin shi jingine jikin kofar yana kallonta. "ina zaki"? A hankali ya furta "ina umma na"? Rikata yayi ya zaunar ya zauna kusa da ita sannna yace "ummanki an tafi da ita", Idonta cike da hawaye ta kalleshi "da gaskene ta rasu"? Ido ya tsura mata kamar mai son gano wani abu. "kinsan duk mai rai mamaci ne kuma Allah baiyi wani dan wani ba Mutuwa kuma bata barin wani dan wani kowa lokacinsa yayi dole yaje koda ciwo koba ciwo" Fashewa tayi da kuka ta dora hannu samman kai "na shiga uku na lalace mie yake faruwa danine haka mie na aikata"? "subhanallahi kinyi kuskure kukar kikace sai bawa ya aikata wani abu Allah yake jarrabarsa, Karki kara wannan tunanin yadda Allah yaso haka yakeyi da bayinsa" kamar bataji mai yake fadiba sai fadin take "na shiga uku na lalace" hannunta ya riko yasa cikin nashi ya matse sosai har saida a kalleshi. Sannan ya juyo yayi facing dinta dan y tabbatar yanzu hankalinta yana gurinshi yace "Manzon Allah ( S. A. W ) yace baya daga cikinmu wadda idan masifa ta sameshi yake yaga tufafinsa yake marin fuskarsa ko ya aske gashin kansa ko yake kururuwa irinta jahiliya ma ana irin wadda kike sonyi yanxu mutun ya rika kiran ya banu ya lalace" Dayan hannunta tasa ta rufe baki tana hawaye,,,,, ©Khadeeja Candy 🍭 [4/19, 8:00 AM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 2⃣3⃣ Ajiyar zuciya ya sauke yace "ina son kisan mutuwa dokene dolene sai mun mutu saboda haka Allah ya kaddarto kuma fadinsa ne kowane rai sai ya dandani dacin mutuwa kuma shi da kansa cikin suratul rahman yake cewa dukan wandda yake bayn kasa kararaene fuskar ubangijiku mai girma da daukaka ita kadaice mai wanzuwa" Kasa juriwa tayi har saida kukan nata ya sake fitowa fili, Sake mata hannu yayi yace "fatima karki butulciwa Allah fa" cikin kuka tace "baka san yadda nake jiba shiyasa mahaifiya fa na rasa kuma ita kadai ta ragemin" "naji amman kiyi hakuri Allah haka yaga damar tsarawa" Haka yayita tausasa mata xuciya harta fara samun nutsuwa, Saida akayi kiran Asuba sannan ya nufi masallacin byan ya nuna mata toilet ya bata carpet. Bayan ya kare sallah kai tsaye dakin da take ya nufo, Tana ganinshi ta tashi tsaye hawaye wanke a fuskata tace "ni zanje gida na gode Allah ya saka maka da Alkhari" ratsawa tayi gefensa zata wuce da sauri ya rufe kofar yace "bari muje na kaiki" "a a kabarahi kawai na gode" bai kilata ba ya dauki wayarsa da carpet ya bude kofar yace "biyoni" ya fice Ba musu ta rufa masa baya Duk inda sukabi sai morning sir ake masa Suna kaiwa parking space ya nufi motarsa front seat ya bude mata ta shiga, Shikuma ya nufo driver set ya tada motar, Saida suka kai gate sannan ya tambaye umguwarsu ta fada masa, Yana hawa t-t ya fara gudu kamar tashin hankali. Cikin kankane lokaci suka iso mabera, Ita tayita masa kwatance har suka iso kofar gidan. Tana fitowa duk indon mutane sukayo kanta kowa kallon tausayi yake mata, Wani irin kuka ne yaxo mata dan ganin mazan da suka dandazo a kofar gidan ya kara tabbatar mata da gaskene umma ta rasu da gudu ta fada cikin gidan nan ma cike yake da mata., Tana kuka ta nufi dakinsu da sauri wasu mata suka riketa ana bata hakuri, Kokuwa ta shiga yi dasu "ku barni naga ummna dan Allah ku kyaleni" Wani dattijo ne daga cikin dattijawan unguwar ya shigo yace "kubarta ta ganta ana son iyalan mamaci su masa kallon karshe kamin akai shi makwancinsa" ba musu suka saketa gudu taka shiga dakin,,,,, ©Khadeeja Candy 🍭 [4/19, 8:34 AM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 2⃣4⃣ Kwance ta iskota cikin karaga an mata sutura kusa da ita fatima ta zauna tana hawaye tayi kusan minti 5 a haka sannan ya Girgirza kai tace "Allah mai iko yau umma gani kusa dake bakice dani komaiba da inna zauna kusa dake saikin tabani ko kinmin magana umma nayi burin kyautata miki amman Allah bai nufaba umma ke uwace ta gari kin doramu akan ta farki madaidaici kin mana tarbiya kin nuna mana addini Allah ga mahaifiya ta nan zata koma gareka Allah kayi mata rahama ka gafarta mata ka sadta da mala'ikon rahama".........kuka tayi sosai sannan ta dauko qur'ane ta karanta mata suratul yasin arrahaman da mulki , Bayan ta kare ta fito waje ta zauna tana kuka sai hakuri ake bata, Wasu maza suka shigo suka dauki gawar umma suka fito da ita fatima ta tashi tsaye tana kuka tana fadin " Alhamdulillah Allah na gode maka Allah duk yadda kayi daidai ne Allah kada ka dora min abunda bazan iya dauka ba Innaillahi wa'inna ilaihi raji'un" Suna kaiwa kofa da ita fatima ta fadi, Ruwa aka debo ruwa aka zuba mata bude ido tayi da sauri tana maiyarda numfashi matan dake zagaye da ita sai kuka suka, Tana ta zaune ta sake sumewa, Ruwa aka kara zuba mata amman shiru aka kara zuba mata nan ma shiru, Abunka da mata nan da nan sai gurin ya kware da ihu wasu na fadin ita mata mutu, Wata daga cikin matan ta fita waje ta kira maza da suka basu karasa wucewa ba gurin kai umma gidanta na gaskiya ba cikinsu harda Dr. Su hudu suka shigo shine na biyar ruwan dake kusa da ita ya dauka yacika baki dasu ya furza mata a fuska Shiru kakeji ko motsi batayi ba ballee batun farkawa. Hannunshi yakai gurin wuyan wuyanta ya dafa, Da sauri naga ya dauke yana fadin bata mutuba numfashita ne yayi nisa, Motarsa ya sakata matar malam rufa'i da wata makociyarsu suja shiga ya dauki hanyar asibiti,,,, ©Khadeeja Candy 🍭 [9:54am, 8/5/2016] ☄DEENY☄SHOMAR☄: [4/17, 4:13 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 1⃣4⃣ Washe gari fatima tun safe ta fara aikin ta koda 9 tayi ta kare komai, Bandaki ta fada bayan ta kare cin abinci tayi wanka. Koda ta fito umma da jidda sun kare shiryawa dan su tun dazu sukayi wanka Sai goma da rabi suka fito gidan. Suka kama hanyar t-t suna tafe suna fira. Har suka iso Tsayi sukayi har suka gaji basu samu mai kekenapep ba kasan cewar unguwar ba acika samun mai kekenapep ba dan bata da dadin shiga balle suda suke can ciki. Har kusan 11 rana sai kara fitowa take. Ganin abun bamai karewa bane yasa umma ta kalli fatima tace " batula kodai mu hau mai achanba ne "? " ae mana umma ni ai tun dazu naso nace haka naga bakyason shine shiyasa " Jidda tace " ae wai ita umma ala dole sai mai kekenapep ga masu achaba nata wuce wa " umma tace " to ai sai ki tare mana ya zamuyi " Umma na rufe baki jidda ta tare wasu masu achaba 2 " qanwata ina zamuje "? Fatima tace " Rabi'ah zaka kaimu gurin area kwamanda " dayan yace "ok to nawa zaku biya "? fatima tace " ku zaku fada ai " " to ku kawo 100 " " a a gaskiya 70 dai in zakuje haka ake kaimu " cewar fatima Dayan ya kalli dayan ya daga masa kai " ok to muje " .unma ta hau dayan fatima da jidda suka hau daya. Mai achaban da umma ta hau kana ganinshi kasan dan shaye2 ne dan wani mahaukacin gudu yake da ita kuma baya tsayawa jiran motoci saidai su2 jirashi, Fatima gabanta sai faduwa yake ganin irin isan da yayi musu akan gudun da yake da umma gashi bata gwane hauwan achaba ba Dan kwantowa tayi kusa da kunne mai achaba tace " dan Allah dayi sauri mu cinma wancan mai achaba ya cika gudu " kai ya daga mata yasa giya Nan da nan ya cin musu horn yayi sannan ya shiga daga mishi hannu Ala'mar ya tsaya. Kai ya daga mishi yaki ya tsaya ganin ya kawo rawon din Ali-akilu, ©Khadeeja Candy 🍭 [4/17, 5:41 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 1⃣5⃣ Da gudu ya shigo rawun din yana kawowa wani mai mota na kawowa kowanesu da gudu "k'iyyyyyyyyy" kakeji kowa wannensu nason yin Brake amman ina saida mai afkuwa ta afku Wani mugun kaura sukayi sama mai achaba yayi ya dawo ya bugu da rawun din umma ta fadi tsakiyar t-t mashin din ya tausheta. Bayan mugun bugun da motar ta mata Nan da nan sai jini mai motar na ganin haka ya kada motarsa yayi gaba dan kawai rashin tsoron Allah da tausayi. Fatima tun kamin mai achabansu ya tsaya ta diro saman babur din ta nufi gurin umma da gudu tana " wayyo Allah na nashiga uku ummaaa " tana kiranta tana kokuwar daga mashin din, Wasu maza sukazo da gudu suka daga mashindin dayan ya rike fatima ikar karfinshi ganin yadda take jijjigar umma Mutane sukayo musu kwaaa kan kace kabo gurin ya cika da jama 'ah wasu kuma suka nufi gurin da mai achaba ya fadi masu aikin daukar pic suka shigayi kowa sai fadin yake basuda rai dan daga umma har mai achaba babu mai motsi cikinsu kowannensu cikin jini wani dattijo mai tausayi yasa akasa masa umma a mota ya nufi asibiti da ita nan shima wani ya dauki mai achaba shima ya nufi asibiti jidda da fatima kuma aka sasu wata motar daker fatima ta shiga saboda kukan da take tana kiran " ummana Allah ummana " AHMAD SPECIAL HOSPITAL aka nufa da ita koda su fatima suka iso an shiga da ita emergency room Bakin kofar sukayi tsaye fatima sai kuka take kamar ranta zai fita ita da jidda ©Khadeeja Candy 🍭 [4/17, 6:41 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 1⃣6⃣ Sunyi kusan 2hr a gurin sannan Dr ya fito hannayenshi duk jini da sauri fatima da mutunen suka taso suna tambayarshi hannu ya daga musu ya nufi wani dakin. Jidda da mutumen suka koma suka zauna fatima kan kasa zama tayi sai kuka takeyi, Nan ma ya dade sannan ya fito da alama toilet ne dan a tsaftace ya fito ba kamar yadda ya shigaba. " Waye yafi kusanci da ita "? Cewar Dr fatima cikin kuka tace " nice likita ta mutune "? Kai ya girgixa mata yace " muje office yanzu " yana kaiwa nan ya juya suka rufa masa baya., Suna shiga ya nuna musu gurin zama bayan sun zauna shima ya zauna. A natse na kallesu yace " wannan matar da kuka kawo ta samu karaya kuma ta rasa jini da yawa bayan haka ma zuciyarta ta samu matsala dan na bincika tana da hawan jini " fatima ba tace komai ba banda ido ta sakarwa dr hawaye nabin fuskata kamar fanfo Dattijon ne keta salati shima idonshi cike da kwalla Can ya kalli Dr yace " yanxu dr mie abunyi "? Takard ya dauko yayi dan rubuce2 sa ya mikawa dattijon yace " wadannnan abubuwan zaku siya sai mumata aikin jini kuma in akwai dan uwanta dazai iya badawa shikenan in kuma ba haka ba dolene sai kun siya shima kuma karku bata lokaci matukar kuna son ranta " Sai a lokacin fatima tayi magana cikin muryar kuka " dan Allah dr dan Annabi ka taimaka mana wlh3 bamuda kowa sai Allah babu inda zamu samu" dr yace " srri young lady bakin taimakon da zan iya muku kenan " Fatima ta sauka saman kujerar ta durkusa da kafafuwanta ta hade hannayenta guri daya tace " bamuda kowa dan Allah ka taimaka mana dan rufin asirin da Allah ya maka kaima ka rufa mana ka taimaka mana " tashi yayi ya dauki wasu takardu da laptop dinsa ya fice Nan fatima ta fadi kwance tana kuka " wannan wane irin lamari ne haka danasan da wannan kaddarar umma daban jaki munzo ba " dattijo ya shiga lallasarta yana bata hakuri Cikin daga murya tace " Allah bamuda gata sai naka bamuda kowa sai kai Allah Allah ga umma ta nan kaceci rayuwarta Allah Kaina rike abun dogaro Allah ka isar min Allah ......" nan kuka yaci karfinta jidda ta shigo da gudu itama tana kukan tace " batula umma ta rasu ne "? Bata iya mata magana ba sai kuka take dattijon ne yace " a a an rubuta muku maganine kuma bata da kudi " ©Khadeeja Candy 🍭 [4/17, 7:32 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 1⃣7⃣ Kuka sosai kukayi ita da jidda sannan suka taso suka fito. Tare da dattijon na ya cire dubu biu da dari takwas yabawa fatima yace ta kara Godiya sosai fatima ta masa da addu'ah sannan yayi musu fatan samun sauki ya wuce Nan fatima ta kalli jidda tace " ki zauna na ni bari naje gida ko Allah zaisa na samu wani abun " " toh Allah ya tsare yasa a samu " fatima tace " amin " ta fice Tana shigowa unguwar su bata shiga gidaba saida ta shiga gidan malam rufa'i ta sanar masa sannan ta shigo gida. Tufafi kawai ta chanja ta dauki hanyar gidan hajiya shafa zuciyarta sai bugawa take har ta isa duk da wata zuciyar nace mata kartaje., Tana shiga cikin sa ah ta tararda hajiya shafa zaune parlor ita da umar Cikin ladabi ta gaisheta hajiya bata amsaba saima jan tsaki da tayi tace " sai yanzu kikaga damar zuwa aikin cikin dare hala dacan kin dauka in baki zoba bikunki zanje "? Fatima ta kalleta cikin fuskar tausayi tace " ba aiki nazo yiba " " to mie kikazo yi "? Cikin sanyayyar murya tace " kudin aikina nazo kibani " Hararar ta umar yayi " amman yarinyar nan bakida kunya baki cika wata ba za a baki kudin aikinki tashi kibar gidan nan yar matsiyata kawai " Nan ta fashe musu da kuka " dan Allah dan Annabi ku bani hakkina wlh ummana tayi hadari harta karye likita yace mu kawo kudi dan Allah hajiya ki bani hakkina " Shiru hajiya shafa tayi harna kusan minti 30 fatima sai kuka takeyi sannan ta bude pose dinta ta jefawa fatima dubu 3 " gashi nan tashi kibar min gida " da sauri fatima ta dauki kudin ta tashi ta har takai bakin kofa ta juyo kamar tace ina Anty Kdeey kuma ta juya ta fice. Direct asibitin ta nufo dan achaba na sauketa ta nufi dakin dr tana sauri. Da sallama ta shiga cikin ladabi ta gaisheshi bayan ya amsa ta mika masa dubu biyar da yan chanji. ©Khadeeja Candy 🍭 [4/17, 7:52 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 1⃣8⃣ Kallon raini ya mata " wannan ai akin banza ne wadannan kudin zasu isa aiki mata aiki nan fa pravate hospital ne ba govt ba kuma ko govt ai bazasu isa sayin koda siyen maganiba balle nan da ko gadon data kwanta saikin biya " Dukawa tayi har kasa " dan Allah dr ka taimaka wlh shikenan abunda na samo"? Dr yace " magana ta gaskiya in kina son ceton rayuwar baiwar Allah nan to kije jinemo kudin daya dace tun lokaci bai kure mikiba tun dazu fa kuka kawo matar nan gashi yanzu 8:30pm ni banida wani taimako da zan iya miki " yana kaiwa nan ya tashi ya fice Tashi itama tayi ta nufo dakin da umma take, Tana shiga ta tararda jidda zaune kusa da ita kallonta jidda tayi " batula an samo kudin "? Kai kawai ta girgixa mata ta nufi gurin umma dake kwance tana bachi. Sai numfashi umma take guda2 a hankali fatima takai hannu ta shafa fuskar umma wasu siraran hawaye suka zubo mata. Da sauri ta juya ta fice Ha rabar asibitin ta fito tana shawaye wani kololon bakin ciki na mata yawo a zuciya intayi nan tayi can sai shafar hannayenta take ana girgixa kai kamar wata tababbeya. Nan kuka ya fara cin karfinta Watsawa tayi da gudu parking space inda babu komai sai motoci da mai gadi. Wani karfe ta rungume ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya...,,,, ©Khadeeja Candy 🍭 [9:54am, 8/5/2016] ☄DEENY☄SHOMAR☄: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 2⃣5⃣ Yana kaiwa ko parking din kirki baiyiba ya fito da ita, Ya nufi emergency nurses sai kokarin karbarta suke amman bai kula suba. ICU ya shiga da ita yana dorata saman gado ya hanyo uksijin yasa mata. Ya shiga saita konfuta da numfashita, Daidai nan Dr. Ramla ta shigo tare da wata Dr tana kallonshi ta gane yana cikin tashin hankali taimaka mishi suka shigayi. Har suka fara samo numfashinta ajiyar zuciya ya sauke yace "ohh god Alhamdulillah" kallonshi kawai Dr. Ramla tayi ta cigaba da abunda take har numfashinta ya daidaita, Dr. Dake tare da Ramla na ganin haka ta juya ta fice, Ramla ma ta rufa mata baya. har takai kofa sai kuma ta juyo tana kallon Dr da yaja kujera ya zauna yana kallon Fatima, A hankali yakai hannu ya shafa kanta yan busar da iskar baakinshi, "wh is she i hv nvr seen hr b4?" zabura Dr yayi dan a zatonsa ta fice Tashi yayi yasa hannayensa Aljihu yana daga kafadun yace "she's my cousin" bai tsaya jiran mai zata sake ce mishi ba ya fice,,, Srry 4 th shrt typing am busy ©Khadeeja Candy 🍭 [9:54am, 8/5/2016] ☄DEENY☄SHOMAR☄: [4/23, 5:51 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA ◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 3⃣0⃣ Da sauri ta janye hannunta ta tsareshi da ido, shima idon ya tsura mata yace "zakici abinci?" Dauke kanta tayi ta mayar gurin window, Plate kawai Dr ya dauko ya zuba abincin kus-kusne da Sauce din kaje, Koma yayi saman gadon ya zauna saida yakai 1 spoon bakinshi sannan ya sake debowa zaikai mata ta kawarda fuska. Murmushi yayi yace "bakya son kus-kusne?" ko kallonshi bata yiba balle ta bashi amsa, Aje abinci yayi ya dauko cup ya zuba mata kunun-aya a hankali ya kai mata a baki kadan tasha ta kawarda fuska, Nan ya tashi ya fita bai dadeba ya shigo rike da gwangon madara fasashe hannunshi yasa ya matse mata fuska saida tayi kara sannan ya shiga zuba mata madarar Saida ta shaye sannan ya dire gwango Kallon tsoro ta masa ya sakar mata murmushi "srry Fatima nasan inba haka nayi miki ba bazaki shaba" batace masa komaiba sai lasar baki takeyi lekon fuskarta yayi yace "akwai dadi ko akaro?" da sauri ta dauke kanta murmushi kawai yayi ya shiga hada mata drip, Yana cikin sa mata akayi knocked yayi kamar baijiba saida akayi sau kusan hudu sannan yace "yes" Turo kofar akayi aka shigo wata nurse ce sanye da karamin hijab dinta Cikin ladabi ta mika mishi alurar dake hannunta saida ya kare abunda yake sannan ya karbi alurar ya risino ya rika hannun Fatima tada tsurawa nurse din ido kamar bata taba ganin mutane ba, Alurar na shiga hannunta ta fara bachi saida ya murza mata hannun ya gyara sannan ya kwantarda ita, Yana kokarin mikawa nurse din syringe yace "hafsa ina kika santa?" saida ta karba sannan tace "gidansu wata friend dinta take ga aiki", "ga aiki kamar ya?" "tana wanke2 da shara da kuma goge2 da wanki da sauran ayukan gida haka ana biyanta every month" busarda iskar bakinsa yayi yanuna mata kayan dake gurin "ok ga abincin nan ki bawa masu moping kulolin kisa min a mota" ya karasa maganar tare da mika mata key din motar, Tana karba ta kwashi kololin ta fice,,,, ©Khadeeja Candy 🍭 [4/24, 6:53 AM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA ◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 3⃣1⃣ Awar Fatima 27 tana bachi duk bayan 1hr-2hr sai Dr ya shigo ya dubata, Sai kusan a'zahar yayi mata wata alurar, Kujara yaja ya zauna ya kafa mata ido, Ba'ayi 1hr a hankali ta fara motsa manunin hannunta sannan ta motsa kafarta Tashi yayi ya matsa kusa ita, Ya bude dan karamin akwatin dake hannunshi ya fiddo wani farin kyale kamar cotton. Ya dora mata saman goshi, Ajiyar zuciya ta sauke ta motsa hannunta na dama a hankali ta bude ido., Dishi2 ta fara gani haka tabi dakin da kallo, har ta fara gani daidai hannu Dr yasa ya dauke kyale, goshinta cike da raba kamar an yayyafa mata ruwa, Juyowa tayi ta kalleshi "sannu Fatima" kai ta daga mishi tana juyarda fuskarta gurin window, Aunata dr ya shigayi babu inda bai dubaba saida da ya kare. Naga yaja kujera ya zaune yana fadin "Alhamdulillah" Ta dade tana kallon window can kuma kamar wadda aka tsokara, Ta zabura ta tashi zaune da sauri tana kallon Dr. "lafiya Fatima mie akayi?" bata bashi amsa ba ta shiga kokarin saukowa daga kan gadon, Tasowa yayi ya zauner da ita yana mata magana "ki kwanta ki huta tukuna in kuma wani abu kike so fada min zan nemo miki"? Fashewa tayi da kuka "umma na gida zanje" "owk zan kije gida amman ba yanzu ba ki saurara kijin ki ya kara saki kinji"? "a'a ni gida zani jidda zan gani wama ya kawani asibitin nan"? Tashi yayi yana fadin "ina zuwa" Ido ta bishi dashi harya ya fice, ©Khadeeja Candy 🍭 [4/24, 8:31 AM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA ◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 3⃣2⃣ Bai dade da fita ba matar malam rufa'i ta shigo, Fatima na ganinta ta tashi tsaye tana fadin "inna ganbo" ta zauna saman gadon fuskarta dauke da damuwa tace "Fatima kin farka"? "ae inna ganbo waya kawo ni asibiti"? "suma kikayi sai wannan likitan ya kawoki tun shekaran jiya" Idonta suka ciko da kwanla tace "umma ta rasu inna ganbo ta tafi ta barmu" rungume tayi "Fatima kiyi hakuri dukan mai rai mamacine kuma Allah baiyi wani dan waniba duk yadda yaso haka take kasan cewa" kuka Fatima ta fashe dashi ba sassauci, Inna ganbo ta dafa tace "kiyi hakuri Fatima kibar mata kuka addu'ah take so kinga yau ma ake rufe kwana uku kibar mata kuka dan Allah" Kamar karta furta haka wani irin sabon kuka yazo mata, Inna ganbo tayi ta lallasar ta har ta gaji bata daina ba, Suna haka Dr ya shigo rike da ledodi wata nurse na rike basket mai dauke da kuloli. Saida ya sauke kayan ya karbi na hannun nurse din sannan ta fice, Saman kujera ya zaune yana kallon inna ganbo dake masa sannu da zuwa yace "yauwa inna mie aka yi mata kuma"? "wlh kukan umma ne takeyi kuma ina fada mata ba kyau ta daina amman ko saurarata batayi" Ajiyar zuciya ya sauke ya dauki dayar ledar da kula ya mika mata "karbi wannan inna barni da ita kawai" karba tayi fuskarta dauke da damuwa ta fice, Tasowa yayi ya zauna saman gadon ya dan leki fuskarta, A hankali ya kira sunanta "Fatima" ko kallonshi batayi sai kuka take, "haba Fatima sai kace ba musulma ba wannan kukan da kike ba magani bane fa itafa addu'ah take so kuma wannan jarabawa ce kuma Allah yana cewa zamu jarrabeku da yunwa da tawayar dukiyoyi da rayuka kayi bushara ga masu hakuri wadanda inda matsifa ta samesu sai suce innaillahi wa'inna ilaihi raji'un" Cikin kuka tace "Malam kabarni nayi kuka inada hujar yin kuka uwa na rasa fa" "nasan kin rasa mahaifiya amman ai hakuri akeyi kuma dan ba dan Allah baya sonki yayi miki haka ba Annabi ( S. A. W ) koda ya tashi baisan mahaifansa ba kuma kinsa Allah yafi sonshi da kowa duniya kiyi hakuri dan Fatima kibar kukan nan" Kallonshi tayi da jajayen idanuwanta tace "naji na daina na gode ni gida zanje" "owk toh ga abinci nan kici inji mummy na" "mummy ka"? Kai ya daga mata tace "inna ta sanni"? "tun lokacin da abun ya fara ta samu labarinki kuma kannena ma suna gaidaki dan sunzo dubaki kina bachi" share hawayen dake zubo mata tayi tace "waye kai"? Ido ya dan tsura mata sannan yace "sunana Dr Ahmad Salisu isa" Kai ta daga mishi ta sauka saman gadon. Da sauri yace "ina zaki ga abinci kici tukuna na kaiki gida" "a'a ni gida zanje" zaiyi magana Dr Ramla ta turo kofa ta'ta shigo fuskarta dauke da murmushi tace "kace kana nan gurin cousin dinka"? Hade fuska yayi yace "wht do u wnt"? Hannayeta tasa cikin Aljihun rigarta ta daga kafada "nting juz ina son ganin jikinta ne" ta dafa Fatima da hannu daya "yaya jikinki my dear"? Cikin sanyin murya tace "naji sauki" murmushi tayi ta kalli Dr. Ahmad tace "gud" ta fice, Tana fita Dr ya zaunar da Fatima ya shiga bata abincin,,,, I REALLY NEED YOUR PRAYERS FRIENDS 😭πŸ˜ͺ ©Khadeeja Candy 🍭 [9:54am, 8/5/2016] ☄DEENY☄SHOMAR☄: [4/21, 12:24 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 2⃣6⃣ Yana fitowa ya nufi office dinsa. Bai karasa kaiwa ba Rukaiya ta kwala masa kira "bro's bro's" Juyowa yayi ya kalleta "ohh sis mie kika dawo yi kuma"? Saida ta karaso kusa kusa dashi sannan tace "mummy ce tace nazo nagani ko lafiya tayita kiran wayarka kashe kuma bakaje gida ba da safe kuma na fada mata labarin yarinyar shine tace kodai wani abun ne ya faru"? Shiru yayi ya tsura mata ido. har nazir ya karaso kusa dasu cikin ladabi yace "morng bro's" kalloshi Dr. Yayi yace "haka kawai zaku taso ku biyoni kamar wani karamin yaro mie haka dan Allah"? Nazir ya nuna rukaiya "ni fa mummy ce kawai tace na kawota ita ta matsa sai tazo duk ta tadama mummy hankali" Harara Dr ya watsa mata ya shige office dinshi. Suka rufa masa baya yana zaunawa ya shiga danna2 telephone banji mie akace mishi ba nadai yayi murmushi yace "zo office dina yanzu" Yana aje telephone din ya jayo wata farar takarda ya shiga rubuce2 , Sai a lokacin rukaiya ta zauna tana leken abunda yake rubutawa "bro's wai har yanzu bata farka ba"? Tsayarda rubutun yayi ya kalli nazir dake dannar masa computer yace "in zakaje gida ka wuce da ita karka kuskura kabarta" batare daya kalleshi ba yace "owk bro's" turo baki rukaiya tayi kamar ta fasa kuka "ni gaskiya bro's sai ka tashi zamuje tare" Daidai nan Dr. Ramla ta shigo fuskarta dauke da murmushi tace "gani sir" rukaiya da nazir suka gaisheta Takarda dayake rubutu ya miko mata "wannan alurorin nake son ki nemo kiyi mata" Ya sake dauko wsu files ya mika mata tare documents "duk aikina na yau ke zakiyi akwai inda xani kuma zan kashe wayana so koma mienene ke za anema" ©Khadeeja Candy 🍭 [4/21, 12:59 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 2⃣7⃣ Hannu tasa ta karba "owk sir sai ka dawo" saida tayiwa rukaiya rankwashi sannan ta fice tana dariya, Daukar keys dinsa yayi ya kashe laptop dinsa ya kalli nazir yace "kai sarkin browsing inka kare ka kashe min computer ta'ta kuma ka fadawa mummy ina nan kalau aikine ya tsayarda ni kuma ka rufe min office kabawa Dr Ramla key" "owk" kawai nazir kece mashi hankalinshi na kan computer Dr ya kalli rukaiya "kuma karki yarda ya barki nan Parrot kawai" Da sauri ta tashi "bro's ina zuwa plz" kai kawai ya girgixa yana murmushi yafice ICU ya nufa saida ya shiga ya duba Fatima da tafiyar munfashinta sannan ya nufo gurinsu matar malam Rufa'i suna ganinshi suka tashi Cikin natsuwa ya shiga musu magana "ku kwantarda hankalinku babu wata damuwa numfashinta ya dawo yanxu tana bachi ne" Godiya suka yiwa Allah Dr. Yyi murmushi yace "ni zan koma gidansu in kunada bukata sai mu wuce tare dan akwai wadda zasu kula da ita" Matar dake tare da matar malam rufa'i tace "ae nima gidan zani inyaso saina dawo tunda ba'abarin marar lafiya shi kadai" Tare suka nufi parking space suka shiga mota harda matar malam Rufa'i suka dauki hanyar mabera, Basu dade da fita ba Rukaiya ta fito ita da nazir suka rufe office din nazir ya mika mata keys din yan fadin "keje ki kai mata ni ina parking space" Karbar key din tayi ta nufi office din Dr Ramla Tana shiga ta mika mata keys din, Ta juyo zata fice Dr. Ramla tace "Rukaiya ya dai naga kin bata rai haka"? "ba komai mudai mun tafi gida" bata jira mie zata ceba ta fice ©Khadeeja Candy 🍭 [4/21, 6:48 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 2⃣8⃣ Gurin karbar gaisuwar Dr ya yini duk wasu maganganu da ake kan Fatima da umma ya kashe kunne yana sauraro, Sai kusan biyar saura yayi musu sallama ya taso. A gaggauce ya karaso gida part dinsa ya fara wuce yayi wanka ya shirya cikin jean n golden T-shirt ya feshe jikinshi da turare ya nufo part din mummy Da dan gudu ya shigo parlor yana sallama. Mummy dake zaune saman kujera ta amsa masa "amin wa'alaikasalam Dr sai yanzu"? Zaunawa kusa da ita yana murmushi yace "ae mummy gurin gaisuwa naje sai yanzu ya dawo mummy a zuba min abincin mutun biu a kula" Ya karasa maganar yana kallon agoggon hannushi "ba nan zaka ciba kuma"? "ae mummy ina busy ne" mummy ta tashi tana fadin "ina yarinyar da Rukaiya take fada min"? "itace ma mummy nake yiwa sauri, dan alurar danasa a mata lokacinta ya kare zata iya tashi ko wane lokaci" "wai nikan Dr wacece"? "mummy zakiji komai a hada min avincin kawai yanzu plz" Dinning area Mummy ta nufa cikin kankane lokacin ta hada mishi komai da tasan yana bukata. Ta mika mishi da sauri ya karba ya nufi kofa "Dr"? Kiran da Mummy ta mishi yasa ya juyo "na'am Mummy" "dan Allah ka kunna wayarka bana son kashewar nan da kake wlh" "owk I'll Mummy amana addu'ah" murmushi Mummy tayi tace "may Allah blss n protect u" saida yace "Amin" sannan ya fice Asibitin ya nufo wata nurse na ganinshi ta taso da sauri ta karbar masa kulolin daya riko tana "evening sir" "evening joy hw was my Patients"? Cikin sauri yake tafiyar yana tambayarta "we ar oll try our bst to tke gud care of thm sir" "gud any Hassle or Mdfction"? "no sir" ( haka al'adarshi take duk lokacin da yashigo sai yayi irin waddannan tambayoyi ) Daidai nan Dr. Ramla ta iso fuskarta dauke da murmushi ta karbi kayan dake hannun joy ta kalli Dr. "welcome sir" murmushi shima ya mayar mata "thank u my Dr." ya kalli joy yace "u may go" "thank u sir" ta wuce da sauri ©Khadeeja Candy 🍭 [4/21, 7:53 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 2⃣9⃣ Saida ta wuce sannan y kalli Dr. Ramla yace "yaya jikin sis na hop u tke gud care of her"? " yes sir tama farka tun dazu saida taki tayi magana kuma taki tasha tea dana hada mata taki yin komai sir sai kuka take kuma tana kalle2" Dr ya cigaba da tafiya yana fadin "wht d u min"? "all wht I undrstd sir somting is wrng wit hr" Daidai nan Dr. Ya tura kofar dakin ya shiga tare da Ramla Zaune ya tararda ita bakinta duk ya bushe idonta sunyi wani fari sai hadiyar yawu take Kujera yaja ya zauna a hankali yace "Fatima" da sauri ta kalleshi ya mata murmushi yace "sannu" kai ta daga mishi ta cigaba da wasa da hannayenta ido ya dan tsura mata sannan yakai hannu ya taba gefen kumatunta ya kalli Dr. Ramla yace "jikinta yayi sanyi sosai" Ramla ta dan duko tana kallonta tace "Fatima akwai inda yake miki ciwo"? Ido Fatima ta tsura mata kamar bata taba ganin taba sannan ta komar dasu gurin Dr tana mishi irin kallon da tayiwa Ramla Ajiyar zuciya Dr ya sauke yace "u ar rght somting is wrong" "wannan shine abunda nake fada maka i thnk she's lost hr mmry" Dr yace "no komau tana yana nan tunanine yayi mata nisa but ba wata matsala bace dana mata alura tayi bachi ta farka zata koma normal" Ramla zatayi magana dr daya duba umma ya turo kofa ya shigo yana fdin "excuse me sir wannan file din dole saikai da kanka zakasa hannu" Kallon Fatima yayi da dan mamaki yace "kema kuma bakida lafiyar ne aiki" Da sauri Dr. Ya karbi file din ya fara sign Ramla ta kalleshi "kasan tane"? Nan kwshe duk abunda ya faru ya fada mata, Ido ta tsare Dr dasu dake sign har ya gama ya mika mishi yana karba ya fice Sai a lokacin ya kalli Ramla data wani hade fuska zuciyarta sai bugawa take Suna hada ido ta dauki kai ta sauke masa abincin shi ta fice Ajiyar zuciya Dr ya sauke dasai da Fatima ta kalleshi, Hannunta yaja ya rike ya sarka mata murmushi ©Khadeeja Candy 🍭 [9:54am, 8/5/2016] ☄DEENY☄SHOMAR☄: [4/29, 5:37 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA ◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 3⃣3⃣ Kadan ta ci koshi dan ya tisata gaba ne, Bai tsaya ci ya tashi suka nufi parking space sauki Fatima take sosai hakan yasa shi shima yin saurin da kansa ya bude mata front seat ta zauna sannan ya shiga driver set yaja motar suka fice cikin sauri, Tunda suka shiga motar bai ce da ita uffan ba Sai dai duk bayan 2min sai ya kalleta ita kuma kanta na kasa sai faman sharar kwalla take, Can naga ya rage gudun da yake ya kalleta a hankali ya kira sunanta "Fatima"! "na'am" cikin muryar kuka ta amsa ba tare data kalleshi ba Handkerchief ya mika mata "karbi ki share hawayenki" karba tayi ta shiga share hawayen Parking yayi ya kalleta sikin sanyayyar murya ya shiga mata magana "Fatima dan Allah kiyi hakuri kibar kuka ina son kiyi imani kibarwa Allah komai shida ya kaddara miki Kamin fa ya sameki ya samu dubu irinki bayanki kuma za ayiwa dubu dan Allah kiyi hakuri wlh bana son kukan nan kinji"? Kai kawai ta daga mishi tare da Kallon motocin dake wuce wa ganin hak yasa ya tada motar ya cigaba da tafiya, Umma ta samu addu'ah sosai kowa sai yabon halinta yake yana mata fatan samun aljana, Ranar Fatima tasha kuka ita da jidda kamar ransu zai fita bama kamar Fatima da tafi kowa shakuwa da Umma, Haka ta wuni kuka tun ana bata hakuri har suka saka mata ido, Bayan magariba Fatima na zaune daki saman carpet tana jan car'bi jidda na gefenta aka shigo da buhun shinkafa 3 da jarkar mangida da manza da sinadaran miya da su doya da sauran tarkacen kayan abinci, Ita bin masu sauke kayan kawai take da ido. Har suka kare, Suna fita inna ganbo ta shigo da sallama Fatima ta amsa mata saida ta zauna kusa da ita sannan ta aje mata bandir din yan dari2-2 guda 2 tace "gashi inji Dr yace ayi cefane wa yancan kayan kuma shine ya aiko" kallon daya Fatima tayiwa kudi ta dauke kai tace "Allah ya saka mishi da alkhari" "amin yana waje yace yana son ganinki" ciki2 tace "tohm" inna ganbo ta yashi ta fice,,, ©Khadeeja Candy [4/29, 9:50 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA ◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 3⃣4⃣ Tsaye ta tararda shi jikin mota yasa hannayensa cikin aljihu kansa a kasa, "Assalamu Alaikum" dago kansa yayi ya kalleta "amin wa'alaikissalam Fatima?" "na'am" "ya hakuri?" "da godiya munga abu mun gode jazakallahu kharan" "amin ai babu komai yiwa kaine abunda yasa nace a kiraki Fatima ina son Da Allah kibarwa Allah komai shi zai miki magani badan baya sonki ya kaddaro miki ba haka lamarin duniya yake sai hakuri wani na cikin dadi wani akasin haka kuma fa kinga ita umma fa addu'ah kawai take so" Haka yayita tausasa mata zuciya da maganganu masu sanyi, Har saida ranta ya dan saki sannan yay8 mata sallama ya nufo gida Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya shigo gidan, Sallamarsa ma ciki2 yayita Mummy da Rukaiya suka amsa mashi, Saman kujera ya zauna yana maida numfashi kallo daya mummy tayi masa ta gane baya cikin walwala, Kallon Rukaiya mummy tayi tace "tashi ki dauko masa ruwa" tashi Rukaiya tayi nufi kitchen. Bata dade ba ta fito rike da gorar ruwa da cup da drink Da kanta ta zuba mishi ta bashi, Kadan ya sha ya jingina da kujerar ya lumshe ido, "bro's lafiya dai?" Rukaiya take tambayarsa "lafiya kalau sis aiki ne ya mun yawa" Mummy tace "a a Dr nasan ka wannan ba aiki bane dn't lie 2 me" da gowa yayi ya kalleta "wlh mummy yarinyar nan da Rukaiya take fada miki ce take raina" "take ranka kamar ya"? "mummy yarinyarce ta bani tausayi sosai wlh gurin gaisuwar naji ance mahaifinta ya rasu gashi yanzu kuma mahaifiyarta ta rasu kuma yarinyar bata wuce 16-17yrs ba" Mummy tace "ayyah Allah ya musu rahama haka Allah yake abunsa sai hakuri amman kan da tausayi gaskiya" Rukaiya maso kusa dashi "bro's wai wacece wannan yarinyar"? Yayi kamar bai jitaba ya dauki keys dinshi dake hannun kujera ya tashi yana fadin "haka ne mummy duk yadda Allah yaso haka yake kasancewa" "haka ne amman dan Allah Dr ka sake ranka bana son yanayin nan naka Dr na damuwa" Murmushi ya danyi "insha Allah mummy saida safe" Mummy tace "da wuri zaka kwanta haka"? "ae mummy na gajine inason indan huta ne" "ok tohm Allah ya tashe mu lafiya" yana kokari juyawa Rukaiya tace "bro's bazaka fada min ba"? Buge mata baki mummy tayi shidai bai ce da ita komai ba ya fice, . ©Khadeeja Candy [4/29, 11:36 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA ◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 3⃣5⃣ Washe gari da wuri Dr ya fito gida dan yanada aiki da yawa a office, Gashi kuma yana son ganin Fatima dan ya kwana da tunaninta, Kai tsaye hanyar da zata kaishi gidansu ya dauka, Cikin yan mintuna sai gashi mabera, Daidai kofar gidan yayi farkin tare da yin horn wani yaro ne ya fito da gudu ya nufo gurin motar yana fadin "wa ake nema"? Sauke glass din motar yayi yace "jeka cikin gida kace ana sallama da Fatima" yaron yace "tana asibiti" "gurin mie?" "Bata da lafiya shine aka kaita tun jiya ma" "ok" kawai yace ya fisgi motarsa gudu ya shiga yi sosai, Cikin kankane lokaci ya iso asibitin Ko parking kin din kirki baiyi ba ya nufo cikin asibitin, Duk inda ya biyo gaisheshi ake har iso gurin wani tebur da nurses ke zaune, Suna ganinshi suka tashi tsaye suna masa "morning sir" bai amsa ba yace "an kawo wata marar lafiya jiya mai suna fatima a nan"? Wata daga cikin nurse din ta kalleshi tace "ae sir Dr Ramla ta karbeta " Dr yace "wane daki take"? "tana Anas room" kai ya daga mata yana kokarin juya wa yaji muryar Ramla "cool down sir yar'uwar tana bachi tun jiya nake kula da ita" juyowa yayi ya kalleta "mie yake damunta" saida ta karaso kusa dashi suka jera suna tafiya sannan tace "fever ne but na mata alura ba wata matsala yanzu" Ajiyar zuciya ya sauke yace "amman mie yasa baki kiraniba"? Kallonshi tayi tana murmushi "ko ni zan iya kula da ita sir dan nasan cousin din ka ce" hade fuska yayi yace "baki bani amsa taba" "ban kiraba saboda munyi waya da Rukaiya ta fada min kana bukatar hutu kuma kana cikin damuwa kuma kasan kace nice zanyi duk aiki daya kamata kayi" Busar da iskar bakinshi yayi ya nufi office dishi,,,,, ©Khadeeja Candy [9:54am, 8/5/2016] ☄DEENY☄SHOMAR☄: [4/30, 8:21 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA ◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 3⃣6⃣ Yana shiga ya cire lap coat dinshi ya aje wasu file dake gaban tebur dinshi ya dauka yana dubawa, Saida yayi marking a wasu2 kuma yayi sign. Saman kujera ya zauna yana sauke ajiyar zuciya, Can kuma ya lumshe ido yana lilo da kujera Fatima kawai ke masa yawo cikin kwakwalwashi ya dade a haka ya ajiyar zuciya yake saukewa, Can kuma ya bude ido kansa jingine jikin kujerar ya kalli wasu file din dabai taba ba ji yayi bazai iya aikin ba wayarsa ya ciro ya dannan number Salima ringing 1 ta dauka "hello sir d u need anytin"? "yes zo office" haka kawai yace ya kashe wayar, Ko minti 3 bai yiba da aje wayar sai gata tana knocking "gyara zamansa yayi yace "yes" cikin ladabi ta shigo "am here sir" nuna mata files din yayi "ga files nan aikin dake ciki nake son kiyi ga computer can ki duba gefenta zakiga documents kiyi copy a computer in kika kare kikaiwa Dr Alex" kai ta daga mishi jikinta ta rawa "owk" tashi yayi yana fadin "gud kuma kiyi aiki mai kyau dan Abuja za wuce dasu" "owk sir insha Allah baza'asamu matsala ba" kai kawai ya daga mata ya fice. ita kuma ta shiga kwasar files din dake saman tebur din Kai tsaye anas room ya nufa da daidaya yake budawa har ya buda wadda Fatima take ciki, Kwance ya hangota kamar gawa da dan sauri ya karasa shiga ya dakin, Hannu yakai gefen wuyanta saida yaji tana da rai sannan hankalinshi ya kwanta duk da jikinshi yana bashi kamar akwai matsala. Yatsan sa ya dora daidai kusuwar hancinta. Yayi kusan 20 seconds da dora hannu anman bai'ji tayi sheda ba har ya fara jin tsoro yana kokarin janye hannunsa ta yaji ta numfasa da garfi ©Khadeeja Candy [4/30, 10:06 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA ◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 3⃣7⃣ Dayan hannunshi ya sake kaiwa nan ma saida ta dade sannan ta numfasa, Da sauri ya fita dakin bai dade ba ya shigo tare da wasu nurses suna turorin gado, Daukarta sukayi suka dora saman gadon suna kokarin fita yace musu "ICU room" duk suka amsa da "owk sir" da gudu2 suke tafiyar yana binsu a yaba har suka iso dakin, Nan suka mata chan jin gado, Da kanshi ya shiga saita numfashinta da computer bayan ya mata oksijin, Cikin ikon Allah da karewar numfashinta ya dawo daidai. Tsaye yayi bayan ya umarci nurses din dasu fice. Ya rumgume hannayensa yana kallonta fuskarsa babu yabo babu fallasa, Yana haka Ramla ta turo kofar dakin ta shigo, Saida ta karso kusa dashi ta shiga masa magana "sir lafiya aka kawota nan mie ya faru"? Ko kallonta baiyi ba yace "fada Ramla mie kika mata"? Da mamaki tace "mie na mata kamar ya"? Sai a lokacin ya kalleta a fusace yace "juz answer me" "ban mata komai baya alura dan naga fever nata yadan hau" "wace irin alura kika mata"? Kallon tsoro ta masa "sir"? Kallon cikin idonta yayi yace "i think bakisan aikinki ba Ramla"! Da garfi ta hade yawu "wht d u mean sir"? Hannu ya daga mata ya lumshe ido "plz left" baki sake tace "sir" ya kalleta fuska a hade "i sy gt ot"!!! Da sauri ta juya ta fice idonta cike da hawaye, Tana kawowa anan room ta jadu da raliya sai kokarin wuceta take Raliya ta rikota "lafiya Ramla mie ya faru"? Bata bata amsa ba ta nufi office dinta da dan gudu saboda kukan dake son fin karfinta, Raliya ta rufa mata baya,,,, ©Khadeeja Candy [4/30, 11:02 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA ◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 3⃣8⃣ Tana shiga ta dora hannayenta saman tebur ta fashe da kuka cike da tashin hankali Raliya ta shigo dakin ta dafata "Ramla lafiya wai mie ya faru"? Bata iya bata amsa ba saida tayi kuka taji ta samu sassauci sannan ya kalleta tace "Dr Ahmad ne Raliya yayi min abunda bai taba min ba" Raliya tace "kamar ya kenan"? "yanzu yace min na fita na fita na bashi gurin kuma yake tambayata wace irin alura nayiwa wata yarinya ake jinya" Raliya tace "nifa ban gane ba mie kike nufi"? Nuna kanta tayi "bai yarda daniba Raliya tunda kikaga ya tambayeni sannan yace na fita bayan yace ban iya aikina ba ya mun tsawa abunda bai taba ba akan wata shegiyar yarinya" Ramla ta zauna saman kujera tace "indai akan wannan yarinyar ne babu abunda bazai miki ba dan yanzu hankalinshi kaf yana gunta ke gudan sahibar tashi" Wani kallon Ramla tayi masa mai dauke da alamar tambaya "mie kike nufi"? "abunda nake nufi kan ai a'bainane yake kinsan shi namiji bai iya soba dan baya boyewa macece take wannan" Ramla tace "kin kara shigar dani duhu plz kimin bayani mana"? "Ramla kema kinsan akwai so tsakaninsu kodai yanzu yake sonta ko kuma dama can soyayyar suke ki lura Ramla tunda aka kawota asibiti nan ina lure dashi aikin komai baya iyawa saidai ya bada ai dazu ma dana shiga office dinshi yamin sign Salima na tarar tana aikin documents din nan kuma kinsan shida kanshi akeso yayishi saboda waje za'a fita dasu amman ya kasa" Shiru Ramla tayi alamar tunani Hakan yasa Raliya ci gaba "kinyi sake kawata da yarinyar nan ta shiga gaban Dr Ahmad gashi daman son da kike masa yafi nashi yawa tunda har yanzu ya kasa ya fito fili ya furta yana sonki sai wasu-wasi yake gashi yanzu har ta kwace miki shi" Murmushi jin haushi Ramla tayi tace "karya ne wlh tayi kadan mutuwa kawai takai haka" Ramla tayi dariya "to mie zakiyi gashi a fili kina gani ai wannan nuna miki ne yake yana sonta sama dake" Kai ta Girgirza "lallai ko in har haka ne to yajanyo mata ruwan dafa kanta" Raliya ta tashi tana fadin "lallai kan kara ki dauki mataki tun dare bai mikiba" ©Khadeeja Candy [4/30, 11:42 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA ◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 3⃣9⃣ Ramla ta nufi window rike da kugu zuciyar sai wani mugun bugu take, can kuma ta juyo "ke wai ya kayi kika sani"? "kinsan kanwata kawar Rukaiya ce kullum gidan take fira so i know a lot of things dake baki saniba" cika bakinta tayi da iska tana rabon ido Raliya zatayi magana suka an murda kofar dakin, A sanyaye ya shigo da sauri Raliya tayi kasa da kanta ta gaisheshi ta fice, Cikin yanayin damuwa ya kalli Ramla yace "am srr Ramla da abunda nayi miki wlh rai nane a bace kuma tunani na a chunkushe Ramla kinsan.... " "no sir karka damu babu komai ya wuce" Wani kallo yayi mata "haba Ramla dn't try 2 hide i knw i hurt u" Ta tari numfashinsa fuska a sake "no sir i cmpltly undrstnd i knw hw u feel" Kallon cikin idonta yayi saida ya tabbatar da gaske take sannan sauke ajiyar zuciya yace "thank u for undrstnd" Murmushi tayi "it's Nthing sir" Cikin kunya yace "bari naje kinsan dole ne Dr ya zauna kusa da ita dan tafiyar numfashi" kai ta daga mishi Har yakai kofa ya juyo ya kalleta "once again am srr Ramla wlh kawai ina tsausayin yarinyar ne" Murmushi tayi har saida sautin shi ya fito tace "nice to hear that sir Allah ya bata lafiya" murmushi shima yadan sakar mata yce "amin" ya fice, Yana fita Ramla tasa hannayenta cikin aljihu tana cizon Lips tana wani kashe ido "hmm tausayi? Hmm Joking kayi gaggawa this is just the beginning"!!! ©Khadeeja Candy [9:54am, 8/5/2016] ☄DEENY☄SHOMAR☄: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA ◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 4⃣3⃣ Tana fita dr ya kalli Fatima yana murmushi "ya jikin naki Fatima akwai inda yake miki ciyo ne"? " a a naji sauki kawai bana jin karfi ne" "ae, zai daina anjima kadan yanzu dai bari na kawo miki abinci kici tukuna ko"? Bata dashi komai ba kasa kawai tayi da kanta yana ganin haka yayi murmushi ya tashi ya fice, Bayan magariba Fatima na zaune ita kaidai cikin dakin inta kalli can ta kalli nan da alamun tunani take, Ramla ta turo kofa ta shigo cike da far'ah wata nurse na bayanta rike da kulolin abinci da mayan ledodi ita kuma tana rike da wata jaka, Fatima dai kallonsu kawai take har nurse ta kare jere kayan ta fice, sannan Ramla tazo ta zauna kusa da ita. Cikin ladabi Fatima ta gyasheta "Anty dr ina wuni"? da murmushi ta amsa "lafiya kalau my dear y jikin naki"? "Alhamdulillah" "to ALLAH kara sauki" "Amin" Ramla ta danyi murmushi "sis ga abinci nan na kawo miki da fruits da yogurt ice cream da chocolate ke harda kasheshiyar kaza dan nasan mai jinya da kwadayi kuma kinga computer na kawo miki ki dan rika kallo dan rage kadaici" ta karasa maganar tana kokarin cire laptop din Tana ajeta kusa da Fatima ta matsa cike da jin tsoro tace "a'a Anty dr ni ko waya ban taba rikawa ba da sunan na taba bare computer kibarshi kawai na gode" Ramla ta dafata tana murmushi "ni ki daina cemin anty ki kirani Ramla dan ni ba Anty kibace ni qawarkice kuma ni zan koya miki yadda ake aiki da computer" Fatima ta kalleta "amman..............." sai kuma tayi shiru Ramla ta sake yin murmushi "amman mie? Karki dubi girma kice kowai dan na girmeki ko wani abu a'a ita abota ba haka takeba dubi fa ki gani tun 6 na kare duty na amman na dawo asibitin nan saboda ke kawai kuma....." Knocking din da akayi yasa ta tsayarda maganar ta'ta tare da fadada murmushinta dan yanayin knocking din ta tabbatar mata da Dr ne, Cikin kirsa tace "yes" turo kofar yayi ya shigo fuskarsa babu yabo babu fallasa. Da sauri ta tashi tsaye tana murmushi "sir ashe kana nan baka wuce ba" saida ya karaso kusa dasu sannna yace "ae ban wuce ba naga shigowarki ai yanzu lafiya dai ko? I dan naga kin kare aikinki kuma da wahala ki shigo da dare"? "lafiya kalau friend dinta na dafawa abinci da dan fruits na kawo mata kuma laptop dan debe kewa" Murmushi ne ya cika fusakar Dr sai a lokacin ya lura da laptop din da kuma abincin dake gefen gadon, Kallon Ramla yayi "thank u so very much my Dr I'm happy wlh may god bless u" Murmushi tayi "ur welcome sir" ta dan sun kuyarda kai ta fice,,,, ©Khadeeja Candy [9:54am, 8/5/2016] ☄DEENY☄SHOMAR☄: [5/4, 6:56 PM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA ◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 4⃣0⃣ Yana tafe yana tunane2 abunda yayiwa Ramla dan yasan bai kyauta, "Dr3" jidda ta nufo shi da sauri tana kwala masa kira. Juyowa yayi a hankali yana ganinta ya dan saki fuskar. "jidda kece"? Kai ta daga mishi tana kawowa kusa dashi tace "ae ina wuni" "lafiya kalau yasu inna"? "kalau suke kaga Fatima"? Shiru ya danyi sannan yace "ae na ganta harma na chanja mata daki ance jiya da dade kuka kawota ko"? "ae da dare ne mukaji jikinta yayi zafi kuma kanta yana cuyo sosai shine aka kawota nan wani wani abun ne"? Ta karasa maganar tana masa kallon tsoro, Dukowa yayi daidai ita yana murmushi "a a kawai na tambaya dan ki kwantar da hankali babu abunda ya sameta" ta mayarda hawayen dake son fito nata "to zata tashi"? "zata tashi mana anjima ka dan zata tashi tana bachi ne kawai ki kwantarda hankalinki kinji" kai ta daga mishi tace "ina ka kaita"? "dakin dana taba kaita farko ICU amman bazaki iya ganinta yanxu ba sai anjima kije gurin inna ki huta kinji"? Kai ta daga mishi ta nufi hanyar data fito. Da ido ya bita saida ta bulle sannan ya juya yasa hannunshi aljihu ya nufi dakin da Fatima take, Yana shiga ya shiga hada mata drip saida ya sake bincika ta sannan yaja Kujera ya zauna ya zuba mata ido kamar yau ya fara ganinta, Yayi 40minutes a haka yana kallonta kamar tv sai faduwa gabanshi yake dan jin yake ta mishi kwarjini, Yana haka wayarsa ta shiga ringing saida ta kusa katsewa kamar bazai dauka ba can kuma ya cirota aljihu yana ganin mai kiran ya dan saki murmushi tare da yin picking "Abdulmalik kardai kace har ka iso" banji mai aka ce mishi ba dariya kawai naga yayi yace "to ka karaso mana ina emergency ICU room 4" dariyar ya sake yi yace "no plz karka min haka mana ka iso banajin barin gurin nan" can kuma naga ya Girgirza kai yace "owk saika iso" yana sauke wayar ya kai hannunshi ya shafa gefen fuskar Fatima Sannan ya tashi tare da kujera ya matsa nesa da ita ya zauna ya shiga danne2 wayar shi ©Khadeeja Candy [5/5, 10:51 AM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA ◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 4⃣1⃣ Knocking ya fara yi sannan ya turo kofa ya shigo yana fadin "mudai shigo ba komai ko"? Wani wawan kallon Dr ya watsa masa yaja tsaki "Mtswww wai kai yaushe zaka rabu da wannan halin naka"? dariya yayi yace "sai ranar da muka girma" "kuka girma kaida wai"? Zaunawa yayi kusa dashi yana fadin "nida kai mana sai munyi aure tukuna komai zai zama daidai" "to waya hana ka sai kayi ai ka huta nidai ya su mummy da kannemu"? "duk suna lafiya kuma suna gaidaku" Amsa mishi kawai yake amman hankalinshi yana gurin Fatima, kallon dr yayi yace "wai wacece wacan kake jinya haka ne"? Dr yadan hade fuska dan yasa halin Abdulmalik yace "am... Ah...uh.. Wata cousin dina ce"! Abdulmalik ya dan jin gina jin bango yana murmushi "ohh feel free malam kasan babu wadda ban saniba cikin family ku dan haka fada min gaskiya" ya tashi ya nufeta yana fadin "kasani ma ko kanwata ce" dr kai kawai ya girgixa Abdulmalik ya dan kwanto yana kallon fuskar Fatima "wow she's so cute gata black Beauty" Dr ya tabe baki "kanka akeji dai" Da gowa yayi ya kalli Dr "wai ko dai ta muce"? Dr ya watsa mai harara "taku kaidawa"? Murmushi yayi yace "ni dakai mana kasan ance abun bro's na bro's ne" Wata irin dariya dr yayi da har saida Fatima ta motsa, Da sauri ya rike bakinshi ya shiga dannar waya "ni bari na sallameka karka hargiza min tunani" Abdulmalik ya dawo kusa da dr ya tsaya yace "au tunani kake kenan wai ko nan muka zube hajar mune"? Bai ce dashi komai ba ya kara wayar a kunne,,,, ©Khadeeja Candy [5/5, 10:51 AM] Khadeeja Candy: 🌸◆◆◆LAMARIN-DUNIYA ◆◆◆🌸 Na Khadija Abubakar Alkali 4⃣2⃣ Yana sauke wayar Abdulmalik yace "wai ni ina Ramla ne"? "tana nan mana akira maka ita"? Kai ya Girgirza "a a kyaleta kawai" murmushi dr yayi zaiyi magana akayi knocking dr ya amsa da "yes" turo kofa yayi ya shigo Abdulmalik na ganinshi ya saki murmushi ya kira sunanshi "Dr Alex" hannu dr Alex ya mika mishi bayan ya mikawa dr Ahmad files din dake hannunshi, Suka shiga gaisawa sai dariya dr Alex keyi dan yadda Abdulmalik yake tsarguwarsa, Shiko dr Ahmad duk ya wani hade rai dan ganin yake zasu tada mashi da Fatima. Dr Alex na ganin haka yayiwa Abdulmalik sallama ya fice. Dan yasan halin maigidan nashi in rai ya bachi komai zai iys faruwa, Yana fita dr Ahmad ya mikawa Abdulmalik files din "karbi gasu kun wani cika mana daki da ihu haka kamar ba marar lafiya ciki" Shiru Abdulmalik yayi yana kallon dr da Fatima fuskarsa dauke da murmushi, Ganin kallon yayi yawa yasa dr ya hade masa fuska "wai mie ne haka lafiya na dai sallameka dan Allah ka kama hanya"? Dariya yayi yace "to har korata akeyi ne to ai baka bani documents ba koda wannan kawai zanje"? Tsaki yaja ya tashi suka fice Abdulmalik na mashi dariya,, Sunyi kusan 2hr suna fira a office din nan ne ma dr yake bashi labarin haduwarsu da Fatima, Sannan ya rakoshi har gurin mota sukayi sallama Har Abdulmalik ya shiga mota zolayarsa yake dr dai in banda murmushi babu abunda yake tsaye yayi parking space yana kallonshi har ya fice sannan ya juyo, ya nufi office dinshi. Yayi kusan 3hr yana rubuce2 da duba marar lafiya har aka kira la asar, Sannan ya tashi ya nufi masallacin dake asibitin. Bayan ya kare ya nufo dakin da Fatima take dan yasan yanzu ta isa tashi, A hankali ya turo kofar dakin ya shigo. Wani sanyi yaji ya ziyarci zuciyarshi daya ganta zaune, Dr Ramla na gefenta tana bata tea, Da murmushi ya karaso kusa a ita ya kalli Ramla "thank u my Dr" murmushi tayi tayi kasa da kanta "it's my duty sir" kasa2 ta wasa mashi harara shiko hankalinshi yana gun Fatima ta a'aje kofin tea ta tashi "excuse me sir" fuskarshi dauke da murmushi ya kalleta "u can go Dr" murmushi ta sake sakar masa ta shafa kan Fatima ta fice,,,,, © Khadeeja Candy GODIYA marar adadi ga masu kirana da masu min text dan suji lafiya na gode sosai Allah yabar zumunci specially u maman husnaπŸ’‹ and Antyna Dr Zulaihatu isa,😘 mrs tijjaniπŸ’‘ and my big anty in the world anty fauziya dahiru Sulaiman😍 da my sweetie blood friend no me with out u no u with out me rose akkafoπŸ’ž Habiba Ismail πŸ’˜ Hannatu kura😜 Nancy naπŸ’• lov u dears na😍😘 Am feeling much better now ALHAMDULILLAH ©Khadeeja Candy Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact form

Name

Email *

Message *