🌳🌳🌳🌳🌳
🎃YAR ♡ TALAKAWA🎃
🌳🌳🌳🌳🌳
Episode 1⃣
By ~ afrah
Bismillahil rahmanil rahim
"Tafe nake a cikin wata kasuwar fruits(kayan marmari),nazo wuce wata rumfa,mai dauke da kayan marmari kala kala, wata kyakkyawar yarinya na hango a ciki, sanye take da wasu kodaddun atamfa riga da skirt,yarinyar ba zata wuce shekaru sha shidda ba, sai tsalle take tana fadin, kuzo ku siya, namu sunfi zaki, tana maganar fuskar ta dauke da murmushi,kumatun ta sun lotsa, mutane dayawa suka tsaya a wurin suna kallon ta,kwanin sha'awa, gata kyakkyawa, ta dauko lemu,ta dauko alaba da sauran fruits din, tana fadi musu anfanin su,dan kawai su siya.
Ni afrah nace bari na bi wannan yarinya mai siyar da kayan marmari, dan kwaso wa masoyana labari.
Wani mutuni na gani ya kira ta ciki, yarinyar na murmushin mai kara mata kyau, tace ya habu har zamu tashi ne, naga akwai sauran jama'a a kasuwar, mu dan kara jira kaji, ya habu ya kalle ta yace NI'IMATU, ke bakya gajiya ne , tun safe kike tsalle tsallen nan, niimatu ta dara, ta kai wa ya habu naushi a hannu, ni ban gaji ba Allah, mudan kara jimawa kaji, ya habu yayi dariya, ke kam da namiji ce , da anyi jarumi.
Niimatu ta daure fuska, ohh ni yanzu ba jaruma bace ashe ko? Ta turo masa dan karamin bakin ta, ya habu yadan dungurar mata da kai, yace a tsalle tsallen kike jaruma, ya wuce waje abunsa, niimatu taja tsaki, sannan ta murmusa itama ta bishi wajen.
Umma !umma! Ina kike gamu mu dawo, umma ta fito cike da fara'a, niimatu tayi saurin ajiye ledar hannunta,tayi wurin umman ta rungume ta, umma tayi murmushi, niimatu bakya girma ko?, niimatu tayi murmushin ta, tana kallon umman tace, umma idan dai a gaban kine ni har yanzu yarinya ce karama, koda na haifi yara dari ne, umma tayi dariya , ya habu ya karaso ciki, yace umma sannu da gida?, umma tace ko keda sannu habu. YAR TALAKAWA COMPLETE