Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, 5 June 2017

WATA SHARI'AH

adsense here

[6:55pm, 8/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* Ina farawa da sunan Allah mai rahama mai jink'ai, dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mad'aukakin sarki, tsira da aminci su k'ara tabbata ga shugabanmu annabi Muhammadu (SAW) tare da Alayensa, na godewa Allah mai kowa mai komai daya bani damar sake kawo maku wannan labarin nawa. Wannan labarin mai taken *Wata shari'ah* k'irkirarren labarine, banyishi dan cin zarafin wani ko wata ba, nayine domin fad'akar da masu hali irin na jarumar cikin littafin, ina fatan za'a amfana da abunda za'a karanta a cikinsa, ina kuma fatan zakuji dad'inshi. Jinjina, godiya, bangirma ga uwa mabada mama, k'ungiya mai albarka *Nagarta Writers Association,* fatana a kullum Allah ya k'ara d'aukaka manaku, Allah ya k'ara baseerah, hikima, ilimi, hazak'a da kuma zak'in hannu. Godiya gareki *Aunty Maijidda Musa* dole na yaba miki saboda yanda kike k'ok'arin yad'a littattafanmu, muna alfahari dake a matsayinki na masoyiyarmu baki d'aya. *RAZ* daku nake tak'ama da tink'aho akoda yaushe, da bazarku nake taka rawa, banida kamarku aduk *online writers,* Allah yabar zumunci yabarmu tare. Sauran masoyana na duk fad'in duniyarnan ina k'aunarku kuma ina alfahari daku, inama ace baki zai iya lissafoku baki d'aya? Aikuwa dana zage damtse wurin jera suyenku tare da sanar daku kaf sak'unanku suna isowa gareni, saidai kuma kash! Ba abune mai sauk'i ba saboda yawanku, saidai ince nima ina k'aunarku kuma ina alfahari daku. *RAZ NOVELLA one and two* ina godiya gareku, Allah yabar minku da soyayya da k'auna. ******************************** {~1~} Yammaci ne mai cike da ni'ima, iska na kad'awa ta ko'ina, ganyaye sunyi tsanwa shar abun gwanin ban sha'awa, sama tayi luf da hadari kwance a cikinta, ko'ina yayi tsit babu ko kukan tsuntsaye, kowa ya ladaftu a gidansa dan gudun saukowar ruwan sama. Tuk'i yake da k'arfin gaske kamar mai shirin tashi sama, Daga gefenshi (kujerar zaman banza) wata mace ce ta hakimce fuskarta sanye da dark glasses, kyakkyawace ajin k'arshe, tanata taunar chewing gum cikin natsuwa take kallon yanda namijin yake sharara gudu abunshi. "Dan Allah Honey ka rage gudun nan da kake, ka bimu a hankali mana" ta fad'a bayan ta zare glasses d'in dake idonta. "Ai dolece tasa kikaga ina gudun nan Sultana, bakiga yanda saman take bane? Ina gudun kar ruwan sama ya saukone, kinsan watan August ruwan sama baya alerting kafin yazo saidai kawai aganshi yazo, kuma da k'arfi yake zuwa yanda dole sai munyi parking har sai lokacin daya tsaya sannan mu tafi" ya bata amsa still yana shararar gudunsa. Shiru tayi bata kuma fad'in komai ba, ganin ya k'ara yawan gudun da yake yasa ta sake maimaitwa, "Abban Hafsa dan Allah ka rage gudun da kake, kasan fa bana son gudu da mota saisa kakeyi". Bai ko kalleta ba yaci gaba da tuk'inshi. "Nikam wai kodai duk cikin fushin nayi winning d'inka a shari'ar yaune yasakaka wannan gudun tsiyar? Nikam karka zubar damu garin fushinka". A fusace ya rage gudun motar ya koma tuk'ata slowly, "Sultana an fad'a miki wai naji haushine dan kinyi winning d'ina shari'ar yau? Kika sani ma ko da gangan na barki kikayi winning d'in nawa dan na ganki sabuwar lawyer ne?" "Kaidai fad'i gaskiya Honey" ta fad'a cikin zaulaya tana masa dariya. "Kaga ai gashi yanzu nasa ka rage gudun ko? Inda ace ban maka hakaba da yanzu kana nan kana sharara gudu damu". "Au! Haka kika fad'a? Zakija inci gaba daga inda na tsaya kuwa" ya fad'a yana k'ok'arin cigaba da gudunshi. "A'a nidai dan Allah kayi hak'uri tunda ai mun kusa isa gidan ma". Tana gama fad'in haka kuwa ruwan sama ya sauko da k'arfin gaske mai had'e da iska sosai, "Kinga abunda nake fad'a miki ko? Inda kin bari baci gaba da gudun aida tuni mun isa", "Ehh nidai na yarda kabi a hankali d'in koma dai yaushe ne zamu isa babu matsala". Saida ruwan sama ya yawaita sosai sannan suka iso gida, Saida yayi horn sau uku kafin maigadi ya fito hannunshi rik'e da lema ya wage gate d'in gidan, D'aga ma maigadin hannu yayi alamar gaisuwa tareda tsaida motarshi a daidai inda aka tanada domin ajiye motoci. A hankali ta bud'e motar ta fito, irin rigar nan ta barristers ce sanye a jikinta da hular kayan, shima namijin irinsu ne a jikinshi, a bayanshi ta bo'ye bayan ya rufe motar dan bata son ruwan sama ya tab'ata ko kad'an sannan suka shiga cikin gidan. Da shigarsu kuwa saiga wata yarinya 'yar kimanin shekara bakwai, sanye take da doguwar riga armless baby pink in colour, da sauri kuwa ta taso "Oyoyo Momy" ta fad'a bayan ta rungumi mamarta, "Oyoyo my Hafsa" itama ta fad'a tana mata murmushi, "Au! Momy'nki kawai kika sani ko? Nima barinje wurin nawa baby'n yanzu" namijin ya fad'a bayan ya d'auke kanshi daga garesu. "Am sorry Abbana, yanzu zanzo wurinka kaima" Hafsa ta fad'a bayan ta saki momy'nta ta koma ta rungumi Abbanta. "Ina Haydar ne?" Ya tambayeta bayan ya cire hular kanshi. "Haydar yana wurin Nany, suna upstairs" ta bashi amsa, "Ok kije kice ta kawo minshi, nayi missing nashi tun safe rabona dashi" Da sauri kuwa ta haye sama don ta kira Nany d'in da Haydar k'aninta. "Ammafa Abbah nayi mamakin yanda nayi winning shari'ar nan ta yau, ni kaina nasan ka sakar min itane kawai", "Thank God da kika fahimci hakan da kanki, yunwa nakeji wallahi", "Ok am sorrie, barin shiga yanzu in dafa maka favorite naka" ta cire rigar jikinta da hular ta shiga d'akinta ta ajiyesu sannan ta fito domin nufar kitchen. K'arar shigowar text message taji a wayarta, da saurinta ta ciro wayar daga cikin jakarta ta bud'e sak'on. Ido bud'e take karantashi cikin mamaki, bayan ta gama karantawa ta kalli mijinta tace "Abbah! Kalli sak:onda aka aikomin yanzu". Karb'ar wayar yayi ya fara karantowa a bayyane. Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [1:11pm, 9/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) {~2~} "Kamar yanda Allah yayiku masu taimako keda mijinki, nake amfani da wannan damar domin rok'onku wata alfarma, An cuceta kuma an hanata kuka, ku taimaka ku taimaketa, ku fiddata daga mawuyancin halinda take ciki". "Subhanallah! To waye yayi wannan rubutun? Kuma da alama koma waye ya sanmu, kuma gashi babu wani cikakken bayani" Barrister Umar ya fad'a yana kallon matarshi Barrsiter Sultana. "Kaima kenan Honey, nikam banma fahimci komai dake ciki ba, bansan inda maganar ta dosa ba". "Barin kira number'n inji, dan wannan ba abune wanda za'ace wrong number ba, dama da niyyar mu d'in aka turomawa" kafin ya gama rufe bakinshi shima wayarshi tahau ruri alamar shigowar text message, exactly irin wanda aka turoma Sultana shima shi aka turo mashi, Bayan ya gama karantawa yace "akwai matsala kam, kinga" ya mik'a mata wayar, "nima irinshi aka turo min yanzu babu ko banbanci, barin kira dai". Kiran lambar ya latsa amma da mamaki sai yaji ana fad'in "the number you are tyring to call does not exist, please check the number and try again", "A'ah" ya fad'a bayan ya sake gwada lambar, still dai abunda aka fad'a ne aka maimaita. "Ya akayi? baka samu bane?" Sultana ta tambayeshi tana kallonshi. "Wallahi kuwa babu itama wai sukace kiji tsiyar MTN, k'iri k'iri yanzu aka turo min text da number amma wai ace babu ita, wannan k'aryane" ya sake kiran layin. Saida ya kira sau goma amma babu ita, hakan yasa kawai ya hak'ura ya ajiye wayar idonshi lumshe yana tunanin wanda ya masu wannan text d'in. "Barinje in dafa maka abincin yanzu honey" ta fad'a bayan ta tashi ta nufi kitchen. Hafsa da Nany ne suka sauko daga upstairs Haydar na goye bayan Nany, Har k'asa ta duk'a tace "sannu da dawowa Alhaji" shiru yayi kasantuwar zurfi da yayi da tunanin wanda ya turo masu wannan text d'in, "Ina yini Alhaji" ta sake maimaitawa dan tasan baijita ba daya amsata. "Lafiya Safiyya ina gajiya?", "Ba gajiya, Momy fa?", "Gata can a kitchen, kawo Haydar d'in" Mik'oshi tayi, bayan ya karb'eshi tace "Alhaji an kawo wata takarda d'azu da bakunan, Haladu ya mik'o yace wani yaro ya kawo wai a aje maku kaida momy". "Ikon Allah! Ina takardar take?" Ya tambayeta bayan ya tashi zaune daga kishingid'awar da yayi. "Gata" ta mik'a mashi tare da nufar kitchen domin ta taya Sultana aiki. Bud'e takardar yayi yaga ab rubuta "nine dai wanda ya rubuto maku sak'on waya, yarinyar tana cikin matsanancin hali, an cuceta kuma an hanata kuka dan anga halinda suke ciki itada mahaifiyarta Kada ku wahar da kanku wurin kiran lambar tawa saboda ba zaku sameni ba, nasan kunada halin taimakon nata, kuyi bakin k'ok'arinku na rok'eku karku bari wanaan damar ta taimakon musulmai ta kufce maku, Allah kad'ai yasan ladar da zaku samu". "Sultana!" Ya fad'a bayan ya gama karantawa. "Na'am honey" ta fito da sauri saboda yanda ya kirata ta tabbatar da akwai matsala. Gabanshi ta gurfana tace "lafiya dai honey?", "Karanta kiga wannan", Goge ruwan hannunta tayi a zanin jikinta sannan ta karb'i takardar a hankali ta fara karantawa. "Towai waye yake aikoda wannan sak'on? Waya kawo takardar?" Ta tambayeshi tana kallonshi, "Safiyya ta bani ita, wai Haladu ya kawo yace ta ajiye mana idan mun dawo ta bamu", "Safiyya!" Ta kira sunan mai aikin tata. Bayan tazota tace "jeki kiramin Haladu kice yazoshi da sauri yabar duk abunda yakey, kar kuma ki biye masa kuita shirmen fad'an nan naku, dan nasan ku bakwa had'uwa wuri bakuyi fad'a ba", "To momy" Safiyya ta fad'a tare da fita da sauri harda gudu gudu takeyi. A waje ta sameshi yana ban ruwan flowers, Murmushi yayi daya ganta yace "ahh! 'Yan matana kece da kanki?", B'ata fuska tayi tace "nifa bana son shashanci waye 'yan matan taka?", "Kece mana Safiyya, ai banida wata budurwa wadda tafiki", "Kai ni ba shirme ya kawoni ba, kajeka momy na kiranka, kuma tace kayi sauri yanzu take son ganinka", "To kije gani nan zuwa" ya fad'a yana mata wani murmushin, "Tace mujemu tare, dan haka kazo mu tafi kana b'atamin lokaci", "Ahh lallai 'yan matana ta fara sona tunda har takeson mujera tare, mu tafi to". Bata kuma ce masa komai ba har suka isa, bayan sun zauna Sultana tace "Haladu waye ya baka takarda d'azu yace ka kawo mana?", Shiru yayi yana tunanin wace takardace take nufi? Sai daga baya ya tuna yace "wani yarone ya kawota nima dai bansan yaron ba, yace min wai an bashine ance ya tabbatarda ya kawota gidan nan". "Oh my God! To waye wannan wai? Ai ya kamata koma waye ya bayyana mana kanshi mu taimaki baiwar Allah'n tare dashi, b'oyon ai bashuda amfani" Sultana ta fad'a. "Wama yasan ko k'aryar banza yake? Irin mutanen nan ne dai masu son su shiga sha'aninmu, dan haka ki fita batun wannan maganar nima na fita, ku tashi ku tafi Haladu" ya sallamesu. Tashi kuwa sukayi, Haladu ya kalli Safiyya yayi mata murmshin soyayya sannan ya tafi, ita kuwa hararshi tayi sannan ta koma kitchen Sultana ma tabi bayanta har yanzu batace komai ba sai tunane tunane da take, Ta tabbatarda akwai magana, bazai yiwu ace koma waye ya k'irk'iri maganar nan ba kawai dan yaji dad'i, zataci gaba da bincike har sanda Allah zai bayyana wannan b'oyayyen al'amarin. Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [4:46pm, 11/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) {~2-10~} Washe gari da sassafe Sultana ta tashi Umar suka fara shirin zuwa aiki, Bayan sun gama shiri ta yima Hafsa da Haydar wanka sannan ta shirya Hafsa cikin Uniform d'in School d'insu, Sauran pepper soup d'in jiya tayi warming nashi sannan ta soya mata Irish da k'wai ta saka a launch box d'inta. "Wow! Kinyi kyau baby na, barin snapping naki" Hafsa uwar iyayi kuwa aka wani yi style na d'aukar hoto, Saida Sultana ta d'auketa hoto kala biyar sannan tace "to ya isa haka, barinyi Feeding haydar shima tunda dai kinga anan zan tafi in barshi", "Ok Momy ki d'iba a nawa ki bashi" Hafsa ta fad'a cike da soyayyar k'aninta, "Ahh Hafsa ai na d'ibar masa nashi daban, gashi kin gani" Sultana ta fad'a tare da nunawa Hafsa sauran Irish da k'wan data ragewa Haydar. Saida suka gama tas Umar ya fito cikin suite d'inshi black and white, Yayi matuk'ar yin kyau kamar in saceshi in gudu, "Yadai Madam? Hope kun gama saboda inada aiki da yawa a Office yau, kuma kema d'in nasan ba zaki rasa ba". "I think bani da aiki nikam, bandai san ko sai naje zan sameshi ba, mun gama dama kai muke jira", "Ok muje kawai" ya fad'a bayan ya soka wayarshi cikin aljihu. Bai gama sakawa ba yaji k'arar text message ya shigo masa, Zarowa yayi ba tare da tunanin komai ba ya fara karantawa, _"Nasan zakuyi tunanin kawai inason inyi wasa da hankalinku ne, to sam ba haka bane, kamar yanda na fad'a maku an cuceta kuma bata da halin karb'ar fansa saboda anfita kud'i, mulki da komai ma, na rok'eku dan Allah da soyayyarshi ga mafificin halitta ku taimketa,_ _Idan har kuna bisa ga ra'ayin taimakonta zaku iya maido min da reply ni kuma sai in baku address nata"_ "Again?" Umar ya fad'a a bayyane. "Menene ya faru honey?" Sultana ta tambayeshi bayan ta gama sakawa Hafsa socks and sandals nata. "Karb'a ki gani" ya mik'a mata wayar, "Ana so ayi wasa da hankalinmu ne kawai, zanje wurin MTN su duba min wannan layin, inhar na gano kowaye yake mana yawo da hankali wallahi sai ya raina kansa, ni bana son raini ko kad'an". Bayan Sultana ta gama karantawa ta mik'a masa wayarsa, "Ni ina ganin honey kafin kayi haka ka tura da reply d'in, tunda har yanzu akace za'a turo mana da address kaga kamar akwai alamar gaskiya a ciki". "Alamar gaskiya? A cikin wannan maganar? Bana tunani kam, koma waye idan da gaske yake ai sai yazo ya tinkaremu da maganar tunda dai yasan gidanmu yazo ya kawo takarda jiya, dan haka wannan shirmene kawai kuma kibar maganar nan kamar yanda na fad'a miki jiya, kuma yau yau d'in nan insha Allahu zanje MTN Office suyi min bincike akan layin nan" yayi gaba bayan ya miyar da wayarsa a cikin aljihu, "Ku fito mu tafi lokaci na tafiya" yayi waje. "Safiyya!" Ta k'walawa Nany d'in Haydar kira, "Na'am momy" ta fad'a tare da saukowa daga kan bene da sauri. "Gani momy" ta fad'a tana kallon Sultana, "Ki d'auki Haydar ki goyashi nasan yanzu zayyi bacci tunda na mashi wanka ya karya kuma". D'aukarshi tayi kuwa ta goyashi, harda ba-bye yayima Momy'n shi, Hafsa ma ta d'aga mashi hannu sannan suka fita suka samu Umar har ya fitar da mota waje yana jiransu. "Afuwan honey, kanata jiranmu", "Hmm! Bakya laifi wifey, ku shigo mu tafi". Saida suka fara dropping d'in Hafsa sannan suka nufi Federal High Court Katsina, Kai tsaye kowa ya nufi Office d'inshi, Zaman Sultana keda wuya kuwa sak'o ya shigo mata, Exactly irin wanda akama Umar ne, Aikuwa bata jira komai ba ta miyar da amsa, _"A shirye muke da taimakonta indai har da gaskene wannan sak'onnin da ake turo mana, kullum burinmu shine muga mun taimaki wanda aka zalunta ko kuma wanda ake k'ok'arin zalunta, dan haka ina jiran address d'inta yanzu"._ Tayi sending tare da ajiye wayar akan desk d'inta. Bada jimawa ba kuwa sak'o ya kuma shigowa, d'auka tayi ta karanta _"Tudun Wada layin farko gida na biyu yana kallon masallaci"._ "Good" ta fad'a a bayyane, "Insha Allahu zan taimaketa, zanyi shiru bazan fad'awa Umar ba har sai na tabbatar da gaskiyar al'amarin sannan in sanar dashi, shima kuma nasan bakin k'ok'arinshi zai taimaketa idan ya tabbatar da maganar". K'arfe hud'u daidai suka tashi aiki, A cikin mota Umar yace "nikam na rasa menene tsakanina da Barrister Sa'eed, kwata_kwata baya k'aunata, ko a hanya na had'u dashi na bashi hannu mu gaisa baya amsa, na rasa dalilin hakan". "Hmm! Ka rasa dalili fa kace honey, ga dalili k'arara a bayyane, Ko ka manta shari'arka ta farko dashi kayi winning? Kuma tun daga nan na kula yake neman shari'ar da zakuyi dashi amma ba'a sameta ba, a tunanina dalilin jin haushinka kenan da yake, Kumafa na samu labarin tunda yake a rayuwarshi kaine mutum na farko daya fara kadashi a shari'ah, kuma har yanzu ba'a samu wani ba", "Ehh hakane kam, amma ni sai naga kamar duk wannan bai isa yasashi jin haushina ba, ki duba kiga tun lokacin da akayi shari'ar, kusan shekaru goma kenan fa k'ilama anfi, me zai sashi ya rik'e wannan abun? Kuma in banda abunshi ma yanda yake babban barrister wanda duk fad'in k'asar nan an sanshi yayi suna me zaisa ya ringa jin haushina ni d'an k'aramin barrister?". "Hmm! Kai kaga haka honey, ai kuwa yanzu idan baka take mashi baya ba to k'iris ya rage ka take bayanshi, yanda yayi suna kaima d'in haka kayi, duk inda ka shiga Barrister Umar Mohd ake fad'i, kaga kuwa ka godewa Allah", "Kema kinyi magana Wifey, Allah dai ya k'ara bamu ikon cin halaliyarmu, Allah ya karemu daga cin kud'in cin hanci da rashawa, burinmu a kullum muga mun taimaki mai buk'atar taimako, bama fatan mu tauye gaskiya akan k'arya kawai saboda kud'i ko wata k'awa ta duniya". Da wannan firar suka isa gida, da sauri kuwa Haladu ya wage masu gate suka shige da motarsu, cike da soyayya suka fito hannunsu mak'ale da juna, Jin k'arar motarsu yasa da gudu Hafsa ta fito tana fad'in "oyoyo oyoyo" ta rungumesu su biyun, "Oyoyo Hafsa" Umar ya fad'a bayan ya saki Sultana ya d'auki Hafsa. Shigarsu ciki suka samu Haydar da Safiyya sunata wasa abunsu cike da so da k'auna, Ganinsu da Haydar yayi yasa ya daina wasan yazo yama iyayenshi oyoyo, "Momy yau Safiyya bataje ta d'aukoni School da wuri ba duk saida aka watse aka barni sannan tazo" Hafsa ta fad'a tare da tunzuro baki ita a dole mai fushi. "Hafsa me naji kin fad'a?" Sultana ta tambayeta, Saurin dafe bakinta tayi tare da fad'in "Aunty Safiyya bataje ta d'aukoni da wuri ba har aka watse aka barni ni kad'ai a School". "Au! Kin gyara kenan? Kuma ma ban hanaki kawo min k'arar Safiyya ba? Na hanaki ko ban hanaki ba?" Ta had'a hannayenta biyu ta zare mata ido, "Kin hanani momy" Hafsa ta fad'a hawaye na shirin fito mata. "To mesa zaki kawo min k'ararta? Sa'arkice ita? Waya fad'a miki ana kawo babba k'ara?", "Babu" ta fad'a bayan hawaye sun fito mata, "Ki bata hak'uri", Juyawa tayi ga Safiyya bayan tayi kneel down ta had'e hannayenta biyu tace "sorry Aunty Safiyya", Cike da so da k'auna Safiyya ta jawota ta d'ora kan cinyarta ta rungumeta, "Babu komai Hafsa nima ki yafe min kinji? Keke napep ce tamin wahalar samu saida nayi trekking har bakin roundabout sannan na samu". "Kema duk laifinki ne ai, dan me zaki tsaya kinama yarinya k'arama kamar Hafsa wai bayanin abunda yasa bakije d'aukarata da wuri ba? Saisa take rainaki wallahi" Sultana ta fad'a dan ta tsani taga k'arami ya raina babba. "Babu komai Momy, Hafsa nada biyayya sosai wallahi, yanzu ma nasan fushi tayi ne saboda babu dad'i a watse abar yaro shi kad'ai a School", "Kudai kuka sani, akwai abinci ne?", "Ehh akwai Momy" Safiyya ta fad'a tare da nufar Kitchen. Dama ta riga da ta zuba a food flasks, d'aukowa kawai tayi takai dining, D'aki Sultana ta shiga ta kira Umar akan yazo suci abinci, "Wanka nake sonyi ne saboda yau na gaji sosai, idan nayi wankan sai in samu d'an k'arfi_k'arfi a jikina", "Ehh hakan yayi, nima kaga sai muyi tare dan bakai kad'ai keson samun k'arfin ba" tayi murmushi bayan ta gama maganar. "Wifey na ta kaina, ina sonki sosai" ya fad'a k'wayar idonshi akan idonta cike da soyayya, "Hmm! Honey ni ba sonka nake ba k'aunarka nake, saboda kasan shi so yana raguwa watan wata rana, amma k'auna bata tab'a raguwa duk tsanani duk wahala", "Hakane wfey, ki kud'ura a ranki *ina tare dake* komai rintsi komai wuya", "Nima *ina tare dakai* honey na" ta fad'a bayan sun kama hanyar shiga toilet, Nidai Amrah gudowa nayi saboda abun yana shirin fin k'arfi na, amma fa ina bakin toilet ina jiran fitowarsu saboda ina son yanayin soyayyar wannan ma'auratan dan ina son in koya nima. Sun jima a cikin toilet d'in kafin su fito, Hafsa zaryarta biyu tana nemansu amma bata gansu ba, Dan haka ta koma ta fad'awa Safiyya cewa Abba da Momy'nta sun b'ata, Dariya kawai Safiyya tayi dan tasan dalilin rashin fitowar tasu. Da fitowarsu kuwa mai ta shafa mashi shima kuma ya shafa mata, k'anana kaya ta fiddo mashi blue jeans sai white T-shirt a jikinta an rubuta *"YOU ARE MINE"* da kalar royal blue, Itama k'ananan kayan ta fiddo, three qurter ne blue itama sai 'yar polo shirt white da logo na polo royal blue bayanta itama an rubuta *"YOU ARE MINE TOO".* Sosai sukayi masifar kyau, nidai "perfect couple" kawai bakina ke furtawa. Mak'ale da juna suka fita kamar ba sune suka aje kamar Hafsa ba. Kai tsaye dining suka nufa inda suka fara feeding junansu duk da idon Safiyya da Hafsa baisa sunji ko kad'an d'in kunya sun daina ba, Koda yake ai a soyayya babu kunya, idan kuwa aka saka kunya to bazaku tab'a jin dad'in rayuwarku ba, wannan haka yake. Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [1:27pm, 12/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) {~11-20~} Yau ta kasance Friday ne, dan haka tun k'arfe sha biyu Umar da Sultana suka tashi daga aiki, Kai tsaye suka wuce Gobarau Academy suka d'auko Hafsa sannan suka wuce gida. A cikin motar Hafsa tace "Abbah yau ina cikin Class Teacher Nasir ya kirani, bayan naje yace min wai wani mutumi ne yazo nemana amma bazai barni in tafi wurin mutumin ni kad'ai ba dan kar aje wani abu ya sameni kuma laifinsu ne, shine na bishi mukaje wurin mutumin a bakin Head Master's Office, Na gaisheshi ya dafa kaina yace min "kece Hafsa ko?", "Ehh nice Hafsat Umar Muhammad" na bashi amsa, Shine yace min wai dama sak'one zai bani wurinku, "Hafsa ki jaddadawa iyayenki cewa taimako yanada matuk'ar muhimmanci, idan Allah ya baka damar taimako to kayi k'ok'arin aikatashi tun kafin damar ta kufce maka" ya kuma ce min "karki manta ki fad'a masu wannan sak'on". Yana gama fad'in haka English Teacher d'inmu yazo harda bulala a hannunshi "Hafsa you are speaking vanacular ba? Hmm!" Naji tsoro sosai Abbah dan nasan sai ya bani kashi idan na koma class, Abbah abun mamaki ashe wannan mutumin wanda ya bani sak'o wurinku ya iya turanci sosai, Aikuwa ya taimakeni ya fad'awa Teacher'nmu cewa ba Hausa nakeyi ba turancine, harda cewa yayi wai yaji dad'in yanda ya jini ina speaking kamar ba 'yar Nigeria ba, kuma sak'o yake bani wurin parents d'ina, daga nan kuma sai ya tafi" ta gama basu labarin hankalinta kwance tana bud'e dash board dake side d'inta. Juyowa Umar yayi ya kalleta taci gaba da wasanta, Bai tanka mata ba, haka Sultana ma batace mata komai ba, "Abbah da Momy kunyi shiru, nidai babu ruwana idan ya tambayeni nasan na fad'a maku sak'onshi". Shiru sukayi har suka isa gida, Bayan Umar ya shiga d'aki ne Sultana ta juyo ga Hafsa tace "mutumin da yayi miki maganar ya yake?", "Momy nifa ban sanshi ba, kawai dai nasan ya iya turanci kuma yanada fara'ah" ta bata amsa. ***** Washe gari. Da sassafe Sultana ta tashi, ita dama haka tsarinta yake kullum ita ke rigar Umar tashi, sai ta gama ayyukanta kaf ta bad'e gidan da k'amshi sannan ta tasheshi yayi wanja, idan yayi wanka sai su karya tare lokacin itama ta shirya kuma ta gyara Hafsa da Haydar. Bayan sun zauna kalaci ne Sultana tace "Abbah yau kuwa ina son fita ko zuwa da yamma ne insha Allahu". Gyaran murya yayi yace "dama kinga nima inason fita, ina zakuje ne sai mu fita tare?". Ido ta ringa zarowa dan batasan kalar k'aryar da zata masa ba, "Gudan Hauwa nake son zuwa, kwana biyu bamu gaisa ba", "Ehh kuma dama jiya ta kirani ni nama manta, tace ince miki Zarah batada lafiya saima yanzu na tuna wallahi, afuwan". "Amma dai honey ka cika mantuwa da yawa, yanzu inda ace bance zanje ba kenan da bazaka fad'a min ba, saidai ta ringa kallona da abun ko? Ai babu dad'i ace yarinya batada lafiya banje na ganota ba", "Nidai kiyi min hak'uri tunda gashi na fad'a miki, anjima d'in kinga sai mu tafi tare nima in dubata da jikin". Damm! Gaban Sultana ya fad'i sai raba idanuwa take saboda bata son ya bita, "A'a kafa san dama ba tare dakai nake zuwa gidan Hauwa ba, bana son inje ka azalzaleni sai na tashi mun tafi gida, ni kuma ina son in zauna muyi fira sosai barin yanzu mun dad'e bamu had'u ba". "To naji uwar son fira, kije yau ni kuma gobe sai inje, kuma inji kince zaki bini yawon gobe in kurta miki rashin mutunci" cike da soyayya yakeyin maganar. "Ehh naji dai babu komai, nima kuma daga can sai mu wuce yawonmu ko Hafsa?" "Ehh Momy, har ki kaini Royal Bakeries ki siya min shawarma da ice cream" Hafsa ta fad'a tana murmushi. "Karki damu ai yawo zamusha sosai cikin garin nan, harda inda wani bai tab'a zuwa bama sai munje ko?" "Ehh momy zanje, shi kuma Abbah sai mu barshi da Haydar ko?" Kwakkwab'e baki Haydar yayi alamar zayyi kuka, "Ni ba jakuje daniba ko? Appa kaji wai bajacu tafi dani loyal ba nima insha ayish kilim", "Woiii Haydar bai iya magana ba, wai ayish kilim, yaro kazo in koya maka magana" Hafsa ta fad'a tana mishi gwalo. Kukane ya fito da k'arfi ya fasashi, yanayi yana kallon Umar dan yaji abunda zai fad'a, "A'a fa Hafsa, wallahi idan kikaci gaba da samin yaro kuka duka ma sai in hanaku fitar, ni kuma gobe muyi tafiyarmu nida d'ana Haydar" Umar ya fad'a yana rarrashin Haydar d'in. "A'a fa wasa take masa, nidai ka barmu mu fita ai hardashi zamu tafi amma fa sai idan yayi shiru da kukan nan", Saurin goge hawayen yayi yace "nayi shilu momy, jaki tafi dani?", "Ehh zan tafi dakai yarona" sukayi murmushi su duka ukun. Ranar tunda wuri Sultana ta d'aura abincin rana, dambun cous cous da sauce d'in hanta ce tayi, cikin lokaci kad'an kuwa ta gama komai ta saka a food flask, Dining suka zauna suka shari abincinsu, Umar harda santi ya ringayi. Ta sake yima Hafsa da Haydar wanka ta shiryasu sannan ta umurci Safiyya ma da ta shirya su tafi tare. K'arfe uku daidai suka fita, motarta k'irar vibe ja suka shiga, Hafsa ce gaba sai Safiyya da Haydar a baya, Basu wani d'auki lokaci a hanya ba suka isa gidan Hauwa kasantuwar babu nisa sosai unguwar. Sosai Hauwa tayi farin cikin ganinsu, Sunsha fira sosai kafin Sultana tace "zanje in dawo yanzu insha Allahu", "Daga zuwa kuma? Ina zakije ne?" Hauwa ta tambayeta, "Ehh zan dawo ai anan zan bar su Hafsa, Tudun wada zanje yanzu bazan dad'e ba ai". "Momy kince fa zaki tafi damu musha ice cream, ya kuma zaki tafi ki barmu?", "Ai yanzu zan dawo Hafsa, ga Zarah nan kuyi wasa kafin in dawo sai mu tafi royal d'in ku zab'i duk abunda kuke so", "Yauwa momy na sai kin dawo", "Ok sai na dawo, Safiyya ki kula da Haydar kin sanshi da b'arna da kuma yawo" Tana gama fad'ar haka ta d'auki hand bag d'inta ta nufi hanyar fita. Kai taaye Tudun wada ta wuce, Wayarta ta fiddo daga cikin jaka ta sake duba text message na address d'inda aka turo mata, A hankali ta ringa driving tana k'ara duba message d'in, Daidai gaban gidan da yake kallon masallacin kuwa tayi parking kamar yanda aka rubuta mata, Bayan ta rurrufe motar ta fito tana rik'e da jakarta. "Assalamu alaikum" Sultana ta fad'a bayan ta zare medical glasses d'inta daga ido. Shiru taji ba'a amsa sallamar ba, hakan yasa ta sakeyin wata sallamar amma har yanzu shiru ne, Sallamah ta sakeyi a karo na uku sannan wata murya ta amsa sallamar. A hankali tayi taku hud'u zuwa biyar ya sadata da cikin gidan. D'an k'aramin gidane ginin jar k'asa, yana d'auke da d'aki k'waya d'aya tal sai band'aki, daga can gefe kuma kitchen ne aka zagaye da langa langa, k'asan kuwa duk jar k'asa ne. "Marhabun, shigo daga ciki mana" matar ta fad'a tana kallon Sultana dukda bata wayeta ba. "to mama nagode" ta fad'a bayan ta shiga cikin d'akinda matar ta nuna mata ta shiga. "Sannu da zuwa baiwar Allah" Matar ta fad'a har yanzu tana kallon Sultana, "Yauwa sannu mama" ta tsuguna k'asa tace "ina yini mama?", "Lafiya k'alau baiwar Allah, saidai kuma ban wayeki ba", "Ehh gaskiya dama nasan ba zaki wayeni ba dan baki sanni ba" ta zaro ID card d'inta, "Sunana Barrister Sultana Saddam Bakori" Dafe k'irji matar tayi tace "na shiga uku! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah dai yasa lafiya ba wani abu mukayi ba", Murmushi Sultana tayi tace "karki damu mama, lafiya lau ba wani abu kukayi ba, zuwana alkhairine insha Allahu", "To ina fatan haka Sultana, Ummimah!" Ta kira sunan a hankali. Daga kan gado wata budurwa 'yar kimanin shekara gona sha takwas ta sauko, A hankali take tafiya fuskarta bushe da hawaye. "Waike Ummimah har yaushe ne zaki hak'ura ki daina wannan kukan? Kukan banza tunda kibsan ba wani magani zayyi miki ba", Saurin goge sabon hawayen daya fito mata tayi sannan tace "sannu baiwar Allah". Cike da tausayi Sultana ke kallonta tare da fad'in "yauwa Ummimah, ya gida?", "Lafiya Sannu da zuwa, barin kawo miki ruwa" ta fad'a muryarta na rawa sosai alamar wani kukan take shirin tayi. "A'a ki barshi wallahi bana jin k'ishi", "A'a indai kinsan ba k'yamarmu kike ba to kisha ruwanmu" Mamar ta fad'a cikin natsuwa. "Hmm! Me zaisa nayi k'yamarku mama? Kuma fa mutane ne kamar ni, Wallahi kawai dai bana jin k'ishin ne yanzu daga wani gida nake, amma dai Ummimah ki kawo min kad'an zansha". Tashi kuwa Ummima d'in tayi sai gata da kofin roba cike da ruwa, Mik'awa Sultana tayi aikuwa tajishi da sanyi kamar daga fridge aka d'iboshi, Kad'an tasha sannan ta ajiye kofin a k'asa ta fuskanci mama da Ummimah. "Nasan baku sanni ba, kuma bakusan dalilin zuwana wurinku ba", "Ehh kam hakane, ni a tunanina ma ko kinyi b'atar hanya ne, amma ke nake saurare sai kin fad'a zan tabbatar ko wurinmun kikazo" mama ta fad'a tana kallon Sultana, "Wurinku kam nazo mama, Kamar yanda na fad'a maku ni lawyer ce, nazo ne muyi wata magana idan har ba zaku damu ba", "Ehh muna jinki Sultana", Ta bud'e baki zata fara maganar kenan wayarta ta d'auki ruri, hakan yasa ta ta fasa yin maganar, fiddota tayi daga cikin jaka sannan tayi picking ta kara a kunnenta. Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [12:50pm, 13/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~21-30~} "Hello honey" ta fad'a a hankali, "Na'am wifey, kina kusa da Hauwa ne? Ina son inyimata ya mai jiki", Shiru Sultana tayi kafin tace "aikuwa na fita yanzu amma zan koma, saidai ko ka kira number'nta ko kuma idan na koma in kiraka sai in bata", "To babu damuwa, idan kin koma d'in sai ki kirani, saboda gaskiya babu tabbas d'in zan samu zuwa gobe gidan nata dan akwai hidimar data taso min goben" "Ok honey sai na koma d'in" tayi hanging up na wayar. Juyowa tayi ga Ummimah da Mama tace "kuyi hak'uri fa mama, maigidana ne ya kirani", "Uhm babu komai Sultana, bari ki fara ji daga bakin Ummimah sannan nima in fad'a miki abunda na sani" mama ta fad'a cike da natsuwa. Ga Ummimah ta juya tace "ina saurarenki Ummimah". "Asalin sunana Aisha Abubakar ne, amma Mamana da babana suna kirana da Ummimah kasantuwar sunan kakata wadda ta haifi babana aka saka min, nice babba a wurin iyayena sai k'annena guda biyu 'yan biyu ne Afrah da Amrah, shekara biyu ke tsakanina dasu tun daga nan kuma haihuwa ta d'aukewa mamana, dama wurin haihuwarsu Amrah tasha wahala sosai. Mahaifina nada rufin asirinshi daidai gwargwado, muna zaune a gidan haya a cikin unguwar Saulawa dake nan cikin garin Katsina, babana yana aiki a wata k'aramar ma'aikata a k'ark'ashin wani mutumi inda ya zama masinjanshi. Akwai shak'uwa sosai tsakaninmu, mukan zauna a koda yaushe muyi raha tare da iyayenmu, Babana ya sakani a makarantar gwamnati saboda bashi da halin da zai kaimu makarantar kud'i duk da yanada burin hakan, Na taso da bala'in son inyi zurfi a karatun boko ina son in karanci fannin education kodan in gyara rayuwar bokon zamani, hakan yasa nake miyar da hankalina a kowane term, tun yarintata ni nake d'aukar first position har na shiga secondary School, Bani da k'awa ko d'aya ni kad'ai nake rayuwata daga ni sai k'annena biyu wanda bana b'oye masu damuwata suma kuma basu b'oye min tasu damuwar, a raina har nakan tambayi kaina akan wa nafi so a cikinsu, *Afrah ko Amrah* (namesy Futha) saidai kuma amsar d'ayace, duk d'aya suke a wurina. Bayan mun rubuta jarabawar JSS ne Allah ya bani sa'a kuwa na samu sakamako mai kyau, ina d'aya daga cikin wanda suka zamo na d'aya a cikin kaf class mates d'inmu, Hakan yasa gwamnati ta d'auki nauyin miyar damu Private School mu uku daga cikin d'aliban makarantar. Babana yaji dad'i sosai saboda ya dad'e yana mafarkin ganin ya kaini private school nida Afrah da Amrah, Nima naji sosai hakan yasa na sake d'aure d'amarar yin karatu sosai har sai inda k'arfina ya k'are. Shigata makarantar na had'u da yara kala kala, wasu 'yan rainin wayone wasu kuma mutanen kirki ne, amma kuma 'yan rainin wayonsu sunfi yawa. Ina zaune ni kad'ai kamar ko yaushe na fiddo chemistry note book d'ina ina k'ara duba wasu equations da akayi d'azu. Wata yarinya ce tayi min sallamah tare da mik'o min hannu don mu gaisa, Cikin mamaki na amsa sallamar nima na mik'a mata nawa hannun muka gaisa, Abunda yasa ni mamaki kuwa dan ban tab'a tunanin akwai irinsu a wannan makarantar ba, tunda naje babu wadda tayi k'ok'arin yimin magana saidai masu bina da kallon banza musamman ma yanda sukaga ina participating a cikin class. Bayan na gyara mata wuri ta zauna ne tace min "sannu", Nima sannun na miyar mata dashi. Murmushi ta sakar min ta sake fad'in "naga kaman You're busy ko? Gashi kuma magana nazo muyi dake". Ajiye littafin nayi nima na miyar mata murmushin nace "babu komai ai, ina maimaita karatun d'azu ne kuma ma na gama, ina saurarenki, Allah dai yasa lafiya". "Ahh lafiya lau karki damu, na kula dake tun shigowarki makarantar nan kinfi son rayuwarki ke kad'ai, baki damu da rayuwar kowa ba, baki da k'awa ko d'aya ko magana bata dameki ba, iyakacinki kawai ki bada amsa idan wani teacher yayi tambaya, kina da k'ok'ari sosai kuma kowane teacher yana alfahari dake, baki dad'e da shigowa makarantar nan ba amma har an fita outing dake kusan sau biyar ko sau shida, kuma duk wata queeze ko debate d'inda zakuje zakiyi winning, shine nake son idan babu damuwa me zai hana mu zama friends? Ba dan komai ba sai dan ki ringa koya min karatu, saboda nidai bana ganewa idan akayi karatu, amma kinga idan ke kika natsu kika koya min zan gane sosai, amma fa idan babu takura". Murmushi kawai na miyar mata dashi, "Babu takura ko d'aya, sai dai matsala d'aya kawai", Kallona tayi tace "matsala? Wace irin matsala?", "Nidai kinga ba d'iyar kowa bace ba face *'yar talakawa* (Afrah), bamu da komai sai rufin asiri, yanzu haka school d'in nan da nake gwamnatice ta d'auki nauyina, iyayena sun min nasiha sosai akan na guji yaran masu kud'i saboda natsalace dasu, suna da wulak'anta talaka sosai, Saisa kullum nake ni kad'ai sabda gudun wulak'anci, gaskiya kiyi hak'uri kinfi k'arfina". Kallona tayi sosai hawaye ya fara kwaranya daga idonta, "Mesa zakice nafi k'arfinki? Kin manta cewa da talaka da mai kud'i duk d'ayane a wurin Allah? Wanda yafi wani shine wanda yafi wani tsoron Allah, dan Allah ki daina wannan maganar, nidai bani da matsala ko d'aya kuma ki tambaya kiji, indai har kinji na kwanta miki a rai to kiyi k'awance dani kar kiji komai" tana gama fad'in haka ta goge hawaye. Shiru nayi mun jima babu wanda ya kuma fad'in komai, Saida na nisa sannan nace "to ki bari zanyi shawara da mamana, duk abunda ta yanke zan sanar dake insha Allahu", "To babu komai, ina fatan zata amince saboda nikam kin kwanta min a rai, ina son mutum mai irin halinki, gaki da kamun kai sosai duk mazan class d'in nan babu ruwanki dasu kin huta", "Nagode sosai sai kin jini" na fad'a bayan na sake bud'e littafina, "Au! Shine ba zaki tambayeni sunana ba ko? To tunda baki damu da ji ba ni ki fad'a min naki sunan", Kunya naji sosai nayi mata murmushi, "Sunana Aisha Abubakar amma anfi kirana da Ummimah, kefa?", "Sunana Salmah Abubakar, amma Gentle ake kirana dashi", "Nice name, surname d'inmu d'aya dake kenan?" Na tambayeta, "Ehh kam hakane". Da haka har lokacin dawowa break fast yayi, malami ya shigo akaci gaba da karatu daga inda aka tsaya. K'arfe uku daidai aka tashi kamar yanda aka saba, 'Yar jakata na rataya a kafad'a, na nufi hanyar titi don in samu keke napep in hau. Gentle ce da sauri ta ringa k'wala min kira, daga farko ban jita ba sai daga baya, hakan yasa na dakata na jirata har ta iso inda nake, "Tunda aka tashi nake rarraba idona ta inda zan hangoki, sai daga baya baseerar in biyoki tanan hanyar ta fad'o min, Ina zakije ko tanan ake zuwa d'aukarki?" Bayan nayi mata d'an murmushi nace "keke napep zan tara in tafi". Da sauri tace min "a'a dan Allah karki tari napep d'in nan, kizo gaya can anzo d'aukata, dama neman da nake miki kenan inji idan ba d'aukarki za'a zo ba sai mu tafi dake a ajeki a gidanku". "A'a nidai ki barshi wallahi nagode", "Raina baiji dad'i ba idan baki zo mun tafi dake ba, dan Allah kiyi hak'uri mu tafi". Dafa kafad'arta nayi nace "Salmah kenan, iyayena zasu min fad'a idan sukaga kun bani lift, kiyi hak'uri babu komai wallahi zan hau keke napep d'in dama kullum ita nake hawa". Badan taso ba tace "to shikenan sai anjima, ki gaishe dasu mama" ta tafi, Kallo d'aya za'a mata asan bataji dad'in rashin bintan ba, nima kuma kaina banji dad'i ba, saidai kuma dole babu yanda zanyi sai dai hakan, babana zai iya yimin fad'a sosai kuma yace na fara bin yaran masu kud'i ina son in canza hali irin b'ara rayuwata, wanda kuma sam ba haka bane, kuma na kula da Salmah ko a cikin yaran masu kud'in ma ita batada mugun hali, tanada halin kirki kuma tanada son kyautatawa. Da wannan tunanin na isa bakin titi na tsayar da keke napep na hau. Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [2:16pm, 15/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~31-40~} A gajiye na koma gida, da hanzari Mama ta tarbeni ta karb'ar min jakata ta makaranta kamar yanda ta saba koda yaushe itace take karb'ar jakata idan na dawo daga School. "Oyoyo Aunty Ummimah" shine abunda ya fito daga bakin Afrah cike da farin cikin ganina. Murmushi na miyar mata dashi, "Sannu Afrah, 'yan JSCE, ya jarabawar? Ince dai tayi dad'i" "Tayi dad'i sosai Aunty Ummimah, ashema babu wahala jarabawar haka nan ake sakamu jin tsoro", "Ai dama na fad'a maku babu wahala, ina Amrah ne?" Na tambayeta saboda ban ganta ba. "Amrah na d'aki batada lafiya, kinsanta ita kingin ciwo ce, kullum daga wannan ciwo sai wancan ciwo". "Subhanallahi! Ina zuwa barin dubata" kai tsaye na shiga d'akinmu. Sosai hankalina ya tashi saboda yanda na ganta sai rawar sanyi take, Kusa da ita na zauna har ina jin gumin jikinta, "Sannu Amrah, ashe bakida lafiya". Muryarta na rawa da k'yar ta iya furta "ehh Aunty", "Ayyah sannu kinji? Kinsha magani kuwa?", "Nasha paracetamol sauran wanda nayi amfani dashi last week da banida lafiya". "Gaskiya ya kamata ace an kaiki asibiti Amrah, zama da ciwo bashi da wani amfani, bazai yiwu a ringa ciwo daban magani daban ba, kullum saidai ana d'irka miki pain reliever, kar aje ciwo ya ringa cinki kuma ba'a san kalarshi ba". Shiru Amrah tayi bata kuma cewa komai ba saidai kuma har yanzu jikinta bai daina rawa ba, idonta yayi jajur tsabar ciwo da yake cinta. Muna cikin hakane Mama ta shigo d'auke da School bag d'ita a hannunta, Bayan na karb'a nace "gaskiya Mama ya kamata akai yarinyar nan asibiti, kinga jarabawa sunayi kar ciwo ya hanata zana jarabawarta kuma azo a samu matsala daga k'arshe, kinsan makarantun gwamnatin nan har korarta suna iya yi daga makarantar", "Hakane Ummimah, amma kema kinsan halin da muke ciki, wurin aikin mahaifinki kusan wata biyu zuwa uku kenan basu samu albashi ba, harma an fara tunanin rufe company d'in za'ayi saboda karayar arzik'i daya samu mai company'n ya daina biyan ma'aikatansa albashi, kinga kuwa ina mukaga kud'in da zamu kai Amrah asibiti?". Ajiyar zuciya na sauke, tabbas maganar mama gaskiya ne, amma kuma ai baza'a bar yarinya ciwo ya ringa cinta ba, duk ta jarabawa ma mai sauk'i ce indai tanada lafiya. Ban kuma fad'ar komai ba kawai na fara cire Uniforms d'ina, saboda har an fara kiran sallar la'asar kuma bana son makara Islamiya. Bayan nayi sallah na shirya cikin uniforms d'in islamiyarmu, riga da hijabi milk colour, sai d'an kwali da wando coffee brown, Har na d'auki jakata na hau kan k'aramin gadonmu na fuskanci Amrah da bacci ya d'auka yanzu, Cikin magagin bacci ta jawo hannuna ya shiga cikin nata, tam ta rik'eni kamar da gangan tayi, hakan yasa na k'i cire hannuna daga nata hannun har hud'u da rabi ta kusa muna a haka dan bana son in cire hannuna kuma hakan yasa ta tashi daga bacci. Mama ce ta shigo ta samemu a haka, "Ki tashi ki tafi islamiya mana Ummimah, Afrah har ta gaji da jiranki ta tafiyarta dan kinsanta ita tsoron bulala gareta". "Mama bazan iya tafiya in bar Amrah a haka ba, na fasa zuwa kawai", "To shikenan ai, kekam wannan soyayyar da take tsakaninki da yarinyar nan tayi yawa, zanga ranar da zaku rabu da junanku, ko kuma ranar da mutuwa ta d'auki waninku tabbas zakusha wahala". Wani irin hawaye naji yana bi min kumatu a lokacin da Mama ke wannan maganar, cike da tashin hankali nace "dan Allah mama kibar wannan maganar, muyi mata fatan Allah ya bata lafiya". Da haka har dare yayi, bayan sallar isha Baba ya dawo daga masallaci, Lokacin kuma Amrah ta d'an samu relief dan har ta fito palor amma dai duk da haka batada wata walwala. Bayan Baba ya gama cin abinci ne na masa maganar rashin lafiyar Amrah, "Baba dan Allah idan ka samu kud'i ayi k'ok'ari ko chemist ne a kaita ayi mata awon jini dan a gane ciwonta". "Hakane Ummimah, insha Allahu gobe zan tafi da ita wurin aikina, zan kaita wurin wani uban d'akina wanda a k'ark'ashinshi nake aiki, zan gwada mishi ita insha Allahu indai ya ganta nasan zai tausaya mata, sai ya taimakemu da kud'in da zan kaita asibitin saboda yana da matuk'ar taausayi, ko kud'in dana baki jiya kika biya maku kud'in islamiya na wata biyu da ake binku shine ya bani su ". "To shikenan Baba, Allah ya kaimu goben, Allah kuma ya bata lafiya" na fad'a cike da tausayin mahaifina, saboda nasan duk wata wahala da yakesha duk saboda mune, babban burinshi shine yaga ya sakamu cikin farin ciki, baya so ya gammu muna buk'atar wani abu shi kuma bayada halin yi mana abun". Ummimah ta fashe da kuka bayan tayi wannan maganar. Barrister Sultana ta kalleta sosai sannan tace "bazan hanaki kuka ba Ummimah, saboda bansan abunda aka miki ba, ban kuma san dalilin kukan ba, amma dan Allah ki daure kici gaba da yimin bayani ko zan samu bayanin da nazo nema a wurinku". Bayan ta share k'wallarta taci gaba da, "washe gari kuwa da sassafe baba ya tafi da Amrah wurin aikinshi, duk da jarabawar da gareta a ranar da safe, Mun yanke shawara akan ni zanje in rubuta mata jarabawar saboda ba lallai bane a iya banbancemu, duk da kamar da Afrah da Amrah keyi amma nafi kamada Amrah, tsaf wanda bai sani ba zai iya cewa nice twin sister d'inta ba Afrah ba, musamman ma yanda na shak'u da ita, duk wata shawara ko matsala da gareni ita nake sanarwa kafin kowa ya sani. Hakan kuwa ta kasance, ni na rubuta mata jarabawar kuma ba'a ganeba har aka gama muka koma gida, Nikam nama manta da maganar Gentle, kwata kwata ban tab'i mama da maganar ba saboda nikam rashin lafiyar 'yar uwata shine damuwata a halin yanzu. Da yamma lik'is Baba ya dawo, kallo d'aya za'a masa asan baya tare da walwala, da k'yar Amrah ta iya sauka daga kan tsohon mashin d'in baba, A hankali take tafiya har suka shigo cikin d'aki, Da sauri na tashi na nufi inda take na rirrik'eta na zaunar da ita akan kujerar dana sauka, ni kuma na zauna k'asa ina kallonta cike da tausayi, "Sannu Amrah, ya jikin naki?", "Alhamdulillah" ta fad'a bayan ta kwanta ta duk'unk'une jikinta akan kujerar. "To Allah ya baki lafiya, sannu kinji? Na rubuta miki jarabawar yau kuma lafiya lau ba'a samu matsala ba", D'aga min kai kawai tayi ba tare data fad'i komai ba, jikinya sai rawa yake, jijiyoyin kanta duk sun tashi, idonta sun k'ara girma sosai dama abunka ga mai manyan idanuwa. "Babansu ya ake ciki ne?" Mama ta fad'a tare da zama kusa dashi, saboda a yanayin data ganshi ciki tasan akwai matsala, amma ita a tunaninta ko kud'in da zai kai Amrah'n asibiti ne bai samu ba. "To lafiya lau zance" ya fad'a bayan ya sunkuyar da kanshi k'asa. Da jin haka gabana ya fad'i, dan nasan tunda baba ya fad'i haka to akwai matsala. "Wanda nake fad'a maku zai taimakeni d'in ya taimaka mana, ya kaimu asibiti kuma asibitin ma ta kud'i, ya biya kud'in duk wasu test da akayi mata, Amma kuma bayan sakamakon ya fito ne hankalina ya tashi, Saboda Amrah tana d'auke da wata cuta a cikin k'wak'walwarta wadda ake kira da *brain tumor,* likitan yamin bayani sosai akan cutar tare da illolinta. Yace min cutace wadda take uncontrolling na cell division na mutum, Cutar bata tsananta ba sosai a jikinta, dan haka yasa mukaga iya alamar hakan a tattare da ita, Idan tayi tsanani sosai tana saka mutum shan ruwa sosai babu control, ya gwada min wani bokiti plastic yace min zata iya shanye baki d'ayanshi ba tare da taji ya isheta ba, sannan kuma fitsari ma babu control zata ringa yinshi, komai dai zai koma mata babu control tamkar mahaukaci, sannan kuma yana hana haihuwa, yayi mamakin yanda cutar ta kama Amrah 'yar shekara goma sha uku, saboda sai manyan mutane take kamawa, yace shi tunda yake ma bai tab'a ganin ta kama mai k'ananan shekaru kamarta ba. Amma da sauk'i tunda abun baikai haka ba, yace min hanya d'ayace wadda za'abi dan ganin cutar batai tsawo kamar haka ba, Saidai idan za'a fitar da ita k'asar waje a fidda mata ita, idan aka fitar da ita kuma akwai wani magani wanda za'a d'orata a kanshi, Duk bayan sati biyu maganin yake k'arewa, kuma an sameshi da sauk'i to dubu talatin da biyar idan ma an samu a k'asar nan kenan saboda maganin Indiya ne ba'a cika kawoshi Nigeria ba, kati biyu ne a cikin wani kwali, duk sati d'aya ake shanye kati d'aya. Wannan maganin shi zata ringa sha har k'arshen rayuwarta saboda ko an cireshi idan ba'a shan maganin to cutar tana iya sake yib dashe a cikin k'walwa, idan ba haka ba kuwa to komai zai iya samunta idan cutar ta tsananta a jikinta". Tunda Baba ya fara wannan maganar nake kallonshi, Ji jake tamkar a mafarki ne da nafi kowa farin ciki. "Yaa Salaam" Mama ta fad'a hannunta dafe a k'irjinta. "Allah gamu gareka, Allah ka fitar damu daga wannan jarabawar" ta fashe da kuka mai cike da tsananin ban tausayi. Mutuwar zaune kawai nayi, kukan baizo ba and i was totally speechless, K'ara kallon Amrah nayi cike da tausayinta, Yarinya k'arama 'yar shekara sha uku ce a cikin wannan hali, Sai a lokacin naji wani irin kuka maras control yazo min, Na d'ora hannuna bisa kai inata sharar kukana, Afrah ma kukan take, Mama kuwa dama tun sanda baba yake maganar ta fara kuka. Shi kanshi Baban hawaye ke zarya a bisa kumatunshi, ya kasa ko rarrashinmu ma, Babban tashin hankalinshi bai wuce inda zai samu har miliyan biyu da rabin da za'ayiwa Amrah aiki ba, kuma ma idan ya samesu ina zai samu kud'inda duk bayan sati biyu za'a ringa siyama Amrah magani?. Ita kuwa Amrah baccinta take batama san abunda ake ciki ba, sai wannan zafin jikin wanda baya yin sauk'i, idan tasha pain reliever ne yake d'an kwanciya na awa d'aya kuma sai ya dawo, ga yawan yin amai da takeyi, wani irin kuka na sake fashewa dashi had'e da rungumarta na mak'alk'aleta har saida ta tashi daga bacci. °•°AKA°•° Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [3:54pm, 16/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~41-50~} A gigice ta farka cike da azabtuwar ciwo, ganin ina kuka yasata k'ara k'ank'ameni itama tana kukan, "Aunty Ummimah ki daina kuka ai naji sauk'i, tunda Baba ya saimin panadol nasha zazzab'in ya sauka, ki kwantar da hankalinki, idan kuna kuka nima sai kisani in ringayi". Wani kukan maras control ya sake fito min da k'arfi, kenan Amrah bata san cutar da take tare da ita ba? Allah sarki baiwar Allah, Allah ya bata lafiya. Fatan da nayi mata a raina kenan bayan na saketa nace, "Barin kawo miki abinci nasan bakici komai ba". Da hanzari Baba ya share hawayensa dan baya so mu fahimci cewa shima kukan yayi, "Ki duba booth d'in mashin d'ina akwai yoghurt na nan ki kawo mata, nasan zata fi buk'atar abu mai ruwa ruwa". Tashi nayi kuwa na nufi inda mashin d'in yake, Bayan na bud'e booth d'in na fiddo yoghurt kai tsaye na wuce palor, Bud'eshi nayi na juye a kofi na fara bama Amrah, Saida tasha kamar rabin kofin sannan na sauke shi k'asa, Kamar tana jirana kuwa sai amai ta fara kwarawa babu sassauci, saida ta harar da komai dake cikinta sannan cike da azabar ciwo ta koma ta kwanta, Hawaye naji sosai suna fita daga idona, Cikin natsuwa na dangwali ruwa a hanky na goge mata bakinta sannan na fara gyara jikina, Har a lokacin Mama da Afrah basu daina kuka ba, kowansu tana tausayin halinda muka tsinci kanmu a wannan yanayi. Bayan na gama gyaran wurin duka na koma kan kujerar na d'ira fuskar Amrah akan cinyata, baki d'aya zazzab'i mai zafi ya taso mata, Kuka nake sosai amma maras k'ara, hawayena ne ya sauka bisa kumatun Amrah, K'ok'arin tashi zaune tayi amma ta kasa, Ganin haka yasa na tasar da ita zaunen ta fuskance ni, "Dan Allah ki daina kuka Aunty Ummimah, na fad'a miki naji sauk'i fa, yanzu ma aman da nayi ne yasa zazzab'in ya sake dawowa". Goge hawayen nayi tare da yi mata murmushin yak'e, itama murmushin tayi sannan ta koma ta kwanta a bisa cinyata, Mama da Afrah kuwa barin d'akin sukayi dan basa so ta fahimci kuka sukeyi. Bayan sati biyu. Zaune muke ina bama Amrah abinci a baki, Kwatsam naji sallamah da muryar mace babba sai kuma d'ayar muryar kamar ta budurwa, A lokacin Afrah ta tafi islamiya Baba kuma bai dawo daga wurin aiki ba, Mama kuma tana d'akinta tana fitar da kayan wanki. Amsa sallamar nayi tare da ajiye abincin a k'asa, "Maraba daku, ku shigo daga ciki". Babbar macen ta fara yi gaba sannan budurwaw ta shigo, Murmushi na saki a lokacin dana Gentle, itama murmushin ta miyar min dashi, Kamarsu d'aya ita da babbar matar hakan ya tabbatar min da mahaifiyarta ce, Sauke Amrah nayi daga bisa jikina na gaishe da matar, "Ahh Salmah kune a gidan namu?, "Wallahi kuwa mune Aisha, na jiki kwana biyu bakizo School ba, shine naje har Principal's Office ya duba min address d'inki, Nayima Momy na bayaninki sai tace zata biyoni mu duba ko lafiya kike, shine fa kika gammu da yammacin nan". Murmushi na mata sannan nace "Amrah baki iya gaisuwa bane?", Jiki babu k'wari ta duk'a har k:asa ta gaishesu, Bayan sun amsa ne Mama ta shigo saboda muryoyin da taji, Fuskarta d'auke da fara'a suka gaisa da Momy, Nayi ma Mama bayaninsu da kuma dalilin zuwansu, Sannan kuma nayima su Gentle d'in bayanin rashin zuwana makaranta, Sun tausaya mana sosai sun kuma tausayawa Amrah, Sai yamma lik'is sannan Momy ta bama Amrah 10k cike da tausayi suka bar gidan. Sosai Momy ta yaba da kirkinsu, hakan yasa ta amince min da yin k'awance da Gentle, koba komai tanada hankali, sannan kuma tanada kula itada mahaifiyarta. Tun daga wannan lokacin kusan kullum sai Gentle ta ziyarce mu, hakan ba k'aramin dad'i yake min ba, Wannan kular da take mana ita ta siye min zuciya baki d'aya, naji Gentle ta kwanta min a rai. Saida mukayi wata d'aya a haka, lokacin har na gama rubutama Amrah jarabawa, hakan yasa na koma makarantata, ammafa rabin karatun da nakeyi hankalina yana gida, ina matuk'ar tausayin 'yar uwata, saboda yanzu ciwon k'ara yawaita kawai yake, kuma gashi babu ko maganar *kud'in aiki* (Raheem and Basmah err lele) barin kud'in magani, saisa a kullum na zauna banida aiki sai kuka. Wata rana cike da murna Baba ya dawo daga wurin aiki, kallo d'aya na masa na gano farin ciki a tattare dashi, Da sauri na karb'i ledar hannunshi, "Balango ne na gani a hanya na siyowa maras lafiya, idan taci sai ta baku sauran", Murmushi nayi na fara bata a baki, Bayan Mama ta shigo d'akin tayima Baba sannu da zuwa, "Nazo maku da albishir mai girma, amma fa sai kun bani goron albishir", Murmushi d'auke a fuskata nace "ka fad'a mana koma menene Baba, zan baka goro babba". "Yanzu na dawo daga wurin likitan da yake duba Amrah, ya tabbatar min da cewa gwamnati ta kawo manya manyan likitoci daga India, wanda zasu duba narasa lafiya wanda suke d'auke da ko wace irin cuta kuma kyauta bada ko sisi ba, zasuyi wata uku sannan su koma k'asarsu, Dan haka ya bani form d'aya na cike da sunan Amrah, nan da sati d'aya zasu fara aiki". Hamdaka muka saki mu duka dake d'akin, harda Afrah da yanzu ta shigo ta tsinci zance, Amrah kam dama bata san ciwon da yake damunya ba, tayi zaton zasu dubata ne kawai akan yawan ciwon da takeyi. Shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakanina da Gentle, ta kaiga bani b'oye mata ko wace irin damuwa haka itama bata b'oye min tata damuwar, Saidai a iya zamana da ita na fahimci sam ibada bata dameta ba, amma dai ina k'ok'arin nunar mata da muhimmancin ibada, Saidai kuma a duk lokacin da zan mata maganar ibada sai ta b'ata rai, wani lokacin ma ba zata sake min magana ba har a tashi daga makarantar. Sam hakan baya sa indaina fad'a mata gaskiya. Yanzu kam mun d'an samu kwanciyar hankali har sati ya zagawo, Baba da Mama da kansu suka kaita FMCK saboda acan ne za'a gudanar da taron likitocin. Likitici biyar suka hau kan Amrah, da manya manyan na'urori suke amfani wanda suke haska mata baki d'ayan k'walwarta, Sun tabbatar da brain tumor ce take d'auke da ita, saidai kuma bata tsananta ba, Dan haka akwai wani gashi da za'a ringa kaita na tsawon wata uku, duk bayan sati za'a ringa gasa mata k'walwarta sannan kuma akwai wani ruwan allura da za'a ringa duba mata a hanci shima dai duk satin ne, Sannan kuma sunma baba bayanin ba lallai bane idan akayi haka cutar ta rabu da ita har abada, amma kuma zata samu sauk'intana wasu shekaru. Duk da hakan Baba yaji dad'i yayi masu godiya sannan suka kama hanyar dawowa gida, Lokacin da Baba yaimana bayani ba k'aramin dad'i mukaji ba, har da sadaka saida Baba yayi duk da shima mabuk'aci ne. Bayan shekara uku ******* Pls kuyi hak'uri da wannan page d'in yayu gajerta, bana jin dad'in jikina ne, luv you all. °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [1:20pm, 17/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~51-60~} A lokacin mun zama 'yan mata cikakku masu jini a jika, Ba yabon kai ba ni kyakkyawa ce koda yake ba saina fad'a miki ba saboda kema kin gani da idonki, Sai a wannan lokacin diri na ya sake fitowa sosai, Samari suka fara kawo min hari amma ni duk basa gabana, Babban burina bai wuce inyi zurfi a karatuna ba, inaso in zama wata mai matsayi a b'angaren education, hakan yasa ko a jamb d'ita na cike Bsc ed. Biology a Talent University Jalingo, Itama Gentle shi ta cike dukda ba shine burinta ba, amma kuma saboda taga hakan nakeso yasa itama tacewa mamanta lallai irin karatu d'aya take son muyi. A duk family d'inmu babu waada baisan Gentle ba, haka itama kag family'nta kowa ya sanni, Maganarta d'aya dai Aisha Abubakar, kullum Ummimah, har wasu daga cikin danginsu itama suke kiranta da Ummimah sabida yawan fad'ar sunan da takeyi. Afrah da Amrah kuwa an girma, yanzu sune suka shiga SS3, mu kuma muna jiran sakamakonmu na jamb ya fito. Bayan sati biyu kuwa ya fito, Alhamdulillah sakamako yayi kyau sabida samu 216, Gentle kuwa 190 ta samu, amma dai lafiya lau babu matsala, saboda 180 akeso ko wane d'alibi ya kawo, Murna a wurinmu ba'a magana, har sadaka nayi saboda wannan sa'ar dana samu, Babana kuwa Alhamdulillah! Yanzu company'n da yake ya d'an tashi, saboda har albashinsu akan lokaci ake basu, dan haka mun saau warwawa sosai. Amrah ta samu sauk'i sosai kamar bata tab'a yin ciwon ba, dan haka muka kasance happy family bamuda matsalar komai duk da talaucinmu bai hanamu sakewa da walwala ba. Cikin mun fara shirye shiryen fara registration ne kwatsam ciwon Amrah ya fara dawowa, Iya tashin hankali mun shigeshi, saboda yanzu ya canja salo ma, harda jini take zubarwa sosai babu cobtrol, ga wannan yawan shan ruwan nata, sannan kuma saurin mantuwa, yanzu za'ayi abu yanzu zata mantashi, Ta zama tamkar tab'ab'b'iya. Hankalim baba ya tashi sosai, hakan yasa ya kama hanyar asibiti ya nufi wurin likitan daya saba kula da Amrah, Bayan ua shaida mashi halin da ake ciki ya dafe kanshi, "Lallai yanzu ina ganin dole sai anyi aikin nan, saboda cutar ta fara zama chronic a jikinta, ina mai shawartarku indai kunada damar fitar da yarinyar nan waje to ku fitar da ita tun wuri ayi nata aiki, saboda inhar kuka zauna a haka da ita tofa zaku iya rasata". Hankalin Baba ya tashi sosai, haka ya kamo hanya ya dawo gida babu nasarah, Cike da tausayin Amrah yayi mana bayanin yanda sukayi da likita, kuma gashi yanzu ma wai kud'in aikin sun k'aru, sun tashi daga miliyan biyu da rabi sun koma miliyan hud'u saboda kud'in jirgi da suka k'aru. "Allahumma ajirnaa fi musibati, wakhlifnaa khairin minha" kawai ke fita daga bakina, da muna murnar Amrah ta samu sauk'i, sai gashi kuma ciwo ya dawo mata. Haka rayuwa taci gaba da tafiya kowace rana sai na karanta mata suratul Yaasiin a ruwa tasha, hakan yasa ta ringa samun sauk'i sosai, amma kuma duk da haka bata daina zubar da jini ba, duk bayan sati biyu sai anyi nata k'arin jini. Da daru da komai na tafi makaranta, da nace bazanje ba saidai inyi asarar admission d'in, nayi niyyar sama in kula da 'yar uwata, Saida Baba ya kirani yace "Bai kamata kiyi hakaba Aisha, wannan karatu da kika samu wata damace wadda bai kamata ki bari ta kufce miki ba, idan kuma kika bari ta kufce miki tofa samun dawowarta ba abune mai sauk'i ba, Kinga da yanda nayi na had'a kud'in registration d'inki, Sannan kuma zamanki a gida ba shine zai warkar da Amrah ba, kiyi hak'uri ki tafi makaranta, ki ajiye hankalinki kiyi karatu, insha Allahu Amrah zata samu lafiya, ki cire duk wata damuwa a ranki, na siyo miki komai da zaki buk'ata suna d'akin mamanku na ajiye jiya dana dawo na samu duk kunyi bacci". Wani irin hawayene ya k'wace min, bana komai bane face na tausayin Babana, ya gwammaci ya rasa komai ya kyautata mana, ya gwammaci ya kwana da yunwa mu kuma ya ciyar damu, ya gwammaci ya k'ask'antar da kanshi ga mutane duk dan ya samu abunda zai rufa mana asiri, lallai iyayenmu abun muji k'ansu ne, bai kamata muna wulak'anta iyayenmu ba, wai har sai kaga yaro babanshi yana magana shima yana magana. Hak'uri Baba ya ringa bani har saida yaga nayi shiru, da yake mutum ne mai barkwanci saida ya sakani dariya sannan yabar d'akin. Bayan kwana uku kuwa na kama haramar shiri, Su Gentle sukazo saboda munyi da ita tare za'a kaimu a motar gidansu, Dan haka da sauri ta shigo tace in fito ana jiranmu. Hak'uri na bata akan tayi min uzuri in jira dawowar Baba, saboda yace in jirashi akwai sak'on da zai kawo min bazai dad'e ba. Ba tare da nuna gajiyawarta ba ta zauna har baba ya dawo, Bawan Alkah ashe waya ce 'yar baby nokia yayo min fafutukarta harda sim card na MTN, Wani hawayen na sakeji amma ban barshi ya fito ba, Har k'ifar gida suka fito rakiyarmu, ciki kuwa harda Amrah dake kukan tafiyata. Shiga motar mukayi gidan baya nida Gentle, kasantuwar driver d'in gidansu ne yasa babu wanda ya zauna a gaba, Suna d'aga min hannu har motarmu ta fita daga kwana. Sai a lokacin kuka ya fito min, Sosai Gentle ke rarrasata amma nak'i uin shiru har sai lokacin dana gaji dan kaina sannan nayi shiru. Kusan awa shida muka d'auka sai gamu a cikin Jigawa, sosai garin ya burgeni saboda yanada kyan tsari sosai, Har cikin makarantar aka kaimu, dama mun kama room dan haka wurin securities na hostel mukaje, number'n room d'in muka fad'a sannan aka bamu key aka shaida mana akwai katifa da gado a ciki. Gentle ta umurci driver d'insu daya tafi kawai, mu kuma muka kwashi kayakinmu muka ringa nufar block B dasu, babban haushin ma wai 3rd floor muke, na tsani hawan bene a rayuwata, Saida mukayi zarya uku sannan muka gama kwasar kayanmu, Salloli na fara gabatarwa, nan ma saida nacema Gentle ta tashi tayi sallah sannan tayi. Aunty Sultana wallahi ban zaton Gentke zata saka min da abunda tamin ba, ashe babu alkhairi a zuwana wannan jami'ar" Ummimah ta fashe da kuka, Koda ta farga ashe Barrister Sultana ma ta dad'e da fara kukan, tun lokacin da Ummimah ke fad'a mata ciwon Amrah ta fara kuka. Da k'yar ta samu ta share hawayen tace "ina jinki kici gaba". "Bayan mun huta na saka wayata a chaji, tana jikin chajin na kunnata, koda na saka layina ashe harda katin dari biyu baba ya saka min, dan haka lambarsa kawai na saka dan inada ita a kaina, Ringing d'aya tayi kuwa ya d'auka, cike da farin ciki yace "'yata Aisha", Murmushi nayi nace "sannu baba, ya gida yasu mama?", "Lafiya k'alau kun sauka lafiya?", "Alhamdulillah baba, mun dad'e da sauka harma mun huta", "To masha Allah, ki gaishe min da Salmah d'in", "To zataji baba, ya jikin Amrah", "Amrah taji sauk'i sosai, gobe ma zamuje a k'ara mata jini", "To baba Allah ya k'ara mata lafiya, a gaishesu duka" nayi hanging up na wayar, na fad'a ma Gentle sak'on Baba na gaisuwa. Haka rayuwa taci gaba da tafiya mana, muna karatu sosai har first semester ta k'are muka koma gida, kasantuwar hutun bashida yawa nan da nan muka koma School, Wannan komawar ce baki d'aya Gentle ta canja halinta, ta xama mace maras kamun kai, duk mazan course mates d'inmu babu wanda bata huld'a dashi musamman ma irin 'yan iskan nan masu sauke wando k'asa. Har ni d'inma ta fara canja min fuska, kuma da zarar na mata magana sai ta nunar da babu ruwana da halinta, inyi irin ruyuwar da nake so itama in barta tayi wadda take so, Wannan canjin da tayi yasa wani lokaci in zauna in yita kuka, Saboda har k'awancen ma ta daina yinshi dani, Ta samu wasu 'yan iska sune abokananta. Wata rana mun tashi lecture 2pm, Tun fitata daga theater nake jiran Gentle ta fito mu tafi amma shiru batazo ba, gashi kuma ina azumi saboda ranar Monday ne, ga rana kuma anayi. Jinta shiru yasa na koma Theater d'in, a tsakiyar maza na sameta sai kashewa suke suna ihu, Jiki ba k'wari na matsa inda suke nace "ke bake jira Salmah kin san azumu nake", Bud'ar bakinta tace "toni ina ruwana da azumin da kikeyi? Nace ki rakani ne iye? Ko kuma bansan hanyar hostel d'in ba?". Da tsawa tayi maganar, tunda nake da ita bata tab'a yimin magana irin haka ba, "Ki tafi ai nima nasan hanya, wannan ma ai kilbibi ne ace wai dole sai tare dani za'a tafi", Shewa abokan nata maza da mata suka saka, bansan lokacinda naji hawaye suna fita daga idona ba, Ban kuma fad'ar komai ba na fita na nufi hanyar hostel ni kad'ai ina mamakin sauyin hali da Salmah ta samu lokaci d'aya. Bayan kwana biyar muka fara second semester exam, sam Gentle bata miyar da hankalinta, karatun ma bata sama barin tayishi. Wata ranar alhamis wadda bazan tab'a mantawa da ita a rayuwata ba, ta zame min bak'ar rana abun gudu ga kowane mutum. Zaune nake ina karatu kasantuwar wata chemistry exam da zamuyi gobe jumu'ah, Course d'in yanada matuk'ar wahala kuma gashi 4 unit ne, amma sam ni bana jin wahalarsa saboda na iya kuma bana missing lecture d'in, Gentle kuwa ban tab'a ganinta ta zauna lecture d'inshi ba, ko magana na mata saidai ta bini da bak'ar magana. Ji nayi bazan iya zama ba ita kuma bata iya ba dan bana son ta fad'i a course d'in. Block A na tafi nemanta wurin wata k'awarta amma k'awar ta bini da kallon banza, Saida ta gama sannan tace "ta tafi wurin saurayinta AK" ta fad'a tak'aice. D'aukar hanyar fita daga hostel d'in nayi na nufi inda naga masu samari suna tsayawa fira. *_ina miki murnar kammala novel d'inki mai suna DAWA ZANYI KUKA?, tabbas kin cancanci a yaba miki saboda novek d'in yayi ma'ana sosai, Allah ya k'ara miki baseerah Aunty'nmu (Sdy Jegal)_* °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [2:25pm, 18/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* _Da gudu na taho har ina cin tuntub'e saboda makarar da nayi wurin mik'a jinjina tare da yabon gwanata kuma namesyna *Futhatul-Khair* akan daddad'an littafinta mai taken *k'awata kishiyata,* da jin sunan ma ba sai an fad'awa mutum kalar ma'anarsa ba, dan haka na tayaki murna, sannan kuma na miki fatan Allah ya k'ara miki baseerah da kaifin ido #onelove#_ {~61~} Fitilar hannuna na ringa haska motocin gaban gate d'in, amma kuma duk wadda na duba babu Gentle a cikinta, Dan haka na k'ara matsawa daga gaba ina hahhaskawa still dai babu ita, Cike da tashin hankali na kashe fitilar wayar tawa, na latsa kiranta saidai kuma naji ana shaida min da babu kud'i kona flashing a wayar, Hankalina ya k'ara tashi, kamar zautacciya na ringa k'wala mata kira amma shiru ne. Har kusan Faculty of Humanities naje da yake shine daga gate d'in hostel babu nisa saishi amma babu ita, Motoci biyu na hanga daga can nesa aikuwa babu shamakin komai na doshi wurinsu, Dalle fitilar nayi ata farkon amma sai samari matasa na gani cike da motar, zasu kai kimanin mutum takwas zuwa goma, harma mamakun yanda motar ta d'aukesu nayi, Hak'uri na basu sabida naga kamar basuji dad'in haskewar ba. "Ke ubanme yasa kika haskemu da fitila? Ko mu sa'anninki ne?" Wani daga cikinsu ya tambayeni cike da muryar maye, alamar yasha ya bugu sosai. "Kuyi hak'uri 'yar uwata na fito nema ne, nayi zaton ko itace anan" na fad'a cike da tsoronsu bayan na doshi inda d'ayar motar take. Basu kuma cemin komai ba har na isa wurin d'ayar motar, Haske cikinta nayi saidai kuma banyi sa'ar kallo ba, Saboda mace da namiji ne a bayan motar sunata aikata alfasha gasu tsirara haihuwar uwarsu, "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!" Kawai na fad'a cike da tashin hankali, saboda sam basa cikin hayyacinsu sun lula can wata duniyar. Har nayi shirin juyawa zan tafi naci tuntub'e da takalmi, Haskawa nayi saboda harda shirin kadani yayi, Cike da mamaki na kalli takalmin na k'ara kallonshi, "Wannan ai takalmin Gentle ne" na fad'a a fili bayan na tsuguna k'asa ina k'are mashi kallo, Daga cam gefe na hangi gyalenta da d'ankwalinta, "Ya Salam" na sake furtawa saboda sam ganin abun nake kamar a mafarki. Tamkar bana cikin hayyacina na koma jikin gilashin motar na ringa bubbugashi da k'arfi, saboda ni a tunanina kota k'arfi da yaji ne aka turata cikin motar. Duk bubbugawar da nakeyi shirune sabida har yanzu basu dawo hayyacinsu ba, K'afar takalmin nata d'aya na fara bubbuga gilashin dashi take kuwa suka zabura su duka biyun a tare, Da sauri mazan dake cikin waccan motar sukayi wurina, "Waike wace irin sakaryar yarinya ce? Ubanme kike a wurin nan? Ina ruwanki dasu?" Wani daga cikinsu ya fad'a kamar zai fad'o min, Saurin matsawa nayi gefe hannuna aka ina tsala ihu ina fad'in "jama'a ku taimaka mana, sun tura 'yar uwata a cikin mota", Kasantuwar babu giccin kowa yasa babu wanda yajimu, Da hanzari cike da kunya macen ta miyar da kayan jikinta bayan namijin ya sauka daga gareta, Fitowa daga motar sukayi su duka biyun suna tambayar abunda ya faru. Gaba d'aya wutar kaina ta d'auke lokacin dana d'ora idona akan Gentle sai rarraba ido take tana fad'in "wai miye haka kukeyi Khalifx? Muna tsaka da jin dad'inmu zamu nemi tsayar damu" har a lokacin bata kula dani dake gefe ba ina binta da kallon mamaki. Cike da tashin hankali nace "Salmah! Kenan da saninki kika shiga motar nan ake aikata alfasha dake?", K'are min kallo tayi ta tabbatar da nice sannan cikin halin ko in kula tace "Ehh da sanina ne sai kuma me? Ke Aisha bari kiji in fad'a miki, tun wuri ki fita daga sabgata idan ba haka ba kuma wallahi ni kad'ai nasan matakinda zan d'aukar miki". Kallonta nayi cikin ido saboda an kunna security light na cikin makarantar, "Kiji tsoron Allah Salmah, ki sani iyayenki da suka kawoki makarantar nan fa sun damk'a miki amanar kanki, idan kikaci amana kuwa sai amana ta kamaki, zina Salmah? Wal'iyadhu billah! Da idona na ganki kina aikatata, sam banyi tsammanin halin naki har yakai haka ba" na fashe da kuka sosai ina k'ara mamakin Salmah. Cike da izgili namijin da suke masha'ar tare yace "To wai ita wannan wacece ne Gentle? Taya zaki baru tana fad'a miki magana anyhow?", Ban ko kalleshi ba saboda banga abunda zan kalla ga mazinaci ba, Dan haka na koma gareta, "Kin cuci iyayenki kin kuma cuci kanki, kiyi gaggawar tuba ga Allah saboda Allahu gafurur-raheem ne, idan kika bi sharud'd'an tuba mai yiwuwa ne ya yafe miki". "Ke wai ina ruwanki danine? Idan ma abunda yafi zina nayi ina ruwanki? Kija k'azamin jikinki ki k'ara gaba" Gentle ta fad'a cike da masifa. "Ke har kinada bakin kiran jikina da k'azami? Ai babu babban k'azamin jiki bayan na mazinata, ko kun manta Allah mad'aukakin sarki yace "wala taqrabuz-zinah", Karma mu kusanci zinar barin har mu aikatata, dan haka dan Allah kiyi hak'uri ki rabu da wannan yaran, Salmah ki koma halayyarki ta baya wadda kika baro gidanku da ita" na k'ara fashewa da kuka ina k'ara tuno k'awancenmu da ita tun ss1. "Aisha Kibar wurin nan tun kafin in d'aukar miki mataki" ta sake fad'a tana kallona cikin ido. "Bazan tafi in bar wurin nan ba Salmah sai idan tare dakene, ki d'auki duk matakinda saki d'auka dan bazan iya tafiya in barki ke kad'ai ba saboda zaku iya komawa kuci gaba da aikata mugun aikinda kuke kanyi". Kyakkyawan mari saurayin nata ya d'aukeni dashi, Take na ringa ganin bishi bishi kamar zan fad'i k'asa, Dakewa nayi na had'iye hawayen daya fito min, na k'udura a raina bazan tafi inbar Salmah a wannan halin ba. "Ka k'yaleta AK, nasan maganinta" ta fad'a tare da sake juyiwa ta fuskanceni, "Wallahi sai nasa anyi miki fyad'e matuk'ar baki bar wurin nan ba". A wasa na d'auki abun saboda wannan maganar ban tab'a zaton zata fito daga bakinta ba, kuma ni nayi zaton b'acin raine ya sakata fad'in haka, Dan haka naci gaba da tsayuwa ina jiranta tazo mu tafi. "Khalifx kuyi mata fyad'e kuma na rok'eku karku sassauta mata, nasan zaku iya ku jata kukai dajin can inda babu haske" Gentle ta fad'a tare da komawarta cikin mota itada saurayin nata wanda naji ta ambata da Ak. Kamar wasa wannan k'artin suka ringa jana da k'arfin tsiya suna k'ara turani cikin daji, Hankalina ya k'ara tashi sosai ganin da gaske suke abunda Gentle ta sakasu suyi min shid'in zasuyi. Ihu nake sosai ina fad'in "Ya Allah ka kareni daga sharrinsu, Baba, Mama kuzo zasu rabani da *martabata* (Ummi Aisha), amma shiru sabida wurin ihunka banzane saboda babu wanda zai iya jina. Samari takwas saida sukayi min fyad'e, idan wannan ya gama sai wannan yazo yayi babu sassauci, Gashi kuma cike da rashin imani sukeyin abun, sosai nake jin azaba, tun ina ihu har ihun ma ya daina fita sai sabbatu da nakeyi wanda bansan abunda nake fad'i ba, Bayan mutum takwas d'in sun gamane na k'arshen yace "Manu saura kai, kazo ka gama da ita mu kaita mu jefar, sabida babu alamar ma tanada rai". Sama sama nake jin maganganun nasu, Wanda suka kira da Manu yace "haba ai wannan rashin imanin naku yayi yawa, taya zakuyiwa yarinya fyad'e har ku takwas? Tunda nake a rayuwata ban tab'a jiba ko a labarai, dan wannan yarinyar ma bana tunanin tana numfashi, gaskiya ta mutu kuma doke zata mutu, gardawa takwas ba wasa ba", "Kai wawane matsalata dakai Sarki Manu, komai kai kace tausayi, an fad'a maka a iskanci akwaa tausayi ne?" Wabi daga cikinsu ya fad'a. "Aini kasan duk iskancina bana yiwa mace dole, sai idan ita ta amince tace taji ta gani sannan nake mu'amala da ita, sab'aninku da aikinku kenan yima yaran mutane fyad'e" wanda suka kira da Sarki Manu d'in ne yayi wannan maganar. Duk abunda akeyi na zama niba rayayyaba ba kuma matacciya ba, Allah dai ya bani ikon sauraren maganganunsu amma kuma ko idona bana iya bud'ewa. "Shikenan ai ku d'uketa ku jefar cikin dajin nan, saboda da alama dai ta mutu wannan gawace", Ina jin sun fad'i haka gabana ya tsananta bugawa, Sai jin muryar Manu naji yayi yace "a'a karku jefarta cikin daji dan Allah, ni ku barni in kaita daga can gefe, yanda za'a iya ganinta cikin sauk'i sai a sallaceta". D'aukata kuwa yayi yakai daga can gefen titinda zai zartar da mutum cikin humanities, a hankali ya ajiyeni tun daga nan baccin wahaka ya d'aukeni wanda ban kuma sanin inda kaina yake ba. _masu karatu dan Allah kuyi hak'uri da wannan, mura nake fama da ita duk ta kashe min jiki, da k'yar na samu nayi wannan ma._ _Jinjina maras adadi gareki 'yar uwa mai albarka my dear Xarah bb, tabbas kin zamo wani jigo a rayuwata wanda bazan iya misaltashi ba, a kullum burinki shine kiga kin faranta min rai, wannan dalilin yasa nima nake k'ara jaddada miki yanda kike a rayuwata, kinada muhimmanci sosai a gareni, na gaisheki sosai da duk wasu masoyana na nesa dana kusa, *Amrah luvs you much.*_ °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ . NWA [11:47pm, 18/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~62~} Farkawa nayi na ganni kwance a bisa gadon asibiti, A hankali na fara bud'e idona saidai kuma idon yak'i bud'uwar tsabar kumbura daa yayi, Sannu sannu na fara tariyo abunda ya sameni wanda yakr mummunan abu ne, Kuka na fasa da k'arfi tare da mimmik'ewa a bisa gado ina fad'in "Baba! Mama!! Shikenan sun rabani da martabata, sun keta min mutuncina wanda ko wace mace take tutiya dashi, wayyo Allah Babana!" Na rintse idona sosai ina k'ara tuno yanda suka ringa yi dani. Cike da natsuwa wani likita ya shigo hannunshi rik'e da file, Sallamah yayi idona rintse na amsa sallamar, "Alhamdulillah anyi ta barka tunda kin tashi, sannu ko?" Likitan ya fad'a tare da zama bisa kujerar da aka tanadar domin zaman likitoci idan sun ziyarci maras lafiya. Jin ya zauna yasa a hankali na fara k'ok'arin bud'e idona, Idon ya bud'e saidai ba duka ba, saboda wani irin mugun kumburi ne yayi. "Sannu kinji Aisha?" Ya fad'a tare da ajiye file d'in akan cinyarshi. Kai kawai na d'aga bayan na gyara kwanciyata, ina mamakin yanda akayi har yasan sunana Aisha. "Ya jikin naki?" Ya sake fad'i kyakkyawar fuskarshi d'auke da murmushi, "Alhamdulillah" kawai na fad'a a tak'aice, "To masha Allah! Ina fatan dai kinsan abunda ya sameki", Ban bashi amsa ba sai wani irin kuka dana sake b'arkewa dashi ina k'ara duba kayan dake jikna, saboda harsu ji nayi na tsanesu baki d'aya. "Anyway, an kawoki asibitin nan ne kwana biyar da suka wuce, daga School Clinic akayi refer d'inki zuwa wannan asibitin a lokacin tamkar baki da rai, saboda ma an fidda tsammanin zaku rayu, Ganin ciwonki kamar yafi k'arfin clinic d'inku saboda manyan likitocin naku duk sun tafi hutu basu dawo ba yasa aka kawoki nan, Ina so ki ajiye hankalinki ki saurareni, karki sake yin kukan nan ki danganawa Allah komai, saboda dukkan abunda kikaga ya samu bawa to muk'addari ne daga Allah, babu wani bawa wanda yafi k'arfin k'addara, dan haka ki saurareni da kunnen basira zan miki bayanin komai". Kai kawai na d'aga masa, ammafa hawayen dake fita har yanzu na kasa tsaidashi daga sintirin da yake a bisa kumatuna. Medical glasses d'inshi ya cire ya sak'alashi a lab court d'in daake jikinshi, Ya k'ura idonshi cikin nawa, da sauri kuwa na duk'ar da kaina k'asa, sabida wani irin k'warjini naji yamin, "Bayan nurses na makarantarku sun kawoki na karb'eki emergency nida abokina Dr. Khalid muka fara duddubaki, Saidai kuma bamuyi tunanin ciwonki ba, kawaidai mun karb'eki ne muka fara yi miki gwaje gwaje inda a take muka gane cutar hawan jini datayi miki sabon kamu dan da alama bata wuce kwana d'aya da kamaki ba, Bayan mun gamane kamar ance in kalla kawai naci karo da jini a bisa cinyoyinki, baku d'aya cinyar tayi sharkaf da jini harda gullamarsa. Hankalina ya tashi sosai nace da Dr. Khalid "kaga babbar matsalar yarinyar nan", Sosai mukaji tausayinki, nan da nan muka fara duddubaki inda mukaci karo da raunuka sosai a k'asanki wanda tunda nake a rayuwata ban tab'a ganin ko mai kama dashi ba, Na tabbatarda wannan fyad'e ne akayi miki, kuma ba wai mutum d'aya ko biyu ne sukayi aikin ba, saboda yanayin wurin ya rarake sosai da sosai. Bansan lokacinda na fashe da kuka ba saboda kin matuk'ar bani tausayi, sannan kuma gaki yarinya k'arama baki wuce 17 ba amma an lalata miki rayuwa, Aune aune mukayi sosai anan muka tabbatarda baki d'auke da kowace irin cuta, kawaidai raunukan ne da kikaji, Harga Allah banyi tunanin zakiyi rayuwa ba, Ganin yawan jinin da kika zubar yasa nayi miki awon jini nan na tabbatarda bakida jini sosai, Dan haka na d'ibi nawa jinin kasantuwar zan iya badashi ga kowa na saka miki, A tak'aice dai kwananki biyar a asibitin nan kuma bakya cikin hayyacinki, shine yanzu wata nurse tazo gittawa taji muryarki kina sabbatu ta kirani, Naji dad'i sosai da kuka tashi sabida jinki nake tamkar 'yar uwata ta jini, saboda duk abunda zai samu wani ko wata sai mutum yayi tunani idan ga wani nashi abun ya faru ya zayyi? Saisa akeso mutum ya zama mai tausayi da jink'ai ga mutane baki d'aya". Har ya gama maganar kaina na bisa k'irjina ban sauke ba, sai wani irin rad'ad'i da zuciyata keyi had'e da tafarfasa, Na rasa me zanyi inji dad'i, k'asana kam baya ciwo sosai saboda yamin alluran kashe zafi, Kaina sai azabar ciwo yake yana min barazanar fashewa, Sunan Allah kawai nake ambato saboda yanayin da nake jin kaina kamar bani ba. "Inaso kibar wannan al'amarin a hannun Allah, shi yasan wanda suka miki wannan abu kuma shi zai saka miki, abun yazo da sauk'i tunda babu cutar data sameki, ki daina kuka kinga har hawan jini ya sameki, ina miki gudun kar tashin hankali yasa zuciyarki kamuwa da wata cuta har tayi silar rasa numfashinki". Cike da k'arfin hali nace "Likita mutuwa itace babban burina a halin yanzu, banida sauran wata martaba, an wulak'anta min rayuwa, ina fatan mutuwa tazo ta tafi dani akan wannan halin da nake ciki", Cikin sigar rarrashin yace, "Ki daina irin wannan maganar Aisha babu kyau kace kafison ka mutu, yana d'aya daga cikin imani fa wato mutum yayi imani da k'addara mai kyau ko maras kyau, dan Allah ki lallab'i zuciyarki, ita k'addara bata tab'a tsallake bawa, Allah yasan halinda kike ciki kuma shi zai saka miki". Cike da gamsuwa da maganarshi nace "babu komai likita, na yarda cewa wannan *k'addarata ce* (My dear Zarah bb), na barma Allah komai shine kawai zayyi min sakayya" na share hawayena da tafin hannuna. Sallamah mukaji anyi tare da bud'e k'ofar d'akin, Zarah da Rabiatu ne suka kunno kai a cikin d'akin, room d'insu shine kusa da namu sannan kuma suma course mates d'inmu ne, Tun lokacinda Gentle ta fara sake hali wurinsu na fara komawa saboda sunada kyawawan halaye irin wanda nakeso k'awayena su kasance dasu, Wani lokacinma idan Gentle bata kwana a hostel ba room d'insu nake tafiya in kwana, suma myn shak'u dasu amma ba sosai ba. D'aga kai nayi na kallesu bayan sun shigo likita ya amsa sallamarsu, File d'inshi ya d'auka sannan ya miyar da gilashinshi yace "Allah ya k'ara sauk'i kinji", "Ameen" na fad'a a hankali tare da miyar da kallona gasu Zarah. Cike da tausayi Rabi'atu ta kalleni ta kawar da kanta daga gareni saboda kukan daya kufce mata, Zarah ce tayi k'arfin halin cemin "sannu Aisha ashe kin tashi", "Ehh na tashi yanzu" na bata amsa, "To ua jikin naki?" Ta fad'a cike da tausayi, "Da sauk'i". Rabiatu ta juyo bayan ta goge hawayen itama tamin ya jiki, Zarah tace, "Kamar wasa fa a ranar da dare muka jiki shiru har sha d'ayan dare bakizo d'akinmu ba, bayan kuma kin saba koda ace ba wurinmu zaki kwana ba kina shigowa ki mana saida safe, Jin shirin yasa muka lek'a room d'inku amma babu kowa a ciki, Zaman jira mukayi dan a tunaninmu ko kin tafi toilet, Shiru dai har dare ya nitsa sosai saiga Gentle ta shigo, Da sauri ku a tare muka mik'e Rabi'atu tace mata "tun d'azu muke nan zaune muna jiran 'yar uwarki bamu san inda ta shiga ba". Tsaki kawai tayi ta kama hunce kayanta ko a jikinta, Kallon Rabiatu nayi itama ta kalleni, "Dan Allah ki mana magana ko hankalinmu zai kwanta, kin san inda taje?", Cike da zafin rai tace min "kai daallah malamai ku shafa min lafiya, gata nan na nad'a a kaina nayi gammo da ita sai ku sauke", Cikin k'arfin hali nace mata "Me yayi zafi Gentle? Hak'k'in zaman tarene ai, dan Allah kiyi hak'uri ki sanar damu inda take idan kin sani". Bud'ar bakinta tace "wallahi idan baku shafa min lafiya ba kuma zansa a maku yanda akayi da ita". Hankali tashe muka fita daga d'akin bamu sake furta komai ba, Iya tashin hankali mun shigeshi, a daren ranar a rintse babu wacce ta rintsa a cikinmu, Dan haka washe gari muna gama sallar asubah muka fita nemanki, Mune har block C muna nemanki amma babu ke babu alamarki, Dama kuwa bamuyi tunanin zamu sameki acan d'in ba, saboda munsan ke ba mutum bace mai yawon zuwa wuraren mutane, A hargitse muka fita bakin gate d'in hostel, A lokacin har gari ya fara haske, Securities d'in gate muka tambaya ko sun ganki amma duka amsar d'ayace basu ganki ba, Wani Baba mai fad'a sosai nasan kin ganeshi, To harda cewa yake wai "wata k'ilama yawon iskancinta ta tafi shine zakuzo kuna wani nemanta", Wallahi ya bani haushi sosai har saida naji kamar in makeshi in huta, Da haka muka fita daga area'r hostel d'in baki d'aya muka tinkari humanities. A can gefen titi muka hangi mutum dunk'ule kamar marsa rai, Cikin tsoro muka fara takawa har muka isa wurin, Dubawar da zamuyi kuwa sai mukaga ashe kece, Gaki kwance male male cikin jini kamar an d'iba an zuba miki, Hannuwa muka d'ora aka muna neman agaji, Can muka hangi wayarki da 'yar purse d'inki a gangarenda zai shigar da mutum dajin nan, Bamu jira komai ba Rabiatu ta sab'eki a kafad'a mukayi School clinic dake, Su kansu hankalinsu ya tashi saboda jinin da sukaga yana fita daga jikinki kamar an bud'e famfo, Ganin abun yafi k'arfinsu yasa aka sakaki a mota muna biye dasu aka kawoki wannan asibitin, Ni na fad'a masu sunanki nayi signing a wata takarda sannan likitan daya fita d'in nan shida wani guda suka hau dubaki, Kullum sai munzo amma mu tayar baki farfad'o ba, saidai kuma likitan yana k'ok'arin kwantar mana da hankali ganin yanayin halinda muke cikinsa, Mun sanar da Gentle abunda ya sameki amma tsaki kawai tayi ko a jikinta, Yanzu haka fitowarmu kenan daga exam d'in Bio1203, kuma munma HOD na Biology complain cewa bakida lafiya, yace idan kinji sauk'i ki sameshi za'asan yanda akayi ayi miki". Nannauyar ajiyar zuciya na sauke bayan Zarah ta gama bani labari, na j'ara tsanar Gentle sosai a raina, Sai yanu nake dana sanin amince mata ta dama k'awata, ga irin muguntar data bini da ita, Na k'ara tuna nasihar da Babana yayi min akan in guji abotaka da yaran masu kud'i, bawai duka aka taru aka zama d'aya ba, amma kuma wasu daga cikinsu basu da tarbiyya. Gashi kuwa na gani da idona, naga kalar k'etar da babbar k'awata ko ince aminiyata tayi min, To ba anan kad'ai abun ya tsayaba Aunty Sultana, duk ta wannan ma mai sauk'i ne akan wasu abubuwan. °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [3:22pm, 20/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~63~} Bayan sati d'aya na fara jin sauk'i, har zama na farayi sab'anin da da ko zaman ma bana iyawa, Sosai Dr. Rafiq yake bani kulawa, komai shi yakeyi min, hatta da magani da kanshi yake siyamin ya bani ruwa insha, K'awayena Zarah da Rabuatu kuwa tamkar 'yan uwana na jini, duk wani abu daya dace suna yiminshi, Abun haushi kuwa har yanzu Gentle batazo da dubani ba. Kwatsam ina zaune Rabiatu da Zarah na gefena, labari muke sosai suna bani dariya, hakan yasa hankalina yad'an kwanta, a gidanmu kuwa har yanzu basu sani ba, saboda Dr. Rafiq yace kar in fad'a masu abunda ya sameni harsai idan na koma gida dan kar in tayar masu da hankali. Securities ne suka shigo roon d'in har mutum hud'u, bayansu kuwa wani babban mutum ne sanye da babbar riga, Bayan shigowarshi saiga wasu securities d'in guda hud'u a bayanshi. Cike da girmamawa muka gaishesu, Mutumin kawai ya amsa sallamar, tun bai rufe baki ba saiga wasu manyan mutanen sun shigo masu yawan gaske, har room d'inma bai iya d'aukarsu ba wasunsu a bakin k'ifa suka tsaya. Hankalina ya tashi sosai ganin manya manyan lecturers d'inmu ne, Kallo suka bini dashi baki d'aya kafin sukayi min ya jiki, Wancan mutumin wanda ya fara shigowa ya gyara zamansa a plastic chair d'inda yake zaune yace "Aisha Abubakar ko?" Cike da mamaki na d'aga kaina alamar ehh, "Good" ya fad'a tare da zaro wata 'yar takarda daga aljihunshi na gaba. D'an rubutu yayi sannan ya mik'ata ga wani yace "PA a ajiye min wannan" sannan ya juyo gareni yace "Ya jikinki?" Alhamdulillah na furta cike da alamar tambaya. "Karki damu ba wata matsaka bace kinji, sunana Khalil MA Khalil" ya furta tare da mik'ewa tsaye yabar d'akin, Securities d'inshi ne suka nara masa baya sannan sauran malamn ma suka fita. "Ya Salam" na fad'a sabida jin sunanshi, Da fitarsu Zarah tayi ajiyar zuciya tace "VC nefa da kanshi yazo dubaki Ummimah, lallai kin ciri tuta, wata k'ila sun samu labarin abunda aka mikine sukazo dubaki", Rabiatu tace "To a ina zasuji labarin? Ke VC fa, wa zai fad'a masa? Kiga gayyar da sukayi fa". Nidai saurarensu kawai nake amma fa sam hankalina bai kwanta da zuwansu ba. Bayan kwana biyu aka gama exam aka rufe School baki d'aya, A ranar nima na nemi sallamah, saboda Zarah da Rabiatu bana son na shiga hakkinsu, sunce wai ba zasy tafi su barni ba. Babu yanda Dr. Rafiq bayyiba akan inyi hak'uri in k'ara samun sauk'i amma kuma na nace sai ya sallameni, hakan yasa ya bani takardar sallamah tare da kud'i masu yawa yace inyi kud'in mota. ***** K'arfe hud'u na rana na sauka Katsina, Akwatina naja tare da tsayar da mai napep nace ya kaini Saulawa, Babu b'ata lokaci kuwa muka isa gida. Cike da farin ciki Afrah ta tareni, jakata ta karb'a tare da kaita d'aki, "Afrah ina sauran 'yan gidan ne?" Na tambayeta bayan ta zauna tana min saanu da zuwa. "Sun tafi sukai Amrah asibiti, booking zasuyi mata, insan ance wai nanda wata biyu ko uku indiyawan nan zasy dawo". Harda tsalle nayi dan murna, hakan yasa na fama ciwona sabida har yanzu raunukana basu gama warkewa ba. Saurin duk'ewa nayi ina matse matse, Da tausayi Afrah tace min "Bakida lafiya ne Aunty?" Kai kawai na d'aga mata alamar ehh, "Ayyah! Sannu gashi kuma kun gaji, kiyi wanka kafin nan na kawo miki abinci, nasan su Baba ma yanzu suna hanya saboda tun safe suka tafi". Haka na tashi jiki babu k'wari na nufi toilet, Har ga Allah naji dad'in bayanin Afrah, Bayan nayi wanka na jiyo muryar su Mama, Aikuwa da sauri na saka kayana na nufi parlor ko mai ban shafa ba. Har k'asa na gaishe dasu Baba, Sunji dad'in ganina sosai Baba yace "Wannan zuwa na bazata, baku fad'a mana zaki dawo ba ai", "Ehh Baba, nafison nayi surprising nakune dama", "Gashi kuwa kinyi ai hankalinki ya kwanta" mama ta fad'a tana kallona. Baba ya k'ara yimin bayanin komai, Naji dad'i sosai na matsa inda Amrah take, "Sannu k'anwata, ya jikin naki?", "Jiki da sauk'i Aunty Ummimah, ya karatu?", "Alhamdulillah, Allah ya baki lafiya". Bayan naci abinci nayi tunanin in fad'a masu abunda ya sameni amma kuma na fasa, Da zarar nayi k'ok'arin fad'i sai wata zuciyar ta haneni, Hakan yasa nayi shiru nabar maganar a cikina dukda cimin rai da takeyi. Idan ma zaune nake na tuno da wannan abu sai hankalina ya tashi, kuka sosai nakeyi ni kad'ai ba tare da kowa ya sani ba, Wata rana ina cikin yin kukan Mama ta shigi ta sameni a haka, Sallamah uku tayi amma duk bansan tayi ba, K'arisowa ciki tayi ta ganni inata sharar kuka, Hankalinta tashe ta tsuguna kusa dani tace "Ummimah lafiya? Me sameki kike kuka?". Zabura nayi tare da share hawaye ina fad'in "Babu komai mama", "Kamarya babu komai? Babu komai shine kike kuka?" Gyara zama tayi sannan tace "Nasan babbar matsakarki itace ciwon 'yar uwarki, dan Allah ki cire wannan damuwar, insha Allahu k'arshen cutarta ya kusa zuwa, saboda muna sa ran nanda wata uku indiyawan nan zasu dawo, kuma wannan karen ance zasu iya tafiya da marasa lafiya a k'asarsu, kinga kuwa insha Allahu Amrah ta kusa rabuwa da cutarta har abada". Goge hawaye nayi nace "Shikenan Mama, Allah ya bata lafiya" na fad'a kamar da gaske abunda ya sakani kukan kenan. Murmushi tamin nima na miyar mata dana k'arfin hali, "Kizo Afrah ta gama girki, nasan kina jin yunwa", Tashi nayi nabi bayan Mama har parlor. Satina biyu a gida Mama tamin maganar Gentle, gar saida gabana ya fad'i data ambata min sunanta, "Naji Salmah shiru kema kuma bakije inda takeba, Allah yasa dai lafiya", Gabana ya fad'i na rasa abunda zan fad'a mata, sai daga baya nace "Ta fad'a min cewa ba'a garin nan zatayi hutu ba, wai Kaduna zata tafi" nama Mama k'arya, "Ahh to babu komai ai, Allah ya dawo da ita lafiya" "Ameen" na amsa mata dashi cikin raina kuwa wata irin k'unar rai nakeji, saboda yanzu babu wadda na tsana a doron k'asa kamar Salmah". Sannu sannu har hutunmu ya k'are na fara haramar yin registration, Da k'yar da wahala Baba ya samo min kud'inda zanyi, Koda naje banki zan saka kud'in abun mamaki da zarar an saka password d'ina baya bud'uwa, An gwada kusan so biyar amma portal d'ina yak'i ya bud'u, Zarah na kira a waya na fad'a mata abunda ke faruwa, "Wannan ba matsaka bace, akwai sauran lokaci kuma kinsan akwai table payment, ki bari a koma School sannan kawai ki biya acan, kinsan dama bank payment d'in nan matsalace dashi". "Hakane k'awata, to nagode sosai". Da haka na kashe wayata tare da ajiyeta k'asa. Sati d'aya daya zagayo na fara shirin komawa, Su Mama sunyi mamaki da sukaji nace masu ni kad'ai zan tafi, Sallamah nayi dasu na nufu tashar mota, Babu b'ata lokaci muka sauka cikin garin Jalingo. Wurin biyan kud'in naje, Abun mamaki ki acan d'inma babu sunana, Abu wasa ba wasa ba har maganar taje sama, Anan ne aka tabbatar mun da anyi expeling d'ina from the University, saboda kamani da akayi da zubar da cikin shege, An samu takardar asibiti wadda ta tabbatar da hakan, sannan kuma likitan daya dubani da kanshi shi ya tabbatar daa hakan. Take jikina ya d'auki rawa, bakina ya kasa furta komai, kaina ya ringa jujjuya min, lummm na fad'i k'asa sumammiya. _ayi hak'uri da wannan, ina fama da ciwon idone fitinanne, ina buk'atar addu'arku._ °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [11:40pm, 22/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~64~} _Na tayaki murnar kammala wannan littafin naki wanda ya ilimantar gamida fad'akarwa, lallai littafin *HARAMTACCEN ZAMA* ya kawo darussa da dama, fatana a kullum Allah ya k'ara miki baseera 'yar uwata ko ince aminiyata *(Rabiatu sk msh AKA Babymsh)* #onelove#_ ***** Tun daga nan ban k'ara sanin abunda yake faruwa ba, sai farkawa nayi na ganni kwance kan gadon asibiti, gefena Zarah da Rabiatu ne sunyi tagumi suna jiran tsammani. Kallo d'aya na masu suka bala'in bani tausayi, domin kuwa na k'ara tabbatarda sune k'awayena na gaskiya wanda suke k'aunata. Basu ankara da farkawata ba saidai shesshek'ar kukana sukaji, Da hanzari kuwa suka mik'e tsaye, Rabuatu ta furta "Alhamdulillah tunda kun tashi, sannu Aisha", Kai kawai na d'aga mata ina hawaye sosai saboda k'ara tunowar da nayi wai yau nice aka kora daga makaranta, an cuceni kuma an hanani kuka. Zarah ta zaro d'an kwalinta daga kanta dake cikin hijabi ta mik'o min "Bana son kina kukan nan Aisha, ya kamata ki d'auki k'addara saboda *KOWA DA K'ADDARARSA,* ba wai Allah baya sonki bane yayi miki hakan, kawai dai *JARRABTARKI KENAN* kuma ina fatan zakiyi k'ok'arin ki cinye wannan jarabawar, Wanda suka cuceki kuma ki barsu da Allah shi zai miki sakayya, kiyi fatan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a gareki, ungo wannan ki share hawaye" ta mik'o min d'an kwalin nata. K'arba nayi na fara share hawaye saidai kuma da zarar na share sai wani ya fito, Da k'yar na iya furta "Babu komai k'awayena, na yarda na kuma d'auka cewa *K'ADDARATA CE* banida hanyar maganceta, na barwa Allah komai saboda shine zai saka min, dan Allah wace asibiti nake?" Zarah tace "inda aka kawoki ne last time, munje School clinic ank'i karb'arki sunce saboda wai ke yanzu ba student bace". Saurin mik'ewa nayi dukda ciwonda duk gab'ob'in jikina suke min, "Na gwammaci in mutu akan in zauna a asibitin nan, Zarah mesa kuka kawoni nan? Kunsan kuma irin sharrinda suka k'ullamin, su da kansu suka rubuta takardar k'arya cewa an zubarmin da ciki, basu fidda takardar gaskiya ta cewa fyad'e akamin ba" na k'ara fashewa da kuka bayan Rabiatu ta rungumeni a jikinta itama kukan take sosai tana k'ara jin tsanar Gentle a ranta, saboda tasan duk sharrintane da makircinta. Duk maganganunda mukeyi ashe a kunnen Dr. Rafiq ne, shigowa yayi jiki babu k'wari ya nufo inda muke tsaye har yanzu ban saki Rabiatu ba, "Ka fita daga nan bana son ganinka, kai mugune kuma munafuki, ka munafurceni ka gwadamin kai mutumin kirkine ashe ba haka bane sai naga sab'anin haka, ka fita kafin in fasa maka kai da kwalbarcan" na nuna kwalbar malt dasu Zarah suka kawo min. "Nasan zayyi wahala ki yarda dani, amma dan Allah inaso ki ajiye hankalinki ki saurari bayaninda zan miki" ya fad'a bayan ya k'ariso inda muke, "Ki koma ki zauna har yanzu jikinki bayyi k'wari ba". Cikin zafin rai na saki Rabiatu, a tsiwace nace "Bazan saurarekaba Dr. Saboda bakada abunda zaka fad'a min in yarda dakai, wallahi ka bani kunya, ka shirya k'arya kanaji kana gani bayan kuma ga gaskiya, to an koreni kun samu abunda kuke so, sai kuji dad'inku da kyau kaida wanda suka sakaka" ina gama fad'in haka na jawo hijabina na saka, Hanyar fita na kama ina kallon yanda Dr. Rafiq yayi shiru alamar yaso in saurareshi amma sam nak'i bashi damar yin magana saboda babu abunda zai fad'a min in yarda dashi. Bin bayana Zarah da Rabiatu sukayi, Purse d'ita Rabiatu ta bani tace "Anata kiranki daga gida, ban d'aukaba saboda bansan abunda zan fad'a masu ba, bana son tayar masu da hankali". Karb'a nayi na zaro wayar daga ciki na danna kiran Baba, Bugu d'aya ya d'auka hankalinshi tashe yace "Aishatu ince dai lafiya kike, tun jiya nake kiranki inji ko kin sauka lafiya", Gabana ya fad'i sosai na k'irk'iro murmushi, "Na sauka lafiya Babana, wayar na jefa a cikin jakata can k'asa, sai yanzu na ganota", "To masha Allahu, dama sauka lafiyar ake fata ai, ina Salmah kun had'u ko?", Har wayar da Baba ma ji nayi bana so, tsinke wayar nayi kawaa naci gaba da kukana tare da kashe wayar baki d'aya. Bayan mun bar asibitin kai tsaye makaranta muka wuce, A bakin gate na tsaya su kuma suka shiga ciki domin su kwaso min kayakina, Ina nan tsaye saiga wata mota tayi parking a daidai bakin gate d'in kasantuwar ba'a barin mota mai tint shiga cikin harabar makaranta, Gentle ce ta fito sanye da irin skirt d'in nan bak'i mai b'arka doguwa daga gabanshi, sanye take da riga 'yar k'arama orange bakin hannu da kwalar rigar anyi ado da burberry bak'i, sai tad'an yafa d'an kwalin after dress k'arami, Babu wanda zaice ita bahaushiyace sai idan dama ya santa, Dariya had'e da shewa ta d'auka a lokacinda taga ina kallonsu, Cike da b'acin rai na kawar da kaina daga garesu itada saurayinta. A cikin hakane su Zarah suka iso, kallo sukabi Gentle dashi Rabiatu ta watsa mata harara, Wata dariyar ta saka bayan sun matso inda muke ita da saurayin nata. "Tunda an koreki ai saiki tattara tsimmokaranki kibar makarantar saboda ba anan aka haifi uwarki da ubanki ba, sai a koma aci gaba da cin k'anzo da tuwon dawa, Ai dama na fad'a miki nafi k'arfinki, wanda ya fikima nafi k'arfinsa, Talent University tamuce mu keda ita, saboda malaman cikinta namune kaf mun gama dasu, tun daga junior har senior lecturers d'in, ke har senate mun gama da 'yan cikinta saboda damu suke damawa". D'aga hannu nayi na d'auketa da kyakkyawan nari saboda maganganun da sukemin sun isa haka, Kanta ta d'ago ta kalleni cike da mamaki tace "Ni kika mara Ummimah?", "An mareki d'in wacece ke da ba za'a marekiba? Ki sani yanzu ni ba d'aliba bace a makarantar nan, inada damar yi miki komai ba tare da naji haufin wani abuba, idan kikaci gaba da fad'a min magana kuma in k'ara miki wani". Saurayin natane ya d'aga hannu da nufin rama mata, Dakatar dashi tayi tareda fad'in "K'yaleta Bash, nasan maganinta", Ta juyo gareni "Ke kuma sai kinyi regreting d'in marina da kikayi, ba gida zakije ba? Ki tafi" tana gama fad'in haka ta wuce cikun School abunta, shima saurayin nata yabi bayanta. "Karki damu k'awata, babu abunda zaki gani a gida sai alkhairi, kar kiji komai ki rabu da ita Allah ya fisu" Zarah ta fad'a cikin sigar rarrashi. Hak'uri sukaci gaba da bani har lokacinda keke napep tazo ta sauke wasu, tsayarmin da ita Rabiatu tayi, Da kuka muka rabu dasu, har mukabar wurin suna d'aga min hannu, Saida sukaga tafiyarmu sannan na hangesu sun shiga cikin makaranta. Wani sabon kukan ne naji yana saukomin, Mai napep d'in yace "Baiwar Allah kiyi hak'uri ki daina kukan nan, tunda na d'aukoki kike kuka kar wani ciwon ya kamaki", "Karka damu bawan Allah, kaidai kayi aikinka" na fad'a cikin muryar kuka. Tashar mota ya kaini babu b'ata lokaci kuwa na samu motar Katsina, Mun jima bata cikaba kasantuwar yamma tayi babu matafiya sosai, Sai wurin k'arfe biyar sannan motar ta tashi. K'arfe tara da rabi na dare muka shiga Katsina, Nice banje gidaba sai kusan goma da rabi kasantuwar abun hawa da yake wahala idan dare yayi, A bakin gidanmu napep ta saukeni, Saidai kuma mutane dana gani mak'il k'ofar gidan, Har shiga kanta da k'yar na sameta, Duk wanda ya kalleni saiya gyad'a kai wasu suna hawaye. _Alhamdulillah! Nagode sosai da addu'o'inku masoyana, yanzu kam nagode Allah na samu sauk'i, idona ya fara warkewa, da wanda suka kirani a waya da wanda suka min addu'ah ta chart duk ina godiya musamman aminiyata *ZARAH BB,* nagode once again._ °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [5:33pm, 23/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~65~} Ganin kallonda ake bina dashi yasa duk na tsargu, nayu tsaye a k'ofae gida kasantuwar babu hanyar shiga, Ganin nayi tsaye yasa wanda ke baki k'ofar duk suka daddare kowa yana kallona, Saurin shigewa gidan nayi gabana sai fad'uwa yake hankalina ya matuk'ar tashi, Da sauri na shige naci karo da Baba yana kuka sosai kamar k'aramin yaro, Hakan ya k'ara tasar min da hankali matuk'a, Wurin Baba na isa tare da gurfanawa k'asa ina kuka, "Baba mefaru? mesa k'ofar gidanmu yake a cike? Mesa kake kuka?" Duka a tare na jefa masa wannan tambayoyin. Bakinshi na rawa yace "Aishatu 'yan fashine sun..." ya kasa k'arisa maganar kasantuwar kuka da yaci k'arfinsa. "Baba me 'yan fashi sukayi? Dan Allah kamin bayani ka daina kukan nan" na fad'a hankalina a tashe. Hannunshi ya d'aga ya gwada min inda aka harbeshi, sai kuma raunuka dake bisa kanshi wanda ban kula dasuba tun shigowata tsabar tashin hankali sai yanzu. "Na rasa mesa sukazo wurinmu, ni nayi zaton ko saa masu kud'i 'yan fashi ke zuwa inda suke, sai gasu nan gidan sunzo mana" Baba ya fad'a bayan ya dafe kanshi saboda wani irin sara masa da yayi, "Sannu Baba, inma a haka abun ya tsaya ai angode Allah" na fad'a cike da tausayin Babana. "Ba anan ya tsayaba Aishatu, akwai matsala babba, sun d'aure Afrah da Amrah sun tafi dasu..." tun bai rufe bakiba na mik'e tsaye ina kallon Baba, "Sun tafi dasu Baba? Wallahi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffaraba wannan cinne ne, turo manasu akayi wallahi Baba" na k'ara fashewa da wani kukan ina tunanin furucin Gentle na k'arshe, "Lallai babu wanda zayyi wannan aikin sai ita, ko tantama babu itace" na fad'a a bayyane dukda a zuci naso maganar ta tsaya. "Wacece ita? Me kike fad'a ne waima?" Baba ya tambayeni a rikice, Samun kaina nayi da kasa fad'a masa sai wani irin kuka da nakeyi zuciyata sai tafarfasa take. "Ki fad'a min abunda yake ranki Aishatu, bai kamata kiyi shiru ba, waima meya dawo dake daga makaranta bayan kuma jiya kika tafi? Ko kin samu labarin abunda ya faru yau d'in ne?". Shiru nayi k'irjina saa dukan uku uku kawai yake, Hankalina ya k'ara tashi, "Baba zan maku bayani amma ka bari sai mutanen nan sun lafa, sirrine tsakanina daku iyayena". Da gudu na k'arisa d'akin mama, na samu d'akin cike da mata sai jaje ake masu, hakan yasa na j'ara fashew ada kuka bayan na rungumeta ina sauke ajiyar zuciya, Itakam babu abunda ya sameta alamar basu tab'ata ba kenan, A kid'ime ta janyo fuskata ta kalleni dan a tunaninta ko Amrah ce, saboda bata tab'a zaton zata ganni a wannan lokacin ba. "Mama ashe abunda aka mana kenan, sun tafi mana da Amrah da Afrah, shikenan mama sun gama damu" na sake fashewa da wani kukan. Sosai mutanen d'akin suka tausaya mana, wasu na hawaye wasu kuwa tagumi sukayi kowa da kalar tunaninsa, babban abun mamakin bai wuce yanda kowa yasanmu mabuk'atane amma kuma wai bama b'arayi masu yawi da sanda ba, 'yan fashi masu amfani da binduga sune sukazo gidanmu. Sau wuraren sha biyun dare sannan mutane suka gama watsewa, hakan yasa Baba ya dawo d'akin mama ya samemu kowa da abunda yake sak'awa, kuka kuwa babu mai rarrasar wani. Inda muke ya zauna ya dafa min kafad'ata, "Komai yayi zafi maganinshi Allah, sannan kuma dukkanin tsanani yana tare da sauk'i haka Allah mad'aukakin sarki ya fad'a a cikin littafinsa mai tsarki, dan haka dan Allah ku daina kukan nan, bana son wata cuta ta sameku a dalilin haka, insha Allahu Afrah da Amrah zasu dawo garemu". "To muna fatan haka Babansu, Allah ya tabbatar" mama ta fad'a tare da share hawayenta. Jikina na rawa na fara labarta masu duk abunda ya faru tun daga farko har k'arshe babu abunda na b'oye masu, Hankalinsu ya k'ara tashi sosai, sun tausaya min kuma suma sun tabbatarda Gentle ce tayi wannan aiken, Babbar matsalar yanda take d'iyar masu kud'i, mun tabbatarda ko munkai maganar ga hukuma babu abunda za'ayi masu. Yanda mukaga rana haka mukaga dare, ko rintsawa babu wanda yayi a cikinmu, sai koke koke dake tashi wanda har Baba kukan yake yana k'ara tausayawa rayuwata, saboda yanzu shikenan an rabani da martabata. Washe gari da sassafe Baba yaje yayi reporting maganar ga 'yan sanda, A tak'aice dai saida akayi sati biyu babu ko labarin su Amrah, gashi kuma yanzu har indiyawanda zasu duba Amrah sunzo, likitanta yayi waya yace a kaita za'a nata aiki dan yayi masu bayanin komai, hakan ya k'ara tayar da hankalinmu, muka rasa duk wata natsuwarmu, Gashi kuma hukuma ta kas ayin komai akai, Har tadin maganarma basu sakeyi ba dukda cikakken bayani da Baba ya masu tun daga abunda Gentle tasa akamin har 'yan fashinda suka tafi da k'annena biyu. A ranarda suka cike sati biyun ne aka tsinci gawar Afrah a daidai kwanarda zata shigarda mutum layinmu, Mutanenda suka tsinci gawar natane suka kawota nad'e cikin buhu jina jina, Bayan sunyi sallamah da Baba ya fitane suka shaida masa avunda suka gani, Amma kuma basu tabbatarda cikin 'ya'yan Baba bane kawai dai sunyi hasashen hakan ne, kasantuwar fuskar duk jinice kallo d'aya ba za'a iya gane ko waye ba. A rikice Baba ya k'wala mana kira nida Mama, Koda jin kiran muka tabbatarda ba lafiya ba, Dan haka muka fito k'ofar gida hankalinmu tashe ko d'an kwali ban nema ba. Bayan ya bud'e buhun ne ya janye yalwataccen gashin Afrah da duk ya b'aci da jini daga bisa fuskarta, Baki d'aya fuskar tayi dameji, Kayan jikintane ya k'ara tabbatar mana da d'aya daga cikinsu ne, *Afrah ko Amrah* saboda mun kasa banbancesu, Jiki na rawa Mama tace "Ko tantama babu Afrah ce, wallahi Afrahta ce wannan, saboda wannan kayan sune a jikinta, Amrah kuma blue shaddace ta saka ba wannan atamfarba". Bansan lokacinda na fasa wani irin ihu mai k'arfi ba, inda buhun yake na tsuguna ina kuka sosai ina k'ara kallon yanda fuskar Afrah ta koma, Tam! Na rik'e buhun ina sauke ajiyar zuciya bayan na nemi hawayenda nake na rasa, Duk abunda ke faruwa har yanzu Baba ya kasa furta komai, Saidai kuma kallo d'aya za'a masa aga tashin hankali k'arara a fuskarshi. Muna cikin haka ne wani mutumi yazo, a biye dashi wasu gardawa ne majiya k'arfi, Cike da izgili mutumin yace "Na gaji da hak'uri nikam hak'urina ya k'are, Dan haka yauyau d'in nan zaku barmin gidana, Shekara biyu kenan ana kan ta uku rabonka da biyan kud'in haya, Dan haka dole ku nemi wurin zama kubarmin nawa yanzu", Kallon gardawan yayi yace "Hame ku shiga ku firfito masu da kayakinsu". Da hanzari kuwa suka shiga, mu kuwa kallon mamaki kawaa muka bisu dashi, Rashin imaninsu ya matuk'ar d'aure mana kai, Basu ko dubi halinda muke ciki ba amma suka ringa jifa da kayanmu, Hakan ya tabbatar min da cewa wannan ma aikene daga Gentle. K'ara mukaji da k'arfi Baba ya fad'i k'asa, Da sauri Mama ta matsa inda ya fad'i d'in tana kiran sunanshi, "Abubakar, Abu dan Allah ka tashi, karka tafi ka barmu a daidai lokacinda muke buk'atar taimakonka, dan Allah ka tashi.." kuka yaci k'arfinta. °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [3:36pm, 24/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~66~} Duk kukan da mukeyi baisa mutanen sunji tausayinmu ko d'aya ba, Cike da rashin imani suka ringa watsi da baki d'aya kayakinmu, Ga gawar Afrah cikin buhu ga kuma Baba da yake kwance baya ko alamar numfashi, Kukanma nemanshi nayi na rasa, sai mama daketa ambatar sunan baba amma har yanzu ko alamar motsi bayayi. "Ku tashuwa min daga k'ofar gida bana son ganinku, idan ba haka ba kuma a wulak'antaku cikin unguwar nan" mutumin mai gidan hayar ya fad'a cike da izgili da gadara. Mutanen da suka kawo gawar Afrah d'aya daga cikinsu yace "Kai kuwa bawan Allah ka tausaya masu mana, bakaga hakinda suke ciki ba? Ka barsu suji da d'aya mana, tunda dai kasa an fitar masu da kaya ai sai ka shafa masu lafiya haka, tunda mai gidan nasu ma gashi nan kwance bama asan halin da yake ciki ba". A wulak'ance yace "Babu ruwana da halinda suke ciki, gidana kawai na sani kuma na basu minti goma subar harabar nan, idan kuma basu bari ba duk abunda na masu su suka ja". Cikin rashin tsoro na tashi tsaye, Ko alamar kuka babu a idona na dubeshi ido cikin ido nace "Kaga malam ka kama kanka, na kula kai baka da tunani kuma baka san darajar d'an adam ba, Munfi k'arfin ka wulak'antamu wallahi, Sannan kuma duk halinda ka tayar damu daga Allah ne, bawai dan Allah baya sonmu bane kaga ya barmu a haka, Jarabtace kuma babu wanda yafi k'arfinta, Kaima bakafi k'arfin Allah ya jarabceka ba". Dariya ya k'yalk'yale da ita tare da fad'in "'Yan mata Kenan, dama an bani labarinki tun kafin inzo, wallahi kinji na rantse, idan na tafi na dawo na sameku anan zakiyi mamakin abunda zan maku, ni nafi k'arfin ki fad'a min wannan maganganun marasa dad'i" yana gama fad'in haka ya juya ya tafi, Gardawansa ma suka mara masa baya. Sai a lokacin na sake jin wani irin kuka maras control yazo min, Wannan mutanen su suka ringa rarrashinmu tare da kwashe mana kaya suna kaiwa gidan d'aya daga cikinsu, A gidanshi aka sallaci Afrah, a lokacin har ankai Baba asibiti domin duba lafiyarsa. Bayan ankai Afrah ne muka tafi asibiti, Mukayi sa'a kuwa Baba ya farfad'o, Farin ciki mukayi sosai Mama ta matsa kan gadon ta rik'e hannunshi, Da k'yar yake iya bud'e idonshi sai hawaye ke fita daga idonshi, A hankali ya iya bud'e bakinshi tare da furta "Ku yafemin nasan tawa ta k'are, Wanda suka zalunceku ku barsu da Allah shi zai maku sakayya, Ku rik'e addu'ah a ranku kamar yanda Baffa da Hassu suka rik'i addu'ah kuma tayi masu jagora a cikin *Dodon Jatau,* duk wanda ya rik'i addu'ah baya tab'ewa, Sannan duk wanda yazo neman aurenki Aishatu karki b'oye masa abunda aka miki, bana son zalunci ya shigo ciki, Idan kika fad'a masa yaji zai iya aurenki shikenan, idan ba zai iyaba kuma sai kici gaba da neman zab'in na gari". Kuka muke sosai nida Mama har babu mai rarrasar wani, Da k'yar baba yaci gaba da fad'in "Ku kuka da rayuwarku, kuyi k'ok'arin rik'e babunku, kar ku jefa kanku a wani hali saboda abun duniya" tari sosai yaci k'arfinshi, Jini ne yabi bayan tarin saigashi gullama gullama yake fita abun tausayi, Salati muka d'auka nida mama, hakan yasa shima baba ya d'auka yanayi, Muna direwa shima yana direwa, bai iya furta komai ba sai ajiyar zuciya da yayi wanda shine fitar ranshi. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Kawai muke fad'i nida Mama. "Bai mutuba wallahi da ranshi, likita! Likita kazo ka tabbatar mana da Abubakar bai mutu ba, nasan bazai tab'a tafiya ya barmu ba" Mama ta k'ara fashewa da kuka. Bayan likita ya shigo ya tabbatar mana da Baba ya mutu, hakan yasa muka k'arfafa kukan namu, Da k'yar muka fita daga d'akin saboda gadon da gawar baba take mama ta rik'e da k'arfin gaske tana kuka. Sai washe gari aka kai Baba, kasantuwar yamma tayi lokacin da ya rasu d'in, ko kafin akai gawar a shiryata ma duhu ya fara. A gidan mutumin daya jagoranci gawar Afrah da Baba muka zauna, Bayan munyi sati biyu zuwa uku a gidanshi a lokacin har mun fara dayayewa ya samar mana wannan gidan da muke ciki anan unguwar Tudun wada, Anan muke rayuwa nida Mamana, sosai kawu Nasiru (wanda ya taimakemu) yake kula damu tamkar 'yan uwanshi na jini, Duk lokacinda nama mama maganar mu tafi wurin danginta kona Babana sai tace a'a, saboda lokacinda zasuyi aure duka danginsu basu soba, Iyayenta sukace inhar ta auri babana to babusu babu ita har abada, A gidansu babama haka akace masa, Sun aminta da hakan sukayi aure sannan suka bari Kaita suka dawo cikin Katsina. Wannan shine labarina, ina fatan zaki taimakemu inhar kinada halin yin hakan, ki k'watomin 'yar uwata inhar tana raye". Ummimah na gama fad'in haka ta fashe da kuka. Mama ta share hawayenta tace "Tabbas duk abunda Aishatu ta fad'a miki gaskiya ne, cutarmu akayi amma an nuna anfi k'arfinmu ta hanyar dukiya, bamuda galihu ko kad'an". Cike da tausayi Sultana tace "Ki daina fad'in bakuda galihu Mama, Allah yana sonku ai, kuma insha Allahu komai ya kusa zuwa k'arshe tunda har Allah ya jefoni a rayuwarku". "To waima waye ya fad'a miki muna cikin wani hali?" Mama ta tambaya saboda abun ya bata mamaki. "Ni kaina ban saniba Mama, ya b'oye kanshi koma waye, Amma kuma yanzu duk ba lokacin wannan bane, Na d'aukar maku alk'awarin zan taimakeku bakin k'arfina, sannan kuma mijina babban Lawyer ne am sure shima zai taimaka min dan ganin mun gurfanar da Salmah a gaban alk'ali". Koda duka duba har dare yayi duk basu sani ba, Da hanzari ta duba wayarta tayi kicib'us da 21 missed calls, Tashi tayi ta masu bankwana sannan ta fita ta shiga motarta tana k'ok'arin dialing number'n Umar mijinta. _gasuwa tare da godiya ga masoya labarin *WATA SHARI'AH* aduk inda suka, nagode da yanda kuke nuna kulawarku gareni musamman 'yar uwata ko ince Aunty'nmu *Ashnur Pyar,* Allah yabar zumunci da zaman tare._ °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [5:47pm, 25/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~67~} Bugu d'aya kuwa Umar ya d'auki kiran cike da zak'uwa yace "Hello wifey" "Honey kamin uzuri dan Allah sai yanzu na kula da kiranka", "Ehh tunanin da nayi kenan dama, ina fatan dai lafiya", "Lafiya k'alau wallahi, ka jini shiru wallahi na jima a inda naje d'in ne, kuma akwai magana sosai sai na dawo, barin d'auko su Hafsa sannan mu wuto gidan da sauri", "Ai su Hafsa tun d'azu suna gida wifey, kuka tayima Hauwa'u wai tunda ba zaki dawo ba ita gida take so, a dole saida naje na d'aukosu", "Oh ni Hafsa ba hak'uri, bari to indawo yanzu gani a hanya", "Ok sai kin dawo" Umar ya fad'a tare da tsinke wayar. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kasantuwar jin matarshi tana lafiya, dama jinta shiru da yayi yasa hankalinshi ya matuk'ar tashi. A jerin missed calls d'inda ta tayar harda na Hauwa, Hakan yasa ta katsa kiranta, Babu b'ata lokaci itama ta d'auka. "Maman Hafsa lafiya dai ko?" Ta tambayeta cikin tashin hankali. "Lafiya k'alau Maman Zarah, na saka wayar a jaka ne ashe a silent take ban sani ba, kin sanmu lawyers da yawon bincike, saisa kukaji shiru ban dawo ba", "To masha Allahu Aunty, Hafsa dai basu yarda sun tsaya ba", "Ehh haka Abbansu ya fad'a min yanzu, bansan mesa ba Hafsa batada yarda, waini gani nayi ga Zarah nasan zasuyi wasa tare ashe bata yarda ba", "Wallahi kuwa, bakiga kukanda tasha ba kamar wacce zan cirewa kai". Dariya Sultana tayi tace "Ai dama dai ku kuka zab'arwa kanku rigimammiya, ga Haydar d'ina d'an albarka yaro shiru shiru babu hayaniya sai natsuwa", Itama Hauwa dariyar tayi "Ai sai shiru shiru d'in, wannan yaron ai saike, yaro sai b'arna da rashin ji? Yau saida ya fasa min kaf k'waina dake cikin fridge, tumaturina kuwa saiya fasa ya fara sha sai ya yar ya sake fasa wani, duk ya gama wulak'anta min kayan fridge, Haydar saike kad'ai Aunty Sultana". Wata dariyar Sultana tayi saboda Haydar ya bata dariya sosai, itama kanta haka take fama da b'arnarshi kullum cikin dukanshi take amma kamar tana tunzurashi. "Aunty Hauwa ai d'an albarkar kenan, danma kun samu ya saka miki albarka a kayan fridge? D'ana yaron kirkine", "Wallahi Aunty Sultana zan kashe wayar nan indai maganar d'ankin nan zakina yimin", "Naji dai Aunty, dama na k'ariso gida yanzu nima, ki gaisarmin da 'yata Zarah, saida safe", "To saida safe, ki shafamin kan Hafsa 'yar albarka", "To Aunty Hauwa zan shafa miki kan Haydar d'an albarka". Murmushi tayi tare da hanginp up na kiran ta miyar da hankalinta ga kwanar gidansu da zata shiga. *** Parking tayi bayan ta shuga gidan, da hanzari Haladu ya iso gareta, hand bag d'inta ya karb'a bayan ya gaisheta, Ciki ta shiga yana biye da ita har suka isa parlor, Bayan ta k'arb'i jakar tayi godiya ta kalli inda Hafsa take kwance tayi bacci hawaye duk sun bushe a idonta, Murmushi tayi tare da furta "Hafsa kayan rigima" ta shiga d'akin mijinta. D'an kishingid'awa yayi yana 'yan rubuce rubuce a wata takarda dake k'ark'ashin wani file, "Assalamu alaika ya Habeebee" ta fad'a cike da soyayya. Kanshi ya d'ago fuska d'auke da murmushi yace "Wa'alaikissalamu ya Habibty", "Sannu honey, ka jini shiru afwan", "Babu komai wifey, ina kika shiga ne kika d'auki wannan tsawon lokacin?" Ya tambayeta bayan ya harhad'a takardun a cikin file, saboda baya had'a aikinshi da kuma kula iyalinshi. "Ka gafarceni Uncle Umar da bayanin da zan maka", Saurin tashi zaune yayi saboda yasan akwai matsala, duk lokacin da Sultana zata kirashi da Uncle Umar to tabbas akwai matsala ne. "Me farune wifey? Allah yasa lafiya" ya furta idonshi kyam a kanta. "Uncle Umar na sab'a maka, ka hanani kula wanda yake turo mana text messages d'in nan amma na kasa hak'uri dole saida na kula, Wadda yake fad'a mana d'in tana cikin wani hali tabbasa tana cikin matsanancin halin, kuma tanada tsananin buk'atar taimakonmu, dan Alkah inaso ka taimaka min mu had'a k'arfi da k'arfi domin k'watar mata fansa". Kallonta ya sakeyi bayan ya rik'e mata hannu cike da soyayya "Anything for you wifey". "Yauwa honey na, sunanta Aisha Abubakar..." ta labarta masa komai tun daga farko har k'arshe bata b'oye masa ba. Ba k'aramin tausayawa Ummimah yayi ba shima, "Lallai ke jaruma ce wifey, kin cika 'yar aljannah, Allah ya bamu ikon taimakonsu", "Ameen mijina na kaina, Allah kar ya kawo ranar rabuwarmu". Murmushi Umar ya mata tare da cewa "Aikuwa dole zamu rabu wifey, akwai ranar da mutuwa zata rabamu". Wata 'yar k'wallah ta d'igo mata take tace "How I wish mutuwar ta d'aukemu tare honeyna, ko kuma ta fara d'aukata, bana fatan ka mutu ka barni saboda bansan yanda zan iya rayuwa idan babu kai ba". Dod'e mata baki yayi yace "ki daina wannan maganar Wifey, lets close the chapter, kije Hafsa na can kwance a parlor ki kaita d'akinsu, Haydar ma yana d'akin Safiyya". "Ok honey" ta fad'a tare da share hawayen daya fara fito mata. Bayan ta d'auki Hafsa ta kai d'aki ta koma d'akin Safiyya ta samu Haydar ya mak'alk'ale Safiyya yana bacci, Ita kuma sai d'an bubbuga bayanshi take itama baccin yana shirin d'aukarta. Kallonsu tayi cike da so, a bayyane ta furta "Allah sarki Safiyya! Akwai soyayya tsakaninki da Haydar, ban san ya zakuyiba idan zakiyi aure". Bud'e idonta tayi tayi murmushi ba tare data furta komai ba. "Yau bacci tunda wuri haka Safiyya? Ko dan bana nan ne?", "Momy kenan, ai idan bakya gidan nan jinshi nake kamar babu kowa a ciki, mun saba kullum wannan lokacin muna tare parlor mun fira, amma kuma yau bakya nan, gashi Hafsa ma k'awar firar tayi bacci tun d'azu". "Hmm! Wallahi Safiyya wata 'yar matsalace ta tsayar dani", "Ayyah Momy, Allah ya warware matsalar", "Ameen Safiyya, kawoshi" ta mik'a hannunta ta karb'i Haydar da jikinshi yayi kace kace da ruwan tumatur duk ya bushe yayi dabbura dabbura. D'akinsu ta kaishi ta saka mishi pyjamas d'inshi sannan ta d'orashi akan baby bed d'inshi blue, Hafsa kuma tana kan nata pink. Bayan ta tofesu da addu'ah ta fita, Kai tsaye alwala ta d'auro ta gabatar da sallolin da ake binta na magrib da isha, tayi shafa'i da wutri sannan tayi addu'ah sosai ta koma d'akin mijinta. Ta sameshi yana kwance yana jiranta, Murmushi ta masa sannan ta isa gareshi tana fad'in "Na gaji wallahi honey" tayi hamma tana kallonshi "Wallahi honey ba zakaji tausayinsu ba sai idan ka gansu, kaga gidan da suke, kaga halinda suke ciki, mamanta fa tace tun daga lokacin da abun ya faru yarinyar bata kuma samun walwala ba, kullum cikin kuka take". "Allah sarki bayin Allah, insha Allahi komai ya kusa zuwa k'arshe, zamu taimakesu sosai bakin k'arfinmu, har School ma zata koma da yardar Allah". "Allah ya yarda mai gidana na kaina" ta kama hannunsa ta bashi peck sannan ta mik'e domin canza kayan jikinta tana mai k'ara son mijinta, tana kuma k'ara jin dad'in yanda yake da taimakon mutane. _Gaisuwa da godiya gareki maman Taslim, ina jin dad'in yanda kike nuna kulawa tare da bibiyar wannan labarin, Allah yabar zumunci da zaman tare, ya raya mana Taslim d'inmu bisa tafarkin sunnah, ameen._ °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [3:51pm, 26/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~68~} Washe gari ta kama ranar lahadi babu aiki, Hakan yasa da sassafe Sultana ta gyara gidanta ta bad'e ko'ina da k'amshi, D'akin su Hafsa ta shiga ta samu Haydar baya nan sai Hafsa kwance a gadonta, hakan ya tabbatar mata da yana d'akin Safiyya. Kai tsaye d'akin Safiyya ta nufa, Ta samu Haydar zaune bisa cinyar Safiyya sai zuba mata surutu yake ita kuma tana dariya. Ganin Sultana yasa Safiyya ta sauke Haydar daga kan cinyarta ta tsuguna har k'asa tace "Ina kwana momy?". Da fara'ah Sultana ta amsa da "Lafiya k'alau Safiyya, an tashi lafiya?", "Lafiya Aunty, ya gajiya?", "Ba gajiya, naje d'akin su Haydar ne na samu bayanan, na tabbatarda nan yayo", "Ehh kuwa nan yayo kam, cikin magagin barci ma yazo, Haydar" ta miyar da kallonta ga Haydar. Hakan yasa ya fahimci inda ta dosa, "Good morning momy" ya fad'a bayan ya duk'a har k'asa. "Morning my boy, ka tashi lafiya?", "Lafiya momyna" ya bata amsa yanayi yana wasa da warwaron hannun Safiyya. "My boy anyi sallah kuwa?", "Ehh momy Aunty Safiyya tasa nayi", "Ok muje ayi wanka" ta d'aukeshi suka tafi d'akinsu. Tashin Hafsa tayi tayi sallah kafin ta gama har Sultana ta gama shirya Haydar. Bayan ta gama shiryasu duka ta fita parlor, dama kuma ta gama had'a break fast tun tashinta daga bacci, Koda ta shiga d'akin Umar ta tayar ya tashi shima har ya shirya, Murmushi k'unshe a fuskarta tace "Barka da tashi mai gidana na kaina". Murmushin ya mata shima yace "Yauwa 'yar aljannah, kin tashi lafiya?", "Lafiya k'alau honey, break fast is ready, kai kawai muke jira", "Alright wifey, idan mun gama akwai maganar da nake so muyi dake", "Ok ba damuwa". Suka fita daga d'akin tare da nufar dining area. Bayan sunyi nat Umar yace "Maganar jiyan nan ce, so inaga kamar ya kamata mu koma gidan tare dake, saboda akwai 'yan tambayoyin da nake so na masu kafin mu shigar da maganar kotu, saboda a tunanina ba zamusha wata wahala ba a wannan shari'ar". "Hakane honey, na shirya dama muje kawai, amma kuma jiya nama su Hafsa laifi, ina so muje tare dasu daga can mu wuce yawo dan in kankare laifina" ta fad'a bayan ta kalli Hafsa ta saki murmushi. "Ok muje?" Ya tambayeta "Ehh muje" ta shiga d'akin Safiyya, Abunda zata dafa na rana ta shaida mata sannan ta fito da sauri saboda su Haydar har sun fita parking area ita kawai suke jira. Kai tsaye gidansu Ummimah suka dosa, A k'ofar gida Umar ya tsaya bai shiga ba, sai Hafsa da Haydar ma a cikin mota basu fita ba, Sallamah tayi tare da jinkirtawa har saida aka amsa sallamar. Kamar jiya ta samu Ummimah tayi tagumi saidai kuma yau babu hawaye, amma kuma kallo d'aya za'a mata a fahimci tsantsar tashin hankali a tattare da ita, Bayan sun gaisa ne tace "Tare nake da mai gidana, Barrister Umar Mohd Bashir", "Ki shigo dashi ciki mana Sultana" Mama ta fad'a had'e da d'an guntun murmushi. Fita tayi kuwa babu jimawa sai gasu sun taho harda su Hafsa, Bayan sun shiga ciki Umar ya gaishe da Mama ta amsa cikin dattako, Ummimah ma ta gaisheshi bayan ta saka hijabinta, Ruwa ta kawo masu a tasa mai fad'i sannan ta koma mazauninta ta zauna. D'aukar ruwan Umar yayi yasha kad'an sannan ya ajiye. "Mama na samu bayanin duk halin da kuke ciki kuma mun d'auki alwashi nida matata insha Allahu zamu taimakeku, kuma da yardar Allah zamuyi nasarah, nazo ne saboda akwai bayanin da nake so na samu daga bakin Aishatu, saboda gobr Monday nake son shigar da maganar kotu". "To babu damuwa Umar, muna saurarenka" Mama ta fad'a bayan ta sauke hannunta daga tagumin da tayi ta fuskanceshi. "Ummimah tambayarki zanyi, A lokacin da aka kaiki asibiti karo na biyu, kin saurari wani bayani daga bakun Dr. Rafiq?". Ajiyar zuciya ta sauke tare da fad'in "Ban saurareshi ba gaskiya, saboda baya da abunda zai fad'a min in yarda dashi duk da insisting da yayi akan lallai sai ya fad'a min amma ban yarda ba". "Kinyi kuskure Ummimah, da kin sani ki saurareshi ai kiji abunda zai fad'a miki, kinga ko nan da mun samu eata hujja, amma babu komai, shi Dr. Radiq d'in d'an can Jalingo d'in ne?", "Wallahi ban sani ba, na dai san wata private hospital ce yake aiki, kuma da alama tasuce shida abokin aikinshi Dr. Khalid", "To yanzu kuna ganin Dr. Rafiq zai iya saurarena idan na sameshi da maganar?", "Bazan iya ganewa ba, saboda na kula Dr. Rafiq munafuki ne, yanada canja magana, kaga dai daga farko ga yanda mukayi dashi, daga k'arshe kuma wai daga asibitin takardar shaidar zubarmin da ciki tazo, kaga kuwa ai babu gaskiya". Kallon Ummimah yayi a karo na farko tare da sauke ajiyar zuciya, "Zan sameshi zamuyi magana dashi, insha Allahu nasan zamuyi nasarah", "To shikenan Uncle Allah ya tabbatar da hakan" "Ameen" duka suka fad'a. Sultana tace "To yanzu ya za'ayi asan address na asibitin?", "Sunan asibitin KADRAQ CLINIC, ba zatayi wahalar ganewa ba, batada nisa da Talent University", "Ok good" Umar ya fad'a bayan ya mik'e tsaye yama su Sultana nuni da su tashi su tafi. Bankwana sukayi sannan suka fita cike da tausayin rayuwar su Ummimah. Royal bakeries duka zarce daga can, suka kwashi ice cream kala kala da chocolates masu yawan gaske sannan Umar ya biya kud'in suka nufi hanyar fita. Suna fita sukaci karo da wasu matasa su biyu a buge da gani sunsha sunyi tatul, Kallo Sultana da Umar duka bisu dashi, "Waiku ya akayi kuke kallonme ne? Ko kun sanmu ne?" D'aya daga cikin 'yan mayen ya fad'a cikin maganarsu ta 'yan maye. D'ayan ma yace "Sai kallonku sukeyi hehe, ga katina ka d'aukeni aiki kaji?" Ya mik'awa Umar complimentry card d'inshi. Da k'arfi d'ayan yaja hannun abokinshi suka k'arisa cikin restaurant d'in, Bin katin da kallo Umar yayi, Degree holder ne kyakkyawa dashi a hoton dake jiki, Ga phone number a jiki da address d'inshi. "Rayuwa kenan, Allah ya shirya mana zuri'ah, kinga wannan matashi dashi da iliminsa amma ya kama sana'ar shaye shaye duk ya wulak:anta rayuwarsa" Umar ya fad'a cike da tausayi yana k'ara kallon katin. "wallahi kuwa honey, Allah dai ya shirya, kawo katin in gani" ta mik'a hannunta ta karb'i complimentry card d'in matashin. "Sulaiman Usman Saraki" ta furta bayan ta kalli katin, "To shi a tunaninshi idan ma d'aukar aikin ne sai a rasa wanda za'a d'auka saishi? Duk mutanen kirkin nan dake neman aiki saishine za'a bama aiki?", "Wallahi kuwa, mu tafi su Hafsa har sun gaji da tsayuwa" suka isa inda suka ajiye motarsu, Purse d'inta ta bud'e ta jefa card d'in sannan suka kama hanyar gida. Har suka isa gida basu daina mamakin 'yan shaye shayen nan ba, suna k'ara tausaya masu. "To yanzu honey ya kake ganin za'ayi? Zamu fara shigar da maganar kotu ne sannan kaje wurin likitan ko kuwa?" Sultana ta tambayi Umar. "Nafi so mu fara shigar da maganar har sammaci akaima su Salmah sannan in fara duk wani bincike" ya bata amsa. Kamar Sultana tana son yin magana sai kuma ta fasa, Safiyya ta kawo masu abinci sukaci kafin nan la'asar tayi ta shirya Hafsa domin zuwa islamiyya. _Gaisuwa gareku 'yan k'ungiyar *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* Allah ya k'ara zumunci yabar zaman tare. #onelove#_ °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [3:38pm, 27/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~69~} Washe gari da sassafe suka kama haramar zuwa aiki kamar yanda suka saba, Kai tsaya Gobarau academy duka zarce sukayi dropping d'in Hafsa sannan suka wuce nasu aikin. Kasantuwar weekend akayi aiki ya taru masu sosai a Office musamman ma Umar, hakan yasa bai shigar da maganar ba sai washe gari, Safiyar talata kam babu b'ata lokaci ya shigar da case d'in su Ummimah, aka kuma ce nan da sati d'aya za'a shiga kotu. Sosai Sultana taji dad'i ta kuma shirya ta tafi gidan su Ummimah dan ta shaida masu halin da ake ciki. Masinjan kotu aka aika gidansu Gentle dan yakai sammaci, saboda koda aka fad'i sunanta da sunan iyayenta kowa ya ganeta, saboda babanta sananne ne sosai kuma yanzu haka ya fito takarar d'an majalissar tarayya. Kai tsaye gidan Alhaji Abu Abu ya dosa, Sallamah yayi a tangamemen gate d'in gidan amma shiru ba'a amsa ba, Saida yayi sallamah sau uku sannan mai gadin gidan ya fito yana taunar asuwaki, Hannu masinjan ya bashi suka gaisa sannan yace "Meke tafe dakai bawan Allah?", "Sak'o ne daga kotu, sammaci ne akace a kawowa masu gidan nan". Cike da mamaki mai gadin ya karb'i takardar, "Sammaci?" Ya tambayeshi. "Ehh sammaci ne, dan Allah a tabbatar da anbawa masu gidan wannan takardar" masinjan ya fad'a tare da juyawa ya tafi. Kai kawai mai gadin ya kad'a sannan ya zarce cikin gidan domin ya basu takardar. Bayan yayi sallamah yaga Ladi mai aiki tana mopping, mik'a mata takardar yayi yace 'ta bama yallab'ai' sannan ya tafi. Saida suka fito karyawa sannan tace "Hajia wai ga wannan mai gadi ya kawo yace a bama yallab'ai", Bayan ta karb'a tace "Alhajina gashi", Murmushi ya mata yace "Bud'e ki karanto min inji". A zahiri kuwa ta karanto cewa 'sammaci ne daga kotu ankai k'arar 'yarsu Salmah bisa laifuka da dama'. "What!?sammaci? 'Yata aka kai sammaci?", Itama Hajiyar tsaye ta tashi tace "Lallai wannan munafurci ne? Salmah dake makaranta abunta hankali kwance shine dan rainin hankali za'a kaita k'ara?", "Ko tantama babu wannan cinne ne daga mak'iyana, suna so inji kunya akan takarar da zanyi ne", "Kaga wai Aisha Abubkar sukayi k'ararta, ga sunan nan a jiki" Momy'n Gentle ta fad'a bayan ta mik'a takardar cike da mamakin wannan al'amarin. Karb'a yayi yace "Wacece wannan? Aisha?" Tun bai rufe bakinshi ba momy tayi caraf tace "Na gane ko wacece, k'awartar nan d'iyar matsiyata ce, saisa tun farko na hanata k'awance da ita amma ta nace lallai sai tayi ita dai tana sonta, wato duk alkhairan da Salmah ta mata da wannan abun zata saka mata? Lallai d'an adam abun gudu ne". Cike da b'acin rai Alhaji yace "Kenan ma 'yar matsiyata ce ta kai 'yata k'ara? Lallai kuwa reshe zai kife da mujiya, saboda duk abunda take nufinta dashi gareta zai koma, wallahi na rantse sai na d'auko lawyer wanda duk k'asar nan babu kamarshi, sai na nuna masu nafi k'arfinsu, su d'in banza!" Ya rofar da yawu bisa center carpet yace "Sai kun wulak'anta I promised" ya jefar da takardar k'asa. Mamaki sosai uwar keyi ta d'auki wayarta ta latsa kiran Gentle, bayan ta d'auka ne ta shaida mata duk abunda ya faru, Taji tsoro sosai amma a zahiri ta nuna al'ajabinta akan al'amarin, Harda kukan munafurci tace "kinga illar talakawa Momy, ba irin maganar da baki fad'a min akan kar inyi k'awance da Ummimah ba amma na nace sai nayi, kinga abunda ta bini dashi ko momy?" Ta k'ara fashewa da kukan munafurci, da haka suka kashe wayar bayan uwar ta shaida mata cewa sati mai zuwa za'a fara zaman kotu, dan haka ta hanzarta dawowa gida saboda babanta yace zai d'auko mata babban lawyer, Dukda hankalin gentle ya tashi amma sai ta samu sassauci jin lawyer za'a d'aukar mata. Sosai take mamakin yanda akayi su Ummimah suka samu lawyer wai harma sukayi tunanin kai k'ararta kotu. Wani shu'umin murmushi tayi tare da furta, "Mugun abunku gareku zai koma maku, wallahi sai kun k'ask'anta, wato na sarara maku kwana biyu shine zaku d'auki wannan matakin ko? Zakuyi regreting" ta katsa kiran d'aya daga cikin 'yan iskanta, Umurtarshi tayi da yaje gidansu Ummimah ya k'ona baki d'ayanshi, yanda zasu mutu kuma ba za'ayi zargin kowa ba saidai ace gobara ce sukayi, Da wannan shawarar ta kashe wayarta tana ci gaba da muguwar dariya mai d'auke da ma'anini kala kala. Shi kuwa Umar sosai ya miyar da hankalinshi ga bincike, yaje Jalingo har asibitin su Dr. Rafiq, amma bai sameshi ba kasantuwar yayi tafiya zuwa Lagos, kuma sai nan da sati biyu zai dawo, Dr. Khalid kawai ya tayar, amma bai tinkareshi da maganar ba yafi so yayi da Dr. Rafiq d'in, Phone number d'inshi ya karb'a a wurin wata nurse sannan ya juyo zuwa Katsina. Alhaji Abu Abu kuwa yama commisioner na 'yan sanda magana an had'ashi da wani Barrister wanda a duk fad'in k'asar nan babu wanda bai sanshi ba, Ya k'ware sosai a aikinshi, haka kuma fuk shari'ar da zayyi da wasu ba'a winning d'inshi saidai shi yayi winnning mutum, Baki d'aya karatunshi ma ba'a k'asar nan yayishi ba, hakan yasa yake da experience sosai akan shari'ah, komai rashin gaskiyar mutum indai ya sakoshi a shari'arshi to sai yayi winning. Sosai Alhajin yaji dad'i saboda yasan yanzu kam asirinshi zai rufu, saboda matuk'ar aka kama Gentel da laifin da ake zarginta ti yasan bazai tab'a samun d'an majalisar jiha da yake nema ba. Haka Umar ya koma gida ba tare da walwalar kirki ba, saboda jin wai ba yanzu Dr. D'in zai dawo ba, gashi kuma shine kawai hope d'inshi a wannan lokacin, kuma shida dawowa har sai anyi zamab kotu na farko, yasan basuda wani evidence a halin yanzu. Zama kawai yayi bisa kujera baki d'aya bashida walwala, Kida Sultana ta ganshi haka tasan akwai matsala, Inda yake ta zauna tace "Sannu da dawowa honey, nasan ka gaji muje kayi wanka kaci abinci", Babu musu kuwa ya tashi yabita, Ganin a gajiye yake yasa ita da kanta tayi masa wankan, Bayan sun fito ta fitar masa da k'ananan kaya jeans bak'i da blue shirt, Fita sukayi ta ringa bashi abinci a baki tana faranta masa rai da labarai masu dad'i, Saida yayi nat sannan ta goge masa bakinsa da tissue suka koma d'akinta. Bayan taga ya warware sosai tace "Honey baka samu likitan bane?", Kallonta yayi yace "ya akayi kika san haka?". Murmushi ta sakar masa sannan tace "Wani abu sai bahaushe, ana tambayarshi shima yana tambayarka", Shima murmushin ya sakar mata kafin yace "wallahi kuwa ban sameshi ba, wai baya nan yaje lagos sai nan da sati biyu zai dawo, gashi kuma kinga saura kwana biyu mu fara zama kotun, ni yanzu damuwata d'aya zamu shiga kuma banida evidence ko d'aya". Ajiyar zuciya Sultana tayi tare da cewa "Gaskiya kam abun ka damu ne wannan, amma ina ganin ka cire damuwar a ranka, karka cire hope na smaun nasarah tunda ai nasan ba zama d'aya za'ayi ba, sai ka rok'a a d'aga shari'ar har lokacin da zai dawo ku tattauna dashi, kaga duk bayanan da muka samu daga gareshi nasan zasu amfanemu", "Ehh hakane wifey, kuma ga lambarshi nan na karb'a so nake sai zuwa dare in kirashi, saboda nasan ta yiwu yanzu he is busy kinsan likitoci, wata k'ila sai dare ne baya komai", "To abunma ai yazo da sauk'i, kaga sai kayi magana dashi a waya ka masa bayanin komai, insha Allahu nasan zai taimaka mana sosai, Kuma saida ka tafi na tuna da k'awayen nan nata guda biyu, suma zasuyi amfani garemu, ina so inje gidan su Ummimah d'in yanzu sai ta kwatanta min inda gidan k'awayen nata yake". Cikin farin ciki Umar yace "Good idea, ni ai nama manta da maganar k'awayen nata, ehh kije ki samo bayanin inda suke daga bakinta" "Ok yanzu zan tafi", Umar yace "ni wallahi tunanina d'aya ma karsu d'auko mana lawyer'n da zaifi k'arfinmu", Kallo Sultana tabishi dashi kafin tace "Bana son jin haka daga bakinka honey, kana tunanin akwai lawyer'nda zai gagareka ne? Kaima fa babbane ko a sahun lawyers", "Hakane, amma fa dole sai mun dage da addu'ah, saboda bahaushe yace 'in kanada kyau ka k'ara da wanka'", "Barin tafi dai honey, yamma nayi" ta zira hijabinta har k'asa ta d'auki makullin mota ta tafi. Washe gari. Wasu mutanene fuskokinsu sanye da mask k'wayr idonsu kad'ai ake gani, Lab'e kawai sukeyi suna sand'o dan basa son a gansu, Dukda dare yayi akwai duhu amma suna tsoron a gansu saboda an gargad'esu akan kar su bari asirinsu ya tonu, A daidai k'ofar gidansu Ummimah suka tsaya su duka biyar d'in, D'aya daga cikinsu hannunshi rik'e da wata jarka babba ya ringa yayyafawa a baki d'aya gidan ta waje, Yana gamawa wani daga cikinsu kuma ya k'yasta ashana, Take duka gidan ya kama da wuta sosai su kuma suka samu nasarar guduwa. Wuta keci sosai babu sassauci har baki d'aya cikin gidanma ya d'auka da duk d'akunan, Saida ya k'one sosai ne mutane suka fara kawi d'auki, Cike da tausayi aka ringa watsa ruwan omo a ciki amma wutar sai k'ara tashi take, Kowa sai karkad'a kai yake saboda sun tabbatar da inhar akwai mutane a ciki tofa babu wanda zai fita da rai, saboda yanda wutar ke tashi sosai duk ta fara cinye katangun dukda na k'asa ne, Wasu kuka suke sosai wanu kuka sunyi tagumi suna kallon wannan wuta, Daga ganin wutar cinnata akayi ba wai kamawa tayi da kanta ba, saboda da alama daga waje ta fara ci. Wani mutumi ne yace "Na tabbatar da matar gidan da 'yarta suna ciki, nasan kuwa wuta ta cisu sosai, barin shiga ciki ko Allah zaisa in dace" ya fara nad'e kafar hannunshi data wando yana k'ok'arin shiga ciki, Da sauri wani mutumi ya kamoshi yace "Kar kayi wannan sayar da ran bawan Allah, kana tunanin akwai mai rai anan ciki ne?", Duk mutane suka hanashi shiga saboda sun tabbatar da kowa dake gidan ya mutu saboda katangun da kansu suke fad'uwa tsabar wuta da sukasha. °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [12:22am, 28/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~70~} _Gaisuwa ga masoyiya ko ince abar k'aunata *Aunty sis๐Ÿ’ž* muna jin dad'in yanda kike kula damu a koda yaushe, bamu san ta wace hanya zamubi don ganin mun gode miki ba, saidai muyi fatan Allah yabar mana ke yaja da rai, Allah kuma ya raya zuri'ah bisa tafarkin manzon Allah (SAW), wannan shafin sadaukarwa ce gareki, Allah yabar zumumci ameen. #onelove#_ ****** Saida wutar ta gama cinye gidan k'urmus sannan mutane suka fara shiga ciki dukda gumin dake tasowa daga cikinshi, Alamar gawama babu a ciki, hakan yasa wasu suka fara tunanin ko wuta ta cinye gawarsune? Cike da tausayi suka ringa fita daga cikin gidan wasu har yanzu basu daina hawayen tausayi ba. **** Sultana ce ke jan mota a sukwane sai faman k'ara wuta take, Can daga bayan motar na jiyo murya ana fad'in "Wallahi bansan garinya na manta kayan sakawar mama ba, kuma abun haushi wai duka nawane kawai na had'a a jikar bakon, babu nata ko d'aya" "Ai saisa kikaga ina gudu dan kar dare ya nitsa sosai bamu koma gida ba, amma da yake kayan ne kawai zaki d'auka ai da sauk'i ma" Sultana ta fad'a bayan ta rage gudu da motar. Murza idona nayi dan tabbatar da muryar wadda naji, ko tantama babu wannan muryar Ummimah ce, to amma garinya hakan ta kasance? Kenan basu cikin gidansu lokacin da wutar ta kama?, Ku biyoni yanzu zaku samu amsoshin wannan tambayoyin. Lokacin da Sultana ta nufi gidan su Ummimah dan ta tambayeta address d'in Zarah da Rabiatu, Ta samesu itada Mama yanzu sun d'an saki ransu akan baya, Bayan sun gaisa ne ta fad'a masu abunda ya kawota, Ko amsa Ummimah bata kaiga bama Sultana ba taji wayarta ta d'auki ruri alamar k'arar shigiwar text message, D'auka tayi ta fara karantowa _ina shawartarki daku d'aukesu daga wannan gidan da suke ciki, saboda muguntar waccan nasan komai zata iya aika masu savoda tasan gidansu, amma idan kika d'aukesu daga ciki kinga shikenan hankalinku kwance kuna tare dasu, sannan kuma ku kanku zakufi samun sauk'in yi masu tambayoyi ba sai kun tado mota kunzo har gidansu ba. #shawarace#_ Cike da mamaki take karanta sak'on, Kanta ta jinjina alamar ta gasgata maganar, "Ina zuwa mama" ta fad'a bayan ta mik'e tsaye ta nufi waje, Umar ta kira ta shaida masa sak'onda aka tura mata, Suna cikin wayar shima nashi ya shigo a k'aramar wayarsa, "Ki d'aukosu kawai idan zasu yarda" ya fad'a cike da mamakin wanda yake turo masu wannan sak'unan wanda su kansu su Ummimah d'in basu sani ba, nima kuma Amrah ban sani ba kawai dai ina baza idona don ganin ko wanene wannan amma kuma shiru har yanzu. Tsinke wayar tayi ta shiga cikin gidan har yanzu bata daina mamaki ba, Bayan ta sauna tace "Dama wata tambayace ta kawoni inyi miki Ummimah, to amma kuma sai mai gidana ya kirani yace idan babu damuwa ko zaku bini mu koma gidanmi da zama na wani lokaci? Saboda zamanku anan zai iya zama matsala koba yanzu ba". Ajiyar zuciya mama ta sauke sannan tace "Tabbas maganarki gaskiyace Sultana, ni kaina tunda aka fara maganar kai k'arar nan hankalina ga baki d'aya bai kwanta da zaman gidan nan ba, dan haka mun amince mu tafi d'in babu damuwa mungode sosai Allah yayi maku albarka, Allah kuma ya mana jagora". Dad'i sosai Sultana taji da Mama bata musa mata ba, "Ameen mama, sai ku had'a kayan da zaku tafi dasu yanzu mu tafi yamma nayi". Tashi Ummimah tayi ta nemi 'yar Gana most go ta fara ziba kayanta, saida ta gama kuma kwata kwata ta manta bata had'a na mama ba, sai hijabi d'aya wadda ke rataye a k'ofa ta saka wadda saboda itane tayi tunanin ta saka kayan mama d'in, ga kuma sauri da takeyi kasantuwar Sultana tace suyi sauri tana so ta d'auko Hafsa daga islamiya. Tafiya kuwa sukayi suka d'auki Hafsa sannan suka wuce gida, Saida dare Mama taje canja kaya suka tuna ashe Ummimah bata saka kayan mama ba, Shine Sultana tace tayi sauri suje can gidan su d'auko kayan mama d'in dan bazai yiwu ta zauna batada kayan da zata saka ba. Wannan kenan. *** Koda suka isa k'ofar gidan basu kula da komai ba har Sultana tayi parking suka fito, Hafsa dake gaban mota ma ta fito itama Ummimah d'in ta fito, Mamaki k'arara a fuskokinsu lokacin da sukaga yanda gidansu ya k'one sosai har wasu katangu sun zuba, "Ya salam" Ummimah ta fad'a hannu bisa kai hawaye sun fara mata sintiri, Kamar a mafarki ta d'auki abun, Cikin hanzari suka shiga ciki har a lokacin mutane basu gama watsewa ba kowa na al'ajabin wannan mummunan al'amarin. Baki d'aya kallo ya koma ga Ummimah dake kuka sosai tana k'ok'arin shiga cikin d'akin, Hamdala mutane sukayi saboda sunji dad'i da bata ciki, amma kuma basu tabbatar da mamanta tana ciki ko bata ciki ba, "Kiyi hak'uri ki daina kuka, kinsan ita k'addara babu ruwanta, idan har abu saiya faru bawa tofa babu makawa sai ya sameshi, ita kuma maman taki data rasu Allah yayi nata rahama" wani dattijo ya fad'a saboda yayi zaton ko mama tana ciki gobarar ta tashi. Share hawayenta tayi tace "Mamana bata rasu ba, bata nan gidan, kamar sun sani sukace mu koma gidansu mu zauna, lallai wannan ikone daga Allah, Allah ya k'ara karemu", "Ameen" kowa ya fad'a tare da yin hamdala ga Allah da yasa wutar bataci kowa ba. Sultana dai nata kallo ne kawai, tana kuma k'ara mamaku sosai, Kamar mutumin yasan haka zata faru ya turo mata sak'o akan su d'aukesu daga gidan, 'To kodai aljani ne wai?' Ta tambayi kanta. "Ki daina kukan nan ki tashi mu tafi Ummimah, dama haka allah ya tsara gobara zata tashi kuma komai naki zai k'one, abunma yazo da sauk'i tunda bataci rai ko d'aya ba ai, dan kayan sakawa ko kayan amfani duk mai sauk'i ne za'a iya hin wasu, rai kuwa k'waya d'aya ne tak ba'a aro ko canjin wani, ki tashi mu tafi kawai" Sultana ta fad'a tare da mik'ar da Ummimah tsaye duk jininta ya b'aci da bak'i inda ta zauna. Babu musu kuwa tabi bayan Sultana, ranta cike da mamakin wannan abu, 'Allah dai yasa wannan d'inma ba aikenta bane' Ummimah ta ayyana a ranta wanda tuni Sultana ta gano hakan, kawai dai tayi shiru ne saboda yanda taga Ummimah ta rikice bata so tayi maganar a cikin mutane. Shiga mota sukayi har yanzu Ummimah bata daina kuka ba, Hakan yasa Hafsa uwar surutu ta koma baya inda Ummimah take, Dafa k'afad'arta tayi tace "Ki daina kuka Aunty, ai mamanku bata mutu ba ko?", Cikin mamaki Ummimah ta d'aga mata kai alamar ehh "Ok tunda tanada rai ai shieknan sai ki daina kuka, idan kayanku kike mawa zan cema Abbana ya siya maku wasu, idan kuma na momy zasu maku sai ku d'auka ku saka, kinga idan baki daina kukan nam ba har muka koma gida zaki saka mamanki ma ta ringa yin kukan, kinga dai ni bana kuka kuma ga momyna ma bata kuka". Har Sultanan ma saida tayi mamakin wannan maganganu na Hafsa, "Hafsa dan Allah ki rage surutu maras ma'ana mana, ki barta taji da abunda yake damunta kar ki saka mata ciwon kai". Bakinta ta kama bayan ta dawo wurin zamanta tace "Nayi shiru momy, na manta kin hanani yawan magana". Ita kanta Ummimah saida abun ya bata dariya, saboda surutun Hafsa idan tana yinshi kamar wata babba haka take. Bayan sunje gida suka labartawa Umar da Mama abunda ya faru, Umar bayyi mamaki ba saboda shi lawyer ne yasan irin wannan abubuwan suna faruwa a case, saidai yaji dad'i da Allah yasa saida suka baro gidan sannan abun ya faru. Mama kuwa hamdala tayi ga Allah tace "Allah mungode maka da saida muka fito gidan sannan wutar ta kama, Allah ya k'ara karemu baki d'aya", "Ameen" Ummimah ta fad'a bayan ta cire takalmin k'afarta duk k'afar tayi bak'i k'irin. "To yanzu mama ya za'ayi da kayan sakawarki? Gashi naki duk sun k'one" Sultana ta tambayi mama. "Haba Sultana ai dan kayan sakawa abune mai sauk'i, ni wallahi basu dameni ba, ke koda kayan jikina zan iya rayuwa duk dare in ringa cirewa ina wankewa, kunga kafin asubah sun bushe sai in miyar a jikina". Dariya suka d'auka su duka kafin Sultana tace "Barin duba ko a kayana inada rigarda zata miki sai in kawo miki masu zani ki saka, kinga gobe akwaa zaman kotu bamuda lokacin siyo miki wasu, sai idan mun samu natsuwa sosai". "Masha Allahu Allah miki albarka, hak'ik'a kun taimakemu keda mijinki ko ince kuna kan taimakarmu, Allah kad'ai ne zai iya biyanku, mungode sosai Allah yashi albarka", "Ameen mama ki daina yi mana godiya, wannan al'kawari ne muka d'aukarwa gwamnati cewa zamu taimaki al'ummah baki d'aya, mu taimaki mai gaskiya tare da karen hak'k'inshi". Da wannan maganar Sultana ta tashi domin ta samowa Mama kayan da zasu mata daidai a cikin nata. Shigarta kuma ta samu Umar mijinta yana waya da Dr. Rafiq. _ina cigiyar k'awata Zarah bb, koda shike bakida lafiya ashe kwana biyu na jiki shiru, Allah ya baki lafiya yasa kaffara ce ameen. #onelove#_ °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [1:00am, 29/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~71~} Zama tayi a kusa dashi jin wayar da yakeyi, hakan yasa ya kalleta ya mata murmushi kafin yaci gaba da wayarsa, Ganin wayar bata k'arewa bace yasa Sultana ta mik'e ta bud'e wardrobe d'inta, Ta samu kaya wanda zasuma Mama daidai harda supopinta da lasuka masu tsada. Har ta fita ta kaima Mama kayan ta dawo Umar bai gama wayar ba, Kwanciya tayi akan k'irjinsa tana wasa da 'yan yatsun hannunta tana k'ara tuno da gobe ne fa zasu shiga kotu. Tashi daga jikin Umar tayi jin ya gama wayar, "Ya kukayi dashi honey?" Ta tambayeshi. Tashi zaune shina d'in yayi yace "Munyi magana dashi yanada kirki sosai, Ya shaida min cewa sai nextweek Friday zai dawo, Ya min bayani cewa wallahi shi kanshi baki d'aya kanshi ya d'aure da wannan maganar, Saboda yasan ya ajiye takardar asibitin Ummimah wadda ta nunar da cewa fyad'e aka mata sannan kuma tana d'auke da cutar hawan jini, Amma kuma wai daga baya ya nemi takardar ya rasa, Saidai wai yaji magana ta fito cewa ciki aka zubar mata, Baki d'aya ya rasa yanda akayi hakan ta faru kuma yaso ya mata bayani tun a lokacin tak'i saurarshi, ya rantse ya kuma rantsewa da Allah akan baisan yanda akaui hakan ta faru ba, Yadai san daga shi sai abokin aikinshi ne suka san da maganar, kuma abokin aikin nashi shi yasan yanda komai ta kasance, Kuma da zarar ya nufi abokin aikin nashi da maganar sai ya nok'e akan baya son maganar, Shidai wai yana zargin Dr. Khalid d'in akan yasan komai ko kuma da had'in hannunshi a wannan maganar, Amma yamin alk'awarin cewa idan ya dawo zai sake tuhumar abokin nashi da maganar ko za'a dace, ya nunar min da farin cikinshi sosai akan tsaya masun da mukayi domin k'watar masu hak'k'insu, kuma shima ya tabbatar min da zai bada gudummawa d'ari bisa d'ari dan ganin mun samu nasarah". Cikin farin ciki Sultana tace "Allah sarki ashe mutumin kirki ne, saisa akeso idan mutum yace ka saurareshi to ka saurareshi d'in, gashi kuwa gaskiya ta fito, Ni kaina ina zargin wancan likitan, to idan bashi ba waye zayyi haka? Su biyu ne kawai suka san halinda ake ciki", "Hakane wifey, dare nayi mu kwanta kinga gobe sammakon fita zamuyi", "Ok dear" ta fad'a tare da mik'ewa ta kashe wutar d'akin. *KOTU* Kotu ta cika mak'il wasu na k'ara shigowa wasu kuwa fita sukeyi savoda rashin halartar alk'ali, Tsabar cika da kotun tayi yasa har wasu basu samu wurin zama ba saidai a tsaye suke. Shigowar alk'ali ne yasa kowa ya natsu akayi shiru har lokacin daya isa mazauninsa ya zauna. Daga can gefe na hangi Mama da Ummimah sunyi zuru zuru hankalinsu ya k'ara tashi dan suna matuk'ar jin tsoron ganin idon mutane ace wai duk yawansu sai sun tashi sunyi magana cikinsu. Mai gabatar da k'ara ne ya tashi yace "A yau d'aya ga watan d'aya shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai ne kotu zata fara sauraron k'arar da Aishatu Abubakar ta kawo Salmah Abubakar akan wai tasa an mata fyad'e wanda hakan yayi silar korarta daga makaranta" ya mik'a file d'in ga alk'ali tare da rusunawa sannan ya dawo mazauninsa. Alk'ali ya gyara zaman gilashinsa tare da yin gyaran murya yace "Idan akwai lauyoyi ko zasu gabatar da kansu?". Tashi Umar yayi bayan ya gyara rigarsa yace "Sunana Barrister Umar Mohd Bashir, a tare dani akwai", Sultana tayi saurin mik'ewa tsaye tace "Barrister Sultana Saddam Bakori" "Mune masu kare wadda take k'ara" Umar ya fad'a sannan suka koma suka zauna. D'ayan Barrister'n yace "Sunana Barrister Sa'eed Bebeji, lauya mai kare wadda ake k'ara" yama Umar shu'umin murmushi sannan ya koma ya zauna. Alk'ali yace "Lauya mai kare wadda ake k'ara, ko kanada hujja?". Tashi Umar yayi ya fuskanci alk'ali yace "Ehh inada ita ya mai shari'ah", "Kotu tana son gani" ya fad'a bayan ya zare gilashinshi. "Zan iya ganin Salmah Abubakar?" Barr. Umar ya tambaya bayan ya miyar da kallonshi ga sauran mutane. Cikin daburcewa Gentle ta mik'e a susuce take taku har ta iso inda aka tanadar domin tsayuwar wanda ake tuhuma. Kusa da ita Umar ya matsa ya kalleta cikin ido yace "Kotu zataso jin cikakken sunanki daga bakinki?", "Sunana Salmah Abubakar" ta bashi amsa a tak'aice. "Salmah kad'ai? Babu wani lak'ani da ake miki?". Cikin in-ina tace "Ana...ana cemin Gentle", "Good malama Gentle, ko zaki fad'awa kotu alak'arki da Aisha Abubkar? Ina nufin wadda tayi k'ararki", "Ehh Aisha k'awata ce sosai tun a Secondary School, mun shak'u sosai da ita hakab yasa har jami'a muka cik'e d'aya a JAMB d'inmu kuma course iri d'aya, tare muke karatu kwatsam naji ance wai an koreta daga makaranta saboda an kamata da case d'in ta zubar da ciki". Har cikin ran Ummimah taji wannan maganar, jin hawaye tayi suna zarya a kumatunta. "Wane irin yanayi kika sjiga a lokacin da kikaji wannan maganar? Ina nufin kin yarda da maganar ko kuwa kin musa?" Ya tambayeta. "Nayi mamaki sosai, amma kuma daga baya sai na cire mamakin saboda mutanen yanzu abun tsoro ne" Gentle ta bashi amsa. "To duk yanda kike k'awance da ita har baki san tana yawon banza ba? Kuna rabuwa kenan?", "Ehh a'a, da dai bamu rabuwa da ita, amma kuma lokaci d'aya ta canja halinta, batada aiki sai yawon banza, idan na mata magana tace babu ruwana da ita, kowa yaji da kansa". "kina nufin bakiji damuwa ko kad'an ba a lokacin da akace an koreta daga makaranta? Amma a yanda kuke da ita ya kamata ace ko yaya kinyi mamaki saboda ace babbar k'awarki wannan al'amarin ya faru da ita abun mamaki ne". Cike da gadara Gentle tace "Nikam banji komai ba gaskiya, saboda dama ta dad'e da canja halinta, kuma ta nuna tafi k'arfina", "malama Gentle kuma bakya tunanin ko wasu k'awayen ne ta canja yasa ta rabu dake? Saboda kinsan zaman da kuke zaku iya gundurar juna, sannan kuma kina nufin ke kullum kina zaune cikin d'aki daga can sai School area kawai kike zuwa? Kenan bakya zuwa wurin kowa?". "Objection my lord!" Barr. Sa'eed ya fad'a a fusace, "Wannan kuma rayuwarta ce bai shafi shari'armu ba, bai kamata barr. Umar yana yima Salmah irin wannan tambayar ba". "Barr. Umar a kiyaye" Alk'ali ya fad'a bayan yayi rubutu a takarda. "Malama Gentle ko kinsan wasu k'awayen Aishatu masu suna Zarah BB da Rabiatu Sk? Sannan kuma bakya tunanin ko wurinsu ne take zuwa wani lokacin saisa bakya ganinta?", "Ehh nasan tana dasu, amma ni bansan ko wurinsu take zuwa ba, saboda suma d'in wani lokaci suna zuwa wurina nemanta idan ta tafi yawon darenta", Murmushi kawai Umar yayi saboda a yanayin kalaman dake fita daga bakinta ma kad'ai ya isa ya tabbatarwa mutum da rashin gaskiyarta. "Zaki iya komawa ki zauna har sai na sake nemeki nan gaba" Umar ya fad'a tare da komawa mazauninsa ya zauna. "Kafin ta koma ta zauna, ko Barr. Sa'eed yanada tambayar da zayyima Salmah Abubkar wacce yake karewa a wannan shari'ar?" Alk'ali ya tambaya. Bayan ya sunkuya k'asa yace "Ehh inada ita ya mai shari'ah" ya matso inda take yace "Salmah inaso ki fad'a mana yanayin alak'arki da Aishatu a tak'aice", "Alak'ata da ita mai k'arfi ce, saboda gidansu talakawa ne ni kuma gidanmu munada hali sosai, So wani lokacinma ni nake taimaka masu da abunda zasuci a gidama barin a School idan tayi broke, komai nata nice kuma tana nuna min jin dad'in hakan, Amma kuma lokacin data fara canja hali na fahimci har abinci idan na dafa bata ci, bama ta zama barin taci, wani lokaci idan tayi dare zatazo da abincin restaurant mai rai da lafiya taci ko kallon inda nake batayi" Gentle ta sharara k'arya hankalinta kwance. "Barin d'an miyar dake baya, naji kincema Barr. Umar suma k'awayen nata wani lokaci suna zuwa nemanta, hakan ya tabbatar da cewa ba kowane lokaci take tare dasu ba kenan, to kina nufin bataje wurinsu ba kenan suma?", "Ehh lallai bataje wurinsu ba kam, tunda inda ace taje wurinsu ai ba zasu zo nemanta inda nake ba". "Objection my lord!" Barr. Sultana ta fad'a bayan ta buga teburi, "Yanayin yanda suke magana bai kamata ace suna yinta ba ya mai shari'ah! Wannan zai iya zama cin fuska ga wadda take k'ara". Jinjina kanshi alk'alin yayi yace "Barr. Sa'eed ka tausasa kalamanka". "Iyakacin tambayar da zan mata kenan ya mai shari'ah, ina neman kotu ta bani dama domin kiran Aishatu Abubakar, wato wadda take k'ara domin akwai tambayoyin da nake so na mata" Barr. Sa'eed ya fad'a had'e da sunkuyawa k'asa yana kallon alk'ali. "Kotu tana son ganin Aishatu Abubakar" alk'alin ya fad'a yana kallon ta inda zata fito. A hankali cike da natsuwa ta taso kanta sadde a k'asa ta tsaya inda Gentle ta fita. °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [6:44pm, 29/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~72~} Cikin izzah da tak'ama Barr. Sa'eed yace "Aishatu shin a cikin kalaman da Salmah tayi ko akwai maganar data fad'a wadda kike da ja akanta?", Da hannunta ta share hawaye jikinta ya fara rawa saboda yanda taga an tsura mata ido, "Ehh...ehh a..akwai" ta fad'a cikin rawar murya. Murmushi Barr. Sa'eed yayi yace "Ki kwantar da hankalinki ki daina rawae murya indai da gaske kinada gaskiya ba k'arya zaki fad'a ba". "Objection my lord!" Barr. Sultana ta fad'a k'ufule, "Bai kamata Barr. Sa'eed yana fad'in wannan kalaman ga Aishatu ba, ya kamata yayi la'akari da yanayin yawan mutanen wurin nan ne yasa take rawar jiki da rawar murya", "Barr. Sa'eed a kiyaye" alk'ali ya fad'a yaci gaba da kallonsu. "uhm, kr nake sauraro" ya fad'a a hankali. "Kusan duk maganganun data fad'a k'arya ne, nasan dai tana yimin wasu abubuwan idan taga inada buk'ata, amma maganar da tace ita ke d'aukar nauyinmu wallahi k'aryane, babana bai rageni da komai ba, kusan duk wata ko baya da kud'i sai ya ranta ya turo min, sannan kuma da tace na canja hali wannan duk halayenta ne, babu inda nake zuwa, idan ma na fita daga room d'inmu to bazan wuce room na kusa da namu ba inda k'awayena Zarag da Rabiatu suke ba". "Ina su k'awayen naki suke a halin yanzu? In da gaskene ai ya kamata ace sunzo nam kodan su bada wannan shaidar ga k'awarsu". Jikin Ummimah ya hau rawa saboda rashin halartar su Rabiatu kotun, tasan ba lallai bane a yarda da maganarta. "Gamu" Zarah da Rabiatu suke fad'a daidai lokacin da suka shigo cikin kotun. Ajiyar zuciya ta sauke farin ciki bayyane a fuskarta, hamdala tayi ga Allah a lokacin da suka iso inda ake son ganinsu. Qur'ani aka basu sukayi rantsuwa da zasu fad'i gaskiya sannan cikin rashin jin dad'in zuwansu Barr. Sa'eed yace "Kune k'awayen nata?", "Ehh mune" suka had'a baki wurin fad'i. Baki d'aya yama rasa tambayar da zayyi masu, saboda sam bayyi tunanin zasuzo ba, dan saida ya tabbatar da babu su a cikin kotun sannan ya nemi yana son ganinsu. Sai daga baya wata fasaha ta fad'o masa yace "Wai da gaske wurinku Aishatu take zuwa wani lokaci?", "Ehh da gaske wurinmu take zuwa duk lokacin da Gentle ta fita tayi dare, wani lokacin ma a d'akinmu take kwana saboda tace ba zata iya kwana ita kad'ai ba" Rabiatu ta bashi amsa. Shiru ya d'anyi kafin yace "To idan da gaske ne mesa wani lokacin idan bata d'akinku kuke zuwa ku tambayi Salmah inda Aishatu taje? Kenan hakan ya tabbatarda ba kowane lokaci kuma d'in kuka san inda take ba". Zarah tayi caraf tace "So d'aya ne tak hakan ta kasance, kuma ranar ma ta fita neman Gentle ne akan tazo suyo karatu dan exam d'in da zamuyia washe gari mai wahala ce, tun fitar da tayi shine vata dawo ba har mukaje nemanta room d'insu". Kallonshi ya miyar ga alk'ali yace "Ya mai girma mai shari'ah, da wannan bayanin da k'awayenta sukayi ya isa ya tabbatarwa kotu da cewa ba kowane lokaci ne take tare da k'awayentan da take cewa suna tare always ba, kenan akwai gyara a maganar Aishatu saboda gashi k'awayenta sun fad'a da bakinsu, ta masu k'aryar zataje ta nemi Salmah domin suyi karatu, amma kuma Salmah ta dawo tace ita batama ga Aishatun ba, wannan ya tabbatar da cewa ta tafi yawo kenan" Ya juya gasu Zarah yace "Zaku iya tafiya ku zauna". "Amm kafin su tafi su zauna, ko lauyoyi masu kare wadda take k'ara sunada tambayar da zasuyi masu?" Alk'ali ya tambaya. "Ehh akwai ya mai shari'ah" barr. Sultana ta fad'a tare da tasowa cike da natsuwa ta iso inda suke. "Bayan kun tambayi Salmah inda Aishatu take, zaku iya tuna amsar data baku?", "Ehh zan iya tunawa, Saida ta bimu da kallon banza sannan tace 'idan har bamu k'yaleta da tambayar inda Aisha take ba wallahi sai ta saka an mana abunda tasa akaima Aisha', duk da vamu san ko menene ba amma hankalinmu ya tashi, babu yanda muka iya dole muka bar mata d'akin baki d'aya ranmi a dagule yake". "Well" Sultana ta fad'a, "To daga nan ku kuma wane irin mataki kuka d'auka?". Rabiatu tace "Babu yanda muka iya duk da tashin hankalin da muka shiga, mun nemeta a duk blocks d'in hostel amma bamu sameta ba, hakan yasa muka koma room d'inmu amma babu wadda ta iya yin bacci a cikinmu, Washe gari tun gari bai gama wayeba muka fita waje nemanta, Acan muka tsinceta cikin jini nesa da hostel, Hankalinmi ya tashi muka d'auketa muka kaita school clinic, Bayan sun dubata sukace suma ciwonta yafi k'arfinsu saidai si kaida wata asibiti, Tare muka tafi da ita ta dad'e bata farfad'o ba, Likitan daya dubata ya tabbatar mana da fyad'e ne aka mata kuma an illatata sosai, yace mana ya rubuta a takarda zai bamu mu tafi da ita idan ta samu sauk'i, Amma kuma sai muka shafa'a, shi bai bamu ba muma kuma mun manta bamu karb'a ba, Saida aka dawo hutu ne akace wai an koreta, kuma harda gwada mana takardar asibitin anyi amma kuma sab'anin waccan ta farkon wadda bamu san dalilin canzata ba". Barr. Sultana zata sake magana kenan alk'ali yace "Kotu zata so ganin likitocin da suka dubata a asbitinsu, Sannan kuma zataso taga ma'aikatan School clinic d'insu domin su fad'a mana 'mesa sukace ciwonta yafi k'arfisu?' Saboda ta yiwu su abunda suka gani daban, zamuso jin komai daga bakinsu idan suna kusa". Cike da ladabi Sultana tace "Likitan da yayi mata aikin mun buk'aceshi da yazo amma kuma yayi tafiya zuwa Lagos, ga wannan takardar" ta mik'awa wanda ya gabatar da k'ara domin ya isar da ita ga alk'ali, "Takarda ce wadda ta tabbatar da likitan baya nan, yaje wani course ne amma ya tabbatar da yau saura kwana hud'u ya dawo, ranar Friday kenan, Sannan kuma bamuyi magana da ma'aikatan School clinic d'inba, Muna rok'on kotu mai albarka data d'aga wannan shari'ar har sai zuwa next week, wanda insha Allahu a ranar ma'aikatan zasuzo, shima kuma likitan kafin nan ya dawo". Shiru alk'ali yayi bayan yayi 'yan rubuce rubuce sannan ya d'ago kanshi yace "Kotu ta d'aga sauraron wannan shari'ar har sai ranar litinin, bakwai ga watan d'aya shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai", Ya buga tuburonshi da guduma tare da fad'in "Kooootu!" Yana mik'ewa kowa ma ya mik'e *** Bayan sun fita daga kotu ne Gentle ta ringa watsawa Ummimah harara cike da tsana, Zarah da Rabiatu sukayi tsaki tare da fad'in "Ta Allah bata mutum ba, kuma insha Allahu sai munyi nasarah, Allah baya goyon bayan azzalumi". K'ara k'ufule Gentle sukayi, Momy'nta taja hannunta da sauri suka tafi dan tasan halin Gentle tsaf zata iya yin dambe dasu a wurin, kuma idan har tayi to mutane zasu tabbatar da cewa da gaske tasa anyima Ummimah fyad'e duk da yanzu ma wasu sun fara gasgatawa. Kallon Rabiatu Ummimah tayi tace "k'awayen kun rufa min asiri sosai da kukazo, inda ace bakuzo ba da bansan yanda zanyi ba, banyi tunanin zakuzo ba gaskiya". Zarah tace "Ai dole ne a garemu muzo Ummimah, an cuceki kuma aka nemi a hanaki kuka, Jiya muna Hostel mukaga text d'in lawyer d'inki, ta mana bayanin komai kuma ta nemi in da hali anada buk'atarmu a kotu, Kinsan akwai nisa daga Jalingo zuwa Katsina, tun da sassafe muka taso amma bamu iso da wuri ba har akayi nisa da shari'ar, Allah yasa daidai muna zuwa muna ji ana nemanmu". Ummimah tace "Kuma fa haka kawai na bata number d'inki, saboda kin san yanzu banda waya, A wata takardata ce dana tab'a ajiye number'n sanda zan miki call me back, Lokacin da zamu baro gida na had'ata cikin jikarmu, Ashe da rabon zatayi amfani". "Aikuwa dai kin gani". Da wannan firar Sultana ta samesu, Takardar dubu d'aya ta zaro a jakarta Ta mik'awa Mama tace "Mama ku hau napep da wannan ku tafi gida, ni inada aiki da yawa a Office". Karb'a mama tayi tace "To mungode sosai Allah yayi albarka, Sai kun dawo d'in" suka tafi yayinda Sultana kuma ta koma Office d'inta. _ina cigiyar *Sadiya Afka* nikam, ko ina ta shige oho? Gashi ba'a samun lambarta idan an kira, Allah dai yasa lafiya inji Amrah._ °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [11:41pm, 31/01/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~73~} Bayan sun koma gida sukaci gaba da tattaunawa inda Rabiatu da Zarah suka ringa tsinewa Gentle bayan Ummimah ta basu kaf labarin abubuwan daya samesu har mutuwar Baba, da kuma ta Afrah, ga Amrah maras lafiya bama asan inda take ba. Sunji haushi sosai kuma suma sukayi fatan samun nasara a wannan shari'ar da ake, saidai kuma a yanda sukaji labarin dukiyar mahaifin Gentle, da kuma babban Barrister d'in daya d'aukar mata, sun shiga kokonton samun nasararsu, saidai kuma sunyi fatan Allah yasa dukiyarsu kar ta amfanesu. Da wannan firar har yamma tayi Sultana da Umar suka dawo gida cike da gajiya, Su kansu a mota firar shari'ar kawai yakeyi, amma shi yana ji a jikinshi next zaman da za'ayi insha Allahu zasuyi nasara bama sai ansha wahala ba. Koda suka shigo gida Hafsa ta taresu, murna fal a ranta ta gaishe da iyayen nata sannan suka k'arisa daga ciki inda suka samu har yanzu su Zarah basu daina firar abunda ya samu su Gentle ba. Bayan sun natsu sosai Umar ya kira Dr. Rafiq, ya k'ara tabbatar masa da cewa fa ranar Monday next week anada buk'atarshi a kotu, ya amsa da 'insha Allahu zayyi k'ok'ari ko zuwa ranar Sunday ya shigo Katsina, saboda ranar Friday zai koma Jalingo', Sallama sukayi Umar ya kashe kiran, Sultana tace "To ya maganar wancan ma'aikatan na makarantarsu?", "wannan kuma ai bamuda case dasu, kotu zata aika da sammacinta" Umar ya bata amsa yana k'ok'arin cire suite daga jikinshi. Taimaka masa tayi ya k'arisa cirewar, itama ta cire nata sannan suka shiga wanka. Fitowarsu suka samu abinci jere a dining, murmushi Sultana tayi saboda tasan babu tantama wannan aikin Ummimah ne, tunda suka dawo gidan da zama ta hana Safiyya yin aiki sosai, komai ita takeyi bata gajiyawa. *Ranar lahadi 10:45pm* A daidai wannan lokacin ne Umar ya latsa kiran Dr. Rafiq domin yaji ko ya iso Katsinar amma shiru bata shiga ba, Sake latsa kiran yayi still dai 'not reachable', Hakan yasa ya fuskanci Sultana da itama shi take kallo yace "Ban san mesa ba number'n Dr. Bata shiga, kinga tun yamma naketa fama kiranshi amma duk maganar guda ce", "Ina tunanin ko yana hanya ne, wata k'ila kuma hanyar babu network mai kyau" Sultana ta bashi amsa tana kallonshi cikin soyayya. Basu kawo komai a ransu ba a haka suka bar maganar su a tunaninsu ko yana hanya, dan haka cikin kwanciyar hankali bacci ya d'aukesu mai cike da walwala da nishad'i saboda yanda suke jin dad'in zasu shiga kotu da hujjarsu babba, wadda suke ganin da ita wannan shari'ar zata kawo k'arshe. *KOTU* Yau ta kama ranar Monday bakwai ga watan d'aya, shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai, Kotu ta cika kamar zaman farko, harma zan iya cewa a wannan lokacin ma tafi cika sosai, Kowa burinsa yaga yanda k'arshen shari'ar zata kaya. Bayan mai gabatar da k'ara ya tashi yace "Yau 7-1-2017 kotu zataci gaba da sauraron shari'ar data fara a makon daya wuce, wadda Aishatu Abubakar ta kawo Salmah Abubakar k'ara akan zargin da take na sakawa an mata fyad'e wanda yayi silar dakatar da ita daga karatunta". Alk'ali yace "Barr. Umar da Barr. Sultana ku muke saurare, kotu na fatan kun kawo mata shaidun data buk'ata a zaman farko", Shiru ya biyo baya kasantuwar daga Umar d'in har Sultana basu tattare da natsuwarsu, Tun shigowarsu kotu suke baza ido dan ganin Dr. Rafiq amma shiru har yanzu baizo ba, Kuma gashi idan sun kira lambarsa bata shiga, Baki d'aya hankalinsu a tashe yake, Ita kanta Ummumah nata hankalin a tashe yake, barin k'awayenta Rabiatu da Zarah da suma basu tattare da tasu natsuwar. "Barr. Umar!" Alk'ali ya fad'a a hasale savoda yayi tunanin ko yajishi. Firgigit suka dawo hayyacinsu, A daburce Umar ya mik'e tsaye duk jikinshi yayi sanyi, Sunan Allah kawai yake ambata a ranshi, saboda yasan matuk'ar Dr. Rafiq baizo ba to shikenan basu ba winning d'in eannan shari'ar. Bayan ya tashi tsaye yace "Kotu tana buk'atar ganin Sister Maryam, Sister Fatima, Sister Rooth da kuma Sister Ifeoma". Wasu mata ne suka taso, biyu daga ciki manyan mata ne ak'alla zasu kai talatin da biyar zuwa da shida, Biyun kuma da ganinsu yaran matane, idan sunyi aurema to sabon aure ne, dan babu alamar sun tab'a haihuwa koda d'aya ce. Bayan sun fito sun jera wuri d'aya rankas Umar yace "Wannan sune nurses na Talented University, wanda sune suka karb'i Aishatu a lokacin da aka kaita". Qur'ani aka bama musulman sukayi rantsuwa da zasu fad'i gaskiya, Christians d'in kuma aka basu bible sukayi ranstuwa da zasu fad'i gaskiya tsakaninsu da Allah, Hakan yasa Ummimah tad'an samu sassauci a zuciyarta. "Rabiatu da Zarah k'awayen Aishatu su fito idan suna kusa" alk'ali ya fad'a yana kallon ta inda zasu fito d'in. A hankali suka taso suka iso inda sisters d'in suke tsaye, Alk'ali ya miyar da kallonshi ga sisters d'in yace "Ko kun shaida wannan 'yan matan kuwa?". Da hanzari Sister Maryam tace "K'warai kuwa na shaidasu, su suka kawo wannan marar lafiyar mai suna Aisha da wata safiya bazam manta ba". Ifeoma ma tayi caraf tace "Yes I can recognise their faces". "Da kyau, Zarah da Rabiatu zaku iya komawa ku zauna" alk'alin ya fad'a bayan ya duk'ar da kanshi yayi rubutu. Umar yace "Zan fara dake Sister Fatima, a lokacin da suka kawo maku Aisha batada lafiya, zaki iya tuna a yanayin da take kuwa?", "Ehh zan iya, sun kawota ita ba matacciya ba ba kuma rayayya ba, amma kuma jikinta duk ya b'aci da jini" ta bashi amsa. "Saura ke Ifeoma, bayan kun karb'eta wane irin treating ne kuka fara bata?" Umar ya tambaya yana yi yana lek'en k'ofa ko zaiga shigowar Dr. Rafiq amma babu ko alamarshi. Cikin dakewa Ifeoma tace "Mun fara k'ok'arin vata first aid domin tsayar da jinin dake fita daga k'asanta amma kuma abun ya gagara, na kira sauran abokan aiki nawa su tayani amma suma sunce abu yafi k'arfinsu, gashi kuma babu Dr. Ko guda a asibitin suna huta" ta fad'a cikin hausarta da bata k'ware ba. "Sister Maryam daga nan kuma sai kukayi me? Sannan kuma ai naga jini ne, taya za'ace kuda kuka karanci nursing kuma kun kasa tsayar da jini, ko kunga wani ciwo ko rauni a wurin ne?". Saida tad'an rarraba ido sannan tace "Gaskiya babu rauni ko d'aya, kawai dai jinin ne mukaga fitarshi tayi yawa, Ga dunk'ulr dunk'ulenshi yana fita, Muna shirin fita da itane mukaga wani k'aton jini ya fad'o, koda muka duba da kyau ashe halittar jariri cr har ta fara fita, hankalinmu ya tashi sosai munyi tunanin ko shikenan yanzu jinin zai tsaya, amma kuma bai tsaya ba saboda da alama ba jariri d'aya bane a cikin cikinta, Da sauri muka shiga mota mu duka harda k'awayen nata muka tafi Kadraq clinic, Mun samu Dr. Khalid eanda yake gaeny Dr. Ne sai waai abokinshi shi kuma ba gaeny bane, Sun duddubata sosai Dr. Khalid ya tabbatar mana da k'wayar zubar da ciki ce tasha kuma mai muguwar illah, ta sata ta zubar da jini sosai kuma inhar ba'ayi saurin k'ara mata ba zata iya rasa rayuwarta, kuma...." bata k'arisa maganar da take ba Zarah ta mik'e a fusace tama manta inda take tace "Wallahi ku munafukai ne k'arya kuke, kuji tsoron Allah mana, ku duba darajar rantsuwar da kukayi ku fad'i gaskiya, haba bayin Allah! Ya da girmanku zaku zubar dashi saboda an baku kud'i? Kud'i masu saurin k'arewa, ko kun manta da akwai babbar shari'ah ne? Wadda ranar baki da ido zasuyi magana, hannu da k'afa zasuyi magana, dukkan gab'ob'in jikin mutum zasuyi magana, wallahi..." Da k'arfi alk'ali ya buga guduma yace "Ki rufewa mutane baki, nan kotu kikr ba wurin shirme ba, ki bari har saa idan kin nemi izini kotu ta baki damar yin magana sannan kiyi". Cike da b'acin rai da kuka Zarah ta koma mazauninta ta zauna, tana tunanin k'araurayin da nurses d'in nan suke sharawa, gashi kuma Dr. Rafiq d'in da zai fad'i gaskiya baizo ba, ta yiwu shima an siyeshi da kud'i shine yak'i zuwa kuma ya kashe wayarshi, Dr. Khalid kuma yazo tun d'azu suka ganshi. A sab'ule Barr. Umar ya koma ya zauna, Yama rasa abunda zai fad'a, he has no idea yanzu kam, yasan dole za'ayi winning nasu. Ita kanta Sultana kuka takr tsabar tashin hankali. Alk'ali yace "Ko lauya mai kare wadda ake k'ara yanada tambayar da zai masu?". Cike da gadara Barr. Sa'eed ya mik'e, saida ya kalli Umar yaga tsantsar tashin hankali a bayyane dashi, yaga kuma Sultana ta dage sai uban kuka take marar sautu, Shu'umin murmushi yayi sannan ya isa inda sisters d'in suke. _Alhamdulillah, masha Allah, dukkan yabo ya tabbata ga Allah mai kowa mai komai, Allah mungode maka daka bawa k'awata ko ince aminiyata (Zarah bb) lafiya, Allah ya k'ara mata lafiya da dukkan sauran marasa lafiya, masu ita kuma Allah ka k'ara masu. #onelove#_ °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [11:08pm, 1/02/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~74~} "Bayan likitan ya tabbatar maku da ciki ne ta zubar sai kuma me ya faru?" Barr. Sa'eed ya jefo masu tambaya yana kallon Sister Fatima da nufin ita zata amsa masa. "Gaskiya munyi mamaki sosai, bamuyi tunanin d'alibar wannan jami'ar zatayi wannan ta'asar ba, ganin munyi mamaki yasa Dr. Khalid ya tabbatar mana da wannan ba shine zubar da cikinta na farko ba, saboda yaga alamomin haka da dama a tattare da ita". Kallonshi ya miyar ga alk'ali yace "Ina so kotu ta bani dama domin gabatar da Dr. Khalid idan yana kusa". "Kotu ta baka dama" alk'alin ya fad'a yana kallon ta inda likitan zai fito. Dr. Khalid ne ya taso a hankali ya tsaya kusa da sisters d'in, Qur'ani aka bashi yayi rantsuwa da zai fad'i gaskiya sannan Barr. Sa'eed yace "Ko zaka fad'a mana cikakkrn sunanka da kuma abunda kayi karatunka a kanshi?". "Ehh zan fad'a" Dr. Khalid ya bashi amsa. "To myna saurarenka", "Sunana Khalid Muhammad Khalid, ni d'an asalin garin Katsina ne amma iyayena suna zama a Jalingo nima d'in acan nake zama, Ni cikakken likita ne ta fannin abunda ya shafi mata, yanzu haka inada asibiti tawa ta kaina wadda duk fannin mata ne kawai a cikinta", "Good" Barr. Sa'eed ya fad'a, "Ko akwai gyara akan bayanan da sisters d'in nan sukayi? Ko kuma wani abu wanda ba gaskiya ba?". Shiru yayi kafin yace "Tabbas babu k'ari ko d'aya a bayanansu, Bayan sun kato Aishatu na dubata sosai na kuma gane irin k'wayar data sha wadda ta nemi illaya rayuwarta, Data farfad'o ne nake mata fad'a akan dalilinta nayin haka, Shine ta cemin wai tana kunyar a ganta da cikin ne, savoda ita duk iskancinta da bin mazan da takeyi a gidansu ba'a san tana yinshi ba, Kuma ta tabbatar min da wannan cikin shine na biyu kuma wancan d'inma zubar dashi tayi, Na mata nasiha akan ta daina bin maza amma tace sam bata san wannan ba, ta rigada ta saba da maza dan haka dole sai ta bi...." bai k'arisa maganar da yakeyi ba Barr. Sultana ta mik'e cikin hawaye tace "Objection my lord! Bai kamata suna fad'in magana irin haka ba, saboda wannan tamkar cin fuska ne". Kallonta alk'ali yayi yace "k'orafi bai karb'u ba Barr. Sultana, Dr. Khalid ci gaba". Wani wawan murmushi Barr. Sa'eed yama Sultana sannan yace "Muna jinka Dr." Ci gaba da zuba k'arairayi Dr. Khalid yayi, ita dai Ummimah mutuwar zaune ma tayi, ta rasa avunda zata fad'a sai tsabar mamakin hali irin na mutanen yanzu take, lallai kam yanzu kowa ba abun a yarda dashi bane. Bayan ya gama duka suka koma suka zauna, Alk'ali ya gyara zaman gilashinshi yace "Ko akwai mai sauran hujjar da zai gabatar kafin a yanke hukunci?". Kai kawai Umar da Sultana suka kad'a cike da takaici, sun san dole ba zasuci wannan shari'ar ba, saboda duk wasu hujjoji nasu anbi an b'atasu, wanda suke da hope akanshi shiru baizo ba, idon Sultana har ya kumbura tsabar kukan da tasha a kotun, Umar kuwa tagumi kawai yayi yama rasa avunda ke masa dad'i. Kallonsu suka miyar ga Sultana da Mama da suma hankalin nasu a tashe yake, jin alk'ali ya fara magana yasa suka miyar da hankalinsu a gareshi. "A bisa hujjoji da suka gabata na wanda lauyoyi masu kare wadda take k'ara, da kuma na wanda yake kare wadda ake k'ara suka kawo, Kotu tayi zurfin tunaninta tare da yanke hukunci. Munji yanda kowa ya kawo nasa hujjar, dan haka kotu ta gamsu da kaf bayanan Barr. Sa'eed, Ta kuma wanke Salmah Abubakar a bisa k'ararta da Aishatu Abubajar data kawo akan ta saka an mata fyad'e, Ita kuma Aishar kotu zata d'aureta har na tsawon watanni bakwai a gidan mata (prison) a bisa b'atawa Salmah suna da tayi, sannan kuma zasu bata tarar naira dubu goma na wahalar zirga zirga data sha, ta baro karatunta ta dawo gida akan wannan shari'ar, Amma kuma Aisha da lauyoyinta sunada damar da zasu d'aukaka k'ara idan hukuncin bai masu ba. Kooootu!". Alk'ali ya mik'e. K'ara ta saki da k'arfi had'e da zubewa k'asa, Mama dake kusa da ita tayi saarin duk'awa tana kuka sosai mai tsuma zuciyar mai sauraro, Zarah da Rabiatu ma tuni suka fashe da kuka, suna bala'in tausayin k'awarsu, Lallai wannan rayuwar ta yanzu avun tsoro ce, dukda cutar Ummimah da akayi amma sai gashi wai ita aka bama rashin gaskiya, Koda yake bataga laifin alk'ali ba, saboda shikam yayi amfani da hujjojin da aka kawo masa ne sannan ya yanke hukunci. Sultana ma tuni ta fasa kukan mai k'ara fiye da wanda takeyi d'azu, Umar nata k'ok'arin rarrashinta dukda shima d'in k'arfin hali ne, Tunda yake a rayuwarsa tun fara aikinsa bai tab'a yin shari'ar maras dad'in wannan ba, Tsabar rashin gaskiya yayi yawa a cikinta, Duk wata hanya da zasubi an dod'e ta. Cikin rashin imani da rashin tausayi Barr. Sa'eed ya kalli Umar tare da mik'a masa hannu domin su gaisa, Sam Umar yak'i bashi hannun saboda cike yake da takaicinshi, Hakan yasa Barr. Sa'eed ya kwashe da dariya yace "Ka tuna shari'arma ta farko dani wacce ka kayar dani? Baka sani ba tun daga wannan lokacin nake jin haushinka, na kuma k'uduri aniyar ka gama kayar dani a shari'ah har abada, Na dad'e ina fatan *WATA SHARI'AH* ta had'ani dakai, sai gashi kuwa wannan shari'ar ta had'amu, na kuma gwada maka cewa nafi k'arfi n k'aramin lawyer kamarka". Cikin dakewa Umar ma ya mik'e tsaye, "Ido cikin ido ya kalleshi yace "Karka damu da wannan Barr. Sa'eed, ka shirya mu had'u dakai nan gaba kad'an idan munyi apeal (d'aukaka shari'ah), mu muna tare da gaskiyarmu kuma Allah ba zai tab'a barinmu muji kunya ba saboda yana tare da mai gaskiya, dan haka ka sake d'aure d'amararka tayin yak'i dani, Ba komai nayi ba a wannan shari'ar sai idan mun d'aukakata zaka tabbatar da k'aramin Barr. Irina yafi babban irinka a fanni da yawa" ya miyar masa da murmushin da bai kai zuci ba. Fuska d'aure Barr. Sa'eed yabar wurin, Har ga Allah bayyi zaton zasu d'aukaka k'ara ba. Gentle kuwa saa washe hak'ora take, Iyayenta ma haka, sai kallon banza suka watsawa su Sultana. Suna cikin haka ne ma'aikatan gidan yari mata sukazo sanye da uniforma d'insu kalar k'asa, Daidai inda Ummimah take suka isa da handcuff d'insu wai sunzo su tafi da ita. _kuyi hak'uri da wannan masoya labarin *wata shari'ah* nasan wannan shafin yayi gajerta akan yanda nakeyi, munata hidimar biki ne saisa ya zama kad'an, magode sosai da soyayyar da kuke nunawa wannan littafin musamman 'yan *RAZ NOVELLA 2*, kunfi kowa son labarin, dan haka Amrah loves youh much. #onelove#_ °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [11:35pm, 2/02/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~75~} _Wannan shafin naku ne masu tausayin halin da Ummimah take ciki, baki d'aya masoyan littafin *Wata shari'ah* ina k'aunarku, Allah yabar so da k'auna. #onelove#_ ****** Saurin mik'ewa Umar yayi ya tari gabansu babu haufin komai haka kuma babu ko alamar tsoro a tattare dashi, Kallonshi d'aya daga cikin matan tayi tare da k'ara b'ata fuskarta. "How dare you malam!? Ka barmu akan aikinmu muke" ta fad'a cikin hausaeta da bata k'ware ba kasantuwar ba bahausa bace, mini skirt d'in dake bisa makeken k'ugunta kawai ya isa ya tabbatar da cewa ba musulma bace. "Hukunci bai yanku ha saboda zamuyi apeal, idan baki yarda ba zaki iya zuwa ki samu alk'ali kuyi magana dashi, bakida hurumin da zaki wabi kwaso jiki domin kama Ummimah ku kaita prison, so you better to leave this place because you are just wasting your time, babu inda zaku tafi da ita" Umar ya fad'a cike da zafin rai. Jin maganar da Umar yayi yasa ta sauke hannun dake rik'e da handcuff d'in, Juyawa baya tayi hakan yasa suma sauran suka juya, tunda suka tafi basu sake dawowa ba. Ummimah kuwa har yanzu bata farfad'o ba, Mamah baki d'aya hankalinta ya tashi, bata fatan ta rasa 'yarta kamar yanda ta rasa mijinta da sauran 'ya'yanta guda biyu. Zarah da Rabiatu kuwa idonsu har ya kumbure tsavar kukan da suka sha, gasu ga Ummimah inda take kwance sai k'ara allawadai da wannan al'amarin sukeyi. Saida Sultana ta gama kwasar kukanta sannan ta taso, Inda suke ta nufa ta tsuguna tana fad'in "Dukkan tsanani yana tare da sauk'i, haka zalika komai yayu zafi maganinsa Allah, Ya kamata duk koke koken nan mu ajiyesu, Muyi k'ok'arin sama mata lafiyarta dan sam bai kamata mu barta anan ba, Gobe Tuesday insha Allahu zamu d'aukaka k'ara, Sai mu dage da addu'ah insha Allahu zamuyi nasarah, Saboda Allah yana tare da mai gaskiya". "Hakane Sultana, Allah yayi mana jagora, Allah kuma ya tashi kafad'un Ummimah" Mama ta fad'a tare da share hawayen fuskarta. Zarah da Rabiatu ne suka kinkimi Ummimah, Kai tsaye bakin motar Umar suka kaita, Tun daga nesa ya bud'e masu kasantuwar mai amfani da remote ce, Bayan sun sakata ya bama Sultana key d'in yace 'ta tafi dasu gida, saboda shi zaije wurin justice suyi magana dashi akan d'aukaka k'arar da suke so suyi'. Har Sultana ta tada mota tabar wurin su Gentle suna tsaye suna kallonsu, Mamaki had'e da haushi ne ya mamayesu ganin Ummimah zata tafi ba tare da an tafi da ita prison ba. A ranar daida Umar ya gama komai daga kotunsu ya miyar da maganar court of apeal, An yankar masu rana talatin ga watan d'aya shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai zasu fara zaman kotu. Umar yaji dad'in yankar masa kwanakin da akayi da yawa, saboda yana tunanin hakan zai bashi damar yin bincike cikin natsuwa har ya samo manyan hujjojin da zai gabatarwa kotu wanda zasu gamsar da kotu cewa lallai Gentle itace tasa akayiwa Ummimah fyad'e. ***** "Dan Allah ku sakarmin uwata hakanan, wallahi ita kad'ai gareni, dagani sai kannena biyu ta haifa, babanmu ya mutu tun muna yara, itace tasha wahala damu tun daga bokonmu har islamiyyarmu, Batak'i ta rasa farin cikinta amma ta faranta mana ba, Ta rasa komai nata a dalilin karatuna na likitanci, Ba zanso na rasata ta dalilin aikin likitancina ba, dan Allah ku saketa ni na yarda kuyi min duk abunda kukaga dama na amince". Dr. Rafiq ne ke wannan maganar fuskarshi share share da hawaye. Wani mutumi k'aton gaske kamar basamude ya k'yalk'yale da dariya kafin daga baya ya d'aure yace Kai ba taurin kai gareka ba? Saida muka gargad'eka akan kar kaje Katsina domin ka bada shaida amma ka nace sai kaje, gashi nan kai bakaje ka bayar da shaidar ba, kuma zaka rasa uwarka". "Ya salam!" Dr. Rafiq ya furta. "Wallahi na maku alk'awarin indai zasu k'ylemin mamana ba zakuyi mata komai ba to ba zanje kotu in bada shaida ba kunji na rantse, Ban had'a umma da kowa ba, bana fatan a dalilina ta rasa rayuwarta, Ina sonta fiye da yanda nake son kaina, Dan haka wallahi ba zanje ko Katsinan bama barin in bayar da shaida indai zaku k'yaleta". Wani d'aya ya tsuke fuska babu ko alamar annuri a tattare dashi yace "Zamu saketa, amma da sharad'in inhar wani abu ya faru tofa zakaga abunda baka so, saboda muna tare da kai, muna sane da duk wani motsinka". Bakin Dr. Rafiq har rawa yake yace "Wal...wallahi...wallahi na amince, na amince". "Da ka kyautawa kanka" wancan d'ayan basamuden ya fad'a yana k'ara zaro mugayen idanuwanshi da suke jajur kamar jan garwashi. Wani d'aki suka shiga wanda yake duhu dund'um ko tafin hannu ba za'a iya gani ba, Kwanceta sukayi da muguwar igiyar da suka nad'eta, Selotape suka kwance daga bakinta da suka nad'e dashi, Janta sukayi da k'arfin gaske suka fitar daga cikin d'akin, Aikuw ahakan ne ya bata damar fashewa da kuka tana k'ara ambatar sunan Allah. Daidai inda Dr. Rafiq yake sukayi jifa da ita, Saurin k'ank'ameta yayi cikin firgici saboda yanda ta koma cikin kwanakin da basu wuce biyu ba amma kamar zautacciya. Suna cikin hakane basamuden nan ya daka masu tsawa, ba arzik'i sukayi shiru sai rawa jikinsu yakeyi. "Gaza d'aure masu fuskokinsu mu fitar dasu daga nan". Wanda aka kira da Gaza d'in ya zaro ido cikin mamaki yace "Ance a k'yalesu hakanan ne?", "Banida lokacin amsarka" basamuden ya fad'a a k'ufule. Hakan ya tabbatarwa Gaza d'in cewa an amince a sakesu d'in ne, saboda wanda ya sakasu aikin bayada babban amini sama da basamude, ya yarda dashi sosai. Bak'in k'yalle ya nema ya d'aure masu fuskokinsu dashi, cikin motarsu mai tint suka sakasu sannan suka tayar da ita suka bar wajen. A daidai GRA suka fiddo Dr. Rafiq da Ummanshi sukayi jifa dasu tare da barin wurin a d'ari uku da hamsin. Da k'yar da wahala Dr. Rafiq ya samu ya warware avubda aka nad'e fuskarshi dashi, Babu wahaka kuwa ya kwance na ummanshi ma. K'ara rungumarshi tayi cike da so da k'aunar d'anta. "Me ka masu ne Rafiqu? Me ka masu suke neman su illatani?" Ta sake fashewa da kuka. "Ummah muje gida zan miki bayanin komai insha Allahu, karki damu babu abunda na masu" ya bata amsa cikin sigar rarrashi saboda halin da yaga ta shiga abun tausayi ce. Da k'yar duka mik'e suka tari napep, har k'ofar gida ya kaisu Dr. Rafiq ya rok'eshi da yayi hak'uri har ya shiga gida ya fito masa da kud'insa, Bayyi kusu ba kuwa hakance ta kasance. Bayan sun natsu sosai k'annen Dr. Rafiq mace da namiji hankalunsu a tashe suka tambayesu inda suka shiga, Hakan yasa ya labarta masu komai har case d'in Ummimah wanda shine silar kama Ummansu da akayi shima kuma suka tsareshi wurinsu kawai dan kar yaje ya bayar da shaida, Ya kuma fad'a masu alj'awarin daya d'auka akan ba zaije ko Katsinar bama. K'anwarshi mace mai suna Dijah ta share hawaye tace "Gaskiya yaya gwara da kace masu ba zakaje ba, saboda nikam ban goyi vayan zuwankan ba, komai zai iya faruwa idan har kaje ka bayar da shaidar, saboda rayuwar yanzu abar tsoro ce". "Hakane kam Dijah, hausawa sunce 'zaman lafiya dukiya' dan haka mu fita batunsu kawai, idanma shari'ar vata warware ba sai su barsu da Allah shi zai masu sakayya, amma kai kam ka zare hannunka kenan" k'aninshi Shureim ya fad'a yana kallonshi. Cike da jarumta ummansu tace "Na amince koda ace zan rasa rayuwata kaje ka bayar da shaidar duk abunda ka sani, a yanda ka bani labarin na fahimci yarinyar tanada buk'atar taimako, kuma idan har gaskiya bata fito ba to za'a iya yanke shari'ar duk yanda akaga dama saboda basuda wata hujja dakai kad'ai suka dogara, dan haka na amince ka tashi ka tafi Katsina yanzu!". Cikin mamaki ya kalli umman tashi yace "Ummah kin amince?", "Ehh na amince Rafiqu, idanma kaga baka yarda daka barni ba sai mu tafi tare, nima zan bada tawa shaidar akan d'aureni da sukayi kawai dan kar kaje ka bayar da shaida". Kallonta ya sakeyi yace "Amma kuma Ummah ai har an zauna shari'ar tun jiya wata k'ilama har an yanke hukunci", "Babu komai nidai muje, insha Allahu sai yarinyar tayi nasarah". °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [11:07pm, 4/02/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~76~} _Jinjinar ban girma gareki k'awar arzik'i *Ayusha Iliasu* hak'ik'a ke jarumace, ki godewa Allah da irin d'umbin baseerar daya baki, kin cancanci yabo akan littafinki mai taken *Hak'k'i* Allah ya k'ara miki baseerah da zak'in hannu, Allah ya k'ara d'aukakaki yasa kifi haka. #onelove#_ ***** A Katsina kuwa Umar ya gama maganar komai yanzu suna jiran ranar shuga kotu ne kawai, Ummimah yanzu ta d'an samu kwanciyar hankali amma ba sosai ba, Saboda gani take yanzu wannan itace damarsu ta k'arshe idan har basuyi nasarah ba tofa shikenan, Addu'ah ta rik'a sosai sannan kuma mamanta ma tana tayata. Ana gobe za'a shiga kotu ne Haydar ya fara zazzab'i, Sosai jikinshi yayi zafi sai rawar sanyi yakeyi, Matuk'ar tashin hankali Sultana ta shiga saboda tunda take da Haydar bai tab'a yin zazzab'i mai zafin wannan ba, Ya mak'alewa Safiyya da ita kawai yake yarda, Hatta da ita Sultana d'in baya yarda da ita ko Umar babanshi. Hakan yasa daren ranae ya nacewa Safiyya yace lallai sai tare da ita zai kwana, Babu yanda Sultana batayi dashi ba akan ya kwana tare da ita amma sam yak'i yarda harda su hawaye, Ganin yana neman ya fasa mata kuka yasa ta mik'awa Safiyya shi tace ya kwaba tare da ita. Har sun kwanta Sultana taje d'akin Hafsa ta d'auketa saboda bai kamata Hafsa ta kwana ita kad'ai a d'aki ba, Sannan kuma a musulunce ma babu kyau su kwana tare da Hafsa saboda shekarunta sun wuce na ma'aurata su kwana tare da ita, D'akin Safiyya ta kaita ta kwantar, Ta samu Haydar ya mak'alk'ale Safiyya tsam kamar ance za'a k'wace masa ita, Cike da tausayi ta kwantar da Hafsa daga can gefe sannan ta tofesu da addu'ah ta koma d'akinta, Haka kawai take jin wani irin yanayi maras dad'i, Kawar da duk wani tunani tayi tare da barin d'akin ta nufi inda Umar. Ta sameshi ya tasa takardu gaba yana rubuce rubuce, Cike da soyayya tace "Sannu da aiki honey", "Yauwa wifey kema sannu" ya fad'a yana mata murmushi. "Bakaga yanda Haydar ya mannewa Safiyya ba, kamar wanda akace za'a k'wacewa ita, Nikam bansan wace irin soyayya Haydar yakewa Safiyya ba, Bansan ya zayyi idan zatayi aure ba, Saboda dai macece dole wata rana zatayi aure, koni bana mata fatan tayita zama a k'ark'ashinmu ba tare da tayi aure ba", "Insha Allahu kafin tayi aure ma yayi wayo, kinga babu maganar wahalar rabuwarsu kenan" Umar ya jefo mata amsa bayan ya rufe takardar da yake rubutu akai d'in. "Hakane honey, har ka gama aikin ne?" Ta tambayeshi bayan ta haye bisa gado saboda bacci takeji sosai yau. "Ko ban gama ba ai dole in daina in kula da iyalina" ya bata amsa had'e da hauewa gadon shima. "Nikam dama kaci gaba da aikinka, saboda bacci nakeji sosai yau, harda wani irin ciwon kai nake tsabar baccin dake idona" ta k'arisa maganar cikin hammar bacci harda d'an guntun hawayen hamma. "Nima dai baccin nakeji sosai, kiyi baccinki to barin k'arisa saura kad'an sai nima in kwanta, bana son in fita gobe ban gama wannan aikin ba", "Ok good night dear" ta fad'a bayan taja blanket ta rufa. _3:30am_ Wasu mutane uku ne fuskokinsu sanye da mask k'wayar idonsu kawai ake iya gani, Hannayensu rik'e da bindigogi k'anana ba masu girma ba, Kayan jikinsu kuwa complete black ne. A hankali had'e da sand'o suke tafiya har suka iso bakin gate, Kasantuwar a rufe yake yasa d'aya daga cikinsu ya zaro wani k'aramin abu daga aljihunsa, A daidai inda sakatar take ta ciki ya zira siririn abun babu b'ata lokaci kuwa k'ofar ta bud'u. Shiga ciki sukayi har yanzu sand'a sukeyi, K'ofar da zata sadasu da cikin gidan ma a rufe take, Yanda yayima gate haka yayi yanzu ma, Aikuwa suka shige cikin gidan a hankali d'aya daga cikinsi ya kunna 'yar fitila maras haske sosai. Tsaye sukayi cak kasantuwar sun rasa d'akin da zasu dosa, Sundai san an basu tabbacin Sultana akeso su kashe amma kuma ga jerun d'akuna nan basu san ta inda zasu nufa ba. D'akin dake fuskantarsu suka taka a hankali suka shiga, Ummimah da Mama ce kwance suna bacci, hakan ya tabbatar masu da babu Sultana a ciki. Fita sukayi daga nan suka doshi d'ayan d'akin, Zarah da Rabiatu ne suma sunata kwasar baccinsu. D'an guntun tsaki daya daga cikinsu yayi sannan suka juya suka fita daga d'akin. Na can nesa da parlor'n suka shiga inda suka samu Safiyya da Haydar kwnace, sai Hafsaacan daga gefensu suna bacci, Wannan ya basu tabbacin Sultana ce saboda sukam ba'a lissafa masu da akwai mai rainon yara a gidan ba. Murmushi sukama junansu sannan wani ya nemi inda ake kunna hasken d'akin ya kunna. Ya kunnawa kuwa Hafsa tayi saurin tashi zaune saboda ita dama indai akwai haske to ba zata iya yin bacci ba, Zaune ta tashi sai rarraba ido take hankalinta tashe take kallonsu, Ita a zatonta ma ko a d'akinta take dan bata san sanda Sultana ta dawi da ita d'akim Safiyya ba. Matsawa tayi inda Safiyya ta bubbugata da k'arfi kuwa ta tashi zaune, D'aya daga cikinsu wanda da alamar shine oga ya zare mask d'inshi had'e da yin wani shu'umini murmushi yana kallon Safiyya, "Barr. Sultana ko? Karki damu saboda damuwarki zata iya sakawa kiyi ihu, ihunki kuwa zai iya kawo k'arshen rayuwarki". Cike da tsoro Safiyya ta dad'e bakinta ta samu kanta da kasa fad'aasu ha ita bace Sultana. Hafs ata bud'e baku zatayi magana kenan ogan yayima wani signal ya fesa wata powder a daidai fuskar Hafsa, take kuwa ta fad'i sumammiya a bisa gadon. Hankalin Safiyya ya k'ara tashi, Tana so tayi kuka amma tana tsoron karsu mata wani abu, Karkad'a kai kawai take alamar kar suyi mata wani abu, Wani bak'in k'yalle suka fiddo tare da fesa garin powder d'in nan a jikinshi sannan suka k'ulle mata bakinta dashi. Kan bindiga wani ya k'wala mata aikuwa itama ta sume sai jini ke fita daga kanta kamar anyi yankan wata dabba, Tun daga nan bata kuma sanin abunda ya faru ba. 'Daukarta sukayi suka nufi waje da ita a hankali dan kar a jisu, saida suka fita suka sakata a mota sannan Haladu mai gadi yaji k'arar motar, Da sauri ya taso a rikice, ganin k'ofar gate a bud'e ne ya k'ara rikita rayuwarshi, D'akinshi ya koma ya d'auko makamai sannan ya fita waje, Hasken motar kad'an kad'an yake hange har suka b'ule, Sosai yaji haushi ya koma d'akinshi yayi tagumi, Baccin da bai koma ba kenan saboda yana tunanin abunda yasa ya iske k'ofa bud'e bayan kuma shi ya tabbatar da ya rufeta kafin ya kwanta, Sannan kuma ga k'arar mota da yaji wadda asukwane suka bar area'n unguwar. _kudai k'ara hak'uri da gajerun shafi, bamu gama hidimar bikin bane, amma daga gobe insha Allahu zamu gama zakuci gaba da samuna kamar ko yaushe._ °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [11:40pm, 6/02/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~77~} _Wannan shafin naki ne masoyiyata *Ummu Nawal,* nagode k'warai da yanda kike kula tare da bibiyar wannan labarin, Amrah luvs youh much #onelove#_ **** Washe gari. Tunda sassafe Haydar ya tashi daga barci, ido ya bud'e bayan ya lalaubi Safiyya bai jita ba, Daga can gefe ya hangi Hafsa tanata sharar bacci abunda cikin kwanciyar hankali. Zaune ya tashi jikinshi zafi rau yana fad'in "Aunt Shafiyya" amma shiru baijita ba dan a tunaninshi ko tana toilet ne, Sauka yayi daga kan gadon ya fara knocking toilet amma har yanzu baiji alamarta ba. Kuka ya fasa da k'arfi tare da barin d'akin ya doshi kitchen ko tana can amma saa b'uruntun Sultana daya jiyo tana had'a break fast saboda sammako zasuyi a kotu. K'arar kukanshi data jiyo yasa tayi saurin fitowa ta tareshi dan dama a tsarinta bata barin yaro ya shiga kitchen saboda tana amfani da gas da electric, "Haydar wats your problem?" Ta tambayeshi bayan ta rungumeshi. "Momy banga Aunty shafiyya ba tunda na tashi" ya fad'a cikin kuka. "Kajika Haydar da wata magana, yo ina zataje kuwa? May be ko ta shiga toilet ne yasa baka ganta ba, kayi shiru ka daina kukan nan ba nisa tayi ba" Sultana ta fad'a cikin sigar rarrashi tana rarrasar d'anta Haydar. Da haka har ta samu yayi shiru ta kwantar dashi parlor kan three seater wani baccin ya d'aukeshi, Murmushi tayi tare da nufar komawa kitchen saiga Ummimah ta fito, "Ina kwana Aunty?" Ta fad'a bayan ta duk'a har k'asa. "Lafiya k'alau Ummimah, ya jiki ya warware ko?", "Alhamdulillah ya warware sosai Aunty, yaune zamu fara zama ko?", "Ehh yau ne kuma yanzu ma bada dad'ewa ba, ance k'arfe takwas ta mana can, saisa na tashi na fara had'a break fast dan karmu makara", "Ok Allah ya taimaka ya bamu nasarah Aunty, baki ba zai iya gode maku ba saboda duk wata hanya da zamubi domin gode maku kun wuceta, addu'ah kawai itace ta dace daku, Allah ya saka maku da alkhairi ya rabaku daga sharrin shaid'an daku da zuriyarku", "Ameen Ummimah, muci gaba dai da addu'ah insha Allahu zamu dace". Murmushi tayi sannan tace "Muje in tayaki aikin Aunty". Tare suka shiga kitchen d'in sukaci gaba da aiki sunayi suna fira, Jin har yanzu Safiyya bata fito ba kuma abunda ba halinta bane yasa Sultana bin sawunta, A hanyar fita kitchen Zarah da Rabiatu ma suka biyosu, Bayan sun gaisa Zarah tace "Munzo mu tayaki aikin ne Aunty". Murmushi fal a fuskarta tace "Ai dama kunyi zamanku wallahi har mun kusa k'arisawa, nasan 'yan mata da son barcin safe", "Babu komai Aunty aima mun tashi tun d'azu har mun shirya" Rabiatu ta fad'a tare da shigewa kitchen d'in Zarah tabi bayanta. D'akin Safiyya ta shiga da nufin taga ta shirya Hafsa amma da mamaki sai taga sab'anin haka, Hafsa kwance har yanzu bata tashi ba sannan kuma babu Safiyya, Mamaki taji sosai sannan tace "Safiyya" amma shiru babu amsa, Bakin toilet d'in ta nufa tace "Wai lafiyanki kuwa Safiyya?" Nan ma dai shiru. Bankad'a k'ofar tayi taga wayam babu kowa a ciki, Dawo da kallonta tayi a gado saima yanzu ta kuka da jini dake kwance bisa zanin gadon, Hankali tashe ta matsa inda jinin yake ta tabbatar da jinin gaske ne. A rikice ta fita daga d'akin ta nufi d'akin Umar duk hankalinta ya tashi, "Uncle Umar banga Safiyya ba, sai jini kwance a bisa gadonta" ta fad'a a hargitse. Fita tayi yabi bayanta shima hankalin nashi ya tashi, Ganin jinin da yayi yasa yaci burki yana k'wala mata kira, "Safiyya! Safiyya!!" Amma babu ita, "Ya salam" ya fad'a a bayyane, "Meya kawo jini a bisa gadonta? To ina ta shiga?" Ya tambayi kansa, Ganin baida amsar tambayar yasa yace "To ai ba zamu tsaya anan ba, wata k'ila ko ta zagaya bayan gida ne". Fita yayi Sultana tabi bayanshi duk da bata zaton Safiyya na baya, saboda inhar tana can to meya hanata shirya Hafsa School? A daidai k'ofar da zata fitar dasu daga parlor sukaci karo da Haladu mai gadi, "Sannu yallab'ai" ya fad'a yana kallon Umar amma shi Umar neman hanyar fita kawaa yake. "Yallab'ai akwai matsala fa" Haladu ya sake fad'i yana kallon Umar. "Kabar wannan matsalar har sai mun gano inda 'yar mutane take sannan ka fad'eta" Umar ya bashi amsa cike da tashin hankali. "Yallab'ai wata k'ila wannan matsalar tanada nasaba da b'atar Safiyya" Haladu ya fad'a bayan ya kawar da kanshi daga idon Umar yana kallon Sultana. Cikin fargaba Sultana tace "Muna saurarenka Haladu". "Yallab'ai dama yau da tsakar dare..." ya kwashe duk abunda ya faru ya fad'a masu, 'Babu ko tantama sun tafi da Safiyya, kuma sunyi tunanin Sultana ce yasa suka tafi da ita' Umar ya fad'a a ranshi. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allahumma ajirna fi musibati, wakhlifna khairun minha' Sultana ta furta bayan ta duk'e k'asa ta saki wani kuka mai k'ara wanda yake cike da tausayi. K'arar kukanta ce ta fito dasu Ummimah, Parlor'n suka iso a bakin k'ofa sukaga Sultana ta had'e kai da guiwa tanata rizgar kuka, Cike da tausayi suka k'arisa inda take, Tambayarta abunda ya faru suka hau yi, bata b'oye masu komai ba tun daga farko har k'arshe saida ta fad'a masu. "Allah sarki nasan duk mune muka ja mata, Allah dai yasa karsu mata komai, duk abunda zasuyi ya tsaya a kanmu muda mukayi laifin ba wai yarinyar da batajiba bata gani ba" Mama ce tayi wannan maganar a daidai lokacin data iso d'akin saboda taji duk maganganun da sukeyi. "Ki daina fad'in wannan maganar mama, insha Allahu idanma dan karmu shiga kotu yau ne yasa sukayi wannan aika aikar to sunyi a banza, saboda da izinin Allah bada jimawar nan ba zamu tafi, duk abunda zasuyi saidai suyi, nasan dai Allah ba zaima bawa abunda ba k'addararsa ba, duk abunda ya samu bawa to tabbasa dama can k'adddararsa ce, dan haka kuje ku fara shiri ba gudu ba ja da baya, kudai kawai ku sakata a addu'ah, bansan ya zanyi ba idan suka kashe Safiyya, mun shak'u sosai ta shak'u da yarana, Harma tafi sanin damuwarsu fiye dani saboda ta fini zama dasu, Idan sun kasheki Allah yaji k'anki Safiyya, Allah yayi miki sakayya, A iya zamana dake baki tab'a k'untata min ba, Kullum burinki shine kiga kin faranta min, Yanda kike son yarana kuwa ko ke kika haifesu sai haka, Idan kuma kina raye sun b'oyeki ne Allah ya bayyanaki, Allah ya kub'utar dake daga hannunsu, Allah ya dawo dake garemu" Sultana ta k'ara fashewa da kuka. Sosai Umar ke rarrashinta amma ina, ko saurararsa batayi, A yanda ta shak'u da Safiyya ko 'yar uwarta ta jini sai haka, Bare kuma dama ita ta rasa iyayenta tunda yarintarta, Ta rasa d'an uwanta Hassan d'inta ta hanyar lalata rayuwarsa da akayi, Daga mijinta sai Safiyya ne da 'ya'yanta kawai take gani taji dad'i, To yau kuma gashi an rabata da Safiyya, bata san inda aka kai mata ita ba, Ita yanzu batama san me zata fad'awa iyayen Safiyya ba. Da k'yar ta iya tashi ta shirya cikin jar atamfa da manyan flower bak'ak'e, d'inkin doguwar riga ne wadda ta saukar nata har k'asa. A daidai fitowarta Su Ummimah suka fito, Dukkaninsu babu mai walwala saboda b'atar Safiyya. Umar ya kalleta cike da tausayi yace "Motar ba zata d'aukemu ba, Ki tafi da taki sai su shiga ciki suma, Hafsa kuma dama ta makara makaranta dole saidai ta bimu, Haydar ma babu mai rainonshi dole tare zamu tafi". Kai kawai Sultana ta d'aga masa har yanzu bata cikin natsuwa. Tare suka fito suka shisshiga mota, Haladu ya bud'e masu gate kenan wata matrix ta tsaya a k'ofar gidan, Alama akayiwa Umar dake gaba daya tsaya, Babu musu kuwa ya kashe motar tare da fita ya doshi inda waccan matrix d'in take. _na tayaka murnar zagayowar ranar haihuwarka Abdul Jega (Mr. Smiles), Allah ya k'ara maka shekaru masu albarka ya baka mata ta gari, sorie for the late wishes my bruh._ °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [11:16pm, 7/02/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~78~} _wannan shafin tukuici ne gareki my dear *Ummu Shureym,* hak'ik'a ke masoyiya ce ta gaske, Allah yabar soyayya da k'auna ya raya mana Shureym bisa tafarkin sunnah. Amrah LYSM #Onelove#_ ***** Mamaki fal a fuskar Umar yake kallon mutanen dake cikin matrix d'in, A hankali mutumin ya fito bayan ya kashe motar, Murmushi yayi tare da mik'a masa hannu yace "Assalamu alaikum", Shima hannun ya mik'a masa amma kuma bai amsa sallamar ba saidai kallo kawai da yake binsa dashi. "Ka daina mamaki Barr. Umar, nine d'in dai Dr. Rafiq wanda kukayi dashi zaije kotu ya bayar da shaida sai kuma wani dalili ya hana, amma yau a shirye yake daya bayarda shaidar duk abunda ya sani kuma tsakaninshi da Allah". Murmushi Umar yayi yace "ina ka shiga Dr. Rafiq? Aimu munyi zaton ko kaima sun siyeka da kud'i ne, tuni aka yanke hukunci amma mun d'aukaka k'ara, yanzu haka shirin tafiya kotun muke saboda yaune zamu fara zama". Muryar mace ya jiyo tace "Ba za'a tab'a siye Rafiqu da kud'i ba d'an nan, shari'ar nan tana ransa kawai dai an nuna anfi k'arfinsa ne..." Umman Rafiq ta kwashe duk abunda ya faru ta fad'awa Umar, Sultana ma tana tsaye tana saurarensu wani irin dad'i taji a ranta, Itakam dama tayi mamakin rashin zuwansa kotun, ta tabbatar da akwai wani babban dalili daya hanashi zuwa lokacin da ake buk'atar ganinshi. Har k'asa ta duk'a ta gaishe da Umman Rafiq sannan ta gaishe da Rafiq d'in ma, Motarsu suka koma Sultana ma ta koma ta shiga tata wadda su Ummimah ke ciki suna hangen duk abunda yake faruwa amma kuma basu san kome ake fad'i ba. Bayan ta shiga ta labarta masu duk abunda ya faru, hamdala Mama tayi sannan tace "Allah majik'an bawa, dama shaidarshi ake nema kuma gashi Allah ya kawoshi, Allah dai ya kawo mana k'arshen wannan shari'ah ya bawa mai gaskiya nasarah", "Ameen" su duka suka amsa dashi sannan Sultana ta tayar da motar, Umar ne gaba sai Dr. Rafiq a bayanshi, Sultana kuma a bayan Rafiq, a hankali suke tafiya har suka isa court of apeal. Sun samu motoci da yawan gaske a pake, hakan ya tabbatar ma Umar da cewa su kad'ai ake jira, Savoda tun k'arfe takwas akace suzo za'a fara shari'ar yanzu kuma gashi har takwas da rabi ta wuce. A hanzarce suka zira rigunansu sannan suka shiga, Wuri d'aya su Sultana suka zauna da Umman Rafiq da k'annenshi biyu, Sultana da Umar kuma suka tafi inda aka tanada domin zaman lauyoyi. Bayan sun zauna baifi da minti biyar ba alk'ali ya iso, Mazauninsa ya zauna sannan mai gabatar da k'ara ya tashi ya gabatar. "Kotu tana son ganin Aishatu Abubakar wadda ta kawo k'ara da kuma Salmah Abubakar wadda ake k'ara" alk'ali ya fad'a tare da yin d'an rubutu a takarda. A hankali Ummimah ta taso ta tsaya cikin akwatin tuhuma, Salmah ma tasowar tayi ta tsaya itama a cikin akwatin tuhuma wanda ke kusa dana Ummimah. "ba sai an tsaya wani dogon bayani ba, kamar yanda kowa ya sani cewa wannan k'ara ce aka d'aukaka, dan haka zamu so wanda suka kawo k'arar su tashi suyi bayanin dalilinsu na d'aukaka k'arar sannan su bamu hujjarsu ta farko". Cike da natsuwa da kamun kai Sultana ta tashi tsaye, "Sunana Barr. Sultana Saddam Bakori, a tare dani akwai Barr. Umar Mohd Bashir, mune wanda muka d'aukaka k'ara, Dalilinmu na d'aukaka k'ara kuwa shine; an yanke hukunci a zamanmu na kotun daya gabata wanda kuma hukuncin bai mana ba, Shine muka d'aukaka k'ara a wannan kotu mai adalci tare da hujjojinmu wanda muke fatan kotu zatayi masu duba ta yanke hukunci ga mai laifi". "Kotu ta gamsu da dalilinku na d'aukaka k'ara, tana jiran hujjarku ta farko" alk'alin mai cike da dattako ya fad'a yana kallon Barr. Sultana. A kotun data gabata, akwai likita wanda yake shine ya duba Ummimah a lokacin da aka kaita, shine ya tabbatar da fyad'e aka mata, Munyi dashi cewa zaije ya bayarda shaida, sai kuma mukajishi shiru baizo ba, kasantuwar dama dashi kad'ai muka dogara yasa aka yanke hukunci bamuda wata hujja, To yanzu dai yana kusa kuma ya halarci kotun nan, Zanso kotu mai adalci data bani dama domin gabatar dashi dan aji ta bakinshi". Kai alk'alin ya jinjina kafin yace "Kotu ta baki dama Barr. Sultana". Tasowa Dr. Rafiq yayi ya iso inda aka tanadar dominshi, Tunda ya taso Gentle ke binshi da kallon mamaki, itakam sam batayi tunanin zaizo ba, Hankalinta kuwa ya matuk'ar tashi dan tasan zayyi bayanin duk abunda ya faru. Qur'ani aka bashi ya dafa tare da fad'in "Nayi alk'awarin zan fad'i gaskiya tsakanina da Allah". Sultana ta matsa inda yake tace "Dr. Rafiq inaso kayiwa kotu bayanin tun dawowarka daga Lagos ina kaji? Sannan kuma me ya hanaka zuwa kotu domin bayarda shaida?", "Ranar dana dawo daga Lagos shine ranar jumu'ah, ko a ranar munyi waya da Barr. Umar kuma na k'ara tabbatar masa da zanzo, Kwatsam ina shirin tahowa da rana tsaka wasu mutane suka shigo mana manya manya abun tsoro, Cike da fargaba na tambayesu 'me sukazo yi?', Basu bani amsa ba saa d'aukeni da mari da babban cikinsu yayi, Fitowa sukayi dani daga d'akina, a parlor na tayar sun nannad'e Ummana da igiya sannan sun nad'e mata bakinta da selotape, A lokacin k'annena basu nan, Tafiya sukayi damu bayan sun nad'e mana fuskoki dan kar musan inda zasuje damu, A wani d'aki suka jefa Ummah ni kuma suka barni a tsakar gida, Saida muka kwana biyu a haka sannan suka min bayanin dalilin kamomu da sukayi, Sukace 'inhar na kuskura na sake ko waiwayarku barin har inyi tunani bayar da shaida sai sun kashe Ummana', Na masu alk'awarin ba zanyi ba, bayan mun dawo gida shine Ummah tace 'kome zai faru saidai ya faru amma sai na bayar da shaida ta amince, tun a ranar mukayi niyyar tafiya amma saboda mun san ana bibiyarmu yasa muka jinkirta vamu taho ba sai jiya, Tun jiyan muke neman gidan Bar Umar muka rasa, Sai daga baya bayan mun sauka hotel muka tambayi wani mutum shine ya mana bayanin gidan, Da safen nan myka nufi gidan shine Allah ya had'amu dasu a hanyarsu ta zuwa nan kotu". Cike da gamsuwa alk'ali ya d'aga kanshi. Sultana tace "Kotu zata so ka fad"a mata duk yanda abun ya faru bayan an kai Ummimah clinic d'inka, Sannan kuma abokin aikinka Dr. Khalid ya tabbatarwa kotu a baya cewa clinic d'insa ce kawai dai ya d'aukeka aiki ne, shin ya abun yake?" Cikin mamaki Dr. Rafiq ya kalli Barr. Sultana yace "Ba gaskiya Dr. Khalid ya fad'awa kotu ba, Asibiti dai tamu ce ni da shi muka had'a k'arfi da k'arfi muka bud'eta, Ya zuba dukiyarshi nima kuma na zuba tawa, a lokacin ma ni kad'ai nayi niyyar bud'eshi sai ya rok'eni akan yana so mu bud'e tare, Saida Ummana ta musa hakan amma daga baya ta amince saboda taga yanda muka shak'u dashi, Na amince masa muka bud'e asibin saisa muka saka mata *'KADRAQ CLINIC'* inada hujjar hakan saboda ina tafe da takardun asibitin baki d'aya, wanda shima kuma Dr. Khalid d'in yana dasu, idan ya musa wannan bayanin da nayi sai ya kawo nashi wanda suka tabbatar da cewa clinic d'inshi ce shi kad'ai" ya duk'a k'asa ya d'auko 'yar jakarsa, A hankali yake d'aga takardu har yakaiga ta asibitin, Mai gabatar da k'ara ya karb'i takardar tare da isar da ita ga alk'ali. Bayan ya karb'a ya dudduba yayi rubutu a takardarsa sannan ya dawo da ita ga Sultana, "Wannan bayanin da hujja da Dr. Rafiq ya kawo kad'ai ya isa ya tabbatarwa kotu da cewa Dr. Khalid mak'aryaci ne, idan kuwa shi mai gaiskiya ne nasan yana kusa, zai iya kawowa kotu takardar da zata tabbatar da asibitinsa ce ita kad'ai". "Objection my lord!" Barr. Sa'eed ya fad'a, "Barr. Sultana tana k'ok'arin ta canja salon shari'ar nan, bayan kuma ba akanta muke ba, tana k'ok'arin tozarta Dr. Khalid ta hanyar k'aryatashi". "K'orafi bai karb'u ba, savoda Barr. Sultana k'ok'ari take dan tabbatarwa kotu da gaskiya ne Dr. Rafiq ya fad'a wanda ta wannan hanyar ce kotu zata san ganskiyar wannna lamari, Barr. Sultana kici gaba" ya miyar da kallonshi ga Sultana dake murmushin jin dad'i. "Ko zan iya ganin Dr. Khalid da takardarshi wadda sata tabbatar da cewa asibitinsa ce?". Cikin raba ido Dr. Khalid ya taso har ya iso kusa da Dr. Rafiq, "Kotu tana buk'atar ganin takardar kamar yanda na fad'a a baya" Sultana ta fad'a tana kallon Dr. Khalid. Cikin in ina yace "Nn.nn...banzo da ita ba, sssaboda banyi zaton za'a tambayeni ba", "Ka kwantar da hankalinka ka daina wannan in inar Dr. Khalid, A ina rakardar take yanzu?", "Tttttana can gida banzo da ita ba" ya bata amsa, "Kotu zata so ganin wannan takarda kuwa" ta jiya ga alk'ali tace "Ya mai girma mai shari'ah, ina neman alfarma da kotu ta d'aga wannan shari'ah zuwa goma ga watan biyu shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai, a wannan ranar muke buk'atar Dr. Khalid ya kawo mana wannan takarda, nagode ya mai shari'ah". Rubutu alk'alin yayi mai d'an tsawo kafin ya d'ago kanshi yace "Kotu ta yarda da alfarmar da Barr. Sultana take nema, Ta d'aga wannan shari'ar har saa gima ga watan biyu shekara ta dubi biyu da goma sha bakwai, koooootu!" Ya buga guduma tare da mik'ewa ya fice. _gaisuwa gareki *Basman mai sanyinta,* nagode da kulawa sosai, Allahu yabar zaman tare. ILYSM._ °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [10:03am, 9/02/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~79~} Tunda suka bar kotun su Brr. Sa'eed ke cuku cukun yanda zasuyi su buga takardar da zata tabbatarwa kotu cewa asibitin Dr. Khalid ce shi kad'ai, Da sa'a kuwa suka samu aka bugata yanda babu wanda zaiga takardar yace ta k'arya ce, ni kaima Amrah nayi,matuk'ar mamakin wannan takardar, saboda tama fi ta kirkin tsaruwa, babu wanda zai ganta yace ta k'arya ce sai ni da nasan kan zancen. Ana sauran kwana uku su koma kotu ne Sultana suka fita ita da Ummimah da Umar zasu koma police station maganar b'atar Safiyya, Sun tsaya a daidai roundabout suna jiran traffic light ya basu hanya, wani irin hold up ne sosai wanda basuyi mamakinshi ba saboda duk ranar Friday ana samun irin hold up d'in a duk fad'in garin Katsina. Wasu matasa ne su biyu akan mashin suna tuk'insu cike da natsuwa har suka kutso ta daidai inda su Sultana suke, Kallon mamaki ta bisu dashi kafin tace "Wai nikam honey ka gane wancan masu mashin d'in?", D'aga kanshi yayi tare da sauke gilashi ya kashe AC, ya kallesu sosai yace "Ya bazan ganesu ba, basu bane mashayan nan wanda muka tab'a had'uwa dasu har wancan na gaban ya bani complimentry card d'insa?", Murmushi ta masa tare da fad'in "Ehh lallai ka ganesu, tunda suka k'ariso nake kallonsu sai daga baya na tuna ashe sune", "Aikuwa dai kinga sune, haka fa rayuwar d'an shaye shaye take, baya da wani galihu a rayuwarsa, kullum a tozarce yake saboda baisan me zai aikata ba a cikin halin mayen da yake", "Wallahi kuwa, vatada wata amfani rayuwar, hatta da matar aure ba lallai ya samu ta kirki ba, to ina dalilin wannan rayuwar kuwa". Suna cikin surutunsu basu san an basu hanya su wuce ba, matasan dake kan mashin d'in kuma basu da hanyar da Asu wuce saboda daga d'ayan gefensu daf ce babba, Hakan yasa suka k'ara kutsowa daidai gilashin da Umar ya sauke na gaban mashin d'in yace "Haba malam ya zaku ringa fira kuma ku kasa bamu hanya mu wuce?". Caraf Ummimah taji muryar da ba zata tab'a mantata ba a rayuwarta, Shiru tayi tare da fad'awa a kogin tunani, Har suka bar wurin bata saa lokacin da suka rabu da masu mashin d'in ba, A bakin police station d'in suka isa duk suka fita a mota amma Ummimah tunani take, Hankalin Sultana ya tashi har ta bud'e motar saitin Ummimah amma duk bata san anyi ba, Zama tayi daga gefenta tace "Ummimah" amma bata san tayi ba, D'an bubbugata tayu firgigit ta dawi hayyacinta tana fad'in "Ina yake? Wallahi yana cikinsu, amma shi bayyi ba, nasan muryarsa bazan tab'a mantawa da ita ba, shine wallahi" ta fashe da kuka sosai tare da duk'ar da kanta bisa cinyoyinta. "Me kike fad'a ne Ummimah? Lafiyanki kuwa? Waye kike magana?" Duka a had'e Sultana ta jefo mata da wannan tambayoyin, Umar na tsaye abunku da Barr. Har ya fara fahimtar wani abu, "Muje kawai mu fito, idan mun koma gida kafin nan ta dawo hayyacinta sai mu mata ko wace irin tambaya", Tashi Sultana tayi tana k'ok'arin tayar da Ummimah, "Ki barta anan kawai ai ba dad'ewa zamuyi ba" ya fad'a bayan ya kama hanyar shiga station d'in, itama Sultana bin bayanshi tayi amma fa kanta d'aure yake, ta mastu taji inda maganar Ummimah ta dosa. Koda suka shiga basu wani dad'e ba, inspector ya shaida masu cewa tsaye suke ana bincike sosai kuma suna sa ran insha Allahu zasu samu nasarah, ya tabbatar masu da cewa yanzu haka akwai 'yan sandansu hud'u da kwanansu biyar basu nan, suna cikin gari banda aikin bincike babu abunda sukeyi. Cikin farin cikin wannan maganar Umar da Sultana suka koma mota, a yanda suka bar Ummimah haka suka sameta, saboda ji take tamkar waai tsohon tabo ne aka fama mata, "Ki daure ki daina kukan nan dukda bansan dalilinki na yinshi ba, kar ki tadowa kanki ciwo kinsan kinada hawan jini". D'ago rinannun idanuwanta tayi ta share hawayenta, amma kuma idan ta share sai wani ya ringa fitowa, A haka har suka isa gida bata daina kukan ba, A parlor suka samu su Mama zaune suna firar kotu ita dasu Zarah, Sallamah Sultana tayi ita dake gaba sannan suka shiga, Koda Mama ta kalli fuskar Ummimah ta tabbatar da ba lafiya ba, saboda idonta yayi jajur sannan har ya fara kumbura, Da gudu ta iso inda take tare da d'ora kanta bisa cinyar mama taci gaba da rizgar kukanta sosai kamar yanzu ne komai ya faru, Itama mama kukam take tana tambayarta abunda ya faru amma ta kasa fad'i. "Haba Ummimah? Ya zaki tayarwa mama da hankali bayan kuma kinsan ku duka biyun ba isasshiyar lafiya ne daku ba? Dan Allah ki daina mana, ki mana bayani tunda dai harmu da muka fita tare d'in bamu san dalilinki na yin kukan nan ba, ki mana bayani idan akwai abunda zamu iya yi miki sai muyi" Sultana ta fad'a cike da tausayi, Umar ma zama yayi daga can gefe yana sauraren abunda Ummimah zata fad'a. Da k'yar tayi shiru ta sauka k'asa, cikin rawar murya tace "Wallahi ko tantama babu muryar sarki Manu ce naji, wanda a cikin mutum tara shine kawai baimin fyad'e ba" ta sake fashewa da kuka. Su duka kallon mamaki suka bita dashi, kowansu ya kasa furta komai sai kallo, Zarah ce tayi k'arfin halin cewa "Ummimah kodai muryarsu tayi kama ne kawai? Naga Sarki Manu a Jalingo suke me zai kawosu Katsina?", "Kamarya me zai kawosu Katsina Zarah? Kinsani ko dama d'an katsina ne? Wallahi ba zanyi kaffara ba muryarsa ce naji, shine kawai yake da imani a cikinsu, shi kad'ai ne yasan ko su waye sukamin fyad'e, ku taimaka ku tayani nemanshi domin ya tabbatarda Gentle ce ta sakasu suyi min fyad'e" ta k'ara fashewa da kuka tana k'ara jin tsanar Gentle a rayuwarta. Umar ya kalli Sultana itama ta kalleshi, bayan ta kawar da kallonta daga gareshi tace "Idan zan iya gano katinshi to tabbas wannan abu ne mai sauk'i, akwa complimentry card d'inshi wanda ya tab'a bamu farkon ganinmu dashi yana cikin maye yace wai Abban Hafsa ya d'aukeshi aiki, ban yar dashi ba yana ajiye, saidai kuma ganoshi ne zayyi wahala dan ba zan iya tuna ko wace jaka bace na fita da ita a lokacin". Saurin tashi tsaye Ummimah tayi ta matsa inda Sultana take, "Muje zan tayaki dubawa, wallahi kin k:ara tabbatarmin da shi d'in ne saboda ko a lokacin da sukamin fyad'e duk a cikin maye suke saishi ne kawai kuma naji suna ambatar yau baisha komai ba, alamar ya saba sha kenan". Tashi Sultana tayi tace "Muje to" bin bayanta Ummimah tayi suka shiga d'akinta. Baki d'aya jakunkunan dake rataye a bag hanger d'in saida ta saukosu, kamar mahaukata suke zazzage jikkunan amma basu samu ko wace takarda ba, Ko natsuwa basuyi waje dubawar har suka kai k'arshe, sake dudfubawa sukayi a karo na biyu amma babu su, Hankali tashe Sultana tace "Wallahi ni nasan ban yar da ita ba na sakata a jakata, amma da yake Hafsa bataji ta yiwu ita ta fitar tayi wasa da ita, amma kuma abun mamaki Hafsa bata tab'a min jaka idan na ajiye, akwai dai inda take". Jiki ba k'wari suka bar d'akin, da fitarsu kowa ya tabbatar da basu samu takardar ba, Umar yace "Ku d'auko duka jakunkunan ku kawo nan a duba a nitse, nasan ba lallai bane idan kun ajiye hankalinku wurin dubawa". Juyawa sukayi suka kwaso duka jakunkunan suka kawo, Cike da natsuwa Umar da Zarah ke dubawa, Rabiatu kam dama uwar kuka ce, tuni itama ta b'arke da kukan tana k'ara tausayin k'awarta. Wata peach hand bag Umar ya d'aga, a cikinta keda purse 'yar k'arama, bud'eta yayi yaci karo da complimentry card d'in matashin daya bashi. "Alhamdulillah, gashi na gani" Umar ya furta fuskarshi d'auke da murmushi. "Alhamdulillahi" duka 'yan d'akin suka had'a baki wurin fad'i. Karb'a Ummimah tayi ta karanta sunan, *'Sulaiman Usman Saraki, Sarki Manu'* Ummimah ta fad'a a ranta, "Yanzu sunan baizo d'aya ba?" Ta tambayesu, Saima yanzu sunan ya fad'o masu a rai, Umar cike da farin ciki yace "K'warai kuwa suna yazo d'aya, ko tantama babu, sarki manu shine mai katin nan". _kuyi hak'uri da wannan saida na rubuta dogo duka ya goge._ °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [10:47pm, 9/02/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~80~} Lambar wayar dake jiki Umar ya danna a wayarsa, latsa kira yayi take kuwa ta fara k'ara, Har ta tsinke ba'a d'aga ba hakan yasa ya sake kira, Saida ya kira sau uku sannan aka d'auka, "Hello-salamun alaikum" Umar ya furya a hankali bayan ya saka wayar a hands free. Daga can d'aya b'angaren aka amsa da "Wa'alaikumussalam, sunana Sarki Manu, how may I help you?", "Alhamdulillah, Sulaiman Usman Saraki, is that your real name?", "Of thats my real name" ya bashi amsa. "Sunana Barr. Umar Mohd Bashir, cikakken lawyer mai zaman kanshi, idan ba zaka damu ba akwai wata magana da nake so muyi da ka". Dafe gaba Sarki Manu yayi bayan ya sauke ajiyar zuciya, "Wace irin magana ce?" Ya tambayeshi. "Nafi so idan babu damuwa mu had'u dakai face-to-face muyi maganar". Shiru yayi kafin yace "Babu damuwa ina zamu had'u d'in?", "Ina kake ganin yafi? Wurinka ko kuma zakazo gidana?", "Ka bani address d'inka ni zanzo ko zuwa anjima ne insha Allahu", "Nagode kuwa abokina, yanzu zan texting maka address d'in" yayi hanging up na wayar. Sosai Ummimah taji dad'i, tasan Sarki Manu yanada sauk'in hali sosai, ba za'a sha wahaka wurin shawo kanshi ba. Bayan sallar isha'i kuwa Sarki Manu yazo k'ofar gidan, kiran Umar ya latsa tare da shaida masa gashi nan k'ofar gidanshi, Cike da jindad'i Umar ya fita ya sameshi tsaye ya paka mashin d'inshi, Gabanshi yaje yace "Har ka iso kenam abokina?", "Wallahi kuwa na iso, ashema gidan babu wahalar gamewa, tambaya d'aya kawai nayi", "Ehh ai dayake unguwar tamu sabuwa ce babu mutane sosai, gida baya wahalar ganewa", "Ehh na gani kam", "Bismillah shiga daga ciki" Umar ya fad'a tare da k'ok'arkn jan mashin d'in dan ya shigar dashi cikin gida. Koda suka shiga gida kai tsaye parlor'n bak'i Umar ya zarce dashi, A waya ya kira Sultana yace da ita 'a kawowa bak'o drink' da kanta ta sira hijabinta ta had'a exotic da cups guda biyu ta d'ora a tray ta kai ma Sarki Manu, Bayan sun gaisa ta fita tana nazarin a halin da suka tab'a samunshi, yanzu kam da alama duk ya tuba da wannan halayen ya daina su, saboda yanda ya sama a full gentle man. "Kasha lemo abokina" Umar ya fad'a bayan ya zuba masa a cup shima ya zuba a d'ayan cup d'in ya sha. Gyatsa yayi tare da hamdala ga Allah yace "Ina saurarenka Barr. Tun lokacin da mukayi wayar nan hankalima bai kwanta ba, na matsu inji neman da kake min, dan nasan koma wace irin magana ce to mai muhimmanci ne, saisa na zab'i mu had'u a gidanka dan mu tattaunata". Ajiye cup d'in hannunshi yayi bayan ya goge bakinshi da tissue yace "Ehh tabbas matsala ce kuma mai girma, abunda ya faru shine;......" ya kwashe komai tun daga farko har k'arshe ya fad'a masa. Saurin tashi tsaue Sarki Manu yayi ido bud'e yana mamaki sosai, "Malam da gaske kake wannan maganar ko da wasa kake?", Shima Umar mik'ewar tsaye yayi ya dafa kafad'ar Sarki Manu yace "Ka kwantar da hankalinka muyi magana sosai, am very serious about the issue, yanzu haka yarinyar tana nan cikin gidana as I told you". Zama yayi har yanzu mamaki yake, Saboda shi sam bayyi zaton Ummimah na raye ba, a yanayin halin da suka barta ciki babu wanda zai tab'a tunanin tanada rai, "in har da gaskene ina son ganin yarinyar, idan itace zan iya ganeta dukda kallon duhu na mata", "Karka damu yanzu kuwa zaka ganta" ya sake latsa kiran Sultana yace mata 'suzo ita da Ummimah yanzu'. Babu b'ata lokaci kuwa sai gasu sun shigo, Kallonta da yayi shi ya tabbatar masa da itace, Saboda ya rik'e kamannnta, nan ya hau tuno lokacin da takema abokananshi magiya akan su k'yaleta amma suka k'i, Wani irin kuka ya kufce masa wanda ya rasa gane kona menene, "Allah yaji k'anku abokaina" ya furta cikin kuka. "Abokanka? Su waye suka rasu?" Umar ya tambayeshi. "A duk cikin wanda suka mata fyad'e yanzu haka mutum d'aua kawai ke raye, kuma shima d'in yana can rai hannun Allah, tun lokacin da suka mata abun a duk cikinsu babu wanda ya sake samun farin ciki, Kullum cikin tashin hankali suke wanda suka rasa dalilin faruwar hakan, Kwatsam sati d'ayan nan daya wuce labari ya riskemu wai sunyi shaye shaye suka shiga mota shine motar ta kife dasu, mutum d'aya kawai ya rayu amma shima tamkar mataccen yake, Magana kawai yake iyayi amma baya ko iya tafiya, komai saidai a masa daga kwance, Sannan kuma a accident d'in yaji masa ciwo a mazakuntarsa wanda babushi babu aure har abada, silar wannan abun daya samesu na d'aukarwa kaina alwashin babuni babu shaye shayen kayan maye har abada, na duk'ufarma istighfari ko Allah zai yafe min laifukana a baya" ya sake fashewa da wani kukan. "Allah yaji k'an wanda suka mutu, shi kuma maras lafiyan Allah ya bashi lafiya, karka damu ai Allahi Gafurur-Raheemu ne, zai iya yafe maka kura kuranka", "To nagode sosai" ya fad'a bayan ya share hawayenshi. "To Sarki Manu zaka iya zuwa kotu ka maimaita duk bayanan da kayi yanzu?", "Me zai hana kuwa? Idan zaka yarda ma tunda yanzu dare yayi gobe muyi sammako mu tafi Jalingo, muje gidansu YB zan masa bayani, kuma nasan shima a shirye yake da zuwa kotu domin ya bada bayanin komai yanda ya faru, tunda dama tuni gang d'inmu muka rabu da AK tunda ya mana iskanci, nasan zai bada bayanin duk abunda ya sani may be ma a samu bayanin da koni ban sanshi ba". Murmushi Umar yayi yace "Aikuwa da naji dad'i sosai wallahi, Allah ya kaimu goben zan biyo in d'aukeka sai mu tafi", "Bama saika biyo ba, ni da kaina zanzo sai mu wuce, zanyi k'ok'arin zuwa da sassafe yanda zamu gama komai cikin lokaci mu juyo goben", "To babu damuwa saraki Allah ya kaimu goben sai kazo". Mik'ewa sukayi tsaye, bayan ya kalli Ummimah ya k'ara tausaya mata sosai yace "Karki damu komai ya kusa zuwa k'arshe insha Allahu, lallaima Gentle wato banda wulak'antaki da tasa akayi ashe harda kisa abun ya kai? Kuma suzo su fiki baki saboda su masu kud'i ne ko? Allah ya fisu tasu tazo k'arshe da izinin Allah". Share hawayenta tayi tace "Nagode sosai Allah ya saka maka da alkhairi", "Ameen" ya fad'a tare da ficewa daga d'akin Umar ya mara masa baya. Abunda ya kasance kenan kuwa washe gari, da sassafe yazo suka tafi Jalingo, Wuraren k'arfe goman safe suka isa, Kai tsaye gidansu YB Sarki ya kaisu, A k'ofar gida Umar ya tsaya shi kuma Sarki Manu ya shiga har cikin gidan, Ya samu hankalin 'yan gidan a tashe sanadiyyar ciwon YB daya motsa sai sabbatu yake yana fad'in mugayen halayen da suka aikata kafin wannan al'amarin ya faru, Cike da tausayi ya zauna kusa dashi yana fad'in "Sannu abokina, ka daina kuka insha Allahu zaka samu lafiya", "Ya za'ayi in samu lafiya bayan aika aikar da nayi kafin cutar ta sameni? Taya kake tunanin zan samu sauk'i Sarki Manu? Na tabbatar da matuk'ar ban nemi yafiya ga wad'anda na cuta ba to Allah ba zai tab'a k'yaleni ba, insha wahala anan kuma inje lahira ma babu kyau" ya fashe da kuka sosai yana matsar kanshu dake mishi barazanar fashewa. "Dan Allah ka daina fad'in haka, wata magana ce ke tafe dani..." ya masa bayanin komai tun daga farko har k'arshe. "Zanje! Wallahi zanje in bada shaida, san fad'a masu cewa mune muka mata fyad'e, zan tonawa Gentle asiri ince itace ta sakamu" ya fara k'ok'arin mirginawa amma ya kasa, Mahaifinshi dake gefe yana sauraren komai yace "Ka shigo da Barr. D'in nan ciki". Tashi kuwa yayi babu jimawa sai gasu sun shigo tare, Gaishesu Umar yayi ya masu ya mai jiki shima ya tausayawa rayuwar da YB yake ciki, Neman k'arin bayani mahaifin YB yayi, Umar bai b'oye masa komai ba kuwa, "Babu damuwa zamuzo tare insha Allahu, komai yazo k'arshe tunda dai ya amsa laifinsa yayi d'in, zai bada shaidar duk abunda ya sani". Da farin ciki su Umar suka bar gidan, yanzu kam insha Allahu komai yazo k'arshe kenan, yanzu abunda ya rage masu kawai su san inda Safiyya take, wannan d'inma sun san indai tana raye to zata bayyana da izinin Allah. _godiya ga masoyana masu bibiyar labarin *wata shari'ah* Amrah LYSM._ °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [11:58pm, 10/02/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~81~} *KOTU* Kotu ta cika mak'il dan zan iya cewa duk zaman da sukeyi babu wanda al'ummah suka halarta sosai kamarshi, Saboda sosai Alhaji Abu Abu ya gayyato mutane dan ya tabbatar da su zasuyi nasarah, tunda dai yasan su Barr. Umar basuda wata shaida saisa suka canja salon shari'ar, kuma ma canjin salon da sukayi bai amfana masu komai ba saboda gashi sunyi takarda wacce taci uwar original one d'in. Mai gabatar da k'ara ne ya tashi ya gabatar sannan alk'ali yace "Kotu na jiran Barr. Sultana domin taci gaba daga inda ta tsaya". Tasowa tayi bayan ta gyara daidaituwar rigarta ta iso inda Ummimah da Gentle suke, "Kotu na son ganin Dr. Khalid idan yana kusa, ya fito da takardar asibitinshi kamar yanda yayima kotu alk'awarin zai kawota yau". Tasowa yayi cike da confidence, takardar ya mik'ama Sultana ta duba sosai, saida gabanta ya fad'i saboda babu wanda zai ganta yace ba ta kirki bace, Ganin reaction d'in fuskarta yasa Barr. Sa'eed sakin murmushin mugunta sannan ya kalli Barr. Umar daya tsurawa Sultana ido dan shima ya fahimci yanayinta. Mik'a takardar tayi har ta isa ga alk'ali, Bayan ya dudduba sosai yayi rubutu sannan ya miyar da ita ga Sultana, "A bisa duba da kotu tayi ga wannan takardar, kotu ta gamsu da cewa asibiti dai ta Dr. Khalod ce shi kad'ai, dan haka batun wannan maganar ta kau". Dukda gabansu ya fad'i amma basu ji komai ba dan sun san duk wannan ba wani abu bane saboda babbar hujjar da garesu ta isa tasa a yanke hukunci yanzu yanzu. Wata takarda Sultana ta sake zarowa tace "Wannan takarda ce wadda ta nunar da cewa anyiwa Aishatu Abubakar fyad'e har sanadiyyar haka ta kamu da cutar hawan jini, Sannan kuma gashi nan k'asa signing d'inka ne farko sai na Dr. Rafiq a k'asa, Kenan kaima kasan fyad'e ne aka mata tunda har kayi signing?". Gabanshi ne ya hau dukan uku uku ya hau rarraba ido, "Ni wannan signing d'in ba nawa bane, akwai dai yanda akayi amma ni bansan da wannan maganar ba, abunda na sani d'aya ne kawai ta zubar da ciki ne, wannan takardar kawai nasan nayi signing amma fa ni ban ma tab'a ganin wannan d'in ba". Murmushi Sultana tayi tare da d'aga d'ayar takardar asibitin da yace itace tashi, "Dr. Khalid ka duba da kyau ka gani mana, waye zaiga wannan signing d'in kuma har ya banbantasu? Ko makaho ya laluba yasan iri d'aya ne kuma mutum d'aya yayisu, kadai canja magana". "Objection my lord! Barr. Sultana tana k'ok'arin forcing d'in Dr. Khalid akan ya amsa abunda bashi yayi ba, ya fad'a mata cewa wannan sugning d'in ba nashi bane amma kuma ita tayi insisting akan nashi ne bayan kuma batada wata hujjar data tabbatar fa hakan" Barr. Sa'eed ya fad'a jin ana neman k'ure Dr. Khalid. "Barr. Sultana a kiyaye" alk'alin ya fad'a tare da miyar da kallonshi ga Sultana. "Iyakar tambayar da zan masa kenan ya mai shari'ah" ta furta had'e da komawa mazauninta ta zauna. "Ko akwai mai magana a cikin sauran lawyers d'in" alk'ali ya tambaya. Tasowa Umar yayi ya gyara zama hularsa yace "Sulaiman Usman Saraki, Yusuf Bilal Mohd, kotu zata so ganinsu idan suna kusa". Daga k'ofar shigowa sarki Manu ya shigo, a bayanshi kuma gado ne irin wanda ake d'ora marasa lafiya d'in nan, YB ne kwance cikin gadon duk yabi ya lalace kamar bashi ba. Ido bud'e Gentle ke kallonsu, Ko a mafarki bata tab'a tunanin wannan rana ba, Shikenan yau tasu ta k'are, asirinta zai tonu kenan, Gabanta sai dukan uku uku yake ta kasa rufe bakinta, Tunani take waima ya akayi hakan ta kasance?, D'an marin kanta take wai idan ma barci takeyi ta farka. A k'asa aka ajiye gadon kusa da Ummimah, Gentke kuwa tasha mamkin halin da taga YB ciki, K'yafta masa ido kawai take tare da d'an murmushin yak'e wanda da k'yar take fiddoshi. Gyaran murya Umar yayi yace "Sarki Manu kotu zata so jin cikakken sunanka, garin daka tashi, sannan kuam menene alak'arka da Salmah Gentle?". Tuni Gentle ciki ya d'uri ruwa, zawayi take ji amma babu halin tace zatayi, Sai raba ido take tana kallon mahaifinta sannan kuma ta juya ta kalli lawyer'nta. "Sunana Sulaiman Usman Saraki, zan iya cewa na d'an tab'a rashin ji a baya kafin Allah ya shiryeni yanzu, alak'ata da ita kuwa ita budurwar wani abokinmu ne Abdul K'adir amma duk da AK muke kiransa". "Ko zaka iya yima kotu bayanin yanayin tarayyar Gentle da saurayin nata AK?", "ehh zan iya mana, yana sonta tana sonshi sosai, harma son da take masa yafi wanda yake mata yawa, hakan yasa ya rainata sosai saboda yaji tana yawan fad'in ba zata iya rayuwa idan babushi ba, Babu abunda zai nema a wurinta ya rasa, zina kuwa sun miyar da ita tamkar abincinsu, sun zama kamar miji da mata, abun nasu har a cikin makaranta yinshi suke kuma kusan kowa ya san da hakan, Wata rana...." ya basu labarin avunda ya faru ranar da akayima Ummimah fyad'e. Salati duka mutanen dake cikin kotun suka d'auka, Alhaji Abu Abu kuwa sai cire hula yayi, dukda sanyin da akeyi amma shi zufa yakeyi tsabar kunya da yaji, gashi d'an siyasa sananne kuma a gaban jama'a wannan abun yana neman ya kasance. "K'arya kakeyi wallahi ni banma sanka ba? A gidan uwarwa ka sanni? Kaji min mutum da sharri, ko tab'a ganinka banyi ba amma kake fad'in haka, ya mai shari'ah karka yarda dashi wallahi k'arya yake". Daka mata tsawa alk'ali yayi had'e da buga teburinshi, "Karki manta nan kotu ce ba wurin shirme ba, ki nemi izinin magana idan kina son kiyi ba wai ki sakota haka ba". Shiru tayi gabanta sai fad'uwa yake, Ji take tamkar k'afarta ba sata iya d'aukar gangar jikinta ba. Ga YB umar ya koma yace "Me zaka iya fad'i game da maganganun da Sarki Manu yayi?" Cikin muryar ciwo YB yace "Babu k'ari ko kad'an a bayananshi, Ina d'aya daga cikin wanda sukama Aishatu fyad'e kuma Gentle ce ta sakamu, Duk sauran wanda mukayi abun tare babu wanda ya sake samun kwanciyar hankali tun daga ranar da muka mata fyad'en, Kwatsam kwanakin baya munyi shayr shayenmu muka had'u da tsautsayin accident, baki d'aya mutanen motar suka rasu nine kawai Allah ya kub'utar dani, Tun daga wannan lokacin nake rok'on Allah ya had'ani da koda kad'an ne daga mutanen dana zalunta in nemi yafiyarsu, Kuma case d'in Aishatu yana d'aya daga cikin abubuwan da nayi wanda suke yawan fad'o min a rai, Tun daga wannan lokacin nake fatan Allah ya gwada mib ranar da san had'u da ita dan neman gafararta amma Allah bayyi ba sai yanzu, Ko tantama babu Gentle itace ta saka muka mata fyad'e, Bayan nan kuma akwai abubuwa da dama wanda ta saka aka mata, Itace ta tura 'yan daba suka sace k'annen Aishatu 'yan biyu, Tasa an kashe d'aya daga cikinsu aka kai gawarta kan layinsu aka yar, Itace ta had'a baki da manyan makaranta aka kori Aishatu akan laifin wai ta zubar da cikin shege harda fad'in wai ba wannan ne na farko ba, Itace tasa aka k'ona gidansu Aishatu wanda da bakinta ta bamu labari saboda ni nayi zaton ma bata raye, dan yanda muka mata fyad'e mu kusan takwas sauk'inta ma duk bamu da wani k'arfi sosai a lokacin saboda yanda muka bugu, Ban tab'a zaton ma tana raye ba saida ita Gentle d'in ta bamu wannan labaran, Ina rok'on wannan kotu mai adalci datayi gaggawar yanke mana hukunci tare da k'watarwa Aishatu hakk'inta" ya k'arisa maganar cikin rawar murya had'e da fashewa da kuka. Duk mutanen kotun babu wanda bayyi mamaki ba, Hamdala kawai ke tashi a ciki banda b'angaren iyayen Gentle da har yanzu suke ganin k'age ne aka mata. "Yanzu haka d'aya daga cikin k'annen Aishatu tana wurin Gentle a b'oye, banda azaba babu abunda ake mata" YB ya fad'a a hankali. Har Sarki Manu saida yayi mamaki sosai, saboda shi duk baima san da wannan mugayen abubuwan da Gentle tasa akama Ummimah ba. Kuka Gentle ta fasa da k'arfin gaske wanda duk fad'in kotun babu wanda baiji ba, "Na shiga uku ni Salmah, na cuci kaina, kai co na ni Salmah, dama hausawa sunce 'kwana dubu na b'arawo, rana d'aya tal ta mai kaya' yau gashi asirina ya tonu abunda ban tab'a zato ba, nasan tawa ta k'are saboda banida wata hujjar da zan kare kaina" a b'oye tayi maganar amma bata san a bayyane tayita ba, Baki d'aya kallo ya koma gareta saboda da k'arfi ne tayi maganar kowa ya ji. _nagode k'warai da yanda kuke bada lokacinku wurin karanta wannan labarin musamman *Asma'u Umar,* kina d'aya daga cikin manyan fans d'ina ina godiya sosai. Amrah LYSM._ °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [11:13pm, 11/02/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~82~} _wannan shafin tukuici ne gareki *Ummi Agoss,* nagode da bibiyar labarina da kike tare da nuna zallar soyayyarki a gareni. ILYSM._ ***** Hayani kotun ta d'auka baki d'aya sai cece_kuce akeyi, Alhaji Abu Abu kuwa mutuwar zaune yayi ji yake tamkar a mafarki ne, Barr. Sa'eed kuwa sai k'arema Gentle kallo yake yana mai tsananin jin haushinta, inda ace batayi maganar ba da yasan ta hanyar da zaibi dan lalata waccan maganar, amma kuma duka ta b'ata zancen. Bubbuga guduma alk'ali yayi da k'arfi sannan kowa yayi shiru, "Salmah Abubakar kinsan ko me kike fad'i kuwa?". Cikin hawaye Gentle ta d'aga kanta tace "Tabbas a duk bayanan da YB yayi babu k'ari ko kad'an a ciki, Da gaske ni nasa ayiwa Ummimah fyad'e, ni nasa aka satomin k'annenta 'yan biyu duk dan in guma mata, Ganin kamar hakan bai dameta ba yasa da nasa aka kashe k'anwarta d'aya daga cikin wanda aka sato, Na samu labarin halin da suke ciki kuma na had'a baki da wanda yakeda gidan hayarsu na maka masa kud'i yaje ya koresu, A dalilin haka babanta ya had'iyi zuciya ya rasu, Naso insa a saki Amrah amma kuma koda na samu labarin cewa wasu Indiyawa zasu taimaki marasa lafiya saina fasa duk dan na b'ata ran Ummimah da mahaifiyarta, Cikin ana shari'ar nan na tura an satomin wata a matsayin Barr. Sultana, kasantuwar basusan fuskarta ba yasa suka sato wadda ba ita ba, Yanzu haka Amrah da mai aikin gidan Barr. Sultana suna wurina amma ba tare suke ba, Amrah tana Malali quaters can bayan gari, Mai aikin kuma tana cikin k'auyukan Barhim. Kai cona ni Salmah, na cuci kaina na cuci rayuwata, nasan yanzu tawa ta k'are saboda dole kotu zata zartar da hukuncinta a kaina" ta fashe da kuka sosai wanda duk wani mai imani dole sai ya tausaya mata dukda yake ita d'in ba abun tausayi bace. Shiru ne ya biyo kotun kasantuwar kowa na al'ajabib hali irin na Gentle, ko a littattafan hausa ko fina finan hausa babu wanda ya tab'a zaton akwai mai hali irin na Gentle, Babu imani ko kad'an a tattare da ita. Wasu 'yan sanda mutum biyu ne suka shigo kotu, bayansu Safiyya ce ta jigatu sosai sai kuma wasu 'yan sandan mutum biyu a bayanta, Rigar bacci ce a jikinta amma jina jina take tsabar azabtuwa da tayi, Tayi ba'ki ta rame tamkar ba ita ba. Kallo kowa ya miyar garesu har suka k'ariso cikin kotun, Kallon mutane take d'aya bayan d'aya har taci karo da Sultana daketa binta da kallon tausyi, Rungumar juna sukayi cikin soyayya, sun jima a haka kafin Sultana ta janyeta daga jikinta tare da samar mata wurin zama daga inda audience suke. "Mai shari'ah waccan daka gani itace mai aikin da nasa aka sacemin, gata nan ta dawo bansan dalili ba, bansan yanda akayi ta gudo ba" Gentle ce tayi wannan maganar cikin rud'ewa sosai tana k'arema 'yan sandan kallo. "Ko zaku mana bayanin abunda yake faruwa?" Alk'ali ya fad'a bayan ya miyar da kallonshi ga 'yan sandan, Kafin su bashi amsa wasu 'yan sandan mutum hud'u suka shigo, hannunsu janye da mutane duka maza mutum shida kowane da ankwa rataye a hannunshi. "Ku k'arisa shigowa dasu" wani d'aya ya fad'a daga cikin wanda suka shigo tare da Safiyya. "Ya mai shari'ah mune 'yan sandan da aka sakamu neman Safiyya tunda aka shugar da case d'in a station, mun jima muna nemanta sai yau Allah ya taimakemu muka sameta a can k'auyukan Barhim, wannan samarin kuwa munyi nasarar cafkesu a bayan gidan da suka b'oyeta" wani d'an sanda ne yayi wannan bayanin cikin natsuwa. Kafin alk'ali ya sake yin magana wani saurayi ya shigo, Kallo d'aya na masa na tunoshi lallai shine saurayin Gentle wato Abdul Kadir AK, Babu neman izini babu komai ya k'ariso daidai gaban Gentle, "Ya mai shari'ah wannan yarinyar da jake gani muguwa ce, batada halin kirki ko kad'an, Ashe duk bayan halayenta dana sani bansan tana yaudarata ba, wai ashe tare take da mahaifina abun kunya har mutane kowa ya sani, da zarar na fita sai a ringa bina da gori ana yimin surutai, Bayan kuma duk wasu kugayen halayena itace ta koyamin, Itace ta sakani na fara yin kisan kai ga abokina kawai dan ya nunarda yana sonta, Tun daga lokacin dana gane tana tare da mahaifina na d'auki alwashin illata rayuwarta saidai duk abunda za'ayi amin, Na tabbatar da akwaa hukuncin kisa akaina daga ni har ita, Dan haka dole sai kinji makamancin rad'ad'in da naji na tarayyarki da mahaifina" da sauri ya lalubi aljihunshi, Wata 'yar kwalba ya zaro ya watsa mata ita a fuska sannan yayi murmushin mugunta ya mik'a hannunshi ga 'yan sanda da nufin su d'aura masa ankwa. Ihu ta fasa da k'arfi na azabar da take ji, Hannunta tasa ta ringa dirzar fuskar wai a tunaninta ko hakan zaisa ta rage jin zafi, Tattalewa fatar fuskar ta hau yi har tsokar dake jikin fuskar ana gani, Kamar mahaukaciya take ihu tana tsalle tsalle tana neman agaji. Mamanta cikin kuka ta taso ta rungumi 'yarta, Banda kuka babu abunda takeyi, Ummimah dake tsaye gefe sosai ta tausayawa Gentle, koba komai tun yanzu ta fara girbar abunda ta shuka. Alk'ali kanshi jikinshi yayi sanyi, lallai al'amarin Allah babu wanda ya usa ya dakatar dashi, lokaci d'aya Allah ya bayyana gaskiya ya kawo k'arshen shari'ar. "Kafin kotu ta zartar da nata hukuncin, Salmah zata kwatanta inda suka ajiye Amrah azo da ita, dole sai anga lafiyarta sannan komai ya wakana, kotu ta bada izini 'yan sanda su tafi suzo da ita sannan aci gaba, za'a tafi hutun awa biyu kafin nan suma sun dawo, za'aci gaba da tsaron Salmah, AK da wanda aka kamo har sanda zamu dawo daga hutu" ya buga gudumarsa sannan ya mik'e ya fice. Da sauri Mama kamar tana jira ta rugo ta rungumi 'yarta Ummimah, Kuakn farin ciki sukeyi sosai tare da hamdala ga Allah, Zarah da Rabiatu ma tasowa sukayi suka dawo gareta suna k'ara tayata murna dukda baca yanke hukunci ba har yanzu. Wani d'an sanda maras mutunci ne ya d'aurawa Gentle ankwa da k'onanniyar fuskarta data gama lalacewa lokaci d'aya kamar ba ita ba. Rik'eta mamanta tayi tam tak'i sakinta ita kuka Gentle kuka, "Ke dillah malama ja can, kina sonta ne kika k'i bata tarbiyyar kirki? Gafaramin can kafin inyi k'asa k'asa dake" yaja hab'ar rigar Gentle da k'arfi tare da fita da ita daga cikin kotun ya kaita d'akin tsaro. Cikin kuka maman Gentle ta koma kusa da mijinta, "Yanzu Alhaji duk kudi'inka kana ji kana gani zaka bari a tafi da 'yarmu cikin ankwa? Shikenan fa idan aka dawo daga hutu hukunci zaca yanke mata" ta sake fashewa da wani kukan. "Karki sakemin maganarta kinji na fad'a miki, taya inaji ina gani yarinya zata kunyatani a gaban jama'a? Kin manta da koni waye? Kin manta da ni d'an siyasa ne sananne? Yanzu fa shikenan bama za'a fitar dani a primary election ba saboda ansan ko an bani ba zanci siyasa ba, nikam na yafe Salmah, na barwa duniya ita babuni babu ita, kinji k'arshen maganata" ya hankad'a babbar rigarsa tare da ficewa, Masu take masa baya ne suka mara masu baya, Maman Gentle kuwa tace babu inda zata je dan jarta tafi a kai mata 'yarta wani wuri. Barr. Sultana kuwa tana wurin Safiyya suna ganawa tana k'ara tausaya mata. *Bayan awa biyu* A daidai wannan lokacin ne kotu ta sake cika kamar yanda aka tsara, 'Yan sandan d'azu ne suka shigo tare da wata budurwa waddaa shekarunta ba zasu wuce sha shida ba, K'ara murza idona nayi sai yanzu na gane ashe takwarata ce Amrah, Ta rame sosai ta k'ara tsayi kad'an, Duk farinta yanzu babushi, ta koma bakca wulik ga kayan jikinta kamar an tonota daga rami, Gashin kanta kuwa tamkar mahaukaciya haka yake duk ya cukurkud'e. Cikin farin ciki Ummimah ta cafke 'yar uwarta tana k'are mata kallo, Bata tab'a tunanin zata sake ganin Amrah ba, sai gashi yau Allah ya had'asu, Lallai Allah abin godiya, shi yake fitar da gaskiya daga k'arya, sannan yake tabbatar da ita ga mai ita. Tabbatarwar da alk'ali yayi cewa ita ce Amrah yasa ya gyara alk'alaminshi ya d'anyi rubutu kad'an sannan ya fara bayani... _ku biyoni gobe insha Allahu zaku samu k'arshen labarin *wata shari'ah,* nagode sosai ga masoyana masu kirana a waya da masu bina ta private chart suna min fatan alkhairi. ILYSM._ °•°AKA°•°Princess Amrah๐Ÿ˜˜ NWA [9:57am, 13/02/2017] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: *WATA SHARI'AH* ๐Ÿ˜ช ๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“๐ŸŽ“ ๐Ÿ˜ช Na Amrah A Msh๐Ÿ’“ *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* (Jan. 2017) *_In dedication to Aunty Sdy Jegal๐Ÿ˜˜_* {~83~} *K'ARSHE* "A bisa shaidu da hujjoji da suka gabata, kowa yaji yanda mai laifi ta amsa laifinta da bakinta, sannan kuma..." shiru alk'ali yayi kasantuwar tari da yaci k'arfin YB, Sosai yake tarin harda jini ke fita daga bakinshi, Cike sa tausayi kowa ke kallonshi, Baifi minti goma a wannan halin ba rai yayi halinshi, Da k'arfi iyayenshi suka d'auki salati had'e da kuka, dama sun san haka na zuwa saboda yanayin ciwonshi babu alamar zai tashi ko kad'an. An d'auki kusan awa d'aya da mutuwar YB harma an tafi da gawarshi Jalingo sannan kotu ta sake zama. "Kotu ta tabbatar da cewa Salmah ita ce ta saka akayima Aishatu fyad'e, bayan nan kuma tasa an kashe mata 'yar uwa wadda a dalilin haka babanta ya yanki jiki ya fad'i ya mutu, Indiyawa sunzo zasu duba lafiyar d'umbin al'ummah wanda a cikinsu harda Amrah k'anwar Aishatu, dalilin saceta da Salmah tasa akayi yasa har likitocin suka k'araci zamansu suka koma k'asarsu, Salmah tasa an sakawa gidansu Aishatu wuta har ya k'one k'urmus, tayi hakan ne da nufin Aisha da mamanta su k'one dan bata san basu ciki ba. Dan haka kotu ta yankewa Salmah Abubakar hukuncin d'aurin rai da rai a gidan yari, Sannan kuma iyayen Salmah wato Alhaji Abu Abu da mahaifiyarta zasu bada tarar naira miliyan goma, wanda a cikin miliyan goma d'in za'a ware kud'in da za'a fitar da Amrah zuwa k'asar Indiya, za'a fidda wanda Aishatu zata koma makaranta saboda Salmah ita tayi silar da aka koreta, sannan kuma za'a fitar dana gidansu da Salmah tasa aka k'ona. Abdul k'adir kuma an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda shi da kanshi ya furta cewa da hannunshi ya kashe Afrah, sannan kuma a gaban kowa yazo ya watsawa Salmah acid a fuska wanda fuskarta tayi dameji harma abun ya shafi idanuwanta. Sauran matasan nan kuwa wanda suka kasance kisa itace aikinsu kamar yanda kotu ta tabbatar, An yanke masu hukuncin kisa ta hanyar harbi da bindiga su dukansu. Sarki manu kuwa bashida laifi saboda kotu bata sameshi da laifi ko d'aya ba saima taimako da yayi, dan haka kotu ta wankeshi daga laifi. Idan Alhaji Abu Abu bayada kud'in tarar da aka yanka masa, kotu zata d'aureshi na tsawon shekaru uku, ko kuma za'aci gaba da tsaronshi har sai lokacin daya kawo kud'in. A k'arshe kotu na bama Aishatu Abubakar hak'uri akan abubuwa da dama, mahaifinta da 'yar uwarta da suka mutu Allah yaji k'ansu, 'yar uwarta maras lafiya kuma Allah ya bata lafiya yasa ayi aiki cikin nasarah". Kabbara kotun aka d'auka baki d'aya mutanen dake ciki, Kuka Gentle ta sake b'arkewa dashi da taji hukuncin da aka yanke mata, Ta tabbatar da zata fuskanci tsangwama sosai a kurkuku saboda damejin da fuskarta tayi, ta zama abun tsoro kamar *dodon Jatau.* "Zan biya, ko miliyan d'ari ne Allah na amince zan bayar akan a d'aureni" Alhaji Abu Abu ne yayi wannan maganar had'e da share guminsa. Murmushin dattako alk'ali yayi dan dama abunda yake jira kenan, da gangan yayi maganar yasan Alhaji Abu Abu ba zai yarda a d'aureshi ba saboda shi d'an siyasa ne, sannan kuma yanada mak'udan kud'in da ko fin haka aka nema sai ya bayar. Ummimah, Amrah, mama, Zarah da Rabiatu kukan farin ciki kawai suke, Barr. Sultana da Barr. Umar kuwa sai farin ciki baki har kunne, Har inda Barr. Sa'eed yake zaune yana had'a gumi Umar yaje, Bayan ya mik'a masa hannu yace "Kamar yanda kayi fatan Allah ya had'amu a *WATA SHARI'AH* gashi kuwa ya had'amu, Yau gashi d'an k'aramin Barr. Ya kayar da babban Barr." Murmushin k'arfin hali Barr. Sa'eed yayi tare da fad'in "Bana fatan Allah ya sake had'amu a *WATA SHARI'AH.* A yau kam na tabbatar da kai ba k'aramin Barr. Bane kai babba ne, dan zan iya cewa kama fini girma daga kai har matarka, tashi tsaye ma mu gwada tsawo inga ni da kai wa yafi wani girma?." Ya kwashe da dariya tare da mik'awa Umar hannunshi sukayi musabaha. Haka suka rabu Barr. Sa'eed na k'ara girmama Umar da Sultana dan ya tabbatar da su ba k'anana bane. Godiya Ummimah tayima Sarki Manu Akan irin halarcin da yayi mata, "Karki damu dama na jima ina neman ta hanyar da zan taimakeki, sai daga baya na samu labarin ke 'yar katsina ce, shine na dage har na samu inda kike, na kuma samu labarin halayen Barr. Umar da matarshi, shine na samu lambarsu na fara tura masu sak'una akan su taimakeki, na kuma k'i bayyanar masu da kaina dan bana so wani abu ya biyo baya , nasan halin lawyers sosai saisa na b'oye masu kaina, sanin zan iya masu amfani yasa dana had'u dasu na fara mayen k'arya wanda duk a lokacin cikin hankalina nake, na basu complimentry card d'ina sannan muka shiga ciki ni da abokina, hatta had'uwar da mukayi da ku a traffic duk tsari ne, saida na fahimci komai zai faru sannan nabi bayanku da mashin d'ina". Godiya ta sake yi masa sannan tabar wurin cikin mamaki. Gidajen television sai faman d'auke d'auken hotuna da videos suke, Har inda su Ummimah suke saida wani d'an jarida yaje da nufin yayi mata tambayoyi, Har tayi niyyar bashi amsa Dr. Rafiq fuska murtuke ya k'ariso inda suke yace "Kai dillah malam ja can, matar auren kake so ka d'auka ka yad'awa duniya?" Kallon mamaki Ummimah ta bishi dashi, 'Taya akayi ta zama matar aure da har ake hak'ilo kanta?' Ta tambayi kanta. Barin wurin d'an jaridan yayi dan yaga Dr. Rafiq da gaske yake ba wasa ba. "Kike kallona koke ba matar auren bace?" Ya tambayi Ummimah had'e da d'an guntun murmushi. "Taya akayi wadda ko saurayi batada shi ta zama matar aure?", "Wadda ko saurayi batada shi? Dan Allah kice Allah kin tuba, ya budurwa kamarki zatace batada saurayi? Gaskiya wasa kike", "Sam babu wasa a maganata, ka yarda dani wallahi da gaske nake". Murmushi yayi dan dama abunda yake so kenan yaji daga bakinta. "Tun kafin in ganki, sunanki da labarinki kawai naji hankalina ya kwanta dake, ki daure ki cije kiso Rafiqu, wallahi zai rik'eki da amana, na jima ina fatan Allah ya kawo min ranar da Rafiq zai kawo min wadda yake so ya aura sai yau, ina fatan zaki karb'i wannan tayin Ummimah" Umman Rafiq ce ta jefo wannan maganar a daidai isowarta inda suke. Shiru Ummimah tayi na tsawon lokaci batace komai ba, Kallon Umman Rafiq tayi sannan ta miyar da kallonta ga Rafiq d'in, Murmushi ta saki wanda har saida hak'oranta suka bayyana, Haka kawia ta sameta cikin nishad'i wanda rabonta dashi an d'auki tsawon lokaci, tun kafin komai ya faru da ita. Wannan murmushin da tayi shi ya tabbatar da amincewarta, Cikin murna k'anwar Rafiq ta rungumeta tana fad'in "Mungode da kika amince da soyayyar yayanmu, insha Allahu zamu kula dake tamkar 'yar uwarmu ta jini", Batace komai ba saidai fuskarta kawai za'a kalla a tabbatar da tsantsar farin cikin da take ciki. Suna nan tsaye sai ga nurses d'in makarantarsun nan su hud'u sunzo kowace tana kuka hannunta rik'e da takarda, D'aya daga cikinsu tana fad'in "Wai yanzu dan wulak'anci tun anan za'a bamu takardar sallamah? Shegen son kud'inmu ya kaimu ya baromu, yau gashi gwamnati ta d'auki nata hukuncin a kanmu tun kafin ayi nisa". Da wannan surutan har suka bar wurin. Ummimah kuwa cikin motar su Rafiq ta bisu suka rankaya sai gidansu Sultana cike da farin ciki dan dama kowa ya koma su kawai ake jira. *Alhamdulillah! Nima kuma anan sai na d'igawa wannan labarin aya, wata shari'ah labari ne wanda zan iya cewa fiye da rabinshi ya faru da gaske. Saidai kuma wadda abun ya sama har yanzu gaskiya tak'i ta bayyana, rayuwarta ta wulak'anta kamar yanda ta Ummimah ta wulak'anta, an koreta a makaranta an nuna anfi k'arfinta ta hanyar dukiya, 'yan uwa musulmai mu taru mu saka wannan baiwar Allah'r a addu'ah ko Allah zai kawo k'arshen mawuyancin halin da take ciki.* Godiya ga masoyana maza da mata, na nesa dana kusa, masu kirana, masu yimin text messages, masu bina ta pchart suna min fatan alkhairi harma da wanda Allah bai basu daman yimin magana ba nagode sosai da kulawarku. Amrah na k'ara jaddada yanda kuke a zuciyarta. A duk inda kaji an ambaci hanta dole a ambaci jini, *RAZ* daku nake tink'aho, da bazaraku nake taka rawa, ban san ya rayuwata zata kasance idan babuku a cikinta ba, fatana a kullum Allah ya kareku daga sharrin mahassada da mak'iya, Allah ya k'ara maku baseerah da d'aukaka. Amrah na masifar sonku. (@Rerbee'art sk and Zarah bb). *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* k'ungiya mai albarka da had'in kai, Allah ya taimakeku ya kareku daga sharrin masu sharri. Wannan littafin sadaukarwa ne Ga Sadiya Labaran Jega (Aunty Sdy Jegal) nagode sosai da kulawarki a gareni. Tukuici ne ga k'awata Aisha Abubakar Gege (Ummimah) sunanki ne a cikin labarin. ILYSVM. Ina fatan wa'azin dake cikin littafin nan zai amfanar da d'umbin al'ummah, mu daure mu turawa wanda basu karanta ba domin su karanta su k'aru da babban darasin dake cikin *wata shari'ah.* *_FASAHAR AMRAH_* "Kiyi hak'uri *KHAULAT,* Nasan irin *YAUDARA* da *DR. RAFIQ* yayi miki, kiyi hak'uri kiyi amfani da karin maganar da hausawa sukace *MAHAK'URCHI* mawadaci. Ina so kiyi koyi da rayuwar *UMMU HAYDAR,* Duk da irin *SO DA SHAK'UWA* dake tsakaninta da mijinta saida ta zama *MAI BAK'IN JINI* a wurinsa. Ya nuna mata *TSANTSAR ZALUNCHI* amma daga baya ta samu *D'AUKAKA DAGA ALLAH* tama Usman *RAMUWAR GAYYA,* ta nuna masa cewa *BABU MARAYA* sai rago. Nasan ba zaki rasa karanta labarin *YARIMA SAIFULLAH* ba kinga irin wahalar da yasha a rayuwarsa. Amrah ma tayi fama da *ZAFIN SO* na wadda batama san tanayi ba, a koda yaushe ta zauna maganarta d'aya ce *'INA ZANGA KDEEY?'* saida ta zama kamar wadda *JINNUL-ASHIQ* ya aura, amma daga baya da tayi hak'uri saida burinta ya cika na ganin Kdeey. Ina so ki nemi labarin *WATA SHARI'AH* ki karanta, nasan zaki k'aru da abubuwa da dama a cikinsa. Idan kin gama kuma sai ki rakani mu d'auko labarin *DAFIN SO,* Inda zakiga yanda soyayya ta miyar dashi kamar zautacce ko kuma ince kamar mahaukaci. Littattafan Amrah kenan, labarin *DAFIN SO* na nan zuwa maku insha Allah. DOle in ambaceku kafin in rufe wannan littafin: Asma'u Umar, Ummi Saddam and Ashnur Pyar, kunfi kowa son wannan labarin. www.princessamrahh.blogspot.com @instagram: miss_amrahmashi. 07037603276 for any correction or comment. Amrah A msh, Also known as Princess Amrah kema kowa fatan alkhairi, Allah ya had'a fuskokinmu a aljannah amin. adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *