Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, 1 March 2019

DUK KYAN TAKALMIII COMPLETE HAUSA NOVEL

adsense here
DUK KYAN TAKALMIII COMPLETE HAUSA NOVEL
Sunana Aisha farida umar, 'yar asalin jihar
katsina amma zama ya kai kakannina garin
shagamu. Anan aka haifi mahaifi har yayi
aure aurensa ya hayayyafa don haka babu
garin da muka fi sani wanda ya wuce
shagamu. Mahaifiyata ma 'yar garin
shagamu ce. Yanzu shekaruna ashirin da
uku a duniya, na fito daga dangi wadanda
suke talakawa liki. Ilahirin dangina kakaf na
wajen uwa dana wajen uba basu da hali.
Koda yake akwai daidaiku masu rufin asiri
amma ba za a kira su masu arziki ba amma
dai sunfi wasu. Wannan dalili yasa bamu
cika karatu mai zurfi ba wasu daga primary
suke tsayawa, wasu sun shiga scondary
amma talauci sai yasa a cire su basa
karasawa. Masu dan gara gara ne ma suke
kammala secondary amma fa jami'a ta
gagaresu sai dai kallo. Danginmu suna da
dimbin yawa mata da maza, yara da manya
gamu da tsofaffi tukuf tukuf Allah Ya ara
musu tsawon rai. Mahaifina yana daya daga
cikin dattijan domin ya tsufa jagof, tun tashi
na daman a tsohonsa na ganshi har ya
makance saboda tsufa. Shine babba a cikin
'yan gidansu don haka yafi kannensa tsufa
kuma yafi sauran 'yan uwansa talauci
kasancewar yafi su tara mata har guda hudu
da tulin 'ya'ya har guda arba'in da uku.
Nice 'ya ta arba'in da biyu a wajensa,
kanwata guda daya kacal mai suna
munauwara. Mu biyu ne kadai muke uwa
daya uba daya a gidan domin mahifiyarmu
ce amaryarsa, ya aure ta tana kankanuwa
yayin da yake tsohonsa. Sauran matansa
ma duka sun tsufa wasu daga cikin manyan
'ya'yansa sun girme ta suma har sun aurar
da 'ya'yansu suna da jikoki wadanda suka
fini ma. Don haka ban mori dadin uba ba,
sanda na fara wayo baya ganina kasancewar
ya makance.
Aikina shine kullum inzo dakinsa in riko
hannunsa in fito dashi kofar gida sai in
zaunar dashi akan kujerar katakonsa sannan
ni kuma in zauna a gefensa ina sauraron
hirar da sukeyi shida abokansa,
makwabtansa da 'yanuwansa tsofaffi. Ina
jin dadin sauraron tsofaffi labarai masu
al'ajabi na mutanen da. Ina fahimta sosai
kuma ina rikewa a kwakwalwata tas, babu
abinda nake mantawa harma idan suka fadi
wata kalma da ban sani ba sai in tambayesu
su bani amsa. Idan babana ya aike ni dauko
ruwa, fura ,koko ko kuma kurtun tofin
yawunsa a dakinsa sai inji duk raina ya baci
saboda za'a tsallake wani shashi daga cikin
hirar. Sai in zura da gudu don inyi sauri in
dawo kada a wuceni, idan na dawo kuwa na
sa su dole su dawo da labarin baya. Anan
na koyi iya magana mai ma'ana da jan
hankalin mai saurarona da kuma fitar da
lafazai masu girma da hikima tamkar wata
babba. Daga nan na samo suna "Farida
tsiri" inji kawayena haka suke kira na domin
duk wanda na zauna dashi zaiyi tunanin
wayona yayi yawa zan cuce sho ko zanyi
masa dubara ko in yaudare shi. Duk sanda
zanji labarin anyi gulmata bai wuce ace na
cika iyayi ba da dadin zance rai-rai-rai
kamar aku. Ko kuma ace na cika kissa da
kisisina bana fushi ko ma za'ayi min, ga tsiri
ina magana kamar wata tsohuwa wacce
taga jiya taga yau. Ina jin dadin halayena
kuma dashi nake cin ribar zaman duniya.
Zan iya zama da kowanne irin mutum ne
komai bakin halinsa da muguwar zuciyarsa,
duk sharrinsa ko alkhairinsa haka kuma duk
in da ya kai ga masifa da zafin rai zamu
zauna lafiya. Da kowacce irin kabira zan iya
zama lafiya. Da bakar fata da inyamuri,
hausa, babarbare, bafillatani, bayarabe,
ibira ne, tangale ne, mumuye ne, margi ne,
basayi ne, ba'are ne, dan niger ne ko kuwa
adon dawo ne dan bur sudan duk na san
yadda zan tafiyar dasu.
Mahaifina yana da yawan magana ba zai iya
zama shi kadai ba, ba tare da bakinsa yana
motsi ba, sai na gado sho don haka tamu
tazo daya sai mu hadu muyi tayi. Har baya
so in matsa daga gabansa don haka ban
cika zuwa makaranta ba, ko yayyena zasu
korani sai in ruga da gudu dakinsa in labe a
bayansa. Sai yace musu "inga mara kunyar
da zai shigo ya banbare aisha daga bayan,
baza taje makarantar ba nan dakin ma
makaranta ce". Aji ne mai zaman kansa don
darasi take duka na iya rayuwar zaman
duniya. Ku fada min ko a jami'a wanne
darasi ne za'a zaunar da dalibi a karanto
masa rayuwa karara balle dan primary aji
daya? To ku kyale ta ba in da zata je sai ta
ga dama sannan zata je makarantar. Dalilin
zuwanta makaranta don ta koyi rubutu ne
kawai. Idan sukaji yana fada basa karasowa
cikin dakin, su gama labe-labensu ina hango
inuwarsu ta jikin asabari sai inki fita, sai sun
gaji da jirana sannan su tafi. Idan hantsi
yayi sai inje zaure in kinkimo kujerar katako
in kai masa kofar gida, sannan in share
wajen in shimfida tabarmi a kasa wasu
tabarmin in shimfida akan wasu dakali biyu
da suke kofar gida. Sannan in dawo dakinsa
in mika masa sandarsa na riko hannunsa in
fito dashi kofar gida wajen kujerarsa, sai ya
laluba ya zauna sannan in koma gefensa in
zauna sai ya fara bani labari ko tatsuniyoyi.
Sannu a hankali sai 'yan majalisarsa su fara
bulbulowa daga gabas wasu daga yamma
wasu daga barin kudu, wasu daga arewa.
Yawancinsu kannensa ne uwa daya uba
daya, ko uba daya. Wasu kuma kakanni
suka hada, wasu makwabtaka ce ta hada ko
auratayya, wasu kuwa manyan abokansa ne
da akayi kuruciya tare. Babu wanda yake da
kasa da shekaru sittin a wajen. Anan na
samu tarbiyar girmama babba duk
kankantarsa, domin idan na gaishe su daga
tsaye ko daga zaune ba zaus amsa ba ko
kuma inji duka dal a bayana wai nayi rashin
da'a. Sai kaji sun daka mintsawa suce inzo
in durkusa har kasa sannan in gaishe su.
Tun ina jin haushin inyi kuka har na daina,
tun ina mantawa har na saba. Sannan na
koyi durkusawa har kasa idan zan mikawa
babba abu koda kuwa da kadan ya girme ni
kuma da hannu biyu. Sun hana ni mikawa
sa'ana ko yaron dana girma abu a
wulakance ko da hannun hagu. Sun
gargadeni ni da na guji wulakanta dan adam
ko da kuwa almajiri ne domin babu kyau
wulakanci da girman kai.
Anan nakoyi daubarun cin jarabawa a
makarantar boko ko kuma saurin haddace
kur'ani a makarantar allao. Sunce in zamana
mai yawan kallon bakin malamina ina
sauraro, ina ganin yadda yake fitar da
lafazinsa daga hanka, ganda, tantanin
makwallato da kuma dumbarun bakinsa. Yin
haka zai sa in dinga fitar da kalma yadda
ake bukata a fada. Kada in dinga zama a
bayan aji, ko da yaushe kujerata ta zamana
a gaban malam saboda gudun yin wasa da
yara. In zama mai yawan tambayar duk
abin da ban gane ba anan take ba sai an
wuce wajen ba. Sannan in dinga kwafar
rubutu daidai in da ban gane ba ko ban
gani ba in tambayi malam ko wani na kusa
dani wanda nasan yasan abin da yake yi.
Kada in sake in koma gida in yarda jakata
ko allona ba tare da nayi bita ba. Sunce da
zarar naci abinci na huta in samu lungu in
shiga inyi ta tilawa zanji na fahimci abin da
ban gane ba a a aji watakila saboda yunwa
ko gajiya ta hana in gane a lokacin. Suka
shawarce in yawaita yin aikin gidan
(homework) tare da yayyena wadanda suke
ajin gaba dani, kada in sake in dinga yi ni
kadai ba tare da wani ya duba min ba. Duk
abinn nan dana fada min na haddace sai dai
anan nake zubarwa saboda bana kaunar
zuwa makaranta, har gara ma makarantar
allo dan itama a kofar gidanmu take dole
inje.
Idan rana ta bude sai majalisa ta yoye, ni
kuma sai kama hannun tsohona in shiga
dashi daki sannan inje in karbo masa
abincin rana daga wajen matar da take da
girki. Tuwo ne dai na masara ko na dawa,
miyar kuka ce ko danyen karkashi. Shinkafa
sai jifa jifa ake siyowa a dafa ko kuma idan
an samu wani dan albarka cikin yayyena ko
sirkiai su kawo mana a dafe ko danye. Da
yamma sai in sake zuwa inyi shimfida in fito
dashi, 'yan majalisarmu basa tashi basa
manta lokacin sai kagansu daya bayan daya
suna bulbulowa. Duk wannan zance da
nake yi muku ina da shekara hudu ne zuwa
tara, ban cika shekara goma ba a duniya
Allah Ya karbi ran mahaifina. Mahaifina ya
rasu a ranar wata juma'a da safe. Bazan
taba manta wannan ranar ba saboda itace
ranar dana taba makara ban tashi da karfe
bakwai na safe banje wajensa ba, domin
kullum karfe bakwai a dakinsa take min.
Wannan kuwa ya faru ne a sanadiyar wata
kasala da wani yanayi da jikina yake min ba
dadi. Ni ba mai barci ba, haka ni ba ido
biyu ba. Tamkar wani abu mai nauyi aka
saka aka dirirritseni na kasa juyi. Sai dai
kuma idona a rufe ba kamar mai tunani
kamar mai mafarki domin abinda nake
nanatwa hirar da mukayi da mahaifina ce a
daren jiya kafin inzo in kwanta. Daga ni sai
shi bayan 'yan majalissa sun watse muna
labari kamar yadda muka saba. Ya laluba ya
dafa kaina yace aisha ki zama mai rikon
amana a rayuwarki yin haka zai ja miki farin
jini a wajen al'umma. Ki kiyayi munafunci,
ma'ana gulma shine yi da mutum yin haka
zai zubar miki da kima. Ki guji sata duk
rintsi kada ki taba abin wani yin haka zai
zubar miki da mutunci ke da zuri'arki gaba
daya za'a dinga yi muku gori. Ki guji yin
zina, laifi ne a wajen Allah kuma rashin
mutunci zai dasu a idon jama'a zaki zama
abar zagi, kowa ya fada miki magana, sai ki
zama ballagaza ko yaro karami ba zai
girmamaki ba. Ki kiyayi kwadayin abin wani,
ki nema naki na kanki duk kankantarsa ki
hakura kiyi amfani dashi shine zaman
lafiyarki da farin cikin rayuwarki. Kada ki
raina baiwar da Allah ya baki, kada ki dinga
ganini wadanda suka fiki. Kada zuciyarki ta
mutu kice ba zaki shiga ku fafata ba, ki
zama mai karfin zuciya da kudiri na alkhairi
kada zuciyarki ta dinga karaya. Sannan ki
zama mai godiya ga Allah a duk halin da
kika tsinci kanki na dadi ko wuya. Ki zama
mai yawan kyauta ko abinda kika mallaka
kalilan ne kada ki makale hannu kice baki
dashi, sai ranar da kika samu da yawa zaki
dinga bayarwa. Ki nemi ilimi mai yawa, na
muhammadiyya dana zamani komai wuya
domin kada a barki a baya a rayuwar duniya
da lahira. Allah Yace mu nemi ilimi a duk
inda yake domin sai munsan shi zamu
bauta masa. Allah baya karbar ibadar jahili,
har baccin mai ilimai yafi jahilin da zai
kwana yana sallah.
Sai naji mahaifiyata tana girgiza ni tana ta
ambaton sunana, idan na bude ido na dube
ta sai in koma in kwanta har sai da ta daga
ni zaune. Tace dani wanne irin bacci ne
haka har tara da rabi tayi baki je kin kaiwa
babnki koko ba, bayan kinsan baya jin dadin
jikinsa? Cikin magagin bacci nace mata yau
baba ya fita kofar gida da kansa, yayi shara
yayi shimfida da kansa. Sai ta harareni tace
karyar banza, a mafarki ko a ido biyu?
Yaushe kika ganshi ke da na tashe ki
dakyar? Sai na tuna ashe mafarki ne don
haka na mike a firgice ko sallah banyi ba na
fita kofar gida na hau shara, na fitar da
kujerarsa da tabarmi kamar kullum. Sannan
nazo na dauki koko a kwanon sha da
kudaya na duma na nufi dakin tsohona.
Wata irin al'ada ce matan gidanmu sukeyi
wai mata mai girki bata shiga dakin miji
saboda kada ayi gulmarta ace ta cika jaraba,
tsohon Allah sai anje an nanike maka,
makahon da yake ta kansa yau da lafiya
gobe babu. Kina shiga dakinsa za'a fara
lekowa ta lungu lungu ana kus kus, kina
fitowa kuwa zaki hadu da harara , zumde,
yafice da habaice habaice. Tsakanin shi
dasu gaisuwa daga bakin kofa ya fadi abinda
zai fada ki juya idan kin zuba masa abincin
ki aiki 'ya'yanki ko jikokinki su mika masa.
Daga baya ma da aka ga nice karama mai
shiga wajensa kullum sai aka dora min
alhakin kai masa abinci kullum, duk wacce
ta gama sai ta kwalla min kira inzo in kai
masa abinci.
Na shiga dakinsa sai na iske shi a lullube
kamar mai bacci, sai na zata lambo yayi ko
fushi yake yi dani dan banzo da wuri ba. Nayi
ta sallama shiru, sai nazo dai dai kunnensa na
durkusa na gaishe shi bai amsa ba, sai na
shiga yi masa bayanin abinda ya tsayar dani,
shimfida nayi har su malam shehu sun fara
zuwa. Sai naji yayi shiru bai motsa ba, sai
kawai na bude lullubin sai ga idanuwansa a
kakkafe yana kallon sama kamar mai
murmushi. Nace lallai baba kana jina ashe kayi
kasake kana kallon sama kana murmushi. Sai
bai bani amsa ba! Ni kuma sai naji raina ya
baci, sai nayi fushi na tashi na fita bakin kofar
dakin na zauna ina kumbure kumbure. Matan
gidan suka fara yimin tsiya suna cewa ke kuma
me akayi miki? Ke da baban naki ne kuma yau
ake jin kanku "yar lelensa wacce baya bari a
taba ki. Sai nace dasu yana ji ina tayi masa
magana yaki kulani, idonsa biyu yaki yi min
magana idanuwansa suna kalllon sama kamar
yana murmushi. Sai jikinsu ya fara basu tabbas
akwai wata matsala domin suma sun leka suna
gaishe shi bai amsa ba duk da dai anji motsin
alwalarsa da asuba amma baya baccin safe.
Sai matansa suka kutsa cikin dakin da sauri
kuma a gigice. Kururuwa da lafazansu ne ya
gigita ni, har yau ban kara jin mummunar
kalma a kunnena irin ta ranar ba. Suka ce
wayyo malam babu, malam ya mutu, munga ta
kanmu, ihu mun shiga uku, rumfa ta gaji da
shirgin kaya ta rushe. Ire iren kalaman da suke
fada kenan suna rusa kuka kururuwa. Sai naji
zuciyata ta hau dukan uku, na dafe kirjina na
fada a bayyane nace Innalillahi wainnailaihi
rajiun. Allah Ya jikanka baba, Allah ya sa
aljannah ce makomar ka. Allah da Ya karbi
abunSa dan yafi mu sonsa, daga gareka muka
zo kuma gare Shi zamu koma. Da ka tafi ba
kayi gaggawa ba haka mu da muka rage ba
muyi nawa ba. Sai manyan maza da mata suka
jeru a kaina suna kallona babu wanda ya kara
magana balle ihu. Mamaki marar iyaka zaka
dinga hangowa daga cikin idanuwansu. Ina
salati ina hawaye cikin natsuwa ba tare da
kwarmato ba. Sai yaya hussaini ya fashe da
kuka yace farida lallai baba ya shigar dake
makaranta, ya saka ki a aji ya koyar dake
darussan dako a jami'a ba za koya miki ba.
Baba yayi gaskiya da yake hana ki tafiya daga
wajensa har sai da kika koya ilimi wanda zai
isheki zaman duniya da lahira. Ya juya ya duba
iyayensa da 'yan uwansa yace wannan abinda
farida ta fada ya zama darasi a wajenku,
wa'azi ne, nasiha ce zuwa gare mu. Ihu da
kwarmato da dora hannu aka kuna fadin mun
shiga uku, ina zamu saka kanmu? Gatanmu ya
fadi. Dawa zamu zauna a duniya? Rumfa ta
gaji da shigi ta rushe. Dukka sabo ne, bata ne,
jahilci ne, azaba kuke karawa mamaci. Tabbas
idan ka saba da abu ranar da zaka rabu dashi
akwai ciwo, kuka wajibi idan akayi mutuwa
amma ba'a son ihu da kururuwa. Kamata yayi
ayai ta karanta innalillahi wainna ilaihi rajiun
sannan ayiwa mamaci fatan samun aljannan.
Ku dubi karamar yarinya nan farida itace kusan
wacce tafi kowa kankanta a cikin gidan nan
amma ita kadai ce tayi abinda ya dace , itace
wacce tafi mu shakuwa dashi, tafi mu sonsa,
kuma itace tafi mu nuna masa kaunar da take
yi masa shine data yi masa addua. Muyi koyi
da ita don tafi mu ilimi, tafi mu sanin ya
kamata. Sai suka daina ihu suka koma suna
ambaton sunan Allah. Yaya hussaini ya tashe
ni tsaye yasa gefen rigarsa ya goge min
hawaye. Yace ki daina kuka 'yar karamar
kanwata, kowa yasan ke aka yiwa mutuwar
nan sai kuma kika fi kowa yin tawakkali haka
Allah yake so. Ina mai yi miki albishir Allah ba
zai bari ki wahala ba, da izininsa ba zakiyi
kaskantaccen maraici a rayuwarki ba, duk da
kin rasa mahaifinki a lokacin da kike da
karancin shekaru saboda baki mance da
Ubangijinki ba wanda shine gatan ki. Allah
Yana tare da duk wanda yasan da Shi kuma
wanda yake neman taimakonsa. Farida nayi
miki alkawari zan dauki nauyinki, zan rike ki
amana har izuwa ranar da zan aurar dake
saboda wannan tawakkalin da kika nuna, zan
rike ki tamkar 'yar dana haifa ta cikin. Wacce
hakkin cinta, shanta, suturarta, tarbiyyarta,
iliminta da suka wajaba a kaina har zuwa ranar
da zan aurar da ita sannan nauyinta ta koma
hannun mijinta. Ki shiga ciki wajen baba kiyi
masa sallama, kiyi masa irin adduar da kika yi
masa yanzu ta neman gafara da rahamar
Ubangiji. Mutuwa ce kadai ta raba kaunar dake
tsakaninku. Na juya da sauri na shiga wajen
tsohona, durkusa a gabansa setin kunnensa na
tofa masa kulhuwallahu ahad uku, sannan nayi
masa adduar samun aljanna da neman hasken
kabari. Nayi masa fatan Allah ya sa ya tashi a
cikin gafartattun bayi a cikin alummar manzon
Allah (SAW). Sannan mahifiyata ta jawo
hannuna muka fito waje, cikin kuka mai tsanani
tace dani farida na yafe miki duk abin da kika
yi min. Allah yayi miki albarka a rayuwarki ta
duniya da lahira. Alhamdulillahi nayi dace da
'ya ta gari, mai jin kan iyayenta. Ina fatan nima
zakiyi min irin wannan adduar idan na riga ki
tafiya. Muna zazzaune a tsakar gida maza
suka shiga sukayi masa wanka, suka hada shi
suka fita da shi akayi masa sallah. Aka dauke
shi aka tafi dashi gidansa na karshe, gidan da
ba'a fitowa unguwa, gidan da ba'a leke, gidan
da ba'a jiyo motsinka balle a gaishe ka ka
amsa wato kabarinsa. Bakina bai gushe da
karanta masa kulhuwallahu ba da inna
a'adaina kalkausar har karshe. Shi ya bani
adduar yace ita ake so a dinga karantawa
mamaci. Da akayi sadakar bakwai sannan aka
watse, lokacin mutuwa ta dawo min sabuwa fil,
idan aka tashe mu daga bacci za'a tura mu tafi
makarnatar boko sai in nufi dakinsa zan buya
sai in ga a rufe sannan in tuna ashe ya rasu,
dole a tura keyata zuwa makaranta raina baya
so, da yamma ma sai a tura ni makarantar
allo. Ina tuna nasihohin da tsohona da
abokansa sukayi min na dabarun samun
nasarar karatu, sai nake bin duk yadda suka
umurce ni sai naga ina ganewa kuma ina cin
jarabawa don haka saina fara jin dadin
makarantun da nake zuwa, na dawo ina zuwa
makaranta da kaina ba sai an tura ni dole ba.
Ranar asabar da lahadi muna zuwa makarantar
allo da safe da yamma amma ranar alhamis da
juma"a da yamma ba ma zuwa koina don babu
makarantar allo, sai na fitar da kujeran babana
in shimfida tabarmi kamar yadda na saba. Sai
inga tsofaffin nan suna zuwa daya bayan daya
suna zuwa suka taru kamar yadda suka saba
da, don har sun daina taruwa tun bayan da ya
mutu. Baba ahmadu ne ya maye kujerar
babana shine babba ina gefensa koda yaushe,
duk sanda suka kalle ni sai inga suna hawaye
suna tausayina da alama suna tunawa da
yayansu, abokinsu, amininsu, makwabcinsu,
abin kaunarsu. Zaman majalisar yakoma ranar
alhamis da juma'a ne kawai da yamma. Kuma
munci gaba da hirarrakin mu kamar yadda
muka saba. Bayan rasuwar mahaifinmu da
shekara guda yaya hussaini yayi aure, ya auri
'yar kanin babanmu mai suna abida dai dai
lokacin daya sami dan karamin aiki a union
bank, da certificate dinsa na secondary a
matsayin masinja a branch na kano dan haka
kano ya kauro damu. Da zamu tafi mahifiyata
ta hada min kayana kakaf tana kuka ina kuka,
kanwata munauwara ma tana kuka, 'yan gidan
kacokan suka fito suna mana fatan Allah Ya
kiyaye hanya da fatan Allah Ya bamu zaman
lafiya, Ya hada mu da abokan arziki a can.
Muka tare masu babura biyu muka hau da
jakunkunan kayanmu muka nufi tasha, muka
hau doguwar mota mai zuwa kano. Kano ta
dabo tumbin giwa, mai mata da motoci ko da
me kazo an fika. Rabona da shagamu kenan
har yau ban sake komawa da sunan zama ba
sai dai inje da sunan ziyara. A wata unguwa a
cikin kano mai suna sharifai zauran tudu, yaya
hussaini daman ya kama mana haya tun kafin
muzo, a gida mai dakuna bakwai muka kama
dakuna biyu. Don haka mutane ne da yawa a
cikin gidan, bandakin daya ne kacal, kicin daya
da tsakar gida daya ake amfani dasu mata da
maza, yara da manya. Abunka da gidan yawa,
kazanta ba'a magana. Gashi daman gidan ya
tsufa ya farfashe ba gyara sai warin bola da
kwata kowa kyashi ya hana shi gyarawa. Idan
ka share cikin dakinka da kofar dakinka ka
gama shara babu wanda zai share tsakar gidan
da zaure balle kofar gidan. Ga gida a lungu ko
mota bata shiga lokon, ga wata tafkekikyar
kwalbati da ta cinye fadin lungun, kowa a
tattakure babu sakewa, yara basa iya wasan
guje guje su more sboda matsi. Haka kowacce
mace ta baza kayan san'arta a cikin gida, cikin
zaure ko kofar gida saboda sai an taimakawa
mazan rayuwar zata tafi dai dai. Daman mazan
da yawansu buga buga sukeyi, wani sai ya
dawo gida babu abinda ya samo, da dan kudin
sana'ar natar za'a yi cefane kuma ta bawa
yaranta kudin makaranta. A gidan ma har gara
yaya hussaini tunda yana daukar albashi duk
tsiya dai karshen wata zai samu duk da dai dan
albashin bashi da yawa kuma rabin kudin a
acaba yake tafiya, kafin wata ya kare sai anci
bashi dole kafin a biya an jigata. Duk da haka
dai munfi sauran, muna dan cancanawa dai
muna rayuwa. Ni da abida muka fara sana'a,
muna soya wainar fulawa a kofar dakinmu,
kuma ana saya ba laifi duk da cinikin naira
biyar biyar ne, duk da haka muna samun na
sayan maggi, gishiri, a ciki ake bani kudin
makaranta da kudin dinkin tsummokaran mu
idan sun yayyage. A makarantar bokon cikin
unguwa aka saka ni, kamar sauran yaran
unguwar haka aka saka ni a makarantar allo da
yamma ta islamiya da daddare. Bana fashin
zuwa makarantar kullum saboda ina tsoron
yaya hussaini sosai, baya yi min wasa koda
yake matarsa ma baya sakar mata fuska ,
mutum ne mai zafin zuciya. Lallaba shi muke
kamar kwai. A daki daya nake zaune babu
komai a ciki daga 'yar karamar katifa sai 'yar
jakar kayana ta buhu a gefe ko ledar daki ba'a
shimfida ba sai tsurar ragargajejjen siminti da
wani yagulallan labule. Dakin su abida da
mijinta ne mai labule mai kauri, an shimfida
leda a kasan da katuwar katifa sai akwatin
kayansu a gefe. Kayan kitchen da danyan
abinci suna dakina wasu a dakinsu. Haka muke
rayuwa amma muna farin ciki saboda mun
sami ci gaba fiye da a garinmu tunda daman
can a cikin talauci aka haife mu. Bayan
kaurowar mu da shekara daya mahaifiyata ta
tara kudin motarta da guzurinta tazo ganina
sabida tun kaurowarmu bamu je shagamu ba,
saboda matsalar tattalin arziki sai ita tazo dan
taga yadda muke rayuwa don koda yaushe
magana ta takeyi don tana sona sosai har fiye
da 'yar autarta. Nayi murna matuka da ganinta
har ita ta fini murna, yaya hussaini da matarsa
ma sunyi murna da ganinta kuma sunji dadin
tsarabar da ta kawo mana. Ni da abida atamfa
dai dai ta kawo mana, yaya hussaini ta kawo
masa yadi, sannan ta kawo mana doya,
dankali, ayaba da lemo jifgi guda. Allah cikin
ikonsa cikin daren data zo muna kwance da ita
a dakina ciwon ciki ya turnuke ta kafin in
bugawa yaya kofa ya fito don a kai ta asibiti
rai yayi halinsa. Ummata ta mutu a gabana ina
kallonta ban isa in hana ta tafiya ba, Ubangiji
ya nemi kayanSa. Sai na tuna wasiyyat da ta
bar min cewar idan ta riga ni mutuwa inyi mata
addua kamar yadda na yiwa mahaifina. Nayi
mata addua sosai kuma ban manta ambaton
innalillahi wa'innalialhir rajiun ba har gari ya
waye. Sai dai nayi kuka mai yawa saboda na
kara wayo na san zafin mutuwar sosai ba
kamar da ba, na tausayawa kaina sai nafi
tausayin kanwata munauwara. Gata karama ita
kadai ta rage babu uwa, babu uba, babu ni 'yar
uwarta. Nasan a gidanmu 'yan ubanci akeyi
kowa yana tattalin 'yan dakinsu, nasan sai dai
dangin mahaifiyta ne zasu dauke ta suma
kuma duka kanwar ja ce, talauci ne tsagoronsa.
Rashin kudin motar da za'a kai gawarta
shagamu shi ya hana yaya ya kai ta can a
binne sai kawai ya buga waya ya sanar dasu
wannan mummunan labari. Sun kuwa gigice da
jin haka sai suka yanke shawara gara wasu su
taho kanon ayi jana'iza a binne ta anan. Allah
Ya rubuto anan kasarta take. Da suka iso sai
akayi mata sallah aka binne ta. Kafin kwana
bakwai wasu daga cikin danginmu sai da suka
zo kano sukayi gaisuwa sannan suka koma,
wasu da yawa basu sami damar zuwa ba, da
yake a can ma ana zaman makokin don ba
kowa yake da kudin zuwa ba. Da akayi albashi
ni da yaya hussaini da matarsa mukaje
shagamu don yin gaisuwa da kuma zancen
abinda ta bari. Baiwar Allah bata da komai
daman mijinta bai bar mata komai ba, dan
matan basu samu gida ba! Basu samu gona
ba. Ko mu 'ya'yan kudi kadan aka bamu da
akayiwa gidan da gona kudi wani yayanmu ne
ya saya dan ba zai rabu ba. Daga ragargajejjen
gadonta sai tsumokaren kayanta aka ajiye
mana shine gadonmu. Na kasance marainiya
babu uwa ba uba, sai ni sai halina sai kuma
yayana hussaini da matarsa sai Allah. Kuma
ina godiya ga Allah a kowanne lokaci don ban
mantawa da nasihohin da mahaifina yayi min
ta karshe. Allah yana ganina, kuma Yana
taimakona, Bai bari na tagayyara ba. Babbar
baiwar da Allah ya min itace daya bani jama'a,
masu sona suna da yawa a duniya, mata da
maza. Yara da manya kowa yana yabon
halayyata koda kuwa an kushe ni sai kaji ana
yabona. Na godewa Allah Shine gatana shine
majibancin al'amurana. Aisha farida ta rushe
da kuka hade da hawaye mai radadin fita.
Hawaye ne yake ta kwaranya tamkar an bude
ruwa a famfo. Barrister Mu'azzam ya juya ya
dubi abokinsa barrister nuruddeen shima ya
kalle shi sannan suka juya su dukka suka sake
duban aisha farida, suka cigaba da mamakin
wannan yarinya mai surutu da zazzakar murya,
ga iya magana tana fitar da kalamai dalla dalla
a jejjere tamkar wacce wani ya labe yake rada
mata. Wannan itace fadi ba'a tambaye ki ba,
amma fa sunji dadin sauraron labarinta, yayi
ma'ana kuma sun karu da abubuwa da yawa
na game da zamantakewar rayuwa. Sannan sun
tausaya mata, ta cancanci a tausaya mata
domin rayuwarta tana cike da abubuwan ban
tausayi. Daga ganin ta a kidme take a dimauce
ta fado musu ta gaishe su, kafin su amsa ta
sami kujera ta zauna ta hau basu labari. Yau
ne rana ta farko da suka fara ganinta a
rayuwarsu itama haka, farida batasan wacce
irin damuwa bace ta hana su zama a gidajensu
suka fito a cikin daren nan suka zauna a wajen
shakatawa mai suna "fish park" dake
nassarawa GRA. Barrister muazzam ya zaro
dan karamin handkerchief fari kal daga gaban
aljihun rigarsa (suit) ya mika mata ba tare da
yayi magana ba, ta dago da jajayen idanuwanta
tana gogewa wani sabon hawaye fil yana
bulbulowa daga idanuwanta. Barrister
muazzam ya mika hannu a sanyaye kan teburin
dake gabansu ya dauko wani kwalin lemo ya
tsiyaya a cikin kofuna biyun da suke gabansu
ya mika mata, sai ta karba sannan tayi godiya
ta fara kurba a cikin nutsuwa yayin da shima
ya dauki daya kofin ya kwankwadi lemon a
cikin kofin ya mikawa abokinsa shima ya karba
ya fara sha ba tare da wani daga cikinsu yace
uffan ba. Sai aisha farida ta fara tunanin ko
kurame ne bata sani ba tazo ta hau su da
surutu, saboda tun sanda ta zo ta zauna ana
fiye da mintuna talatin babu wanda yayi ko tari
a cikinsu har yanzu sai kallonta kawai sukeyi
da ido. Ta kurbi lemo ta ajiye kofin akan teburi
ta sharce hawaye da hankicin dake hannunta
tayi murmushi. Tace bayin Allah shin baku
magana ne, ko kurame ne?
Kallonta kawai suke yi har yanzu babu wanda
ya tanka mata, su kalleta su juya su kalli
junansu. Sai taji hankalinta ya tashi, tayi ajiyar
zuciya tace yaya sunanku? Barista nuruddeen
ya dubi barr muazzam ya kifta masa ido
alamar kada yayi magana. Suka ci gaba da
sauraronta tana ta magana ita kadai, sai taji ta
zama tamkar wata mahaukaciya wacce bata
san ma abinda take yi ba, taji duk ta tsani
rayuwarta, sai ta tashi a sanyaye ta juya zata
tafi. Barr muazzam yaji tausayinta sai yace
aisha farida meyasa zaki tafi? Ta juyo da sauri
ta dube shi sai ta girgiza kai tace kuyi hakuri
ban san na takura muku ba, na shiga masifa,
na shiga kunci har na dimauce ban san dalilin
da yasa nazo wajenku na dinga zazzago muku
labari baku tambaye ni ba. Na ganku
kammalallu dan haka na zata zaku karbe ni
hannu bibibuy , kuba bani shawara dan ban san
abinda zanyi ba anan gaba. Barr muazzam
yace dawo ki zauna, shirun da mukayi miki don
bamu sanki ba kuma bamu san manufarki ba
kinsan duniya abar tsoro ce bai kamata nan da
nan ka yarda da mutumin da baka taba gani
ba. Kuncin rayuwar kuwa mun fiki shiga shine
ya fito damu nan ko Allah zaisa muji dan
sanyi. Ta dawo ta zauna a sanyaye ya yin da
take tuhumar kanta da laifin rashin hankali,tana
jin haushin kuskuren data tafka daga ganin
mutane bata san su ba kawai ta zo ta zauna ta
hau basu labari,ta fadi sirrinta bayan ba'a
tambaye ta ba,lallai dole suyi mata kallon wata
sakarya. Ta tambayi zuciyarta shin ko cutar
tabin hankali ce ta kama brain din ta domin
sanda ma ta fara magana bata sani ba.
Mu'azzam ne ya ktse tunanin da take yi ya ce
"ni sunana Barr Mu'azzam,abokina kuma Barr.
Nuruddin. Mecece takamaimiyar matsalarki?
Menene dalilin da ya fito da ke daga gidanku
zuwa nan a cikin daren nan? Naga ba tare da
mijinki ku ka zo sayan kifi ba kamar yadda
nake ganin wasu ma'auratan hausawanmu na
yi? Me kika fito nema? Wanne irin taimako kike
nema daga garemu? Kina so mu saya miki kifi
ne ko kuwa kudin mota ki ke nema? Ta yi
murmushi ta ce "gaskiya ne,na cancanci a
tambaye ni domin ban yi kama da mai kamun
kai ba. A rude na shigo nan dan yau ne rana ta
farko dana taba zuwa nan,ban san inda zan
nufa ba sai na hango ku kawai na ji a raina
tamkar naga yayyena,wadanda zasu iya
taimakona shine na taho wajen ku ko Allah zai
sa ku kwace ni daga mugun dan sandan da
yake shirin cutar da rayuwata. Barr nuruddin ya
dubi abokinsa ya tsuke fuska ya ce "kai kada fa
ka yayumo mana ruwan dafa kanmu,ka bar
yarinyar nan ta kama gabanta. Me yasa ka
dawo da ita har ta yi niyyar tafiya? Ka cika
kwashe- kwashe kamar baka san irin yan
matan nan ba ne yan club? Idan ba yar club ba
wacce budurwar kirki ce zata baro gidan
iyayenta ta shigo wajen nan da dare? Ka duba
ka ga nisan unguwarsu tun daga cikin gari
zuwa nan? Zuwa ta yi ta tsara mu ko daya
daga cikinmu zai dauke ta. Ke yarinya ki kama
gabanki mu ba irinki bane,je ki can ki sami yan
uwanki irin ki. Shawarar da zan baki kuma ita
ce ki koma skul ki taimaki lyf din ki don yawan
duniya ba riba sai asara,akamr yadda kika ce
mahaifinki ya yi maki wasiyya kafin ya rasu"
aisha farida tayi dariya maimakon ta ji haishi
sai ta gyada kai tace "gaskiya ne yayana na ji
dadin shwararka kuma zan dauka insha Allah
zanyi amfani da ita. Sai nauyi da kunya ya
kama barrista mu'azzam ya ji kamar ya nutse
a cikn kasa saboda baranbaramar da abokinsa
yake yi,baya kara,ba kunya balle jin nauyi yake
maganarsa,ya harare shi yace haba nuraddin
kai fa mtsalata da kai kwaba mahgana babu
taunawa. Ka bari ka ji uzurinta idan ka gama
jin inda ta nufa sai ka yanke mata hukunci.
Kamar ba lauya ba ai sai ka gama sauraron
labarinta tun daga farko har karshe sannan ka
gama jero mata tambayoyi ta gama amsawa
ka kula da inda ta nufa sannan ka yi mata
nasiha ba fada ba. Yanzu da a kotu muke sai
ka fadi a sharia dan kawai kana jin haushin ka
sai ka huce akan yar mutane,to ba ita ta kar
zomon ba ko rataya ba'a bata ba.
Posted by Bashir Sani Mahmud on 22 Aug 2017
Aisha farida tayi karfin hali tace ba damuwa, ai
laifina ne dan banyi kama da mai kamun kai
ba, tunda ba'a tambaye ni ba nazo na fara yi
muku surutu, nasan ba'a son mace marar
kamun kai. Barr muazzam ya girgiza kai yace
zuwanki nan ba laifi bane dan kin zo kin zauna
a kusa damu, kujeru ne a jejjere kowa zai iya
zuwa ya zauna. Da kika zo kika same mu kinyi
mana sallama duk da tun kafin mu amsa har
kin zauna. Daman kamata yayi ki gabatar
mana da kanki kuma kinyi hakan sai dai kika
zarce da bamu labari shine abinda ya daure
mana kai kenan. Kallon junan da kikaga muna
yi ina tunanin ya sanki ne, shima yana tunanin
ko na sanki ne. Aisha bani labarin takamaiman
abinda ke damunki, muma nan da kika ganmu
matsala ce take addabarmu, ki saki jiki ki fada
mana mu dake sai mu taimaki juna da
shawarwari. Barr nuruddeen ya fusata ya mike
tsaye ya dubi abokinsa yace malam in ka gama
kazo ka same ni a cikin mota mu tafi, dan ba
zan iya zama ina sauraron wannan shirmen
naku ba. Bansan sanda ka zama marar aji ba,
daga haduwa da 'yar tasha sai ka hau hira da
ita kai ma kana baza sirrinka, idan taji
matsalar ka me wannan zatayi maka? Itama
bata san yadda zatayi da kanta ba balle ta
bawa wani shawara. Kada ka sake ka ambaci
sunana a cikin labarinku kai dai ka fadi taka
matsalar. Ya juya a fusace ya tafi bai daina
fada ba yana tafe yana magana yana wurwurga
hannu har ya fice daga cikin gate din. Aisha
farida da barr muazzam suka bishi da kallo har
sai da suka daina hango shi. Ta sunkuyar da
kanta kasa sai hawaye ya fara zubowa daga
idanuwanta. Kada ki yi kuka aisha, ki mayar da
komai ba komai ba. Kece fa kika gama bani
labarin cewa zaki iya zama da kowanne irin
mutum a duniya. Inji brr muazzam. sai tayi
murmushi ta shiga goge hawayenta tace ko
kusa ban damu ba, banji haushi ba. Kawai dai
abokinka yayi min kallon ballagar mace, 'yar
tasha, 'yar club, karuwa kenan. Shine mutum
na farko a rayuwata daya taba jifata da
wadannan munanan sunaye, saboda bai sanni
ba, sai dai ina fatan ya sanni nan gaba. Barr
muazzam yace yi hakuri kanwata, ki cigaba da
bani labarin rayuwarki, ina jin dadin sauraronki.
Haqiqa Aisha farida,labarinki yakai maqura
gurintausayi,nayi kuka sosai,rabena da
irinkukannan yaukimani wata takwas
kenan.tunrasuwar yayata,ayau nafisa mamawa
kinsani cikintausayin ki,maganardanakeyi
yanzuhaka nakasa tsayarda hawayendake
zuba'a idona. kitaimaka kibani lbrin cigabanki
da daukakardakikasamu kozansamisukuni
yau...wallah nafisa natausayamiki sosai. BABI
NA BIYU Da na karasa makarantar primary sai
yaya hussaini ya kaini wata makaranta a wajen
sabongari na zana jarabawar common entrance
ta shiga makarantar federal. Allah cikin ikonsa
sai naci jarabawa aka turani makarantar da na
zaba wato FGC kano. Yayi min sayayya iya
karfinsa ya kaini, ya bibbiya dukka kudaden
makarantar da aka bukata, ya dawo gida ya
barni a can. Nayi kuka saboda rashin sabo,
gashi bansan kowa ba a makarantar amma
daga baya na saba da dalibai 'yan uwana sai
na fara jin dadin rayuwar makarantar. Jama'a
na sona saboda yadda nake da fara'a, ladabi
da son aiki bana kiwa don haka kowa yana son
ya jani a jiki saboda ina da matukar tsafta. Na
yi suna a makarantar nan da nan malamai ma
suka sanni saboda kwazona da wayo, ga iya
magana. Na gama aji uku hutun da zamu shiga
aji hudu aka cireni, abu ya ci tura hidimomu
sun karu, yayana ba zai iya cigaba da yi min
siyayya ba da biyan kudin makaranta ba
kasancewar shima ya hayyayyafa. A jejjere ba
kakkautawa abida take haihuwa, 'ya'yanta na
farko ma 'yan biyu ne maza abubakar da umar,
sai ta haifi mace mas'uda ga wani cikin a
jikinta ko yaye ta goyen bata yi ba. Ga kudin
haya ya karu, cefane ya karu, farashin abinci
ya karu, gashi an kara kudin makaranta ya
kusa ninka na da ma. Daman duk sanda zan
koma makaranta sai ya ciyo bashi kafin ya
harhada ni in tafi. Ya kira ni daki ya zaunar da
ni yayi min bayanin halinda ake ciki, sai ya bani
hakuri cewar zai mayar dani makarantar
gwamnati ta ;yan mata dake shekara. Dole na
koma makarantar shekara naci gaba da karatu,
daga aji 4 na fara, sai na zama zakaran gwajin
dafi nafi kowa kokari saboda dana sami horo a
FGC a wajen yaran kabilun da basa jin hausa
da yaran hausawan da suka sami horon turanci
tun daga primary. Ajin kimiya na shiga (science
class) har Allah ya kaini aji shida aka bani
shugabar dalibai, duk wata gasa ko muhawara
ta turanci tsakaninmu da wasu makarantun ni
nake tsayawa makarantarmu, idan bana nan
babau abinda yake tafi dai dai. Shugabar
makarantar mu tana alfahari dani, kullum tana
kwatance dani saboda kokarina. Da muka
gama makarantar ita da malamai sai da sukayi
takaicin rashina saboda ba'a sami madadina
ba. Bayan gama makarantata da wata uku
yayana ya harhada 'yan kudadensa ya bani
kudin mota da guzuri na zuwa shagamu,
saboda duksanda yake zuwa shi da matarsa da
'ya'yansa ina makaranta ba'a zuwa dani.
Tsofaffin abokan hirata har sun gaji da
tambayata wasu ma sun mutu, haka wasu
daga cikin yayyena sun murmutu duk banje ba.
Ina samun wasikun kanwata munauwara akai
akai duk sanda ta sanda ta sami mai zuwa sai
ta bayar an kawao min, ta shaida min cewar
an cire ta daga makaranta tana secondary aji 3
anyi mata aure saboda rashin kudi. Ni kadai
yaya hussaini ya saka a mota zuwa shagamu,
dana isa garin shagamu a tasha na hau acaba
zuwa gidanmu, ban manta hanya ba. Da yawan
'yan gidanmu basu shaida ni ba sai daga baya
suka gane ni, sunga na girma nayi kyau. Duk
da rashin wadatar da muke ciki a kano sai
naga na fisu kyawun gani, cikakkiyar lafiya da
gogewa. Na zagaya dangi na kusa dana nesa
har sai da naji kafafuwana zasu gutsire saboda
yawansu. Na ziyarci gidan kanwata dake agege
a lagos anan take aure, rayuwarta abin tausayi,
gida ne irin na haya mai dauke da dakuna fiye
da ashirin, yare kala kala kamar hausawa,
yarbawa, igbo, da wasu yaruka daban daban.
Bandaki daya ne kacal, tunda asubahi ake fara
layin shiga bandaki. Mijinta iliyasu shima dan
shagamu ne amma a lagos yake facin taya, ita
kadai ce sana'arsa. 'Ya'yansu biyu a lokacin.
Saboda tausayin halinda na same ta kusan
dukka kayana na sakawa na bata kyauta,
sannan na hada mata mayafai, sarkokina,
takalmana, guda dai dai na rarrage. Duk
kudaden dana samu na bata dukka kudin mota
na komawa ta kano kadai na ware. Muka sha
kuka tare da nazo tafiya, kukan da muke na
tunawa da iyayenmu ne da kuma kukan
rabuwa, don munsan zamu dade kafin mu sake
haduwa. Na dawo kano jakata kwalam babu
komai duk na rabar da kyana kuma da masu
kyan na tafi dasu. Tsummokaran, tsofaffin,
yagaggun kadai na bari a gida. Haka nazo na
dinga karancin kaya duk sun ragargaje dan
haka na daina zuwa taron biki ko gidan
kawayena. Abida tayi ta min fada tace nayi
garaje ai ba'ayin haka tun da nasan ban ajiye
wasu ba a lufge kuma bani da mai dinka min
wasu ai bai kamata in rabar ba. Idan fita ta
kama ni dole sai dai in ari kayan abida in saka
inje, ina dawowa in cire mata. Abinka da
cakudi, zaman saka ido, kowa yana kula da
shige da ficenka. Gulmammaki iri iri bayan
zumde da yafice zaka ga anayi mana, abin ya
kai har su dinga kiran 'ya 'yan abida suna
bugun cikinsu suna tambayarsu wai ina kayana
suka ga ina arar na abida? Irin wannan gutsiri
da tsomar sai da ta wuce kan matan gida ta
koma wajen mazansu, su kuma suka
tseguntawa yayana hussaini, suka ce masa bai
dace in dinga arar kayan abida ina fita kofar
gida ina tsayawa da samari ba, ina yawo da
kawayena a gari. Idan ba an lura ba in a
duhune sai a zaci abida ta fara bin maza.
Sukayi ta zuba masa bayanan da dole
hankalinsa yayi matukar tashi, ransa yayi
mummunan baci. Ya shigo dakina ransa a bace
ya iske ni a kwance yace min in kira abida
itama ta shigo nan dakin yana da magana da
ita. Mukazo muka durkusa a gabansa muna
karkarwa saboda yadda muka ga ransa a bace
gashi mutum ne mai zafin zuciya. Ya umarci
abida ta fada masa gaskiya kada ta kuskura
tayi masa karya akan abinda zai tambayeta,
haka nima ya gargadeni kafin ya yi mana
tambayoyin. Muka yi masa alkawarin zamu
fada gaskiya, ba zamuti karya ba. Cike da
fargaba mai tsanani muke sauraron abinda zai
fada mana. Ya cewa abida da gaske ne aisha
farida tana aron kayanki ta saka ta fita yawo a
gari? Sai abida ta dafe kirji tace Innalillahi
wainna ilaihir rajiun! Ya daka mata tsawa mai
firgitarwa yace baki bani amsa ba. Nan da nan
ta fara hawaye, jikinta na karkarwa tace eh
haka ne. Sai ya kai mata mari har sai da ta
fadi kasa, ya fada cikin fushi yace to ta hada
kayanta ta tafi gidansu. Na rushe da kuka na
dinga rokarsa ya yafe mata ba laifinta bane
nice na tambaye ta. Nima din ya yafe min na
daina daga yau. Sai ya rufe ni da duka yana
duma, yana tattaka ni da kafa tamkar zai kashe
ni. Munafukan matan gidan ne suka zo suka
kwace ni dakyar, ransa yayi matukar baci sai
fada yake yana zaginmu wai sai mun harhada
kayanmu mun bar masa gidansa. Ana bashi
hakuri tamkar zuga shi akeyi dakyar ya haukra
ya kyale mu amma tun daga lokacin baya raga
mana, komai mukayi sai ya hantare mu, sai
harara koda yaushe. Sai na daina fita koina ,
koda yaushe ina fama da dinkin yaga da zare
da allura. Abida ta iske mijinta a dakinsu ta
ajiye masa abinci sannan ta durkusa ta gaishe
shi. Ya amsa dakyar cikim fushi, bata damu ba
ta zauna a kusa dashi ta dauko muhuci ta fara
yi masa firfita. Sai yayi mata tsawa yace ta
bari baya so, ta tashi ta fita ta bashi waje.
Cikin lallausar murya tana zubar da hawaye
tace ka yafe mana laifukan da muka maka,
munyi kuskure, fushin da kake yi damu ya
hanamu sukuni, bama jin dadin rayuwarmu,
rayuwa tayi mana kunci. Dan ban fada maka
bane halin da ake ciki kada ranka ya baci, ashe
dana fada maka ma zaifi sauki. Aisha farida ce
ta rabar da kayan sakwarta kakaf a shagamu
saboda tausaya musu da tayi, ta gansu cikin
tsumma, shine ta dawo bata da kaya sai
yagaggu. Dan haka bata iya fita wajen
kawayenta shine nake bata aron kayana ta
saka tana dawowa take cirewa, bansan abinda
'yan gulma suka fada maka ba har ya jawo
ranka ya baci ka dauki mataki cikin fushi. Sai
yayi shiru yana sauraronta can yace ai duk
laifinki ne, meyasa ba zaki fada min halin da
ake ciki a cikin gidana ba har sai da wasu suka
fada min a waje? Kinsan irin zaman da mukeyi
da 'yan gidannan, zaman saka ido ne, duk
shige da ficen mu akan idonsu. Ashe gaba daya
lungunnan gulmar ku ake yi shiyasa raina ya
baci. A take ya bata naira dubu biyu yace ta
bani inje in sayo atamfofi guda biyu 'yan naira
dari takwas takwas inyi dinkin dari bibbiyu.
Abida mace mai hakuri da tsananin wayo, ta
iya zama da mijinta duk zafin zuciyarsa, tabbas
macen da bata da hakuri da wayo ba zata iya
zama dashi ba, sai gashi da kansa yayi
nadamar aninda yayi mana, sai yaji kunya yazo
yana lallaba mu. DUK KYAN TAKALMI 5
Saurayina guda daya nake kulawa mai suna
musbahu, lungun mu daya dashi kowa yasan
mu tare, yana sona sosai nima haka saboda
yana kula dani. Tun sanda na gama sakandire
yake so ya aiko gidanmu ayi zancen aure sai
aka sami matsala daga gidansu, mahaifiyarsa
bata sona 'yar kanwarta take so ayi musu
auren gida, shi kuma ni yake so ya
aura.mahaifiyarsa ta tsane ni haka kawai, ko a
hanya na gaishe ta bata amsawa shiyasa na
daina zuwa gidansu don da ina zuwa wajen
kanwarsa jamila kawata ce ajinmu daya a
shekara. Musbahi ma yaji labarin duka dana
sha saboda aron kaya, sai naga ya siyo min
leshi guda daya da atamfa ya hada min da
naira dari biyar kudin dinki, sannan yayi min
fada in daina boye masa sirrina saboda yadda
yake sona a ransa, matsalata ai matsalarsa ce.
Yace duk sanda na shiga matsala in fada masa
ko bashi da kudi zai ciyo bashi yayi min komai
in dai baifi karfinsa ba. Yaci gaba da bani
hakuri akan halinda yake ciki shi da
mahaifiyarsa, ita ta hana shi ya turo gidanmu
zancen aurenmu. Ya umarce ni da mu dage da
addu'a Allah Ya karkato da zuciyar
mahaifiyarsa kaina taji tana sona ayi auren
dani. Sakamakon jarabawar mu na sakandire
ya fito naci credit takwas, geography ne kadai
naci pass shima dan a ranar da muka yi
jarabawar bani da lafiya. Sai misbahu yace idan
ya sami kudi zai saya min form din jamb in
wuce jami'a. Sai nace ba zan iya karatu a
jami'a ba saboda 'ya'yan masu kudi ne sukeyi,
bani da mai bani kudin mota da kudin sayan
handout, gashi dole sai an saka sutura masu
kyau. Sai shima ya gasgata zancena yaga
shima bashi da halin da zai dauki nauyin duk
wadannan sabida dan abinda yake samu ba
mai yawa bane. Duk da wasu lokutan sukan
sami ayyuka da yawa suna samun kudi a
business center yake aiki, suna typing a
computer, suyi kalandu ko meme. Sai yace to
zai samo min management in fara, nan ma
nace bana so nafi son inyi schl of nursing
saboda ba ruwana da neman kayan sakawa,
suna da uniform, sai yace shikenan zai binciko
yaji duk yadda akeyi a shiga amma in fara jin
ra'ayin yayana. Yayana ya amince da
shawararmu kuma yaji dadi musamman da
musbahu yazo har kofar gidanmu ya sa akayi
masa sallama da yayana hussaini ya kara yi
masa bayani. Yace zai taimaka min da wata
dawainiyar kudin makarnatar sai ya amince
yayi masa godiya. Musbahu da yayana ne suka
hada gwiwa suka bani duk kudaden da ake
bukata na shiga makarantar koyar aikin jinya
ta malam aminu kano dake unguwar court
road. Karatun shekara uku ne a shekara ta uku
ne muke zuwa asibiti koyar aiki don haka
karatu na yi tayi haikan, ban taba samun
matsala ba cinye jarabawata nake yi koda
yaushe. A asibitin malam aminu kano ake horar
damu koyar aiki (attachment). Ina zuwa
kkullum daga unguwarmu sharifai zuwa court
rd akan acaba saboda idan nace zan hau bus
zan bata lokacina zanyi in makara. Kudin
acabana kit da kit babu canji wata rana ko
purewater zan sha sai dai kawayena su saya
min. Duk da idan za'a je sayan abinci ko shan
lemo sai in gudu bana binsu saboda kullum sai
dai su saya min, ni kuma na fara jin kunya sun
gane bani dashi. Kawata khadija sani ismail
kadai wacce bata gajiya da taimakona kuma
duk sanda tace muje cin abinci naki zuwa ko
na sulale na gudu sai ranta ya baci, har tayi
fushi dani. Sai inyi tayi mata bayanan karya in
kirkiro uzurin dana je nayi ba guduwa nayi ba
sai ta ki yadda tasan karya nakeyi. Ba ita nake
ji ba, sauran kawayenmu nakeji don suna nuna
min bakin hali daga baya kuma in dinga jin
kananan maganganu cewar na cika san banza
kullum bana fitar da kudina ina sayawa kaina
abu balle in sayawa wani, sai dai ni kullum a
saya min. Rashin sani yafi dare duhu, kallon
kitse sukeyi wa rogo. Hakika ni mai yawan
tsafta ce in kula da fararen kayan makaranta
ta, kullum tsaf dani, ina kalkale jikina tas a
wanke ga karin guga. Gani nafi duk 'yan ajin
mu kokari yawanci ni nake basu amsa. Khadija
bazata iya rabuwa dani ba dan bata da kokari
sai dai gata, tunda iyayenta suna da hali. Duk
wasu manyan littattafai na karatu (text book)
babanta yana saya mata duk tsadarsu, sai nafi
morarsu don ni ce mai hazakar karatun ba ita
ba. Da taimakon Allah da taimakon khadija sani
nake cin jarabawa dan ba zan iya sayan
littattafan nan masu tsada ba. Badan Allah Ya
sa na iya kitos ba ina yiwa makwabta, da wata
rana ma ba zanje makaranta ba saboda duk
ranar da yaya hussaini ya tashi bashi da kudi
sai yace in hakura kada inje makaranatar randa
ya samu naje. Ni kuma bana so inyi fashi, da
kudin kitson nake harhadawa in tafi duk da
kitso a unguwar bashi da tsada, kan manya
naira talatin ko arba'in, na yara kuwa naira
ashirin ko goma ne. Ban taba fadawawa
kawayena sirrina ba, duk da yawan kawayen da
nake dasu a ajinmu mata da maza, sai dai ayi
hayaniya wasa da dariya a watse, ina taka
tsantsan da harshena a koda yaushe. Babu
wanda a cikinus ya san yadda gidanmu yake,
basu taba zaton haka nake rayuwa ba, sai dai
sun fahimci wani abu akwai wasu matsaloli
wanda ba zasu boyu ba. Suyi ta zargi da sake
sakensu a ransu su kadai, ni dai bazasu ji daga
bakina ba kuma ba zasu iya tara ta su
tambaye ni ba. Ni daman bana zuwa gidan
kowa balle azo gidanmu, mu hadu a abkin gate
ne mu rabu idan an tashi. Bana jin dadin
rayuwata a wannan bangaren saboda bani da
wata takamaimiyar kawa ko masoyin da zan
amayar musu da radadin da zugin matsalolin
da suke addabata. Kawata guda daya, itace
aminiyata, yayata, masoyiyata wato matar
yayana abida. Muna zama ni da ita mu raba
dare ko mu yini muna tattauna matsalolinmu,
koda yaushe ina samun nutsuwa da kwarin
gwiwa idan abida ta bani hakuri akan talaucin
da na tsinci kaina da shawarwari, sai inji sanyi
a raina, tawakkali ya kama zuciyata sai inji ta
tuno min da nasihohin da mahaifina yayi min a
baya. Idan nayi haka sai in dawo da walwalata,
ni burina guda daya ne shine in gama karatuna
in fara aiki in taimaki kaina, in taimaki 'yan
gidanmu. Babbar matsalar ma da tafi damuna
shine zaman cakudi a gidanmu, cikin tsagoron
kazata da cinkosa, babban burina ba wuce inga
mun bar gidan nan da umguwar mu canja gida
ko haya ce dai mu kama gidan da muke mu
kadai. Dakina daya da yara, ga dakin dan
karami mun cunkushe gashi su dukka yaran
abida fitsarin kwance sukeyi dan haka sun ruba
katifar sai zarni take dan haka na hakura da
katifar na bar musu. Na koma kwana akan
tabarma, idan na tashi da safe sai inyi salla
akai in nada in jingine a lungu sai zan sake yin
wani sallar sannan in shimfida. Har yanzu
kayana a jakar bagco yake a gefen shimfidata,
rayuwata ba irin na 'yan matan 'yan boko bace,
tamkar a kauye nake ba'a birni ba. Ko inyi
tunanin shiga hanyar banza, ban taba sha'awar
makalewa gidan kawaye ba ko arar kayan
kawa, na rike talaucina na kama kaina bana
sha''awar kayan wani. Daga makaranta sai
gida, a gidan ma nafi zama a daki kullum ina
karatu. Idan kaga na fito aiki nazo taya abida,
wankan 'ya'yanta , tsarkinsu ko aikin girki. Sai
'yan gidanmu da sauran 'yan unguwa suka
shiga yimin shaidar girman kai ne dani dan ni
'yar boko ce, basa ganin fara'ar da nake yi
musu. Kullum ina gaishe su ko basu ganni ba,
tabbas mutum ba'a iya iya masa, saboda dan
Adam ya kasance mai butulci ne. BABI NA UKU
Wata rana ranar litinin da misalin karfe daya na
rana muna cikin a sibiti, a bangaren marasa
lafiya muke wadanda aka kwantar dasu
sakamakon wasu kurajen da suka feso a
jikinsu. Muna biye da ma'aikaciyar jinya matron
maryam tana nunnana mana yadda ake aiki,
domin neman karin bayani sai tace bari ta
hada mu da kwararren likita wanda ya kware a
bangaren fata. Ta tura wani daki ta shiga
muma muka bita a baya da alama dakin
daukan darussa ne sabida naga kujeru ne zalla
da allo makale a jikin bangon. Kamar yadda
naji ta ambaci sunansa, dr shureim imran. Mun
iske shi tsaye a tsakiyar ajin tare da wasu
daliban likitoci guda 3 maza biyu, mace daya
da alama sunzo sunyi masa tambayoyi ne akan
wasu abubuwan da basu gane ba. Bayanai
yake yi musu cikin harshen turanci kai kace
baturen america ne, kalmomin kimiyyar
(botanical names) da yake ta ambato yana
jerowa layi layi da ka ba tare da yana duba
littafi ba, kai kace shine ya lakaba musu sunan
don ya haddace. Muna sake kutsawa cikin
ofishin yayin da zazzakar muryarsa, daddada
take sake shiga kunnuwanmu sai duk muka
kagu mu isa gabansa don mu kalli fuskar mai
muryan nan daddada. Kasancewar kofar ta
cushe muna shiga don muna da yawa, ga
dalibai likitoci nan suna kokarin fitowa sun
gama daukar darasin. Kowa ya kagu yayi ido
hudu da mai daddadar muryar nan, keyarsa
kawai na fara hangowa daga nesa sai na
tabbatar bakar fata ne dan uwana saboda ban
hango jan kunne ba da farin gashi irin na
turawa ba. Bakin gashi ne tattaura irin namu
na hausawa, sai dai gashin a gyare yake yana
shekin mai kuma ya kwanto lambar zuwa
karshen keyarsa. Kansu babu hula, yana sanye
da bakaken kaya riga da wando (suit), farar
riga mai dogon hannu daga ciki, ya daure
wuyansa da jan kyalle wato necktie. Dana
matso ciki sai na fara hango gefen fusakarsa,
wata lafiyayyiyar fata na fara hangowa mai
dauke da launi mai tsananin kyau. Irin kalar da
take tsada a duniya wato hasken duhu
(chocolate color). Ko dana sake samun daman
na matso kuda dashi sai ga gefen fuskarsa tar
ina gani wato idonsa daya da gefen hancinsa,
sai kawai naji wata mummunar fadywar gaba
ta far min ni ma bansan dalili ba har wadanda
ke kusa dani zasu iya jiyo karar ajiyar zuciya
danayi. Tunda nake a rayuwata ban ta ba ganin
irin wadannan dara daran idanuwan ba masu
tsananin haske daga ciki, da bakar kwayar ido
mai tsananin baki, aka zagaye idon da wasu
gashin ido da gashin gira masu yawa da
tsananin baki, ya gyara su sunyi kira mai kyau
suna sheki. A nutse ya waiwayo da kyakkyawar
fuskarsa gaba daya ya dube mu, bani kadai ba
duk wata 'ya mace da take wajen sai dataji a
ranta dama ace wannan kadarar mallakarta ce.
'Yan uwansa maza ma sai da suka raya a
ransu dama ace sune shi, ga kyau ga ilimi.
Ashe a da dana ke hango gefen fuskarshi ban
hango komai ba, kyau mai sunan kyau sai ka
kalle shi gaba dayansa daga kafarsa zuwa
kansa. Dogon mutum ne sosai ma kyawun
sura, bashi da kiba da yawa, haka bashi da
rama. Yayi kama da irin bakaken turawan nan
da ake kira african American, hukuncin da na
yanke masa kenan dan ko kusa baiyi kama da
'yan nigeria ba! Tabbas ruwa biyu ne suka
hadu suka same shi bakar fata da farar fata.
Saurayina guda daya nake kulawa mai suna
musbahu, lungun mu daya dashi kowa yasan
mu tare, yana sona sosai nima haka saboda
yana kula dani. Tun sanda na gama sakandire
yake so ya aiko gidanmu ayi zancen aure sai
aka sami matsala daga gidansu, mahaifiyarsa
bata sona 'yar kanwarta take so ayi musu
auren gida, shi kuma ni yake so ya
aura.mahaifiyarsa ta tsane ni haka kawai, ko a
hanya na gaishe ta bata amsawa shiyasa na
daina zuwa gidansu don da ina zuwa wajen
kanwarsa jamila kawata ce ajinmu daya a
shekara. Musbahu ma yaji labarin duka dana
sha saboda aron kaya, sai naga ya siyo min
leshi guda daya da atamfa ya hada min da
naira dari biyar kudin dinki, sannan yayi min
fada in daina boye masa sirrina saboda yadda
yake sona a ransa, matsalata ai matsalarsa ce.
Yace duk sanda na shiga matsala in fada masa
ko bashi da kudi zai ciyo bashi yayi min komai
in dai baifi karfinsa ba. Yaci gaba da bani
hakuri akan halinda yake ciki shi da
mahaifiyarsa, ita ta hana shi ya turo gidanmu
zancen aurenmu. Ya umarce ni da mu dage da
addu'a Allah Ya karkato da zuciyar
mahaifiyarsa kaina taji tana sona ayi auren
dani. Sakamakon jarabawar mu na sakandire
ya fito naci credit takwas, geography ne kadai
naci pass shima dan a ranar da muka yi
jarabawar bani da lafiya. Sai misbahu yace idan
ya sami kudi zai saya min form din jamb in
wuce jami'a. Sai nace ba zan iya karatu a
jami'a ba saboda 'ya'yan masu kudi ne sukeyi,
bani da mai bani kudin mota da kudin sayan
handout, gashi dole sai an saka sutura masu
kyau. Sai shima ya gasgata zancena yaga
shima bashi da halin da zai dauki nauyin duk
wadannan sabida dan abinda yake samu ba
mai yawa bane. Duk da wasu lokutan sukan
sami ayyuka da yawa suna samun kudi a
business center yake aiki, suna typing a
computer, suyi kalandu ko meme. Sai yace to
zai samo min management in fara, nan ma
nace bana so nafi son inyi schl of nursing
saboda ba ruwana da neman kayan sakawa,
suna da uniform, sai yace shikenan zai binciko
yaji duk yadda akeyi a shiga amma in fara jin
ra'ayin yayana. Yayana ya amince da
shawararmu kuma yaji dadi musamman da
musbahu yazo har kofar gidanmu ya sa akayi
masa sallama da yayana hussaini ya kara yi
masa bayani. Yace zai taimaka min da wata
dawainiyar kudin makarnatar sai ya amince
yayi masa godiya. Musbahu da yayana ne suka
hada gwiwa suka bani duk kudaden da ake
bukata na shiga makarantar koyar aikin jinya
ta malam aminu kano dake unguwar court
road. Karatun shekara uku ne a shekara ta uku
ne muke zuwa asibiti koyar aiki don haka
karatu na yi tayi haikan, ban taba samun
matsala ba cinye jarabawata nake yi koda
yaushe. A asibitin malam aminu kano ake horar
damu koyar aiki (attachment). Ina zuwa
kkullum daga unguwarmu sharifai zuwa court
rd akan acaba saboda idan nace zan hau bus
zan bata lokacina zanyi in makara. Kudin
acabana kit da kit babu canji wata rana ko
purewater zan sha sai dai kawayena su saya
min. Duk da idan za'a je sayan abinci ko shan
lemo sai in gudu bana binsu saboda kullum sai
dai su saya min, ni kuma na fara jin kunya sun
gane bani dashi. Kawata khadija sani ismail
kadai wacce bata gajiya da taimakona kuma
duk sanda tace muje cin abinci naki zuwa ko
na sulale na gudu sai ranta ya baci, har tayi
fushi dani. Sai inyi tayi mata bayanan karya in
kirkiro uzurin dana je nayi ba guduwa nayi ba
sai ta ki yadda tasan karya nakeyi. Ba ita nake
ji ba, sauran kawayenmu nakeji don suna nuna
min bakin hali daga baya kuma in dinga jin
kananan maganganu cewar na cika san banza
kullum bana fitar da kudina ina sayawa kaina
abu balle in sayawa wani, sai dai ni kullum a
saya min. Rashin sani yafi dare duhu, KALLON
KITSE sukeyi wa ROGO. Hakika ni mai yawan
tsafta ce in kula da fararen kayan makaranta
ta, kullum tsaf dani, ina kalkale jikina tas a
wanke ga karin guga. Gani nafi duk 'yan ajin
mu kokari yawanci ni nake basu amsa. Khadija
bazata iya rabuwa dani ba dan bata da kokari
sai dai gata, tunda iyayenta suna da hali. Duk
wasu manyan littattafai na karatu (text book)
babanta yana saya mata duk tsadarsu, sai nafi
morarsu don ni ce mai hazakar karatun ba ita
ba. Da taimakon Allah da taimakon khadija sani
nake cin jarabawa dan ba zan iya sayan
littattafan nan masu tsada ba. Badan Allah Ya
sa na iya kitos ba ina yiwa makwabta, da wata
rana ma ba zanje makaranta ba saboda duk
ranar da yaya hussaini ya tashi bashi da kudi
sai yace in hakura kada inje makaranatar randa
ya samu naje. Ni kuma bana so inyi fashi, da
kudin kitson nake harhadawa in tafi duk da
kitso a unguwar bashi da tsada, kan manya
naira talatin ko arba'in, na yara kuwa naira
ashirin ko goma ne. Ban taba fadawawa
kawayena sirrina ba, duk da yawan kawayen da
nake dasu a ajinmu mata da maza, sai dai ayi
hayaniya wasa da dariya a watse, ina taka
tsantsan da harshena a koda yaushe. Babu
wanda a cikinus ya san yadda gidanmu yake,
basu taba zaton haka nake rayuwa ba, sai dai
sun fahimci wani abu akwai wasu matsaloli
wanda ba zasu boyu ba. Suyi ta zargi da sake
sakensu a ransu su kadai, ni dai bazasu ji daga
bakina ba kuma ba zasu iya tara ta su
tambaye ni ba. Ni daman bana zuwa gidan
kowa balle azo gidanmu, mu hadu a abakin
gate ne mu rabu idan an tashi. Bana jin dadin
rayuwata a wannan bangaren saboda bani da
wata takamaimiyar kawa ko masoyin da zan
amayar musu da radadin da zugin matsalolin
da suke addabata. Kawata guda daya, itace
aminiyata, yayata, masoyiyata wato matar
yayana abida. Muna zama ni da ita mu raba
dare ko mu yini muna tattauna matsalolinmu,
koda yaushe ina samun nutsuwa da kwarin
gwiwa idan abida ta bani hakuri akan talaucin
da na tsinci kaina da shawarwari, sai inji sanyi
a raina, tawakkali ya kama zuciyata sai inji ta
tuno min da nasihohin da mahaifina yayi min a
baya. Idan nayi haka sai in dawo da walwalata,
ni burina guda daya ne shine in gama karatuna
in fara aiki in taimaki kaina, in taimaki 'yan
gidanmu. Babbar matsalar ma da tafi damuna
shine zaman cakudi a gidanmu, cikin tsagoron
kazanta da cinkoso, babban burina ba wuce
inga mun bar gidan nan da umguwar mu canja
gida ko haya ce dai mu kama gidan da muke
mu kadai. Dakina daya da yara, ga dakin dan
karami mun cunkushe gashi su dukka yaran
abida fitsarin kwance sukeyi dan haka sun ruba
katifar sai zarni take dan haka na hakura da
katifar na bar musu. Na koma kwana akan
tabarma, idan na tashi da safe sai inyi salla
akai in nada in jingine a lungu sai zan sake yin
wani sallar sannan in shimfida. Har yanzu
kayana a jakar bagco yake a gefen shimfidata,
rayuwata ba irin na 'yan matan 'yan boko bace,
tamkar a kauye nake ba'a birni ba. Ko inyi
tunanin shiga hanyar banza, ban taba sha'awar
makalewa gidan kawaye ba ko arar kayan
kawa, na rike talaucina na kama kaina bana
sha''awar kayan wani. Daga makaranta sai
gida, a gidan ma nafi zama a daki kullum ina
karatu. Idan kaga na fito aiki nazo taya abida,
wankan 'ya'yanta , tsarkinsu ko aikin girki. Sai
'yan gidanmu da sauran 'yan unguwa suka
shiga yimin shaidar girman kai ne dani dan ni
'yar boko ce, basa ganin fara'ar da nake yi
musu. Kullum ina gaishe su ko basu ganni ba,
tabbas mutum ba'a iya iya masa, saboda dan
Adam ya kasance mai butulci ne. BABI NA UKU
Wata rana ranar litinin da misalin karfe daya na
rana muna cikin a sibiti, a bangaren marasa
lafiya muke wadanda aka kwantar dasu
sakamakon wasu kurajen da suka feso a
jikinsu. Muna biye da ma'aikaciyar jinya matron
maryam tana nunnana mana yadda ake aiki,
domin neman karin bayani sai tace bari ta
hada mu da kwararren likita wanda ya kware a
bangaren fata. Ta tura wani daki ta shiga
muma muka bita a baya da alama dakin
daukan darussa ne sabida naga kujeru ne zalla
da allo makale a jikin bangon. Kamar yadda
naji ta ambaci sunansa, dr shureim imran. Mun
iske shi tsaye a tsakiyar ajin tare da wasu
daliban likitoci guda 3 maza biyu, mace daya
da alama sunzo sunyi masa tambayoyi ne akan
wasu abubuwan da basu gane ba. Bayanai
yake yi musu cikin harshen turanci kai kace
baturen america ne, kalmomin kimiyyar
(botanical names) da yake ta ambato yana
jerowa layi layi da ka ba tare da yana duba
littafi ba, kai kace shine ya lakaba musu sunan
don ya haddace. Muna sake kutsawa cikin
ofishin yayin da zazzakar muryarsa, daddada
take sake shiga kunnuwanmu sai duk muka
kagu mu isa gabansa don mu kalli fuskar mai
muryan nan daddada. Kasancewar kofar ta
cushe muna shiga don muna da yawa, ga
dalibai likitoci nan suna kokarin fitowa sun
gama daukar darasin. Kowa ya kagu yayi ido
hudu da mai daddadar muryar nan, keyarsa
kawai na fara hangowa daga nesa sai na
tabbatar bakar fata ne dan uwana saboda ban
hango jan kunne ba da farin gashi irin na
turawa ba. Bakin gashi ne tattaura irin namu
na hausawa, sai dai gashin a gyare yake yana
shekin mai kuma ya kwanto lambar zuwa
karshen keyarsa. Kansu babu hula, yana sanye
da bakaken kaya riga da wando (suit), farar
riga mai dogon hannu daga ciki, ya daure
wuyansa da jan kyalle wato necktie. Dana
matso ciki sai na fara hango gefen fuskarsa,
wata lafiyayyiyar fata na fara hangowa mai
dauke da launi mai tsananin kyau. Irin kalar da
take tsada a duniya wato hasken duhu
(chocolate color). Ko dana sake samun daman
na matso kusa dashi sai ga gefen fuskarsa tar
ina gani wato idonsa daya da gefen hancinsa,
sai kawai naji wata mummunar fadywar gaba
ta far min ni ma bansan dalili ba har wadanda
ke kusa dani zasu iya jiyo karar ajiyar zuciya
danayi. Tunda nake a rayuwata ban ta ba ganin
irin wadannan dara daran idanuwan ba masu
tsananin haske daga ciki, da bakar kwayar ido
mai tsananin baki, aka zagaye idon da wasu
gashin ido da gashin gira masu yawa da
tsananin baki, ya gyara su sunyi kira mai kyau
suna sheki. A nutse ya waiwayo da kyakkyawar
fuskarsa gaba daya ya dube mu, bani kadai ba
duk wata 'ya mace da take wajen sai dataji a
ranta dama ace wannan kadarar mallakarta ce.
'Yan uwansa maza ma sai da suka raya a
ransu dama ace sune shi, ga kyau ga ilimi.
Ashe a da dana ke hango gefen fuskarshi ban
hango komai ba, kyau mai sunan kyau sai ka
kalle shi gaba dayansa daga kafarsa zuwa
kansa. Dogon mutum ne sosai ma kyawun
sura, bashi da kiba da yawa, haka bashi da
rama. Yayi kama da irin bakaken turawan nan
da ake kira african American, hukuncin da na
yanke masa kenan dan ko kusa baiyi kama da
'yan nigeria ba! Tabbas ruwa biyu ne suka
hadu suka same shi bakar fata da farar fata.
Duk da tashin hankalin da na shiga da naji
bayananta sai nayi murmushin karfin hali nace
subhanallah! Bai kamata kice zaki bi kowacce
hanya ba gara ma kice zaki bishi da addua in
da alkhairi Allah ya yi. Khadija tace bawai ina
nufin zan fita daga musulunci ba akansa ba,
amma fa dole saina saka malamaina sunyi min
addua. Na fahimci maryam ahmed da mansura
mahmud suna sonsa kin san su da bin
malamai, in ban dage ba sai sun janye
hankalinsa. Gaskiya tunda nake a duniya ban
taba ganin Kyakkyawan bakar fata irinsa ba, ko
kin taba gani? Na girgiza kai nace ban taba
gani ba, amma shima yana ji da kansa dan
yasan ya hadu kuma mata suna nuna masa
haka. Ba kya ganin 'yan matan nan medical
student suna ta kawo hare harens garshi?
Khadija tace tabbas na gani, shiyasa nace sai
nayi da gaske fa. Ai mu uku ne kadai muka
amayar da maitarmu a waje, nasan mata da
yawa sun dasa a ajin fada ne kawai basu yi ba.
Kin burge ni aisha umar, sai naga kwata kwata
ba ya gabanki, ko a bayan idonki muna yabonki
don kina kama kanki bakya shiga rigimar da
tafi karfinki. Sai kawai nayi murmushi nace a
raina kallon kitse kike yiwa rogo, aini zuciyata
tuni ta kunsa min abinda zuciyoyinku basu
kunsa muku ba. Tabbas nasan burina da fatana
akan dr shurain yafi nasu. Aisha umar kalli
motar can, inji khadija yayin da ta matse 'yan
yatsunna don gigicewa. Na juya da sauri, sai
naga wata dankareriyar mota baka mai farin
gilashi. A cikin motar kuma zankadeden mutum
ne, sanye da farar riga da bakin gilashi a
fuskarsa. Ya kalle mu, muma kallonsa mukayi
sai ya kawar da kai ya fisgi motarsa da gudu
ya nufi gate din fita. Na dubi motar har da
waiwaye sannan na juyo na dubi khadija nace
motar nan ta hadu, haka mutumin da yake
cikin motar ma ya hadu. Wanene shi? Tace au
baki gane shi bane? Dr shuraim ne likitan da
muke zancensa yanzu. Dan halak yaki ambato.
Sai nace kai bashi bane, ai shi bakar suit ya
saka. Tace bakar ta saman ya cire, ya bar
farar ta ciki. Baki shaida jan neck tie din bane?
Sai nayi shiru saboda haduwarsa tafi karfin
tunanina, sama ta yiwa yaro nusa ba zai iya
tabawa ba sai dai ya daga ido ya hango. Sai
na tuna ai Allah ne ya halicce shi wanda ya
halicce ni, babu wanda yafi wani a wajensa sai
wanda yafi bauta masa don haka na daina
raina kaina. Na kudira a raina zan sake rikar
addinina yadda zan sami babban rabo a lahira,
koda kuwa ban sami wanda nake so a duniya
ba. Zuciya ta fara warwarewa daga kuncin
daya damke ta na son maso wani. Tun ina
sauraron surutun da khadija takeyi har na
daina ganewa, burina kawai in ganni a gida na
shige lungun dakina. Ina hau yamutsattsiyar
tabarmata in kudindina inyi ta aiyano ni tare da
abin kauna ta shuraim. Ina daukar jakata sai
nayi musu sallama na nufi gate din fita a
sanyaye ina tafe ina tunani. Na fita waje na
tsayar da acaba kamar kullum na haye ya kai
ni kofar gidanmu. Tun daga zauren gidanmu
nake cin karo da matan gidan suna ta
hidindimunsu na saye da sayarwa da surutin da
suke yini suna yi, ayi gulmar wannan, a zagi
waccan, yau sai suka ganni ba kamar kullum
ba. Da bayan na gaishe su sai in dan zauna ayi
barkwanci sannan in wuce cikin gida, yau babu
kanta da kyar nake magana, sauri kawai nake
yi in shige ciki. Sunyi zaton yunwa nakeji, har
suke zolayata da cewa abida ba ta nan, ba'ayi
abinci ba. Na wuce abu na, na iske abida tana
dafa a binci a risho. Tana ganina tayi kasake
tana kallona, ta san akwai damuwa tunda bata
jiyo muryata ba, bata gano murmushina ba
saboda ina da yawan dariya. Ta dube ni tace
aisha farida kalau kuwa, ko allura zakiyi wata
mara lafiya ta kwace ta tsira miki? Nayi dariya
nace haba dai ayi haka kuwa? Bana jin dadi
dai. Tace Allah ya sawake, shiga daki kihuta
kafin abinci ya dahu ki ci zaki murmure. Ina
shiga daki na cire uniform dina sai na daura
tawul na dauki kwandon wanka zan je in watsa
ruwa dan inji dan sanyi a jikina saboda na
kwaso rana.sai na ga abida ta shigo tana
dariya tace da ni "af ashe wanka zaki yi da
labari zan baki mai dadi kuma marar dadi." Na
ajiye kwandon wanka na jawo hannunta muka
zauna.Na ce bani in sha ai na fasa wanakan,me
ya faru? Ta yi dariya tace labarin musbahu
tsohon saurayinki da matarsa lubabatu zan
baki daman,aure dai yaki dadi har ya yi mata
saki daya dazun nan aka yi rigimar. Lungun
nan ya cika da mutane mahaifiyarsa dai sai a
taya ta da addua don ta cika naci,ce masa tayi
idan ya sake furta kalmar saki sai ta tsine
masa dole sai ya zauna da lubabatu tasan
akan aisha farida yake yi mata wulaqanci kala-
kala. Tayi rantsuwa tace ko bayan ranta idan
ya saki lubabtu ya aure ki Allah ya isa. Kin ji
wata kiyayya sabuwa ko? Na yi murmushin
karfin hali nace,Allah ya kyauta,ta ma daina
kokarin tsinewa danta a kaina tuntuni na yi
masa sallama nace ya bi mahaifiyarsa don ya
sami rahama. Ya na aiko min da kudi tun ina
karba sai na daina karba daga baya idan ya
aiko sai in mayar da dan aiken in ce bana so
don zaman lafiya. Abida tace haka ya fi,ai gara
da kika yi. Masa haka kin taimake shi. Ni na
dauka ma zancen kika ji tun daga zaure da na
ga kin shigo ranki a bace. Amma fa ki godewa
Allah AF saboda kin samu kyakkyawon yabo a
ung nan. Ba kiji. Yadda kowa yake yabonki
ba,ake ta tsine mata ita kuma. Kowa ya dinga
cewa me ye laifin AF har da bata so danta ya
aura? Yarinya mai nutsuwa da hankali mai ilimi
da fara'a tana gaishe da mutane. Ta zo ta
tauyewa yaro rayuwarsa ta cusa masa
dakalkalalliyar macen da ba ta da tsari. Nace
au daman an sanni da yawa a ung nan haka?
Abida tace "ji ki da Allah da neman magana
waye bai sanki ba,musamman da kika shiga
skul of nursing kina karbar haihuwa kina allura
a cikin ung sai ki ji kowacce mata tana cewa
wajen aisha likita zan je ta rubuta min magani.
A nan dai muka tashi muka rufe hirar nan
zuciyata cike da tausayin musbahu ba don
mahaifiyarsa ba ta sona ba da na aure shi mun
zauna mun rufawa juna asiri,in huta fadawa
cikin hatsarin da nake shirin jefa kaina. Bayan
na yi wanka na ci abinci sai na wartsake na
shiga cikin matan gidan muna ta hira har ma
na ji na fara mantawa da abunda yake damuna
a zuciyata. Sai da kowa ya shiga barci dare ya
fara nisawa sai tunanin Dr shureim imran yace
da wa Allah ya hada ni in ba da ke ba,sai na ji
gaba daya daya zuciyata ta kasa sukuni. Da
zarar na rufe ido sai in ganshi tamkar a zahiri.
Sai na yi ta yaki da zuciyata ina ture shi daga
tunanina.kai in takaice maka a cikin satin nan
ban gane kaina da kaina saboda tsananin
tunaninsa. Idan na je asibiti bana walwala haka
idan na dawo gida ba na jin dadin zuciyata
kada ma dare ya ji labari sai ka ga idona ya
wartsake garau na burma tunanin DR shureim
imran. Da gaske sonsa nake,so ba da wasa
ba.tun ranar kuma ban sake ganinsa ba sai dai
kullum sai khadija ta yi min labarinsa.Albishir
din da ta yi min shi ne ta sami lambar wayarsa
amma tana tsoron kira don tana ganin zai yi
mata wulaqanci. Ta shaida min ta rabawa
malamai kudi ana ta ragargaza mata addu'a ta
koina,a kalla ta raba musu zunzurutun kudi ya
kai N25,000 so take sai an gama addua tas
sannan ta kira shi dolensa ya amince. Sai na
sake jin jikina ya yi sanyi na sake yi wa
zuciyata fada da ta yi ta- ka tsan- tsan ta
daina cusa abunda zai iya kasheta.idan da
khadija. Zata lura duk sanda ta fara yi min
zancen Dr shureim sai jikin yayi sanyi kuma na
kan rasa amsar da zan bata ko shwara.
Kallonta kawai nake tsayawa ina yi yayin da
zata iya ganin hawaye yana cika min ido sai
inyi sauri in mayar da shi ina tauisayinta na fi
tausayin kaina domin na san zuciyata ta fi tata
shiha hatsari kuma ta fini sanin yadda zata yi
da kanta. Ni ko wayar ma bani da ita babu
kudin saka kati balle in saka rai ko zan karbi
lambar in kira inji dadi. Na zama na rasa
walwala ta ko abincin kirki bana iya ci na
dukufa da adduar Allah ya yaye min don sonsa
ya zame min ciwo.naji duk na tsani kaina karfi
da yaji nake fisge tunaninsa daga cikin
zuciyata.amma abu ya ci tura sai ma karuwa
yake yi. Idan naki tunaninsa karfi da yaji a ido
biyu da zarar na kwanta sai nayi mafarkinsa,
sai gani cikin dare ina kuka wiwi ina sallah da
adduar Allah Ya yaye min, Allah Ya kawo abin
da zai sa inji na tsane shi ma. Duk satittikan
nan da nayi ina jinyar sonsa ko a hanya ban
hadu dashi ba balle ma in ji dan sanyi a raina,
ina so ina kara ganin suffarsa don in kawata
tunanina domin kamanninsa suna kokarin
disashe min. Ranar talata da sassafe ina
dirowa daga kan acaba a kofar shiga gate din
asibitin aminu kano sai na yi kicibus dashi a
cikin wannan tsaleliyar motar tasa. Na
waiwaya da sauri na dube shi yayin da shi ma
yake dubana har da rage tafiya amma fa duban
da yake yi min bana kauna bane, hararata yake
yi game da nuna tsana mai yawa a bayyane.
Sai yayi tsaki ya girgiza kai ya kada sitiyarin
motarsa yayi wucewarsa. Sai na dankare a
tsaye ni ban ciro kudin mai acaba na biya shi
ba, ni banyi gaba ba balle ace mantuwa nayi.
Bani kudin mana, inji zalamamman dan acba.
Na ciro kudin na mika masa ya karba yana
shirin ya miko min canjina naira ashirin sai na
girgiza kai nace kayi min sadaka, ku taya ni
addua don bani da lafiya. Sai ya tsaya yana
kallona cike da tausayi yace to ko gida za a
mayar dake idan ba zaki iya aikin ba? Ai komai
sai da lafiya akeyi. Nayi murmushin karfin hali
nace ciwona addua yake bukata ba hutu ba, ko
shan magani. Sannan maganin ciwon yana
cikin asibitin nan, idan na koma gida ai babu
maganin a can. Yace gaskiya ne duk wani
magani yana asibiti. Allah Ya yaye miki
kowanne irin ciwo ne wannan. Na amsa da
amin nagode. Na juya a sanyaye ina tafiya
kamar kwai ya fashe min a ciki. Ina mai
matukar mamaki da takaicin kallon wulakancin
da yayi min. Na kasa tantance ni kuwa laifin
me nayi masa a rayuwata da ya tsane ni,
yaushe ma ya taba ganina banda sau daya
shima a rubibi, yaushe zai ganeni? Aisha farida
umar, karaf naji an kira sunana daga gefena.
Nayi firgigit na juyo da sauri. Khadija sani
ismail na gani ta tsaya da motarta hience 2008
ta sauke gilashin wundonta kasa, na tsallako
inda take na bude gaban motar na shiga. Ina
kokarin gaishe ta sai ta katse ni cikin murna
take magana tace albishirinki? Na kira Dr
shuraim imran jiya ya dauka, sai dai mun fara
magana yace in bashi bane wanda nake newa
wrong number ce, ya katse wayar. Sai na tura
masa sako nace ni dalibarsa ce , na kira in
gaishe shi. Kinga amsar daya bani. Sai ta miko
min wayarta, sai hannuna ya hau kakkarwa,
har sai da ta tsaya tana kallona saboda gaba
daya jikina bari yake yi. Na duba na karanta
sai naga ya runuta "thanks". Sai na lumshe ido
don dadin ganin rubutunsa da lambarsa, naji
dama nice nake yi masa waya da tura sako da
ko amsar da ya bawa khadija na samu ya bani
kadai na gama jin dadin rayuwata, ta isheni
abin farin ciki. Na bude baki nayi magana da
kyar, nace lallai kinji dadi. Tace dadi ka-n jiya
ai jar da barci da munshari don samun
kwanciyar hankalin dana ji. Dole in karawa
malamaina kudi su sake dagewa da addua
sosai. Nayi ajiyar zuciya nace ya san sunanki?
Tace bai tambaye niba, ki kyale shi sai a
hankali, dan wulakanci ne fa wannan da kike
gani. Muka isa bangaren da muke,mun bar
bangaren masu kuraje mun koma bangaren
yara. Muna shiga ciki muka iske 'yan ajinmu a
tsaitsaye kowannensu da dan littafinsa a hannu
da biro, da alama matron ta fara bayani akan
wannan yaro mai ciwon amai da gudawa. A
tsaye nake ina kallon bakin yaron a hannun
mahaifiyarsa yana tsala kuka, amma ban
fahimci bayanan matron ba, ko kadan ban san
me take cewa ba. Tunanina kawai daman ace
dana ne wannan jaririn muka haifa tare da Dr
shureim imran. Sai da ta gama bayani ta juya,
naga an bi ta duuu a baya zuwa gadon wani
yaron marar lafiya, shi kuma mai ciwon
pneumonia ne, sai na ja birki na tsaya cak na
ki bin su saboda kafafuwana da kwakwalwata
sun gaji ba zasu iya daukar abubuwa guda biyu
ba, tunanin dr shuraim imran shi yafi matsa
min, gara in yi shi shi kadai, shi yafi
muhimmanci a gareni don haka na juya na nufi
ofishinmu inda muke zama mu huta da ajiye
jakunkunan mu. Ina shiga sai naga maryam
ahmad tayi kasake a zaune akan kujera tana
matsa wayarta, fuskarta babu walwala. Nayi
mata magana sai naji da kyar take amsa min.
Na tambaya cikin damuwa maryam lafiya? Me
ke damunki? Baki da lafiya ne. Ta girgiza kai
tace lafiya kalau. Ni dai na dame ta da
tambaya lallai sai ta fada min abin dake
damunta. Ko a mafarki ban zata amsar da zata
bani ba kenan. Budar bakin ta ke da wuya tace
waye inba dr shureim ba? Sai naji gabana ya
fadi daf! Na fada a gigice me yayi miki? Sai ta
dube ni kwalla ta cika mata ido tace aisha
farida na yarda dake shi yasa zan fada miki
sirrina, na san kina da rike sirrin jama'a ba
ataba fada miki magana kin yada ba, na san
zaki bani shawarar da ta dace. Ina matukar
son dr shureim imran, har zuciyata sai naga da
in tsaya labe labe shi ma mutum ne kamar ni,
me zai hana in tunkare shi in fada maas tunda
ni bazawara ce, kunyar me zanji? Duk inda
mace ta kai na kai, ina da kyauna da ilimina da
arzikina, gani 'yar asali karewa ma 'yar
sarauta. Dazun nan na tare shi a bakin ofis
dinsa yana ganina ya bata rai na gaishe shi ya
amsa da kyar, ya bude kofar ofis dinsa ya shiga
sai na bi bayansa. Muna shiga sai ya daka min
tsawa yace lafiya? Nace nazo in gaishe shi ne.
Ya fada a fusace yace to naji sai anjima. Nace
kuma ina da magana da nake tafe da ita. Sai
yace fadi maganarki ki fita. Nace so nake mu
saba in karbi lambarka, ka karbi tawa. Ko rufe
bakina banyi ba yace bana bukatar in saba da
ke, haka bana son lambarki, sai anjima. Sai ta
fashe da kuka ta rungumeni. Bansan sanda na
dora hannu aka ba nace mun shiga uku, Allah
Ya jikaina. Maryam ta dago cike da mamaki
tace aisha farida menene? Nayi sauri na gyara
zancen nace ai da kika fada min abin da yayi
miki sai naji kama zan hadiyi zuciya in mutu,
shine nace Allah yaji kaina. Tace meye
shawararki? Shawarar da na ba wa kaina ita
nake kokarin in bata, itace tayi hakuri ta rabu
dashi, taci gaba da addua. Allah ya yaye mata
sonsa ya hadata da mai sonta wanda yafi shi.
Sai tace a'a ai ba isa ba, sai ya san ita yayi
ma wulakanci. Ai ko zata salwantar da
dukiyarta kakaf sai ta rama abinda yayi mata.
Sai tayi masa asirin da sai ya kwanta a kasa
ta murje shi da takalmin kafarta. Ban sake
magana ba na tsaya kawai ina kallonta, yayin
da naji tausayinsa ya kama ni, bana so a
wahalar min da abin kaunata. Daga nan na
kara cire ran mafarkin samun dr shuraim imran
a rayuwata. Naci gaba da jinya ina jiran ranar
ajalina domin mutuwata ce kadai zatayi min
maganin ciwon nan. DUK KYAN TAKALMI 7 Sai
ta fashe da kuka ta rungumeni. Bansan sanda
na dora hannu aka ba nace mun shiga uku,
Allah Ya jikaina. Maryam ta dago cike da
mamaki tace aisha farida menene? Nayi sauri
na gyara zancen nace ai da kika fada min abin
da yayi miki sai naji kama zan hadiyi zuciya in
mutu, shine nace Allah yaji kaina. Tace meye
shawararki? Shawarar da na ba wa kaina ita
nake kokarin in bata, itace tayi hakuri ta rabu
dashi, taci gaba da addua. Allah ya yaye mata
sonsa ya hadata da mai sonta wanda yafi shi.
Sai tace a'a ai ba isa ba, sai ya san ita yayi
ma wulakanci. Ai ko zata salwantar da
dukiyarta kakaf sai ta rama abinda yayi mata.
Sai tayi masa asirin da sai ya kwanta a kasa
ta murje shi da takalmin kafarta. Ban sake
magana ba na tsaya kawai ina kallonta, yayin
da naji tausayinsa ya kama ni, bana so a
wahalar min da abin kaunata. Daga nan na
kara cire ran mafarkin samun dr shuraim imran
a rayuwata. Naci gaba da jinya ina jiran ranar
ajalina domin mutuwata ce kadai zatayi min
maganin ciwon nan. Abida ta lura bana cikin
walwata kullum ina cikin damuwa, ta
tambayeni har ta gaji na kasa fada mata
wannan badakalar cutar da zuciyata ke fama
da ita, babu abinda nake boyewa abida amma
wannan dai ba zai fadu ba. Na gwammace a
dauki gawata a dinga tunanin fuju'an na mutu
babu ciwo ni da Ubangijina munsan abinda ya
kashe ni. Sai na shiga tunanin ko shi yasa ya
dinga hararata saboda masu irin uniform dina
ne suke damunsa ya zata nice? Haka ne ma
babu tantama ya dauka khadija da maryam ce
ni. Bansan takamaiman ofis dinsa ba, don haka
kaina tsaye na tunkari ofishin dr lukman likitan
kwakwalwa dauke da file din matron maryam
ta umurce ni da in kai masa. Ofis na uku tace
min daga hannun dama, don haka kaina tsaye
nan na kwankwasa na shiga tun kafin a bani
izini, saboda saurin da nake yi don inyi in koma
wajen daukan darasi. Abin da nagani a cikin
ofishin shi ya firgita ni har sai da kowa ya gane
na tsorata, dr shureim imran na gani a zaune a
kan kujera da laptop dinsa akan table yana
danne danne, maimakon mai ofis din dr
lukman. Wace wannan? Ya kika koma da sauri?
Wa kike nema? Tambayoyin da na jiyo ana yi
min kenan daga cikin ofishin ni kuwa tuni nayi
waje. Na rufo kofar a hankali na fara sanda zan
juya, jikina yana rawa ina gudun wulakancinsa.
Wata murya naji an kira ni, har na kai kan
barandar waje. Ina juyawa naga mai gadi ce
(security). Tace inje inji doctor. Hankalina ya
tashi kan kace kwabo na fara gumi tamkar ana
gasa ni a garwashi. Ofishin dr lukman kuwa ta
nuna amma ban ga kowa a bakin kofar ba,
kuma har yanzu kofar a rufe. Ni kaina ban san
ayoyin da nake karantawa ba har na isa bakin
kofar, na tura kofar na shiga ina mai jan dan
gajeren hijabina ina rufe rabin fuskata. Ina
sauraron yadda Allahi Zaiyi dani kuma. Nayi
sallama na shiga amma na kasa daga ido in
dube shi. Yaya kika leko kika koma? Wannan
karon kuma wata sabuwar murya naji daban ba
irin ta dazu ba, sai na dago ido da sauro na
dube shi. Dr lukman na gani zaune yana danna
laptop dinsa ba dr shureim imran bane. Sai
mamaki ya rufe ni a zahiti har ya fahimci haka,
na tabbatar son dr shureim yayi min yawa da
har ya fara yi min gizau. Nayi murmushi na
dauka ba ofishin na shigo ba shiyasa na juya.
Na matso na mika masa file din yana dubawa
ya girgiza kai yace me yasa matron zatayi min
haka, ni ba wannan nace ta aiko min ba. To
iyakacin kalmar da na fahinta kenan daga nan
na daina sauraronsa saboda dr shureim imran
na gani ya fito daga bandaki da alama alwala
yayi don jikinsa daruwa. Kallo daya nayi masa
na zazzare ido sai na sunkuyar da kai kasa
yayin da jikina ya hau rawa, zuciyata ta hau
tsalle tana oyoyo ga abincin da na dade ina
yunwarsa. Shine ma dai yayi min kallo sau biyu
ya watsar ya shige lungu ya shimfida abin
sallah. Kafin ya tayar da sallah dr lukman ya
tsokano shi da ci gaba da hirar da suke yi.
Yace wato dr shureim ka tsani ka ga 'yan
acaba kenan? Yayi dariya yace yadda naki
mutuwata haka naki inga mutum ya hau acaba
musamman mace ina takaicin wannan abu, sai
inga ba gara mutum yaje ya kwanta a sibiti ba
yace a zuke jininsa gaba daya a rabawa
marasa lafiya saboda ya mutu, gara yace a
yayyanki duk sassan jikinsa a raba sadakatul
jariya. Dr lukman ya kwashe da dariya har da
buga kafa a kasa. Yace haba dai doctor har
abin ya kai haka? Yace haka ne mana, saboda
yadda zaka ga suna kutsawa a jikin tirela. Na
fada maka fa acaba ne ya kashe san uwa na
uwa daya uba daya, kuma ina tsaye ina kallo
ya kutsa dashi karkashin tirela. Daha cewa dan
acaba kai ni can in siyo batir motarmu ta mutu
a hanya, shikenan ya warce shi sai karkashin
tirela sai gawarsu aka kwakulo. Tun daga
lokacin idan naga mutum akan acaba sai kaga
na bar abun da nakeyi na rike kai, ina taya shi
da addua har sai na daina hangensu.
Musamman mace sai inji kamar in fasa ihu ince
ga motarta nan zo ki hau na tafi da kafa.
Wadanne irin maza ne zasu bar matarsu taje
ta hau acaba, ko bashi da mota ai sai ya bata
kudin drop har inda zata je a mota. Sai a
lokacin na tabbatr da dalilin da yasa yake
hararata rannan ashe, don na sauko daga kan
acaba ne. Ya tayar da sallah, dr lukman ya
miko min file biyu da wanda nazo dashi da
wanda yayi cike cike yace in mayar mata ince
bashi ba, koren file din zata bayar. Na durkusa
na karba na fito da sauri, yayin da zuciyata ta
cika da murna saboda yau taga abinda take
muradi. Sai ya sake burge ni dana ga yana
sallah, naji dadi danaji dalilin hararar da yayi
min rannan ba tsana ta yayi ba. Sai na fara
tunanin hanyar da zanbi in shiga harkarsa ba
tare da yayi min wulkanci ba. Naci sa'a kuwa
ina zuwa nayi mata bayani sai ta miko min
koren file din da yace ta bani in kai masa. Na
taho hanya ina farin ciki hade da fargabar abun
da zanje in tarar. Na isa ofishin sai faduwar
gaban da nake ji ta karu, na fara karanta
ADDUAR WANDA YAJI TSORON MUTANE
"Allahummakfinihim bimaa shi'ita" (Ya Allah Ka
isar mini dasu da abin da kaso). Ina tura kai
sai nayi sallama. Dr lukaman ne ya amsa, har
yanzu gogan nawa yana kan abin sallah ya idar
amma yana jan carbi. Na dago ido na dube shi
a hankali, sai muka hada ido ni dashi, bansan
wanda ya fara kawar da kai gefe ba. Na matsa
lungu ina jiran dr lukman ya gama dubawa sai
da na tabbatar lungun da na shige ko ya daga
ido ba zai ganni ba. Na nutsu kai kace a gaban
sarki nake, yadda nake sanda kai kace da
kayan sata aka kamani, za'a yanke min
hukunci. Wayar dr shuraim imran ce take ruri,
kidan ringing tone din yana tashi a hankali,
wakar soyayya ce ta celen dion mai taken come
bake to me, sai ya danna amsa. Kalmar da ya
fara ambato a cikin harshen turanci ita ta
gigitani, tasa na dimauce sai na tsinci kaina
har da kwalla mai radadin fita saboda kishi.
Daga ji ba sai an fada min ba da matarsa yake
magana, wacce yake tsananin so da kauna fiye
da kowacce 'ya mace a duniya. Tunda nake a
rayuwata ban taba jin namijin bahaushe da ya
fadawa matarsa wannan kalma, ko da yake ni
'yar gargajiyace na tashi cikin 'yan gargajiya
tsakanina da matansu sai ke zo nan, dauko,
dafa, wanke, goge. Kullum sai hantara dube ki
ballagaza, kazama, kwadayayyiya. Haka na
saba ji tun tashina tsakanin miji da matarsa.
Amma dr shuraim imran yace da abar
kaunarsa, salam my dear, my heart, my life
how are you and how is your trip? Hope cool.
Duk da ban jiyo abinda zata fada ba itama da
daddadar kalma ta mayar masa. Ya juye
harshe sai turanci yake zazzagowa ya tambaya
kuna ina yanzu? Sai ta bashi amsa, banji
amsar ba sai yace ok kun bar london yanzu
kuna amsterdam? Awa nawa zaku yi transit
din? Ta fada masa, sai yace karfe goma dai dai
zaku iso kano, ni kuma karfe tara a airport zata
yi min da izinin Ubangiji. Ina kewarki, ina
babyna? Can sai naji ya fara magana cikin
muryar yara yana yiwa yaro wasa, sai na
tabbatar 'yarsa ce itama da turancin yake mata
magana. Kalmar da ya fada ta karshe daga ita
ya kashe waya itace "I love u baby, I miss u
too, I am eager to see ur beautiful face. Take
care bye". Na dinga dauki ba dadi da zuciyata
don so take ta tsinko fado kasa ta ragargaje
don tashin hankalin da ta shiga. Dr lukman ya
dube shi yayi dariya yace madam ce? Ya
lumshe ido tace madam ce ita da baby sun
taho yanzu suna amsterdam sun baro london.
Kaji matar da take makaranta shine ta bar
karatunta ta biyo ni. Dr lukman yace ah da
gaskiyarta, yaushe zata zauna a can mijinta
yana nan? Dr shureim imran yace toh ai
matsalar ba zata iya zaman bane a nan, tana
yin sati biyu a daddafe zata fara magiya inzo
mu koma london, ita ba ta zauna tayi karatunta
ba a can, ita bata bar yarinya tayi karatunta
ba. Dr lukman yace ai da ta dinga barin
yarinyar a gidan iyayenta ba suma a london din
ba gidansu yake? Sai iyayenta su rike muku
'yar kai da ita ku karaci walagiginku tsakanin
london da Nigeria. Dr shureim imran yayi dariya
yace toh ai yarinyar harta fi uwar damuwa ai
ita tace take so uwar tace sai an kawo ta ta
ganni, sai tasa uwar tayi min waya fiye da sau
goma a rana ace min ga baby tana kuka, wai
tana son magana dani. Ina daukar wayar kasan
abinda zata ce min? Daddy I miss you, sai ta
kashe waya shikenan. Su dukka suka kwashe
da dariya, dr lukman yace gaskiya ku canza
tsari, ko kai ka hakura da zaman nigeria ka
koma can ku zauna, daman a can kuka hadu.
Dr shureim imran ya rike baki yace cafdi! Ai ba
zai yiwu ba, ka manta halin babana ai ba zai
bari inyi aiki a can ba, kasan shi da kishin
kasar nan, babu dansa da bai dawo nigeria ba
yanzu. Karatu kadai ya amince muje muyi, aiki
kuwa dole mu dawo mu bautawa kasarmu, mu
taimaki alummar hausa, fulani, musulmai 'yan
uwanmu, bai damu da yawan albashin can ba.
Dr lukman yace haka ka fada min, gaskiya ya
burge ni. Ina ma za'a sami dattijan arewa
irinsa masu kishin YARENSU DA ADDININSU da
kasar nan, da kasar nan ta gyaru. Dr shureinm
yace ai kuwa sanda zanyi aure hana ni yaso yi,
dana dage ina so ni da ita ya shimfida mana
sharudda masu tsauri. Tace taji ta gani zata bi
duk abinda yace. Sharadi na farko da ya
shimfida mana shine dole ta biyo ni nigeria mu
zauna dindindin idan munje london hutu muka
yi da zarar hutu ya kare mu dawo. Sannan dole
ta bar shigar dan siket da wando ta saka
atamfa ko leshi da mayafi don shi ya tsani
english wears. Tace ta yarda yanzu ma zaman
da ya bari tana yi na dan shekaru ne saboda
karatu, ta kusa kare makarantar da zarar ta
kare yace ta hado kayanta kakaf ta kaura kasar
nan, dole anan kasar zatayi aiki ba a can ba.
Tags :
Itama kuma bata iya zaman kasar na, tsoron
sauro takeyi, ko kuda ta gani sai ta hau kuka
ta tashi da gudu. Baby kuwa tana burge ni
babu abinda ba taci, kuma babu in da bata
shiga ta zauna lafiya a kasar nan, bata
damuwa da duk wani canji kuma itama a can
aka haifeta kamar yadda aka haifi uwar a can.
Dr lukman yayi dariya yace ah wannan ita ta
biyo kakanta alhaji, komansu na gargajiya ,
babu zancen cewa ma kai ta biyo, don kai ma
bature ne. Dr shureim imran yace ai kuwa baka
san bature ba, ai ni ko a gidanmu sun san nina
biyo alhaji sak, saboda ko wajen abinci bana
cin su shinkafa, taliya , cake, macaroni da
sauransu. Idan aka ga naci irin wadannan toh
a london nake, ko abj don babu yadda zanyi.
Nifa har kwano nake bawa direbana ya dauka
ya tafi cikin gari unguwar su wani abokina
neman danwake, dambu, ko gurasa mai
kulikuli. Dr lukman ya kwace da dariya yace har
da yawon neman dambu kake sawa ayi? Lallai
dagaske kake. Ni kuma abinda ba'aci kenan a
gidana ko tuwo zasu yi sai dai suyi min
abincina daban, haba ai an wuce wannan
lokacin ina yaro in nadi dambu da tuwo, yanzu
da wayona da 'yan canjina a aljihi inci dambu?
Ko ba haka ba 'yar boko, har yanzu kina cin
dambu? Ya tambayeni, sai nayi sauri na dubi
dodona dr shuriem, domin shi nake tsoro.
Gogan nawa sai yayi dif bai sake magana ba,
yaji an dako dani a zancensu. Jikina ya sake
yin sanyi, nayi murmushi nace bana cin dambu
nima. Dr lukman yace yawwa ashe bani kadai
ne na gaji da cin tuwo ba, muna da yawa.
Daga lokacin hirar ya koma ni da dr lukman
kadai, dr shureim yaki tsoma baki. Dr lukman
yace dani ke 'yar gidan matron maryam ce,
naga kuna kama? Wannan karon ne ma naga
dr shureim ya dubeni kasa kasa, sai yayi wuf
ya mike tsaye yana nade abin sallah, ya linke
ya ajiye sannan ya shiga daura neck tie a
wuya, ya saka bakar suit dinsa. Cikin sanyi jiki
nace a'a ni ba 'yarta bace, malamata ce kawai,
muna shiri sosai. Dr lukman yaci gaba da
rubutu yana magana yace ke ba 'yar gezawa
bace kenan. Tunda matron maryam 'yar
gezawa ce. Nayi dariya nace a'a ni ba 'yar
kano nace ba ma, ni 'yar shagamu ce. Sai ya
tsaya da rubutun ya dube ni ta cikin gilashinsa
yace da gaske kike, ko kanwar yahaya umar
ce? Babban abokina ne, ajinmu daya a
sakandiren da muka yi a yobe. Sai nayi caraf
nace yayana ne, babanmu daya. Sai ya fasa
rubutun ya ajiye biro yace yanzu dan Allah
yahaya umar yayanki ne? Na gyada kai nace
yayana ne. Yace llallai kuwa naga kama, kina
cewa ke 'yar shagamu ce sai naga fuskarku iri
daya daman tun sanda na fara ganinki na rasa
wanda kika min kama. Yana ina yanzu? Yana
nan lagos yana aiki a tasha dan union ne. Yace
subhanallah! Yanzu duk kokarin nan na yahaya
umar bai cigaba da karatu ba a aikin tasha ya
kare? Kinsan fa ni dashi muka kudiri niyyar sai
munyi karatun likita. Tunda muka gama
makaranta a. Yobe na dai ganinsa, naje
gidansu a nan yobe nemansa ban same shi ba
aka ce ya koma garin babansu shagamu, ashe
dangin mahaifiyarsa ne a yobe ko? Shikenan
rabuwarmu dashi, sai dai duk sanda aka
ambaci shagamu sai na tuno shi, saboda dan
shagamu muke ce masa. Mun shaku sosai
dakinmu daya, ajinmu daya. Nayi murmushi
nace eh dangin mahaifiyarsa ne suka rike shi a
yobe, tun yana yaro, daya gama sakandire sai
ya koma gida shagamu, bai cigaba da karatu
ba kuma. Ina rufe bakin dr shureim ya shirya
tsafa, ya dauki jakar laptop dinsa ya dubi
abokinsa dr lukman. Yace ni na tafi sai kuma
gobe. Dr lukman yace aini ma na tashi, ka jira
ni yarinyar nan zan sallama kawai, ka ga ashe
ma ni kanwata ce, haba tun sanda nake
ganinta nake ganin kamar na san fuskar, ashe
kanwar abokina ne childhood frnd yahaya umar.
Ya tabe baki yace a'a ni dai nayi gaba, sai ka
taho kawai. Ya fice ya bar mu. Bai ma bada
amsar labarin da ya bashi ba saboda a kaina
ne ba zai tsoma baki ba, sai na fara dankarawa
zuciyata zagi akan ko taki ko taso sai ta rabu
da son wannan marar mutuncin. Me yayi zafi?
Dan kawai Allah yayi masa baiwa kala kala,
yayi masa farin jini, ana sonsa sai ya dinga
wulakanci, shi waye? Namiji ne fa kamar
kowanne namiji, gasu nan birjik a titi suna bin
mace tana musu yanga kafin ma ta kula su.
Suna 'yar murya suna yi mata wahala, don ta
saurare su. Haka na dinga kushe shi a zuciyata
don in samu sukuni, duk yadda zanbi in raba
zuciyata da sonsa bi nake yi don shine samun
saukina. Dr lukman ya rufe file ya bani,
tambayi lambar wayar abokinsa yayana yahaya.
Nace bani da waya, amma zan karbo masa
lambar a wajen yayana hussaini gobe zan kawo
masa. Sai yayi mamaki don nace bani da waya,
sai ya tambaye ni, yace faduwa wayar taki tayi
ne? Kuma baki hadda ce lambarsa ba? Na
amsa da eh faduwa tayi. Saboda sauri nake in
fice daga ofishin saboda abin kaunata baya
nan, daman saboda shi naji tsayuwar da nake
yi bata isheni ba tun dazu, yana barin ofishin
sai naji duk ofis din ya gindure ni. So nake in
fito inga in daya nufa, kuma da wacce irin mota
yazo yau. Nayi wa dr lukman sallama na fito
bakin barandar da sauri, na waiga kowacce
kusurwa sai ban ganshi ba, ko alamunsa babu,
sai naji haushin dr lukman ya rufe ni, da bai
bari na fito da wuri ba, gashi nan har ya tafi.
Sai zuciyata tace ke da kike yi min fada in rabu
dashi, ina ke ina takaicin don baki gan shi ba?
Nayi ajiyar zuciya mai karfi naci gaba da tafiya
maimakon inbi doguwar baranda sai na sauko
na dinga kutsawa ta kasa cikin motoci. Ban sa
ran ganinsa ba ko kadan amma dai nasan dole
ta nan ya bi, idan zai dauki motarsa ko sawun
takalmansa na taka ai naji sa'ida a raina.
Kamar daga sama naji wata murya mai shige
da tasa daga gefena, abin da yake fada kuwa
shine "wait, wait dr hidaya, na fada miki na
sake fada miki don Allah ki daina damuna da
waya cikin dare, yau matata zata zo kasar na,
bana so ki jawo mana matsala. Aiki ne ya hada
mu anan idan an tashi daga aiki to ban sanki
ba kowa ya kama gabansa. Wanne irin abu ne
haka, ina zan saka raina? A asibiti a dame ni
har gida ma kun fara bina? Yaya akayi kika
nemo gidanmu har kika ba mai gadinmu sako
ya bani? A wanne dalile zakiyi min sayayya ki
kai min gida? Zaki jefa rayuwata cikin damuwa
tsakanina da matata, da kuma iyayena. Na
dinga tafiya a hankali ina kallonsu, a tsaye suke
a jikin motarsa har ya bude mota zai shiga sai
ta tsayar dashi. Ransa a bace yake magana
cikin matsanancin fushi, sai ita ma ta fusata ta
magana cikin kuka da fada. Dr shureim in har
ni 'yar halak ce a cikin uwata da ubana na
kyale ka, har abada ba zan sake nemanka ba.
Ya fada cike da gadara yace shi yafi sauki, naji
dadi sosai kuwa. Ta juya a fusace tana sharce
hawaye, yayin da farin gilashin idonta ya fado
kasa, ido daya ya fita. Na karaso da sauri na
dauko mata na mika mata, sai ta dube ni
jajayen idanuwanta ta karba gami da ce min
thank u very much. Ta wuce da sauri. Dr
shureim ya dube ni, ya sake bude ido ya kalle
ni sosai, na tsaya cak kamar yadda yake tsaye
kyam yana dubana. Na harare shi sama da
kasa naja dogon tsaki na kada kai na wuce na
bar shi nan a tsaye bai daina kallona ba, ni dai
ban waiwaya ba. Na san ya cika da mamakina,
ni dai burina ya cika tunda na fara ramawa
kaina wulakacin da yayi min da sauran
wahallalun mata da 'yan uwana masu sonsa.
Na kudiri aniyar kallon arziki ya daina hada mu
sabida na san ba zan same shi ba kamar
sauran da suka fini haduwa, ga kyau basu
same shi ba. Kamar daga sama naji wata
murya mai shige da tasa daga gefena, abin da
yake fada kuwa shine "wait, wait dr hidaya, na
fada miki na sake fada miki don Allah ki daina
damuna da waya cikin dare, yau matata zata
zo kasar na, bana so ki jawo mana matsala.
Aiki ne ya hada mu anan idan an tashi daga
aiki to ban sanki ba kowa ya kama gabansa.
Wanne irin abu ne haka, ina zan saka raina? A
asibiti a dame ni har gida ma kun fara bina?
Yaya akayi kika nemo gidanmu har kika ba mai
gadinmu sako ya bani? A wanne dalile zakiyi
min sayayya ki kai min gida? Zaki jefa
rayuwata cikin damuwa tsakanina da matata,
da kuma iyayena. Na dinga tafiya a hankali ina
kallonsu, a tsaye suke a jikin motarsa har ya
bude mota zai shiga sai ta tsayar dashi. Ransa
a bace yake magana cikin matsanancin fushi,
sai ita ma ta fusata ta magana cikin kuka da
fada. Dr shureim in har ni 'yar halak ce a cikin
uwata da ubana na kyale ka, har abada ba zan
sake nemanka ba. Ya fada cike da gadara yace
shi yafi sauki, naji dadi sosai kuwa. Ta juya a
fusace tana sharce hawaye, yayin da farin
gilashin idonta ya fado kasa, ido daya ya fita.
Na karaso da sauri na dauko mata na mika
mata, sai ta dube ni jajayen idanuwanta ta
karba gami da ce min thank u very much. Ta
wuce da sauri. Dr shureim ya dube ni, ya sake
bude ido ya kalle ni sosai, na tsaya cak kamar
yadda yake tsaye kyam yana dubana. Na
harare shi sama da kasa naja dogon tsaki na
kada kai na wuce na bar shi nan a tsaye bai
daina kallona ba, ni dai ban waiwaya ba. Na
san ya cika da mamakina, ni dai burina ya cika
tunda na fara ramawa kaina wulakacin da yayi
min da sauran wahallalun mata da 'yan uwana
masu sonsa. Na kudiri aniyar kallon arziki ya
daina hada mu sabida na san ba zan same shi
ba kamar sauran da suka fini haduwa, ga kyau
basu same shi ba. Da na koma gida, dare yayi
sai bacci ya gagare ni, na shifa zulumi da
fargabar kallon da nyi masa. Naji kwata kwata
ban kyauta ba, tausayinsa ya rufe ni, yayin da
sabon sonsa ya tsatsafo daga cikin zuciyata.
Na dora hannu aka ina fadinn na kashe kaina
da kaina, me ya kaini yi masa wulakanci ni da
nake addua, ina saka ran zan same shi
watarana? Na shiga adduar Allah Ya sa baiji
haushina ba. Gari na wayewa na shiga
shiryawa, na tsaya na tsarawa fusakata
kwalliya yadda zanyi kyau sosai. Nayi sauri na
tare yaya hussaini zai fita aiki, nace ya bani
lambar yaya yahaya wani abokinsa likita ne ta
ke nema. Naci sa'a ya rubuta min akan wata
'yar takarda anan take ya miko min, ko karya
kumallo ban tsaya na yi ba, na fice. Allah cikin
ikonSa ina sauke kafata daya daga kan acaba
ko dayar ban sauke ba a bakin gate din asibiti,
sai ga dr shurim ya karyo zai shiga gate. Ya
galla min harara sannan ya figi motarsa ya
wuce, sai naji dariya ta subuce min, nasan
dalilin hararar da yake min bai wuce don na
hau acaba ba, ni kuwa ko a jikina. Acaba kuwa
yanzu na fara hawa tunda ya tsani yaga mace
akan acaba. Idan baya so mu hau sai ya saya
mana motar hawa ni da 'yanuwana mata masu
hawa acaba. Sai na tsinci kaina ina tafe ina
farin ciki, ko babu komai dai yanzu ya fara
sanina, hararar dana samu ma naji dadi, nafi
wadanda bai san suna raye ba. Kai tsaye
ofishinsu na bishi, kafin in isa har ya kai cikin
ofis. Ina murda kofa sai ta wangale sai gani
kicibus gabansa, bai amsa sallamata ba sosai a
ciki ciki ya amsa kamar baya so, kallo daya
yayi min ya dauke kai yaci gaba da dube duben
littafin da yake kan teburinsa , yana tsaye. Na
gaishe shi yayi kamar baiji ba, na fada cike da
gatsali dr lukman nake nema. Ya fada cike da
takaici, kuma aka ce miki nan ne ofishinsa ko?
Na fada cikin tsiwa eh a nan na ganshi jiya shi
yasa yau nazo nan nemansa. Sai ya dago da
sauri ya dubeni cike da mamaki. Can ya dukar
da idonsa kasa, yaci gaba da dube dubensa, bai
bani amsa ba. Na rike kugu nace ga sakonsa
dan Allah ko zaka ajiye masa? Ya sake dagowa
a fusace ya fada cikin fushi, ke an fada miki
nan ba ofishinsa bane, kije ki tambayi inda ofis
dinsa yake. Ko nayi miki kama da wanda zaki
bawa sako? Na murguda baki nace saboda nan
matron maryam tace min inzo in same shi jiya
shiyasa yau ma nazo. Na juya a fusace na fice
na ki rufo masa kofar sosai. Sai naga ya biyo
bayana, ya dade a tsaye yana kallona ina tafiya
har na fice daga harabar, na barshi zuciyarsa
cike da takaici. Na fara samun sa'ida a
zuciyata tunda na fara samun damar yin
magana dashi, duk da ba maganar arziki bace.
Dana dawo ofishin da rana, sai na sami dr
lukman a ofishin dr shureim baya nan. Mun
dade muna hira da abokin yayana, naki tafiya
da wuri ina saka ran ko zai dawo sai bai dawo
ba, takaici ya isheni. Na koma gida cike da
tunaninsa da sonsa zokar a cikin zuciyata, ko
rufe idona nayi suffarsa ce ke fado min. Ina
matukar son abinda ba zan samu ba, sai inyi
kuka inyi dariya ni kadai bana mantawa da
addua, ina neman agaji daga wurin Ubangijina.
Nafi adduar Allah Ya yaye min sonsa akan
adduar Allah Ya karkato da tunaninsa kaina,
saboda a ganina shi zaifi yi min sauki duk da
babu abinda ya gagari Allah. Sai inyi ta
shawagina cikin asibiti a satin nan ko Allah zai
sake hada ni da dr shureim, ban ganshi ba ko a
hanya, ni kuma bana so inje ofishinsu saboda
zai gane akwai wani abu a zuciyata. DUK KYAN
TAKALMI 9 Sai dai kash! Na rabu da karatuna
har 'yan ajinmu sun gane hankalina baya kan
abinda ake koya mana, ban ma cika tsayawa a
wajensu ba, bini bini a neme ni a rasa. Nima na
rasa kaina, duk likitan da naga ya wuce da
bakar suit sai na bishi da kallo in zata abin
kaunata ne, sai inga ashe bashi bane, raina
yayi ta baci. Matron maryam ta lura da haka
sai tayi ta tambayata, amsar dai ita ce babu
komai, idan aka dame ni ince bana jin dadin
jikina. Haka ma dai a gida amsar iri daya ce,
data makaranta ga duk wanda ya dame ni da
tambaya. Na zama tababbiya a cikin satin nan
da ban ganshi ba. Addua nake Allah Ya yaye
min amma tamkar sonsa karuwa yake a
zauciya, ban taba sanin haka dacin soyayya
yake ba a rayuwata ko a film da littafi ban taba
ganin irin abin da ya faru dani ba. Haka kawai
na fara son mutumin da bai san inayi ba.
Shiyasa a rayuwa ba a so ka cika baki akan
abu, muddin ka cika baki akan wani abu
tabbas abun nan sai kaga ya same ka. Bazan
manta ba shekaru hudu da suka wuce akwai
wata kawata ummi, ajinmu daya a shekara.
Allah Ya jarrabe ta da son wani malamin mu
mai suna abdul yasar, shima danji da kaine
kamar dr shureim. Duk sanda taje wajensa sai
yayi mata wulakanci ita kuma tazo tana kuka
tana fada min, takaici ya kama ni maimakon in
bata hakuri sai inyi ta zaginta, ina Allah wadari
da halinta. Kullum sai ince mata me akayi aka
yi da namiji? Har zata je yana wulakanta ta,
duk a cikin samarinta ma babu kassararre,
talaka, bakauye ma irinsa, duk sunfi shi
haduwa ta rabu dashi mana. Sai tace min ita
dai shi take so bata son sauran. Kuma taci
gaba da nace masa tanayi masa wahala bayan
mun gama makaranta daga karshe ya aureta.
Ranan wata asabar da hantsi na shirya naci
ado da wata atamfata shudiya, tunda ranar
babu makaranta saina zankadawa yayana da
matarsa karya nace a asibiti ake nemanmu
zamu yiwa yara allurar rigakafi, yayana ya zaro
kudin acaba naira dari biyu kamar yadda ya
saba bani kullum. Na nufi gidan ummi domin
inji hanyar da ta bi ta samu mai gidanta abar
kaunarta abdul yasar. A kofar nasarawa
gidanta yake duk da na dade banje gidan ba,
amma naci sa'a na gane, rabona da gidan tun
ranar da muka kai ta, haka da ta haihu ma a
gidansu muka same ta muka yi mata barka,
'yar unguwar zango ce. Cike da fargaba na
shiga gidan don kada ace min bata nan inyia
asarar kudin babur din da na kashe nazo, ga na
komawa gida. Sai naci karo da maigidanta a
zauren gidan. Nayi sauri na duka na gaishe da
malamina, ya amsa a gaggauce ko kallon kirki
baiyi min ba, da alama dama ya tsane ni.
Nasan dadin soyayya yasa ummi ta zazzage
masa shawarwarin da na sha bata cewar ta
rabu dashi bakauye ne, bai hadu ba. Babu
wanda ya fada min haka, na lura tun a lokacin
bikin yana kula sauran kawayenmu nice kada
baya son yiwa magana. Na wuce cikin gidan
sadan sadan don banga fuskar da zan tambaye
shi tana nan ko bata nan ba. A tsakar gida na
ganta ta buga tagumi da alama akwai damuwa
a tattare da ita. Tana ganina sai ta mike da
sauri ta rungume ni, na dauka dariya takeyi, sai
naga hawaye. Na cika taf! Na tumbatsa da
mamaki na rike ta ina tambayarta ko lafiya?
Taja ni zuwa cikin dakinta muka zauna a gfen
gado tana magana cikin kuka. Tace aisha farida
wulakancin da yassar yake min ya isheni, don
kawai yaga bazan iya rabuwa dashi bane. Nayo
shiru na kasa magana, yayin da na shiga
hankalina na fasa tambayar abin da nazo
tambaya. Ashe har yanzu da sauran rina a
kaba, ko a yanzu na auri dr shureim ashe idan
naje gidan ma wulakanci yana nan zokar.
Zuciyata ta fara yimin fada tana cewa farida ki
yi ta kanki, ki cire son dr shureim imran idan ba
kin zabi ciwon zuciya ya zama ajalinki ba. Na
tambaya cikin sanyin jiki wai ke ummi yaya aka
yi ma tun farko ya amince ya aureki bayan
baya sonki? Tace ashe ba dake muka je ba, da
maijidda lawan mukaje wajen wani malami a
kurna. Sai na dafe kirji na fada a gigice, na
shiga uku ummi! Malami kuma? Ta gyada kai
tace shine yayi min aiki yace dole sai yasar ya
zo ya aure ni ko ba a hayyacinsa ba. Kuma
yazo din ya aure ni, har nake juya shi yadda
nake so, sai bayan da na haihu ban koma ba.
Kinsan ance idan mace ta haihu duk wani sihiri
da tsarin da yake jikinta karyewa yake yi, sai
tayi sabon shiri. Kuma kin san halin malaman
zamanin nan sunfi so ka dauwama kana zuwa
wajensu kana kai musu abin da ka kwakwala
daga wajen mazan, idan ka dauke kafa bayan
bukata ta biya sai su karya maka aikin, komai
sai ya cakude dole sai ka dawo. Sannan yanzu
bani da waya, bama magana dashi ta waya,
daya fada min irin sadakar da zanyi dan duk
ranar laraba yanayi min waya yace nayi
sadakar sukari ko nono na aljanar da take kula
da soyayyar da yasar yake min, kinga na dade
banyi sadakar ba. Hankalina ya tashi, abin da
nake gani a film yazo har gida. Nace ummi
tsafi kenan fa? Tace haba dai tsafi, babban
malami ne fa ya iya jan aya, baki ga matan
manya da masu kudin garin da suke layi a
gidansa ba, talakawa irina kadan ne. Ya iya
aiki fa. Zuciyata ta fara rabuwa gida biyu, inje
ko kar inje? Amma fa jikina bari yake yi, naji
tana ambaton aljana a cikin al'amuran. Daga
karshe zuciyata ta yanke min, kawai inje ni ma
ayi min asirin da dole zaizo ya so ni ko da
daga baya asirin ya karye ai dai naci riba tunda
bani da buri a rayuwata irin in ga na same shi
yayi min magana ma kawai, balle ace yazi
gidanmu har anyi maganar aure dashi, ya aure
ni na tare gidansa, ai ba karamar riba bace a
rayuwata. Kuma idan haka ne in anyi auren ai
sai in ringa komawa wajen malamin ina kara
masa kudi yana cigaba da sona, yana fada min
abinda zan bayar sadaka ina yin sadakar yadda
son ba zai tafi daga zuciyarsa ba. Tunda kafin
lokacin bikin na gama makaranta na fara aiki,
ko da albashina na dinga biyan malam ko bai
bani kudinsa ba. Sai na gyara zama nace ummi
nima fa matsalar da take tafe dani kenan, nima
irin naki ne ta same ni. Allah ya jarrabe ni da
son wani likita a asibitin da nake attachment,
amma fa likitan yafi ni haduwa nesa ba kusa
ba, gashi daji da kai da wulakanci, har yafi
malam yasar dinki. Na rasa yadda za'ayi ya
saurareni ma balle ayi zancen soyayya. Baki ga
yadda hadaddun likitoci mata suke binsa ba
yaki sauraronsu. Kawayena biyu suke yi masa
asiri dan ya sosu amma bai kama shi ba, ina
jin ya shirya kansa asiri baya cinsa. Wani
babban tashin hankali ma yana da mata ina jin
ma baturiya ce a london suka hadu sukayi
aure, ita ma yanaji da ita, nasan ta fini kyau
nesa ba kusa ba. Ya zanyi? Ummi ta daki
kafada ta tace ke dalla wawuya daman ke irin
wannan mutumin kika samu amma zaki bari ya
subuce miki? Lallai kin cika wawuya baki da
wayo. Ai kawai kije a zuba miki aiki tuntuni
zaiji ya tsani baturiya ya biyo ki, balle mai kudi
ne, kina shiga zaki fanshe kudafen da kika
kashe a kansa. Na girgiza kai nace babu
ruwana da taba matarsa, suyi zamansu ni dai
yaso ni kawai, tunda ina sonsa. Idan kuma
akwai abin da malamin zai yi min na daina
sonsa ni nafi son haka, saboda nayi iyakacin
adduar da zanyi don na daina jin sonsa na
kasa dainawa kullum karuwa yake ma. Ummi
tace yaya za'ayi kice a cire miki sonsa ai
shirme kenan. Ace yaji abin da kike ji koma
ince fiye da yadda kike ji don an fi son namiji
yafi na mace sai afi zama lafiya. Ke ban da
abinki wata budurwar ba irin wannan take
nema ba ma ta kai shi wajen malami a rike
mata sai ko ta wanne hali, ko ba komai ai ka
tsira da kudi ko babu soyayyar. Na girgiza kai
nace ai ni ba kudinsa nake so ba, shi nake so.
Ni na yadda ya so ni kada ma yabani kudinsa,
na yarda idan na fara aiki in ciyar da kaina ba
sai ya ciyar dani ba. Ummi ta rike baki tace
Aisha farida haka kike sonsa kamar ki cinye
shi? To ko asiri yayi miki irin wannan son dai
bana lafiya bane. Na girgiza kai nace ko kadan,
Allah ne yayi masa baiwar kyau, ilimi, arziki, da
jan aji dole mata suke sonsa. Shi kansa baya
son haka. Bai ma san inayi ba balle ace shi ma
yana sona har yaje yayi min asiri. Jarraba ce
kawai ta afka min, nima ba don ina so ba, haka
Allah ya tsaro min. Sai na fashe da kuka. Ta
rungume ni tace taso muje in kai wajensa
yanzu, nima daman ina shawarar zuwa yau ko
gobe, al'amarina ya cabe ni da yassar. Na mike
tsaye ina goge hawayena yayin da ita kuma ta
canja kayan jikinta ta saka wata jar atamfa
riga da zani ta goya 'yarta da take barci akan
gado, muka fito ta kullo dakin. Ta leka tayi wa
matar kanin mijinta sallama wacce katanga ce
kadai ta rabu tace da ita zamuje bakin asibiti
zata raka ni inyi sare sare. Muka fito muka
kama hanya tun a hanya na sanar mata ko
kudin mota bani dashi, tace babu komai zata
biya min, gakudin cefanenta nan yau ko
cefanen ma bazatayi ba. Ce masa zatayi dan
aiken ya zubar da markade. Ta juyo ta dube ni
tace to ke yanzu da baki da kudi yaya za'ayi
miki aiki? Dole fa sai kin kashe kudi idan kina
son aiki yace. Tafiya mai nisan gaske mukayi a
motar bus mai zuwa kurna, sai da muka hau
acaba muka niki tafiyar kafa saboda babur ma
ba zai iya shiga lokon ba, wahala iri iri muka
sha kafin muka isa gidan. Nace muje dai muji,
na san yadda zanyi. Sai na fashe da kuka. Ta
rungume ni tace taso muje in kai wajensa
yanzu, nima daman ina shawarar zuwa yau ko
gobe, al'amarina ya cabe ni da yassar. Na mike
tsaye ina goge hawayena yayin da ita kuma ta
canja kayan jikinta ta saka wata jar atamfa
riga da zani ta goya 'yarta da take barci akan
gado, muka fito ta kullo dakin. Ta leka tayi wa
matar kanin mijinta sallama wacce katanga ce
kadai ta rabu tace da ita zamuje bakin asibiti
zata raka ni inyi sare sare. Muka fito muka
kama hanya tun a hanya na sanar mata ko
kudin mota bani dashi, tace babu komai zata
biya min, gakudin cefanenta nan yau ko
cefanen ma bazatayi ba. Ce masa zatayi dan
aiken ya zubar da markade. Ta juyo ta dube ni
tace to ke yanzu da baki da kudi yaya za'ayi
miki aiki? Dole fa sai kin kashe kudi idan kina
son aiki yace. Tafiya mai nisan gaske mukayi a
motar bus mai zuwa kurna, sai da muka hau
acaba muka niki tafiyar kafa saboda babur ma
ba zai iya shiga lokon ba, wahala iri iri muka
sha kafin muka isa gidan. Nace muje dai muji,
na san yadda zanyi. Munci sa'a babu layi
sosai, mun tarar da maza uku a kofar gida,
mata biyu a cikin gida. Muka gaishe su muka
bi layi. Gabana sai faduwa yake tamkar
zuciyata zata fito sarari, sai in zunguri ummi
ince na fasa ta tashi mu tafi. Sai ta mintsine ni
tace ba inda zamu je sai mun shiga. Na daure
har layi yazo kanmu, muka shiga ciki. Daga
sanda naga kasar duba da dogon carbi sai na
tabbatar na kauce hanya, domin nasan
makomar masu bin 'yan tsubbu masu duba, in
har kaje wajen mai duba ya fada maka gaibu
ka yarda dashi, to baka da sallah har tsawon
kwanaki arbain. Allah ba zai karba ba. Ya san
ummi sosai, ya san matsalolinta don haka sai
ya hau mata bayani. Tace malam a bincika min
dai. Sai ya jawo farantin kasa yayi zane
zanensa ya hau yi mata bayanai kamar wanda
ke karantawa. Na dubi kasar naga babu rubutu
babu alamarsa na rasa inda yake karanto
wadannan labarai, sannan na dubi sama da
kasa banji motsin wanda yake fada masa ba.
Yace ummi wannan tsohuwar budurwar nan
tasa da yake so itace take raba ku, ta tashi
tsaye tana asiri sai ta fitar dake ta shiga gidan,
sannan faccalatki matan kanin mijinki da kuke
gida daya, itama tana saka miki hannu saboda
mijinki ya fi nata zuciyar nema, kin fi ta
hutawa, don haka take so ta raba ku.
Tags :
Ummi ta fusata ta hau bayani. Lallai biri yayi
kama da mutum, domin tun sanda mijina ya
siyo mana generator sai ta yini a daki baata
fito tsakar gida ba, haka ma zance tsohuwar
budurwarsa ba su rabu ba suna tare har yanzu,
naga sakonta a wayarsa. Yanzu malam yaya
za'ayi? Sai naga ya karkace ya zayyano mata
abubuwa kamar su turarruka na wuridi, kaji,
dan akuya ja, farin kyalle da kudin yaran
dazasu zauna aiki, dubu ashirin da biyar. Ko ta
nuna damuwa ma batayi ba sai kawai ta ce
gobe zan kawo dubu goma sha biyar a fara,
don Allah malam ka ragargaza min su kamar
yadda suke son su raba ni da mijina suma a
rabasu da mazansu, ni kuma mu zauna daram
ina so a kama min shi don wulakanci yake yi
min kwanan nan har da cewa bai san inda yake
kallo ba ya aure ni, don ni ba irin tsarin
rayuwarsa bace. Sakacinki ne inji malam. Ya
juyo ya dube ni sai na takure a lungu kirjina
yana dukan ukuk uku. Yace ke fa meye
matsalarki, ko baki fada ba zan iya ganin
asiran da akayi miki a jikinki, ki tashi tsaye
wajen neman tsari. Ummi ta kwanto da 'yarta
daga bayanta ta gyara zama tace malam, aisha
farida kawata ce, a taimaka mata. Matsalarmu
kusan iri daya ce, ayi mata bincike tukunnan.
Ta bukaci ina saka abin sadaka kafin ya fara,
sai ummi ta zaro dari biyu zata mika masa na
rike hannunta nace ba sai an bincika min ba
malam zan fada da bakina. Na koro masa
bayani tas, sai yayi dariya ya kyakyata yace
wannan karamin aiki ne a wajena, idan har zaki
sayi kayan aiki na baki kwana biyu inda dr
shureim imran ne kim gama samunsa. Ina jin
haka sai naji farin ciki ya lullube ni nayi dariya,
na tambaye shi me dame za a siya? Sai yayi
min zancen abubuwa daban daban, wasu na
sansu wasu ban sansu ba. Aka hada kudin ya
kama naira dubu ashirin da daya. Sai na dafe
kirji nace malam bani da kudi ko zaka yi min
bashi idan komai ya kankama sai in biya? Ya
dubi ummi cike da bacin rai yace ina kika samo
min wannan yarinyar? Baki fada mata dokar
aikina bane? Sabon shiga ce ko? Toh ni bana
fadar farashi a nemi ragi balle ace inyi a bashi,
a cikin kudin nan babu sisi nawa, duk na
rauhanai ne. Ummi tace ayi hakuri malam,
laifina ne ban fada mata dokokinka ba zamu
dawo gobe tare zamu nemo kudin mu kawo.
Mun goda. Banyi godiya ba na kada kai na fito,
hankalina ya gama tashi. Muna fita kofar gida
ummi ta hau yi min fada tana cewa me yasa
ban bari anyi min bincike ba inji bayani dalla
dalla ba, sannan me yasa nace ayi min aiki
bashi alhali tun a kan hanya na baki labarinsa?
Nace to bani da kudi ko naira hamsin ta kaina
bani da ita. Me zance? Tace ki sayar da
kadararki mana. Nace ai bani da ko barimar
gwal balle dan kunne. Ta tabe baki tace ni dai
shawarar da zan baki itace kije kisan abinyi
don nima nan da kika ganni bashi zanje in ciyo
in kai masa idan aiki yaci da kansa zai baki
kudi kije ki biya. Malamin nan fa aikinsa kamar
yankan wuka, sha yanzu magani yanzu. Kije
kiyi tunani zuwa gobe ki samo kudi, kizo mu
kai don ni ma daga nan gari zan shiga neman
bashi. Ta bani kudin mota mukayi sallama na
shiga motar unguwarmu, ita kuma ta shiga
motar dawanau ban san inda ta nufa ba. Ina
zaune a mota tamkar gunki ina tunani, sai da
kondasta yyayi ta magana sannan na gane dani
yake, na mika masa kudin mota. Haka da aka
zo inda zan sauka ma na manta har aka wuce
dani, sannan na ankara nace a sauke ni. Saida
na dawo baya. Na shiga gida a cakude, narasa
inda zan saka raina, tunanina gaba daya ya
koma wajen inda zan samo rancen kudi in
kaiwa malam gobe. Cikin unguwar nan da
batsewarta babu matar da zata iya fitar da
dubu biyar ma kai tsaye saboda talauci. Da
yamma na shirya na fita neman kudi gida gida,
da kyar na hado rancen dubu biyu. Na zarce
kai tsaye shagon da musbahu yake sana'a. Sai
yayi matukar mamakin ganina ya tambayeni
lafiya ya ganni a hargitse haka? Na fada masa
cewar matsalar kudi ce ta taso min, bani da
lafiya. 'Yar karamar tiyata za ayi min gobe a
asibitin ana neman naira dubu ashirin. Sai ya
dafe kirji yace aisha farida babu inda zan sami
dubu ashirin a yau. Ai ko bashi babu in da zan
samu. Ko idan anyi wa likitan bayani zai yarda
yayi miki aiki a bashi karshen wata sai in biya
shi. Na girgiza kai nace babu zance bashi
kuma dole in hada kudin daga yau zuwa dare.
Yace to inje gida zai aiko yaro ya kawo min
abin da ya sauwaka. Zaije ya fita ya nemo
abinda ya samo. Nayi godiya na tafi. Ko awa
guda banyi ba da shiga gida sai ga dan aike da
dubu uku har da doguwar wasika yana mai
bani hakuri abin da ya samo kenan. Amaa zaici
gaba da nemowa zuwa gobe. Ya jero min
kalaman soyayya ko gama karantawa banyi ba
na yayyaga na zubar, burina in hada kudin nan
in kai. Ina zaune a mota tamkar gunki ina
tunani, sai da kondasta yyayi ta magana
sannan na gane dani yake, na mika masa kudin
mota. Haka da aka zo inda zan sauka ma na
manta har aka wuce dani, sannan na ankara
nace a sauke ni. Saida na dawo baya. Na shiga
gida a cakude, narasa inda zan saka raina,
tunanina gaba daya ya koma wajen inda zan
samo rancen kudi in kaiwa malam gobe. Cikin
unguwar nan da batsewarta babu matar da
zata iya fitar da dubu biyar ma kai tsaye
saboda talauci. Da yamma na shirya na fita
neman kudi gida gida, da kyar na hado rancen
dubu biyu. Na zarce kai tsaye shagon da
musbahu yake sana'a. Sai yayi matukar
mamakin ganina ya tambayeni lafiya ya ganni
a hargitse haka? Na fada masa cewar matsalar
kudi ce ta taso min, bani da lafiya. 'Yar
karamar tiyata za ayi min gobe a asibitin ana
neman naira dubu ashirin. Sai ya dafe kirji yace
aisha farida babu inda zan sami dubu ashirin a
yau. Ai ko bashi babu in da zan samu. Ko idan
anyi wa likitan bayani zai yarda yayi miki aiki a
bashi karshen wata sai in biya shi. Na girgiza
kai nace babu zance bashi kuma dole in hada
kudin daga yau zuwa dare. Yace to inje gida
zai aiko yaro ya kawo min abin da ya
sauwaka. Zaije ya fita ya nemo abinda ya
samo. Nayi godiya na tafi. Ko awa guda banyi
ba da shiga gida sai ga dan aike da dubu uku
har da doguwar wasika yana mai bani hakuri
abin da ya samo kenan. Amaa zaici gaba da
nemowa zuwa gobe. Ya jero min kalaman
soyayya ko gama karantawa banyi ba na
yayyaga na zubar, burina in hada kudin nan in
kai. Uwani uwar adashe ita kadai na tabbatr
zan iya samun rancen kudi a wajenta ko nawa
ne saboda itace naga koda yaushe mata suna
aiko mata da zubin kudin adashe, ina hango
shigarsu da fitarsu daga windon dakina domin
dakinta na kusa da dakina. Ina idar da sallar
magriba na tabbatar abida tana daki tana
wuridi ba zata fito tsakar gida ba, sai tayi
sallar ishai kamar yadda ta saba. Sai nayi
sanda na fito dakina na fada dakin uwani, sai
tayi mamakin ganina a wannan lokaci, naci
sa'a maigidanta bai dawo ba. Ta saka fitilar
kwai a gaba tana kirga kudi kashi kashi. Farin
ciki ya rufe ni da naga kudin nan sai na shiga
marairaice mata inayi mata dadin baki cewar
ta ranta min dubu goma sha bakwai zan biya
ta gobe da yamma. Ta tsorata matuka har da
dafe kirji ta tambaye ni, me zakiyi da kudi
haka? Na shaida mata kawata ce zata haihu a
asibitinmu ance ba zata iya haihuwa da kanta
ba sai an yi mata tiyata. Ga mijinta ba ya gari
yana lagos. Amma ya sako kudin ta banki, to
kasancewar asabar ce babu banki, lahadi ma
babu aiki ba za a iya fitar da kudin ba, sai
ranar litinin. Shine tace in ranto mata zuwa
litinin zata biya. Uwani tace a'a aisha farida
kinsan halin mutane kayi musu rana suyi ma
mutum dare. Ki zo ki taimake su suki biya, ko
kuma ni in taimake ki, kiki taimakona. Kinsan
dai kudin nan da kika gani kudin cizo ne, bana
kashewa bane da masu shi. Gobe haj rabi ce
zata dauki adashen nan dubu talatin. Mace
dayace bilki bata saka mata ba, na aika tace
gobe zata aiko yana aikowa sai in hada in
aikawa haj rabi daukarta. Yanzu idan na baki
aka zo aka sami matsala yaya zanyi? Kinsan
bani dashi, lada suke bani duk wata dubu daya
dan tarawar da nakeyi. Niko ikon sgiga
adashen ma bani dashi dan bani dashi. Nace
na sani uwani, idan Allah Ya yarda babu
matsala, ranar litinin da sassafe zanje bankin
da kaina in karbo miki. Tace to shikenan gashi
nan. Ta kirgo dubu goma sha bakwai tabani, na
karba na kirga sun cika cas, nayi godiya.
Sannan na roki arzikin ta rufa min asiri kada ta
fadawa kowa ko abida kada taji, salin alin zan
dawo mata da kudinta. Tayi min alkawari babu
wanda zaiji. Na shiga daki na hada kan kudina
na adana a jaka. Naira dubu ashirin. Farin ciki
fal a zuciyata, har sai da abida ta fuskanci
haka a daren, a da bana iya cin abinci sosai,
amma a daren taga har da kari nayi. Da bana
son magana sai taji na isheta da labari a ranar.
Ta san na daina fara'a amma a ranar na ishe
ta da kyakyata daria har da wake wake.
Saboda na riga na sami kudin da bana tantama
na gama samun dr shureim imran. Gari na
wayewa na shiga tunanin karyar da zan
shiryawa yaya hussaini wacce zai bari in fice,
domin ranar lahadi ce babu aiki, kuma kulle
yake min. Na shirya tsaf na kira abida gefe na
shirga mata karyar cewa zanje asibiti yau ma,
ana yiwa wata nurse bikin gama aiki, tayi retire
ance kowa sai yaje kuma da kayan gida. Na
santa da wayo ta san yadda zata fadawa
maigidanta ya aminta da ita. Ta shiga daki ta
tsaro shi sai ga ta da dari biyu kudin babur.
Naji tausayinsu ya kama ni saboda nafi su kudi
yanzu, da sun san kudin da yake jikina da basu
rabu da dari biyunsu ba. Nayi godiya na karbe
na tafi, abida ta rakani har zaure tana yi min
fatan alkairi. Tana jaddada min in ragowa
'ya'yanta kayan walima. Na amsa mata da zan
rago musu da yawa ma kuwa. Ina fita na hau
acaba sai gidan ummi kawata. Da yake sassafe
ne mijinta ma bai fita ba yana daki, tajani
zuwa falonta muka zauna muna magana cikin
sirri. Ta tambaya yaya ake ciki, na samo kudin
kuwa? Na ciro mata himilin kudin daga jakata
sai ta rike baki tace lallai kinyi kokari, nima na
hada dubu goma sha biyar bari inje inyi masa
karya inzo mu tafi. Yau lahadi ba zai fita da
wuri ba, gara muyi tafiyarmu. Ta shiga daki ba
dadewa ta fito a shirye da goyonta muka nufi
kofar fita, har mun kai zaure faccalarta ta biyo
mu da sauri. Tana cewa ummi unguwa zakije
baki fada min ba mu fita tare? Yau ne sunan
mariya 'yar jummai, ki tsaya in shirya mu fita
gaba daya mana. Ummi ta doka mata harara
tace dani aisha faida da Allah muje, dole ne sai
mun fita tare. Myka kada kai muka fice muka
bar ta a tsaye tana kallonmu har abin tausayi.
Muna fita nace da ita haba ummi ya za ayi kiyi
mata wulakanci? Ai sai ki bata amsa mai dadi
ko ba kya so tabimu. Ummi ta tabe tace ai na
daina raga mata tunda bincike ya nuna bata
kaunata. Ni da mutunci da ita har abada. Nace
to amma ai maganar malamai ce, babu tabbas
zaiyiwu kirkira yayi. Ta harare ni tace lallai kina
wasa da aikin malamin nan. Idan yayi miki
duba tabbas zaki ga komai a hankali daya
bayan daya. In bai gani ba zai fada ne ko da
ya taba ambato sunanta in ba yanzu ba, kuma
nima na lura tun sanda muka sayi generator ta
canja min, taga mun cigaba a rayuwa. DUK
KYAN TAKALMI 11 Bansake magana ba dai har
muka isa gidan malam. Yana ganin mu ya fara
washe baki, fara'ar yau tafi ta jiya. Muka
zazzage masa kudaden jakarmu kakaf domin
bayan dubu ashirin da dayan da ya karba sai
da ya sake kwakwalo min wasu kudaden daban
daban har dubu biyar da dari biyar. Kuma na
harhada na bashi, a takaice dai har cikon dubu
daya da dari biyar nan gaba zan ciko masa. Ita
ma ummi ya kara mata wasu kudin, idan ta
tashi cikowa ba dubu goma zata ciko masa ba,
goma sha uku zata ciko. Yace ya bamu
kwanaki uku mu dawo, ranar laraba kenan kafin
komai zai daidai ta. Muka fito muna murna,
ummi tana tabbatar min komai zai daidaita in
kwantar da hankalina. Na tafi gida ita ma ta
koma gidanta, na sake shirgawa abida wata
karyar tunda ban taho da kayan walima ba,
naso in siyo musu lemo da biskit amma na
juyewa malam kudin dukka, da kyar ma na
karaso gida, sai da kudi ya kare. Ko kusa ban
damu da himilin bashin dake kaina ba, burina
aiki yaci in mallaki dr shureim shine a gabana.
Na yina ina hidindimuna da 'yan gidanmu cikin
walwala da farin ciki. Da dare yayi na shiga
barci sai na tsinci kaina na canza tunanina ba
irin na da bane. Yanzu tunani nake gani a
gidansa har mun zama ma'aurata, gani dare-
dare a cikin hadaddiyar motar nan tasa muna
tafe muna hirar soyayya. Na dade ina
tunaninsa sannan nayi bacci, na dora da
mafarkinsa mai dadin gaske. Na sa wa
zuciyata na sami dr shureim na gama kamar
yadda malam ya bani tabbaci. Naso in makara
saboda dadin mafarki, na tashi a gaggauce na
shirya na karbi kudin babur a wajen abida.
Yayana ya bata ta bani donshi yana riga ni fita
ma. Sai uwani ta biyo ni zaure da sauri ta
tsayar dani tace yanzu zaki karbo kudin daga
banki? Ko sai kin taso zaki taho dashi? Bilki ta
kawo zubinta jiya na wajenki kawai nake jira in
aikawa haj rabi na fada mata yau da rana zan
aiko mata. Sai zuciyata ta hau dukan uku uku
na fara zullumin inda zan nemo wadannan
makudan kudi. Na hau rawar murya ina kame
kame, nace sai an taso zan taho da kudin. Ina
kan babur ina tunanin yadda za'ayi idan na
dawo gida babu kudin? Ina shiga cikin asibiti
naji farin ciki ya lullunbe min zuciyata saboda
ko ba komai an fara aiki, zuciyarsa ta fara
bugowa gare ni. Sai kuwa naci sa'ar a ranar an
tura mu bangarensu dole zan ga ofishinsa ko
ba ma wajensa aka mu tura mu ba. Muna
shiga kuwa dakin darasin muka ci karo dashi
da dr lukman suna fitowa medical students
suna biye dasu zasu je zagayen marasa lafiya
(ward). Na tare su da sauri na gaishe su, sai
naji caraf ya amsa hadda kallon fuskata, ba
murmushi yake ba haka bai bata rai ba. Dr
lukman ne yake dariya, har yake yi min wasa
yace ke 'yar shagamu ina kika shiga kwana
biyu, rannan har yahaya umar yace in baki
waya ku gaisa, nace ba kya kusa. Nayi dariya
nace to yaushe zanzo ka kirawo min shi a
wayar muyi magana? Da yake yana tafiya ne
sanda yake magana, har yakai barandar waje
banji abin da yace ba. Sai wani dalibi ne yake
bayansu ya juyo yace min cewa yayi kizo gobe.
Na yini ina farin ciki saboda naga canji wajen
amsa gaisuwata da kuma kallon mutuncin da
dr shureim ya min. Ban fara fargaba ba sai da
aka tashi daga makaranta na tunkaro hanyar
gida. Na shiga zullumin karyar da zan gina
wacce ba za'a rutsoni ba, dakin uwani na nufa
kai tsaye sai ta fara murna tana gyara hannu
zata karbi kudi ta kidaya. Sai na zube a
gabanta ina marairaice murya ina bayani. Nace
wallahi tun safe ban huta ba muna ta kai kawo
a cikin asibitin saboda matar bata da jini, don
haka ba za'a yankata ba dole sai an kara mata
jini. 'Yan uwanta ne suka zo maza da mata
muna ta auna jinin har a sami wanda ya dace
da nata shi yasa ban samu fita daga asibitin
ba naje banki, amma gobe da sassafe zanje in
karbo. Uwani ta bata rai, yadda ta amsa min a
ciki ciki na san bata so haka ba, ta bini da kallo
har na fice daga dakin. Ina cin abincin rana na
fice wajen musbahu ban same shi ba, na bar
masa doguwar wasika. Nazo giftawa ya
makoftanmu nayi ido hudu dahare ta leko
kenan ta ganni, ita ma dari takwas ta ranta
min kudin dinkinta zata kai domin ta kusa
haihuwa, ita ma ranar litimin din nace zan
kawo mata. Dole na shiga gidan na tsara mata
karya iri iri na ce gobe zan kawo mata. Itama
ta nuna min bataji dadi ba, har mijinta yayi
fada da yaga kayan dinkin a ajiye bata kai ba.
Naji hankalina ya sake tashi na fito a gigice na
shiga gidan mu har sai da abida ta shiga
damuwa ganin yanayin da na shigo. Tayi ta
tambayata ko lafiya? Nace lafiya kalau. Idan
naji damuwa ta gallabeni sai in tuno menayi da
kudin, kuma nan gana me zan samu. Sai inji
sanyi a raina. Washe gari talata na fita zuwa
makaranta, kai tsaye ofishin dr lukman na
wuce. Ina shiga na iske shi zai fita. Yace dani
ke kuwa baiwar Allah ai ba da sassafen nan
zaki zo ba, sai da rana in aiki ya lafa ko? Nayi
turus banji dadin amsar daya bani ba, ya wuce
abinsa ya barni a tsaye. Sai ga gogan nawa
yau kuma shigar hausa yayi, shadda ruwan
bula tazarce ya dora hular da ta dace da kalar
kayansa. Ya ratayo laptop dinsa a kafadarsa
sai naga ya kara yin kyau matuka babu wacce
zata kalle shi bata sake kallonsa ba. Ya tari dr
lukman sukayi magana, sannan kowa ya wuce.
Sai naji zuciyata na tafarfasa saboda shaukin
so, kai kace zakanya ce mai tsananin jin
yunwa ta ga nama haka zuciyata ta dinga zillo
tamkar ta ballo ta fito da taga abincinta. Sai
dai wannan abincin bana lasa bane, yafi
karfinta. Tamkar soyayyen nama ne aka soya
yana kamshi amma aka zazzaga masa guba
kaga duk kwadayin mutum doke ya kalla ya
wuce ko da kuwa marmarin naman zai kashe
shine. Na fara takawa a hankali na matsa daga
bakin kofar kafin ya karaso. Tun daga nesa na
amshi wata galleliyar harara daga gareshi.
Daya karaso bakin kofa kafin ya lalubo mukulli
ya bude kofar sai da ya waiwayo bayansa inda
nake a tsaye ya wurgo min wata hararar wacce
tafi ta dazu wulkilewa. Sai nayi sauri na juya
na fara tafiya ba tare da nasan inda zanje ba,
sai gani a bakin gadon marasa lafiya nayi wuki
wuki suna kallona ina kallonsu. Sannu likita,
zoki duba cikinsa ki gani ya kumbura. Inji wata
tsohuwa mai zaman jinyar danta. Na girgiza
kai nace ki kira likita ni ba likita bace. Nayi
saurin barin wajen na dawo bakin kofar ofis din
na tsaya, nayi kamar in tura kofar in shiga sai
na fasa. Na hakura na tafi ba don zuciyata
tana so ba. Ina zuwa ofishinmu na iske
kawayena suka hau min surutu. Wai aisha
farida ina kike shiga ne aka nemeki aka rasa
kullum har anyi test jiya ba kya nan? Nayi
shiru na koma gefe na zauna na rasa abun da
yake min dadi. Naci sa'a khadija sani tace inzo
in rakata ta siyo ruwa zata sha magani. Ashe
itama ta kunso labarai kala kala take so mu
kebe ta fatsar. Ta dube ni ta tabe baki tace
baki tambayeni dr shureim ba. Sai naji gabana
ya fadi, sai na zargi kaina ina ganin kamar
kowa yasan halin da nake ciki. Na zabura nace
kamar yaya ban tambaye ki dr shureim ba?
Tace kin manta inda muka kwana na nuna miki
sakonsa a wayata? To in fada miki an gasa
minshi da addua, ba adadi har sai da yaji ba
dadi. Ina kiransa ya amsa, yace dani wacece?
Sai na fada masa sunana khadija sani ismail.
Ni daliba ce a schl of nursing tanan aminu
kano, kuma ina attachment a nan cikin asibiti,
sai yace yayi kyau lafiya? Nace lafiya so nake
yayi saving lambata zan dinga kira muna
gaisawa. Na dafe kirji nace yayi saving lambar?
Tace kwarai kuwa, don da na sake kira sai da
ya ambaci sunana. Sai naji kwalla ta cika min
ido, kishi ya kamani, jikina yayi sanyi kalau.
Taci gaba da cewa da na sake kira sai yayi
tsiyar. Na tambaya a sanyaye meye tsiyar?
Tace wulkanci yayi min kamar zai zageni, wai
kada in sake kiransa. Kuka wiwi nayi da
hawaye na hakura dashi ma ni yanzu. Allah Ya
sa bai san fuskata ba, na goge lambarsa na
daina kiransa yanzu. Dadi ya rufeni, amma fa
na kara tausayawa kaina. Na bata shawarar
tayi hakuri taci gaba da addua, Allah Ya
musanya mata da abin da yafi alkhairi. Ta
amsa min da ameen. Da aka tashi daga
makaranta sai na kasa komawa gida, sai
nacewa khadiji sani ismali zanbi ta gidansu
somin 'yan gidanmu ba sa nan sun tafi unguwa
sai dare zasu dawo. Khadija tayi farinciki da jin
haka, sai muka dunguma muka tafi har yanzu
labarin dr takeyi min. Ban cika bata amsa ba,
tamkar tana min famin gyambon da yake
damuna da zugi ne. Kwakwalwata ta cunkushe
na rasa abin da yake min dadi, na kasa
tantance abin da zanyi. Abinci kala kala aka
jera min a gabana, amma na kasa ci da yawa
saboda damuwa. Khadija sani ta dube ni tace
wai don Allah aisha farida me yake damunki ne
kwana biyu kin susuce tamkar bake ba. Ba kya
son magana, ba kya son karatu gashi ba kya
son cin abinci tundazu dan abincin da kika
zuba kin kasa cinyewa, bakiga yadda kika rame
ba, kika kwanjale ba. Kin cika zurfin ciki, ba a
jin sirrinki daman. Wai me yake faruwa ne?
Nayi murmushi nace haka kowa yake ambata,
malaria ce ke cin jikina. Tace toh kisha magani
mana, yaya zaki zauna da ciwo kina malamar
asibiti, ko in saya miki babu kudi hannunki? Ta
soso min inda yake min kaikayi, na gyara zama
nace kamar kinsan satin nan cikin matsalar
kudi muke, kinga yanzu haka yayana ne aka
bashi ajiyar kudi, ya kawo gida aka shiga har
daki aka sace, ya rasa yadda zaiyi. Mai kudin
yana ta damunsa har da zai kai shi police
station yake ambato. Khadija tace a garin yaya
aka shiga har daki aka yi muku sata, babu
mukulli ne? Nace maso abinka ya fika dabara,
kinsan rayuwar cikin gari, gidan yawa aka shiga
aka dauke. Khadija tace babu dadi, Allah Ya
kiyaye gaba. Shi kuwa mai kudin bai san
kaddara bane? Yayi hakuri mana sai ya samu
ya biya shi. WaLlahi nima a cikin matsala nake,
domin na karbi kudi a wajen abba yayi dubu
hamsin kwanan nan haka ma a wajen mama.
Har sun gane ba'a makaranta nake kashewa ko
na tambaya basa bani. Sai tambayata suke me
nayi da kudi a cikin satin nan, naki fada, ai ban
isa ince malamai na kaiwa ba sai a kusa kashe
ni.
Tags :
Bansake magana ba dai har muka isa gidan
malam. Yana ganin mu ya fara washe baki,
fara'ar yau tafi ta jiya. Muka zazzage masa
kudaden jakarmu kakaf domin bayan dubu
ashirin da dayan da ya karba sai da ya sake
kwakwalo min wasu kudaden daban daban har
dubu biyar da dari biyar. Kuma na harhada na
bashi, a takaice dai har cikon dubu daya da
dari biyar nan gaba zan ciko masa. Ita ma
ummi ya kara mata wasu kudin, idan ta tashi
cikowa ba dubu goma zata ciko masa ba,
goma sha uku zata ciko. Yace ya bamu
kwanaki uku mu dawo, ranar laraba kenan kafin
komai zai daidai ta. Muka fito muna murna,
ummi tana tabbatar min komai zai daidaita in
kwantar da hankalina. Na tafi gida ita ma ta
koma gidanta, na sake shirgawa abida wata
karyar tunda ban taho da kayan walima ba,
naso in siyo musu lemo da biskit amma na
juyewa malam kudin dukka, da kyar ma na
karaso gida, sai da kudi ya kare. Ko kusa ban
damu da himilin bashin dake kaina ba, burina
aiki yaci in mallaki dr shureim shine a gabana.
Na yina ina hidindimuna da 'yan gidanmu cikin
walwala da farin ciki. Da dare yayi na shiga
barci sai na tsinci kaina na canza tunanina ba
irin na da bane. Yanzu tunani nake gani a
gidansa har mun zama ma'aurata, gani dare-
dare a cikin hadaddiyar motar nan tasa muna
tafe muna hirar soyayya. Na dade ina
tunaninsa sannan nayi bacci, na dora da
mafarkinsa mai dadin gaske. Na sa wa
zuciyata na sami dr shureim na gama kamar
yadda malam ya bani tabbaci. Naso in makara
saboda dadin mafarki, na tashi a gaggauce na
shirya na karbi kudin babur a wajen abida.
Yayana ya bata ta bani donshi yana riga ni fita
ma. Sai uwani ta biyo ni zaure da sauri ta
tsayar dani tace yanzu zaki karbo kudin daga
banki? Ko sai kin taso zaki taho dashi? Bilki ta
kawo zubinta jiya na wajenki kawai nake jira in
aikawa haj rabi na fada mata yau da rana zan
aiko mata. Sai zuciyata ta hau dukan uku uku
na fara zullumin inda zan nemo wadannan
makudan kudi. Na hau rawar murya ina kame
kame, nace sai an taso zan taho da kudin. Ina
kan babur ina tunanin yadda za'ayi idan na
dawo gida babu kudin? Ina shiga cikin asibiti
naji farin ciki ya lullunbe min zuciyata saboda
ko ba komai an fara aiki, zuciyarsa ta fara
bugowa gare ni. Sai kuwa naci sa'ar a ranar an
tura mu bangarensu dole zan ga ofishinsa ko
ba ma wajensa aka mu tura mu ba. Muna
shiga kuwa dakin darasin muka ci karo dashi
da dr lukman suna fitowa medical students
suna biye dasu zasu je zagayen marasa lafiya
(ward). Na tare su da sauri na gaishe su, sai
naji caraf ya amsa hadda kallon fuskata, ba
murmushi yake ba haka bai bata rai ba. Dr
lukman ne yake dariya, har yake yi min wasa
yace ke 'yar shagamu ina kika shiga kwana
biyu, rannan har yahaya umar yace in baki
waya ku gaisa, nace ba kya kusa. Nayi dariya
nace to yaushe zanzo ka kirawo min shi a
wayar muyi magana? Da yake yana tafiya ne
sanda yake magana, har yakai barandar waje
banji abin da yace ba. Sai wani dalibi ne yake
bayansu ya juyo yace min cewa yayi kizo gobe.
Na yini ina farin ciki saboda naga canji wajen
amsa gaisuwata da kuma kallon mutuncin da
dr shureim ya min. Ban fara fargaba ba sai da
aka tashi daga makaranta na tunkaro hanyar
gida. Na shiga zullumin karyar da zan gina
wacce ba za'a rutsoni ba, dakin uwani na nufa
kai tsaye sai ta fara murna tana gyara hannu
zata karbi kudi ta kidaya. Sai na zube a
gabanta ina marairaice murya ina bayani. Nace
wallahi tun safe ban huta ba muna ta kai kawo
a cikin asibitin saboda matar bata da jini, don
haka ba za'a yankata ba dole sai an kara mata
jini. 'Yan uwanta ne suka zo maza da mata
muna ta auna jinin har a sami wanda ya dace
da nata shi yasa ban samu fita daga asibitin
ba naje banki, amma gobe da sassafe zanje in
karbo. Uwani ta bata rai, yadda ta amsa min a
ciki ciki na san bata so haka ba, ta bini da kallo
har na fice daga dakin. Ina cin abincin rana na
fice wajen musbahu ban same shi ba, na bar
masa doguwar wasika. Nazo giftawa ya
makoftanmu nayi ido hudu dahare ta leko
kenan ta ganni, ita ma dari takwas ta ranta
min kudin dinkinta zata kai domin ta kusa
haihuwa, ita ma ranar litimin din nace zan
kawo mata. Dole na shiga gidan na tsara mata
karya iri iri na ce gobe zan kawo mata. Itama
ta nuna min bataji dadi ba, har mijinta yayi
fada da yaga kayan dinkin a ajiye bata kai ba.
Naji hankalina ya sake tashi na fito a gigice na
shiga gidan mu har sai da abida ta shiga
damuwa ganin yanayin da na shigo. Tayi ta
tambayata ko lafiya? Nace lafiya kalau. Idan
naji damuwa ta gallabeni sai in tuno menayi da
kudin, kuma nan gana me zan samu. Sai inji
sanyi a raina. Washe gari talata na fita zuwa
makaranta, kai tsaye ofishin dr lukman na
wuce. Ina shiga na iske shi zai fita. Yace dani
ke kuwa baiwar Allah ai ba da sassafen nan
zaki zo ba, sai da rana in aiki ya lafa ko? Nayi
turus banji dadin amsar daya bani ba, ya wuce
abinsa ya barni a tsaye. Sai ga gogan nawa
yau kuma shigar hausa yayi, shadda ruwan
bula tazarce ya dora hular da ta dace da kalar
kayansa. Ya ratayo laptop dinsa a kafadarsa
sai naga ya kara yin kyau matuka babu wacce
zata kalle shi bata sake kallonsa ba. Ya tari dr
lukman sukayi magana, sannan kowa ya wuce.
Sai naji zuciyata na tafarfasa saboda shaukin
so, kai kace zakanya ce mai tsananin jin
yunwa ta ga nama haka zuciyata ta dinga zillo
tamkar ta ballo ta fito da taga abincinta. Sai
dai wannan abincin bana lasa bane, yafi
karfinta. Tamkar soyayyen nama ne aka soya
yana kamshi amma aka zazzaga masa guba
kaga duk kwadayin mutum doke ya kalla ya
wuce ko da kuwa marmarin naman zai kashe
shine. Na fara takawa a hankali na matsa daga
bakin kofar kafin ya karaso. Tun daga nesa na
amshi wata galleliyar harara daga gareshi.
Daya karaso bakin kofa kafin ya lalubo mukulli
ya bude kofar sai da ya waiwayo bayansa inda
nake a tsaye ya wurgo min wata hararar wacce
tafi ta dazu wulkilewa. Sai nayi sauri na juya
na fara tafiya ba tare da nasan inda zanje ba,
sai gani a bakin gadon marasa lafiya nayi wuki
wuki suna kallona ina kallonsu. Sannu likita,
zoki duba cikinsa ki gani ya kumbura. Inji wata
tsohuwa mai zaman jinyar danta. Na girgiza
kai nace ki kira likita ni ba likita bace. Nayi
saurin barin wajen na dawo bakin kofar ofis din
na tsaya, nayi kamar in tura kofar in shiga sai
na fasa. Na hakura na tafi ba don zuciyata
tana so ba. Ina zuwa ofishinmu na iske
kawayena suka hau min surutu. Wai aisha
farida ina kike shiga ne aka nemeki aka rasa
kullum har anyi test jiya ba kya nan? Nayi
shiru na koma gefe na zauna na rasa abun da
yake min dadi. Naci sa'a khadija sani tace inzo
in rakata ta siyo ruwa zata sha magani. Ashe
itama ta kunso labarai kala kala take so mu
kebe ta fatsar. Ta dube ni ta tabe baki tace
baki tambayeni dr shureim ba. Sai naji gabana
ya fadi, sai na zargi kaina ina ganin kamar
kowa yasan halin da nake ciki. Na zabura nace
kamar yaya ban tambaye ki dr shureim ba?
Tace kin manta inda muka kwana na nuna miki
sakonsa a wayata? To in fada miki an gasa
minshi da addua, ba adadi har sai da yaji ba
dadi. Ina kiransa ya amsa, yace dani wacece?
Sai na fada masa sunana khadija sani ismail.
Ni daliba ce a schl of nursing tanan aminu
kano, kuma ina attachment a nan cikin asibiti,
sai yace yayi kyau lafiya? Nace lafiya so nake
yayi saving lambata zan dinga kira muna
gaisawa. Na dafe kirji nace yayi saving lambar?
Tace kwarai kuwa, don da na sake kira sai da
ya ambaci sunana. Sai naji kwalla ta cika min
ido, kishi ya kamani, jikina yayi sanyi kalau.
Taci gaba da cewa da na sake kira sai yayi
tsiyar. Na tambaya a sanyaye meye tsiyar?
Tace wulkanci yayi min kamar zai zageni, wai
kada in sake kiransa. Kuka wiwi nayi da
hawaye na hakura dashi ma ni yanzu. Allah Ya
sa bai san fuskata ba, na goge lambarsa na
daina kiransa yanzu. Dadi ya rufeni, amma fa
na kara tausayawa kaina. Na bata shawarar
tayi hakuri taci gaba da addua, Allah Ya
musanya mata da abin da yafi alkhairi. Ta
amsa min da ameen. Da aka tashi daga
makaranta sai na kasa komawa gida, sai
nacewa khadiji sani ismali zanbi ta gidansu
somin 'yan gidanmu ba sa nan sun tafi unguwa
sai dare zasu dawo. Khadija tayi farinciki da jin
haka, sai muka dunguma muka tafi har yanzu
labarin dr takeyi min. Ban cika bata amsa ba,
tamkar tana min famin gyambon da yake
damuna da zugi ne. Kwakwalwata ta cunkushe
na rasa abin da yake min dadi, na kasa
tantance abin da zanyi. Abinci kala kala aka
jera min a gabana, amma na kasa ci da yawa
saboda damuwa. Khadija sani ta dube ni tace
wai don Allah aisha farida me yake damunki ne
kwana biyu kin susuce tamkar bake ba. Ba kya
son magana, ba kya son karatu gashi ba kya
son cin abinci tundazu dan abincin da kika
zuba kin kasa cinyewa, bakiga yadda kika rame
ba, kika kwanjale ba. Kin cika zurfin ciki, ba a
jin sirrinki daman. Wai me yake faruwa ne?
Nayi murmushi nace haka kowa yake ambata,
malaria ce ke cin jikina. Tace toh kisha magani
mana, yaya zaki zauna da ciwo kina malamar
asibiti, ko in saya miki babu kudi hannunki? Ta
soso min inda yake min kaikayi, na gyara zama
nace kamar kinsan satin nan cikin matsalar
kudi muke, kinga yanzu haka yayana ne aka
bashi ajiyar kudi, ya kawo gida aka shiga har
daki aka sace, ya rasa yadda zaiyi. Mai kudin
yana ta damunsa har da zai kai shi police
station yake ambato. Khadija tace a garin yaya
aka shiga har daki aka yi muku sata, babu
mukulli ne? Nace maso abinka ya fika dabara,
kinsan rayuwar cikin gari, gidan yawa aka shiga
aka dauke. Khadija tace babu dadi, Allah Ya
kiyaye gaba. Shi kuwa mai kudin bai san
kaddara bane? Yayi hakuri mana sai ya samu
ya biya shi. WaLlahi nima a cikin matsala nake,
domin na karbi kudi a wajen abba yayi dubu
hamsin kwanan nan haka ma a wajen mama.
Har sun gane ba'a makaranta nake kashewa ko
na tambaya basa bani. Sai tambayata suke me
nayi da kudi a cikin satin nan, naki fada, ai ban
isa ince malamai na kaiwa ba sai a kusa kashe
ni. DUK KYAN TAKALMI 12 Sai naji hankalina
ya tashi, har na fara nadamar katobarar da na
tafka. Ta bude jakarta ta zaro dukka kudin da
yake jakarta, dubu daya da dari biyu ne kacal
sai 'yan canji. Ta miko min naira dubu daya, na
karba nayi ta godiya. Tayi ajiyar zuciya tace
wallahi dr ya cuce ni, na kashe kudina a banza
ko gezau baiyi ba. Na fada cikin marainiyar
murya nace karki damu kaddara ce Allah Ya
aiko mana. Sai nayi sauri na gyara zancen son
naga tayi sauri ta dubeni, sai nace ciwon 'ya
mace na 'ya mace ne, tunda ya shafe ki nima
ya shafe ni. Bakiji yadda zuciyata take tafasa
ba don takaici. To shi dr dame yafi sauran
likitoci su basa wulakanci sai shi? Khadija tace
yafi sauran mana ke kuwa, shifaa a london yayi
karatunsa, ke har pri sa secondary duk a can
yayi rabin rayuwarsa, sai da yazo nigeria fisha
ya tafi. Ance dai yayi aiki a asibitin nan
shekara 2 a lokacin yana karamin likita. Sai ya
koma ya sake shekaru hudu ya zama
consultant sannan ya dawo kwanan nan. A
bangaren ilimi addini kuwa a saudia yayi
karatun kurani, larabawa suka koyar dashi,
ance yafi kowanne likita sanin kurani. Don tun
yana yaro yaje saudia sai da ya sauke ya dawo
london, ya karasa primary kinga kuwa Allah Ya
yi masa baiwar da ba kowa yake da ita ba.
Gashi dan attajiri shima attajiri, ga ilimi dukkan
bangarorin biyu, ga wani kyau tamkar sai da
zaba aka bashi. Kowacce mace dole taso shi,
sai dai idan ta ga ba ta samu bata hakura
irina. Maryam ahmad ma na gano sonsa
takeyi, har wani kishi takeyi dani, nace kije na
bar miki in dai shureim ne zaki gaji ki kyale shi.
Amma ke aisha farida naga bai dadaki da kasa
ba, ko zancensa ma ba kya so. Kowa yana
yabon kyawunsa, ke ko ki kula. Baiyi miki
bane? Sai naji tamkar an saki bom a kahon
zuciyata, saboda faduwar gaba. Nayi firgigit
nace yanzu khadija ina ta kaina ina ni ina cusa
kaina wajen irin wannan halitta? Ai sai ku
kyawawa, masu mota 'ya'yan attajirai. Khadija
tace kin hutawa kanki wallahi kina burge ni
yadda kike tafiyar da rayuwa, ba kya jajubo wa
kanki abun da zai wahalar dake. Nima nayi
nadama ba zan sake shiga irin wannan hatsarin
ba. Yanzu mun bata da malaman nan
makaryata, wai yaga aurenmu har da haihuwar
'yan biyu. Shine ai na saki jiki nayi ta tura
musu kudi suna cemin zai zo da kafarsa
nemana ga mutum kamar zai yayyaga ni cikin
waya don masifa. Bani ba wani malami ai
yanzu na rufawa kaina asiri nace mohd ya aiko
da iyayensa muyi aure. Ina laifinsa yaro
matashi, yana da mota da gidan kansa da aikin
bankinsa, nima da aikina ya ishe mu rayuwar
duniya. Sai naji hankalina ya tashi, dana sani
ta afko min. Na gyara zama nayi tagumi ina
duban khadija na rasa in da zan saka raina, sai
yanzu na fara gane kuskuren da na tafka a
rayuwa. Ummi ta cuce ni. Na fada a cikin
zuciyata yayin da hawaye ya cika min ido.
Nace da khadija kina so kice min gaba daya
asirin da malamanki suka sha zabgawa ko
daya bai taba shi ba, asiri baya cinsa kenan?
Tace baya cinsa tunda bai ci shi ba, babu abin
daya yi masa. Malamina daya ne ya fada min
gaskiya tun da farko naji haushinsa, daga
karshe na gane gaskiya ya fada min. Yace dani
yaron nan da kike so gaskiya ya rike adduar
neman tsari dare da rana, da wuya a jefe shi ya
taba shi, sai dai kawai kije kiyi addua in da
alkhairi Allah Ya hada ku ta wata hanyar, a
dadin rai yazo, kuma ina so ki sani ba'ayiwa
Allah dole. Khadija tace aiki ma daina damuwa,
Allah Ya ganar dani har na dade ina istigfari.
Su maryam anmad ne suka rage suma Allah Ya
ganar dasu. Shiyasa aka ce wani kyau bala'I
ne, sai a dilmiyar da kai in bakayi taka tsan
tsan ba. Yanzu dr shureim in ba don Allah Ya
sa nutsatte bane da mata sai sun halakar
dashi. Haka ma mace mai kyau idan baatayi a
hankali ba maza su halakar da ita, su rude ta
da kudi tabi su koda kuwa tana da aure. Ke dai
Allah Ya sa mu gane gaskiya. Sai naji khadija
ta burge ni, tafi ni gaskiya. Ina ma a llokacin
da naje neman shawara wajen ummi khadija na
samu ta fada min abinda ta fada yanzu, da ba
wa zuciyata hakuri, da ban je na jefe kaina a
rigima ba. Yanzu gashi komawa gida ya
gagareni. Da me zan biya wannan dimbin
bashin na kaina gashi babu alamar nasara a
aikin malamin. Khadija ta katse min tunanina
tace duk inda ya kai da takama da kwalliya, da
yanga karshen alewa dai kasa. Dole mace zai
aura, ba auri kansa da kansa ba. Kuma dole
yayi 'yar murya kafin a bashi ita, dole ya kashe
kudi ya bauta mata saboda Allah Ya wajabta
masa ciyarwarta, sutura, kula da lafiyarta,
muhallinta da duk wata dawainiyarta. Daman
dai ance DUK KYAN TAKALMI dole kafa ce zata
saka sannan a taka kasa. Lallai zanso inga irin
macen da zai aura, karshenta fa ya kare a
mummuna, baka, 'yar talakawa, kinsan karshen
irinsu kenan. Nace yana da mata fa har da 'ya,
kema kinsan dr shuriem ba zai auri kucaka ba.
Khadija tace ke aisha farida wa ya fada miki
wannan? Nayi murmushi nace matarsa ma
baturiya ce a london suka hadu, a london take
zaune. Da bakinsa naji yana fada. Kuma a
gabana sukayi waya da ita cikin harshen
turanci ko hausa bata ji. Khadija ta gyara zama
tace don Allah da gaske kike? Ni da kin fada
min haka tuntuni ai da ban wahalar da kaina ba
wallahi. To wai ina kika ganshi ne har kika ji
yana waya, nifa tun ganin nan nasa da mukayi
yana motarsa ban sake ganinsa ba. Ko dai ba
shi kika gani ba? Nace shine wallahi, abokin dr
lukman ne, likitan kwakwalwa wanda matron
maryam take aikena wajensa. Kinsan tana da
kanwa mai matsalar kwakwalwa, to yana duba
to ko ba ranar clinic ba. Khadija tace lallai ba
zai saurari kujari-kujari irinmu ba, mai mata
baturiya mai zaiyi damu? Naji zuciyata tana
kokarin bugawa, sai na mike na tayar da sallar
la'asar daman da alwalar azahar dina bamu
dade dayi ba. Nayi sallama nayi addua, Allah
Ya biya min bashin da yake kaina. Na yunkura
zan mike in tashi, sai khadija tace dani aisha
farida gaskiya akwai abinda yake damunki,
saboda duk jikinki yayi sanyi, yanzu ko yanayin
sallarki ya canza ba irin na da ba, ba kya
samun nutsuwa wajen yin sallh, kin daina
doguwar addua bayan kin idar da sallah. Nayi
shiru ina tunani nace a raina yanzu son dr
shureim har addinina zai taba, bayan karatuna
da ya tava ga zaman lafiya dana rasa. Sai na
zuba wani zazzafan hawaye nayi sauri na boye
fuskata don kada ta gane. Na dauki jakata na
rataya nace mata zan tafi gida. Ta rako ni har
bakin titi na hau acaba na tafi, ita kuma ta
koma gida. Sai a hanya na fara tunanin halin
da zan fada idan naje gida, don haka nace dan
acaba ya kai ni zango gidan ummi kenan. Ina
isa cikin gidan na tarar da kofarta a kulle
alamar bata nan, sai naji banji dadi ba don
haka na leka bangaren faccalarta na
tambayeta. Tace min bata nan tun jiya ta tafi.
Sai naji zuciyata ta buga na dafe kirji na
tambaya kafiya? Ta tafi unguwa tun jiya bata
dawo ba? Amsar da ta bani itace babu komai.
Na sami kujera na zauna nace da ita ki fada
min gaskiya, ummi kawata ce bata boye min
komai. Sai tace to kiyi mata waya mana sai ta
fada miki da bakinta tunda aminiyarki ce. Na
jikina a sanyaye nace to sai anjima na tafi. Sai
naga ta bini da kallo alamar tausayawa tace
dani gaskiya ummi tana gidansu mijinta ya
sake ta. Kuna fita shekaran jiya ya kai mata
takardar sakinta gidansu, ashe bai bata izinin
fita ba ta biki kuka fita har ina cewa ku jirani in
shirya kuka ki. Na dawo na tsuguna a gabanta
nace innalillahi wainna ilaihir rajiun. Yanzu
yassar saboda dan wannan dalilin ya saki
ummi? Tace a'a ba wannan kadai ba, daman
akwai wata kasa. Ummi bata da kunya, ga ta
da bin bokaye da 'yan tsubbu kowa yasani,
mijinta ya sani saboda yana tono binne binnen
da takeyi, da kuma barbade barbade da takeyi
masa a abinci. Da zarar sun fada mata karya
sai ta zai tana habaici ta bata da kowa, har
uwarsa da ta haife shi bokanta yace uwar
mijinta bata sonta. Yanzu ya dace ace ummi
tazo ta zazzageni? Jiya ita da kannenta da
kyar aka fitar dasu daga gidan nan wai sai sun
dake ni. Har da cewa yadda na raba zamanta
da mijinta nima zamana da mijina sai ya kare,
sai in babu malamai a kano. Kinga kenan
malaminta ne ya fada mata ina yi mata asiri.
Ta tabe baki ta harareni tace to ai fitar da
kukayi gidan boka kuka je, saboda yassar
yabiku a baya har yaga inda kuka nufa, shi
yasa ya kai takardar sakinta gidansu. Ko kin
dauka ban gane ki bane munafuka kin san inda
take. Aiko ki tayi kizo ki barbada min wani abu
ko? Na zabura na mike tsaye na dafe kirjina
nace ni?? Wallahi bansan ummi ba ta nan ba
da bazan zo ba. Ba na irin wadannan halayya
kuma ba da wata manufa nazo ba. Tace dani
fita daga gidan nan kafin in tara miki jama'a.
Kuma duk ranar da kika kuskuara kika hadu da
yassar yace sai ya balla miki kafa, tun a
sakandire kike yi mata hudubar tsiya, yasan kin
tsane shi, shine kika biyo ta har gidan aurensu
kika kai ta gidan boka, wato a kashe shi kuci
gado ko? Tunda nake a duniya ba a taba yimin
cin mutunci, kazafi da wulakanci irin na
wannan ranar ba. Duk irin gulmace gulmacen
nan da ake yi a lungunmu tun ina yarinya ba
ataba cewa ga abin da aisha farida tace ba.
Lalli na jefa rayuwata cikin wani mawuyacin
hali saboda son dr shureim imran. Na gaggauta
ficewa daga gidanta kafin ta tara min jama'a
kamar yadda ta fada, kuka nake wiwi na hau
acaba ba tare da nasan inda na nufa ba. Sai da
dan acaba ya tambaye ni sau uku hajiya ina
zan kaiki? Sannan nace ka kaini gadon kaya.
Gidansu maryam ahmad kenan. Ita ma inje inji
halin da take ciki da dr shureim dinta. Duk da
haka ban daina sonsa ba. Maryam ahmad tayi
mamakin ganina, amma ganin ina fara'a ta san
lafiya kalau kenan. Tace dani shegiya aisha
farida umar daga ina kike, ba ki koma gida ba
ne har yanzu na ganki da uniform a jikinki?
Nace ke dai bari, yau bana jin komawa gida da
wuri, zumunci nake ji, zuwa nayi in gaishe da
su mamarki. Sai taji dadi taja hannuna har
dakin mahaifiyarta muka gaisa, na gaisa da
kannenta da 'ya'yanta biyu wanda Allah Ya
yiwa mijinta rasuwa ya barta dasu amma fa da
dimbin dukiya. Muka koma dakinta muka zauna
akan wani makeken gado, ta kunna mana AC
yayin da ta dinga kwallawa 'yan aikin gidansu
kira suna kawo min abubuwa kala kala kamar
su juice, kayan marmari, cincin da cake. Sai
taga duk na kasa ci sosai, ina yawan yin shiru
idan tana magana kamar hankalina baya tare
da ita. Sai ta zungureni nake dawowa
hankalina, na rasa yadda zan dauko mata
maganar dr shureim domin kada ta zargi wani
abu ta gano saboda zancensa na zo gidansu.
Domin ban taba zuwa ba gidansu haka kawai
ba, sau daya na taba zuwa kuma daga
makaranta muka zo muka yi mata gaisuwar
mijinta, da yake gidanta na kallon gidansu ne.
Muka shigo nan ma muka yi mahaifiyarta, to
anan na san gidansu. Da kanta ta dauko min
hirarsa tace baki tambayeni likitana ba dr
shureim. Sai na zauna dai dai nace yaya akayi?
Ki bani labari, akwai cigaba ko? Tace wanne ci
gaba ni da tun kafin aikin da na rabawa
malami bai je ko ina ba abu ya dagule gaba
daya, nace to su daina adduar yafi karfina. Dr
shureim yafi karfin ya kwanta in taka shi da
takalmin kafata, kinji. Anya mutumin nan
haifarsa akayi ba tikowa yayi daga sama ba?
Ace mutum ya hadu ta ko ina babu aibu a
tattare dashi? Sai naji na kara tsanar kaina, na
fada cikin shamulalliyar murya, me ya faru?
Tace mutuminki na same shi a ofis dinsa
wancan sati, malamina ya bani laya na kunshe
a karkashin harshena wai in dai da layar nan
duk abin da nace masa ya zauna babu musu.
Bayan turarukan da na dume jikina da goshina
dasu, wasu masu wari kamar na 'yan bori, ni
kaina sun isheni da wari balle shi dan gayu. Ina
shiga kaina tsaye ko fargaba banayi saboda an
bani tabbaci, ni kuma na yarda da cewar na
same shi na gama kamar yadda suka bani
tabbaci. Shi da wata likita mace ina jin dai
daliba ce, bata gama ba. Ta cika tayi taf kamar
zata fashe saboda fushi. Ta wani galla min
harara nima na harare ta saboda abin da ya
kawo ta shi ya kawo ni. Da na gaishe su babu
wanda ya amsa sai na sami kujera na zauna a
kusa da ita, shima yana zaune a kujerarsa. Ya
juyo ya dubeni sarai sannan ya dukar da kansa
yaci gaba da rubuce rubucensa. Ya gama ya
mika mata takarda, gami da cewa Allah Ya
sawake jeki. Ta tabe baki ta dubi takardar da
alama magani ya rubuta mata sai tace inje in
sha wannan kenan? Ya ce eh In sha Allah
kurajen zasu warke. Sai tace doctor muje ka
kaini chemist din mana, nina fi so ka tabbatar
masu kyau ne. Sai ya bata rai yace ba aikina
bane in rubuta miki magani, kuma in raka ki
zabar miki wanda zaki saya ba, komai a rubuce
yake zasu karanta su baki. Tace kaki zuwa ka
duba ni a gida, kwanana biyu ban fito ba har
waya nayi na fada maka. Na turo maka sakon
adireshina kaki zuwa. Sai ya harare ta yace
bani da lokacin zuwa duba dalibaina don basu
da lafiya. Ta sake turo baki tace amma ai
daliban daban daban ne, ba daya nake da
sauran ba. Ya daka tsawa ya zazzare mata ido
yace dalibaina dukka daya suke, daidai kike da
wannan. Ya nuna ni, ita kuma ta wurgo min
harara, nayi murmushin jin dadi nima na harare
ta sama da kasa. Yace idan baki da abin da
zaki fada min mai ma'ana game da karatunki ki
tashi ki tafi, kada ki kara shigo min ofis. Ta fice
sai ya juyo wajena ya tambaye ni cikin fushi,
ke kuma fa? Menene? Ina fitowa na kira
malamin da ya bani laya da turaren nan mai
daga hankali don wari kamar na 'yan bori.
Yana daukar wayar sai yace malama an sami
nasara kuwa? Nace nasarar me mutum kamar
zai mare ni? Sai yace to an sami kuskure ne
daga wajenki ina ganin baki yi yadda nace ba.
Nace komai daidai nayi banyi kuskuren komai
ba. Yace yaushe zaki zagayo sai in sake
bincikawa muga ta hanyar da zamu sake
bullowa kuma? Nace Allah Ya sawake in sake
kashe wani kudin bayan wanda na tula maka
na baya har da yankan rago amma a banza.....
Kafin in rufe bakina ya kashe wayarsa, nayi ta
kira har yau a kashe. Ko yau ma na gwada a
kashe, yaga na gane shi dan damfara ne babu
abin da ya iya. Haka nabi duk sauran malaman
naci musu mutuncu sukayi ta kame kame, sai
yanzu na gasgata cewar malaman zamanin nan
sun raina wa mata wayo, sun mayar dasu
jahilan karshen zamani. Idan kura tana
maganin zawayi tayi wa kanta, ke kina ganin
malaman kinga wahalallu masu matsala sun
kasa maganin matsalarsu, wai suce zasuyi wa
wani maganin matsalar su, sai suyi ta canke
canke don basu ma san ya ake duban ba. Ai ni
na dawo daga rakiyarsu na goge lambar
kowannensu, ko sun kira ni tsuye su nakeyi, sai
su waya da sauro. Ko wata na gani zata bata
lokacinta wajen bin malamai zan hanata sai dai
idan taki yadda in kyale ta, idan taje taga uwar
bari zata dawo da kanta tayi min bayani. Duk
wadannan bayanai da maryam keyi tuni sun
ragargaza min zuciya, kwakwalwata ta riga ta
dau gobara, na rike kai kawai tamkar mai
ciwon kai yayin da na sulale na kwanta akan
gadonta tamkar sumammiya. Na yarda da
cewar komai ya sami bawa rubutacce ne, in ba
haka da ya za'ayi tun farko inji wadannan
labarai akan malamai kuma in dauki
zunzurutun kudi in kai wa wani? Nace a raina
me yasa na fara zuwa gidan ummi neman
shawara banzo wajen khadija da maryam sun
fada min halin malaman zamani ba? Tun daga
lokacin na tabbatar kudin sun mula kuma ba
zan sami dr shureim ba. Maryam labari take
bani kala kala, amma bana fahimta ina can ina
tunanin abin da zanje in tarar a gida, haduwata
da uwani mai adashe da sauran makoftan da
na ciyo bashi, sannan bayanan da zanyi wa
yaya hussaini in da naje na kai dare bayan tun
karfe biyu na rana muka tashi.
A gidan su maryam nayi sallar magriba, na yi
ishai muka ci abincin dare. Taga bani da niyyar
tafiya sai ta fara mamaki, tana jero min
tambayoyi iri iri kasancewar ta sanni ba mai
bin gidan kawaye bane kwata kwata balle tace
na saba daman. Sai da na fuskanci har ta fara
gyangayi , tara da kwata na dare sannan na
fara haramar tafiya gida ba don naso ba,
saboda niyyata sai karfe goma sha daya na
dare zan koma gida kafin nan kowa yayi bacci.
dole na fito ta raka ni kofar gidansu na hau
babur na tafi. Ina tafe ina adduoi har na isa
unguwarmu, daga nesa da gidanmu nace mai
acaba ya sauke ni, don bana so 'yan gidanmu
suji karar babu na san idonsu yana kan hanya
suna zuba idon dawowata. Na biya dan acaban
kudinsa yayin da nake tafiya tamkar hawainiya
ina yi ina waige waige tamkar barauniya. Da
sanda na shiga zauren gidanmu naci sa'a babu
'yan matan gidan masu zance a zaure da
samarinsu. Sai na leka tsakar gidan, nan ma
ban ga kowa ba. Sai na cire takalmana na rike
a hannuna ina sanda dana zo giftawa ta
windown dakin uwani sai na tsugunna nayi
duku duku na wuce don kada taga giftawata,
najiyo motsin mutum a daki ina kyautata zaton
ba ta yi bacci ba. Da yake babu wuta sai
hasken fitilar kwai da kyandira zaka dinga
hangowa a dakunan don haka na hango kyallin
kyandir a dakin abida ina hango inuwarta a
tsaye jikin labule, sai dai ba zan tantance abin
da takeyi a tsaye ba. Na duba kofar dakin sai
naga takalman yaya hussaini da alama ya
dawo, nan da nan tsoron da nake ciki ya karu.
Nayi maza na tura kofar dakina na shiga na
iske ta shimfidar da 'ya'yanta ta rage hasken
fitilar kwai a gefe. Shiga ta dakin ke da wuya
ko jakata ban ajiye ba naji motsi a kofar
dakinmu, nan da nan na tsuguna na takure a
lungu. Sai na sankare saboda firgici. Abida ce
ta shigo hankalinta a tashe, tana ambaton
subhanallahi, yaya zanyi yau. Tana rufe bakinta
sai muka hada ido yayin da zaka dinga hango
mamaki a cike da fuskarta gami da firgici. Ni
kuma ina tsugunne ina kokarin daidaita
numfashina domin na shide, don tsoron yaya
hussaini da uwani a tunanina daya daga
cikinsu ne. Aisha farida lafiya? Yaushe kika
dawo? Ina kika shiga yau tun safe? Abida ce ta
jero min wadannan tambayoyi masu wuyar
amsawa. Na mike tsaye a sanyaye ba tare da
na san abinda zance mata ba. Ta sakke kallona
tace da ban ganki ba yanzu da kin jawo min
masifa yau, saboda yanzun nan yayanki ya
shigo ko minti biyar baiyi da shigowa ba, ya
shigo da ciwo a kafarsa sun fadi akan babur
shine yace in taso ki, ki rubuta masa allura ko
maganin da zai sha ko ki dauko akwatin
taimakon gaggawa (first aid box) ki zo kiyi
masa dressing. Na kasa ce masa bakya nan,
shine na shigo nan ina tunanin abin da zance
masa. Ina kika shiga kika sa hankalina ya tashi
ko abincin dare banci ba? Me yake faruwa
tsakaninki da uwani tayi ta zuwa nemanki
ranta a bace tunda rana? Na zazzare ido nace
me tace miki? Abida ta girgiza tace nayi nayi
ta fada min dalilin nemanki din da takeyi, sai
tace inkin dawo in tambayeki ita ba zata fa.
Ranta fa a bace har zage zage nake jiyowa
tanayi daga dakinki. Ke kuwa aisha farida me
ya hadaki dasu uwani ke da ba a zama a yi
gulmar wani dake, me ya kai ki tsoma baki a
maganarsu? Nasan wata gulma suka hado aka
ce dake a ciki, to ni shawarar da zan baki gobe
da sassafe kafin ki fita kije ki samu uwani ku
sulhunta, idan kinsan kin fada ki basu hakuri,
idan baki fada ba ki wanke kanki tun kafin
yayanki yaji abinda yake faruwa yaci miki
mutunci, kinsan halinsa. Duk kin susuce a
kwanakin nan kin canja halinki sai kiya ta nuku
nuku kamar mara gaskiya. Nayi shiru ina
sauraronta yayin da na cire kayan makaranta
na saka doguwar rigar baccina na saka katon
hijabi na dauko 'yar akwati na wuce gaba, tana
tsaye tana kallona cike da mamaki da takaici.
Nayi sallama a kofar dakinsu, yayi min izini na
shiga, na durkusa na gaishe shi yayin da ya
miko min kafarsa naga ciwon nayi masa sannu
da adduar Allah Ya kiyaye gaba. Sannan na
bude akwatin na shiga aikin saka iodine da
auduga. Ita kuwa abida tana can tana kinkimar
'ya'yanta daya bayan tana kai su fitsari. Naga
gama masa yayi min godiya na fito. Har yanzu
abida na dakina tana jirana bata gama jero min
tambayoyin da suka cika zuciyarta dam! Ta
dube ni ta yatsune fuska tace baki fada min ba
fa in da kika je ko daman kinsan da maganar
su uwani shiyasa baki dawo gida da wuri ba?
Na bata rai na turbune fuska nace ni ba
wannan bane ya tsayar dani, bayan mun tashi
daga asibiti aka ce mu dawo za'ayi mana
darasi daga karfe hudu zuwa shida, wani sabin
likta ne zai gabatar da wata sabuwar cuta
shine naga ba zan iya dawowa gida ba in sake
komawa da yamma ba, sai nabi khadija sani
gidansu da yamma muka koma, bamu baro
asibiti ba sai da karfe bakwai ana sallar
magriba, tace inzo gidansu idan nayi sallah sai
in wuce. Shine kuma muka zauna muna hira
bansan dare yayi haka ba. Abida ta tabe baki
da alama ba ta yadda da bayanai na ba. Ta
sake dubana tace aisha farida me ya hadaki da
musbahu kuma shima ya dinga aiko wani yaro
da wasika, zuwansa biyu. Nayi nayi ya bayar a
ajiye mike yace a'a, ance hannu da hannu zai
baki. Sai na sake gigivewa na hau kame kame
nace musbahu kuma? Meye hadina dashi? To
ina jin bani aisha faridar ba. Abida tayi
murmushin takaici tace kila na fara zama
kurma har a ambaci aisha farida inji ba daidai
ba. Babu abinda zance miki tunda boye boye
kike yi min tun yanzu. Sai dai kiyi hankali da
mutane, ki kuskuri bin shawarar batattun
kawaye, ki rike mairaici da talaucinki. Ta juya
ta fice ta rufo mana kofa. Na sulale na kwanta
na dora hannu aka ina juye juye, sai dai ban
fasa karanto innalillahi wainna ilaihir rajiun ba.
Yadda naga rana haka naga dare, barci ya
gagareni. Fargaba da tunanin haduwata dasu
uwani ta gallebe ni. Haka na kwana ban rintsa
ba saboda tashin hankali, don haka da asuba
kiran sallar farko na mike na shiga bandaki
nayi wanka, duk da sanyin ruwan ban damu da
saina dumama ba, na fito nayi sallar asuba na
kakaba kayan makaranta. Na dauki jakata na
dauko biro da takarda na rubutawa abida
wasika na ajiye takardar a bude akan
tabarmata yadda zata gani daga shigowarta.
Na fita daga dakin ina sanda tamkar barauniya
nayi sauri na fice, da yake kofar gidan a bude
take maza masu zuwa masallaci sun bude. Na
rufe fuskata saboda kada inci karo da mazan
gidanmu, duk da banji motsin fitowar yayana
ba, daga dukkan alamu kafar ta matsa masa
da ciwo tunda bai fito sallar asuba ba, dan
baya fashi in dai lafiyarsa kalau. Sai nayi ta
tafiya da kafata sabida rashin babura
kasancewar gari bai waye ba duku duku ne. Na
dade ina takawa da kafata sannan Allah Ya
jeho min mai babur na hau, mun dade da fara
tafiya ba tare da nasan inda zance ya kaini ba.
Ya sake tambayata malama ina zan kai ki? Da
farko nace masa asibitin aminu kano, har
munyi nisa na canza shawara nace ya kaini
jakara, umguwarsu ummi wato gidan iyayenta.
Muka isa kofar gidan na sauka daga kan acaba
sannan na biya shi kudinsa. Abinka da cikin
gari 'yan gargajiya basu san baccin safe ba
kowa ya tashi ya shiga safgoginsa. Mai kosai
ta ta fara suya, masu waina suna danawa.
Haka masu koko da masu shayi da biredi sun
fara tafasawa. Duk inda ka waiga yara ne
dauke da 'yan kwanuka a kansu an aiko su
sayan abin karin kumalllo. Na shiga cikin
gidansu ummi cike da fargabar abinda zanje in
tarar, ummin na iske a tsakar gida ita kadai ta
saka buta a gaba da alama alwalla za tayi,
tunani da damuwa sun hana ta sukuni. Ta
buga tagumi kamar mai tunani yayin da
idanuwanta sukayi luhu luhu. Tayi matukar
firgita data daga ido ta dubeni , ta cika da
mamakin ganina a daidai wannan lokacin. Ta
fada cikin firgici aisha umar lafiya? Sai na fara
zubar da hawaye shar shar shar daga
idanuwana. Ta mike tsaye da sauri taja
hannuna zuwa dakin da take kwana, a cike
yake da yara daga dukkan alamu kannenta ne,
yara 'yan kuci kuci da masu dan wayo.
Kowannensu barci yake da munshari yayi da
zarnin fitsarinsu da warin daudar jikinsu suka
daki hancina. Kamar inyi amai, na dai daure na
zauna akan wata dakwalkwalalliy ar katifa da
ummin take kwana don naga 'yarta a shimfide
a gefe. Anan tace in zauna bari taje tayi alwala
tayi salla sai tazo mu zauna. Kallonta kawai
nakeyi tamkar gunki na kasa magana, na dubi
yaran da suke linkaya a cikin fitsari babu
abinda ya dame su. Naji dama nice su nake
linkaya a cikin fitsarin nan da irin wannan
rayuwa da na jefe kaina. Ba jimawa ummi ta
shigo sanye da hijabi da alama ta idar da
sallah ko addua batayi ba sabida rashin
mutuswar dake tattare da ita. A firgice ta shigo
tana sauri kamar zata ci da kai, ta goya 'yarta
duk da himilin fitsarin da ta ci a napkin, zarni
kwar. Tace in taso mu tafi gidan malam. Na
mike da sauri muka fice ba tare da ta leka
dakin mahaifiyarta tayi mata sallama ba. Tafiya
muke fankam fankam tamkar fatake, muna tafe
muna tayar da kura kamar shanu, mu dukanmu
hankalinmu a tashe. Na juya na dube ta nace
ummi malamin nan kuwa yana da gaskiya?
Nifa har yanzu banga komai ba. Ummi ta tabe
baki tace uhmm ke dai bari. Ai shiyasa nake so
muje mu ritsa shi kafin ya gudu, macucin
banza. Kinsan mijina ya sake ni kuwa? Korar
kare yayi min fa. Na zabura na dafe kirji nace
au daman kinsan macuci ne kika kaini wurinsa.
Tace ke dai muje muji abinda zai ce mana. Na
fada a bayyane innalillahi wainna ilaihir rajiun.
Allah ba Ya dorawa bawanSa abinda ba zai iya
ba sai dai bawa ya dorawa kansa. Ina zan
sami himilin kudin da na ranta in biya masu
shi, ummi yaya zanyi? Ummi ta dubeni a
fusace tace to ni kinsan irin zaryar da ake yi
min a gidanmu saboda bashi? Ke dai kawai
Allah ya rufa mana asiri. Na fusata nace babu
wanda ya taba saka ni a tozarci da tashin
hankali a rayuwata irinki. Ta harare ni tace dan
Allah aisha ki rufe min baki, gara kema baki
aure shi ba balle ya sake ki, nifa har da goyo,
na zama bazawarar karfi da yaji. Haka dai
muka tafi muna ta fada a hanya kamar zamu
cinye kanmu a cikin bus. Tana jin haushina ni
har nafi jin haushinta fiye da malamin ma.
Muka iske shi a zaure yana ganawa da wasu
guda biyu da alama hamshakan masu kudi ne,
daga ganin motar da suka zo da ita da kuma
kayan da yake jikinsu. Malam yana ganinmu
sai ya bata rai, bai amsa gaisuwarmu bai sai
bakinsa ne suka amsa. Muka wuce jikinmu a
sanyaye zuwa cikin gidan, da kyar daya daga
cikin matansa ta bamu tabarma muka zauna
sai wani irin kallon banza suke yi mana dan
suna suyar dakwalen kajin da aka karba daga
wajen mutane na sadaka amma suke juyewa a
cikinsu babu wata sadaka. Shi da iyalansa sun
zama tika tika saboda da cin kaji da raguna da
suke karba da sunan za'a rabawa almajirai. Na
zunguri ummi na nuna mata kajin da ido, ta
gyada kai ta fada a hankali tace eh kudinmu
ne, ai yau sai na masa rashin mutunci. Can
malam ya shigo ko kallonmu baiyi ba ya wuce
dakinsa, yayin da matarsa daya ta dinga
wucewa da abinci kala kala tana kai masa,
kamar shayi, kaji soyayyu, wainar kwai da
biredi. Mu dai muna zaune muna kallon ikon
Allah. Su kayi kasonsu a faranti yara da manya
suka dauka kowa yana ci babu ko sala daya da
suka bamu. Malam yaci ya gyatse, yazo ya
wuce ya shige wanka. Ya fito ya shiga daki ya
fesa kwalliya da farar shadda mai kyau sannan
yazo ya wuce ciki daki in da yake ganawa da
baki. Sannan ya aiko matarsa yace ta kiramu.
Muka shiga muka iske shi a tsaye a tsakiyar
dakin, muka sake gaishe shi ya amsa a
gaggauce. Yace daman yau mu kayi daku zaku
dawo? Haushi ya kama mu, sai ummi ta kalle
ni, nima na kalle ta sai ta murguda baki tace
yau ne laraba ko? Kuma yau kace mu dawo. Ya
kalli agogo yace kuma ce muku nayi kuyi
sammako? Ummi ta fada a fusace, kamawa
tayi ka ganmu yanzu kasan ba lafiya ba. Ni dai
ina zaune a lungu nayi kuri ina kallon irin
wannan damfara kiri kiri, a lokacin da zai karbi
kudinmy yana fara'a yanzun da muka zo karbar
aiki rai ya baci. Ummi tana durkushe tana
kokarin sakko da goyonta. Sai yace ba sai kin
sauke goyonki ba yanzu zan sallame ku akwai
inda zanje don sauri nake yi. Ummi tace ko
yanzu zaka sallame mu ai na sakko da 'yata
tasha nono ko? Tunda ta farka tana kuka. Yace
meye ma yake tafe daku? Ummi ta waigo ta
sake dubana tace kinji ya manta ma. Saina
sankare a zaune na tabbatar mun fada hannun
mayaudati kamar yadda kawayena khadija da
maryam suka fada. Ummi ta sake cewa malam
gaskiya komai ya kwabe tsakanina da mijina,
har ya sake ni. Ga kawata ma taji shiru bai zo
ba. Yace kuje zan bincika naga abinda yake
faruwa, amma aiki dai na gama. Ummi tace
wanne bncike kuma, kai da ka mance abinda
muka fada maka. Ya zazzare mata ido yace ke
ba'ayi mana tsiwa ana kibi a hankali. Ummi ma
ta zare masa ido tace tsiwwa ko zance
gaskiya? Ni dai ba zan gidan nan ba sai an san
abin da za'ayi, kudin da muka biya a banza
kenan, bashi muka ciyo muka kawo maka.
Aisha farida kiyi magana kyayi shiru. Na fada a
sanyaye mai zance ummi? Ya jawo wata jakar
leda a fusace sai ga daurin rubutu kashi kashi,
ya miko min daya ya mikawa ummi daya, ya
sake kwance wata ledar ya miko min laya daya,
ya mika mata daya. Duk iri daya ce. Yace kuje
kusha rubutun nan a tsaye, sannan ku kasance
layan nan a jikinku sai kuyi kokari ku hadu da
mazan da kuke so, ku tambayesu duk abinda
kuke so daga gare su zasu yi muku. Ummi ta
karba ta tabe baki tace mu fa ba wani abu
muke nema a wajen mazan ba illa soyayyarsu.
Yace to ai haka nake nufi ko soyayya ko kudi
duk zasu baku. Na zuba abubuwan daya bani a
cikin jakata na mike tsaye nace da ummi taso
mu tafi. Ta mike a fusace tace zamu tafi
malam, sai dai gaskiya idan bamu ga canji ba
zamu dawo, asan abinyi dan bangane irin
wannan aikin ba. Muka fice yayin da ya bimu
da harara, muka fito tsakar gida dukkanin mu
rai a bace. Matansa sunyi carko carko suna
kallonmu domin suna jiyo duk abubuwan da
ummi take fada. Ta harare su tace Allah Ya isa
kudinmu da ake damfarar mu ana cin kaji, ko
wacce shegiya tayi bul- bul da abincin haram.
Ni dai nayi wuf na fice kada a biyo mu da duka,
har zaure suka rako ummi suna zaginta tana
zaginsu. Naja hannunta muka tafi, a hanya ta
fashe da kuka don takaici, ni kukan ma na kasa
yi sabida tsananin tashin hankali. Tace dani
aisha kinga macutan malamai ko? Wallahi ni
ban taba kula da cutar da wannan dattijon yake
min ba sai yau. Duba kiga yadda komai ya
dagule mana. Nayi ajiyar zuciya nace yanzu
ummi meye abinyi? Tace kije wajensa ki gwada
ki gani bayan kin sha rubutun kin daura layar.
Nima yanzu gidan yassar zanje in gani ko zai
kula ni, idan abinda ya bani bai yi aiki ba
wallahi sai na dawo na tarawa malamin nan
mutane. Nace kina ganin wannan rubutun da
layar daya bamu ta gaskiya ce? Ta wa da naki
fa iri daya ne, babu wani suna daya tambaya
balle ace kowa daban, rubutun ma daga gani
ba namu bane saboda baiyi niyyar bamu komai
ba sai da yaji kince babu inda zakije idan baiyi
wani abu ba sannan ya bamu. Tace ke dai
muje mu gwada mu gani. Mukayi sallama na
hau acaba zuwa asibitin malam ummi kuwa ta
hau bus zuwa unguwar zango gidan yassar. Ina
sauka na bude jakata na zaro kullin runutu na
tashi tsaye kamar yadda ya umurce ni na
shanye, yayin da na ciro layar nan na damke a
hannuna na nufi ofishin sahibina. Ina mai
karanto adduoi don neman dacewa. Zuciyata
cike da fargaba. Na tura kofar ofishin a
sanyaye gami da yin sallama, zazzakar
muryarsa ce ta amsa sannan na tura kai na
shiga. Kallo daya yayi min ya dukar da kansa
kasa bai sake dagowa ba yaci gaba da rubuce
rubucensa. Na gaishe shi ya amsa a shelake
yayin da fuskarsa babu annuri. Na dade a tsaye
bai ce dani komai ba kuma yaki dagowa ma ya
kalle ni. Nayi ajiyar zuciya na tambaye shi a
tsorace dr lukman ya zo kuwa? Da yazo da
baki ganshi ba. Amsar da ya bani kenan. Nace
likita ina da tambaya game da kurajen fuska.
Sai yace dani ke fita ki bani wuri, nan ba
ofishin dr lukman bane, ya koma ofishinsa a
room 8 an gama masa gyaran, kada ki sake
shigowa nan nemansa. Nayi sadan sadan na
fice, na dade a tsaye a bakin kofar daga waje
ina takaici tamkar in rusa ihu. Sai wata zuciyar
ta raya min ko in saka layar a bki in tauna zata
fi aiki. Sai na zura ta a baki ina taunawa na
sake tura kofar na zura kaina ciki. A tsaye a
tsakiyar ofishin na iske shi yana duba wani
littafi a jikin durowar littattafan dake kusa da
bakin kofar. Nace dan Allah likita zan iya bar
ma sako ka bawa dr lukman? Naje ofishinsa
baya nan..... Ban rufe bakina ba naji ya banko
kofar ya rufe booom saura kada ya bame da
fuskata, ba dan na daka tsalle nayi baya ba,
daya illata ni. Tunda na kalli kofar waje
bansake waiwayr ofishinsa ba, na saka a raina
ni dashi har abada koda kuwa zan mutu banyi
aure ba a duniya dan wannan wulakancin ya
isa. Naji na tsane shi na tsani kaina. Na tsani
ummi da ta saka ni a hanyar halaka kuma na
tsani malamin daya cuce ni ya tagayyara ni. Na
toho da layar daga bakina na farke ta saiga
takadda a ciki babu abinda yake ciki sai zanen
wani hatimi mai gida gida an rubuta alifun,
ba'un, ta'un kawai aciki. Na fusata na yayyaga
kuci kuci na watsar yayin da kuka ya turnuke
ni. DUK KYAN TAKALMI 14 Kawata ummi
wacce na taba baki labari tana son wani
malamin mu a sakandirw abdulyasar shi kuma
baya son ta amma daga baya ya fara sonta har
ya aure ta, ita na tuntuba don ta bani shawara.
Sai tace dani malamai ne suka yi mata aiki,
dole akayi masa yazo ya aure ba a hayyacinsa
ba. Don haka sai ta jani wajen malaminta ya ce
in kawo masa naira dubu ashirn da biyar zaiyi
min asirin da dr shureim zai zo har inda nake
da kansa, ya aure ni. Dogon salati abida ta
dauka ta dafe kirji tace farida boka? Me ya
kaiki bin bokaye akan wannan 'yar karamar
matsalar? Sai na daga ido da sauri na dube ta,
ina mamakin yadda ta ambaci matsalata 'yar
karamar matsala. Nace a raina lallai abida bata
san yadda dr shureim take ba da yadda
halayensa suke ba shiyasa take ambaton haka.
Abida ta dora hannu aka tace innalillahi wa
inna ilaihir rajiun. Aisha farida kinyi kuskure.
Wai shin ina wayon nan naki? Ina dubarunki?
Ina iya zama da jama'ar da kika koya daga
wajen magabatanki? Ai wannan matsalar taki
karama ce. Ke kika zamar da ita babba gashi
kin cuci rayuwarki duniya da lahira. A duniya
kin jawowa kanki bashin da zai kaiki zuwa ga
kotu a daure ki, kin dauko hanyar rugurguza
karatunki. Sannan kin taba lahirarki domin
ibadae ki ta ragu saboda damuwa da kika jefa
kanki, kinje wajen boka mai duba wanda Allah
Ya haramta, duk wanda yaje wajen mai duba,
mai zuba wuri ko mai bugun kasa kuma ya
gasgata abin da ya duba ya fada masa tabbas
bashi da sallah har kwana arbain , Allah ba zai
karba ba. Idan kika mutu a tsakanin wadannan
ranakun me zaki cewa Ubangijinki? Kin zama
makaryaciya domin karairayi iri iri kike
shirgawa wanda ada ba halinki bane kuma
kinsa makomar makaryaci wuta ce. Baki kyauta
min ba farida da baki fada min matsalarki ba
har sai da komai ya cabe. Na girgiza kai nace
na hakura da dr shureim yadda iyayena suka
bar duniya na san na rabu dasu har abada
haka na rabu da shi daman bai san abinda
nake yi ba. Wallahi anty abida ba da ganfan na
dorawa kaina sonsa ba haka na tsinci kaina,
nima ba da son raina ba. Abida tace haba haba
kamar yaya zaki hakura dashi bayan wadannan
bala'I da kika fada a dalilin sonsa ai ba zai tafi
a banza ba. Nayi miki alkwarai da izinin Allah
(SWT) sai kin sami soyayyar dr shureim cikin
ruwan sanyi. Na kasa kunne ina sauraron
maganar abida tamkar tatsuniya. Na dauke ta
a matsayin mai iya zance don hankalina ya
kwanta kawai. Duk da nasan babu abin da ya
gagari Allah, amma abin da kamar wuya wai
gurguwa da auren nesa. Abida ta luta da
tunanin da nake yi a zuciyata ta ga alamar ban
yarda da abubuwan da ta fada min ba. Tace
aisha farida kin manta da yadda akayi na auri
yayanki hussaini? Kin manta ra'ayinsa na son
girma ba zai auri kanwarsa ba a lokacin da
iyayenmu suka yi sha'awar hadamu aure yake
kokarin bijirewa? Kin manta yadda muka fara
zama dashi a gidan nan, ni dake muna
tsoronsa ko muryarsa muakji jikinmu sai ya
dau rawa muna guje guje? Yaya kika ga
zamana dashi a yanzu? Bari in fada miki
abinda baki sani ba farida, yayanki hussaini a
tafin hannuna yake yanzu idan naso in daga shi
sama, idan naki sai in kifa shi kasa ya fado.
Yaya hussaini a halin yanzu baya iya bacci
idan ina fushi dashi sai ya bani hakuri na
hakura sannan hankalinsa yake kwanciya.
Hussaini baya boye min komau na game da
samunsa, baya boye min duk halin da yake ciki
na game da abokan sa zuwa danginsa balle
'yan matan waje domub mazan zamaninan
ba'a rasa su da 'yan matan zamani, ko basu ce
suna sonsu ba su 'yan matan zasu kawo
kansu. Ki tambaye ni ya akayi haka ta faru? Ta
ina na samo kansa? Farida wallahi ban taba
zuwa wajen wani boka ko malami ba nace ina
neman a mallake min hussaini. Mutane suna
mamakina yadda nake tankwasa hussaini yake
yin abinda nake so, har wasu kawayena da
'yanuwana suke tsokana ta wai ina hada su da
malamina wanda ya tankwara min hussaini.
Idan na fada musu ban taba zuwa wajen wani
malami ba a rayuwata sai suki yadda. Aisha
farida bana addua har karshen rayuwata in
taka kafata wajen wani malami ko boka don
yayi min adduar mallaka. Ina daga hannayena
sama in roki Allah Ya mallaka min mijina, mu
zauna lafiya, yasoni kamar yadda nake sonsa.
Na girgiza kai nace na fada cikin kuka anty
abida na hakura da dr shureim saboda bai san
halin da nake ciki ba, mutumin da baya kallon
fuskata baya amsa min gaisuwata, ta yaya zai
soni? Kawayena guda biyu har mota gare su
kyawawa ne, ko khadija bata fini kyau ba.
Maryam ta fini kyau suma dole suka gaji da
wulakancinsa suka hakura dashi. Na rasa
yadda zanyi in daina sonsa duk da adduoin da
nake kwana ina yi don Allah Ya yaye min sonsa
amma sai karuwa yake yi na fada tsaka mai
wuya, hatta da karatuna ya tabarbare saboda
sau biyu supervisor dina yana zuwa yana duba
ni daga makarantar mu bana nan. Don haka na
san in banyi da gaske ba dole sai na maimata
attachment dinnan wata shekarar. Ko a littafi
ban taba karanta labarin wacce ta fada irin
wannan matsananciyar soyayyar da na fada ba,
makauniya kuma gurbatacciyar soyayya don
bai san dani ba balle ya san abinda nake yi ba.
Sai na rushe da kuka. Abida tayi murmushi ta
dafa kafada ta sai ta girgiza ni tace haba
farida, ke macece fa, dama akwai wani da
namiji da zai baki tsoro duk haduwarsa? Ina so
ki yadda da kanki, ki dauka duk in da wata
mace ta je zaki iya zuwa, ki dauka duk abinda
tayi zaki iya yi. Ki manta da farar fatar
baturiyar da yake aure, ke bakar fata sai ki fita
a wajensa. Sai naji abida ta fara bani haushi da
wadannan maganganun nata masu kama da
almara. Na rasa yadda zanyi in fahintar da ita
waye dr shureim. Na tambaye ta cike da
damuwa ta yaya zan samu soyayyarsa, har
nafi baturiya farar fata da yake matukar so? Na
fada miki fa bai sanni ba, yana dai ganina daga
dukkan alamu ma ya tsane ni da zara ya ganni
yake hada rai. Abida ta sake yin dariya tace kin
manta kissar matan nan da akayi mana a
makarantar islamiya? Kin manta matar nan da
take wajen malami ta nemi da ya bata abinda
zata mallake mijinta. Kissar ta rabu gida biyu,
an samu sabanin malamai, sabanin malamai
kuwa rahama ce duk dai abu daya suke
nunawa. Na farko aka ce ta da ta fadawa
malamin cewar maganin mallaka take so ya
bata, sai ya umurce ta data je cikin daji ta
nemo masa gashin idon zakanya mai rai da shi
zai hada mata asirin mallaka. Matar nan ta
firgita da jin wannan babban aiki sai tace dashi
malam ina zanje in samo gashin idon zakanya
mai rai ai bazata bari a tsinka ba saboda
fadanta. Cinye mutane take yi. Malam yace shi
dai gaskiya saida wannan gashin zai iya hada
mata wannan magani. Matar nan ta tashi ta
koma gida zuciyarta cike da zullumin tadda
za'a yi ta iya cirar gashin idon dabbar da tafi
kowacce irin dabba a duniyar nan hatsari. Da
farko sai taje kasuwa ta sayi rago aka fede
mata ta dauki himilin nama ta shiga dawa, tana
hango zakanya da 'ya'yanta daga nesa suka
fita neman abinci sai taje bakin ramin ta ajiye
mata naman nan ta gudu ta labe. Da zakanya
ta dawo sai ta iske abinci lafiyayye a kofar
dakinta ita da 'ya'yanta suka taru suka ci.
Washe gari ma haka matar nan ta kawo
gyararren rago ta ajiye mata bayan ta tafi kiwo
ta sake labewa bayan ta ajiye. Zakanya taje
neman abinci ta dawo ta iske abinci har gida
suka ci ita da 'ya'yanta. Haka matar nan ta
dinga yiwa zakanya sai dai su dan matsa daga
bakin ramin don su dawo su tarar da abinci. Da
zarar sun matsa kuwa matar sai tazo ta ajiye
musu sai su dawo su tarar da abinci kamar
kullum. Zakanya ta tabbatar lallai kawai wata
mai kirki da take kyauatta mata dan haka ko
sanda taga matar ta ajiye mata abinci bata
biyo ta nemi ta lahanta ta ba. Ba sai dai tazo
taci kawai. Har suka fara sabawa tana ajiye
mata abinci a gabanta bata guduwa. Har ta kai
ta kawo matar ta fara shafa jikin zakanyar nan
bata motsawa. Tayi ta shafata don sabo har
ranan matar ta samu ta tsigi gashin idon
zakanya ba tare da zakanyar taji zafi ba. Mata
ta kaiwa malam gashin nan ya karba ya duba
ya tabbatar gashin idon zakanya ne mai rai
don yaga jini jini a jikin gashin. Sai ya cika da
mamaki ya tambayeta ta yaya akayi ta samo
gashin? shine ta bashi labarin yadda tayi.
Malam yace to haka zakije ki yiwa mijinki
kamar yadda kika yiwa wannan zakanya babu
wata mallaka da tafi hanyar nan da kika bi kika
saba da zakanyar nan. Na tambaye ta cike da
damuwa ta yaya zan samu soyayyarsa, har
nafi baturiya farar fata da yake matukar so? Na
fada miki fa bai sanni ba, yana dai ganina daga
dukkan alamu ma ya tsane ni da zara ya ganni
yake hada rai. Abida ta sake yin dariya tace kin
manta kissar matan nan da akayi mana a
makarantar islamiya? Kin manta matar nan da
take wajen malami ta nemi da ya bata abinda
zata mallake mijinta. Kissar ta rabu gida biyu,
an samu sabanin malamai, sabanin malamai
kuwa rahama ce duk dai abu daya suke
nunawa. Na farko aka ce ta da ta fadawa
malamin cewar maganin mallaka take so ya
bata, sai ya umurce ta data je cikin daji ta
nemo masa gashin idon zakanya mai rai da shi
zai hada mata asirin mallaka. Matar nan ta
firgita da jin wannan babban aiki sai tace dashi
malam ina zanje in samo gashin idon zakanya
mai rai ai bazata bari a tsinka ba saboda
fadanta. Cinye mutane take yi. Malam yace shi
dai gaskiya saida wannan gashin zai iya hada
mata wannan magani. Matar nan ta tashi ta
koma gida zuciyarta cike da zullumin tadda
za'a yi ta iya cirar gashin idon dabbar da tafi
kowacce irin dabba a duniyar nan hatsari. Da
farko sai taje kasuwa ta sayi rago aka fede
mata ta dauki himilin nama ta shiga dawa, tana
hango zakanya da 'ya'yanta daga nesa suka
fita neman abinci sai taje bakin ramin ta ajiye
mata naman nan ta gudu ta labe. Da zakanya
ta dawo sai ta iske abinci lafiyayye a kofar
dakinta ita da 'ya'yanta suka taru suka ci.
Washe gari ma haka matar nan ta kawo
gyararren rago ta ajiye mata bayan ta tafi kiwo
ta sake labewa bayan ta ajiye. Zakanya taje
neman abinci ta dawo ta iske abinci har gida
suka ci ita da 'ya'yanta. Haka matar nan ta
dinga yiwa zakanya sai dai su dan matsa daga
bakin ramin don su dawo su tarar da abinci. Da
zarar sun matsa kuwa matar sai tazo ta ajiye
musu sai su dawo su tarar da abinci kamar
kullum. Zakanya ta tabbatar lallai kawai wata
mai kirki da take kyauatta mata dan haka ko
sanda taga matar ta ajiye mata abinci bata
biyo ta nemi ta lahanta ta ba. Ba sai dai tazo
taci kawai. Har suka fara sabawa tana ajiye
mata abinci a gabanta bata guduwa. Har ta kai
ta kawo matar ta fara shafa jikin zakanyar nan
bata motsawa. Tayi ta shafata don sabo har
ranan matar ta samu ta tsigi gashin idon
zakanya ba tare da zakanyar taji zafi ba. Mata
ta kaiwa malam gashin nan ya karba ya duba
ya tabbatar gashin idon zakanya ne mai rai
don yaga jini jini a jikin gashin. Sai ya cika da
mamaki ya tambayeta ta yaya akayi ta samo
gashin? shine ta bashi labarin yadda tayi.
Malam yace to haka zakije ki yiwa mijinki
kamar yadda kika yiwa wannan zakanya babu
wata mallaka da tafi hanyar nan da kika bi kika
saba da zakanyar nan. Don haka babu wani
asiri da ci idan babu biyayya, na kaskan da kai,
ba tsabta, ba kalamai mai taushi tsakanin mata
da miji. Nima nan da kika ganni da wannan
kissar nayi amfani har na sami hussaini tamkar
jaririn da sai an dauka, sai an juya, haka zaki bi
ki samu soyayyar dr shureim. Na dube ta a
shelake nace ta yaya? Ta nisa tace zan fada
miki abubuwa guda biyar idan kika kiyaye zaki
sami shureim a garabasa ba tare da kin wahala
ba, kamar kibtawar ido da bismillah. Fardida
duk inda namiji ya kai da ji da kai, da daga kai
karshensa dai mace zai aura kuma dole ta
bautar dashi ko yaki dan kada ya bare sai yayi
dan Allah Ya wajabta akansu dole suyi. Dole ne
miji ya ciyar da matarsa, dole ne tufatar da ita,
dole ya nemo mata muhalli, dole ya kai ta
asibiti idan bata da lafiya. Idan aka sami marar
tsoron Allah wanda ba zaiyi dan Allah ba to
zaiyi ko dan kada duniya ta zageshi. Dan idan
ya bar ta cikin tsumma, ba abinci za'a nuna ta
agari ace matar wane ce baya kula da ita. Dan
haka DUK KYAN TAKALMI, duk tsadar takalmi,
ba za'a daura shi a wuya ba ko a goshi ba,
dole kafa za'a saka kuma a taka a kwata,
shiga daji, a shiga bandaki, a tako kazanta, a
taka bola ko a tako kaya dashi. To haka dr
shureim zai zama a wajenki da izinin Ubangiji,
babu boka babu malam. Naji tamkar tana busa
mi sarewa a kunnuwana saboda dadadan
bayananta, na gyara zama nace meye abu
biyar din da zan kiyaye....? Ban rufe bakina ba
sai muka ji ana buga mana kofa kamar za a
karya, hayaniyar matan da muke jiyowa daga
nesa ya matso bakin kofar dakin mu. Fadi ake
ke aisha farida, ki fito ko a balle kofar nan.
Yaya zakici kudin mutane ki shiga daki ki buya,
ga 'yan sanda nan an kira su, suna kofar gida
za'a tafi dake. Ko ki bude ko a kirawo su, su
shigo ciki su tafi dake. Na dora hannu aka na
fashe da kuka nace anty abida yaya zanyi? Na
shiga uku , yanzu ankwa 'yan sandan nan zasu
saka min su wuce dani ta gaban mutanen
unguwar nan ko kamar wacce nayi sata kowa
yana ganina ko? Hawaye ya zubo daga
idanuwanta itama, sai ta mike tsaye ta tashe ni
tsaye nima, ta dafa kafaduna da hannayenta
biyu. Tace kiyi ta karanta innalillahi wainna
ilaihir rajiun. Ki fita kice da yan sanda su rufa
miki asiri kamar yadda Allah ya rufa musu asiri,
su taimake ki kada su saka ki a gaba, zaki hau
babur kije can sai su same ki acan ba sai sun
saka ki a gaba ba. Nace ai bazasu yadda ba,
sai sun saka ni a gaba kamar wacce tayi sata.
Tace ke dai kici gaba da addua, ki fada musu
hakan zasu yadda. Idan kinje can ki basu
hakuri kice a baki kwanaki biyu zaki nemo
kudin ki biya su, ni kuma anan zan tilastawa
yayanki dole ko rance ne ya fita ya nemo a
biya su kudinsu kaddara ce ta hau kanki kada
ki damu. Kuma koda wasa kada ki sake ki
fadawa wani ko wata abinda kikayi da kudin
nan, dan kada ma labari ya dawo kunnen
yayanki kenje wajen boka, ki barshi a kawarki
kika taimakawa aka yi mata tiyata mijinta
bashi da hali, yafi sauki dan idan muka
kusukura mu ka bari yaji wannan labari sai ya
bata mana rai. Dazu na siyar da samiruna hudu
na biya su maijidda, dahare da dija dillaliya da
kikaje suma kika ranto kudadensu. Wata tace
dari takwas kika karba mata, wata dari bakwai,
wata dubu daya, suma na suka zo suke daga
min hankali suna nemanki danaji kudin ba yawa
sai na aika kasuwa aka karyar min da su nazo
na bibbiya su. Na uwani ne naji kudin da yawa
ba zan iya biya ba. Kiyi hakuri aisha farida, kiyi
ta istigfari game da wajen bokan da kika je,
kinyi wa Allah laifi kuma kiyi ma Sa alkawari
har ki koma gare shi ba zaki sake zuwa ba.
Kiyi ta karanta wannan adduar ta neman biyan
bashi "Allahumma bi jalika an haramika wa
agnani fadhlika amman siwaka". Sannan ta
bude kofa da sauri muka fito saboda bugun da
ake yi ya tsananta. Dandazon matan gidanmu
da matan unguwa da yaransu sun taru suna
kallona. Abida na rike da hannuna muna kuka
muka nufi hanyar waje. Muryar yaya hussaini
mukaji ya daka tsawa mai firgitarwa har sai da
kowa ya firgita. Yace da matarsa ta sake ni in
tafi ni kadai ta dawo daki inje can in karata ni
kadai. Ni da ita muka fashe da kuka. Ta
rungumeni sannan ta lalubo hannuna ta damka
min kudi naira dari biyu. Ta juya ta bar mi, sai
na cigaba da tafiya a sanyaye na fice yayin da
dandazon mata suke biye dani suna ta cece
kuce. Masu bada hakuri nayi, masu neman
ba'asi nayi, haka masu zuga nayi. Uwani kuwa
sai mayar da zancen take yi. In da Allah Ya
taimake ni duk sanda nazo wucewa ta ofishin
'yan sandar unguwarmu sai na duka na gaishe
su kullum, suna ganina suka gane ni nima na
gane su. Kalmar da suka fara ambato itace ah
kece daman? Ke kuwa yarinyar nan mai hankali
meya jawo kika shiga rigima irin wannan? Na
fashe da kuka nace ku taimake ni dan Allah ina
neman wata alfarma guda daya. Sai mai kivar
cike yace yarinya ai babu wata alfarma da
zamu iya yi miki anan, duk wata alfarma sai
dai ayi ta a ofishinmu. Tunda an riga an kira
mu dole mu tafi dake. Nace daman zanbi ku,
bana so ku saka ni a gaba da ankwa ku wuce
dani ta gaban mutanen unguwa yara suna bina
suna kallo kamar wacce tayi sata. Zan hau
babur ya kain ni sai mu hadu a can. Wallahi ba
zan gudu ba. Sai suka yi dariya suka ce idan
kin gudu ma ai zaki dawo, ba gamu a kofar
gidanku ba. Ko zaki shiga duniya ki bar
iyayenki saboda bashin da bai kai dubu ashirin
ba? Suka yi min izini na tari acaba na hau, duk
da babu nisa daga gidanmu. Na dan dade ina
jiransu sannan suka karaso, aka shiga da mu
uku ofishin mataimakin DPO, 'yan kallo aka
barsu a farfajiyar suka ci gaba da gulmace
gulmacensu. Saii a lokacin na gane makiyana
wadanda ada na dauka masu kaunata ne,
wadanda ada bana kulawa ashe sune masu
kaunata, sune masu jimamin abinda ya same
ni, sune masu nemar min afuwa a wajen
wadanda na yiwa laifi, sune masu fada har da
tayar da jijiyoyin wuya idan aka zage ni. Uwani
ta mayar da zance, haj rabi ma haka sai aka
tambayeni shin abinda suka fada gaskiya ne
kuwa? Na amsa nace haka ne, sannan na basu
hakuri gami da yin alkawari zan biya nan da
kwana biyu. Uwani ta zabura tace karya nakeyi
bani da ko kobo, don haka yace a kulle ni babu
ruwansa. Mataimakin DPO ya sake tambayata
haka aka yi? Na amsa masa da haka ne. Don
haka yace aje a kulle ni har sai yayana yazo
yayi belina kuma yayi alkawarin zai biya
sannan a fito dani, idan kuwa yaki zuwa sai a
kaini kotu alkali ya yanke min hukuncin dauri
daidai laifina.
DUK KYAN TAKALMI 2* 1
BABI NA BIYAR Washegari misalin karfe
bakwai saura kwata na safe aisha farida ta
shirya tsaf tana sauraron 'yan gidan su
tashi. Ta hada kudaden nan ta kidaya naira
dubu goma sha biyu ne cif cif tasan dai
uwani zata daga mata kafa tunda sauran
naira dubu biyar ne kacal har zuwa wani
lokaci. Abida ce ta fito kofar daki tayi
hamma tayi mika yayin data murtsike luhu
luhun idanuwanta wadanda suka kumbura a
sanadiyyar kukan da ta sha yi a cikin dare,
ga rashin bacci. Ta tura kofar dakin aisha
farida don ta duba yaranta, tayi matukar
firgita a lokacin da ta ga fararen kayan jikin
aisha farida a tsaye a tsakiyar daki har sai
data daka tsalle tayi kara. Nan da nan aisha
farida tayi magana tace anty abida lafiya
kika firgita? Nice fa. Abida ta dafe kirji tayi
ajiyar zuciya tace aisha yaushe kika dawo?
Tayi murmushi tace ai anan na kwana.
Abida ta tambaya cike da mamaki yaya
akayi kika fito daga wajen 'yan sanda? Aisha
farida ta sake yin murmushi tayi ajiyar
zuciya sannan ta fito da himilin kudin nan
daga aljihun wandonta. Tace kinga na hado
naira dubu goma sha biyu saura naira dubu
biyar. Ai zasuyi min hakuri har in samu ko?
Abida tayi shiru kamar mai tunani yayin da
hankalinta yayi mummunan tashi ta dubi
aisha farida cike da fargaba. Ina kika sami
wadannan makudan kudin a dare daya?
Anya kuwa aisha kin kwana a gidan nan?
Kada ki boye min komai, ni mai baki
shawara ce a gaba daya matsalolinki.
Matsalarki matsalata ce, damuwarki
damuwata ce, haka duk abinda kika yi aka
zage ki a gari bake kadai aka zaga ba, ni sai
na fiki jin zafin zagin. Yadda hankalin abida
ya tashi na aisha fariida sai ya fi nata tashi,
nan da nan ta dago ta kafawa abida ido
tana kallonta yayin da kalma daya rak ta
gagare ta furtawa don tashin hankali. Kan
kace kwabo hawaye ya fara zazzagowa daga
idanuwan ta. Abida ta lura da tashin
hankalin da farida ta shiga sai itama ta fara
hawaye ta fara magana cikin sanyayyiyar
murya. Aisha farida ba wai ina zarginki
bane sai dai ina gudar miki fadawa
mummunan rayuwa a sandiyar dan karamin
bashin nan. Kije ki cuci rayuwarki a banza.
Dole in tuhume ki don nima nasan dole
yayanki zai tuhume ni haka kuma ya
kamata a shariance. Aisha farida ta matse
hawaye ta langabar da kai tace tabbas na
kwana da shirin zaki tambayeni haka amma
ban taba zaton zance a gida na kwana ba ki
karyata ni ba shine abinda ya bata min rai
amma inda zan yiwa Allah godiya shine na
hadu da yaya dazu da tsakar dare ina fitowa
daga bandaki shi kuma zai shiga har ya
ambaci sunana na amsa da alama shima
yayi mamakin gani na. Abida ta gyara
tsayuwar ta da alama taji dan sanyi a ranta
ta dubi aisha farida ta tambaya cike da
zumudi. Yaya akayi kika fito daga ofishin
'yan sanda? Kuma a ina kika samo
wadannan makudin kudi?
Aisha farida tayi murmushi ta jawo hannun
abida suka zauna akan tabarmarta tayi
ajiyar zucia sannan ta gyara zama ta
zayyanowa abida labarin duka abinda ya
faru da ita jiya tun daga sanda ta fita qofar
gida wajen 'yan sanda da yadda sukayi acan
ofishinsu da zamanta dakin da aka kulleta
zuwa lokacin da akayi belinta da kuma
zuwanta fish park harta hadu dasu barrister
mu'azzam da hirar da sukayi
Har zuwa yadda ya bata kudi da kuma
sanda ya kawota gida abida ta gamsu da
labarin Aisha humaira kuma taji dadi har
saida ta daga hannun sama tayi wa Allah
godia ya taimakesu ya basu yadda zasuyi su
biya bashin da basu dashi.kibani kudin nan
sannan ki tashi ki tafi makaranta salin. Alin
basai yan gidan sun tashi sun ganki ba
kuma babu ke babu bawa wasu labarin
abinda ya faru ko labarin inda kika samo
kudi gudun kada yayanki wata rana yaji
yazo ya titsiyeni da tambaya sannan
kibarshi akan kin yi mata tiyata kada ma ki
sake kiyi zancen malam kika kaiwa kudi
koda wasa kibarni dasu ni nasan
Ni nasan yadda zanyi inyi musu bayani kada
kice komai jikin A.farida na karkarwa da
dauki jakarta ta rataya tana gaggawa ta nufi
qofa zata fice abida ta kira sunanta a
sanyaye ta juyo ta kalli abida da cike da
tausayiabida tace kina da kudin acaba ne?
A.farida ta gyada kai tace inada naira 150
ragowar wanda canjin 200 dinda kika banina
hau acaba jiya zuwa ofishin yan sanda.abida
tayi ajiyar zucia tace kiyi haquriki gyara duk
abubuwanda aka wuce ki ki mayar da
hankalinkisosai harsai kin kamo 'yan ajinku
domin anbarki baya.A.farida ta gyada kai
tace insha'allah zan mayar da hankali akan
karatuna na tafi saina. Dawo ta juya a gigice
cikin sauri ta kuwa ci sa'a bata ci karo da
kowa ba a tsakar gida haka qofar gidansu
harta fito unguwarsu sannan ta samu acaba
ya fisgeta sai asibitin malam aminu kano
tana shiga cikin asibiti sai ta nufi bangaren
da pfishin gogan nata yake ba har sauri ta
qara gami da kawar da kai gefe don kada
ma ta kalli bangaren.bata marmarin taci
karo dashi ma balle ta tuna dinbin bacin ran
da ya kimtsa mata a baya ta qudiri niyya a
ranta ita dashi har abada koda kuwa shine
kadai da namiji da yayi saura a fadin doron
qasa.tana shiga aji sai yan aji suka mata
caaa!suna tambayarta ina ta shiga ne ta
bace kwata-kwata ba'a ganinta koba da
lafia ne? kasancewar ramar datayi kuma duk
tayi baqi don wahala.ai kuwa kun san
amsar da zata basu balle ma sun saka ta
akan hanya cewar ko bata da lafia ne? tuni
ta amsa musu da eh bani da lafia ta qara da
cewa harda kwancia a asibiti'',haka tayi ta
bin metron da nurses tayi musu irin
wadannan gunduma-gunduban karairayi su
kuwa suka bita da sannu Allah ya sauwaqe
dole su yarda mana saboda tsananin ramar
da tayi gata daman ba jiki ba.bata yi qarya
ba tabbas data sha jinyar zuci jinya a zucia
kuwa wani lokacin har tafi jinyar jiki ta rame
qurqet saboda tashin hankali.
Daga nan ta duqufa tambayar abubuwan da
kayi bata nan ta dinga kwafar jotin dinda
frnds sukayi akan cuttutuka da yawa ta
tabbatar an wuce ta sosai a cikin satitikan
da take qin zuwa.tambaya take tun qarfi
abun daba ta gane ba daga dalibai ,metrons
da doctrs abun da ya shafa sannan ta
bazama ta koma makarantarsu wajen
malamin da yake alhakin duba ta wato
(supervisor )dinta yazo har sau 2 baya
samunta don haka tana cikin matsananciyar
matsala idan batayi da gaske ba.saita
maimaita attachment din nan next year
hankalin A.farida yayi matuqar tashi a
lokacin da yan ajinsu suka zagayeta ta suna
neman mata mafita kowa yana bata
shawarar abun daya kamata tayi ta shiga
matsancin kokonto ana tantama anya kuwa
har akwai wani bayanin da zata yiwa malam
basiru ya saurare ta yadda ransa ya baci
yana ta fada akan yazo 2X duba ta bai same
ta.hawaye mai radadi ne ya surnano daga
idanunwanta yayin data tuno wanda yayi
mata silar abun daya same ta taji haushin
5r shuraim ya rafe ta .ta cije lebe ta girgiza
kai tace a ranta shuraim na biyewa sharrin
zucia a karo na farko na wahalar da kaina
insha'allah ba za'a sake ba a. Karo 2 zucia
nafi qarfinki yanzu duk inda kika kai ga
hango haduwar dr shuraim bazan saurare
kiba kece kika yi qayatamin shi a rai kika
dinga zuga ni gashi a kusa-kusa zan same
shi kikayi ta zurmuqani a rami har sai dana
yi zurfin da na kasa fita saida aka agaza min
na fito to ba za'a sake ba zanyi yaki dake
har inda qarfina ya qare babu ke babu
hasko min dr shuraim shi daban ni daban
kowa ya tsaya a matsayinsa.ta sharce
hawaye ta miqe ta suri jakarta ba tare da
tayi wa kowa sallama ba ta fice daga
asibitin kai tsaye ta nufi makarantarsu
ofishin malam basiru ta nufa sai dai kash ta
daki gurbi ya fitaa ita kuma tazo abokan
aikinsa suna ce mata yanzu zai dawo-yanzu
zai dawo taki qarewa abun qarfe 12 na rana
sai ga Aisha farida a zaune ofishinsa har
qarfe 5pm dole ta tafi gida tinda bai dawo
ba.
Ranta bace hankalinta a tashe ga qishin
ruwa da yunwa yini guda bataci abinci ba
dadinta ma dai tana zuwa tayi salla sannan
ta dawo tavi gaba da jira domin A.farida
bata wasa da sallarta.ta iso gidansu da
misalin 5:45saida ta hadu da jama'ar
unguwarsu da dama qofar gidansu zauren
gidansu da tsakar gidansu sai suke jin
kunyarta wasu ma basu iya hada da
ita.tana gaishe su suna qasqantar da ido a
qasa tamkar sunga surukarsu sai mamaki ya
rufe ta tana shiga dakin aunty abida ta tura
kai ta shiga kasancwar yay husaini bai dawo
ba kafin abida tace mata wani abu
Aisha.farida ta jero mata tambayoyi zokat
suka mata zucia tace anyi abida lafia yan
gidan nan kuwa?me yake faruwa ne?me
kika fada musu suke kasa hada ido da ni?ko
suna zargina da aikata wani abun kunya ne?
abida tayi murmushi ta girgiza kanta tace
ko daya kada kiyi zargin duk wannan jeki ki
cire kayan makarntarki ki dauki abincinki
kici yana gefen kayan ki kici naga alamar
kina jin yunwa ki saurareni ina zuwa dakin
naki yayanki ne yasani aiki yanzu zan gama
kada ya dawo ya iske ban gama ba ransa ya
baci.A.farida ta fice a sanyaye a zuciayarta
cike da fargabar abun da abida zata fada
mata ta cire kayan makarantarta ta saka
wata yar yaloluwar t-shirt fara da baqin
skirt kan ba kwali ta shinfida yar tabarnarta
ta jawo kwanon abincinta ta bude wake da
shinkafa ne da mai da yaji ga tashin hankali
ga abincin ya sanqare sannan ga
matsananciyar yunwa turawa take da kyar
take hadiyewa maqogwaronta ya tsuke
yayin da hanjin cikinta duk sun kanannade.
Ta miqe da sauri ta bude wani farin bokiti
mai murfi da moda akai shine ruwan da
suka tadana na musamman don shansu ta
debo a kofi ta dao ta zauna tana tura garau-
garau tana korawa da ruwa ta kusa gama ci
sai ga abida ta shigo fuskarta cike da
murmushi tazo gefen Aisha ta zauna yayin
da Aisha tayi qasaqe tana sauraronta abida
tace Aisha. Yay makaranta?yaya kuma
gogan naki likita?nan da nan Aisha ta hade
fuska murtuk daga gani zuciayrta ce ta
dugunzuma da jin kalmar sunan likita abida
bata sami wannan amsar ba don haka saita
sauya hira nan da nan.tace Aisha tayi ajiayr
zucia tace na shigo unguwar nan sai na ga
jama'a musamman mata suna ta kawar da
kai basa iya kallona idan na gaishe su sai
naga sun sunkuye-sunkuye haka dana shigo
gidan nan ma duk basa iya hada ido dani
me yake faruwa ne?abida ta tuntsire da
daria tace ai daman haka rayuwa take
maganinsu nayi''maganinsu kamar yaya?
Aisha farida ta tambaya yayin data ajiye
cokalin da yake hannunta gaba daya ta
tattara hankalinta gaba daya wajen abida
abida ta langwabar da kai gefe tayi shiru
zuwa wani dan lokaci tace bayan fitarki
dazu da safe nayi fiye da mintina 30 ina
zaune ina tunanin qaryar da zan shiryawa
su uwani da husaini yadda zan wanke ki
daga zargi na tshi na shiga daki na iske
husaini sai na fito da kudaden nan ina
qidayawa yayi min tsawa yace ina na samu
kudi da sassafe?
Nace masa ai kudin nan a hannuna ya
kwana tun bayan magrib aka kawo min sai
yace waye ya kawo min?na gyara zama
nace mace mai jegon da Aisha ta taimaka
mata itace ta taso da ita da mijinta suka
kawo kudin da yake Aisha tayi musu waya
ta fada musu halin data shiga a sanidiyyar
bashin data ci don ceto rayuwarta.dole
suma hankalinsu ya tashi a lokacin suka
bazamo suka hado kudin nan 12k suka
kawomin sannan suka je office din yan
sanda suka fito da Aisha ai a gidan nan ma
ta kwana a daki ta labe taqi fitowa sai da
safen nan ta shirya ta fice makaranta
husaini yayi shiru can yace dani ashe da
gaske ne kudin asibiti ta biyawa qawarta,ba
qarya take ba?nace da gaske ne mana me
Aisha zata yi da zunzurutun kudi kudin nan
yarinyar da abin dunia bai dame taba,bata
da buri ko kadan duk abun da ta samo
komai kanqantarsa sai ta godewa Allah.yace
yanzu saura nawa ne cikon kudin nace
saura saura cikon 5k shima sunce zasu je
su nemo su cika a cikin satin nan ma zasu
kawo sai ya miqe ya je ya bude aljihun
rigarsa ya zaro wasu kudade yan dubu_duba
sai ya qirgo 5k ya bani yace gashi idan
wadancan sun kawo sai a bani nima ba
kudina bane kudin qungiya muke hadawa a
office don tallafawa duk wanda ya shiga
damuwa a cikinmu rashin lafia ko aka
yimasa haihuwa ko kuma idan zaiyi aure a
bashi tallafi''na karba cike da murna gami
da durqusawa nayi masa godia bayan na
shirya shi na shirya yara sun tafi nima nayi
wanka na kammala dan aikin gida.hantsi
yayi kowacce ta fito da tabarmarta tsakar
gida ta zauna majalisar gulma ta hadu ta
cika tayi damqam da munafukan mata har
maqota kowacce ta zaro gyale ta shigo taji
inda aka kwana da maganar kudin wajen
Aisha.a wanne hali kike a can ofishin yan
sanda? shaci fadi iri-irihaka mugaye kalamai
ne ke fitowa daga bakunan masu dadin
zance sai sun ga nazo giftawa ma sannan
ake sake daga murya ana ambato
sunanki,harda mai cewa lallai Aisha ta
dauko ruwan dafa kanta a shekara 1 ma
bazasu iya wadannan kudade ba sai dai tayi
zaman gidan yari kawai.
Na dauko kujerata na nufo inuwar da
dandali yake fuskata cike ta da murmushi
na gaishe su wasu ne suka amsa a sheleqe
wasu kuwa sai suka kawar da kai gefe suka
yatsune fuska suka ci gaba da ambaton
Aisha tayi ganganci gobe ma ta qara na
dade a zaune na buga tagumi ina dubansu
ba kunya ba tsoron Allah a gabana basu
daina mugayen furucinsu ba akanki.talaka
ya shiga 3 a duniayar nan maganin abun
kada ka taba kayan wani saika zauna lafia
amma muddin ka shiga gonar wani tofa ka
hadu da wulaqanci Allah yabamu yadda
zamu yi don alfarmar Annabi Muhammad
(S.A.W)''Aisha farida ta karbi salatin suka
qarasa a tare suka shafa ta dafe qirji saboda
tsabagen fargaba ta qagu taji abun da ya far
tace me kika ce musu ke kuma? abida ta
gyara zama tace biyi kisha labari daman sai
irin haka ta same ka zaka su waye jama'ar
da kake zaune dasu su yan gidan nan ashe
haushin abin da kika yi ba ma suke ji ba
suna yi mana baqin cikin ashe daman can
akan irin rufin asirin Allah yayi mana ne
suke adawa.ummulkhairi ta tabe baki tace
ato qarshen alewa qasa qarshen tika-tiki
tik! qarshen qarya dai yazo da anayi mana
yatsuna ana wanka ana qalqale qafa ana
siyowa yara gwanjo suna tsukewa ana yi
mana gani-gani mu ba mu iya kula da miji
ba sai iya bini-bini ana kusa da miji ana
yimasa fari da ido.uwani tace kin manta a
dafa abinci haka kawai sai an zuba kori yayi
qamshi an yayyanka salat da tomatoes da
albasa''Mairo maqoriyarmu tace au irin
wannan iyayin ake yi muku ashe a gidan
lallai kuna shan kallo.
Ummulkhairi tace idan kince kallo ma ai
daya ke nan sai idan miji zai shiga bandaki
zoki ga yadda za'ayi ta kuza ruwa ana
sharewa ana yayyafa abin qamshi kamar fin
mazanmu yayi su da suke shiga da
zarnin''uwani tace kun manta yar gayun
gidan nan wai ita 'yar boko Aisha magana
daya sai an sako turanci goma kullun ana
qalqale kayan makaranta ana goge kaushi
anayi wa manu yan matan gani-gani saboda
suna soya awara a qofar gida su basu zuwa
boko''Aisha ta zubo da hawayen daya cika
mata ido ta girgiza kai anti abida me ya
kawo duk wannan? daman haushinmu suke
ji? abida ta zubo da hawaye tasa gefen
zaninta ta matse tace ke kya fada farida
daman sun dade suna so suci min mutunci
to basu ga fuska ba don bana shiga
harkarsu zunde da yafice kala-kala kullun
suna yimin basu isheni. Kallo ba sai in nuna
ban san suna yiba saboda iya zama da
jama'a.zan gaishe su ko baza su ansa ba.
Zan bawa ya'yansu duk abun dana dafa ko
su basu amsa ba zan bawa 'ya'yansu duk
abunda dana dafa ko su ban basu ba.bana
bari suga hudar da zasu shigo jikina balle
ayi gulmar wata dani haka ban damu da sai
naji gulmata da akeyi ba.bani da lokacinsa
sai lokacin mijina da ya'yana kema bakida
lokacin kanki ma balle na wasu mu ba yan
gari bane amma munfi sy yan garin sanin
jama'ar arziki da samun Alkhairi shine
haushinsu sai yanzu suka sami damar
amayarwa da abun da yake zuciyarsu.yadda
kika ga na zuciyarsu.yadda kika ga na zubo
da hawayen nan sau 1 na sharce da gefen
zanina haka nayi bance komai ba sai na
saka hannuna a gefen zanina na zaro
wadannan kudi na miqawa uwani ta zazzare
ido sai hannunta ya dauki karkarwa ta karba
a sanyaye.tana qirgawa a yayin da
idanuwan masu leqe suka fi nata firfitowa
masu kama baki sunayi haka masu susar
tsohuwar kwarkwata suka fara yi ba tare da
sun san ma abun da suke yi sunyi matuqar
mamakisun razana haka sun ji kunya uwani
da yan tayinta suka kidaya kudi naira 17k ta
cika cif-cif.
Uwani bata iya dago da ido ta dube ni ta
iya ce min komai ba sai nice tambaye ta
nace sun cika ko da saura kudin da farida ta
ranta?ta gyada kai tace sun cika haka suke
nace to ki kaiwa haj rabi kice tayi haquri ba
za'a sake ba yanzu ma qaddara ce Allah ya
aikowa Aisha tayi jihadi ne don ta ceto ran
qawarta data qoqarin mutuwa akan gadon
asibiti zata haihu saboda bata da jini kuma
ba zata iya haihuwa da kanta ba sai tiyata
shine tazo ranci kudin ta kai kafin mijin ya
aiko daga lagos anan aka sami matsala da
bai aiko da wuri har ta kai aka kai ta wajen
yan sanda aka daure.Allah yana bayan mai
gaskia. Allah yana taimakon wanda ya
nemi. Taimakonsa Allah yana duban zuciyar
na gari da mugu kuma yayi hukunci a kansu
tun daga nan dunia da qawar Aisha mai
jego taji labarin halin da Aisha ta shiga a
dalilinta tuni ta taso daga kan gadon asibiti
taje ta fito da farida ta kawo ta gida ta hado
kudin nan da aka ranta Allah ya dubi zuciyar
Aisha yaga kyakyawar niyyarta ya taimaketa
ya fitar da ita daga tozarci da abin kunya.
A gida aisha farida ta kwana, ta tashi da
safen nan ta tafi makaranta taci gaba da
karatunta. Yanzun abinda ya rage shine
idan ta dawo da yamma kuje wajen 'yan
sanda ku tabbatar musu da ta biya kun
janye kara, sai a soke shikenan a zauna
lafiya. Uwani mun gode da taimakon da
kikayi mana, akasi aka samu har ya zama
rigima. Kiyi hakuri, itama ba haka taso ba.
Su dukka suka yi shiru kamar wadanda ruwa
ya cinye su. Nayi murmushi na dube su
daya bayan daya nace ku gafarce ni, daman
ina da matsala daku bansani ba, kuma babu
wacce ta tare ni ta sanar dani? Ai da
tuntuni kun sanar dani halin da ake ciki don
ban san inayi muku laifi ba ma a tsawon
zamana daku, kusan shekaru goma. A
bangarena bani da matsala daku ko kadan,
ina taka tsantsan kada in batawa wani, ina
iyakacin kokari inga na fitar da hakkin
makotaka da Allah Ya wajabta a kaina shine
inyi muku sallama, in gaishe ku duk sanda
muka hadu a tsakar gida, in duba ki idan
baku da lafiya, inyi muku jaje ko gaisuwa
idan kun rasa wani dan uwa ko wani abu. In
taya ku murna idan aure ko haihuwa sun
same ku. Menene yayi saura kuma baya ga
duk wadannan? Ku gafarce, laifi daya ne da
nake muku, kuma ba zan daina ba shine ina
kula da mijina yadda ya kamata, ku kuma
ba kwa so. Nayi alkwari bazan daina tsafta
ba, haka ba zan daina ciwa 'ya'yana ado ba
da gwanjo, haka ba zan daina wankewa
mijina bandaki ba duk sanda zai shiga, haka
ba zan daina sanya curry ba ina dafa masa
dadadan abinci, koda kuwa ace mijinmu
daya ne daku, balle babu hadina daku.
DUK KYAN TAKALMI 2* 2
A gida aisha farida ta kwana, ta tashi da
safen nan ta tafi makaranta taci gaba da
karatunta. Yanzun abinda ya rage shine
idan ta dawo da yamma kuje wajen 'yan
sanda ku tabbatar musu da ta biya kun
janye kara, sai a soke shikenan a zauna
lafiya. Uwani mun gode da taimakon da
kikayi mana, akasi aka samu har ya zama
rigima. Kiyi hakuri, itama ba haka taso ba.
Su dukka suka yi shiru kamar wadanda ruwa
ya cinye su. Nayi murmushi na dube su
daya bayan daya nace ku gafarce ni, daman
ina da matsala daku bansani ba, kuma babu
wacce ta tare ni ta sanar dani? Ai da
tuntuni kun sanar dani halin da ake ciki don
ban san inayi muku laifi ba ma a tsawon
zamana daku, kusan shekaru goma. A
bangarena bani da matsala daku ko kadan,
ina taka tsantsan kada in batawa wani, ina
iyakacin kokari inga na fitar da hakkin
makotaka da Allah Ya wajabta a kaina shine
inyi muku sallama, in gaishe ku duk sanda
muka hadu a tsakar gida, in duba ki idan
baku da lafiya, inyi muku jaje ko gaisuwa
idan kun rasa wani dan uwa ko wani abu. In
taya ku murna idan aure ko haihuwa sun
same ku. Menene yayi saura kuma baya ga
duk wadannan? Ku gafarce, laifi daya ne da
nake muku, kuma ba zan daina ba shine ina
kula da mijina yadda ya kamata, ku kuma
ba kwa so. Nayi alkwari bazan daina tsafta
ba, haka ba zan daina ciwa 'ya'yana ado ba
da gwanjo, haka ba zan daina wankewa
mijina bandaki ba duk sanda zai shiga, haka
ba zan daina sanya curry ba ina dafa masa
dadadan abinci, koda kuwa ace mijinmu
daya ne daku, balle babu hadina daku.
Menene laifin aisha farida kuma a cikin
gidan na, ko kuma ince a cikin unguwar
nan? Hana idanuwanta baccin da take yi ne
take zuwa karbar haihuwarku komai dare?
Ko kuwa allurar da takeyi muku idan likita
ya rubuto muka ta hutar daku zuwa
chemist? Kitson da take yi muku kyauta ko
kuwa ko yawa 'ya'yanki karatun da takeyi,
duk sati ba tare da ko sisinku ba? Taya ku
girki da takeyi, ko kuma rainon 'ya'yanku
da take yi muku koda yaushe shi ya zama
laifi? Gaishe ku da takeyi koda yaushe, ko
hirar da take zama kunayi da ita shine
laifinta? Allah sarki rayuwa, ai kuwa Aisha
farida mutum ce babu wacce bata morarta
a cikin gidan na, koma nace a layin nan
gaba daya. Ummulkhairi na dade da sanin
cewar ke kike wanke kafa kike zuwa ki sami
mahaifiyar musbahi ki caccaka mata karya
da gaskiya don ta tsani aisha farida a
matsayin surukarta, burinki ya cika har sai
da kika haddasa wannan gaba a zuciyar
uwar musbahu, ta tsinewa aurensa da aisha
farida, tace idan dai tana raye ba zai aure ta
ba. Na sani aisha farida ta sani, musbahu ne
ya fada mata shima ya sani. Sai
ummulkhairi ta mike tsaye ta hau
bambamin fada mai tafe da borin kunya
tsagwaronsa. Tana jan Allah Ya isa ba zata
yafe sharrin da nayi mata ba. Na mike
tsaye nima na nuna mata ruwa ba sa'an
kwando bane, haka shiru shiru ba tsoro
bane gudun magana ne. Kalmar da na fada
mata ta karshe daga ita na gaggauta barin
wajen itace kinji dadi, kin raba auren
musbahu da farida, amma baki isa ki hana
Allah Ya bata wani mijin ba, daga wani
bangaren, bangaren da baki sani ba. Kuma
wanda baki da matsayin da zaki taka kiyi
gulma. Ummulkhairi ke da sauran makiya,
ku bude idonku sosai zaku sha mamaki,
zaku sha kallo, zaku ga irin mijin da aisha
farida zata aura idan har muna raye.
Insha'allah sai Aisha farida tayi auren da
babu wacce ta taba yin irinsa a gaba daya
unguwar nan bana a layin nan ba ko gidan
nan Allah yana tare da mu kuma da shi
muka dogara yan gulma suka hau gasgata
maganata suka hau nadama suna fadar
alkhairin Aisha farida data taba yimusu a
rayuwa nan da nan na bar wajen na kyale
su suna ta kame- kame kanka ce kwabo
dandali ya rore ya qare daya bayan daya
suna ta sulalewa suna guduwa saboda
kunya Aisha farida ta riqe baki don mamaki
gami da farin ciki abunda abida tayi.tayi
mata dai-dai ta burgeta tayi murmushi tace
anty abida dama ke iya fada?amma
bantaba ganin kinyi ba?abida tace habah
meye abun burgewa a iya fada kuma?ni
zubar da mutunci ne fada dole ce tasani
sun kaini qarshe ina ruwansu da tsakanina
da mijina idan zancen kudi ne zasu suyi duk
zagin da zasuyi suyi akan haqqinsu ne mu
muka taba su haqqinsu ne muka jawo wa
kanmu amma ace tsaftar dana keyi da girki
dana keyi da tsaftace 'yayana duk laifi ne
ina ruwansu?aida haushi mu ba mijinmu
daya ba balle suce nazo zan kwace musu
miji banzaye,qazamai maimakon suyi koyi
dani saina na zama abar zagi,abar kyama
daqa-daqa dasu sai suyi kwana 3 ba wanka
suna yawo da dauri qirji a tsakar gida ba
kitso bare yankan qumba,bare ayi zancen
su qunshi da turaren wuta ko turaren jiki
basu gyara jikinsu ba ina zasu gyara yara
bare wani miji?
Insha'allah sai Aisha farida tayi auren da
babu wacce ta taba yin irinsa a gaba daya
unguwar nan bana a layin nan ba ko gidan
nan Allah yana tare da mu kuma da shi
muka dogara yan gulma suka hau gasgata
maganata suka hau nadama suna fadar
alkhairin Aisha farida data taba yimusu a
rayuwa nan da nan na bar wajen na kyale
su suna ta kame- kame kanka ce kwabo
dandali ya rore ya qare daya bayan daya
suna ta sulalewa suna guduwa saboda
kunya Aisha farida ta riqe baki don mamaki
gami da farin ciki abunda abida tayi.tayi
mata dai-dai ta burgeta tayi murmushi tace
anty abida dama ke iya fada?amma
bantaba ganin kinyi ba?abida tace habah
meye abun burgewa a iya fada kuma?ni
zubar da mutunci ne fada dole ce tasani
sun kaini qarshe ina ruwansu da tsakanina
da mijina idan zancen kudi ne zasu suyi duk
zagin da zasuyi suyi akan haqqinsu ne mu
muka taba su haqqinsu ne muka jawo wa
kanmu amma ace tsaftar dana keyi da girki
dana keyi da tsaftace 'yayana duk laifi ne
ina ruwansu?aida haushi mu ba mijinmu
daya ba balle suce nazo zan kwace musu
miji banzaye,qazamai maimakon suyi koyi
dani saina na zama abar zagi,abar kyama
daqa-daqa dasu sai suyi kwana 3 ba wanka
suna yawo da dauri qirji a tsakar gida ba
kitso bare yankan qumba,bare ayi zancen
su qunshi da turaren wuta ko turaren jiki
basu gyara jikinsu ba ina zasu gyara yara
bare wani miji?
Aisha farida kwarai kuwa hakane ai ana
zuba qazanta a gidan nan dukansu qazamai
ne duk dakin daka nufa warin datti ne abida
tace kece ma mai iya shiga dakunansu har
ki zauna ki cakumi gashinsu ki kitse ni ina
zan iya jure wari?ai shi yasa. Nakeso kici
gaba da dagewa har sai kin sami dr shuraim
shi kadai yafi dacewa da rayuwarki wani juyi
Aisha farida tayi tashin farko ta kifa ta
kwanta ta juya baya bata sake cewa komai
ba saboda bata da abun fada taki jinin a
ambaci sunan dr shuraim a halin yanzu
balle ayi hirarsa.Abida tayi dariya tace au
kiran sunan shuraim ma ba kya so shi ne
kika juya mun baya? masoyin naki ne ya
zama haka yanzu a wajenki?haba farida
kada kiyi fushi kada ki sare da wuri mutane
suna rasa ransu wajen neman abinda
zuciyarsu keso ke yanzu wacce wuya kika ji
har da zaki zame?keda shuraim kuna nan
daram ba gudu ba ja baya ina nan akan
bakana duk kyan takalmi qafa ce zata
tattaka shi''Aisha farida ta jawo filo ta dora
kanta ta toshe kunnenta sabida bata
buqatar ci gaba da sauraron abun da abida
ke cewa tamkar tana zuraro mata tsohon
gyambon data dade da warkewa bata fatan
gyambon nan ya dawo mata danye tafi son
idan ya warke ya warke kenan har abada
bata buqatar dayen ciwo ko maqiyinta bata
masa fatan ya shiga halin data shiga.
Abida ta fice tana daria ciki-ciki fitar abida
ke wuya sai ta tashi zaune ta jawo jakar
makaranta ta zubo littafanta da manyan
text books dinda ta aro daga wajen khadija
isma'I'll don ta karanta abubuwan da akayi
bata nan.tabbas an wuceta. Da yawa sai
tayi da gaske zata kamo su tana karatu
zuciyarta na zogi idan ta tuno dalilin daya ja
mata wannan matsalar sai taji haushin
kanta da kanta ta qudiri niyyar ba zata sake
bawa zuciyarta wannan dama ba balle takai
ta ta baro ta.bata fito ba sai data ji ana
kiran sallar magrib fitowarta keda wuya tayi
kicibis da yayanta ya dawo daga aiki ya
kuwa wurgo mata harara sai ta zube a qasa
ta kwashi gaisuwa ko amsa mata baiyi ba ya
shige dakinsa Aisha farida ta sake
gasgatawa har yanzu da sauran rina a kaba
maganar bata wuce ba kenan da saura?ta
miqe a sanyaye taje tayi alwala ta dawo
daki tayi sallah kafin ta idar taji motsin
shigowar abida daga dukkan alamu wajenta
tazo don har yanzu tana tsaye a kanta sai
da ta idar da wuri taji abinda ke tafe da ita
tana idarwa ta juyo ta dubi abida tace
aunty lafia? Abida tace ki zo inji yayanki
amma kada ma ki damu ba wani abu bane
kinsan dai duk abubuwan dana shirya to
duk abunda ya tambayeki ki haka zaki tsara
masa yanzu ya du da mijin uwani a qofar
gida suka tattauna suka wa juna haquri
shine zasu je wajen yan sandan su sunar
musu cewar an sulhunta an janye qara ba
sai kun je ba.Aisha farida ta miqe da sauri
dafe da qirji tace anti abida me zance masa
game da cikon 5k dinsa da kike ce zasu ciko
min?Abida tace a hakan zaki barshi zasu
ciko din,idan basu ciko ba ai laifinki bane
kuma ba zai kai ki qara ba dai shima sai ya
dauki asara daba ki samo 12k bama ai dole
ya nemo yayi belinki ba tunda ba zai bari a
daure ki ba wata da watanni.nasan dai zaki
sha fada ne da zagi kawai zagi kuwa baya
qari idan da sabo ai kin saba''
Abida ta wuce gaba Aisha na biye da ita a
baya ta sunne kai a cikin hijabi hannayenta
kuwa dukka 2 na dafe da qirjinta sai
karanto addu'io take iri-iri ba adadi tana
mai neman agaji daga wajen rabbil
samawati duk abun da zai zo yazo mata da
sauqi.Allah mai amsar addu'ar bawansa sai
ya sanyaya zucia yaya husaini maimakon
yayi mata fada data bayyana a gabansa sai
ya shiga yi mata nasiha yaji tamkar shima
ya fashe da kuka lokacin daya ga hawaye a
idon qanwarsa sai yaji tausayinta ya shiga
nasiha mai hade da rarrashi yace farida
haha farida kefa mai hankali ce mai sanin
ya kamata ga natsuwa nayi mamakin yadda
kike jefa rayuwarki cikinmatsla don kawai ki
fitar da wasu daga matsala ba'a hana
taimako ba amma kina so kina so kice min
bata da dangi ne ko dangin mijin sai ke kika
fiso sonta dasu?suna raye zasu bari ta mutu
ne basu samo kudin da za'ayi mata tiyata
ba sai ke?farida kinsan halin da muke
ciki,ta kanmu muke yi,bamu da wani
mataimaki sai Allah kullun hade-hade da
kame- kame mukeyi sannan muci abinci sai
naji tamkar na bar garin nan saina tuna
talauci dana baro a shagamu har gara nan
ma.ki riqe maraicinki ki riqe talaucinki ki
riqe matuncinki ki riqe karatunki ki lallaba
ki gama ki fara aiki ko zamu sami sa'ida
babu ke babu sake cin bashin wani babu ke
babu katsalandan akan matsalar wani ki
tashi ki tafi Allah ya kiyaye gaba Aisha
farida ta rushe da kuka tace nagode
insha'allah zan kiyaye ta fice ta nufi dakinta
ta shige ta takure tayi ta rusa kuka tana nai
tuno iyayenta da suka rigamu gidan gaskia
tabbas husaini ya fada mata gaskia dole ta
nutsu tasan me ye a gabanta kuma ita wace
ce a rayuwa?hawaye ya surnano daga
idanuwan husaini yasa hannu ya goge abida
ta matso kusa dashi ta fada cikin
sassanyiyar murya tace yaya kaima kukan
kake yi?kada ka damu fa kada ka saka
damuwa a ranka ciwo ya same ta tsautsayi
ne qaddara ce komai yazo qarshe ba za'a
sake ba insha'allah.
DUK KYAN TAKALMI 2* 3
Husaini ya girgiza kai yace ina son Aisha
saboda babanmu yana sonta tayi kama
dashi don haka idan na dube ta ina yawan
tunawa dashi hawayenta ne yake tayar min
da hankali.farida abar tausayi ce marainiya
babu uwa ba uba nida nake riqe ta talaka
ne ina matuqar tausayinta idan na ganta a
cikin qawayenta yan gata masu mota
baiwar Allah bata damuwa a haka take
daurewa tayi karatu sai naji tamkar dama
ina da yadda zanyi farida mata sami duk
abubuwan da yan mata suke buqata kamar
kayan kwalliya da dinkuna to babu
misbahun ma da yake sonta yake
taimakonta shima an raba su fatana Allah
ya fito mata da miji na gari inda zata huta
ko bayan raina ta taimaki kanta kota riqe
min 'ya'yana ba''Abida tayi shiru tana
tunani a ranta tace babu mijin daya dacewa
da ita irin dr shuraim insh'allah farida saita
sami shuraim ko don na hucewa mijina
takaici a ransa ko don in cika masa burinsa
na ganin farida ta sami gidan hutu nayi
alqawalin zan yaqi zuciyar shuraim da
addu'a da kuma kyautatawa har sai yaso
farida yaya husaini ya katse tunanin da
abida keyi yayi cimak ya miqe tsaye yace
zanje waje malam yusha'u na jirana mijin
uwani zamu je wajen yan sanda nan don a
janye casa dinsu Aisha.Abida tayi masa
fatan ya dawo dashi lafia ya fice da sauri.da
Aisha ta idar da sallar isha'I ko abinci bata
ci ba wajen datayi sallak kan tambarmarta a
wajen ta kudindine ta kwanta babu abin da
take yi sai sheshekar kuka da ajiyar zucia
har barci ya dauke ta.
Babu irin tashin da abida bata yimata don
taci abinci taqi tashi tace ta qoshi a haka ta
kwana saboda gajia da barcin data keji basu
bari taji yunwaa ba bata farka ba sai da
asuba kiran assalayu a kunneta ta miqe a
nutse tana mai addu'io taje tayi alwala tayi
sallah sannan ta shiga cuku-cukun yin
wanka da saka kayan makaranta so take
gari ya waye ta fice saboda gidan ya zama
mata tamkar kurkuku haka tunaninta da
hankalinta kakaf ya koma kan karatunta
bata da wani buri illa taga ta gyara inda ta
kuskuren kuma ta kamo yan ajinsu inda
suka wuceta ta zamana mai nadama akan
kuskuren data tafka a rayuwarta a kwanakin
baya a dalilin shuraim sai kuma ta qudiri
niyyar natsuwa da cire duk wani abu da zai
gundiri rayuwarta giftawar husaini ta gani ta
tagar dakinta ya dawo daga masallaci zai
shiga dakinsa sai tayi wuf ta fito ta durqusa
ta gaishe shi ya juyo ya dube ta duba mai
cike da tausayi kasancewar yaga ta rame
idanu wanta duk sun kode mata
musamman data kwana 2 baka kwalli ba ya
fada cikin yar siririyar murya farida lafiayar
qalau kuwa ko baki lafia?tayi sauri ta
sunkuyar da kai qasa gami da yin
murmushin qarfin hali ta girgiza kai tace
babu abinda yake damuna yay yace za a tafi
makaratar ne har kinci dumame?ta gyada
kai tace eh yasa hannu a aljihu ya dauko
wata tsohuwar 200 ya miqa mata kamar
kullun kamar yadda ya saba bata kudin
acaba zuwa da dawowa da kuma na shan
pure water.ta durqusa ta karba tayi godia
ta shiga daki shima ya shige daki tana shiga
ta mistsika yan powder a fuskarta ta gyara
dan guntun hajabin da yake jikinta sai ta
rataya jakarta a kafada gami da saqula 200
a zip din dake jikin jakar ta fito a bakin qofa
suka hadu da abida lokaci daya suka yiwa
juna murmushi Aisha ta gaishe ta abida ta
amsa gami da cewa har kin fito ki tsaya
kisha koko mana.Aisha tace sauri nake
kada na makara supervisor nake son gani
abida tace yunwa kuwa baza ta dame kiba
ba kici komai da daddare ba na jiya da
ranar ma da yawa kika ci ba Aisha ta
langwabar da kai tace ba damuwa idan na
dawo zanci abida ta kuncegefen zaninta ta
dauko 100 ta miqawa farida tace kici abinci
a can don nasan dole kiji yunwa farinciki
yaa lullube Aisha ta karba gami da
murmushi ta duqa tayi godia sannan ta juya
ta nufi hanyar fita harta kai zaure sai taji
muryar abida ni kiran sunanta sai ta juyo ta
tsaya cak!tana dubanta kanar marar gaskia
ta qarso inda take taja. Hannunta zuwa
bayan kyauren zauren.
Ta fada cikin rada daman inaso na tambaye
ki dazu, to nasan halin kunnen hussaini, sai
ya jiyo mu. Hankalin farida ya tashi ta dafe
kirji tace me ya faru? Abida tace dr shuraim
mana, zaku hadu yau kuwa? Kafin kace
kwabo farida ta bata fuska ta kara da kai
gefe, ta zumburo baki. Tace ba zamu hadu
ba. Ta juya a fusace zata fice. Abida ta sake
jawo hannunta tace fushi kike don naayi
mmiki zancen shuraim? Kin daina sonsa ne?
Aisha farida tayi caraf ta fada cike da gadara
da takaici tace eh. Sai abida ta kwashe da
dariya, yayin da aisha farida ta fice a fusace
ko waiwayowa ba ta sake yi ba. A hanya ta
hadu da musbahi ya fito daga gidan akan
babur dinsa zai tafi wajen nema, sai ya
tsaya a kusa da abar kaunarsa yana mata
murmushin kauna. Sai dai kash! Zuciyar
masoyiyar tasa a bace take, sai ta kawar da
kai taki yin dariya ta gasihe shi ranta a
bace.
Wai kwana biyu nan wa yake taba minke?
Musbahu ya fada yayin da yake duban
fuskarta, yake murmushi. Ta kawar da kai
gefe ta fara tafiya ba tare da ta bashi amsa
ba. Yayi sauri ya sake biyo ta, ya tari
gabanta har yanzu yana zaune akan babur
dinsa. Abun mamaki sai yaga hawaye yana
zubowa daga idanuwanta, nan da nan sai
hankalinsa ya tashi ya shiga lallashinta yana
bata hakuri, gami da rokonta ta hau bayan
babur dinsa ya kai ta asibitin. Da farko taki
sai da kyar ta hau suka fara tafiya. Ba tare
da wani ya sake magana ba a cikinsu,
sheshekar kuka kawai farida keyi a ciki ciki.
Cikin marainiyar murya ta ambaci sunansa
tace makarantarmu za ka kaini ba asibiti
ba. Nan da nan ya amsa mata da to...to
farida. Har bakin ofishin malam basiru ya
kaita, ta sauko tayi masa godiya ba tare da
ta dube shi ba. Ya kira sunanta cikin
lallausar murya, ta juyo a tsanake tana
sauraronsa, sai taga hawaye ya surnano
daga idanuwansa, ta sake dubansa sosai, sai
tayi mamaki tace lafiya? Yace farida kiyi
hakuri ki yafe min nima ba da son raina
haka ta faru ba. Ta tambaya cike da
damuwa meya faru? Yace kwanan na ga kin
shiga matsananciyar damuwa, har aka ce an
kai wajen 'yan sanda an kulle ki duk da ba
fada min takamaiman laifin da kikayi ba.
Farida da ace tun sanda kika gama
sakandire muka yi aure, da na killace ki duk
da haka ba ta faru ba. Amma nasan komai
mukaddari ne daga Allah, bawa bai isa ya
tsarawa kansa rayuwar da yake so ba, sai
yadda Allah Ya so dashi.
Sanin kanki ne duk duniya ke nakeso, kuma
har abada ba zan daina sonki ba, matsalar
daga wajen goggo ne ba don ita ta haife ni
ba ina tsoron bakin uwa ba da tuni nayi faci
da maganarta munyi auren mu. Na kasa
son matar da ta aura min, na kasa cire raina
a kanki. Ba yadda zanyi nace kada kiyi aure
ki jirani, idan nayi haka na zalunce ki, tunda
bansan ranar da goggo zata hakura ba
amma kada kiyi gaggawar yin aure ki barni,
kullum ina ta fadawa Allah, nasan kema
kinayi. Toh muci gaba. Farida ta rushe da
kuka, tabbas musbahu yayi gaskiya, abin da
yake ranta kenan, cewar ba don yaki
aurenta ba da ya za'ayi ta afka cikin
wannan hatsarin? Sai ta juya da sauri ta nufi
ofishin da tazo, yayin da musbahu yake
kwalla mata kira taki ta waiwayo ma balle
ta amsa. Tana shiga ofishin taci s'a ta iske
malam basiru yana nan shi da abokinsa
malam sulaiman. Bayan ta gaishe su sai ta
barke da kuka marar kakkautawa, sai suka
shiga damuwa suka shiga yi mata
tambayoyi, lafiya take kuka? Suka bata
kujera ta zauna cikin sheshekar kuka ta fara
bayani. Sannan suka fahimci inda ta nufa da
kuma dalilin kukan nata.
ba 31 da 32 zan ci gaba da 33
Supervisor ya turo hula gaban goshi yace
rashin lafiyar da kikeyi ce ta hana ki aiko
'yan uwanki suzo su fada min ko kuma ki
aiko a rubuce a kawo min? Gashi yanzu sau
biyu ina zuwa duba ku ba kya nan, yaya
kike so nayi miki yanzu? Kije kawai wata
shekarar ki dawo ki maimata attachment
din. Ta sake fasa kuka taci gaba da ba da
hakuri. Mal sulaiman ya dubi abokinsa yace
a'a ba za'a yi haka ba, ka dai duba ka
taimaka mata. Itace fa monitor kasan aisha
umar bata da wasa, lalura ce ta jawo haka
da dai Khadija sani ce, kawarta ba zan ma
shiga zance ba, don nasan bata da kokari.
Malam basiru ya gyada kai yace shikenan
kije nan da kwana biyu zan shigo asibitin in
duba kiki zama cikin shiri dan a koda
yaushe zan iya fadowa. Ta durkusa tayi
godiya. Aisha umar ta fito tana matse
hawaya, amma zuciyarta cike da farin ciki,
hankalinta ya fara kwanciya. Tayi mamaki
da ta iske musbahu har yanzu yana nan
yana jira bai tafi ba. Jikinsa na rawa ya
kunna babur ya karaso inda ta ke yana
tambayarta ta gama su tafi, ko akwai inda
zai kaita kuma? Ta girgiza kai tace cikin
asibiti kawai zanje. Ta hau babur suka tafi
har yanzu ma dai babu wanda yake magana
a cikinsu, tana nuna masa hanya har ya
kaita inda take so, sannan ya tsaya.
Tana saukowa sai taga ya dauko kudi ya
mika mata, dubu daya 'yan dari biyar guda
biyu. Yace karbi wannan bashi da yawa, a
cikin kudin da na ranto miki ne ma zanje na
biya su, amma ba zai gagara ba. Daga nan
zuwa yamma zan cika in biya su. Aisha
farida ta girgiza kai tace ka barshi na gode.
Yace a'a ki karba farida babu komai, a shirye
nake nayi miki duk abin da kike so idan
baifi karfina ba, ko bani dashi zan nemo
bashi na baki. Ta mika hannu ta karba a
kunyace, ta duka tayi godiya. Ta dube shi
sai taji sanyi a ranta ganin annuri a fuskarsa
murmushi kawai yake yi mata naso da
kauna. Ta rike kan babur dinsa tana
murmurdawa ta dube shi tayi fari da ido.
Tace musbahu na gode da dawiniyar da ka
dade kana yi dani, nagode da kulawarka da
damuwar da kayi dani a tsawon zamana da
kai baka taba gajiya dani ba. Ko kadan ban
taba zarginka ba akan rashin aurenmu,
nasan daga inda matsalar take, ina adduar
Allah Ya zaba mana abin da yafi alkhairi
amma ba zan boye maka ba musbahu bana
jin a jikina zamu iya aure, don banson nayi
auren da zan kasance bani da kwanciyar
hankali. Saboda mahifiyarka ta fito baro
baro bata son abun. Koda naji sonka zai
mamaye min zuciyata nakan yi addua Allah
ya yaye min, sai nayi sauri na juya akalar
zuciyata wani bangaren.
Musbahu ya girgiza kai alamar takaici yace
yanzu aisha farida har addua kike Allah Ya
cire miki sona a ranki, koda yake bakiyi laifi
ba idan kinyi hakan, amma ni ban taba
fatan na daina sonki ba, ko da kuwa bama
tare. Wa kike so yanzu bayan ni? Nasan dai
ba zaki rasa ba, tunda a maganarki yanzu
kin furta wata kalma da take nuna
hakan....ke 'yar shagamu, lah lah lah zance
ma kikeyi da sassafen nan? Muryar da ta
jiyo daga bayanta kenan ita da musbahu
suka waiwaya da sauri, maza biyu ne suke
tafe akan doguwar barandar, su dukka suna
sanye da wando da riga na bakar suit
wuyansu sakale da abin gwaji. Ko ba a fada
maka ba manyan likitoci ne. Dr lukman ne
mai maganar, na kusa dashi kuwa dr
shureim ne, daga dukkan alamu daga duba
marasa lafiya suke, domin da daliba na biye
dasu a baya. Ta dubi dr lukman tayi
murmushi ta rufe ido da hannayenta biyu
ta fada a kunyace a'a ba zance nake yi ba,
yayana ne. Musbahu yace yayanmu ai
kanwata ce na kawo makaranta. Gogan
naka dr shureim baice komai ba, amma
yana tafe yana dubanta kasa kasa har suka
wuce. Kallo daya tayi masa ta watsar ba ta
sake waiwayarsa ba, taci gaba da duban
abin kaunarta musbahu, ta shiga yi masa
bayanin inda tasan dr lukman. Abin mamaki
abinda ya sake tsorata ta sai taji musbahu
yana yabon kyawun dr shureim.
Yace shi kuma daya likitan yay sunansa?
gaskia yana da kyau irin wannan ne fa yake
sawa wasu mazan suke hana matansu zuwa
aiki idan suna ganin mazaje kyawawa irin
wannan sai su tsani mazan su sai taji
zuciayarta ta harba bumm! don fargaba ta
tambayeshi me kace?ya maimaita abun da
fada tace a ranta haqiqa na daukowa kaina
ruwan dafa kaina amma Allah ya hayar dani
dana gane gaskia gaskia ce wato 'yar
uwansa maza ma kyawunsa suke gani balle
yan mata lallai shuraim ba sa'an soyayyarta
bane zuciata tayi garajen cusa kanta wajen
ajalinta.tayi zuciayarta ta yamutse fuska
tace bansan sunansa ba nima dai ina
ganinsa dai kawai misbahu yace kina
burgeni farida duk irin kyalkyalin dunia bai
cika damunki ba har dana fara kishi
musamman dana ga yana kallonki qasa-
qasa na dauka shima ya sanki Aisha tayi
murmushi tace ni banma kalleshi ba balle
insan yana kallona kai ka lura da hakan
misbahu yace aini tun daga nesa na hango
su suna tahowa kece baki gansu saboda kin
juya baya tunda ya tunkari mu yake kallo
har na tsorata na dauka shima yana ciki
Asiha tace aa ni ban ma sanshi bama zai
wuce babur dinka yake harara bana ji ance
ya tsani yaga mace ta hau babur.misbahu
ya kwashe da daria yace kai dalibai akwai
sharri waya fadawa haka?a zamanin kuwa ai
sai an hada da hawan babur abu zai tafi dai-
dai ba kowa yake da kudin daukar taxi drop
na musamman mu talakawan da muke
zaune a lunguna koda yake su manya ne
matansu ba zasu hau babur ba sai mota
ko? farida ta tabe baki tace shi ya sani
wannan matsalarsa ce ni har bana son
zancensa ma ya cika dagun kai.
Dadi ya kama misbahu kansa ya fara
huruwa wato saboda sonsa da farida keyi
har bata ganin fuskar wani da namiji sai shi
sai ya shiga washe baki tamkar sakaran
daya ga sabon dinki yace in dawo na dauke
ki idan kin tashi? ta riqe baki ce rufa min
aisir misbahu qasada ce ma yanzu dana hau
mashin dinka a unguwarmusaboda safiya ce
babu jama'a da bazan hau ba sai a yi mana
sharrin da ba zamu fita ba.anga mun fita
tare sannan da yamma aga mun dawo me
kake tunanin za'a ce mana?kaje kawai
nagode sai wani lokaci idan Allah ya sake
hada mu a hanya don goggo ta hana ka
zuwa qofar gidanmu kuma bana so ka saba
mata ta juya ta tafi tabarshi zaune akan
babur yana dubanta zuciyarsa cike da da
tsananin sonta gami da takaicin abun da
mahaifiyarsa tayi masa ina ma za'a hada
farida da matarsa?aiko kusa basu hadu ba
farida mutun ce kuma abar so ce yarinya
kyakyawa mai fara'a ga son mutane iya
magana tafiya a nuste da dadadan kalamai
mai dadin murya da iya kallo da sai kaji
kwakwal war kanka za zillo.ga kyakyawan
halaye bata da hassada ba kyashi ko
mugunta bai motsa ba har sai da ta bace
masa ya daina hango ta yayi ajiyar zuciya ya
girgiza kai ya kunna babur dinsa ya tafi a
sanyaye gabobinsa sunyi sanyi.
DUK KYAN TAKALMI 2* 4
Cikin satin nan kakaf babu abinda farida
keyi sai karatu agida da makaranta. Bata
shiga kawaye, har a gida ba ta fitowa tsakar
gida. Tana lungu ko da yaushe littafiinta ne
a hannunta. Burinta ta kamo 'yan ajinsu
inda suka wuce ta, ga uwa uba a cikin satin
supervisor dinta zai zo ya duba ta. Ta cire
damuwa a ranta, haka bata da sauran
tunani yanzu, sai karatunta. Abinci ma ba ta
fiye son ci ba, sallah ce kawai ta zame mata
dole ta tashi tayi, sai bacci barawo idan ya
sace ta, tayi kadan ta farka taci gaba. Kafin
kace kwabo farida ta rame, kowa ya kalle ta
sai yayi maganar ba ta damu ba, haka bata
tsahirta ba. Burinta taci nasara akan abin
da ta sa a gaba. Duk da wannan jajircewar
da tayi, da dagewa ta haddace kusan duk
inda take tunani za'a tambaye ta daga
kowane bangare na karatunsu zata amsa.
Amma sai ta hada da addua tana mai
neman taimakon Allah akan karatunta.
Alhamdulillah da supervisor yazo dubata a
karo na farko ta amsa tambayayin dukka
har sai da yayi mamakinta. Sati mai zuwa
karo ba biyu ya sake zuwa ya duba ta, a
wannan lokacin ta sake shiri sai yaji
rugurguza tambayoyin da ya jero mata har
ma tana kara masa bayanai akn abin da bai
tambaye ta. Ya jinjina mata, kuma ta burge
shi matuka. Taci maki da yawa don tafi
dukkanin 'yan ajinsu ci. Daga karshe ya
shawarce ta yadda take da kokari ta daina
wasa da karatunta, taci gaba da dagewa ta
fita da sakamako mai kyau, shi kuwa yayi
mata alkawari zai taimaka mata wajen
neman aiki, kuma ko cigaba da karatunta
take so zai taimake ta.
Farida dai sai farin cik take tana yi masa
godia ji take tamkar an sauke mata nauyin
da yake kanta sai yanzu hankalinta ya
kwanta walwalarta ta dawo ta shiga cikin
qawayenta kamar da suka ci gaba da
karatunsu da kuma koyon aikinsu.idan ta
dawo gida taci gaba da wasa da dariyarta ita
da abida da 'ya'yanta duk da Asiha bata
nunawa 'ya gidansu da maqotansu bacin
ranta akan abubuwanda da suka yimata
suna gaisawa sosai tayi musu fara'a amma
ta daina zama cikinsu tayi hira dasu kuma
sai suka dinga jin kunyarta ba kasafai bama
suke iya hada ido da ita ba saboda kunyar
abun da suka yimaya domin Aisha tana da
kirki kuma tana taimaka musu ta kowace
hanya.tun yaya husaini na tambayar kudin
da ka ranta 5k har ya gaji da dadin bakin
abida yayi shiru ya daina tambayarta.ranar
lahadi misalin qarfe goma sha biu na rana
bayan abida da aisha sun gama aikin tsaf
sunyi wanka sunyi wa yaransu wanka sun
tura su islamiyya yayin da yaya husaini ke
cikin daki yana shigar baccin gajia kamar
yadda ya saba ranar labadi ce kawai baya
zuwa aiki itace kadai ranar hutunsa a
sati.don haka abida da yaranta basa garajen
yin shige da fice a dakin abida kada a tashe
shi tunda sassafe take hado musu yan
komatsansu ta kawo dakin Aisha a karo
masa qofa daga ya karya kumallo yake
kwacia saida azahar kuma zai farka.Aisha ta
gama rangawa abida kitso ras a kanta kai ka
ce fula ce akasa dan kyau sannan itama
abida taya ta tsifar nata kan Aisha na
kwance akan tabarta yayin data dora kanta
akan cinyar abida wacce ke zaune ta
mimmiqe qafa hira kala-kala Aisha ke zaune
ke rerowa abida hirar da data yanzu ta
shagamu data kano hade da qawayenta na
makaranta.abida ta dubi Aisha sai tayi
murmushi misbahu kuwa yana nan? farida
ta gyada kai gami da yin
murmushi .misbahu yana nan kin manta
kwanaki na fada miki yabani 1k harna
saywa sa'id takalmi kito? abinda tace haka
ne na tuna Allah sarki misbahu yana sonki
har yanzu amma wannan uwar tasa bata
kyautawa danta ba taci amanar haihuwa
koda yake mijin wata baya auren matar
wani mijinki na nan tafe.Aisha ta dago ta
dubi abida saita mayar da kai ta kwanta
jikinta a sanyaye ta fada cikin marainiyar
murya insha'allahu.Abida tace ina dr
shuraim?
Takaici ya hana ta magana har zuwa wani
lokaci mai tsawo babu wanda ya sake
magana a cikinsu abida tayi ajiyar zucia tace
farida kin cika sarewa baki da juriya akan
abunda kike nema ki zama jaruma ki jajirce
har sai kin sami duk abunda kike so kada ki
tsorata domin qaramin aiki ne samun
shuraim amma kin biyea maganar qawaye
duk sun tsorata farida ta girgiza kai tace ba
zai yiwu ba nan da nan farida ta juyo ta
dube ta cike da mamaki marar misaltuwa ta
fada a bayyane ikon Allah yai naga abunda
yafi qarfina sai suka kwashe da dariya su
duka abida ta gyara zama taci gaba dayi
mata tsifa yayin da har yanzu farida na
kwance ta dora kanta akan cinyarta abida
tace idan dai har yanzu kina son shuraim
bana so ki fitar da ran sumunsa domin Allah
yana bawa bayinsa duk abin da suka roqe
shi;farida ta girgiza kai tace aunty na
haqura da dr shuraim ko maganarsa bana
so ayimun abida tace kin haqura akan dole
ko kin daina sonsa ne kwata-kwata?Aisha
tayi shiru yayin da hawaye ya cika mata ido
idan ta matse sai wani ya sake tsattsafowa
abida ta shafa kanta tace kiyi haquri kukan
naki zai koma dariya da izinin ubangiji idan
baki manta ba na umarce ki daki riqe abu 5
wannan abu 5 din zai kaiki da samun nasara
ki sami shuraim cikin ruwan sanyi uhmmm
farida ke ambato tana kwance ta kasa
magana sai bugun zuciyarta ke tsananin
yi.Abida tace bazaki tambayeni abu 5 din
bane? cikin sanssayar murya tace meye
abun 5 da zan riqe? abida tayi murmushi
gami da jiyar zucia tace Alhamdulillah a
cikin 5 din nan zan fara fada miki 3 daga
baya inga miki saura 2 a hankali.Aisha ta
daga kanta a hankali ta dubi Abida zuciyarta
cike da fargaba abun da abidar zata fada
tana tantama ko zata jure su don ta qudiri
aniyyar ba zata sake yin wahala ko zubar da
ajinta ba wurin shishigewa dr shuraim abida
tayi daria tace kada ki tsorata zaki iya ba
wani abun wahala bane.farida tayi ajiyar
zucia ta dafe qirji ta lumshe ido gami da
qirqiro wani basashen murmushin da bai
kai zuci ba ita dai a ranta tafi son abar
maganar dr shuraim kawai shi yafi
sauqi.abida tace abu na farko dana keso ki
riqe a rayuwarki itace addu'a idan kika
yawaita addu'a akan dukkan lamuranki zaki
ci nasara Aisha ta gyada kai tace ina addu'a
sosai ma kuwa abida tace wannan ta
musamman ce a tsakaninki da shuraim ki
roqi Allah ya zabar muku abinda da yafi
alkhairi amma ke alkhairin wajenki shine ki
sami soyayyarsa tunda kina sonsa,babu
hijabi tsakanin ubangiji da bawansa ki roqi
duk abunda kike nema a dunia da lahira
idan dai halak ne ki zayyano masa duk
yadda kike so babu kunya Allah mai karbar
addu'a ne idan kika riqe addu'a ki yarda
Allah zai amsa miki kin cika abu daya.Aisha
ta gyada kai naji menene na 2?
Abida tayi ajiyar zucia tace abu na 2 da zaki
riqe bayan addu'a shine kizama mai
tsananin haquri sai mai haquri ne yake cin
ribar rayuwa ki daure ki jure duk abunda
zaki gani haka duk nisan lokacin da za'a
dauka ki daure kada ki qagu ko ki girgiza ko
ki razana ba'a yiwa Allah dole kuma
gaggawa daga shaidan take ma'ana duk
tsawon lakacin da za'a dauka kafin shuraim
ya karkato gareki kada ki gaji kiyi fushi kice
kin haqura.sai na 3 shine ki riqe
mutumcinki. Kada ki fito da maitarki fili ya
gane halin da kike ciki na sonsa ma'ana kaja
ajinki.Aisha ya yamutse fuska alamar nuna
rashin fahimtarta a fili abida tayi murmushi
tace zaki fahimce sai a hankali.farida ta
tashi zaune ta dubi abida zuciyatra cike da
quna tace aunty abinda kina nufin inyi ta
bin shuraim ina zubar da ajina yana
wulaqantani shine haquri? idan ba haka ba
yaushe shuraim yasan dani balle yasan ina
haquri dashi wata rana yaso ni?kin kasa
gane waye shuraim idan ba office muka je
ba bama ganinsa abun da ya fiye min sauqi
shine na rabu dashi ni yanzu ko a hanya ma
bana so mu hadu bawai na tsane shi bane
ko yayimun wani laifi aa ko kadan bana
zarginsa don bai ma san abun da anke yi ba
sai dai don na samarwa zuciya ta
salama.abida ta girgiza kai ai wannan itace
juriyar da haqurin da nake kiyi ki taka inda
yake ki ganshi ya ganki sannan kija masa aji
Aisha taji tamkar abida ta dora mata dunia
akanta don nauyin da kanta yayi taji
hawayen takaici ya tsatsafo mata ta girgiza
kai tace aunty abida zancen jan aji kuma a
nan in har naje inda yake? ai na sayi
wulaqanci da kudina abida tayi murmushi
tasa gefen hannunta ta gogewa farida
hawaye tace ki biyo ni a sannu a hankali
zaki fahimce ni kuma zaki ga canji a wajen
dr shuraim insha'allah ke dai kija mu je ki
riqe matakan 3 addu'a.haquri da riqe
mutunci.farida ta koma ta kwanta akan
cinyar abida a sanyaye yayin da hawaye
yayi ta zuba ta tuna mata abinda taci gaba
dayi mata tsifa tana zayyano mata dadadan
kalamai game da yadda zata sami shuraim
idan har zata riqe addu'a zata riqi
haquri.Aisha farida tana yin duk abun da
abida ta shawarceta ta duqufa da yin addu'a
safe da rana harda tsakar dare dama can ita
gwanar yin addu'a ce tana da juriyar yin
addu'a sai dai lokacin taji a ranta kamar
abun ba zai yiwu ba bata lokacinta kawai
takeyi sai ta tuno abubuwan da abida ta
fada mata cewar ta roqi Allah duka abinda
take so kada ta boye babu hijabi tsakanin
bawa da ubangijinsa sai taci gaba dayi bata
gajiyawa.tafi ambaton Allah kasan ina son
shuraim idan da alkhairi shima ya soni.
A CIKIN ASIBITI Aisha farida ce ke zaune
akan wata doguwar kujera tana jiran
matron maryam ta fito daga duba mara
lafiya a babban dakin mata, zata bata sakon
data aike ta ta karbo. Duk da ita ma daliba
ce zata iya shiga, amma security ta hanata
wucewa tace sai dai ta jira anan kasancewar
shugaban asibitin aminu kano ne yake
zagaye. Don haka manyan likitoci sai
tururuwar wucewa ciki suke yi. Tana zaune
tana jira har ranta ya fara baci, don ba don
sakon nan ba da babu abinda zai rabota da
karatunta, ita yanzu bata so a wuce ta koda
dakika daya ne. Taji tamkar ta barwa
security sakon inta fito ta bata, sai ta tuna
zai iya bata kuma sakon yana da
muhimmanci, don ba dan faridar ba ma da
matron ta yadda da ita babu wacce zata
aika ta karbo mata. Kudi ne da wasika ta
karbo mata daga wajen matron aisha, a
dakin 'yan awo. Aisha farida taja dogon
tsaki sannan ta harari security din da ta
jawo mata wannan dogon bata lokacin,
sannan ta duba agogon dake daure a
tsintsiyar hannunta. Karfe goma da rabi na
safe daidai, ta daga ido zata kalli kofar dakin
da matron ke ciki. Kicibus idanuwanta
sukayi da abin da ya gigitata har sai ta
zuciyarta ta daki allon kirjinta don firgici.
Bata manta da ambaton innalillahi wainna
ilaihi rajiun ba, yayin da ta daure bata nuna
razanar da tayi a fili ba. Dr shuraim ne ya
tunkaro inda take a zaune, yana tafe
tamkar dawisu, cikin kyakkyawar shigarsa
wato bakar suit, hannunsa rungume da file.
Kallo daya tayi masa tayi saurin dauke
idanuwanta, haka nan da nan ta kawar da
fuskarta gefe daban, ko da ya karaso
saitinta sai tayi sauri ta sunkuyar da kanta
kasa har ya wuce bata dago ba. Wucewarsa
ba dadewa sai taji wata sassanyar murya
wata mata tayi mata sallama, da ta daga kai
ta dubi matar sai taga wata zankadediyar ce
fara sol, doguwa 'yar gayun gaske, mai
kamshi na alfarma. Gefenta kuwa wata 'yar
budrwa ce ke goye da yaro a baya, da
alama dai mai aikinta ce ke goye da danta.
Aisha farida tayi murmushi gami da amsa
mata sallamar. Ta zauna kusa da aisha
farida, sannan ta umarci mai aikinta ma
tazo ta zauna, yayin da ta dubi aisha farida
ta gaishe ta hade da tambayarta. Sai dai
fargabar da farida ke ciki ta sake karuwa,
don wannan zankadediyar matar dr
shureiim take tambayarta. Aisha farida tayi
sauri ta girgiza kai tace a'a bansan shi ba,
sai dai ki tambayi security, nasan dai duk
manyan likitoci suna ciki.
Sai matar tace ai naga kamar security din
nan bata da mutunci, bari kawai in kira shi
a waya, da zan fito daga gida munyi waya
yace min yana nan female medical ward,
naga kuma ba a bari a shiga. Ta jawo
wayarta sabuwa dal kirar blackberry ta
matso sunan dr shureim idanuwan aisha
farida na kai yayin da taci gaba da zazzare
ido tana tunane tunane kala kala daban a
ranta. Shin wannan wacece take neman
abin kaunata? Toko matarsa ce? Cikin
harshen turanci tayi masa magana tace
faridarka ce ina nan female medical ward,
an hana ni shiga. Aisha farida ta maimaita a
zuciyarta. Faridah! Faridah!! Daman yana
da wata farida bayan ni? Lallai abida tana
so ta kaini ta baro ni, domin wahala kawai
zansha babu alamar nasara a nan. Sai ta
tuna da abubuwan da abida tace cewar tayi
addua kuma tayi hakuri. Farida ce ta katse
tunanin da aisha farida keyi, ta dube ta tace
gashi nan zuwa ashe, baya ciki ya dan fita.
Aisha farida ta gyada kai tace okay! Matar
ta sake duban aisha farida tace yaya na
ganki a nan zaune, ke ba ma'aikaciya bace,
ko wani kike jira? Aisha farida tayi
murmushi tace wata matron nake jira, ta
shiga ciki aini daliba ce. Security ta hana ni
shiga. Kuma dai yau ne ake hana mu shiga
shima saboda shugaban asibitin yana
zagaye.
Haj farida tace toh shiyasa naga duk an
koro 'yan zaman jinya a waje? Alla dai Ya ba
wa kowa lafiya. Nima wallahi yarona na
kawo bashi da lafiya, kwana yayi zazzabi
kuma ga amai. Aisha farida tace
subhanallah, ko hakori ne? Haj farida tace
anya kuwa hakori ne? Bana jin hakori ne,
don ya gama hakoransa, shekarunsa fa biyu
da rabi, don kin ganshi a baya ne kamar
jariri. Ina ga canjin yanayi ne, kinsan sauron
kasar nan. Aisha farida ta gyara zama tace
daga wacce kasa kukazo? Haj farida tace
daga london, ai can nake aure. Nan da nan
jijiyoyin jikin aisha farida suka rike, ta kasa
cewa komai, babu makawa itace matar dr.
To amma sai dai in 'ya'yan nasa guda biyu
ne babbar mace ce, kuma tayi wayo don
tana amsa waya radau. Cikin sanyin murya
aisha farida ta tambaya shi kadai ne danki,
ko akwai wasu? Haj farida tayi murmushi
tace akwai yayarsu na baro ta a gida.
Tabbas matar dr ce wannan, amma Allah
yayi kyau da gayu a nan. Ai ruwa ma ba
sa'an kwando bane, ina ni ina jera kishi da
wadannan mata masu shigen kama da
matan hurul ain? Aisha farida ta fada a
ranta.
Taji gaba daya bata da sauran wani tunani,
kuma tasan shuraim yayi mata nisa. Rashin
sanin shuraim na hakika ne abida take
wannan daddagwar tana cewa sai anyi. Haj
farida ta dubi aisha tayi murmushi tace
yaya sunanki? Aisha farida tayi jim kadan,
can tace sunana farida. Wow! What a
coincidence is that? Sunanmu daya ai nima
farida sunanan. Matar ta fada yayin da
takeyin dariya, fararan hakoranta suka dau
walkiya. Aisha farida ma tayi dariya tace oh
haka ne kuma naji sanda kina waya kin fadi
sunanki. Yaya sunan yaronki? Tace rislan.
Aisha farida ta gyada kai tace rislan suna
mai dadi, yaya sunan yayarsa ta gida? Tace
sunan mamanmu ne aka saka. Aisha amma
muna kiranta da momi. Aisha farida tace
Allah Ya raya su. Haj farida tace amin.
Yawwa ga dr shuraim nan zuwa. Aisha
farida tahi wuyanta ya sage, har ba zata iya
juyawa ta dubi bangaren da ya taho ba, don
haka can gefe ta juyar da kanta har ya
karaso gabansu ya tsaya. Kamshin turaren
jikinsa mai sanyi shine ya daki hancin aisha
farida, yayin da tattausar muryrasa da
hadadden turancinsa yake ta dukan dodon
kunnuwanta a inda aka hau dambe tsakanin
zuciyarta da idanuwanta, idanu suka su juya
su kalle shi, yayin da zuciyar ke son kallon
abin da take kauna. Idanu suka rinjayi
zuciyar aisha farida taki dagowa ta kalle shi
Me yake damun dana ne? Oh my God rislan
ciwo ne ya taba min kai? Inji dr shuraim a
lokacin da yake shafa kan rislan. Haj farida
tace jiyya bamuyi bacci ba wallahi, sai naji
kamar yau in yanki ticket in juya london. Dr
shuraim yayi murmushi yace no kar ki
damu, mu nan asibitin muna da kwararrun
likitocin yara, bari in kira kawata dr
rukayya. Ya dauko hadaddiyar wayarsa kirar
blackberry ya matso sunan dr rukayya ya
fara da sallama, sannan ya gabatar da
kansa. Yace dr shuraim imran ne yake
magana, nasan baki san wannan layin nawa
ba ko don sabo ne? Dr rukayya tayi
murmushi tace ai kowa ya sanka da canje
canjen layi kullum. Ya aiki? Dr shuraim yace
alhmdlh, dama ina so in turo miki patient
dinku, sister tace farida imran yaronta bashi
da lafiya nake so ki duba shi, duk wani
taimako da ya kama kiyi musu. Dafatan dai
kina cikin asibitin? Dr rukayya tace haba
meya abin yi min magiya, kanwar ka ai
kanwata ce, to ka turo ta razo ina nan
speciality yanzu. Dr shuraim yace nagode,
gata nan zuwa. Sannan ya kashe wayar ya
mayar aljihunsa
DUK KYAN TAKALMI 2* 5
Aisha farida taji wani irin sanyi a ranta da
Allah Ya sa kanwarsa ce ba matarsa ba, sai
a lokacin kamanninsu suka bayyana. Tabbas
kamarsu daya tamkar an tsaga kara. Har
yanzu bata kallonsa ta juyar da kanta can
gefe, amma fa kunnuwanta radau a bude
tana sauraronsu. Dr shuraim ya dubi 'yar
uwarsa yayi murmushi yace kinga ni yanzu
ina tsakiyar aiki, bari in samo wacce zata
raka ku speciality don nasan baki san kan
asibitin nan ba, da sai in kwatanta miki,
kuma ma da nisa. Ya dade yana kallon aisha
farida, sai taji a jikinta kamar ana kallonta,
tana dago ido sai suka hada ido dashi, nan
da nan ta bata fuska, har da murguda baki,
ta kawar da kanta gefe, don kada ma yaga
fuskar aikenta. Shima yayi saurin dauke
idanuwansa daga kanta ya bata fuska, ya
juya ya nufi wani office ba jimawa ya fito
tare da wata daliba likita na biye dashi a
baya. Suka iso inda aisha farida ke zaune.
Haj farida kuwa sai takalo aisha farida
takeyi da hira, yayin da ita kuwa bata cikin
hayyacinta. Dr shuraim ya kade mata
hankali gaba daya ta rasa me yake
damunta, sai da ta sake ganinsa ta tabbatar
har yanzu sonsa na nan dankare a zuciyarta
sai taji haushin zuciyarta da take jawo mata
masifa iri iri.
Dr shuraim yace ga dr zainab dalibata ce
zata raka ku, kuma zata tsaya ki gama
komai, sannan ta dawo. Dr zainab farin ciki
fal a zuciyarta fara'a cike a fuskarta saboda
yau dr shuraim ya kula ta har ya zabe ta ta
raka kanwarsa, don haka ji take tafi kowa
samun shiga. Tayi sauri ta duka ta gaishe da
haj farida yayin da ta hau shafa kan rislan
tana ta faman iyayi. Tanayi tana satar kallon
dr shuraim, shi kuwa gogan abin da yafi
tsana kenan, irin wannan shishigin sai ya
fara bata fuska. Aisha farida tayi murmushi
a zuci tace a ranta wayyo zainab ina
tausaya miki indai dr shuraim ne zaki hadu
da tsagewar zuciya bama bugun zuciya ba.
Muma nan munyi mun warke. Haj farida da
mai aikinta suka mike suka dunguma suka
fara tafiya har haj farida ta wuce sai ta tuna
ba tayiwa aisha farida sallama ba, sai ta
waiwayo da sauri. Tace af kawata,
takawarata na tafi ko, sai Allah Ya kara sada
mu da alkhairi. Aisha farida ta dube ta, tayi
dan murmushi ta gyada kai. Tace yawwa sai
anjima Allah ya sadamu da alkhairi, Allah Ya
bashi lafiya. Yayin da dr shuraim ya dubi
kanwarsa ya juya ya dubi aisha farida da
alama yana mamaki kuma daga dukkan
alamu akwai alamomin tambaya a tattatre
da bakinsa. Abin da kunnen aisha farida ya
jiyo mata bayan sun juya suna tafiya shine
ya dubi kanwarsa yace a ina kika san
wannan yarinyar har ta zama kawarki, kuma
takwararki? Haj farida tayi murmushi tace a
nan na santa, yanzu ma na taba ganinta a
duniya. Dr shuraim yayi dariya ya girgiza kai
yace hmm mata, akwai kwashe kwashe,
daga dan zaman da kukayi tare shikenan
har kunsan juna, har da dogayen lanarai da
sanin sunan juna. Suna ta maganar har
sukayi nisa ta daina jiyo abin da suke cewa
Aisha farida tayi ajiyar zuciya yayin da farin
ciki ya rufeta, tasan dr shuraim yanzu ya
santa duk inda suka hadu zai shaida
fuskarta sannan zai tuna da sunanta tunda
dai ba zai mance sunan kanwarsa ba uwa
daya uba daya ba. Ko ba komai aisha farida
taci riba tunda har ya damu yake yi wa
kanwarsa tammbayoyi akanta. Ta fara Allah
Allah a tashi daga asibiti taje gida ta bawa
abida labrin cigaban da aka fara
samu......bata gama tunanin da takeyi ba
taji karan takalmi ana tahowa a baranda, ko
da ta daga ido dr shuraim imran ta hango
yana tahowa. Kallo daya tayi masa sai tayi
sauri ta kawar da kai gefe, sai da ya wuce
ta sai ta sake juyar da kai wani bangaren ta
rantse shi dinne dai ba zata kalla ba. Abin
mamaki sai taga ya wuce yana kallonta har
da waiwaye. Don son ya gasgata abun da
yake gani, sai ya dawo ya sake wucewa ta
gabanta, wannan karon ma can gefe ta
muskuta bayan kan ma har da jikinta ta juya
ta nuno masa keya. Ya fice ya sake
dawowa, sai yaga ta juya daya bangaren
gaba dayanta. Tabbas ya shaida dashi take
ba zata kalle shi ba. Baifi minti uku da
shiga ba dakin marasa lafiya ba, sai gashi ya
fito a karo na uku yana ta waya, amma fa
yanayi yana duban aisha farida donya ga
abun da zata yi. Sai tayi saurin dangwafar
da kanta kasa ba ta dago ba har ya wuce
waje, iyakacinsa kan baranda yaje ya dawo
har yanzu wayar yake yi, da alama da
kanwarsa farida suke magana tana wajen
likita. Bata dago ba, sai da ta tabbatar ya
shige babban dakin kwanciya na mata. Sai
mamaki ya rufe aisha farida matukar
mamaki kuwa. Wato ashe rububin nan da
mata sukeyi a kansa da kallonsa, da
shishige masa dadi yake ji kenan? Da
gangan yake basarwa yasan ana sonsa
kenan, ai ga shi yanzu bai ji dadi da ta share
shi ba, tabbas ya bata satar amsa ya hadu
da shariya sai ta rama duk abubuwan da
yayi mata, inyaso ta rabu dashi daman ta
fitar da ran samunsa. Bata gama tunanin da
takeyi bi sai ta tsinkayo shi ya fito shi da
matron maryam suna tafe suna magana har
da kyakyata dariya. Dariyarsa tana tayarwa
da aisha farida hankali, saboda sai yayi
dariya kyawunsa yake kara bayyana.
Aisha farida ta mike tsaye a nutse tana
duban Matron maryam ita kadai, yayin da
suka tunkaro inda take tsaye. Bai kalle ta
ba, haka itama. Matron maryam ta dafa
kafadarta tace Allah sarki 'ya ta yi hakuri na
zaunar dake ko? Ina so in fito aka tsayar
dani ai munyi waya da ita tace ba ta baki
sakon ma yana nan waje shima yazo tun
dazu, gezawa zai kai. Wannan shiriirta tawa
dai Allah Ya shirya na barku ku biyu kuna
jira, ke baki sanshi ba shi bai sanki ba balle
ince ki bashi. Gashi baki da waya da na baki
lambarsa, dole dai sai nazo.
aisha farida tayi murmushi tace babu komai
matron. Ta duka cikin ladabi ta mika mata
'yar karamar ambulan din. Matron maryam
ta karba tayi godiya fuskarta cike da fara'a.
Dr shuraim na tsaue a gefe hannayensa
dukka biyi na cikin aljihun wandonsa kansa
a sunkye a kasa bai cika kallonsu ba, yayin
da aisha farida take gaggawar barin wajen,
matron kuwa sai tsayar da ita take tana
damunta da surutai barkatai. Dr shuraim ya
dubi agogon dake hannunsa ya huya ya
dubi matron yace sister maryam zan koma
ciki, zamu hadu anjima, kinsan ina duba
patient. Tsaya tsaya kanina, gara mu gama
magana don idan ka zille min bansan sanda
zan sake nemo ka ba, da gaske nake ni da
mijina muna neman visa london ya za'ayi
kenan? Aisha faroda ta samu ta sulale ta
barsu nan a tsaye suna magana. Tana tafe
tana mamakin wannan kyauta da Allah yayi
mata a yau, Ya jeho mata sahibinta ta
ganshi har ta gaji sabanin da, da sai ta yini
tana zagaye bata ganshi ba.
Tabbas abida tayi gaskiya, babu abinda yafi
irin ka daga hannu ka roki Allah abinda kake
so, zai biya maka bukatunka cikin gaggawa.
Ta kudiri niyyar zagewa ta lullunka yin
addua fiye da yadda take yi a baya. Ta isa
wajen 'yan ajinsu sunyi aiki yadda ya
kamata, har zuwa lokacin tashinsu, kowa ya
lura yau aisha farida tana cikin walwala har
ma wasu na tambayarta meyasa take
murna yau. Da ta isa gida tun daga tsakar
gida abida ta lura da yawan fara'arta don
haka sai tabi ta cikin daki tana tambayarta.
Lafiya meya faru yau naga kina ta fara'a? Ko
aisha farida bata fada ba, abida ta canki
daidai cewa tayi nasan dr shuraim ne ya
saka ki walwala yau. Aisha farida ta kwashe
da dariya ta gyara zama ta zayyane mata
duk abubuwan da suka faru a yau.
Tambayar da farida ta furta itace anty
meye abunyi a nan gaba? Abida har kamar
tafi farida farin ciki, sai tayi dariya tace ki
zuba min ido gobe ni nasan abin da zanyi
masa. Mamaki mara iyaka zaka iya gani
daga idanuwan farida, zatayi tambaya abida
ta katse ta, tace kada ki tambayeni, ki saka
min ido kawai. Allah Ya kaimu gobe. Asuba
ta gari AISHA SHURAIM!!!
Washe gari da asuba kiran farko aisha farida
ta bude ido, abin mamaki sai ta dinga jin
motsi a kofar dakinta. Ta kame a kwance
sannnan dai ta tabbatar ba aljanu bane,
haka ba bakin dare bane wato barayi.
Motsin abida ne don ta jiyo tarinta. Aisha
farida ta cika da mamaki me ya fito da
abida ne daidai wannan lokaci? Shine me
takeyi a waje ta dade haka? Aisha farida ta
mike a hankali tana sanda taje ta tura
window ta leka duhu kirin tsakar gida,
amma da hasken fitilar kwai a gaba abida,
tana gaban murhu tana dahuwa. Sai
mamaki ya sake lullube zuciyar aisha farida.
Ta ambaci sunan abida atsorace a hankali
cikin rada. Nan da nan abida ta dago ido ta
dubi window tayi murmushi tace farida
tsoro kika ji? Kada ki firgita nice dahuwa
nakeyi. Aisha farida ta maimata dahuwa?
Me kike dafawa da tsakar daren nan? Abida
tayi dariya tace asuba ce ai yanzu, idan ya
dahu zaki gani. Tayi wuf ta bude kofa ta fito
tana kokarin bude tukunyar don taga abin
da ake dafawa. Abida ta rike mata hannun.
Tace idan ya dahu da safe zaki gani, abincin
mijina ne. Aisha farida tace bulaguro zaiyi?
Abida tace eh. Aisha farida tace ina zaije?
Abida tace lagos. Aisha farida tace zai bi ta
shagamu? Abida tace ba lallai bane don
daga ofis zasu tafi. Aisha farida tace zai
dade ne? Abida tace zai kwana biyu, kina da
sako ne a fada masa? Aisha farida tace a'a
zan so muyi sallamai dai kafin ya tafi
saboda halin tafiya. Abida tace kada ki
damu zan masa magana kafin ya fita sai
kuyi sallama. Aisha farida tayi murmushi
tace anti bari nayi alwala inyi nafilfili kafin a
kira assalatu, sai inzo inci dadi, ina jin dai
kaje ne ake rababbaka mana. Abida tayi
dariya ba tare da ta bata amsa ba. Doguwar
sujjada aisha darida keyi tana ta addua tana
kai kukanta wajen Ubangijinta Ya bata abin
da take so wato dr shureim idan har shine
mafi alkhairi a gare ta. Idan kuwa babu
alkhairi tana rokon Allah Ya yaye maata
sonsa Ya bata wanda ya fishi alkhairi. Sai
taji hawaye yana surnanowa daga
idanuwanta, don tana tausayawa kanta da
kanta, halin da ta tsunduma na soyayya.
Ba ta bar kan tabarmar sallarta ba sai bayan
datayi raka'atanil fijr da kuma sallar asuba,
ta tofa adduoi a tafin hannunta ta shafa a
fuska sannan ta mike zuciyarta cike da farin
ciki tana da tabbacin Allah Ya amshi
adduointa. Don shi kadai ne mai bayarwa
wahidul kahharu. Daga nan sai ta shiga cuku
cukun yin wanka da shiryawa saboda tafiya
asibiti. Kafin ta kammala gari ya waye
wasai, sai ga abida dauke da dan faranta da
cokali a ciki ta mikawa farida. Aisha farida
ta karba da sauri cike da mamaki, sai ta
duba taga ai dambun shinkafa ne ya sha
zogale da gyada, ya tiraru kuwa sai kamshi
yake yana hayaki, da zafinsa kau. Ta koma
ta zauna ta dandana, sai taji zakwai ya sha
maggi da gishiri, ga dan yaji yaji sabida
attaruhu da albasar da aka yayyanka yiri yiri
a ciki, aka turara dasu sai kamshi yake
tashi, hade da kamshin man gyada ziryan.
Aisha farida ta girgiza kai ta sosa kunne
tace tunda Allah Ya halicce ni ban taba cin
dambu mai dadi irim wannan dambun ba.
Lallai yaya yana cabawa irin wannan
haduwa haka? Abida dai na tsaye a kanta
murmushi kawai take yi bata ce komai ba
har yanzu yayin da aisha farida ke faman
turawa a cikinta tana ta santi.
Aisha farida ta dagi ido ta dubi abida tace
abin mamaki kuma dambu da aka sanshi da
shakewa mutum makogoro sai gashi
wannan dambun baya shake mutum silif
silif yake wucewa. Wai, yaushe rabon in
karya kumallo a gida, lallai yau zanfi jin
dadin aiki don cikina yayi nauyi. Allah dai ya
saka da alkhairi, Yaya hussani yayi sa'ar
mata. Da dambun zai tafi a cikin food flask
su dinga ci a hanya? Abida ta fita bakin
kofa, sai ga tata shigo riki riki dauke da dan
kwandon roba mai marika, irin wanda ake
saka flask din abinci. Aisha farida tace lallai
haduwa irin wannan sabon food flask haka?
Yau aka bude shi daga leda duk saboda
yayana tabbas babu mu babu kara aure.
Abida tayi dariya tace bude ma kiga yadda
aka shirya ciki. Aisha farida ta jawo
kwandon ta daga wani babban hankici sakin
ulu, wanda dashi aka lullube saman. Ta zaro
wani dallelan flask mai madaidaicin girma,
tsaka tsaki karkashinsa kuwa farantai biyu
ne na tangaran da babban cokalin diba
wato serving spoon da cokula biyu
dukkansu sababbi ne filfil a wanke tas tas.
Aisha farida ta gyada kai tace lallai wannan
kwandon abin sha'awa ne tun kafin na
bude ma abinda yake ciki. Abida tace bude
mana ki gani. Aisha farida tayi bismillah ta
bude, tana budewa sai wani kamshi ya daki
hancinansu. Aisha farida tace humm lallai
abin ma son kaine ko anty, ashe har da
hanta da koda aka yayyanka a ciki shine ba
a sako min bako daya sai maigida aka
tulawa gasu nan burjik a ciki.
DUK KYAN TAKALMI 2* 7
Abida tace me kika yi masa haka a rayuwa
da zai tsane ki? Ba zai tsane ki ba, saboda
kin riga kin kai kararsa wajen mahaliccinsa,
zan sake baki wasu adduoi masu zafi
wadanda suke kara soyayya da tausasa
zuciyar wanda kake so. Idan kina karanta su
hakika dole yaji yana sonki sosai. Adduar
itace "Allahumma ya mukallibul kulubi
wamusarrafuha kaifa ya sha'u usaibarul
muhabbati fi kalbi (ambaton suna) bi hakki
ismikal wadudu Ya wadudu. Ya wadudu sai
dubu daya da dari daya da goma sha daya.
Kiyi tayi kullum har zuwa lokacin da zai
sanke kece mai dambu sai ya hadu da
kaunar dambun da aikin wanna adduar su
fara aiki. Ni kuma a lokacin zan fada miki
abu na hudu da zaki rike nan gaba, kinsan
yanzu uku na fada miki shine ADDUA,
HAKURI da RIKE MUTUNCI. Bazan fadi na
hudun ba, sai a lokacin da kika tabbatar min
ya gama saninki. Idan ya ganki a ko ina zai
shaidaki, zai kira sunanki, zaiyi miki
murmushi, zaki gaishe shi ya amsa cikin
farin ciki, to sai na jeho miki makami na
hudu wato taryo soyayyarsa. Aisha farida ta
lumshe ido don dadi tace kamar a mafarki
nake jina. Sai nake jin bayaninki kamar na
samu shuraim na gama. Abida tace shi yasa
ake so mutum ya rike Allah, Shi zai biya
masa bukatunsa banda bin boka ba ko 'yan
bori. Shiyasa mata muka fi yawa a wuta,
saboda karamin tunaninsu da gaggawa.
Gaggawa kuma daga shaidan take, yanzu da
kika riki Allah zaki ga yadda Allah zai
taimake ki, ko baki samu shuraim ba zai
musanya miki da wanda ya fishi, kuma zai
tanadar miki babban rabo a lahira. Aisha
farida ta gyada kai tace haka ne. Allah Ya sa
mu dace, wadanda suka bata irin su Ummi
Allah Ya ganar dasu gaskiya. Abida tace
amin. Ci abinci ki fita kije ki cefano min
kayan dambu. Asuba ta gari AISHA
SHURAIM!!
Washe gari aisha farida tayi sammakon
zuwa ofishin dr lukman tayi sa'a kuwa tana
isowa kamar tare suka zo, shima yazo yana
bude ofis dinsa, don haka sai suka dunguma
suka shiga tare. Ta gaishe shi ta ajiye katon
kwandon mai dauke da katon food flask din
abinci, babban na jiya ne da farantai hudu
da cokula hudu. Dr lukman yayi murna da
ganin dambu kuma yayi godiya. Yau ma yayi
kokarin bata kudin taki karba, tayi gaggawar
fita daga ofishin ta rufo masa kofa. Misalin
karfe uku da rabi ta koma ofishin ta iske
ofishin a kulle baya nan, amma ta jiyo
muryarsa a ofishin dr shuraim, don haka sai
ta sadada ta bar wajen. Ta dade a labe tana
hango kofar ofishin ko zai fito bai fito ba,
sai ta hakura ta tafi gida. Yau dai bata
walwala sosai, don bata jiyo sakamakon
jarabwar dahuwar dambu ba. Shin gogan
nata yaci koma bai ci ba? Ya yaba ko ma bai
yaba ba? Data fadawa abida sai tayi dariya
tace ai ya ci ma kawai tunda kika jiyo
muryar dr lukman a ofishinsa suna tare,
babu yadda za'ayi yaga dambun yaki ci.
Aisha farida tace ya za'ayi kuma gobe?
Abida tace dan wake zanyi musu ki kai
musu tunda shuraim yana son dan wake.
Aisha farida tace a'a kada ayi, ki bari dai a
kwana biyu kada lukman din ya zargi wani
abu, ko yaji tsoro. Abida tayi darriya tace
tsoron me? Idan kika kai musu dan waken
kika dauko duka food flask dinn sai muyi
shiru muji abinda zasu ce, kuma muji
wanne suka fiso, suka fi jin dadinsa. Sai mu
dinga yi musu shi. Aisha farida tace ni sai
nake ganin kamar duk ba zai damu da sai
yasan waye yake dahowa ba, balle ya
sanni. Abida tayi murmushi tace kin manta
abinda nake fada miki, ki zama mai hakuri
duk mahakurci shi yake cin riba.
Aisha farida ta jinjina kai tace haka ne,
shikenan zanci gaba da hakuri. Abida tace
yawwa tashi muje mu daka yaji mai dadin
gaske yadda zasuji dadin danwaken sosai.
Sai ki siyo tumatur, albasa, kokunba duk a
yayyanka musu a ciki. Aisha farida tayi
dariya tace har naji yawuna ya tsinke,
gaskiya danwaken nan zaiyi dadi, zaiso shi.
Rana ta uku ranar alhamis kenan kamar
kullum da sassafe aisha farida ke fitowa
daga gida tana fin kowa sammako. Tayi jira
fiye da awa biyu sannan dr lukman ya iso.
Sai da ya jima da shiga sannan tabi
bayansa. Yayi farin ciki da ganinta, sai dai
yayi matukar mamaki da jin dadi da ya ga
ta sake dire masa wani kwandon abinci a
gabansa. Yace lafiya, meye wannan kuma?
Dama kin dauki kwandon jiya? Ta girgiza kai
tace nazo baka nan sai na wuce gida kawai.
Wannan wani ne na kawo muku, wannan
karon ba dambu bane, wani launin abincin
gargajiyar ne. Dr lukman yace a'a 'yar
shagamu kinaso muyi fada ko? Yaya zaki
tayi mana wahala, kartai muna taruwa
muna cinyewa babu ko sinsinmu? To
gaskiya bazan karbi wannan ba, ki koma
dashi gida, ko ajiyar ma bazan yi ba. Aisha
farida tayi dariya tace yi hakuri yayana,
daga yau shikenan. Yace kwanukan jiya
suna ofishin dr shuraim, kuma bana jin yazo
yanzu, don bai cika zuwa da wuri ba. Ina da
mukullin ofishinsa bari in bude in dauko
miki kwandon da farantai da cokulan,
amma ainahin food flask din ta tafi dashi
gida, dambun jiya yayi dadi sosai, har yafi
na shekaran jiya. Sai yace dole ya kai wa
babansa yaci yaji irinsa, donshi ya koya
masa cin dambu. To wallahi kinji yadda
akayi, sai anjima zai zo zan ma sake yi masa
waya kada ya mance dashi a gida, lallai lallai
ya taho dashi. Tuni farin ciki ya cika zuciyar
aisha farida, taji tamkar ta daka tsalle don
murna. Tayi dariya tace ba koma dr ai ko
food flask dinnan ba yanzu zan dauka ba,
sai da yamma. Yanzu aji zan tafi. Sukayi
sallama aisha farida ta tafi, kowannensu na
farin ciki.
La'asar sakaliya Aisha ta tunkaro ofishin dr
lukman saita hango gogan nata yana shige
da fice tsakanin wannan ofishin zuwa
wancan dauke da wasu fayil don haka saita
diro daga kan barandar ta shige lungu ta
samu waje ta zauna har saida ta ga fitarsa
ya shiga motarsa ya tafi gida bata bari ya
ganta ba.ta tashi cimak ta nufi ofishin dr
lukman hankalinta a kwance baby wata
fargaba dr lukman ta iske shi kadai da
alama shima ya miqe yana shirin tafia gida
yana ganinta yayi dariya yace yar shagamu
gaskia kin iya girki kice daman tun farko a
shagamu na nemi mace ba'a yobe ba
kinsan yadda mukayi santin dan waken nan
dr shuraim har cewa yayi week end zaizo in
kaishi ya gaida kakata mai dambu da dan
wake da yake nace musu itace take daho
min Aisha ta tuntsire da daria tace lallai
kuwa daka zo shagamu an baka mata daka
sha girki mai dadi ya miqo mata
kwandunanta guda 2 yana godia tana godia
suka yi sallama ta tafi tana fitowa bakin get
ta dane acaba sai gida tana mai farin cikin
zuwa sanrwa da abida labari.Abida na
ganinta sai tabi ta daki suka rungume juna
suna murna tun ma kafin abidar taji labarin
abunda ya faru. Aisha tace zauna in baki ki
sha suka zauna Aisha ta zayyana mata suk
abubuwan da suka faru yau tsakaninta da
dr lukman da abunda dr shuraim ya
fada.Abida tayi murna sai ta shiga bubbude
food flask din ta bude na farko saiga kudi
yan 500 sabbi har guda 4 tayi sauri ta bude
daya food falsk saiga yan 1k har guda 3
suma sabbi sai su duka suka bude baki suna
mamakin wannan kudi da suka gani Aisha
tasa hannu a hankali ta debo yan dari biyar
din ta shinshina saita a jiye a gefe ta sake
yan 1k ta shinshina saita lumshe ido tayi
murmushi ta dubi abida tace wadannan
kudin daga dr shuraim suka fito shinshina
kiji qamshin turarensa Abida ta karba da
sauri ta shinshina tace ehmm qamshi farida
har a jikin kudi kike gane qamshin turaren
masoyinki?lallai kin laqanci qamshin
turarensa to shine ya zuba wadannan kudi
kenan dr lukman ya zuba yar dari 500
dinnan daya ga kinki karba?Aisha tayi fari
da ido tace Allah sarki mai karbar addu'a
kalli daki-daki yana koro mana hanyar
haduwa da shuraim a cikin ruwan sanyi
yanzu ga kudinsa ya shigo hannu cikin
hikimar ubangiji sai ta fara kuka Abida tace
kada kiyi kuka kici gaba da dagewa da
addu'a to yanzu kin ga kudin dr
shuraimkinyi kuka ina ga ranar da kika
ganshi kacokan a qofar gidanku yazo zaance
balle ranar da zaki ganshi a dakinki a
matsayin mijinki?sumewa zakiyi kenan don
dadi?Aisha tayi daria tace gobe jumu'a yaya
za'ayi a sake musu ko a bari?abida tace aa
tsahirta gobe jumu'a sai kije ofishin dr
lukman kice doctor ranar litinin me kuke so
a dafo mukudambu ko dan wake kiji
abunda zai zaba saiki zo tun ranar asabar
mu fara aikin hada musu mai dadi da kunun
gyada ko kunun tsamiya zakiyi musu mu
zuba kofuna qanana zasu so shi kinga suma
duk abincin gargajiya ne Aisha tace gaskia
koba a fada ba dr shuraim zai so kunu sosai
shike nan haka za'a yi.Anan dai suka bar
hirar Aisha ta hadawa abida dukka kudin 5k
ta ce ta riqe a wajenta ba sai ta dau ko sisi
ba tunda ita ce take cefanen nan a aljihunta
asuba ta gari farida shuraim.
Khadija sani isma'I'll ce ta duni Aisha tace
wai me yasa kullun idan nace kizo ki rakani
babban daki na maza saiki turje ki tsaya
daga nan kice inje in dawo ba kya son
shiga?Aisha tace babu komai wlh ni dai
kibar ni nan kije ki dawo zan jiraki ko hour
nawa zakiyi khadija tace idan dai bazaki
raka ni ba nima ba zan je ba daman ba
wani abu zanyi ba illa in leqa ta wajen ofis
din kyakyawan likitana dr shuraim musu
mukeyi da mrym kinsan yanzu ta saki ranta
ta daina kishin dani data ga ta rasa nima na
rasa kuma bazamu samu ba mu duka sai
dai in mun hadu muyita labarinsa cewa tayi
yafi kama da larabawa ni kuma nace kyan
indiyawa gare shi shine nake so mubi ta
ofishinsa mu tantan ce nida ke kinjin Aisha
ya ne ya buga bummm!don fargaba nan da
nan taji hankalinta ya tashi tace a ranta
daman har yanzu khadija da maryam basu
daina son abuda nake matuqar so ba? Lallai
ashe akwai hargitsi a nan gaba gara ma dai
kawai in haqura da son mutunmin nan in
hutawa raina abida ce taqi haqura dana cije
na daure na watsar da son koda kuwa
zuciata zata lahanta koda ciwon zucia zai
zama shine ajalina in mutu in huta.sai taji
kwalla ta cika mata ido sai khadija ta
mungure ta sannan ta fara fahimtar
maganar khadija keyi khadija ta kalli farida
tayi murmushi tace kiyi min wannan
taimako yau dai ki raka ni har ofishinsa ba
komai zanyi ba illa in kare masa kallo in
tantance nidai nasan akwai wanda yayi min
kama dashi a film din india Aisha ta fusata
tace shirme kenan haba khadija kamar
wasu yan primary?ki tuna fa jami'a muke
shirin gamawa kuma manyan ma'aikata
muke shirin zama ma'aikatan ma na jinya
masu kula da lafia jama'a wadan ake
girmamawa a al'umma ya kike abu kamar
marar ilimi?kinsan mutumin nan kinsan
halinsa ke za ki fadawa wani irin salo da
launin wulaqancinsa.ke kika cemin min kin
haqura dashi baki yadda kika burge ni ba
har kika umarci muhammad saurayinki ya
kawo kudin aure ya kawo aka saka muku
rana tamkar matar aure kike saboda anyi
miki baiko ma'ana anyi wa wani alqawalin
bambancinki da matar aure kadan ne
mijinki kyakyawa dan gayu mai ilimi babban
ma'aikacin banki da kadan shuraim yafi shi
kyau habah khadija kada kibani kunya mana
ashe har yanzu akwai namijin da zai burge
ki bayan mijinki?kada fa ki zama irin matan
nan da zasu yi aute kuma suna son wasu
mazan a waje babban bala'I ne yin haka
dunia da lahira halaka ce.idan kin san
zuciayarki bata kwanta da auren
muhammad ba gara kada ayi kice kin fasa
kizo mu tayaki yaqin neman soyayyar
wannan dan wulaqancin!kahadija ta tuntsire
daria tace dadina dake Aisha umar akwai
fadar gaskia komai dacinta wlh ko dan
bazan zama daga cikin irin matan nan da
kika zano ba insha'allahu ba zan sake zuwa
ganinsa ba daman sai na manta dashi sai
maryam ta tsokano min zancen itace har
yau bata gama haqura ba Aisha umar ta
kalli barandar can ki gani.
Aisha ta wurga ido da sauri dr shuraim
imran ta hango yana tahowa tafia yake a
tsanake fuskarsa cike da fara'a jama'a suna
ta gaishe shi yana amsawa idonsa ne ya
wurga ya wurgo kansu Aisha farida
wadanda ke tsaye a jikin bishiyar dake kusa
da barandar da yake tafe kai kace ita da
khadija saurayi da budurwa ne suke
zantawa sun fuskanci juna suna tsaye cirko-
cirko babu wanda ya sake magana a cikinsu
yayin da khadija ke kallonsa tana yi masa
murmushi. Aisha kuwa sauri tayi ta juyar da
kanta gefe bata duban bangaren da yake
ma Aisha taji tamkar ta kurma ihu don
takaici tada ji khadija ta maqe murya ta
gaishe shi saii ya amsa cikin farin ciki ya
wuce abinsa sai da yayi nisa khadija ta
zungure ta tace amma bakida kirki kina
ganin malaminki amma kika qi gaishes shi ?
naga alama fa baiji dadin ba da baki gaishe
shi ba Aisha ta tabe baki tace yaya akayi
kika san baiji dadi ba? Khadija tace saboda
naga irin kallon da yake yi miki ne leqen
fuskarki yane tafe yana waiwaye so yake ki
juyo ya ganki Aisha tace ai ba dole ne in
gaishe shi ba tunda in an gaishe shi sai
yaga dama yake amsawa ke rabi ni da
wahala kinji ta kaina nake bani da lokacin
kowa.khadija tace kin huta ai shiyasa kike
burgeni ina son halinki ko bayan idonki ina
fada daman tun farko ma dai naga alamar
kin tsani dr shuraim ko zancensa ba kya ayi
miki Aisha tayi wani lalausan murmushi ta
gyada kai tace me yasa zan tsani musulmi
dan uwana ?aa wlh ban tsane shiba ko
kadan ina sonsa so tamkar raina zai fice
kamar yadda nake son dan uwana na jini
saboda shi ma musilmi ne musulmin ma
mumini mai riqe addini irinsa khadija tayi
doguwar ajiyar zucia ta dauka Aisha ma zata
ce itama ta mato a sonsa yadda itama take
sonsa sai taji farida tayi kwana.suna tafe
suna firarsa har zuwa bangaren da suke
wato wajen masu ciwon hawan jini da
ciwon suga Akan barandar da suke tafe a
nan shuraim ya taho suna daga ido sai suka
hango shi daf dasu shi yana tahowa su suna
tafia sai suka yi gum da bakinsu don birarsa
suke a lokacin dan halak yaqi ambato inji
khadija Aisha ta duqar da kanta qasa bata
sakw dagowa bahar sai daya gifta ya wuce
kamshin jikins ya daki hancinta sai ta
lumshe ido ta fada a zuciayar ya Allah ina
son wannan bawa naka sannu likita sanna
da qoqari kalaman da suka rikito kunnen
Aisha ke nan daga bakin khadija take
fadawa dr shuraim dai-dai sanda yazo
giftawa ya fada cikin qasaita thank u ya
wuce abinsa Aisha farida tafia take kawai
amma tamkar ta hadiyi zucia don jin
haushin barar da ajin da khadija keyia
wajen bawan Allah nan.
Khadija ta zunguri Aisha tace saki dago da
kanki dodon naki ya wuce don naga ko
kallonsa ba kya son yi ikon Allah shi kuwa
sai ya tsura miki iso yayi ta kallonki don
Allah ki dinga gaishe shi bin na gaba fa bin
Allah ne Aisha tayi ajiyar zucia tace Allah
yabamu ikon bin shugabanninmu amma
wadanda suke bin Allah khadija tayi daria
tace shegiya Aisha umar akwai iya magana
nasan baki yarda da abun dana fada miki ba
zaki dinga gaishe shi ba kenan?kin jini ne
dai kawai Aisha tace uhmm kawai take
fadin sai kuma gyada kai take tayi tamkar
kadangaruwar ta kasa cewa komai saboda
ganin dr shuraim dinnan da tayi yau yayi
mummunan fama mata son data keyi masa
Aisha shuraim haquri shine maganin zaman
duniya! Aisha ta cika mamaki a lokacin da
yaro ya leqo dakinta yace tazo wani yana
sallama da ita a qofar gida a motarsa a
zaune ta duba agogo karfe 7:30 na dare ko
isha'I ba'a kira ba yadda take zaune akan
abun sallarta sanye da hijabi da carbi a
hannuta haka tayi zunbur ta miqe tace da
yaron tsaya ni mu tafi tare ka kai ni wajen
mai yin sallamar dani faruk ta gani dan
abida a tsakar gida tace idan mamarka ta
idara salla a kace mata anyi kirana a qofar
gida ina zuwa ya amsa da to aunty Aisha
zaki siyo mun alewa da biscuit?aisha ta
girgiza kai banyi maka wannan alqawalin ba
nima nan daka ganni na dade ban sha
alawaba ta wuce da sauri ita da dan aike ta
kama hannunsa tace yaro a ina mai motar
yake?wayace ka kira?yaron yace a wajen ya
tsaya kafon a hayo sai ya kirani yace inzo
nan gidan nan mai bishiyar dirimi in kira
masa Aisha umar qanwar husaida mijin
abida shine nake ta leqawa ina tambaya har
aka nuna min dakinki mamaki ya sake
lullube farida ta dafe qirji tace inalillahi wa
inna ilaihi raji'un Allah yasa baqon nan
baqon Alkhairi ne toni waye wannan?ba dai
dr lukman bane balle in saka ran dr
shuraim sune kadai nasani a dunia masu
mota su kuwa basu san gidanmu ba haka
yaro yaya suffar mutumin take?yaro yace
dogo ne haka fari mai dan gemu a habarsa
kyakyawa mai kudi motar hadaddiya Aisha
ta juya kawai tana kallon yaron tana
mamakin yadda yake suffanta
mutumin.tabba s suffofin dr shuraim ya
zano mata amma tana tabbacin ba dr
shuraim bane a wanne dalilin ma zata saka
ran dr shuraim zaizo gidansu mutumin da
har yanzu bai game gane taba a hanya balle
wata hulda ta hada su harma ya tako a
qafarsa ya zo inda take don haka ta cire dr
shuraim a tunanin ko shine sai ta koma
sake saqen wasu daban suna tafe fakam-
fakam sai sauri suke zubawa ta sake juyowa
ta dubi yaron tace yaro shi kadai ne koda
macea motar?yace shi kadai ne! Aisha ta
fada a bayyane toni Aisha waye wannan da
akwai mace a motar sai ince khadija ce ta
kawo min mijinta mu gaisa yaro kawo bakin
wata dalleliyar motar qirar BMW baqa
wuliq sabuwa dal!har sheqi take ya ce ga
motar mutumin yana ciki,
Gabanta ya yanke ya fadi daf-daf taja ta cije
ta tsya a gefe tace kwankwasa masa gilashi
kace masa gata ka kira ta don inga ko waye
yaro ya qarasa da sauri ya daddage ya daki
glass kai kace qofar qarfe yake bugawa
lallausan hannu hade da kyakyawar fuskar
dan adamu ne ta fito fili sai gashi ya
bayyana a lokacin da ya sauke gilashin
wundonsa qasa Aisha ta kaikace tana
leqensa daga nesa har yanzu bata gane shi
ba kasancewar akwai duhu wajen duk da
akwai hasken redio motarsa na haska shi
kadan yaron ya dawo wajen farida yace ki
qarasa kinga har yabani N100 Aisha tace
lallai ka caba kaje na gode tafia take a
nutse amma a tsorace kamar ace kulle tace
cas!nauyi kunya fargaba da tsanaanin tsoro
sun gallabe ta ta isa jikin window da yake
zaune ya zuba mata ido yana kallonta
fuskarsa cike da annuri yana nuna farin cikin
da ganinta ta kasa kallonsa saita duqa ta
gaishe shi ya amsa cike da fara'a hadi da
cewa hajia Aisha farida yar shagamu nasan
zakiyi mamakin ganina ko?wannan karon da
sauri ta dago kai ta dubi kyakyawar fuskarsa
domin tana jin muryarsa ta gane ko
wanene tabbasa muryarsa ta tabbatar mata
dashi dinne wanda take zato a lokacin data
dubi fuskarsa.dadi marar misaltuwa suka
tabbata a zucia yar Aisha ta dafe qirji ta
fada cike da mamaki marar adadi barista
mu'azzam yau kaine a gidanmu nayi
matuqar mamaki hade da dinbin farin ciki
dana ganka a gidanmu ka kyauta gaskia
Allah ya bar zumunci yayi daria yace miki
wannan shine zuwana na farko aina sha
zuwa nansai in aika yaro ya dawo yace min.
Ance ba kya nan kai rannan ma ce min kayi
gidan naga wasu maza 3 a zazzaune akan
tabarma suke cemin kina ciki amma
shwararda zasu bani kada in sake dawowa
ba kula zaki yiba haka yayanki ma idan ya
ganni korar kare zaiyi min.na fahimci dai
hassada ce kawai na tafi na barsu yau dai
Allah yasa na sami yaro mai wayo nace ya
shiga ciki ya nemo har. Dakinki ya kirawo ki
amma wanne irin zama kuke da
mutanengidanku haka shin bakwa shiri ne?
sai hawaye ya fara surnanowa a idontaAisha
tana sharbewa da hijabinta barista
mu'azzam ya warwaro toilet paper ya miqa
mata yace aa qanwata kin fara koke -koken
naki ko?bana son kukan nan yanzu zaki
kore ni fa Aisha farida ta goge idanuwanta
tace na daina kuka yayana abun ne yabani
mamaki muna zaune dasu zucia daya muna
qoqarin kyautata musu su basa qaunarmu
ba'a son ci gabanmu ko zaka rufe motar
kazo muje kan dakalin qofar gidan mu
zauna kada in shiga motarka ayi ta
yamudidi dani a unguwa da sharri kala-kala
Alhamdulillah daka san yadda mutanenmu
suke. Barista mu'azzam yace kwarai kuwa
yi gaba zan biyo bayanki kada a ganmu mun
jera muna tafia Aisha tayi sauri ta shiga
gida don dauko sallaya da pure water.
Abida tabi ta daki a gigice tana tambayarta
wai waye yazo a dalleliyar mota ne, naji
matan gidan nan suna ta yamadidi, har
suna aika 'ya'yansu suje su gano musu ke.
Aisha farida ta rike baki tace mun shiga uku
da zaman haya, au faruk ba fada miki sakon
dana bashi ba, nace ana kirana a waje na
tafi. Abida tace bai fada min ba a tsakar
gida nake jiyo gulmar. Kada fa kice min dr
shuraim ne? Aisha farida tace in dr shuraim
ne ba sai mu gudu ba? Bashi bane, barister
muazzam ne. Ta kwashe labarin daya bata
ta fadawa abida, na 'yan hassada. Mamaki
ya rufe abida ita ma sai da tayi kuka. Aisha
farida ta hanzarta daukar sallaya da pure
water guda biyu ta fice da sauri ta iske har
barrister muazzam ya karaso kofar gidan,
kasancewar bayan magriba ne don haka
yawancin mazan gidan duk suna masallatai,
sai anyi sallar ishai zasu dawo. Ta shimfida
akan dogon dakalin mai fadi, sannan ta
umurce shi da ya zauna. Yana zama sai ta
duka ta mika masa pure water ko sanyi
babu, ya karba yayi murmushi yace nagode
ki zauna mana ya zaki tsaya a tsaye, ai ina
ganin akwai tazara a tsakanin mu idan kin
zauna a karshen dakalin, ni ma ina karshe
ba za a ce kinyi rashin kunya ba dai ko? Don
naga alamar unguwar nan taku abar tsoro
ce, suna da saka ido da gulma, koda yake
duk cikin gari haka suke, 'yan gargajiya ne
kawai. Babu maganar wayewa a tattare
dasu.
Aisha farida tayi murmushi ta zauna a
tsorace ta sake gaishe shi, sannan tace yaya
muazzam sai hakuri, bamu da fridge kuma
inda ake sayar da ruwan sanyi babu saboda
munfi sata ba a kawo mana wuta ba, zaka ji
ruwan babu sanyi. Muazzam yayi dariya
yace kada ki damu, yanzun nan na sha ruwa
har roba biyu a mota, na karba ne dai don
kar kiji babu dadi, nagode. Aisha farida tayi
dariya tace a'a nice da godiya, naji dadi da
na ganka, Allah Ya bar zumunci. Ina
abokinka barr nurruddin? Ina baraka
matarsa? Ina kuma matarka dr janan? Barr
muazzam ya kwashe da dariya yace har kin
daura mana aure ne ta zama matata? Duk
suna nan lafiya kamar yadda kika barsu,
babu wanda ya sauya a cikinsu. Nuraddin
yana nan yana taurin kansa, da gallazawa
baraka. Haka itama baraka tana nan tana
hakuri. Ko da yake kwanan nan ta fara ce
min hakurinta ya fara karewa, zata fadawa
magabata a raba auren. Ita kuwa janan
tana nan a daure ana ta tafka sharia babu
wani canji a tsakanina da ita. Iyayenta ne
dai kawai suke ganin kokarina da nake a
kanta, ita har yanzu bana gabanta. Ni har
haushin kaina nake ji wata rana ince to wai
me yasa na nace sai janan bayan a gari ga
'yan mata nan reras wadanda ma suka fi ta
kyau da kwalliya, saboda a yanzu idan kika
ga yadda janan ta koma idan kinsan ta a da
ba zaki ce ita bace, kamar wacce aka sauya
ta gaba daya duk tayi muni, tayi baki, an
aske wannan gashin nata mai tsawo sai
kwas kwas. A ficika wani ba zai dauke ta ba,
amma har yanzu zuciyata bata daina sonta
ba, kuma ita kadai nake so bana son wata.
Wannan al'amaro yana bani tsoro da
mamaki. Aisha farida ta girgiza kai tace
Allah sarki rayuwa, har naji tausayinka.
Wannan shine ake kira soyayyar gaskiya, so
saboda Allah kenan ba don wani abu ba.
K KYAN TAKALMI 2* 9
Dr lukman yace kin tabbata baki gane abin
da yake nufi ba? Kada ki boye min komai.
Aisha farida ta girgiza kai ta zubo da
hawaye da ya cika mata ido tace bansani ba
wallahi. Yace to jeki zanyi miki waya anjima
kada kiyi kuka. Aisha farida ta tashi da sauri
ta fice yayin da dr shuraim ya bi ta da
harara. Tana fita sai ta rufe kofar kuma ta
labe ta dora kunne a jikin kofa tana
sauraronsu. Dr lukman ya juya ya dubi
shuraim yace wai me yake faruwa ne?
Yarinya ce fa kimtsatsiya. Tana bin maza ne
ma'aikata? Dr shuraim yace kaji matsalar ku
kenan, baku da kyakkyawan zato, nan da na
sai ku ballo bala'I. Meya kawo wannan
zargin kuma? Dr lukman ya juya ya dubi dr
mohd yace don Allah dr a kasar hausa idan
aka dubi mace akace ki kama mutunci da
darajarki ta 'ya mace meke nan? Ba 'yar
iska ba kenan? Dr mohd yace kwarai kusa,
kasan bature ne su a london ustazan mata
ake fadawa haka. Suka kwashe da dariya su
dukka, dr shuraim yace uhumm kai kake
ganin hankalin yarinyar na, ai ni tuni nasan
maciji sari ka noke ce. Nafi ku karantar
halayanta. Wato tunda Allah Ya halicce ni a
duniya tsakanin jinsin mace ko namiji ban
taba ganin wacce ta iya hawa acaba irin
wannan yarinyar ba. Sai su dr lukman suka
kwashe da dariya, yayin da dariya ta
kubcewa aisha farida sai tayi sauri ta toshe
bakinta. Dr shuraim ya bata fuska yace ai
ku abin ma dariya ya baku? Wallahi ba abin
dariya bane, ya kamata kayi mata fada.
Hawan jini ne kawai rannan banyi ba,
shekaran jiya ne ma ba adade ba. Caraf
zaka ga ta haye acaba da yake ba nauyi ne
da ita ba, kuma ta kware. Dan acabar nan
ya wulwula da ita suna kallon kudu sai sai
gasu sun juyo arewa ba tare da ya duba ko
ya saka sigina ba, suka rufta kan wasu 'yan
acabar suka tafi tangal tangal kamar zasu
fada kwalbati. Allah Ya kiyaye basu fada ba,
ya tashi hayaki da kara mai tsanani, sannan
ya zuga da gudu kamar zai tashi sama.
Kunsan yarinyar nan ko a jikinta, mutane
babu wanda bai dora hannu a ka ba ya dau
salati don ni sankarewa nayi a zaune wallahi
na dade a daren banyi bacci ba. Dr lukman
yace to don wannan ne ma shine kaki fada
a gabata, kaga ka tayar mata da hankali har
tana kuka.
Dr lukman yace to don wannan ne ma
shine kaki fada a gabanta,kaga ka tayar
mata da hankali har tana kuka. Dr shuraim
yace kukan munafunci ne, tasan abinda
nake nufi ai tana shigowa ta kalli idona ta
dauke kai, tasan na ganta kuma da zata lura
dani tasan na tsani hawan acaba to yadda
kasan tsokanata take yi, ina yawan hango ta
ta dane. Da ace tasan ni ta san ra'ayina
akan tsanar mace ta hau babur da sai ince
da gangan take yi, don inji haushi. To bata
sanni ba, amma tana bani haushi wallahi.
Dr lukman yace ni kuwa yarinyar burge ni
take yi, tana da natsuwa. Dr shuraim yace
tana da hankali amma da ace zata rabu da
hawan acaba da tafi hankali. Aisha farida ta
shafa kirji tayi ajiyar zuciyar jin dadi, ta daga
idonta sama tayi wa Allah godiya, sannan
taci gaba da kasa kunne tana sauraronsu.
Bata damu da mutanen da suke wucewa
suna ta kallonta ba, ko tantama babu sun
san gulma take saurare.
Dr lukman yayi dariya yace zaka sake ganin
hankalinta ma idan yau na sanar maka
cewa ita ce mai yi maka daddadan dambun
nan da danwake wanda kake ci kana santi
kullum. Yanzu ma kiran da nayi mata kenan
zan fada mata ta daho mana gobe. Shine
daga shigowarta kuka hau yi mata
shakiyanci, har kuka sakata kuka, shikenan
duk kun huta gobe ba cin dambu. Dr
shuraim ya sankare, ya dade baiyi magana
ba. Sai dr mohd ne yace ba ruwana wallahi,
data gaishe mu ma ni kadai na amsa, dr
shuraim ne ya share ta. Dr lukman yayi
dariya yace kai ka fara iskantarta kake cewa
wai ko kanwar zamani ce, alhali lallabata
nakeyi, don kada ta zata mun mayar da ita
baiwar mu. Ko kudin na bata ba ta karba,
duk kyauta muke ci in dai ba dubara ba zata
karba ba. Gashi daga dukkan alamu ba su
da hali sosai, dole ce ma yake sawa ta hau
acabar ba zata iya biyan shatar adaidaita
sahu ba, inajin kuma gidansu ba hanyar bus
bane. *nxt page din is damaged, bana
ganin rubutun sosai*
Dr lukman yayi dariya yace zaka sake ganin
hankalinta ma idan yau na sanar maka
cewa ita ce mai yi maka daddadan dambun
nan da danwake wanda kake ci kana santi
kullum. Yanzu ma kiran da nayi mata kenan
zan fada mata ta daho mana gobe. Shine
daga shigowarta kuka hau yi mata
shakiyanci, har kuka sakata kuka, shikenan
duk kun huta gobe ba cin dambu. Dr
shuraim ya sankare, ya dade baiyi magana
ba. Sai dr mohd ne yace ba ruwana wallahi,
data gaishe mu ma ni kadai na amsa, dr
shuraim ne ya share ta. Dr lukman yayi
dariya yace kai ka fara iskantarta kake cewa
wai ko kanwar zamani ce, alhali lallabata
nakeyi, don kada ta zata mun mayar da ita
baiwar mu. Ko kudin na bata ba ta karba,
duk kyauta muke ci in dai ba dubara ba zata
karba ba. Gashi daga dukkan alamu ba su
da hali sosai, dole ce ma yake sawa ta hau
acabar ba zata iya biyan shatar adaidaita
sahu ba, inajin kuma gidansu ba hanyar bus
bane. *nxt page din is damaged, bana
ganin rubutun sosai*
Dr shuraim ya ja doguwar ajiyar zuciya yace
Lukman don Allah da gaske kake ita ce ke
dafa ma dambun nan da kanta?dan iska
kace kakarka ce ko kakarku daya ne? Dr L
yayi dariya yace ka taba ganin dangina a
kano balle in yi kaka? wallahi itace ta ke
kawo min da farko ma ajiya ta kawo ta
dahowa kawarta an kwantar da ita anan
asibitin to bata san an sallameta ba nace
mata za mu dandana tace mu cinye dukka"
dr Sh yace to me yasa ka boye mana kace
kakarka ce take dahowa? Lukma yace kawai
don inji dadin bakina ni ma kun koya min
shakiyanci ne ai? Dr sh yayi shiru can yace
kuma yarinyar ta tabbatar maka da
hannunta take dafawa ko dai mamanta?
Lukman yace eai kai me ye abun mamaki ta
tabbatar min ita take dafawa zata min
karya ne?Shuraim yace ashe alkawarinmu
ya tashi ke nan da muka saka ran zuwa
gaishe da tsohuwa mai dambu,ashe
karyarka ce? Lukman yace ga yarinya mai
dambu ta gaishe ka ka ki ka amsa ka yiwa
kanka"shuraim yayi murmushi yace Daman
ai don kai take yi ba don ni ba idan ka yi
mana bakin ciki don kada mu ci to ai shi ke
nan don ta ni mai sauki ne don kada mu ci
to ai shi ke nan don ta ni mai sauki
ne .kada yake Abbana fa ya kamu da son
dambun nan jiya ma ya tambaye ni yaushe
zan kawo masa dambun nan mai dadi inda
ya sake son dambbun ma da nace ba na
gidan sayarwa bane a gida ake yinsa na
musamman ga tsafta"
Lukman yace ka ci albarkacin abba bari in
kirata ta zo in ce ta yi mana"dr shuraim
yace kada ka bari ta san mune muke ci
kasan abun da zaka fada mata"Dr L yace
ban iya karya ba ko karyar kuma zaka koya
mani? Ya dauko wayarsa ya lalubo sunan
Aisha farida ba ta ankara ba ta ji wayarta
tana kokarin daukar kara alhali ga ta a
jingine a jikin kofarsu sai ta falla da gudu ta
fita daga farfajiyar ofisoshin sannan ta
matsa dr Lukmn ya ce kanwata kina kusa
ne ki zo mana ina da magana dake"Aisha ta
amsa masa na da yi nisa yayana sai nan da
minti 30 zan karaso"yace babu komai sai
kin zo tana ganin Dr Shuraim da Dr Mohd
suka fita daga ofishin Dr Lukmn don kada ta
zo ta same su ita ma saboda su din ne ta ki
zuwa da farko da suka fice sai ta yi wuf ta
fada ofishin.Dr L yayi murmushi da ganinta
yace a'a ai ko minti 5 baki yi ba kika zo?ta
ce Ashe zamu gama da wuri na dauka zamu
dade kasan tafiya shi ne muka dan harhada
kayayyakinmu"yayi dariya yace mata dai
duk inda kuka je sai an barbaza shirgi wato
dan zaman da kukayi asibitinmu har kun
baza mana shirgi kenan? Aisha Farida ta yi
dariya tace Wallahi kuwa don wasu jaka
guda cika a nan suke cire kayan
makarantasu wata ma jakar kayan
siyarwarta a nan take bari duk a ofishin
metron Maryam.
Doctor ina so inyi muk dambu da danwake
gobe, ina fatan kana gari ko? Yayi dariyar
farinciki yace kai haba! Kina wahala da
kanki, ki bari kawai. Aisha farida tace a'a ai
nayi niyya ba a mayar da hannun kyauta
baya. Dr lukman yayi dariya yace koda yake
na bankwana ne ko? Gashi zaki tafi ba
ganinki zamu dinga yi ba. Aisha farida tace
haba yayana ko kasar ka bari inda hali ai
zan ziyarce ka balle nan da nan. Ai duk
sanda kake da bukatar dambu ko ba kai
bane, ko abokanka ne kada kaji komai, kayi
min waya kawai. Dr lukman yayi godiya
yace to amma abin da yasa zaki sage min
gwiwa idan na baki kudi ba kya karba, ni
kuwa banga dalilin da tika tika damu mun
daukar albashi mai tskoka zamu zauna
muna tsotse dan alawus din dalibarmu. In
kina so mu shirya to duk abin da na baki ki
karba, idan da ciko na yadda ki cika mana
idan babu yawa, idan kudin sunyi yawa ki
rike canjin. Haka ake rayuwa, sai muma mu
sami kwarin gwiwar cewa a kawo mana
gobe. Aisha farida tace to yayana amma
banji dadin kudin da zan dinga karba ba,
adduarku manyanmu muke nema. Dr
lukman yace kaji uwar iya magana, kin cika
wayo kanwata. Baki tambaye ni laifin da
abokina yake zarginki dashi ba. Kin fita kina
kuka, na dauka kina shigowa abin da zaki
fara tambaya ta kenan.
Aisha farida tayi murmushi ta langabar da
kai kasa tace bana son in cika tambayar
manya, amma tambayar tana raina. Dr
lukman yace uhmm aisha tsiri kenan, ko ba
haka bane sunanki, don naji haka yahaya
yake kiranki. Kina da hankali sabanin 'yan
matan zamanin nan. Dr shuraim yace kina
da hankali amma da zaki daina dane bayan
acaba da sai kinfi hankali. Suka tuntsire da
dariya su dukka. Dr lukman yace ai baya
son yaga mutum akan acaba, musamman
ma mace. Aisha farida tace a zuciyatya ni
da acaba kuwa har abada, tunda yin haka
zai jawo min samun kaunar wanda nake
kauna. Kudin da dr lukman ya miko mata
ne jimus dashi ya firgita ta, ta dafe kirji tace
na meye wannan kudin? Karbi mana. Ya
fada cikin tsawa a lokacin da yake zunguro
mata kudin gabanta. Ta girgiza kai tace dr
kudin yayi yawa fa. Yace nawa ne kike
tunani? Naira dubu uke ne fa kawai, ba
yawa don dai 'yan dari bibbiyu ne shiyasa
kika gansu da yawa. Nifa bana son mu
dinga irin wannan abun, ke fa ni yayanki
ne. Bana son ina baki abu kina kin karba.
Aisha farida tasa hannu biyu ta durkusa ta
karba sannan tayi masa godiya tayi masa
sallamaa ta tafi. Yau farin cikin da yake
lullube a cikin zuciyarta Allah ne kadai Ya
sani, saboda ta sami canji da yawa daga
wajen masoyinta.
Ba ta da wani buri wanda ya wuce ta ganta
a wajen abida ta bata labarin abubuwan da
suka faru tsakaninta da dr shuraim a yau. Ai
kuwa tana isa gida ta iske abida a zaune ita
da matan gida dankar suna hira, suna ta
soya awarar siyarwa. Aisha farida ta kasa
daurewa ta bari har sanda abida zata gama
ta shiga daki sannan suyi hira don haka sai
ta damko hannunta. Tace maman farouk zo
muje ciki in baki sakonki daga shagamu.
Abida na biye da aisha farida har cikin daki.
Suna shiga aisha farida ta jefar da jaka. Tace
Allah Shine Allah, Allah Shi ne mamallakin
duniya da lahira, Shine mai yawan kyuta ba
Ya gajiyawa. Tsarki da yabo sun tabbata ga
Ubangijina, sarkin sarakuna. Bai haifa ba, ba
a haife shi ba. Abida ta runguma aisha
farida yayin da ita ma farin ciki ya lullube
zuciyarta tun kafin taji abin alherin da ya
sami aisha farida, ko ba a fada ba tasan
akan dr shuraim ne. Tace alhmdl farida me
ya faru? Dr shuraim ko? Aisha farida ta jawo
hannun abida suka zauna ta jawo jakarta ta
zaro kudin da dr lukman ya bata ta mika
mata. Tace inji dr lukman suna son dambu
da danwake gobe. Abida ta karba cike da
murna, ta kirga ta daga ido ta dubi aisha
farida ta harare ta. Tace na dauka dr
shuraim ne ya baki kudin da kansa yace a yi
masa?
See Translation
DUK KYAN TAKALMI 2* 10
Aisha farida tace antina kin cika gaggawa,
karkade kunnenki kiji labari. Aisha farida ta
zazzagewa abida labarin abin da ya faru yau
a asibiti tsakaninta da dr shuraim babu dadi
babu kari. Daga karshe ta zurawa abida ido.
Tace kinji abin da ya faru, meye shawararki
kuma meye abinyi nan gaba? Abida tayi
dariya tace Ikon Allah kenan, farida kinga
faidar addua ko? Kinga banbancin
madanfaran bokaye ko? To duk abin da kike
so ki nema a wajen Allah Shi kadai, kuma ki
yarda Zai baki. Aisha farida ta gyada kai
tace na yadda da haka na dade da yin imani
da wannan. Abida tace a yanzu da Allah Ya
sa shuraim ya sanki, yasan kina raye, yasan
sunanki, yasan kina da amfani a wajensa, ya
fara damuwa da rayuwarki, ya fara gane
halayyarki, ya yabe ki da bakinsa. To anzo
gangara, lokaci yayi da zan fada miki mataki
na hudu da zaki taka. Aisha farida ta gyara
zama ta dafe kirji da hannayenta biyu taja
doguwar ajiyar zuciya tace Allah Ya sa zan
iya. Abida tayi dariya ta dafa kafadar aisha
farida tace kada ki damu, ba abu ne mai
wuya ba, guda ukun na farko sun fishi
wahala. Ai abin bi da bi ne, na daya yafi na
biyu wahala, na biyu zai fi na uku wahala,
na uku zai fi na hudu wahala, na biyar duk
yafi su sauki.
Har yanzu dai ajiyar zuciya aisha farida take
yi, zuciyarta sai dukan uku uku takeyi don
fargabar abin da abida zata fada, so take
taji mai yiwuwa ne ko ba mai yiwuwa bane?
Abida tayi shiru kamar mai tunani, can
dagao ta kalli aisha farida tace idan na fada
miki wannan mataki na hudu, ba wai ina
nufin ki zubar da matakai uku na baya ba,
a'a duk zaki hada kici gaba. Kici gaba da
addua sosai ki ma kara wata akan ta da.
Haka hakuri sai kin sake ci gaba sannan ki
hada da na ukun ki rike mutuncinki sai na
hudun da zan fada....saboda kaguwa aisha
farida ta katse ta tace fadi na hudun
wannene? Abida tayi murmushi ta gyada
kai tace ki zamo mai yawan biyayya da
ladabi a gare shi. Jikin aisha farida sai ya
dauki rawa ta rike abida cike da rudani tace
antina ban fahimce ki ba, ta yaya zanyi
masa biyayya ni da ba ganina zai dinga yi
ba, musamman ma mu da zamu bar asibiti?
Abida ta mike ta dube aisha farida tayi
murmushi tace haba farida bafa na son
rikicewa, kina tsoron shuraim kamar wani
malaikan da zai dauki ranki alhali
TAKALMIN da zaki sura ne ki saka a kafarki.
Ki dauki wannan ruguntsumin da ake ciki
tamkar wasan 'yar tsana ne da yara suke yi,
ki dauka tamkar wasan kwaikwayo ne don
nishadi, ki dauka tamkar cartoon din tom
and jerry ne da yara suke kallo a talabijin,
sai ki daina fargaba. Ko kin manta DUK
KYAN TAKALMI KAFA CE MAI TAKA SHI?
Nace ki saka a ranki daurin dan kwalin da
kike yi a kanki yafi wahala akan samun dr
shuraim. Abu ne sassauka dalilina kuwa
shine kince yana da ilimi, yana da wayewa,
yana da tausayi uwa uba yana da riko
addini, ma'ana tsoron Allah ne. To sai kibi
duk hanyoyin nan da kika san yana so kiyi
kane kane. Abin nufi ki zama mai amfani da
iliminki duk abinda zakiyia agabansa, ki
zama mai wayyayyen kai, idan yana wajen.
Ki zama abar tausayi don ya tausaya miki,
sannan ki nuna masa kinfi shi rikon addini,
sai kiga hankalinsa ya karkato gare ki. Aisha
farida ta dora hannu biyu aka tace anti kin
sake rudani, don Allah yi min misalin yadda
zanyi. Abida ta girgiza kai tace bazan fada
miki yadda zakiyi ba, saboda ke mace ce,
kuma nayi imani kowacce mace an haife ta
da irin tata kissar a jikinta. Musamman ke
aisha tun kina yarinya kin kware da iya
zama da mutane da lafazai dadada. Haba
kin manta zamanki a cikin tsofaffi ne? Kin
manta halinki na kissa wanda ko zaginki
akayi sai kiyi dariya ki ba wa mai zaginki
hakuri? To shine wannan. Kije Allah Ya baki
sa'a, sai mun hadu a mataki na biyar in kinci
nasarar cinye wannan jarabawar. Abida ta
juya zata fita, aisha farida ta lngwabe kai
tace anti mataki na hudu yafi na daya dana
biyu dana uku wahala. Abida tace hakuri
yafi komai wahala, tunda kikayi hakuri zaki
iya wannan. Idan baki gane biyayya ba, to
bansan yadda kike so nace miki ba. To bari
dai in baki misalain abin da nake nufi, ki
durkusa har kasa ki gaishe dashi a duk inda
kika ganshi, zaki fita daban daga cikin 'yan
mata a idanuwansa, don 'yan matan yanzu
basu da wannan tarbiyar. Ki rabu da hawan
acaba tunda baya so, sauran kuma kinfini
sani. Aisha farida tayi ajiyar zuciya tace sai
yanzu na fahimce ki, godiya nake. Abida ta
fice yayin da aisha farida ta daka tsalle ta
rungume pillow gami da cewa waYyo
shuraim dina. Da tazo kwanciya ta jima
tana juyi, don tunanin shuraim yayi mata
katutu a rai, ta rasa dalilin da yasa ta tsinci
kanta tana cikin farin ciki yau. Ta kagu gari
ya waye ta dauki dambu ta kai masa da
alama hadin da sukayi wa dambun nan zaiyi
dadi. Daga barci ya soma wartarta sai tayi
firgigit ta bude ido ta jawo wayarta ta duba
agogo tana gudun kada asuba ta shude su
makara ba ta tashi ta dora dambu ba. Karfe
uku saura ta mike taje tayi alwala tazo ta
fara sallah. Rakaoi ba adadi, doguwar
sujjada take yi tana zayyanowa Allah yadda
take so ta kasance a cikin zuciyar shuraim.
Karfe hudu da rabi ta fita ta fara kokarin
dora dambu don ya turara sosai, bayan ta
dora da jimawa sannan taji motsin fitowar
abida daga daki. Abida ta shigo dakin ta
dube ta tayi dariya. Tace kaji mai himma,
wato kin daura dambun tun kafin assalatu
tayi, koda yake aikin shuraim ne babu bata
lokaci. Aisha farida tayi murmushi ba tare
da ta bata amsa ba, saboda tana wuridi.
Karfe 8 saura kwata a babur din a daidaita
sahu ta yi wa aisha Farida ita da kwandunan
abincinta har guda 2.ba ya ga kayataccen
food flask guda 2 manya,daya a shake da
hadadden dambu daya a shake da danwake
sai farantunan tangaran 3 sai cokulla sai
wasu robobi 3 yan kanana masu murfi daya
yaji ne mai dadi gaske ya sha maggi daya
man gyada zaryan aka soya da albasa sai
kamshi yake dayar kuwa salad ne aka yanka
shi kanana da tumatir da albasa da
kokunba.ta isa ofishi kanta tsaye babu
shajja ba tsoro,don ba ta ga motar gogan
nata ba tasan bai iso ba don bai saba zuwa
da wuri ba.
Karfe 8 saura kwata a babur din a daidaita
sahu ta yi wa aisha Farida ita da kwandunan
abincinta har guda 2.ba ya ga kayataccen
food flask guda 2 manya,daya a shake da
hadadden dambu daya a shake da danwake
sai farantunan tangaran 3 sai cokulla sai
wasu robobi 3 yan kanana masu murfi daya
yaji ne mai dadi gaske ya sha maggi daya
man gyada zaryan aka soya da albasa sai
kamshi yake dayar kuwa salad ne aka yanka
shi kanana da tumatir da albasa da
kokunba.ta isa ofishi kanta tsaye babu
shajja ba tsoro,don ba ta ga motar gogan
nata ba tasan bai iso ba don bai saba zuwa
da wuri ba.
Ta kwankwasa kofa sai ta murda ta tura kai
dauke da kwandunan abinci riki-riki a
hannunta ta yi sallama ta shiga sai ta ga
wayam babu kowa a ofishin.babu tantama
ko ya shiga bandaki ne don haka sai ta daiki
gwandunan ta tura lungun da take ganin
yana ajiyewa dan ta kawo masa.tana tsaye
a gaban teburin tana jiran ya fiti amman
shiru kuma abun da ya bata tsoro ba ta jin
motsin komai a bandakin. Motsi ta ji an
turo kofa da karfi yayin da ta waiwaya da
sauri fuskarta cike da fara'a tana murna da
ganin yayanta.tace a ranta ashe ba'a
bandaki yake ba yana waje"sai dai kash da
ta hada ido da mai shigowar ba fuskar Dr
Lkman ta gani ba tayi matukar firgita gami
da razana a bayyane wanda shi kansa
wanda aka yi razanar dominsa ya gane.
Kallonta yake yi a nutse har sai da ya shigo
cikin ofishin ya mayar da kofar ya rufe ya
fara tafiya a hankali zuwa gaban teburin
kusa da inda take a tsaye. Numfashinta ne
yake kokarin daukewa, idanuwanta kuwa
sai suka kasa tsayawa a waje guda suka
dauki farfari yayin da ta nemi yawun
bakinta ta rasa, balle ta samu damar fitar
da lafaxi guda daya. Ya dauke kansa daga
kanta ya zagaya ya jawo kujera ya zauna
yaci gaba da bincike wani file. Da taimakon
addoui aisha farida taji numfashinta ya
daidaita, ta sami nutsuwa a cikin zuciyarta.
Ta dube shi cikin kunya hade da ladabi ta
sunkuyar da kai kasa, sannan ta kaskantar
da muryarta kasa ta zakaka makoshinta, ta
duka har kasa ta gaishe shi. Dr shuraim ya
daga ido ya dube kasa kasa da alama yaji
dadin yadda ta gaishe shi, sai ya amsa cikin
sakin fuska. Ya kara da cewa kina neman
lukman ne ko? Ta gyada kai ba tare da ta
iya hada ido dashi ba, tace eh. Ya dube ta
da gefen ido yace ai bai karaso ba, sai
anjima nine na bude ofishin. Aisha farida ta
duka tace nagode. Sannan ta juya zata fita.
Kamar a mafarki taji yayi mata magana.
Babu abinda za'a ce masa? Ta juyo a nutse
ta dube shi sannan tayi masa wani
dandasheshen murmushi, wanda ta
tabbatar an sha tabbatar mata idan tayi shi
yana kara mata kyau. Siririyar wushiryarta
ta bayyana yayin da kumatunta gefen dama
ya lotsa, fararen hakoranta sai su sake
haske. Tace dama sakonsa ne na kawo
masa, gashi can na ajiye masa. Sai ta nuna
lungun data ajiye kwandunan. Ya wurga
dara dara idanuwansa ya kalli wajen sannan
yaci gaba da dube duben file dinsa. Har
yanzu aisha farida tana tsaye a jikin kofa ta
rike kofa ita bata fita ba, ita bata dawo ciki
ba. Ya dago da kai a hankali ya dube ta,
yayin da ita kuma ta sunkuyar da kanta
kasa a hankali. Yace okay zan fada masa.
Tace kace masa kanwarsa ce aisha farida
umar. Ya dago da kai ya dube ta da alama
yaso yayi mata wata tambaya ya fasa, sai ya
gyda kai yace idan nace masa kanwarsa mai
hawan acaba ai ya sani. Sai ta ya danyi
murmushi lokacin da yake karshen
maganar. Ta langwabe kai ta marairaice ido
kamar mai shirin fasa kuka. Tace yaya
lukman ya fada min laifina jiya, nayi
kuskure bazan sake ba, nima nayi tunanin
naga ban kyauta ba. Sai ya kalle ta kawai ya
ci gaba da rubutu, can yayi magana ba tare
da ya sake dubanta ba. Yace hakan dai zaifi,
ki yiwa kanki fada, don ke mace ce, a
addinance ma bai dace ba. Dan wasu 'yan
acaba ba su da hankali. Ta duka tayi masa
godiya ta murda kofa ta fita. Ta jawo kofar a
hankali ta tafi. Taji kamar ta fasa ihu, ko ta
daka tsalle ta dire don murna. Ta shaki iska
ta lumshe ido ta daga ido sama tayi wa
Allah godiya gami da yiwa alkawarin zata yi
ma Sa azumi gobe don godiya, da Ya fara
karkato da hankalin dr shuraim kanta.
ALLAH ABIN GODIYA!!
BABI NA GOMA Nan da nan aisha farida ta
ajiye aikin ta take yi ta jawo gyalenta da
sauri ta biyo dan aike ta fito don taga mai
sallama da ita da yammacin nan. Tana
fitowa sai taga muazzam ne. Sai ta ji farin
ciki ya rufe ta, tayi sauri ta durkusa har kasa
ta gaishe shi, yayin da ta nemi izini a
wajensa zata shiga ta dauko sallaya ta
shimfida masa akan dakali. Sai ya dakatar
da ita, yace ta bari kawai daman daga wajen
aiki yake hanya ta bullo dashi tanan, shine
yace bari ya karaso su gaisa. Aisha farida
tayi murmushi ta lngawabar da kai tace sai
in rasa harshen da zanyi amfani dashi wajen
gode maka yayana. Allah Ya saka maka da
alkhairi da wannan zumuncin da kake
gudanwarwa a tsakanin mu, nagode. Ai na
sayi waya da wannan kudin da ka bani,
ashe ban karbi lambarka ba, na rasa inda
zan nemo ka, dole na hakura. Na kagu inji
halin da kake ciki, kai da janan. Muazzam
ya lumshe ido yace alhamduliilahi kanwata,
naga falalar addua da hakuri, kuma na rike
mutuncina yadda kika ce. Naje mata da
siyayya iri iri na kaimata, ko kallona takiyi.
Sai na sami waje na zauna nace mata janan
ina so ki saurari bayanina kiji dalilin zuwana
wajenki yanzu. Ada na soki ba kya sona, a
yanzu naso ki bakya sona, don haka na
hakura ba a dole a soyayya. Allah Ya sauya
min da wacce take sona har ma an saka
mana ranar aure. Kiyi hakuri da takura miki
dana yi a da. Ina so a yanzu ki saki jikinki
dani, ki dauke ni a matsayin yayanki, kuma
lauyanki bayan nan babu wata alaka
tsakanina dake. Ina gama fada naga
alamaun jikinta yayi sanyi. Kullum naje sai
inga tana yawan kallona tana kuma bude
baki tayi min magana, duk tambayar da
nayi mata. har na hada baki da wata matar
yayan, sai tayi ta kirana a waya a dai dai
lokacin da nake tare da jana, sai na dinga
amsawa kamar da budurwata nake
magana. Sai inga fuskarta kamar bata jin
dadi. Aisha farida ta cika da mamaki tace
duk a kurkukun ake wannan? Barr muazzam
yace eh ai ana bari na in shiga sai a
kirawota a hado ta da maikaciyar kurkukuk
daya,ta kawo ta inyi mata tambayoyi
saboda neman hujjojin da zan bayar da
kuma nemo shaidu a kotu. Aisha farida tace
lallai ni abin da na lura janan tanan sonka,
tsabar jan aji take yi maka don ta tabbatar
kana sonta, kuma baka fushi duk
wulakancin da zatayi maka. Muazzam yace
haka ne wallahi, sai yanzu na yadda da
haka. Ai nuna mata nake bata gabana kwata
kwata yanzu. Baraka ma ta samu sauyi na
fada mata duk yadda zatayi, kuma ta
aiwatar tana addua kuma tana hakuri,
sannan kuma tana jan ajinta tana yi masa
girki, ta tsaftace gida, ammma ta fita
harkarsa bata bari ma su hadu a gidan,
kwana biyu ko uku tana gidan bata bari ya
ganta. Sai gashi yana fada min wai baraka
ta sauya halinta yanzu ta daina damuwa
dashi, in bashi ya leka dakinta ba, ita ba ta
fitowa. Sai na kalle shi na watsar nace au
har dakinta kake takawa ita da kake korarta
da idan ta shiga dakinka? Sai yace ai dole in
leka inga halin datake ciki, kar inje ta shiga
daki ta kashe kanta ko ta hadiyi zuciya ta
mutu. Nace masa ashe kasan kana kuntata
mata har zata iya hadiyar zuciya ta mutu
ko? To kaji tsorn Allah. Sai yayi shiru bai ce
komai ba. Itama barakar take cemin wallahi
ya fara sauyawa, yanzu da kansa yake
dawowa gida yaci abinci, dga lokacin cin
abinci yayi, da kuwa har kifarwa yake yi a
gabanta idan ta matsa masa yaci. Aisha
farida tayi dariya tace alhamdulillahi, Allah
Ya kara yi mana jagoranci. Barr muazzam ya
dube ta yace ni naga duk kin rame, lafiya
kuwa? Ko dai shuraim din ne ya taba min
ke? Aisha farida ta girgiza kai tace babu
ruwansa bawan Allah, wlhi antina ce abida
bata da lafiya sosai, gabobinta gaba daya
tun daga kafa har wuyanta duk inda
mahadar kashi take ta kumbura suntum,
tana yi mata ciwo, da kyar take tafiya.
Shien muke ta sunturi asibitin kashi na dala
(autopeadic). Anyi xray da gwaje gwaje
sunce basu ga komai ba, ciwo kima sai
karuwa yake. Yanzu da kyar take iya
takawa komai sai anyi mata. Shiyasa kaga
duk na susuce. Subhanallah, Allah Ya bata
lafiya. Inji barr muazzam.
Aisha farida tace amin ai munyi sati biyu da
barin asibiti, rabona da dr shuraim kenan
amma akwai cigaba sosai. Ta zayyanowa
barr muazzam labarin abubuwan da suka
faru tsakaninta da dr shuraim da kuma
mataki na hudu da abida ta karanto mata.
Barr muazzam ya dubi aisha farida cike da
rashin fahimta yace to ni kamar ni ta yaya
zan yi mata biyayya? Kuma kamar baraka
wacce tayi biyayyar a baya bata ci riba ba,
sai da ta share shi ta fara samun saukin
wulakancin? Aisha farida tace ai a ganina
duk daya ne mu ukun. Yanzu kamar baraka
taci gaba dayi masa haka har lokacin da zai
karkato sosai, yana son zaman nata sai ta
dawo tayi masa biyayya sosai, tayi duk abin
da yake so, ta bar abinda baya so, ta nan
zai fara mantawa da nafisa. Ko kuma zai
fara kokonto ko ya rike matarsa ne, ya rabu
da waccan don na tabbata ba zatayi masa
biyayyar da baraka take yi masa ba. Saboda
wadannan dalilan nawa na farko kace babba
ce har ta dade da gama jam'ia. Na biyu
tasan yana sonta don haka zatayi ta jansa a
kasa kasan halin mata. Barr muazzam ya
gyada kai yace lallai kanwata na yadda da
tunaninki, kamar kina zaune a wajen duk
yadda kika fada haka ne. Aisha farida tayi
dariya tace kai kuma a bangarenka kaci
gaba da nuna mata ka sami wata bata
gabanka yanzu. Kada ka bari alakarku ta
rabe, ku cigaba da yawan haduwa ko bayan
ta dawo gidan a matsayin abokinta zaka ga
ta dawo. Kada ka fada mata da wasa kake
da wuri, kayi ta kyautata mata, kanayi mata
duk lallashi da tarairaya. Kayi ta yin duk
abin da kasan tana so, ka kiyaye wanda ba
taso tabbas zataji kai kafi dacewa da
rayuwarta, ko bata zo tace tana sonka ba,
zata nuna alamu. Barr ya gyada kai yayi
murmushi yace gaskiya ne wannan kinyi
hikima, Allah Ya sa mu dace. Bani lambarki
don muci gaba da tattaunawa a waya. Ya
zaro wayarsa daga aljihun, aisha farida tana
karanto masa lambar yana rubutawa har
suka cika. Sannan ya kira lambar ta shiga,
amma wayar tana gida. Aisha farida tace
idan na shiga ciki zanyi saving. Barr
muazzam ya zaro kudi daga aljihu, naira
dubu biyu ne 'yan dubu dubu guda biyu, ya
mika mata nan fa ake tataburzar, don aisha
farida ta tubure ba zata karba ba, shi
kumwa yace sai ta karba. Ko zubarwa zatayi
sai dai ta zubar. Sai da ta ga ya dage sosai
har ransa zai baci sannan ta durkusa ta
karba, tayi masa godiya suka yi sallama ya
tafi, tashiga gida cike da farin ciki kamar
kuwa yasan suna cikin tashin hankalin
rashin kudi, asibiti duk ya cinye musu
kudin. Cefane ma sai harhade harhade ake
yi, a dafa a ci ba dadi don kar a mutu.
Ciwon abida kamar da wasa, abu ya fara
tsananta hankalin kowa ya fara tashi, don
har hussaini yayi waya ya sanarwa da
iyayenta da 'yanuwansu na shagamu.
Babban likitoci yanzu take gani a asibitin
kashi, don ciwon ya wuce kananan likitoci.
Magani take dirka amma fa a banza, ko
alamun canji bata ji a jikinta. Daga nan sai
suka rabu da zuwa asibitin kashin ma, suka
dawo gida aka fara na hausa, wannan yace
sanyin kashi ne, waccan tace mayu ne.
Kowanne magani hussaini yaji sai ya karbo
ya kawo, burinsa matarsa ta sami lafiya.
Abinka da mai ilimi aisha farida bata son
wannan gwafje gwafejen magungunan
gargajiyar ko hussaini ya kawo ya bata, sai
ta boye bata bari tasha. Gara ma na
shafawa a gabobi tana shafa mata kamar na
sanyin kashi da aka karbo musu a wajen
sarkin ruwa na wudil. Maganin sanyi kashi
ne da man shanu ake kwabawa a shafa a
gababin. Sai man tafarnuwa dashi ma akace
ta dinga shafa mata a gabobi shima tana
shafa mata kullum da daddare kafin su
kwanta.
DUK KYAN TAKALMI 2* 11
Babu abinda abida ke iya yi, sai anyi mata
tana kwance kawai. Amma tana magana
radau kuma idan an bata abinci tana ci
sosai. Sai tsananin sanyin da take ji, sai tayi
ta makerketa duk da bargunan da aka lufga
mata, kuma a lokacin zafi ne. Ba asiha
farida da hussaini da 'ya'yan abida ba kadai,
duk wani mahalukin da yake da dison imani
a cuciyarsa hankalinsa sai ya tashi idan yaga
ciwon nan kuma ya tausaya mata. 'Yan
dubiya basa karewa layi layi mata suna
shiga, wasu na fitowa. Sai yanzu 'yan gida
da 'yan unguwa suke zayyano kyawawan
halayen abida. Idan akace yau asabar da
lahadi ce lokacin yaya hussaini yana gida
baije aiki ba, to mazan unguwa da abokan
aikinsa sai suyi ta tururuwar zuwa dubiya.
Kuma yawanci basa zuwa hannunsu haka ,
suna riko kayan dubiya kamar ayaba da
lemo, ko kayan shayi, wasu kuma sai su ba
da dan kudi suce a sayi magani. Aisha
farida ta labe tayi kuka har ta gaji, addua
take Allah Ya tashi kafadun abida uwarta,
ubanta, yayarta kuma kawarta, sannan
aminiyarta mai bata shawara. Aisha farida
ta tari yaya hussaini a bakin kofar dakinsa
ya shirya ya fito zaije aiki. Bayan ta gaishe
shi ta shawarce shi tana son ta kai abida
asibitin malam aminu kano a duba to ko
Allah zai sa a dace.
Hussaini yayi shiru can yace kina ganin aje
asibitin nan alhali na tabbatar ba ciwon
asibiti bane, tunda ga kasusuwan sun
kumvura suna ciwo, amma likitocin kashi
sunce basu ga komai ba. Aisha farida tace
ina ga ai ba bangarensy bane, wata kila
ciwon ba a jikin kashi yake ba, gara in kai ta
tunda can akwai likitoci manya manya zasu
gano ciown. Hussaini yace kinga abin da
yasa nace bana asibiti bane, idan tana bacci
sai tayi ta zabura har sai na rirrike ta cikin
dare. Aisha farida tace haka ne yaya, ai
asibitin ma suna da maganin razana da
zabura. Ya lalubo kudi ya bata yace suje,
Allah Ya sa adace. Aisha farida ta harhada
'yan kudaaden da take adanwa na masu
dubiya, misbahi ma dubu daya ya bata,
haka wani yayansu da yazo daga shagamu
shima dubu daya ya bata, taje ta hado
cefanen dambu ta shirya wa rabin ranta dr
shuraim. Bayan ta yi wanka ta fesa kwalliya
da wata doguwar rigarta bakai mai dankwali
(abaya). Sai ta shirya abida aka kirawo
musu mai adaidaita sahu yazo har kofar
gida. Sai da matan gidan suka taimaka mata
aka rirriko abida aka saka ta ciki domin duk
gabar da aka rike mata ciwo takeyi mata.
Sai ta dau kuka kamar wacce ake balla mata
kashinta don azaba. Aisha farida rike da
kwandon abincinta ta shiga adaidaita sahi
suka tafi. Ta dubi abida ta zubo da hawaye
don tausayi tace wannan dambun ne nayi
wa su dr shuraim in kai musu ko in kyale
su? Abida tayi murmushin karfin hali ta cije
baki saboda tsananin ciwo ta gyada kai tace
ki kai masa.
Mai adaidaita sahu ya kai su har bakin
GOPD kafin su sauka, sai aisha farida ta
shiga ciki da sauri tayi magana da maikatan
suka bata kujerar tura marar lafiya. Lebura
daya ta dauko kujerar ta biyo ta da ita. Nan
ma sai da aka agazawa aisha farida sannan
aka dora abida akan kujerar saboda tsabar
ragargazar da kashinta ke yi har kara zaka ji
yana yi bas! Bas! Idan ta motsa. Aka turata
aka shiga dasu wajen bude file kasancewar
duk ta sanu ba ta bi dandazon layi ba aka
bude musu, nan da nan aka mika musu file
din dakin likita. Nan ne fa za asha jira
sabida likitoci basu karaso ba, don haka
dole a sha jira akan bencina. Aisha farida ta
dubi abida wacce har yanzu take kan wheel
chair tace inje ofishin dr lukman in dawo,
zaki iya zama ke kadai? Abida tayi
murmushi tace kije a tsanake ki gama
abinda kike yi, kada ki damu don kin barni,
ni kadai zan zauna a cikin kabarina. Ni kadai
zan zauna babu mai tayani zama, saini sai
halina. Sai aisha farida ta runtse ido yayin
da kuka ya kcece mata, ta kasa magana
saboda jama'ar dake kallonsu. Cikin sanyin
jiki ta dauki kwandon abincin ta tagi.
Hawaye yake ya tsaya har ta kusa isa
ofishin dr lukman don haka ta sami lungu ta
labe tayi kuka har ya isheta, ta goge
hawayen ta fito. Amma kuwa kallo daya
zakayi mata kasan kuka ta sha, don
idanuwan sunyi luhu luhu.
A sanyaye take tafiya cikin nutsuwa ta
kwankwasa kofar ofishin dr lukman ta
shiga. Bata iske shi ba, sai wasu daliban
likitocu guda biyu ta samu suna zazzaune
suna jiransa. Bayan sun gaisa sai ta tura
kwandon abincin a lungun da saba ajiyewa,
sannan ta tambaye su inda ya tafi. Suka
tabbatar mata yace su jira shi yanzu zai
dawo, ba zai dade ba. Sai ta sami kujera ta
zauna tana zama sai taji an bude kofa,
yayin da gaba daya hankalinsu ya tafi wajen
kofa. Dr lukman ne a gaba, dr shuraim ba
biye dashi. Kowannensu da laptop dinsa a
rataye a kafadarsa. Idanuwan dr shuraim
akan aisha farida ya fara dira, yayin da ya
jima yana kallonta sannan ya dauke idonsa.
Ita kuma murmushi kawai takeyi tana mai
sunkuyar da kai tana jin kunya. Dr lukman
ya dube ta yayi dariya yace 'yar shagamu
daga ina kika diro? Na dauka ai da aka gama
karatu sai kika hada 'yan komatsanki kika
koma shagamu. Tayi dariya tace ina nan
yyayana, kai ka share ni ai ba ka nemana
gashi kuwa na taso takanas na zo in gaishe
ku. Dr lukman yayi dariya yace kin kyauta
'yar shagamu, ni daman nasan kinfi ni kirki,
to bari inje in sallami daliban dana zaunar
tun dazu suna jirana. Ya juya ya dube su
yace to ku taso muje lab din in nuna muku.
Suka bi shi a baya suka fice, sai ita sai gogan
nata dr shuraim kadai aka bari a ofishin.
Yana zaune akan kujera ya bude laptop
dinsa yana dube dube. Ta dubi
zankadediyar fuskarsa sai taji zuciyarta ta
hau dukan uku uku saboda tsananin kyawun
dataga ya kara yi. Ta fara tambayar kanta
da kanta “anya kuwa mutumin nan bai fi
karfina ba? Anya kuwa zan kai labari a
tafiyar nan? Anya kuwa hakata zata cimma
ruwa”? Sai bayanan abida ya fado mata
cewar babu abinda ya gagari Ubangiji,
samun dr shuraim ba wani abin wahala
bane idan har ta rike matakan nan guda
biyar. Ta silmiyo daga kan kujera ta gaishe
shi cikin wata kintsatsiyar murya bata mike
daga durkuson ba har sai da ya amsa mata,
sannan ta koma ta zauna. Tayi shiru kanta a
sunkuye a kasa, sai dai su biyu suna hada
ido in dai ta dago zata kalle shi, sai taga
shima ya dago ido ya dube ta.
Sunyi mintuna biyar cur babu wanda ya
sake magana a cikinsu. Sai taji muryarsa
kamar a mafarki ya ambaci sunanta. Yace
aisha farida, 'yar shagamu, 'yar acaba.
Wanne ne sunanki a cikin su. Sai ta dago ta
dube shi tayi masa lallausan murmushi ta
sunkuyar da kai ta sosa goshi alamar kunya.
Tace sunana aisha farida umar shagamu.
Yayi wani dan siririn murmushi yace kin
amsa sunayen uku daya kika cire, mai yasa?
Ta girgiza kai tace ai na daina hawan acaba
yanzu. Yayi murmushi yaci gaba da
daddanna laptop dinsa. Yace kinsan sunan
wa kike dashi? Sunan mamana ne aisha,
haka farida sunan kanwata ce wacce take
bina. Ya akayi kike amfani da sunaye biyu?
Aisha farida tayi murmushi tace mai suna
aisha ai farida ce duk daya ne. Yace okay
kenan ummata da farida sunansu daya ni
ban ma taba ji ba. Aisha farida tayi
murmushi tace haka ne, ai ba kowa ne ya
sani ba. Ya dube ta da wutisyar ido yace
baki da lafiya ne? Ta dago ido da sauri ta
dube shi cike da mamaki ta girgiza kai tace
lafiyata kalau. Ya girgiza kai yace shikenan,
naga kinyi kama da marar lafiya ne, ko kuka
kikayi ne? Wannan tambayar tasa ta sake
bata matukar mamaki, sai taji kamar a
mafarki. Tayi shiru har zuwa dan lokaci
sannan tace eh. Ya dago ido da sauri ya
dube ta sai ya cika da mamaki yayin da ya
maimaita amsar da ta bashi eh??! Yaci gaba
da duban laptop dinsa ya ma rasa tambayar
da zaiyi mata. Ta sharbe hawaye tace
yayata ce bata da lafiya sosai, har bata iya
tafiya ita na kawo asibiti. Yayi shiru na wani
dan lokaci sannan ya nisa ya ce me yake
damunta? Aisha farida ta zubo da hawaye
mai dumbin yawa tace an kasa gano ciwon.
Dr shuraim ya girgiza kai yace a'a bakuje
inda za'a gano muku ciwon ba dai, har
akwai ciwon da ba a ganewa, ko wanda
bashi da magani? Aisha farida ta matse
hawaye da hannunta ta dagi da jajayen
idanuwanta ta dube shi, ta girgiza kai. Tace
asibitin kashi na dala muka yi ta zuwa suna
bata magani, amma bata jin sauki. Sai ma
gaba yake. Shine yau na kawo tana, tana
GOPD a layi, likitocin ne basu karaso ba. Ya
tambaya cike da kulawa yaya take jin
ciwon? Aisha farida ta kwatanta masa duk
yadda ciwon ya fara har izuwa yanzu. Sai
yayi shiru can yace ciwon yayarki
rheumathoi athritis ne ko systemic lypus
erythramatosis. Aisha farida ta kalle shi
cike da rashin fahimta tace na'am? Ya
girgiza kai yace kada ki damu likitocin da
zasu duba ta yanzu zasu hada da likitan da
ya dace. Allah Ya bata lafiya. Aisha farida
tace amin nagode. Sai ta mike a nutse ta
duka tace zan tafi saboda kada likitocin
suzo a kira mu bata iya tafiya, nice zan
shiga da ita. Ya gyada kai yace okay, Allah
Ya ba da sauki. Ta fice cike da farin ciki,
tana fita ta dafe kirji tana ambaton Allah na
gode ma Ka, Allah Ka sake cika min burina
akan shuraim. Tana tafe tana fara'a tamkar
an biya mata kujerar makka. Sauri take ta
karsa wajen abida ta bata labari, amma da
ta tuna abida babu lafiya sai jikinta yayi
sanyi musamman data je ta iske abida ta
galabaita a inda take zaune, ta gaji da
zaman duk jikinta ciwo yaje. Hawaye kawai
ke fitowa daga idanuwanta. Ita kadai tasan
me takeji, sai dai duk wanda ya dube ta
yasan tana jin jiki saboda gaba daya
gabobinta a kumbure suke. Aisha farida ta
rike ta, ta gyara mata zamanta tana mai
lallashinta tayi hakuri likita yazo. Suna
zaune shiru aisha farida na ta sake
maimaito hirar da suka yi da rabin ranta, sai
tayi murmushin jin dadi ta waiwayo da
sauri ta dubi abida tana shirin ta bata
labarin dr shuraim sai taga mawuyacin halin
data ke ciki, sai taji hawaye ya cika mata
ido.
BABI NA GOMA SHA DAYA Aisha farida tayi
kuka, har ta godewa Allah a wannan rana ta
asabar saboda jikin abida ya matsa, babban
yayanta yaya lurwanu yazo da mota har
kofar gida, yace a bashi ita ya tafi da ita
shagamu ayi maganin hausa. Yaya hussaini
ya zama bashi da zabi kasancewar shima
yana ganin ciown bai yi masa kama da na
asibiti ba, don sunyi ta yin na asibitin babu
alamar jin sauuki, kullum ciow kamar kara
shi ake yi. Aisha farida ta dage wajen yi
musu bayani, sunki su fahimce ta, suna
ganin don ita 'yar boko ce kuma malamar
asibiti shiyasa take son a dauwama da na
asibiti don likitoci ba sa kaunar a hada
maganinsu dana gida. Sunfi karfinta, tana ji
tana gani yaya hussaini da yaya lurwanu
suka ciccibi abida tamkar 'yar jaririya da
kayanta aka saka ta a mota. Yaya lurwanu
ke tukawa, yaya hussaini yana zaune a
gefensa, yayin da ita kuma aka kwantar da
ita a bayan mota. Aisha farida ta mika
hannu ta tagar motar ta rike kumburarrun
yatsun abida a hankali yayin da hawaye ya
surnano daga idanuwansu su duka. Aisha
farida tace Allah Ya baki lafiya. Abida ta
girgiza kai tace ba zan dawo ba farida, ki
kula da 'ya'ya na, kada ki manta abu uku
dana fada miki. Ki zama mai yawan addua,
mai tsananin hakuri mai yawan kama
mutuncinki. Biyun kuwa ba yanzu zan fada
miki ba sai nan gaba idan ban mutu ba.
Yaya hussaini ya juyo da sauri yana kallonsu
ba tare da ya fahimci abin da suke ba, shi
da lurwan suka cika da mamakin jin
kalaman da marar lafiya ta ke furtawa.
Hussaini ya tambayi aisha farida meye
hakan kuma yake nufi? Zance me kuke yi?
Aisha farida ta goge hawaye tace a'a sako
take bani. Yace sakon me kuma naji ana
maganar soyayya? Ki koma gida ki kula da
yara, gasu can suna ta kuka, nima gobe
zandawo na bar miki dari biyar a daki akan
katifa. Idan anyi wa yara hutun makaranta
sai mu dunguma mu tafi shagamu, ni ina jin
ma gara ku kaura can kacokan, ni zan dinga
zuwa ina dawowa, gara mu hakura da
zaman kanon ma. Kirjin aisha farida ya buga
bamm! Don fargabar tana tunanin yaDda
zata rabu da rabin ranta dr shuraim. Ta
zame hannunta a hankali daga hannun
abida, sai abida ta dago ido ta dube ta, tayi
mata murmushi. Tace Allah Ya baki nasara
akan abin da kike nema. Kuka yaci karfin
aisha farida, ta rushe da kuka. Tace Allah ya
tashi kafadunki anti abida.
Nan da nan yaya lurwanu yaja mota ya tafi,
saboda suma sun fara jin hawaye yana zubo
musu don tausayi. Idanuwan yaya hussaini
ya cika fal da kwallah. Aisha farida ta kame
a inda take tsaye tana kallon motar har sai
da suka kure sannan ta juyo gida. A hanya
jama'ar unguwa sai sannu suke yi mata, da
kuma fatan Allah Ya ba wa abida lafiya.
Kowa ya tausaya wa aisha farida ganin
kukan da take sharba, idanuwanta sunyi
jajawur. Ita kanta tana so kukan ya tsaya,
amma yaki saboda tsananin kunar da take ji
a ranta. Ta kama hannun 'ya'yan abida su
hudun dukka maza, faruk, sa'ad, muhd, da
ishak idan taja hannun wannan sai wannan
ya arce da kuka. Da kyar matan gida suka
taya ta da kamo su ana lallashi da alewa da
biskit. Da kyar suka zazzauna a daki suka
daina kukan. Aisha farida ma tazo ta zauna
a gabansu tana kallonsu, ba tare da ta iya
musu magana ba. Abin duniya ya ishe ta, ta
rasa abin da yake yi mata dadi. Ji take
tamkar zuciyarta zata fashe. Tana ambaton
Allah kar ka kashe abida, ina son abida a
rayuwata. Wayarta ce tayi kara, ta mika
hannu a sanyaye ta dauka, ta duba wata
lamba ce bakuwa babu suna, sai dai lambar
ta musamman ce, saboda kusan lambobin
duk iri daya ne. Tayi ta kallon lambar amma
batayi mamakin wanda ke kira ba, domin
'yan ajinsu da dama suna karbar lambarta
su kira ta maza da mata. Saboda bata cikin
hayyacinta , don haka bata son yin magana
har wayar ta katse ba ta amsa ba. Can ta
mike ta fito tsakar gida ta jawo risho ta dora
ruwan zafi a karamar tukunya, ba tare da ta
san abin da zata dafa ba.
Ta dubi babban dan abida faruk tayi
murmushin karfin hali tace yaya me zamu
dafa yau? Maganar ma shi ma dakyar yake
yi, sai ya langwabar da kai yace wake da
shinkafa. Ta dubi sa'ad mai binsa tace kai
fa dan lelena mai zan dafa muku? Shima
yace wake da shinkafa. Sai ishak yace
shinkafa da miya. Mohd yace a'a tuwon
shinkafa da miyar taushe. Aisha farida tayi
dariya tace a'a su yaya sun fiku gaskiya, ku
rage min aiki tunda muna da yaji mai dadi
da daddare sai inyi mana tuwo. Tana zaune
a dokin kofa tana tsice wake sai wayarta ta
dau ruri. Nan da nan yara suka hau tseren
dauko waya, ana dambe dai kamar za a yar
da wayarta samu ta karba. Taba dubawa
taga lambar dazu ce, sai ta tabbatar ko
waye wannan mai kiran wayar tana da
muhimmanci tunda ya sake kira, don haka
nan da nan ta danna. Cikin nutsuwa tayi
sallama, taci gaba da sauraron mai wayar,
mace ko namiji? Muryar namiji taji ya amsa
da wa alaikumul salam. Tayi kasake tana
sauraon abinda zai fada mata, har yanzu
bata gane muryar ba. Amma daga dukkan
alamu ta taba jin kamilalliyar muryar. Ya
tambaya don Allah ina magana da aisha
umar ne? Ta amsa da eh aisha ce. Yayi
gyaran murya kadan yayi murmushi yace
farida kina magana da dr shuraim imarn ne,
daga nan asibitin aminu kano. Tsarki ya
tabbata ga Ubangijin talikai. Kalmar da
aisha farida ta fada kenan a cikin zuciyarta,
yayin da ta sulale ta durkusa gwiwoyi guda
biyu a kasa don mamaki da kidimewa. Ta
rasa kalma daya da zata furta, sai gumi take
jikinta yana bari, ta rasa inda take. Shin
mafarki ne, ko kuma idonta biyu?
Ya ambaci sunata har sau biyu. Farida!
Farida!! Tayi doguwar ajiyar zuciya, ta
lumshe ido ta amsa cike da ladabi, cikin
sassanyar murya na'am. Yace kina mamaki
ne? Kada kiyi mamaki. Na sami lambarki ne
daga wajen dr lukman jiya aiki ya hana in
kira ki, sai yau da yake weekend ne, ina
gida. Ta mike ta shige dakin abida ta turo
kofa ta datse saboda hayaniyar yara, ta
sami lungu ta shige ta takure kai kace sanyi
take ji. Ta gaishe shi cikin nutsuwa. Ya
amsa cike da fara'a ya tambayeta ya mai
jiki? Cikin sanyi jika tace da sauki. Yace yaya
maganin da take sha, tana samun sauki?
Tayi jim kadan tace tana sha dai, amma
ciwon kamar gaba yake tayi. Yace
subhanallah, to yanzu abinda za a yi, ranar
litinin ki kawo ta wajen zan hada ta da
likitan da ya kamata ta gani, wato
rheumatologists. Ba damuwa idan nayi
masa magana zai duba ta ko babu
appointment. Hawaye ya surnano daga
idanuwan farida, ta marairaice murya tace
ai bata nan, anzo daga gida an dauke ta,
wai na hausa zaayi. Babu yadda banyi ba su
kyale ta muci gaba dana asibiti suka ki.......
Bata rufe bakinta ba sai ta rushe da kuka
cikin wata irin sautin murya mai ban
tausayi. Dr shuraim ya zabura yace
subhanallahi, wannan suna so su jawo mata
ciwon koda, daman ciwon yana da alaka da
ciwon koda. Kada su sake su bata sassake
sassake ta sha, don akwai mummunan
hatsari wajen shan jike jike. Kuka kawai
farida ta keyi, ba tare da ta iya magana ba.
Yayi ajiyar zuciya ya ambaci sunata cikin
wata lallausar murya. Yace farida kuka kike
yi? Daman ke haka kike sarkin kuka ce? Na
hadu dake fiye da sau hudu kullum kina
kuka, meya damuwarki? Ta girgiza kai ta
goge hawaye tace babu abinda ban fada
musu ba, babu irin maganar da banyi ba
akan su kyale ta, suka ki. Mijinta ma tun ba
ya yadda yanzu har ya yadda. Yanzu ko nay
waya shagamu nayi bayani kada su bata
maganin hausa ba zasu saurare ni ba. Shine
nake jin tsoro kada su jawo mata ciwon
koda.... Ta sake barke wa da wani kukan
DUK KYAN TAKALMI 2* 12
Ya sake jan doguwar ajiyar zuciya yace kada
ki damu, mu dukka muslmaii ne, mun yadda
da Allah Shi ne mai warkarwa, ba magani
ba. Muyi addua Allah Ya bata lafiya, Allah Ya
tsare duk wani tsautsayi. Ya ya kike da ita
marar lafiyar ne, mamarki ce? Aisha farida
ta marairaice murya tace anti abida yayata
ce, kakanninmu daya, kuma tana auren
yayana da muke uba daya, itace marikiyata
tun ina karama, itace tamkar uwata, ubana,
yayata, kuma aminiyata mai bani shawara
akan duk lamurana. Sai yayi murmushi ya
lumshe ido yace amma kin iya kwatance
yadda mutum zai gamsu. Ko kon taba bata
labarin wani dr lukman da abokinsa dr
shuraim da suke cinye miki dambu da
danwake? Aisha farida ta kwashe da dariya
tace a'a baka bani izinin na sanar mata ba.
Yayi dariya yace nasan kin fada mata. Ta
sake tuntsirewa da dariya tace sai dai yanzu
na fada mata. Yayi dariya yace to Allah Ya
sauwake Ya bata lafiya sai anjima. Aisha
farida tace nagde Allah ya saka maka da
alkhairin, sai anjima. Ya kashe wayar yana
lumshe ido saboda jin dadin muryarta. Har
yanzu aisha farida sankare take a lungu ta
kasa sauke wayar daga jikin kunnenta. Ji
take tamkar mafarki take yi, yayinda
farinciki marar misaltuwa suka cika
zuciyarta, ta cika da mamaki marar adadi,
sai ta tuna da bayanan ABida da tace babu
abin da ya gagari Ubangiji. Idan bawa ya
roke Shi, yana amsa ma sa duk sanda Ya so.
Ta ajiye hannunta a hankali daga jikin
kunnenta ta dafe kirji taji sassanyayiyar
bugun da zuciyarta take yi. Ta daga hannu
sama tayi wa Allah godiya sai ta malale ta
kwanta akan katofa tamkar ruwa.
Ta jawo wayar da sauri ta duba lambar, ta
kayatu ita kanta lambar abar kallo ce, sai ta
sumbaci wayar. Ta dannan lambar ta kira,
bugu daya ta shiga ta fara ruri, sai taga an
kashe. Hankalinta yayi mummunan tashi,
nan danan ta zabura ta tashi zaune ta dafe
kirji, yayin da farin ciki datake yi ya koma
ciki. Ta fada a bayyane innalillahi wainna
ilaihir rajiun! Me ya kaini sake kiransa, gashi
ya katse? Shikenan zai tsane ni. Ta na
zaune ta hada kai da gwiwa tana tunani sai
taji wayarta tayi ruri. Nan da nan ta zabura
ta dauka ta duba, sai taga lambar dr shiraim
ce, tay sauri ta dannan gami da yin sallama
cikin nutsuwa. Ya amsa mata gami da cewa
naga kin kira ko? Ta lumshe ido tace eh
daman zan tambaye ka ne, ranar litinnin
dambun zan kowa muku ko danwake? Ya
girgiza kai tamkar yana gabanta yayi
murmushi yace a'a babu, ba sai kin kawo
mana komai ba, mungode. Ta marairaice
tace haba doctor meyasa, ni ina so na kawo
muku. Yace a'a ki bari sai wani lokaci, idan
muna bukata zamu fada muki. Yanzu na
kira ne naji halin da marar lafiya ke ciki,
don na damu nasan ciwon nan yana da
tsananin zafi, sannan na damu da yadda
naga kinta ta koke koke na kora najji halin
da kuke ciki. Tayi murmushi tace nagoda ka
kyauta, nayi farin ciki da jin kiranka. Ko zan
iya saving din lambarka don mu dinga
gaiswa. Yace ba damuwa, zaki iya. Tayi
godiya, shima yayi mata godiya, suka kashe
waayar. Tayi tsalle akan katifa ta dire don
murna. Ta dubi gabas da yamma, kasa da
sama tana tunanin wanda zata ba wa
wannan kyakyawan labari. Ta tuno abida,
taji yau dama abida na nan ta fada mata
yadda sukayi da dr shuraim. Taji hawaye ya
cika mata ido, ta fada a bayyane. Allah sarki
anti abida, Allah ya baki lafiya. Tana rufe
bakinta faruk ya shigo dakin da gudu ya ce
anty aisha ruwan da kika dora a wuta yana
ta tafasa tun dazu, har ya kusa ya kone. Ta
zabura da gudu ta fito don ita har ta manta
da shi, tabbas yaro yayi gaskiya , ruwa dai
ya gaji da tafasa har ya kusa konewa. Sai da
ta kara wani yayi zafi sannan ta zuba wake
da shinkafa suka dahu. Ta ba wa yara suka
ci, yayin da farin ciki ya kosar da ita, ta kasa
ci, yunwar ma bata ji. Bayan tayi sallahr
azahar sai ta dinga jero nafilfili ba adadi,
duk ta godiya ce ga Allah da ya kawo mata
dr shuraim.
A cikin satin nan haka take yini cike da farin
ciki, saboda ta sami dr shuraim, sai dai
matsala daya ce take addabarta a rayuwa,
idan ta tuno rashin lafiyar abida sai taji
jikinta yayi sanyi lakwas. Koda yaushe sai ta
saka lambar dr shuraim a gaba tayi ta kallo,
sai taji kamar ta kira shi ko ta tura masa
sako, sai kuma ta fasa. Amma ranar juma'a
ta tura masa sakon adduoin juma'a amma
bai bata amsa ba. Ta fara shiga damuwa,
amma sai tayi masa uzuri , watakila bai cika
karanta sakonni ba kasancewar aiki yayi
masa yawa. Ranar litinin da misalin karfe
goma da rabi na safe aisha farida na
kwance akan tabarmarta tayi shiru tana
tunani, rashin lafiyra abida tana damunta
matuka, musamman yanzu da tayi waya
shagamu tayi tayi su ba wa abida waya suyi
magana, aka ce bacci take yi. Sai take ganin
kamar jikin ne yayi tsanani suke boye mata.
Tana so ta tashi ta dora abincin rana, domin
yara sun kusa dawowa daga makaranta,
amma ta kasa tashi saboda damuwar da
tayi mata yawa a zuciya. Wayarta tayi ruru
tayi sauri ta dauka ta duba, sunan yaya
hussaini ta gani, sai tayi matukar mmaamki
da ganin kiransa, don bai dade da fita aiki
ba ya bata kudin cefane. To me yasa ya
kira? Ko mantuwa yayi ne a gidan? Take
tambayar kanta da kanta. Tayi sauri ta
dannan gami dayi masa sallama cike da
tsananin fargaba, tayi shiru tana sauraron
abin da zai fada mata. Yayi gyaran murya
yace yaya kuke? Gidan duk lafiya? Yara basu
dawo daga makaranta ba ko? Sai tace eh
basu dawo ba. Ina gida kowa lafiya kalau.
Yace to madallah, daman na kira ne naji
halin da kuke ciki. Kada ki damu, ki cigaba
da hakuri, kici gaba da kula da yara. Muyi
wa abida addua, naga kin damu duk kin
rame, kina yawan koke koke. Nima na
damu har bana iya aiki yadda ya kamata,
har 'yan ofis dinmu sun gane ina cikin
damuwa. Yanzu na yanke shawara a raina
idan yara suka yi hutu sai nima na dauki
hutu mu tattara mu kaura shagamu. Idan
hutuna ya kare sai na dawo, idan kuma na
samu aikin yi a shagamu ko wata sana'a sai
muyi zamanmu ba sai mun dawo kano ba.
Rashin abida a kano ya zama tamkar tuwo
gaya babu miya. Ni, ke da yara duk bamu
jin dadin rayuwarmu. Ko abinci kika dafa
babu wanda yake iya ci yadda kika kawo
min haka kike zuwa ki dauke, haka na lura
yara ma ba sa iya ci, kema haka. Tulin
abinci ake juyewa almajirai kullum. Aisha
farida ta rushe da kuka, yayin da shima
kukan ya turnuke shi, sai yayi sauri ya katse
waya. Ta kifa kai akan filo tayi ta rusa kuka
tamkar idonta zai fashe. Tana ta addua
Allah Ya yayewa abida wannan ciwon.
Wayarta ce ta sake yin kara. Nan da nan ta
katse kukan ta dauka ta duba sunan barr
muazzam ne. Ta goge hawaye da sauri ta
tashi zaune, sannan ta matsa waya da yin
sallama. Barr muazzam yayi murmushi yace
kanwata kwana biyu, kina nan kuwa? Tayi
murmushi tace ina nan yayana, na sha
kiranka baka amsawa, ko aiki ne yayi maka
yawa? Yace kwarai kuwa, satittikan nan uku
duk bana zama, daga bakwai na safe zuwa
na dare. Alhmdlh abin da ake nema ya
samu. Daman case din dr janan ne an tafka
sharia na shawo kanta, ta bude baki tayi
bayani, ta tonawa su izzuddin asiri, ta kuma
fadi inda za a iya samunsa shi da abokansa.
Aka yiwa 'yan sandan can garin waya don su
kamo shi. Sun kawo mana shi kano, har ya
bayyana a kotu, kuma ya amsa laifinsa.
Yanzu haka kotu ta wanke janan, an
tabbatar ba ta da laifi, an sake ta tana
gidansu shi kuma yana daure. Farin ciki ya
lullube aisha farida, tayi dariya tace
alhmdlh, Allah Mai iko, amma yaya
muazzam na taya ka murna, Allah ya kiyaye
gaba. Yanzu a wanne hali kuke ciki kai da
ita? Yayi murmushi ya lumshe ido yace
komai ya daidaita amma dai ba dukka ba,
kinsan komai sai a hankali. Kanwata na riki
abubuwan nan guda uku, nayi addua, nayi
hakuri matukar hakuri kuma naci riba. Naja
mata aji, na nuna mata yanzu babu zancen
soyayya a tsakanin mu, ina da wacce zan
aura. Na nuna mata bani da wata alaka da
ita face ta aiki. Ta bani hadin kai kawai in
gudanar da aikina yadda ya kamata. Data
tabbatar da haka, sai ta saduda ta ajiye
wannan zaren da take ja na aji ta bude baki
ta amsa duk abubuwan da na tambaye ta,
sannan ta gudanar da duk abin da na
umurce ta tayi a kotu.
Na lura ashe daman tana sona, boyewa
kawai takeyi, ko kuma nace yanzu ta fara
sona da taga halaka. Ni daman bani da
matsala da iyayenta, tun da can suna sona
balle da suka ga irin taimakon da nayi
musu. Ji suke tamkar su dauko ta su kawo
min ita gidana. Ba soyayyar iyayenta nake
nema ba, ina so janan ta soni da kanta ba
sai wani ya tilasta mata ba, ko don wani
dalili ba. Ta soni don Allah, muyi zaman so
da yadda a tsakanin mu, ko babu ran
mahaifanta. Aisha farida tace gaskiya ne
wannan. Allah Ubangiji Ya tabbatar da
alkhairi. Yace amin malamata, menene
mataki na hudu da zan taka, kin san fa duk
abin da kika ce dashi nake amfani, don kin
fini wayo ke kuma anti abida ta fiki wayo.
Ku dora min karatun. Aisha farida ta
kyalkyale da dariya, tace uhmm yayana
kenan, har ka bani dariya wallahi. To mataki
na hudu da abida ta fada min shine tunda
yanzu ta san da kai, ta kuma san abinda ake
ciki, sai ka zama mai yawan kyautata mata,
da haka zata so ka fiye da kowa. Barr
muazzam yayi murmushi yace idan haka ne
to ai na riga na haye mataki na hudu don ni
mai yawan kyautata mata ne, har ita da
kanta ta rubuto min sakon godiya a waya,
ta yaba da hakan. Dazun nan ta rubuto min
wannan sakon. Mene mataki na biyar
kuma, ko baka taka shi ba? Aisha farida
tace eh to inaga nima a mataki na hudun
nake amma abida ta fada min mataki na
biyar din tace ka nuna kama sonta tamkar
kafi kowa sonta a duniya. Kamar kulawa da
duk halin da take ciki, da kuma tattalinta,
tamkar kwai, ka nuna ko kuda ba kaso ya
taba ta. Idan ka yi mata haka ita ma zata so
ka, zatayi kokarin ta mallake ka a
rayuwarta, kaga sai ka aure ta.
Barr muazzam yayi ajiyar zuciya yace kice
min gangaro na kusa samun janan kenan?
Zanje na dorawa baraka wannan karatun.
Aisha farida tace af! Na manta ban
tambaye ka baraka ba, ina take? Wanne hali
take ciki? Yayi dariya yace mutuminki
nurudden dai ya saduda daya ga ta share
shi, sai yake shishige mata, ita kuma tana
watsar dashi. Yanzu haka ya fara neman
shawarata wai yana ga zai rabu da nafisa.
Yace min baraka tace ta amince ta auro
nafisa ya hada su, su biyu. Ita kuma nafisa
tace sai ya saki baraka kafin ta aure shi.
Shine yake cemin da ya saki baraka gara ya
fasa auren, domin baraka ce mace ta gari
da take yi masa biyayya. Aisha farida tace
yawwa ka cewa baraka ta taka mataki na
hudu shine taci gaba da kyautata masa fiye
da na da. Sannan mataki na biyar ta nuna
masa tsantsar soyayya kamar tafi kowa
sonsa a duniya fiye da yadda nafisa ke
sonsa. Brr muazzam yace lallai ke malama
ce, ke kuma yaya naki gogan, me kuke ciki?
Tayi murmushi ta lumshe ido tace alhmdl.
Dr shuraim yasan dani yanzu, ya san
sunana, har ya damu da halin da nake ciki.
Ta kai ta kawo dr shuraim ya nemo lambar
wayata ya kira ni a waya ya gaishe ni ya
tambayi jikin antina abida. Ina ga yanzu zan
taka mataki na hudu, zan cigaba da
kyautata masa sosai har sai ya kaunace ni
yaji sona tamkar ransa zai fita, sai ya saki
jiki dani, don bana tantama ya fara sona.
Sai in taka mataki na biyar shine ina nuna
masa tsantsar kauna nima. Barr muazzam
yace amma abu yayi kyau, Allah ya tabbatar
da alkhairi, Ya zaba mana abin da yafi
alkhairi a rayuwarmu. Har yanzu jikin anti
abidar ne bataji sauki ba? Aisha farida ta
marairaice tace ba za'a ce babu sauki ba,
amma har yanzu ana nan ana fama. Babbar
matsalar ma da 'yan uwanta suka zo suka
dauke ta shine dr shuraim din yake fada
min kada su jifga mata sassake sassake ya
jawo mata ciown koda, domin ciwon yana
da alaka da ciwon koda. Barr ya girgiza kay
tace subhanallah! Allah Ya kiyaye, Allah Ya
bata lafiya. Kiyi kokari ki kira su a waya ki
fada musu abinda likita ya fada, kada su
bata sassake. Yanzu zan turo miki katin
waya don kiyi magana dasu yadda ya
kamata. Aisha faida ta matse hawaye tace
nagode da wannan hidima da kake yi min
ko wani dan uwan nawa na jini ba yayi min
abin da kake yi min.....sai ta rushe da
kuka. Ya girgiza kai yace dadina dake saurin
kuka kamar wata tsohuwa. Ki daina kuka
kinji ko? Duk abin da ya samu bawa
Ubangiji Yana sane, kuma Zai yaye masa.
Sai kinga sakona sai anjima. Aisha farida
tace sai anjima, Allah Ya saka da alkhairi.
Ya kashe waya ba dadewa taji kara a
wayarta, da alama sako ne ya shigo. Tayi
sauri ta duba sai taga brr ne ya turo mata
da kati. Data loda sai taga na 1500 ne. Ta
kira shi har ta katse bai dauka ba, sai ya
kirata daga baya. Tace dama godiya zanyi
maka, naga kati na gode. Yace ba damuwa
ba sai kin yi min godiya ba, don nabaki
wannan dan kati. Ya kashe wayar ta koma
ta kwanta ta dubo lambar dr shuraim tayi ta
kallo tana shawara a ranta ta kira shi ko
kada ta kira shi? Sai ta yanke shwarar ta
kyale don ta lura baya son damu, idan ya
kira da kansa zaifi kamar yadda rannan yaga
dama ya kira da kansa. Sai ta jiye wayar a
gefe zuwa jimawa sai ta sake jawo wayar ta
fara rubuta masa sakon gaisuwa da fatan
alkhairi. Har zata tura sai ta fasa ta goge da
ta tuna ta tura masa na juma'a bai bata
amsa ba, kuma bai kira ba. Ta duba agogo
karfe goma sha daya da rabi 'yan
makaranta karfe goma sha biyu zasu fara
dawowa daga makaranta, gashi bata dora
abinci ba, don haka sai ta mike tsaye zata
je ta dora abincin sai taji wayarta ta dauki
ruri. Ta dawo ta zauna da sauri ta jawo
wayar ta duba, sunan dr lukman ne ya
bayyana, sai farin ciki ya rufe ta, tayi
murmushi tayi sauri ta danna, cike da fara'a
tayi masa sallama gamu da cewa yayana ina
ka shige ne kwana biyu naji ka shiru? Yayi
dariya yace kaji marar kunya. Ni zan neme
ki ko ke zaki kira ki gaishe ni ki samu lada?
Ko baki kirani ba naga flashing ko pls call
me ai zan kira ki. Amma baki neme ni ba.
Ko da yake jan aji ne irin na 'yan mata ko?
Yanzu muke maganarki da abokina dr
shuraim. Aisha farida ta dafe kirji ta lumshe
ido ta tambaya cike da zumudi, me yace?
Dr lukman yace yanzun nan ya fice da yaga
zan kiraki. Daman nace sai na fada miki ko
baya so. Wai ya akayi kike burge abokina
ne, ni tunda nake dashi a asibitin nan
shekara da shekaru ban taba ganin macen
da ya taba maganarta ba balle ya yabe ta,
sai ke? Yace kina burge shi saboda kina da
hankali. Ga ki da kunya, kara, kawaici, ga
hakuri da shiga ta mutunci, uwa uba kin da
aji ba ki cika shishigi da rawar kai irin na
'yan matan yanzu ba. Sannan haka kawai
yake tausayinki musamman da ake ce ke
marainiya ce. Sannan yace kina da matukar
kirki da yaji ashe kace kike daho mana
dambu da danwake. Kinsan da hannunsa ya
dauki lambarki a wayata, yace zai kiraki ya ji
jikin yayarki. Aisha farida tayi ajiyar zuciya
tayi dariya. Tace Allah sarki, haka Allah Ya
ke shirya al'amuran Sa duk yadda yake so.
Dr lukman yace munafukai ne ke dashi,
kunsan abin da yake tsakaninku. Ai idan
tayi tsami zamuji. Shima sai kwana kwana
yake yi min, idan na tambaye shi. Amma
gaskiya na sha mamaki da naga yana yawan
USA Novels BOOK
DUK KYAN TAKALMI 2* 13
Damuwa dake, don ni nasan shi nasan
ra'yainsa, nga yadda yake kushe mata. Ban
taba jin ya yabi wata budurwa a duniya ba
ma balle a cikin asibitin nan, shine na kiraki
naji meye sirrrin? Aisha farida ta kyalkyale
da dariya tace ba wani sirrri wallahi, Allah
ne Ya hada jininmu, nima yana burge ni
sosai. Dr lukman ya gyada kai yace gaskiya
kanwata idan har wannan abu zai tabbata
tsakaninki da shuraim zanfi kowa taya ki
murna, don kinyi dace da mutum na gari,
mai tsananin kirki da tausayi, mai kulawa.
Aisha farida ta dafe kirji ta lumshe ido tace
Allah yayana haka ne? Yace inayi miki fatan
alkhairi, sannan ina taya yayarki da addua ta
samin sauki. Zanje wajen marasa lafiya, sun
taru suna jirana. Ya katse hiran. Aisha
farida ta sulale ta kwanta, tayi shiru tana
sake maimaita kalaman dr lukmann,
mamaki ya rufe ta, tamkar a mafarki ba a
ido biyu abubuwan suke faruwa ba. Anya
kuwa itace, ko dai mafarki ne? Take
tambayar kanta da kanta. Ta sake
gasgatawa babu abin da yafi addua da
hakuri a duniya. Ta dinga yi wa Allah godiya
da Ya nuna mata wannan rana. T dinga
kwararo addua tana rokon Allah ya karawa
dr shuraim sonta, kuma Ya sa ya aure ta. Ta
tuno abida taji daman abida tana nan taji
irin wannan dadadan labari. Sai tayi wa
abida addua Allah Ya bata lafiya. Tana
zaune ta kasa tashi ta dora abinci bata
ankara ba, sai taji muryar 'yan makarnata
sun fara dawowa. Ta ji wani kara
kwarakwacam anyi wurgi da jaka da robar
abinci a bakin kofar dakinta, ta san gajiya ce
da yunwa take addabarsu. Tayi wuf! Ta fito.
Ta shiga llallabasu tana yi musu dubaru
tana koda musu dadin garin kwaki da mai
da yaji, ta aika su suka siyo ta kwada musu
suka ci suna murna. Tace musu haka 'yan
makarantar kwana suke yi, gara ku fara
koyon ci kafin ku tafi sakandire ta kwana.
AISHA SHURAIM HIMMA BA TA GA
RAGO!!!
BABI NA GOMA SHA BIYU Fiye da sati biyu
dr shuraim bai kira aisha farida ba, itama
bata kira shi ba. Don haka sai ta fara shiga
kokonto anya kuwa dr shuraim yana sonta?
Da yana sonta ai ba zai share ta haka ba,
wata kila tausayinta kawai yake yi ba
soyayya ba. Jikinta yayi sanyi, ta fara shiga
damuwa, bata da walwala abubuwa suka
taru suka yi mata yawa. Kowa ya kalle ta sai
ya tambaye ta me yasa ta rame. Taci gaba
da daurewa tana ta addua tana neman agaji
daga Ubangiki Mai kowa, Mai komai. Son dr
shuraim ya zame mata tamkar ruwan
shanta, ya zame mata abincin cinta, kuma
mayafin lullubarta. Duk da daurewa da tayi,
sai da ta kai ta kasa cigaba da daurewa
saboda ji take tamkar zuciyarta zata yi
bindiga ta fashe don kunci. Tsananin son dr
shuraim da kuma rashin abida abokiyar
shawararta, itace mai bata shawara da
kwantar mata da hankali. Tasan da tana
nan da tuni ta fada mata abin da ya kamata
tayi nan gaba. Ranar talata bayan yaya
hussaini ya fita aiki, yara sun tafi
makaranta, sai ita kadai a gida. A kwance
take a daki ba tare da tana jin dadin
kwanciyar ba. Ta yanke shawarar tunda ga
dan kudi a hannunta bari ta harhada tayi
musu danwake, ta kai musu asibiti ko Allah
Zai sa ta dace ya ganta ya tuno da ita don
tana tunanin ya manta da ita ne. Tayi
zumbur ta miike ta shiga shirye shiryen yin
dan wake. Kafin karfe goma na safe ta
gama tsab, ta zubawa yara na su a flask. Ta
shiga tayi wanka ta fito ta dauki fiye da
mintina talatin tana kwalliya.
Wata sabuwar atamfarta ta saka diamond
mai kore da ja, aka dinka mata riga da skirt
matsattsu, ta sami bakin gyale da bakin
takalmi ta saka. Sai dai kash! Ta juya ta
sake juyawa ta dubi jikinta sosai, sai taji ba
zata iya fita a haka ba. Ta san shi kansa dr
shuraim din ma ba burge shi zatayi ba. Don
haka ta ajiye gyalenta ta dauko bakin
hijabinta sabo dal ta siya kwanan nan naira
dubu daya irin wanda ake siyarwa a dinke
mai hannaye kamar riga. Ya shiga da
takalminta mai dan tsini. Ta kullo kofar
dakunan bayan ta debowa yara kayan
makarantar islamita da flaski din abincinsu
ta mika dakin uwani taroke ta arziki idan
yaran sun dawo ta basu abincin su ci su
sauya kaya idan lokacin islamiya yayi su tafi.
Tace itama ba dadewa zatayi ba, zata kai
wa marar lafiya abinci a sibiti. Uwani ta
amsa mata cike da fara'a gami da alkwarin
zata aiwatar da abin da ta umurce ta, ta
hada ta yiwa marar lafiyar adduar samun
sauki. Aisha ta dauki kwandon da ta saka
flask din abinci da plates da cokula, bayan
yaji dakakke a 'yar roba, da 'yar robar
mangyada. Tana tafe cikin nutsuwa har ta
fito daga lokonsu ta sami adaidaita sahu
nan da nan ta haye. Ita kanta tasan tayi
kyau, ko ba a fada mata. Jama' da dama
sun dasa don samari suna ta binta sun kai
su uku sunayi mata magana. Suna sonta
bata kula su ba. Kuyi hakuri an riga an bada
ni. Amsar da take ba su kenan.
Tana isa cikin asibitin malam ta doshi
ofishin dr lukman, sai taji kirjin ta ya fara
dukan uku uku, don fargabar abinda zata
tarar daga dr shuraim. Tana hawa kan
barandar ofishin sai ta hango dr shuraim da
wasu dattijai maza su uku sun tunkaro ta,
ma'an suna fitowa ita kuma tana shiga. Sai
taji wani mummunan faduwar gaba. Ya
tsura mata ido sosai yana kallonta, har sai
ta taji kunya ta sunkuyar da idanuwanta
kasa. Suka wuce ita ma ta wuce, ta juyo a
hankali zata dube shi, shima ya juyo sai
gaba dayansu suka gaggauta juyawa da
sauri. Ta shiga fargaba saboda ta dimauce,
bata gaishe shi ba, kuma ya kamata ta
gaishe shi din. Don haka ne ma yake ta
kallonta har da waiwaye. Abin da zuciyarta
ke zayyano mata kenan. Jikinta a sanyaye
ta shiga ofishin dr lukman, taci sa'a yana
nan shi da abokinsa dr mohd. Bayan ta
gaishe su, sai ta ajiye kwandon abinci a
gaban dr lukman. Tace ga danwake nayi
muku. Yayi farin ciki, yayi godiya sosai. Dr
mohd ta dubi dr lukman yace lukman zaka
bani 'yar kanwar nan taka kuwa? Ina sonta
tun ranar da na fara ganinta. Kirjin aisha
farida ne ya burededen dukan uku uku har
ta fara dana sanin zuwanta nan a yau. Ana
wata sai ga wata, yanzu idan dr shuraim
yaji ko da wasa dr mohd ya furta yana
sonta, ai bar masa zaiyi ba zai kara nuna
alamar so ba. Ta tsunduma cikin wannan
dogon tunani, sai da dr lukman ya ambaci
sunanta ta dawo da hankalinta gare su.
Yace kanwata kinji wai in bashi ke? Tayi
murmushin karfin hali tayi shiru. Dr mohd
yaci gaba da kallonta, kallo mai cike da so
da kauna. Ta sunkuyar da kanta kasa, tana
mai tsananin jin kunya hade da bacin rai. Dr
lukman yayi dariya ya daki kafadarsa yace
kai da kake min tsiya wai ba kanwata bace,
bamuyi kama ba, sai inga wanda zai baka
'yar. Dr mohd yayi dariya yace yi hakuri
don Allah, yaya na daina. Yana rufe bakinsa
sai dr shuraim ya shigo. Nan da na hankalin
aisha farida ya sake tashi. Ta fara addua
kada Allah Ya sa acigaba da zancen soyayyar
nan. Tayi sauri ta sulalo daga kan kujera ta
gaishe shi. Ya amsa cike da far'a, sannan
yaci gaba da kallonta. Can yace lukman
dama kanwarka ce na hadu da ita a baranda
nake mata kallon sani, amma ban gane ta
ba. Naga ta sauya. Aisha farida ta dube shi
a kunyace ta sunkuyar da kai. Dr lukman
yace me ka ga tayi? Ta sake yin kyau ko? Ai
an gama makaranta ana hutawa a gida. Dr
mohd yace kai fa lukman yaya ne ka bari in
fadi da bakina mana, sai kace tayi kyau, kai
yayan kwabo ne ko? Su biyu suka tuntsire
da dariya yayin da dr shuraim ya tsaya cak!
Ya dubi dr mohd ya juya ya dubi dr lukman
ya juyo ya dubi aisha farida nan da nan taji
zuciyarta na dukan uku uku. Daga dukkan
alamu dr lukman ma baiji dadi da dr mohd
ya fadi haka a gaban dr shuraim ba, domin
yana kyautata zaton dr shuraim yana son
aisha farida, furatwa ne kawai baiyi ba.
Dr shuraim ya gaggauta daukar ajiyarsa a
loka ya fice da sauri. Aisha farida ta kame a
zaune, yayin da numfashinta yake kokarin
daukewa gaba daya, babu wanda yake
magana a tsakanin su biyun, dr mohd ne
kadai yake surutunsa. Haushi da tsanarsa
suka bayyana a fuskar aisha farida. Ta
dauke shi a matsayin tamkar mutumin da
ya dauko wuka mai kaifi ya dubi cikinta ya
burma mata, ma'ana ya kashe ta. Domin ya
rugurguza mata walwalar rayuwarta duniya
da lahira. Dr mohd yayi ajiyar zuciya, ya
dubi aisha farida yace bani lambar wayarki
aisha umar. Ta dago da sauri ta dube shi,
duba na takaici ba tare da ta iya furta
kalma gida daya ba. Dr lukman yayi sauri
yace ita zaka tambaya ko ni yayanta zaka
tambaya na ba izini ka karba? Ita ma na
umurce ta ta baka? Tayi murmushin karfin
hali ta mike tsaye a sanyaye ta yi musu
sallama zata tafi. Dr mohd ya nemi ta kara
zama suyi hira, tace gidan babu kowa sai ita
kadai, don haka take so ta koma da wuri.
Dr lukman ya ciro naira dubu daya ya mika
mata, yace tayi kudin mota. Tace ya bari ba
zata karba ba, tana kudin motarta. Dr
mohd ya zabura yace ka bari kawai zan
bata ko kuma ma marasa lafiyan da suke
jirana suyi hakuri sai na kai matata gida
sannan zandawo. Dr lukman yace wannan
kyautata ce ta daban a matsayin na
yayanta, kai da ita kuma daban. Kuma
wallahi sai kin karba kinji ma na rantse.
Aisha farida ta saka hannu biyu ta karba
gami da yin godiya, cikin sassanyiyar
murya. Dr mohd yace Allah sarki, kaji
yarinya mai ladabi, gaskiya nifa da gaske
nake. Lukman zanje in kai ta gida in dawo
muyi maganar gaskiya ba wasa nake ba.
Tayi wuf! Ta fice da sauri don bata so ya
biyo ta, shima ya fita da sauri ya biyo
bayanta ta, ya umurce ta ta jira shi su tafi
tare. Wani babban tashin hankalin kuma sai
ya tura kofar ofishin dr shuraim ya leka sai
ga dr shuraim a zaune a kan kujerarsa yana
danna laptop. Ya dagi da kyawawan
idanuwansa ya dubi dr moh sannan ya sake
daga ido ya hango aisha farida a gefensa.
Sai ya sunkuyar da kai, yaci gaba da danne
dannensa. Amma daga kallon fuskarsa
kasan zuciyarsa a bace take. Dr mohd yace
abokina zo muyi rakiya, wancan dan iskan
lukman yaki yace shi a dole babban yaya
ne. Ya girgiza kai yace nima yaya ne, ba
zanje ba. Kaje sai ka dawo. Aisha farida tayi
wuf! Ta bar wajen, tafiya take ba tare da
tasan inda take jefa kafarta ba. Kawai wani
lungu ta samu ta dinga kutswa cikin asibitin
maimakon ta nufi bakin gate sai tayi ciki.
Kafin dr mohd ya waiwayo sai yaga wayam!
Bata nan. Ya fito da sauri ya dudduba
hanyar gate ba ta nan. Ya duba kudu da
arewa, babu ita babu dalilinta. Sai ya cika
da mamaki, ya shiga kokonto da wasi wasi
don haka ya koma ciki da sauri don ya
shaidawa yaya lukman. Dr lukman yayi
dariya yace kunyarka takeji, kuma tana da
tarbiya bata so a ganta da namiji , ni nasan
halin kanwata. Dr mohd ya takura sai an
kitay a waya yaji inda take. Aisha farida ta
isa ofishin matron maryam ta iske bata nan,
sai sababbin dalibai da aka turo daga
makarantarsu. Yawancinsu ma duk sun
santa. Bayan sun gaisa ta tambaye su
matron sai suka ce ta fita. Aisha ta jawo
kujera ta zauna tana huci, nan da na suka
hau tambayarta bata da lafiya ne? Tace
gajiya ce kawai, tana so ta huta sannan ta
tafi. Bata rufe bakinta ba sai wayarta ta dau
kara. Ta bude 'yar karamar jakar da ta saka
kudin motarta da wayar ta zaro wayar,
sunan dr lukman ne ya bayyana. Sai taki
amsawa har ta katse. Tana katsewa ya sake
kira, don haka ta tabbatar kiran yana da
amfani, sai ta amsa. Tambayar da ya fara
mata itace kina ina? Tayi inda inda sannan
tace ina cikin adaidaita sahu hanyar
komawa gida. Yace toh shikenan. Allah Ya
kaiki gida lafiya. Ya kashe wayar tana jiyo
muryar dr mohd amma bata gane abin da
yake cewa ba. Anan zan dakata mu hadu a
DUK KYAN TAKALMI 3 kuji yadda zata
kasance. Daga 'yar uwarku JUT.
See Translation
January 10, 2015 at 7:26pm · Public
35
DUK KYAN TAKALMI 3* 1
Tayi ajiyar zuciya mai karfi.sannan ta
kwantar da kanta akan teburin da yake
gabanta don ta rasa abun da yake yimata
dadi innalillahi wa inna ilahi raji`un,ta ke ta
ambato,sai da ta dauki tsawon mintina 20
bata iya dago waba,ta mike tsaye da kyar
yayin da idanuwanta suka yi ja,alhalin kuma
ita ba kuka takeyi ba daliban dai har yanxu
tambayarta sukeyi,anya kuwa lafia? tace
lafia kalau kawai dai gajiya ce. Tayi musu
sallama tabar musu sako su gaishe da
metron maryam sannan ta tafi,ta cikin
lunguna ta kurkurda ta fito gate,tana fitowa
taci sa`a ta sami A dai- daita sahu babu
kowa a ciki,don haka tayi wuf ta shigo
batare da ta fada masa inda zai kai ta ba
balle suyi cinikin kudin da zai karba,tana
shiga ta zauna tana daga kanta, sukayi ido
hudu da dr shuraim cikin tsaleliyar motarsa
discussion continues,shi ma kallonta yake yi
alokacin da yake kokarin tsallakawa titi,ta
sunkuyar da kanta da sauri,yayin da
shikuma ya tsaya cak yana kallonta,daga
dukkan alamu yana mamaki da ya ganta
yanxu,mai adaidaita sahu yaja ya tafi yayin
da aisha farida ta rike kai,saboda nauyin da
taji kan yanayi mata sai da mai adaidaita
sahu yayi da gaske sannan ta bashi amsa, ta
fada masa inda zai kaita tana shiga gida
sallan azahar kawai tayi ta shiga lungun ta
kwanta ba tare da ta san a duniyar da take
ba,taji dadi da ganin yara a zaune a dakin
uwani,sunci abinci suna hutawa,don haka
tace suyi zamansu a nan zatayi aiki idan
lokacin makarantar islamiyya yayi su
tafi,saboda kawai bata son damu da
magana cikin wanan hali da ta riski kanta
Allah sarki soyayya ruwan zuma tayini tana
duban numbr dr shuraim,sai taga kamar shi
take gani,koda yaushe kunnenta da
idanuwanta ta suna yi mata gizau,taga
kaman shine yake kiranta da zaran an
kirata,idan taga bashi bane sai ranta ya baci
tana so takirashi amma tana tsoro kada ya
wulakantata kuma bata ma san abun da
zata ce masa ba idan takira din. washegari
ta tashi acikin bacin rai kaman yanda ta yini
a jiya ta yankewa kanta shawarar gara ta
hada ta kaura shagamu kawai tayi
rayuwarta acan ,idan sakamakonsu na exm
ya fito ta karbi takardunta taje can ta nemi
aiki a asibitin garinsu shi yafi mata
sauki,saboda son dr ya zamar mata annoba
musamman idan tana ganinsa. wayarta tayi
kara alokacin da take wanke-wanke ta arto
da gudu ta dauka tana addu`a Allah ya sa
dr ne,sai taga wata bakuwar no ce,ta yi
sauri ta danna,muryar wani kamillan
mutum taji ya ambaci sunanta,aisha umar
ce ko? ta amsa eh,nice" yace dr mohd ke
magana!
Ta sulale ta zauna,yayin da takaici ya
lullube xuciyarta,ta gaishehsi taja bakinta
tayi shiru tana sauraronsa,yace sai kika
gudu kuma ko tsorona kike ji? ta kame a
zaune,domin tana jiyo muryar dr lukman da
dr shuraim a gefensa,hankalinta ya tashi
har abada sai hawaye ya surnano daga
idanuwanta bata iya bashi amsa ba,yace ki
kwatanta min gidanku zan zo,tayi shiru can
tace ai zan shigo asibitin gobe zan karbi
kwanukan da na kawo muku,yace kash
gobe ai bana gari sai dai ki zo jibi tana jiyo
muryar dr lukman yana cewa to ka fasa
tafiyar mana idan da gaske kake yin son? dr
shuraim kuwa bai sake furta komai ba yana
gefe guda yana kallonsu,tayi sauri ta katse
wayar ta rushe da kuka,tayi sauri takira
wayar shagamu gidansu abida,lambar
mamarta,bugu daya ta dauka ta gaisheta,ta
shaida mata aisha farida ce daga
kano,kasancewarta tsohuwa ba iya karanta
suna tayi ba. Goggo tace ai na gane
muryarki yar baba,kamar yadda wasu suke
kiranta da haka,ina anti abida,ya jikin nata?
goggo ta amsa,mungode Allah,amma dai
jikin abida to sai yadda Allah yayi,gata nan
yanzun nan tace a tashe ta zaune ta gaji da
kwanciya,aisha farida ta fashe da
kuka,goggo ma ta fashe da kuka,aisha tace
a bawa abida wayar,goggo tace sai dai in
kara mata wayan a kunne,bata iya daga
hannunta, bazata iya rike wayar ba. Muryar
abida ce ke karkawa tace farida maiyasa
kike kuka? zan samu lafiya da izinin
Ubangiji. Aisha ta matse hawaye tace, anti
abida so nake ayi wa yara hutu na taho
shagamu na dinga ganinki bana jin dadin
gidan nan
Bana jin dadin kanon, duniyar ma gaba daya
ta isheni,Allah ya baki lafia. Hawaye ya
surnano da idon abida, tace bana so ki
kaura shagamu,har sai kin cika burinki akan
dr, Farida ta fashe da kuka tace anti bana
jin zan cika wannan burin nawa,domin
yanxu wani abokinsa ne yake sona,mai suna
dr mohd kuma har dr shuraim din ya
sani,nasan zai hakura ya bar wa dr mohd ni
kuma bana son dr mohd din,shuraim nake
so. Yanxu haka suna tare,kuma agaban dr
din yayi min waya,abida ta cije baki saboda
tsananin ciwon da yake addabarta,tace
kada ki damu duk irin abunda zai faru ki
zubawa sarauta Allah ido,ki gode masa kici
gaba da addu`a,kanwata duk irin wannan
wata hikimar Allah ce wacce ba ki sani ba,ki
ci gaba da nemawa zuciyarki abun da take
so har sai kin cika burinki,ina yimiki fatan
alheri. Farida ta katse wayar ta rusa kuka
ita kadai a daki ta fada a bayyane,wayyoh
abidata wayyoh shuraim,inna lillahi wa inna
ilaihi raji`un, Allah ka taimake ni ka cikamin
burina,ka karbi adduoina guda biyu,kaba wa
abida lafia ka bani dr. Tayi kuka tayi addua
har muryarta ta ddisashe,yau ma dai yara
sun sha wahala har karfe 2 basu ci abincin
rana ba,don bata iya dorawa da wuri ba.
kuyi hakuri ku yafemun yara ni kadai nasan
halin da nake ciki inji farida lokacin d take
cuu-cukun xuba musu abinci bayan da ta
tabbatar sun galabaita. Faruk ya dubeta
yace anti aisha meyasa kullun kike kuka? ko
mamarmu ta mutu ne? Hawaye ya surnano
da idonta tayi saurin ta dukar da kanta
kkasa don kada ya gane kukan zata sakeyi
ta girgiza kai tace mamanku bata mutuba ta
samu sauki,na muku alkawari ranan asabar
zansaka kati a wayata inkiramuku ita daya
bayan daya kuyi magana da ita zakuji
muryarta radau taji sauki sosai. sai taga sun
hada ido sunhadu sunyi daria suka hau
murna bayan tabasu abinci sunaci a tsakar
gida tashiga daki tarufe tashige lungu
tadinga kuka tana addua ya Allah kana sane
da halin danake ciki kasa abida ta warke
nasani baka barin wani dan wani yaji dadi
Allah ka duba kananan yaranta har hudu ka
tashi kafadunta,suna tanbayata mamarsu
yaya zance musu idan tarasu Allah kada
kabarsu sutashi a marayu kaman ni,Allah
kabani mijin danake so dr, insan dadin aure
dan idan na auri wani bashiba farin cikina
ragaggenai. Ya Allah kafini sanin abunda
yafi Alkhairi a rayuwata Allah nagode maka
kaciga da taimakona da kai kade na dogara,
adduoin da Aisha farida keta zubawa kenan
a wannan yinin,bata iya fitowo tayi hira da
yan gidan ba,har sai da ta tabbatar
magruba ta karato yaya husaini ya kusa
dawowa sannan ta fito,ta fara cukuncukun
dora abincin dare. Washegari jummaa ta
shirya da wuri ta fita,karfe tara a cikin
asibiti tayi mata,kasancewar juma`a ce don
kada a rufe hanya,ta isa ofishin dr.lukman
sai taji a kulle wata kila bai iso ba,tunda bai
isoba tasan dr shuraim bai karaso ba.
Amma dai taja jikinta ofishin ta tsaya,ta
karanta sunansa ta sake karantawa sai taji
sanyi a ranta,ko sunansa ta gani a rubuce
dadi takeji ,ta lumshe ido,tasa hannu a
hankali ta rike hannun kofar,sai taji tamkar
ta shafi hannunsa ta san tabbas ya taba da
hannunsa,ta murda da wasa don tana da
tabbacin a kulle take,bai karasoba kwatsam
sai taga kofa a bude har ma ta wangale sai
ga dr radau a zaune akan kujera suna hada
ido taji tamkar ta zura da gudu don fargaba,
tayi wuki-wuki da ido tana kallonsa cike da
mamaki yayin da shima haka har tsawon
lokaci suna kallon juna. Shigo mana inji shi,
ta fara tafiya a hankali kanta a sunkuye a
kasa cike da kunya,sai yanxu ta dubi kayan
da ta sako a jikinta,birkideden hijabi ne har
kasa yana jan kasa,shi ma mai hannu ne
kaman riga ake sakashi,maroon color sai ta
saka takalmi shima kalar hijabin mai dan
tsini,yayin da fuskarta bayan hoda bata kara
komai ba,babu kwalli balle jagira,don bata
saka ran zata hadu da shi ba.niyyarta tazo
ta kwashi kwanunkanta tayi wa asibitin
sallama daman tasan dr mohd baya nan yau
shi yasa ta garzayo dan bata son su hadu.
Sai kallonta yake tundaga sama har
kasa,har saida ta karaso gabansa ta durkusa
har kasa ta gaishe shi yace tashi tashi ki
hau kujera ki zauna, ta tashi a hankali ta
zauna kan kujerar har yanxu kanta a
sunkuye yake a kasa,har zuwa lokaci mai
tsawo batayi maganaba shima haka danne
dannensa kawai yakeyi a laptop.
Can ta dago ta dube shi sai taga ya dago da
sauri ya dube ta,tayi murmushi tace yaya
lukman be karaso bane?? naje ofc dinshi a
kulle,ya gyada kai kawai bai yi magana ba
sai taji hankalinta ya tashi,ta tabbatar yana
jin haushinta ta yunkura ta mike tace,bari
in jirashi a waje ya girgiza kai ba tare da ya
kalleta ba,yace ba damuwa ki zauna a nan
har yazo,ta koma ta zauna yayin da taji dan
sanyi a ranta,taci gaba da sunkayar da kai,
idan ya dago ya dubeta sau daya, sai yaci
gaba da kallon laptop dinsa. Kamar daga
sama taji ya ambaci sunan ta,ta dago da
luhu-luhun idonta ta dubeshi ta amsa cikin
nutsuwa. Ya tsaya cak da abunda yakeyi
yace lafiyarki kalau,ko akwai abunda yake
damunki ne? tayi murmushin karfin hali mai
kayatarwa,tace lafiata kalau dr. Yace bawan
da yataba gayamiki kin rame kwanan nan?
ta sake murmushi ba tare da tasan amsan
da zata bashi ba, yace don wa kike dafa
abincin nan da kike kawowa? Shi kansa
yasan ta firgita da jin wannan
tambaya,domin ta dago da sauri ta dubeshi
ta tabbatar yau wulakancinsa yau ya motso
kanta ,taji hankalinta ya tashi,sai kwalla
tacika mata ido,ya sake maimaita
tambayarsa, hakika amsa yake bukata kuma
ya xuba mata ido,ta runtse ido tayi shiru.
Can ta dago ta dubeshi tace saboda kai da
dr lukman nake kawowa. Yayi daria yace
harda ni ba saboda lukman kawai ba? to
mun gode kuma munji dadin abincki sai dai
ina rokonki ki daina wahala da mu,kada ki
kara kawowa. Kallo na rashin fahimta take
yimasa,har sai da ya gane haka. Yayi ajiyar
xucia yace bana so naga mace na
wahala,macen ma mai suna mai daraja irin
naki AISHA FARIDA. Sai taji dadi ya rufeta
tasa hannu ta sosa goshinta saboda
kunya,tayi murmushi tace dr ba damuwa ni
ba ya damuna,in har zaku ci,ya girgiza kai
yace kiji maganata,ki daina kawowa in
muna so zamuyi miki waya ki kwatanta
mana gidan mu zo mu dauka,ba sai kinxo
ba kinji ko? nan da nan ta amsa da to,in
sha Allah zanyi amfani da abunda kafada.
Yace yawwa na gode yaya mai jiki,ta
langwaba da kai,tace tana can shagamu
tana fama har yanxu bana jin tana samun
sauki, sai ta fara kwalla. Ya tsaya cak ya
daina abinda yake,yana dubanta yace ban
taba ganin randa zan ganki ba kya kuka
ba,farida waya gaya miki ke kadai kike da
matsala a duniya,mu me yasa bama kuka
kullum? Waye ya shagwabaki kike yawan
kuka? tasa hannu ta matse hawaye,tayi dan
murmushi tace ba kowa....yace kidena
kuka ni kukan yaro ma bana so balle babba
kuma mace,baki san duk sanda naga
hawaye a idonki ba ,idan kika tafi damuna
yake a xucia ba? to ni haka nake a
rayuwata,matsalar wani matsala tace,ki
fadamun ko akwai abinda yake damunki a
rai,sai in baki shawara nima abokin lukman
ne.
Tayi dariya ta girgiza kai tace babu komai
idan ma akwai ina fadawa Allah ya kawo
mun sauki. Yace wannan yayi kyau ko meye
damuwarki ki fadawa Allah. Kuka da saka
damuwa a rai matsala zaki jawowa lfyrki,mu
likitoci bama son haka. Musamman
bangaren yayanki lukman kwakwalwa suna
hana mu2m yawan 2nani da damuwa. Ki
kiyaye kina karamarki zaki cuci rayuwarki a
banza. Ta gyada kai tace naji likita ngd.
Yace shigarki tayi min kyau ta burgeni. Sai
taji tmkr ba shi yake magana ba. Ta kalle
shi ya kalleta, shima ya gane ta shiga
mamaki. Sai yai murmushiyace,kina burge
ni fa, i lyk ur style. Dgwar ajiyar zuciya yaji
taja, har yanzu kallonsa takeyi kawai. Yace
zaki jira ni in tashi daga aiki na mayar dake
gida? Wannan karon ma sake zaro ido tayi
ta dube shi cike da mamaki. Yayi dry yace,
ba kya bani amsa fa, me yasa kike
mamamki ne? Tayi mrmshin krfn hali tace,
to. Yace ki jirani a nan ofishin bayan sallar
juma'a sai na dauke ki a motata mu
fita,idan na kaiki gidana kika gani muka dan
huta bayan magruba sai muje in mayar
dake gidanku nima naga gdnku. Ko ban zo
ba ke saiki zo gidana 2nda ni kadai ne a
gdn kema kuma antinki bata nan, babu
wanda zaisa miki ido. Yau dr. Lk ba zai xo
ba,tare suka yi tafiya da dr. Mohd saini
kadai kinga sai kiyi zamanki a ofishina ki jira
har bayan sallar juma'a ko? Kuma dk
abunda zai faru a tsakaninmu bana si ki bari
wani ya sani har lk sirri ne. Ta zazzare ido
tana dubansa,taga shi ko a jikinsa
maganarsa yakeyi kansa a tsaye. Sai taji a
ranta ta tsani kanta, kuma t tsani
rayuwarta. Ashe dan iska ne bata sani
ba,har take yabonsa? Sai taji gaba daya ya
sure mata taji daman bata sanshi ba,bata
taba ganinsa a raywrta ba. Ya dubeta duba
na kurilla yayi mrmushi ya daga mata gira
yace,baby kin amince dani? Zan kawo miki
canji a rayuwa. Soyayya da jindadi ga dukiya
mai yawa. Dn Allah ya dora min sonki a lkc
guda kece baki sani ba,kina da kyau,gaki da
diri,kinfi sauran mata. Taji tmkr ya caka
mata wuka a kahin zuciya ta fada a
zuciyarta, innalillahi wa'inna ilaihir rahi'un!
Dr shuraim me yasa halinka ya zama haka?
Wayyo Allah na dama ace yadda kake da
kyau kanada kyawun halyya a boye kmr
yadda a zahiri kake kamilalle mai rukon
addini
Ya katse 2naninta yace, bari inje clinic ona
da patient zan bar miki ofishin ki bude firij
akwai fruits da juices kisha wanda kike so.
Ya dauki laptop dinsa ya fice yayin da ta
bishi da kallo harya fita. Ta dafe kirji ta
zabura ta mike tsaye sai taji jiri ya kwasheta
ta koma ta zauna ta rushe da kuka. Ta fada
a bayyane, Allah ka fini sanin dalilin daya sa
na tsinci kaina a cikin irin wannan rayuwa.
Ina abida? Abida ko zo kiji halin da nake
ciki. Tayi kuka ta gaji,ta dubi ko ina a cikin
ofishin babu abnda take hangowa a cikin
lokokinsa daga manyan littafan likitoci dai
kur'anai izifi sittin-sittin. Ta daga ido ta
dubi bango taga gaba daya firem ne a
rubuce da sunan Allah da manzonsa. Ta
dubi kasa sallayar sallarsa a lungu da carbi
dan yayi sallah yake ja. Sai taji ranta ya
sake baci,ta fada a ranta. Dr shuraim ya
zama babban munafuki a addini a fili yana
nunawa shina Allah ne,fasikancu ne kuma a
boye. To ashe duk 'yan matan nan da yake
wulakantawa dk sai daya gama lalata su
tukunnan sannan ya koresu? Ka cuci kanka,
ka cuci kyakkyawar hallitarka. Allah ka yaye
min son fasikin mu2m a rayuwata. Ta sake
rushewa da kuka,tayi zumbur ta mike ta
bude kofar ta leko taga bayanan, sai ta fito
ta jawo kfr ta rufo. Tana tafe tana waiwaye
waiwaye. Abin mamaki sai taga ofishin dr lk
a bude har wani dalibi ya kwankwasa ya
tura kfr ya shiga. Ta sake tabbatarwa dr S
makaryaci ne,makiri,azzalumi,yayi niyyar
cutarta. Tayi kmr ta shiga ofishin ta dibi
kwanukanta, in yaso tayi sallama dasu har
abada. Sbd abokin fasiki shima in ba a yi
sa'a ba fasikin ne. Sai taji ranta kawai har
kwanukan bata so,suje su rike. Tayi wuf! Ta
fice da sauri tfy take ko waiwaye bata yi
burinta kawai ta ganta a cikin adaidaita
sahu.
UK KYAN TAKALMI 3* 2
Tazo fita ta get kenan sai taji wayarta ta
dau
ruri tayi sauri ta dauko 'yar jakarta,ta duba
sai taga sunan dr. Lk ta danna a sanyaye sai
yace, Aisha Farida kina inane? Ta dafe kirji
tayi shiru can tace ina gida. Yace ashe bake
bace wata na gani a cikin asibiti kmr ke sak!
Ta gifta. Sai ya katse wayar, ta tsaya cak!
Ta
dubi hanyr ofishinsa ta dubi hnyr waje.
Yayin data dinga shawarwarin inda zataje.
Taji kmr ta koma ofishinsa ta shaida masa
abun da abokinsa yayi mata,sai taga meye
amfanin shaida masa din? Watakila ma
bakinsu 1. Dn haka tayi tfyrta. Tana cikin a
dai daita sahu tana sharbar hawaye ta
sauka
a unguwarsu ta gangara gida, dk wanda ya
hadu da ita a hnya saiya tmbyeta farida lfy?
Tace bani da lfy. Sbd sunga kuka takeyi
haikan, kuma tfy take kmr zata fadi. Ta
kunshe fuska a cikin hijab, ta shiga gida dn
bata son mutanen gida su gane tana kuka.
Ta bude daki ta shiga sai ta yaye hijabin ta
urgar ta dora kannu aka ta rusa kuka mai
sauti. Tayi sauri tasa hannu ta kunshe
bakinta, dn kada 'yan gidan su jiyota. Ta
drkushe kasa tana fadin, Allah ngd maka
daka bayyana min waye dr.S 2nda wuri.
Allah ka yaye min sonsa, ka masanya min
da wanda yafi shi alkhairi. Ashe abida tayi
gsky data ce in rike addu'a, Allah shi yasan
dai-dai idan bawa yana son abu yaga Allah
bai bashi ba. Bai sani ba ko abun ba
alkhairi
bane a gareshi. Na rasa Dr S,na rasa ka har
abda, na hakura da kai. Bana sonka, bana
marmarin in sake haduwa dakai a
rayuwata. Ta jawo wayarta ta nemo sunan
goggon mahaifiyar abida,dk da tasan halin
da abida ke ciki,amma babu yadda zatayi
ne, dole ita din zata fadawa don in bata
fada ba zuciyarta zata iya fashewa a yau.
Ina anti abida? AF ta tmbyi goggo ko
gaisuwa babu. Lfy? Ta tmbya cike da
damuwa. Jikinta zan tmbya,kuma ina so a
bata waya mu gaisa. Inji AF. Goggo tace
bana so kuna maganr nan, dn kuka naga
tanayi, ban san me kike fada mata ba.
Marar lfy baya son damuwa fa farida. Ta
jiyo muryar abida tana cewa, googgo ki
kawo min wayar, bakiu san abn da zata
fada min ba. Farida bata da kowa a duniya
saini. Idan da sauran nmfashi na a duniya
ban mu2 ba,ai zan saurari matsalolinta.
Goggo taje ta karawa abida waya a kunne.
Abida ta ambaci sunanta sai AF ta rushe da
kuka. Tace anti ashe Dr.S dan iska ne? Wai
zai kaini gdnsa mu huta. Abida tayi dariya
tace,kada ki yanke hukunci,kibi a hnkl. Ba
gsky bane, kici gaba da addu'a kanwata.
Takaici ya sake bullowa daga cikinzuciyar
AF
da taji amsar abida, saita katse wayar.
Karar shigowar sako ne ya shigo wayarta.
Ta
duba da sauri sunan Dr.Lk ne nan da nan ta
cika da mamaki. Tana kokarin budewa ta
karanta sai wani sakon ya shigo. Ta duba
taga sunan Dr.S ne,ta gyara zama ta mike
kafa yayinda hawaye ya hadu da gumi suka
damalmale mata fuska, ta dora hannu aka
ta fasa kuka. Taji hnklnta ya tshi dn bai
kamata ta zama haka ba a wajensu dr.lk
ba,
abn arzikin data keyi musu bai dace su
saka
mata da tsiya ba. Me tayi musu a rayuwa
da zasu hada aki su cuce ta. Ashe son da
Dr. Mohd yace yana yi mata dk tsokana
ce,yaudarata sukeyi kenan? Zuciyarta tana
duka 3 3 a lkcn da zata bude sakonnin dn
fargabar abnda zata karanta. Sai
idanuwanta sikayi dusu dusu har bata gani
sosai sbd tsananin kuka. Ta bude na frko ta
karanta,sai ta dafe krji yayin da ta bude na
2 ta karanta,sai ta damko wuyanta dan
mamaki,kuma sakonnin iri daya ne babu ko
digo daya daya bambanta. Ta zabura ta
mike tsaye ta sake karanta dukka 2n hakika
abn data gani dazu shine ba gizo
idanuwanta keyi ba,gsky ne.
Kin ci jarabawa Aisha Umar,fito muna kofar
gidanku". Abinda Allah ya nuna mata kenan
a cikin wayarta(kunji ta fa sai kace wani
wahayi wai Allah ya nuna mata lols) sako
daga Dr.S da Dr.Lk,dukka abu daya suka
rubuta mata. Ta cika da mamaki sai tayi
sauri ta jawo wani tsohon zaninta ta
fafface
ta goggoge fuskrta tayi wasai,sannan ta
goggoga 'yar hoda ta sake saka hijabnta.
Hannunta sai karkarwa yake ta sala
takalminta ta fito a nutse tana sanda. Bata
tabbatar da abunda suka rubuto mata ba
ko gske ne,amma dao gara taje ta duba. Da
fitarta Dr. S I ta fara hangowa tayi sauri ta
sake duban na kusa dashi, Dr. Lk ne,sai
taga sun dubi junansu sun kyalkyale da
dariya. Ta snkyr da kanta kasa ta karaso
gabansu ta durkusa ta gaishe su. Dr. Lk
yace,srkn kuka, kin daina kukan ne? Dr.S
yace,farida kin bar min ofishina a bude har
an yashe ni. Tay ajiyar zuciya,ta grgza kai
ba tareda tasan abnda zata fada ba.
"Kin ci jarabawa Aisha Umar,fito muna
kofar
gidanku". Abinda Allah ya nuna mata kenan
a cikin wayarta(kunji ta fa sai kace wani
wahayi wai Allah ya nuna mata lols) sako
daga Dr.S da Dr.Lk,dukka abu daya suka
rubuta mata. Ta cika da mamaki sai tayi
sauri ta jawo wani tsohon zaninta ta
fafface
ta goggoge fuskrta tayi wasai,sannan ta
goggoga 'yar hoda ta sake saka hijabnta.
Hannunta sai karkarwa yake ta sala
takalminta ta fito a nutse tana sanda. Bata
tabbatar da abunda suka rubuto mata ba
ko gske ne,amma dao gara taje ta duba. Da
fitarta Dr. S I ta fara hangowa tayi sauri ta
sake duban na kusa dashi, Dr. Lk ne,sai
taga sun dubi junansu sun kyalkyale da
dariya. Ta snkyr da kanta kasa ta karaso
gabansu ta durkusa ta gaishe su. Dr. Lk
yace,srkn kuka, kin daina kukan ne? Dr.S
yace,farida kin bar min ofishina a bude har
an yashe ni. Tay ajiyar zuciya,ta grgza kai
ba tareda tasan abnda zata fada ba.
"kinsi jarabawa farida". Inji dr.S. Dr.Lk
kuma yace wlhy abokina gwadaki yayi
muna
zazzaune a cikin motata a lkcn da kika fito
kika nufi get shiyasa nayi miki wannan
wayar. Niyyarmu mu dauko ki mu dawo
dake gida,sai yace gara mu biyo ki a baya
muga gidanku. Ta sake yin dgwr ajiyar
zuciya ta dago da sauri ta dubi Dr.S sai yayi
mata mrmshi ma kayatarwa. Taji sanyi a
cikin zuciyarta,farin ciki marar misaltuwa ya
tabbata a zuciyarta. Ji take tmkr anyi mata
albishir zata shiga aljanna. Dr.S yace yanzu
ke in aka ce miki haka nake zaki yarda? Ina
da kyakkyawan zato a kanki saina ke so in
tabbatar da hakan, dn haka ni da abokina
muka shirya jarabawa muka baki. Allah
cikin
ikonsa sai kika cinye dukka. Mrmshi takeyi
har yanzu,bata ce komai ba, mun baro aiki
da yawa muka taho a yi hkr a gafarce mu
idan munyi laifi da muka shiryo wannan
gwaji,sbd mun saka ki kuka da yawa. Ta
rufe ido tayi dariya tace, bakuyi laifi ba
yayana. Dr.Lk yace,idan akwai yaro yazo ya
biyo mu mota ya karbar miki kwandon ki
mun taho miki dashi. Tace, to bari in shiga
gida in turo yaro ngd sai anjimanku.
Kallonta kawai Dr. S yakeyi harta shige ciki.
Ya grgza kai yace, lk nan ne gidansu da
gaske? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
Yanzu daman a irin wannan gidan take
rayuwa? Dr Lk yace, da alama kuwa gidan
haya ne basu kadai bane dn ina nan a tsaye
ina ganin mata iri iri suna leko mu. A cike
gidan nan yake, irin hayar nan ta dakuna
birjik,bandaki daya. Yanzu a cikin bakin
gidan nan daman ake dafa mana dambu da
danwake muke ci? Dr.Lk yace, to bakin
gida, bakar tukunya ce? Ai kanwata tana da
tsafta,a tsaftace abincinta. Kai fa a ni'ima
kake shiyasa baka san ana wahala ba a
kasar nan. Dr.S yace, gsky ana wahala aini
ban taba shigowa lungun nan ba 2nda Allah
ya halicce ni. Ai bansan irin wannan gidan
farida take ba, daban zargeta ba don tana
hawa acaba. Alla srki ashe rashi ne yake
sakata hawa acaba.
Bai rufe baki ba saiga wani
dakwalkwalallen
yaro hancinsa fal da majina yace, wai gani
inji Aisha Farida kuna kirana. Dr S ya dubi
yaron ya juya ya dubi Dr.Lk sai suka tun
tsire da dariya. Dr.S ya ce Allah mai
halitta,yaro Allah yasa kayi ilimi ka fita fili
ka rabuda irin wannan rayuwa. Ya kama
hannunsa yace, zo muje abokina,yaya
sunanka? Yaro yace,sunana Dahiru. Dr. S
yana tafe yana sake waiwayawa yana
duban
gidan su Aisha Farida,yana sake kallom
unguwar da kwatoci, baya ga sauro da
kudaje suna ta shawagi. Dr. S ya dorawa
Dahiru kwando aka ya bashi naira #500
suka shiga mota suka tafi. Har suka isa
asibiti Dr. S bai fasa jajantawa wadannan
bayin Allah ba, musamman abar kaunarsa
AF. Yaji ya sake tausaya mata, ya kara
sonta,kuma ya kudiri niyyar taimakonta.
AF ta shiga gida zuciyarta cike da frn
ck,harma ta kasa fasalta irin frn ckn data
tsinci kanta a yau. Tana shiga daki ta cire
hijabi ta dauki waya ta kirasu abida aka ci
sa'a knwrta maimuna ce ta dauka. Byn sun
gaisa sai tace tabwa anti A zasuyi mgna.
Maimuna ta karawa Abida a kunne. Abida
tace AF ya ake ciki? Tayi dry tace, Anti A
ngd wa Allah ngd miki. Yanzu Dr.s yabar kfr
gdn nan shida Dr.lk ashe mgnr nan daya
fada min so yake ya gwasa ni yagani 'yar
iska ce ni? Yace naci jarabawa. Abida tayi
mrmshi tace, naji a jikina Dr.s m2mn kirki
ne, ko byn raina ki zama mai kyakkyawan
zato a kansa. AF taji jiknta yayi sanyi
tace,zaki ji sauki anti,ki daina fdr haka.
Ngd. Abida tayi mrmshi tace, yanzu zaki
wuce mataki na 4 zaki taka mataki na 5
shine ki nuna masa tsantsar soda kulawa.
Idan ya gasgata kina sonsa sbd Allah sima
zai soki a zuciyarsa,yasoki harma ya fara
2nanin yadda zaki kasance a matsayin
matarsa, ku zauna din-din-din. AF taja dgwr
ajiyr zuciya tace, to antina ngd,Allah ya baki
lfy. Abida tace Amin.
BABI NA GOMA SHA UKU Dr. S ya shigo
falon mahaifinsa a wannan safiya dn ya
gaishe shi,ya iske shi a zaune akan dgwr
kujerarsa. Byn sun gaisa shrm ya zauna a
kasa kan kafet a gabnsa yayi murmushi ya
dubi mahifinsa. Yace, Abba naga alama
kana
jin dadin jikinka,maganin nan da aka sauya
maka yafi wancan karbarka. Ya jawo
kafarsa
ya dora akan cinyarsa yana mammatsa
masa yatsun kfrsa. Abba ya dubi S shima
yayi mrmshi yace, Alhmdllh,ciwon kafar
yana yin sauki. Dr.S yace,Allah ya kara lfy
abba. Ka dinga rage zirga'zirga ina ganin
kana dan takurawa kfr da yawn tfy,dk da
ana so a dnga dan tattakawa amma ba dgn
yawo ba yadda kake yi,baka son yawo
amota sosai. Abba yayi dry yace, shuraim
zumunci a kafa yake,idan da kfr nan zata to
tabbas bazan zauna ba sai na taka naje na
gaisa da 'yanuwa da abokan arziki. Kada ka
damu,dk anda kaga m2m yayi sai yanada
halin yi zaiyi, musamman lfy. Idan a
kwance nake ina ciwo ai zama ma sai an
zaunar dano. Haka idan ina kabari,ai
zancen
ziyara ya kare 2nda ina raye to dama ce
dani. Ka sani kada ka yanka zumunci,dmn
zumunci abune mai girma,shi zikai ka
aljanna.
DUK KYAN TAKALMI 3* 3
2ni dr.s ya sulale ya kishingide akan dgwr
kujerar da yake zaune,sbd tsananin jin
dadin kalaman abar kaunarsa dadada. Yayi
mrmshi ya lumshe ido yace, kin ceto
rayuwata wacce take cikin garari da hatsari
ada, dn 2nu na fara sallam frn ck akan
rashin samun bayananki. A zatona na fada
trkn mace, allah zai sakawa wadanda suka
dade suna son maso wani, kuma suna
zargina nine sila. AF tayi mrmshi tace, na
fhmce ka, ni zan baka labarin wannan, dmn
mune a bayn fage, mun fika ganin
abubuwan da suke faruwa. Kai takalmi ne
mai tsananin kyau da tsada dmn tmkr anyi
ka daruwan zinare da lu'u'lu'u. A ganina,ko
kuma nace a wajena, ban taba ganin
kyakkyawan takalmi kayatacce irinka ba,sai
masu kudi ne suke iya takawa dk da haka
ba a sallama musu ba. Mu talakawa kuwa
daman sai dai mu daga ido mu kalla, ko
kusa dashi ba zamu iya karasawa ba, balle
mu gani sosai harmu taya. Sai mai takalmin
wanda ya halicci takalmin da kansa,
Wato Allah (s.w.t) ya ce farida ga takalmin
nan na baki kyauta babu ko sisisna. Ka
kwatanto wanne itin frn ck ne bazanyi ba?
Dole na fashe da kuka dn murna. A halin
yanzu sbd tsananin kyawun takalmin bana
so yayi kura,bana soya wahala. Takalmin da
aka sanshi a kafa sai gani ina daura shi a
goshina,mutane suna kallona sbd basu taba
ganin tsadaddade kuma kyakkyawan
takalmi kmr irin nawa ba. Abnda suke tmby
ta shine yaya akayi kafata babu takalmi ina
yawo a titi a haka,maimakon in saka
takalmon sai kuma na daura a goshi?
Amsar
itace, wannan takalmin daban ne bana
takawa bane a kafa,dmn yafi karfin kafata.
Dan naso na rasa raina,na rugurguza rywata
akan neman takalmin nan, ubangiji ya dube
ni, ya bani tabbas zanfi kowa tattalinsa
shiyasa ma nake daura shi a goshi dn bana
so yayi kura. Dr.s yayi shiru yana
sauraronta, 2nda Allah ya halicce shi bai
taba haduwa da yarinya mai kima da iya
magana ba, hausa ckn jausa,sai AF. Ya
fhmci wasu abubuwa data ke nufi, wasu
kuwa sai ita da ubangijinta suka sani. Yayi
mrmshi yace, "Lallai kin kawata takalmin
nan,har kin kara masa kyawun da bashi
dashi. Kin kara masa drjr da bai kai can ba.
Dole mutane su kalleki idan suka ga ki
daura takalmi a goshi,maimakon ki saka a
kafa. Nima baz zanso ki zama abar kallo
da
nunawa ba a duniya,sbd kyakkyawan
takalminki,kyawun takalminki baifi na
kowacce mace ba. Dk iri 1 ne a idanuwanki
ne ke kadai kike ganisa da kyau,da daraja
irin yadda kika suffanta shi. Idanma yana
da
kyau, to baifi krfn a saka shi a kafa ba a
taka, ina umartarki daki sauko da
kyakkyawan takalmin nan naki daga gshnki
ki saka shi a kfrki ki tattaka shi, domin
'DUK KYAN TAKALMI' a kafa ake takawa.
Yayi dariya ya kashe wayar ba tareda ya
jira
abinda zata fada ba.
Tana zaune ta daskare ta zama tmkr an
sassakata sbd al'ajabin abubuwan dta ga
suna gudana. Ta fada a ranta, banda
ubangiji wa zaiyi min wannan kyautar haka?
Haka dr.s ya fara sona yanzu? Tsarki ya
tabbata ga ubangijin talikai. Allah ngd
maka,Allah ka bawa abida lfy,ta zo ta ganni
tare da dr.d a wannan kyakkyawar inuwar
da muke ciki. Sai yanzu sakon katin brsta
mu'azzam ya shigo,ta kalla tayi mrmshi
tace, yayana aika makara 2n yaushe
takalmin goshina ya dawo kafata? Sai dai
ban fara taka kasa dashi ba har yanzu ina
zaune akan katifa dashi.
BABI NA GOMA SHA HUDU Rayuwa mai
sauya salo dr.s baya jin dadin rayuwarsa
idan bai kira AF sau 3 ko 4 a rana ba. Kiran
sassafe, da hantsi ko da rana, wataran ya
kira da yamma sannan kiran dare sole ne
idan yazo kwanciya. Tana mamaki dajin
dadadan kalamansa,sai ta fara neman
bakin
ciki da damuwa ta ra,dk sun baje. Abu daya
ne ya kasa gushewa a ckn zuciyarta,kuma
ta
kasa daina buya tana kuka a kanshi,shine
rashin lfyr abida. Tana ma2kar addu'a Allah
ya bawa abida lfy,tazo ta ganta da dr.s.
Allah mai yadda yaso da bayinsa,abida na
can a kwance jiya-i-yau, sai an tayar sai an
kwantar. Allahu akbar. Sati uku ya rage
yara suyi hutu yaya hussani ya tattara su,su
kaura shagamu kacokan, musamman
wannan satin da yaje dubata yaga yadda ta
sake kumburewa, sai hnklinsa ya tashi yana
kuka suna kuka haka suka rabu. Harya fara
shirye shuryen barin aiki yana 2nanin
sana'ar da zai fara a shagamu,son idan
babu
abida a kano babu zancen sauran jin dadi a
kano a rayuwarsa. Ya sanarwa da AF dn ta
fara kammala kayansu gaba 1 a waje daya,
hnklnta ya tashi ma2ka sbd rabuwa da dr.s
shine kadai abnda zatayi takaicin rabuwa
dashi a kano,bayan shi dk sauran wasa ne.
Ta kasa 2nkarar yayanta ta fada masa
tsakaninta da dr.s haka ta kasa fadawa dr.s
zasu kaura shagamu,dn kada ta tayr masa
sa hnkli.
Yace,sweet heart yaya akayi ne? Nazo fa
daf
da zauren gidanku,ina bakin kofa. Taji
zuciyarta ta sake harbawa,muryarta na
karkarwa tace,gani nan zuwa. Ta danna
lmbr y.husaini dn ta nemi izini, bai dauka
ba,dn haka saita tashi da sauri ta sauya
kayan jikinta. Wata sabuwar atmfrta ta
daura mai suna binta,dinkin raga da siket
ne, matsattsu,hoda da kwalli kawai ta saka
ta dauko hijabinta ta saka. Sai taji wayarta
tana ringin ta duba taga yayanta ne yake
kiranta dn yayi mamaki da gani kiranta a
daidai wannan ljcn sai hnlklnsa ya tashi
ma2ka,zuciya mai sake sake saita dinga
sassaka masa abubuwa daban2. Babu
abnda bai tuna ba,ya aiyana a ransa ko
bala'i ne yasamu dya daga ckn 'yayansa ko
ita AF, ko kuma mai kacokan abar kaunarsa
ce ta mutu aboda. Cikin sauri ta amsa,
muryrsa na karkarwa ya tmbyta farida,lfy?
Kmr yadda ya shiga tshn hnkl haka ya jiyo
alamun itama tana ckn hnkli irn nasa dan
haka sai ya sake sukurkucewa. Mryarta na
rawa tace, yaya,dr.s ne yazo yana kfr gida
inje wajensa? Ya fusata ya daka mata
tsawa
yace, waye dr.s? Tace mu2min daya zo
rannan.makwabta suka fada maka kace
karka sake ganinsa a gidan nan.
Ya sake hasala yace, kince nace kada ya
sake zuwa, me ya kawoshi yanzu? Kice
masa yabar min kfr gidana idan nazo sai
naci mu2ncin ku keda shi. Ya katse waya.
Ta dora hannu akai ta rushe da kuka tana
fadin, innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Yau ya
zanyi? Wayyo sr.s dina,ina sonka bana so
na rasaka. Yaya me nayi maka zaka rabani
da frn ckn rayuwata? Wayar tace tayi kara
saita duba taga s ne,nan da nan ta damma
ba tareda tasan abnda zata ce masa ba
yana magana ckn marainiyar murya.
Yace,sry farida,na takura miki ko,nazo ba
tareda na sanar dake ba? Ba damuwa bari
na tafi zamu hadu wani lkcn. Sai taji hnklnta
ya sake tashi kuka mai tsanani ya rifto
mata. Yace,kukan meue kike farida? Cikin
sheshekar kuka tace, dr.s kayi hkr ka yafe
min. Sai ya sulale ya zauna akan dakalin kfr
gidan dan da a tsaye yake sbd gigicewa.
Lfy? Ya tmbyeta. Kuka kawai take ba tareda
ta iya yi masa bayani ba sai ajiyar zuciya.
Yace,farida fito ina kfr gdnku muyi magana
sosai. Ya kashe waya yacigaba da huci sbd
tafrfasar da zuciyarsa takeyi masa. Da aka
jima bata fitoba dr.s ya sake kiranta sai ta
amsa kuka kawai take ba tareda ta iya yi
masa bayanin komai ba. Yayi ajiyar zuciya
yacemfarida,fito ina kfr gidanku muyi
magana sosai. Saiya kashe wayr bai bari ta
bashi amsa ba. Ta yanke shawarar ta fita
wajensa koda kuwa yaynta zai kasheta.
Tana fitowa sai taga abin kaunarta yayi
shiru kmr mai 2nani,hnklnsa dk a tashe. Ta
durkusa ta gaishe shi,bai amsa ba sai
hararar daya dinga harba mata,musamman
yadda yaga idanuwanta sun kumbura sunyi
jajur sbd tsananin kukan da tasha yi. Ya
grgza kai dn takaici yace, faridah,haduwata
dake wani sirri ne kuma hikima ce daga
Allah, ba zato babu tsammani Allah ya jeho
ki sikin rayuwata,kuma cikin hikimarsa ya
smr miki wajen zama mai fadi a ckn
zuciyata. Na tsinci kaina ina mai frn ck da
saninki,dn naji a jikina ke alkhairi ce a
gareni. Naji ina sonki,halayyarki a zahiri tayi
min. Sai dai kash kina da wata damuwa,ko
manufa a ckn zuciyarki wacce tayi bam
bam
da tawa. Ina zafgn bakya sona na takura
miki ko kuma ince akwai wanda kike
so,amma kun rabu wala Allah ya rabu dake
kina tsananin sonsa,koya rasu kina cikn
kaunarsa,idan nazo ko kikaji maryata sai
inyi miki fami ki 2no dashi. Haka ne koba
haka bane?
tayi sauri ta girgixa kanta hawaye ya sake
kwaranyowa tace ba haka bane yaya
abinda
kake xargina dashi.kuma ina patan xaka
yarda da abubuwan da xan pada maka
yanxu don bana 2nanin ko a maparki in
pada maka karya a rayuwata saboda kana
daya daga cikin mutanen da sukeda
muhimmanci arayuwata
Tayi sauri ta girgiza kanta,hawaye ya sake
kwaranyowa,tace,ba haka bane yaya,abun
da kake 2nani gaba 1 baiyi shige da abun
da kake zargina dashi ba. Kuma ina fatan
zaka yarda da abubuwan da zan fada maka
yanzu dn bana 2nanin ko a mafarki in fada
maka karya a rayuwata,sbd kana 1 daga
cikin mutanen da suke da mahimmanci a
rayuwa. Dr s, zaka iya mamaki idan nace
kaina kadai frn ckn rayuwata, ina yi maka
son dakai baka yimin. Haka ina maka son
da
ban taba yiwa wani d'a namiji ba a duniya.
Son da zan iya shiga halaka idan na rasa ka.
Kuka da nakeyi na frn ck ne sbd Allah ya
amsa addu'ar dana dade ina yi akan Allah
ya
hadani da bawansa mai kyawawan
halaye,kuma mai kaunata sbd Allah yasoni
a
yadda nake talaka,kuma marainiya. Ya
kawo
min kai wanda ko makahon dabai taba
ganin duniya ba ya tsaya a tsakiyarmu
yasan ka wuceni a komai. Dr.s bazan boye
maka komai ba,yau kukan da nake na tshn
hnkli ne,domin yayana yana kokarin ya
rabani dakai,frn ckn rayuwata a sanadiyyar
'yan gulma da suka soke ka. Yaki ya tsaya
nayi masa bayaninka, da kuma inda muka
hadu,yace, na cika shige2,na dauko wanda
yafi mu zan jawo masa masifa da tshn
hnkli
kada in jawo azo a kama shi.
Y.husaini zai tafka babban kuskure idan
yayi
gangancin rabani da frn ck na, dn zai iya
rabani da rayuwata gaba daya. Ta fashe da
kuka yayinda dr.s yana zaune ya zuba mata
ido yana dubanta kawai tmkr a hoto. Babu
abnda yake sai mamakin yadda Allah ya
sauya masa rayuwarsa nan da nan akan
mace. Bai taba tsintar kansa ckn irin
wannan hargitsin ba, abn da yakeji a gari
yazo kansa. Bai iya cewa komai ba har
yanzu kallonta yake,ta sharbe hawaye
face2
a hannayenta. Tana waigawa gefenta saita
hango yaya husaini ya sauka daga kan
acaba. Nan take dr.s yaga tana
makyarkyata ta fara ja da baya. Da sauri ya
soma tmbyrta, mene ne kuma? Ta nuna
yayanta da hannu tave, yaya hussaini ne,
idan ya sameni anan dukana zaiyi. Dr s ya
umarce ta data shiga gida,tayi wuf ta fada
cikin gida jikinta na bari. Cincirindon matan
gida da 'yayansu ta gani a lallabe suna leko
su. Ta kalle su sama da kasa ta watsar ta
shige daki taci gaba da kuka, ta kasa zaune
ta kasa tsaye,addu'a kawai take
kwaranyowa tana fatan Allah ya huci
zuciuyar y.husaini kada ya yiwa dr s
wulakanci. Idan ta zauna saita zabura ta
mike tsaye tana ta kai kawo daga frkn daki
zuwa karshen bango tmkr zararriya. Gashi
babu tagar da zata leka ta hangosu. Bata
san halin da suke ciki ba.
Dr s ya dubi y.h yayinda shima y.h yake
kallonsa 2n daga nesa kallo ne mau tafe da
harara galleliya,kokari y.h yake ya shige
cikin gida ba tareda ya tsaya sun gaisa da
dr
s ba. Shi kuwa dr s saiya 2nkaro shida sauri
yayi mrmshi yayi masa sallama gamida
mika
masa hannu. Babu yadda y.h zaiyi a dole
ya
amsa masa sallamar ya mika masa hannu
ba dn zuciyarsa naso ba. Suka janye
hannunsa a lkc 1. Har yanzu y.h kokari yake
ya shiga gida yabar dr s a tsaye. Ya sake
matsowa yasha gabansa. Yace, sunana dr s
i. Ina aiki a asibitin malam aminu kano.
Nine wanda nake zuwa wajen af kanwarka.
Y.h ya yamutse fuska a dole ya tsaya cak
ya
saurari dr s yace,na sami labarinka ai. Dr s
yayi lallausan mrmshi alhali zuciyar na cike
da tsananin takaicin wulakancin leburan nan
keyi masa. Yace, nazo in nemi alfarma 1 shi
ne,kada ka zargi kanwarka,kada ka
zageta,koka doke ta bata da laifi ni nake
sonta,kuma na biyo ta gidansu ko a yanzu
fitowar data yi tazo ta fada min ka hanata
fitowa inyi hkr in tafi sai gaka nan ka dawo.
Na 2 kuma nazo neman izini,kabani dama
in
dinga zuwa wajen kanwarka,sbd ina
sonta,idan kuma Allah ya lamunce min
inaso in aureta. Y.h ya sake daga ido ya
dubi dr s cike da mamaki,yayi masa kallon
mayaudari. Yace, ta yaya zaka aureta? Dr s
yayi mrmshi yace, malam husaini yi hkr da
tmbyr da zanyi maka. Da Allah kana ganin
nayi maka kama da lalatattun samari zauna
gari banza,masu yausarar 'yan mata? Am i
nt responsible..... Dakata ba wannan na
tmbyeka ba malam,farida kanwata ce ina
da alhakin in zaba mata mijin da yayi dai-
dai
da rayuwarta,inda ba zata wulakanta ba.
Y.h ya fada a fusace gamida dago
hannunsa
ya tsayar da dr s. Ai anan dr s ya daskare a
tsaye yana kallonsa kawai ba tareda yasan
kalma 1 dazai furta ba. Hakika ya kasa
gane
ida y.h ya dosa. Yabi shi da kallo har ya
shige ckn gida. Ya sulale ya zauna akan
dakalin kfr gidan yayi shiru kansa a sunkuye
a kasa yana 2nani. Babu abnda zuciyarsa
bata aiyana masa ba. Ya aiyana ya tashi
yayi tfyrsa kawai ya rabu da Aisha farida
har
abda, sai ya tuna nasihar da mahaifinsa
yayi
masa cewar, ya zamana mai yawan hkr a
wajen neman auren,domin aure ya gaji irin
wadannan sabani da matsaloli daga
kowanne bangare. Yaji yana son farida a
ransa ba karamar wahala zaiyi ba idan yayi
garajen rabuwa da ita. Yaji a jknsa jihadi
zaiyi babba idan ya aure ta ya fitar da ita
daga wannan kangin talaucin. Saiya saka a
zuciyarsa zaiyi damarar yaki tsakaninsa da
y.husaini har saiya wayar masa da kai ya
gane kyautar da Allah ya 2uro masa har
gida.
 KYAN TAKALMI 3* 4
Yaga maza suna ta daura alwala suna
tunkarar wani karamin masallaci kusa da
gidan,don haka sai shima ya bisu a baya. A
bakin masallacin ya samu buta ya tsugunna
yana alwala sai ga y.hssn ya wuce shi zai
shiga masallaci. Da alama y.hssn yayi
matukar razana zuciyarshi ta cika da
mamaki da yaga dr shrm bai tafi ba, kallon
kallo suka dinga yi har ya shige domin har
an tayar da ikamar sallah. Da aka idar da
sallar magaruba da yawa basu tafi ba, sai
aka hau kara karatu a takaice dai islamiya
ce ta maza. Dukda babu wutar lantarki
babu genereto sai fitilon kwai da hasken
wayoyi ake haskawa ake karatun. Ya hssn
yana daga cikin dalibai sai dr shrm ya matso
gefen sa ya zauna yayain da shima ya samu
qurani ya bude yana karanta duk surar da
ake dora masu. Kallon dr shurm kawai suke
ba tare da sun san daga inda ya fito ba,
musulmi danuwan musulmi ne saboda haka
basu razana ba, basu tsorata ba kuma basu
damu su tambayeshi daga inda ya fito ba.
Da aka idar da karatu sai aka kiRa sallar
ishai kan kace kwabo masallaci ya cika sai
aka tayar da ikamar sallar ishai. Ya hssn ya
fito da shi da yangidan su suka nufi kofar
gidan bayan an idar. Tsilun ya sake ganin
Dr shrm a cikin tawagarsu suka iso har
kofar gida akan tabarmin su suka zauna,
inda aka fara fito da kwanukan abinci daga
kowanne daki ma'ana ciyayya suke idan
anci na wannan sai aci na wannan. Malam
yushau ya dubi Dr shrm cike da mamaki
yace samari daga ina? Tundazu nake ganin
ka a masallaci yi hakuri da tambayata bamu
sanka ba. Ya hssn yayi caraf yace tare muke
dashi. Sai su duka suka cire tsoro da
damuwar da suka tsunduma tuntuni, amma
tambayoyi ne cike a zuciyoyin su, ina hssn
ya samo wannan fallelen yaron, gashi
masinja wannan kuma sai dai ace manaja
ne a bankin, ina suka hadu suke abota? Dr
shrm yaji dadin amsr da ya hssn ya basu ya
samu kwarin guiwar fuskantar ya hssn yace
yaya zan tafi ina ganin ba sai na tsaya cin
abinci ba a koshe nake. Sai mutanen wajen
suka yi masa caa akan ya tsaya yaci abinci
harda yaya hssn. A dole dr shrm ya saka
hannu ya gutsuri wani tattauran tuwon
masara gabza wacce ba'a tankade garin da
tsaki ba aka tuka shi, haka ya dangwalo
wata bakar miyar kuka wadda ba'a sa nama
ba sai warin daddawa kawai take. Ya kai
baki babu abinda yake ji sai dandanon kafi
zabo kawai a bain sa cauuu! Kan kace
kwabo zuciyarsa ta hautsine yana shirin ya
kwalaye amai amma ya daure da kyar ya
runtse ido ya hadiye. Tun daga wannan
lomar bai sake garajen kara kai wata lomar
bakin saba, haka dai ya rinka tsoma hannu
kamar ci yake ya debo tuwo ya dangwalo
miya ya sake danna hannunsa cikin kwanon
tuwon. Su kuma gogayen basu lura ba
lomar tuwo kawai suke kaiwa cikin bakin
su, kasancewar duhu ne babu mai ganin
wani dadin abincin su suke ji yankan tuwon
nan kawai suke suna kwaso miya suna afka
shi a birnin cikin su. Kai kace naman kaji ne
ko na talo talo. Mamakin su kawai dr shrm
keyi yadda yaga suna iya cin wannan
gabzar, sai yaji imani ya sake shigar shi, yaji
ya sake godema Allah akan baiwa da
ni'imar da yayi masa. Idan suka cinye
wannan kwanon sai su janyo wani, a na
janyo kwanon Aisha farida dr shrm yaji a
jikinsa wannan na Aisha fard ne,saboda
wasu dalilai da yaji a jikin sa, na farko ga
irin food flask din da take kai musu abinci,
na biyu ana budewa yaji irin kamshin
abincinta na ukku kuma ga irin dambun da
take kai musu. Ya dauki buta ya wanke
miyar kukar da ta bata mai hannu, sannan
yazo ya luma hannu cikin dambun da shi
aka ida cinyewa cin gaske yai ma dambun.
Kuma yana farin ciki don yasan daga
masoyiyarsa ne. Ko tantama ba yayi yasan
saboda shi tayi dambun nan saboda da
zafin sa kauu! Ba a dade da sauke shi ba,
yasan tana da labarin yana nan bai tafi ba.
Tunda ga kan abincin nan yasan farida ta
fita daban da sauran matan unguwannan,
girkinta yafi na kowacce mace dadi da
tsabta, haka yaji sauran mazan suna santi
da yabawa. Saboda tsananin ansan cewa
shine mai dadi sai aka barshi shine karshe.
Da suka gama ci sai suka wanke hannu, dr
shrm yaga alamar ya hssn bai da niyyar
sake mike kafa yai ana sabuwar hira, sai ya
mike ya babba su hannu yayi musu sallama,
da alama ya hssn bai da shirin biyoshi su
kebe, don haka sai ya dube shi yace yayana
zan tafi kuma ban gama baka sakon da
nazo ma da shi ba. A dole ya taso ya biyo
dr shrm suka tafi can gefe guda suka tsaya.
Dr shrm ya dubi ya hssn har yanzu sai cin
magani yakeyi, zuciyar shi zuciyar shi tana
yi masa kuna amma ya daure ya duka yace
yayana zan koma amma fa bazan bar kofar
gidan nan ba sai naji amsa daga bakinka.
Amsar me ya fada cike da gadara. Dr shrm
yai ajiyar zuciya yace ka bani dama in zauna
da ku ahankali zaka san ko yaya nakeson
farida. ... Wurin is not clear.. Tana da
bukatar nazari sosai, ka bani lokaci har sai
na nemeka. Dr shrm yayi shiru na wani
lokaci yana kallon ikon Allah, ya rasa me yai
ma ya hssn haka ya tsane shi, ko da wasa
bai taba tsammanin zai tsinci kansa a cikin
hali na wulakanci irin haka ba, lallai ashe da
bai san rayuwa ba sai yanzu ya fara sani?
Da kyar ya bude baki yayi magana yace to
yaya na gode ISA zaka sameni mai
kiyayewa kuma da yin biyayya akan duk
abinda kace, kuma yadda kace haka za'a yi.
Ka bani lambar wayarka sai na kiraka naji
duk abinda ka yanke. Ya zaro dalleliyar
wayarshi sai yaga msd calls din AF har guda
ukku, yay hssn ya karanto mashi nmbr ya
rubuta ya kira nmber ya hssn ya ciro
kwarabbyar wayarsa ya kalli nmber yace to
na gani zan adana nmbr. Dr shrm yayi
godia suka yi sallama ya nufi motarsa yayn
da ya hssn ya dawo kofar gida inda ya barsu
ya iske su suna hira da suka ganshi ma basu
daina yi ba domin yaji abinda suke fadi.
Mllm sadisu ne ya dubi mllm yushau yace
ni wannan ba shine mutumin da suka zo
wajen AF ba wadanda suka zo da wata
babbar mota ba, mllm yushau yace shine
mana ai daga ganin wannan yaron
mayaudari ne, ba maganar aure bace ta
kawo shi. Malm lawal yace to ni ba wannan
ba ma, mutumen da ba'a san asalin sa ba
ba'a san asalin kudin suba. Ya hssn dai yana
gefe yana kallon su yayin da zuciyarsa ta ci
gaba da gasgata zancen su, mllm sadisu ya
kalli ya hssn yace kai yaro ne kuma kai bako
ne mu muka san kano muka san mutanen
ta, don haka ka gaggauta raba shi da
kanwarka, gara dan unguwa da aka san
asalinsa da sana'arsa. Sauran ma suka
tsoma baki suna goyon bayan abinda mallm
sadisu ya fada. Ya hssn yaji kanshi yai nauyi
kamar zai fashe saboda toshewar tunani, ya
yanke a ransa raba AF da Dr shrm shine
abu mafi sauki a rayuwarsa. Dr shrm ya kira
AF yana fitowa daga unguwarsu, basu daina
magana ba har sai da ya iso gate din
gidansa, mai gadin sa ya bude masa gate.
Ya shaida mata ya iso gida zai shiga yayi
wanka ya ci abinci zai kirata kafin ya
kwanta. I love you baby ita ce kalmar
karshen da yake gayama duk lokacin da
suka gama waya.
Ta sulale ta kwanta akan tabarmarta don
dadin da zuciyarta keyi, Dr shureim yayi
mata hira mai dadi wanda bai taba yi mata
irinta ba tun sanda suka hadu, ya fayyace
mata abinda ke cikin ransa watau irin
dimbin kaunar da yake mata, yace ta
kwantar da hankalin ta, duk rintsi yana tare
da ita babu gudu ba ja da baya. Yana da
kykkyawan zaton matsalolinsu sun kusa
karewa saboda ya fara shawo kan ya hssn
sannan ya shaida mata ra'ayin sa akan ta
idan Allah ya ruboto mas uzasu zamanto
miji da mata yana da ra'ayin ya aureta.
Dama ta dace da irin matar da ya keson
zama da haka ma mahaifinshi. Dukkan
godia sun tabbata da Allah SWT abinda
Aysha f take ta maimaitawa kenan take
kuma fadi a zuciyarta. Kamar bango zai
tsake ras haka ta ji ana ambaton sunanta
muryar yaya hussain ne daga dukkan alamu
a fusace yake. Sai tayi firgigit ta tashi zaune
ta dafe kirjinta tana fadin innalillahy wa
inna ilaihir rajiun! har yanzu bai daina kwala
mata kira ba sai ta mike da saukri, tana
amsawa muryarta na kakkarwa ta fito da ga
dakin ta sauri ta iske shi a bakin kofar
dakin, tayi sauri ta durkusa a gabansa cike
da ladabi. Ki biyoni dakina ya fada a fusace
sai ya juya.... Maganar boye boye ta kare
dan kowa yau zai fadi ra'ayinshi yau ita da
shi, don daga dukkan alamu baiyi amanna
da zuwan Dr shrm ba itama kuma ba zatayi
amanna ya raba ta dashi ba. Ayau tayi
damarar tunkarar duk wata muzgunawa,
zagi, duka da duk bakaken maganganun da
zai yi mata, don ba zata iya dadada masa
ba ita ta kuntata rayuwarta. Bata taba yi
masa mus ba amma yau zata fara saboda
kyakyawan takalminta Dr shurm. Ya hussn
ya shiga daki ya zauna a gefen katifa yayin
da AF ta tsugunna a bakin kofa. Ya daka
mata tsawa shigo ciki ki zauna munafuka.
Ta shige lungu yayin da jikinta yake ta rawa
don fargaba. Ya dade yana harbo mata
harara, takaici yasa ya kasa magana, can
yayi tsaki yayi ajiyar zuciya yace. Farida
yaushe kika zama jin magana, marar daukar
magana? Waye yake zugaki kike yin abinda
kika ga dama? Wai ke kin waye ko kina
ganin yanda wayayyun kawayenki sukeyi
kina kwaikayonsu, to bari kiji in gaya maki
bazan dauki nauyin wannan a gidan nan ba.
Ta sunkuyar da kanta kasa ta kasa magana
sai hawaye ne ke ta kwarara daya bayan
daya. Yay hssn ya ci gaba da magana cikin
fusata tun rannan na fada maki kada ya
sake zuwa baki ji ba, a waya nace kada kije
wajen sa kika fita din, in yaso in kashe ki.
Sannan yazo ya nace man yaki tafia sai na
saurtare shi, to ki fada masa karshen
magana kar in sake ganin kafarshi a gidan
nan don kowa yasan yaudarece yakeyi ba
auren ki zaiyi ba. Yaje can ya auro dai dai
shi yar masu kudi, kima ki samu talaka dai
dai ke ki aura yafi kwanciyar hankali.
DUK KYAN TAKALMI 3* 5
Ta sa hannu ta goge hawaye ta gyara
durkuson da takeyi, ta dube shi duban keke
da keke tace yaya hussaini naji abinda kace
amma naso ka bani dama nayi maka bayani
kaji ta bakina nima tunda kaji ta bakin masu
kawo maka gulman. Ya fusata yaji tamkar
zai kai mata bugu sai ya fasa. Ta fada cike
da tabbaci tace mutanen gidan nan mata
da mazansu, wadanda ba sa kaunarmu da
alkhairi. Burinsu kullum suga mun tozarta.
Baka sani bane dan baka zama dasu a
gidan. Ya sake fusata yace da na turaki
karatu makaranta aka tura ki asibiti sai
akace kije jajibo soyayya? Ashe daman ba
karatun kike yi ba? Ke gwanar iya magana
zakice min magulmata ne suke hadawa?
Bangani da idona bane ko bai fada min shi
likita bane daga asibitin? Ni bani da hankali
sai wani ya fada min? Toh barikiji farida
bake babu mutumin nan, idan kina so ki
cigaba da jin dadin zama dani a rayuwarki.
Farida ta dago da sauri ta dube shi tace naji
abinda kace yaya, na yadda da abin da ka
fada, amma ka sani raba ni da shuraim
dinnan da kake kokarin yi tamkar rabani da
raina ne.
Sai ya dago ido da sauri ya dube ta yayi
mamakin ganin idanuwanta a tsaitsaye tana
magana cike da tabbaci ko alamar kuka ma
babu. Ta sake cewa shuraim bashi da aibu,
kuma shi mai sona ne tsakani da Allah. Ina
son shuraim fiye da yadda yake sona kuma
sai da naci uwar wahala kafin na same shi.
Anti abida tafi kowa sanin yadda abubuwa
suka faru. Babu irin masifun da ban shiga
ba a sanadiyyar sonsa. Sai yanzu da Allah
Ya amshi adduata ya kawo min shi har gida
sannan zasu zuga suce a raba mu? Ya sake
cika da mamaki da jin kalamenta, yaci gaba
da yi mata duba na rashin fahimta. Can
yace farida me kike so kice min? Kina nufin
kun dade tare dashi? Tun abida na da
lafiya? Aisha farida ta muskuta ta zauna
sosai ta fayyace masa gaba daya labarin
abin da ya faru tsakaninta da dr shuraim
tun daga ranar da ta fara ganinsa a duniya
har zuwa rana irin ta yau. Yaya hussaini yayi
shiru yana jujjuya maganan nan yadda abida
tayi kicin kicin a cikin maganar. Sai yanzu da
ta fada masa wannan labarun yake ta
tunano wasu abubuwa da ya gani suna
faruwa. Shiru kawai yayi musu. Misali a
ofishin 'yan sanda ance wani namiji ne yazo
ya fito da aisha farida babu mace yayin da
abida tace masa mata da mijinta ne suka
fito da ita. Haka yana sane da girke girken
da sukeyi da asuba a jujjuye a sababbin
foodflask , idan ya tambaya abida tace mara
lafiya ake kaiwa kawar aisha farida
Yaya hussaini yana matukar son abinda
abida take so, shima zai so ace ya cika
mata burinta koda bata raye. Yayi mata
nuni da hannu alamar ta tashi tafi ya
sallame ta don ya kasa sake cewa komai.
Aisha farida tayi wuf ta fice daga dakin
yayin da ta danji sanyi a cikin zuciyarta don
taga alamar zai saduda. A cikin daren sunyi
waya da dr shuraim kuma ta shaida masa
yadda sukayi da yayanta. Duk da dai bata
fada masa duka ba amma ta fada masa
abubuwan da ta fada masa cewar raba ta
dashi tamkar yana shirin raba ta da ranta
ne. Sai dadi ya rufe dr shuraim, ya cika da
mamaki. ASUBA TA GARI 'YAR SHAGAMUN
LIKITA!!!
BABI NA GOMA SHA BIYAR "Zuwa nayi ki
maimaita min kalmar da kika fada min a
waya a daren jiya. Inji dr s yake fadawa af a
lkcn da suke tsaye a kfr gdnsu suna zance
da yammacin ranar asabar. Af tayi mrmshi
tasa hannu ta rufe ido dn kunya. Yace,
daman na sani ba zaki iya fada ba,idan kika
ganni amma a waya harda fada da
maimaitawa. Toni bari na fada miki 2nda
ba zaki iya fada min a fili ba. Ina sonki kmr
yadda kaza take son kwanta,bazan iya
rabuwa dake ba kmr yadda ba za a iya raba
hanta da jini ba. Koba haka kika ce min jiya
ba? 2nda nake ban taba jin irn wadannan
kalamai ba sai jiya a bakinki. Kin iya
hausa,sannan da wuya ki fadi marar
amfani,shiyasa kike kara shiga raina. Na
yaba da yadda kike sona sbd allah haka iana
jindadin yadda kike kula dani a kowanne
hali nake ciki,kina kula ki turo min sakon
tausayawa da tausasa zuciya. Duk da har
yanzu y.husaini baice min komai ba akn
hukuncin daya yanke a kaina. Idan na
kirashi ina jinsa faram2 nasan babu
matsala.idan ma akwai matsala ina addu'a
allah ya kawar da ita ya tankado mana da
alkhairai. Af ta marairaice ido tayi mrmsh
tace, amin ya allah. Tana rufe bakinta sai
taji an daka mata duka a baya ance,shegiya
aisha umar zance kikeyi da yamman nan?
Tayi sauri ta waiwaya cike da takaici sai taga
ummi kawarta ce. Al'amarin ummi sai
addu'a sbd ta zama abar a tausaya mata,
kai kace sabuwar mahaukaciya ce sbd
rashin kwanciyar hnkl da talauci ko zanin
daurawar kirki babu a jikinta,ita da goyon
bakikirin a cikin tsummokarai. Yadda dr s ya
kaikaice yana kallon ummi sama da kasa
shiyasa af jin kunya. Da kunya ta nuna
ummi tace kawarta ce,dk da ba zaman
karya suke yi ba ita dashi. Sai suru2 ummi
takeyi barkatai babu nutsuwa idan tayi
magana daya saita dakawa farida duka ta
dauko ashar ta kwararo mata,ta dauka
burge shuraim takeyi. Kokari take ta
tonawa farida asiri dn harta fara cewa badai
wannan mu2min an bane,yazo da kafarsa?
Suna shiga dakin af sai ummi tace,aisha
umar wanne malamin ne ya tsaya miki kika
sami wannan tsalelen,nima ki raka ni? Kada
dai kice min likitan nan ne da kikeso baya
sonki,wanda malam yayi miki aiki a kansa.
Kinsan aikin malamn nan fa yanaci,yanzu
gashi naki yaci yazo har kfr gidanku,gsky
mu2mn nan ya hadu nifa na zaci baya jin
hausa,na dauka farar fata ne,mu2min nan
kadara ne,ga kyau ga kudi harya fiki kyau
fa. Daman banda aikin malami yaya za a yi
mu2min nan ya kalle ki,kinga yadda yake
sonki kuwa naga sai wani kallonki yakeyi.
Nima dai ba laifi ina dan ganin cigaba a ckn
ayyukan dana rarrabwa malamai kashi-kashi
matsalar da ake samu ni inayi,budurwarsa
ma tanayi,uwarsu ma tanayi dn su raba mu.
Shiyasa bana ganin abubuwana suna tafiya
dai-dai. Dadin dadawa bani da kudi,kin san
aiki sai da siyen kayan sadaka,duk kayan
dakina sun kare,yanzu ko kmen zanyi ma
banida ko katifa dk na siyar. Kinga yanzu
ma daga wajen wani nake a lungun sharifai
makociyarmu ta hadani dashi,shima dubu 3
yace nakai za a yi aiki,sannan a yanka
kaza,shiyasa naji dadin dubu biyun nan daya
bani. Af tayi shiru dn takaici ko iya kallon
fskrta batayi na,tacigaba da kirga himilin
kudinta data iske a cikin ambulan din daya
bata. Sababbin 'yan dubu dubu ne har guda
ashirin,dubu ashirin ya bata hade da wani
dan karamin kati (greeting card) mai dauke
da kalaman soyayya dadada
2nda Allah ya halicce taba a taba yi mata
kyautar kudi mai dimbin yawa ba irin
wannan,dadin dadawa kyautar daga wajen
masoyinta ne. Ta gama karanata katin, saita
rungume shi a kirjinta, tace Allah srk
likitana. Kai Allah kaine abun godiya ngd
maka. Ummi tazo ta nanikewa af,tace,cafdi
dk wannan himilin kudin,ke ya bawa?
Daman ance ana yin asirin bada kudi sai
kaga mu2m yanayi maka kyauta ba a
hayyacinsa ba,irinsa nake so a yiwa yasar.
Dn Allah farida ki raka ni wajen
malaminki,kinga tsakaninmu dake babu
boye-boye. Takaicin abn data ke fada da
warin dattin bakinta,dana 'yarta ne suka
addabi af,taji kmr zata yi amai,tmkr
xuciyarta zata hautsuno ya fito waje. Ta
daga ido tana kallon ummi dn takaici ta
kasa ce mata komai. Ta mike tsaye ta daga
labulen kofa dn iska ta shigo,ta kade kauri
da karnin da dakin ya kidime. Ta wuce taje
kwandon kayan wanke wanke ta dauko
kwano da kofi ta zubo mata abnci da ruwan
sha ta kawo mata. Taga alamar yunwa
sukeji daga ita har 'yarta. Tana kawo musu
suka hau ci hannu baka hannu kwarya tmkr
wadanda suka kai azumi a lkcn rani. Af ta
koma gefe taci gaba ga rangadawa
masoyinta sakon gdy a cikin wayarta,ta
tuttura masa. Ummi zata sake yi mata
maganr bokaye af ta dakatr da ita da
hannu. Tace ummi dn Allah kici abincinki
kiyi shiru,kada ki kware idan kin gama kya
yi mun tatsuniyar. Ummi ta maimaita,
tatsuniya kuma?
DUK KYAN TAKALMI 3* 6
Af tace,ai gara ma tatsuniya,yara suna
karuwa sbd dk tatsuniya gargadi ce,amma
wannan lbrn naki gara in saurari kidan
garaya da in cigaba da sauraronki.allah ya
shrye ki ummi. Ummi ta koma ta zauna tayi
kulas tana ci tana gyada kai tana fadi a
ranta,lallai dan adam, wulakanci aisha umar
zatayi min dk irin halaccin danayi mata na
rakata inda aka jawo mata hnklnsa yazo
yana sonta,har yake cusa mata kudi,shine
na zama abar kyara a wajenta? Da ummi da
'yarta suka gama con abinci aisha farida ta
kwashe kwanunkan ta dawo ta zauna, ta
dubi ummi wacce 2ni alamomin bacin rai
sun bayyana fskrta. Af tace, ummi yaya su
hjyrki? Ta tabe baki tace, suna na kalau.
Keda naki sake nemana ba 2n ranar da
muka rabu dake daga gidan malam. Ai kya
zo kice min wannan bukata ta samu kiyi
min godiya. Amma shiru babu ke babu
labari. Koda yake ba zaki zoba dn kin fara
samun daula,gashi harda waya a hannu kina
daddannawa ai dole ki guje ni.af tayi
mrmshn krfn hali tace, naje nemanki mana
na tarar ba kya gidanki,facalarki tace an
sake ki. Har kinyi rshn m2mci kala2 kince
asiri sukayi miki ke ma saikin ga bayansu.
Haba ummi me yake damunki ne,kina abu
kmr baki taba shiga aji ba?
Ummi ta fusata tace, dole mana kice
haka,ai ke aiki yaci ni da baici ba sai in
zauna in zura ido? Kina ganin har yassar
yayi aurensa yaki ya mayar dani ko ganina
baya son yi. Af tace, yayi min dai-dai gsky
ba dn kin tako kinzo gidanmu ba har aba
bana son ganinki,kuma koda kuskure bazan
kara taka gidanku ba. Sbd kin kusa halaka
ni,kin tozarta ni duniya da lahira. Ke ba
kawar kirki bace ummi,dk mai yawo dake
ma sai ya halaka. Ummi ta fusata tace, to
naji kuma dk wulakancin da kika yimin nina
tako nazo gidanku, dk ranar da kika ganni a
gidanku kiiyi min dk wulakancin da kika ga
dama. Ta zabura zata mike af ta riketa ta
mayar da ita ta zaunar. Tace, yo hkr gsky
nakeso na fada miki,ita kuwa gsky daci
gareta. Ummi,fada miki ne ban yi ba amma
jana gidan boka da kikaui kika zuga ni na
ranto kudi,kin jawo min bakar masifa a
rayuwata. Aikinsa bai min amfanin komai
ba,har kulle ni akayi a ofoshin 'yansanda
sbd wannan kudi,shi kuwa wanda akayi min
asirin dn yasoni saima ya sake tsanata.
Ummi bazan boye miki ba saida nayi kuka
da hawayena,nayi allah wadai da halayenki.
Ni mai yafiya ce, na yafe miki,amma fa kin
cuceni. Ummi ta harari af tace me kike so
kice min bayan nan kin samu,gashi nan yazo
wajenki? Af ta soko mata tata harara tace
har yanzu baki saduda bako, ba zaki daina
gasgata karairayin 'yan danfara bako? To
bari na fada miki wannan mu2min da kika
kaini wajensa macuci ne,kema kinsan da
haka,tawada ce ya zuba a ruwa ya bamu sai
laya aka rubuta alifun,ba'un da sauransu
tsabar ya mayar damu jahilai. Ke bari ma
na baki labarin dk abnda ya faru bayan
rabuwata dake. Kinci sa'a anti abida bata
nan, da yau saita wanke ki,sbd taki jinin
taga mace mai bin bokaye. Habba ummi
yanzu mai bin boka ya kara miki,kin kadar
da dk abnda kika mallaka a duniya kina
yawo a cikin tsumma keda 'yarki ko wanka
babu. Mai yassar zaiyi dake a haka kmr
tababbiya? Ai har abada ba zaki ga dai'dai
ba idan dai baki daina bin bokaye ba. Ummi
da nayi istigifari na mayr da gaba daya
lamurana wajen Allah a saukake. Ya kawo
min dr s cikin kwanciyar hnkl. Ina ma zaki
bi hanyar dana bi dakin samu yassar cikin
sauki ba tareda kin kashe ko sisi ba. Da
rayuwarki ta gyaru duniya da lahira,hnkli ya
kwanta,kin fita daga talauci dacin bashi.
Ummi tayi sororo da alama jikinta yayi
sanyi,ta fada cike da sanyin jiki. Aisha umar
fada min yadda kika yi. Af ta gyara zama ta
bawa ummi labarin dk abnda ya faru da
ita,2n daga ranar da suka rabu da ita,har
izuwa rana irin tayau. Ummi ta buga tagumi
tana sauraron af daga dukkan alamu tana
gasgata nasihohinta. Da af takai aya,sai
ummi tayi ajyr zuciya. Tace,aisha umar kinyi
gsky,to yanzu meye shawararki? Ta ina zan
fara? Af tayi dry tace, ta inda na fara zaki
fara,kum kema ki riki wadannan matakai
biyar da abida tabani, ki riki kissar malamai
nan da yasa matar na ta debo masa nonon
bauna. Ki rabu da bin 'yan tsibbu ba sai
wani ya fada miki ba,kema kin san babu
riba. Ummi ta sharce hawaye tace, gsky ne,
nima ina tsoron haduwata da
ubangiji,sannan ga sunanan ya baci a garin
nan dk wanda ya danni,yasan ina bin
bokaye,har da 'yan ina da kare nake bi.
Yanzu yaya zanyi aisha umar? Saita rushe
da kuka. Af tace, laifin da kikayi tsakaninki
da ubangiji zai yafe miki,idan kika tuba.
Laifin da kikayi wa wani ne Allah bazai yafe
miki ba saikin je kin nemi gafarar wadanda
kika yiwa laifin. Wannan shine mataki na
farko da zaki fara takawa. Kiyi ta istgifari da
lahaula kiyi ta addu'a akan Allah ya juyo
miki da hnklin yassar ya dawo gareki. Abu
na biyu ki zamo mai tsananin hkr, karki ga
idan kinga an sami jinkiri,bai kuyo gareki
bada wuri. Na 3 ki kama mu2ncinki,kija
ajinki kada ki sake binsa ko waninsa kina
rokonsa ya mayr dake. Idan kika rike guda
ukun nan zaki ga yadda Allah zai yi dake.
Ummi ta zauna shiru tana 2nani,ta kasa
cewa komai,canta dago ta dubi af. Tace,
yassar fa ya tsaneni, ya tsani ya ganni ko a
hanya. Sai naje nayi masa hayaniya nema
yake aiko min da dubu 1 ko 2 a wata na
abincin 'yarsa. Af tace,to saime? Bake kika
jawa kanki ba? Ai halin mu2m ke sawa a
tsane shi,ki gyara halinki ki gani idan baiso
kiba. Ki dinga wanka kina tsaftace jikinki
dana 'yarki,ki rage magana barkatai da
yawo a gari,ki zauna a gidanku ki riki sallah
da zumi da lazimi,kina ta addu'a kiga yadda
Allah zai sauya ki. Ummi tace, insha Allahu
zanyi duk yadda kik ce min, yanzu ma daga
nan gidan sirikata zanje na nemi gafararta
da facalata dashi kansa yasar din,nace
kuskure nayi dana biyewa zancen malamai.
Sai in koma gida in zauna in daina yawo in
dinga sana'a ina biya dimbin bashin dake
kaina. Aisha umar ngd,madalla sai kin ganni
kuma. Ta tashi ta dauko 'yarta ta goya a
baya,jikinta sanyi kalau. Af ta bude jakar
kayanta ta tsinto mata atamfofi kala biyu
tsofaffi ta bata,ta sake zaro nairi dubu 1
daga cikin kudin da dr s yabata ta hada
mata. Sai gdy ummi keyi tana murna. Ta
rakata har bakin titi ta hau acaba ta tafi. Af
ta dawo gida cike da tausayin kawarta mayi
mata addu'ar Allah ya shirye ta, Allah ya sa
abunda take fada a bakinta ya shiga har
cikin zuciyarta ASUBA TAGARI UMMIN
YASIR
BABI NA GOMA SHA SHIDA Yaya husainai
ne yaketa shige da fice tsakanin dakinsa
zuwa kfr dakin 2n kafin gari ya karasa
wayewa. Da duku-duku af ta tashi dn tayi
sallah ta kuma kai yara fitsari kasancewar
lahadi ce babu mkrnta,in yaso bayan sunyi
sallah saisu koma suci gaba da bacci. Tayi
mamaki da ganin y.h a tsakar gida yana
tsaye cak kmr mai 2nani. Mamakinta ya
sake karuwa alkcn data fito daga bandaki
har tayi alwalla bai koma daki ba,dai kai
kawo yake tayi tsakanin dakinsa zuwa
zaure. Ya shiga ya fita. Bayan tayi sallah
yaran dk sunyi sallah,saita sake kwantar
dasu sannan tayi wuf! Ta fito dn taga y.h
yana nan? Ta iske shi a tsaye daf da kfr
dakinta ya sakale hannayensa a bayansa ya
sunkuyar dakai kasa kmr mai 2nani. Saita
dafe kirji dn bugawar da zuciyarta keyi.
Yaya lfy? Ta tmbyeshi. Ya dago jajayen
idanuwansa ya dubeta da kyar ya iya bude
bakinsa yace,lfy? Ta tsaya a jkin kofa tana
kallonsa babu abnda zuciyarta bata aiyana
mata akan abida ba. Tasan tabbas wannan
damuwar tasa tana da alaka da abida. Yace,
aisha yaushe ne zaa yiwa yara hu2n
mkrnta? Muryarta na rawa tace, gobe litinin
zasu fara jarabawa, ranar juma'ar kuma za a
yi musu hutu. Lafiya? Sai yayi shiru, can ya
dago sai taga idanuwansa sharkab da
hawaye, yace, ina ganin su hkra da
jarabawar ki hada muku kayanku mu tafi
shagamu yanzu. Ta sulale ta durkusa ta
dora hannu aka ta fasa kuka mai tsananin
sauti da gigitar da mai sauraro. Tace,
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Wayyo Allah
anti abida,wayyo antina, Allah ya
jikanki,Allah yayi miki gafara. Sai y.h ya
fisgota ya toshe mata baki ya grgza ta fadi
yace, rufe min baki,waye yace miki abida ta
mu2? Kan kace kwabo yaran abida suma
sun fito daga daki da gudu,suna kuka.
Mutanen gidan yaransu da manya,maza da
mata sun firfito a gigice suna tmbyrsu ko
lfy? Af dai bata ji bata gani,ba kuma ta gane
dk abubuwan da jama'ar da suka taru
akanta suke fada ba. Kuka take,faduwa
take ana riketa bata kakkautawa. Abida
bata mutu ba. Kalmar da y.husaini keta
ambato,amma fa shima din kuka yake yi
haikan. Mutanen gida maza da mata sai
suma suka dinga hawaye dn tausayawa su
AF. Af ki hada kayanku a babbar jaka da dk
wani abu mai amfani ki shiga dakina ki
harhada kayana dana abida kakaf gara mu
kaura shagamu meyi jinyarta 2nda har
yanzu bata warke ba,ni bance miki ta mutu
na. Bari naje na nemo mana tasi wacce zata
kaimu tasha. Ba dn ma tfyr ba ta shiri bace,
aida motar ofis zan aro in zuba mai mu da
kayan mu kakaf mu tafi, to ba shiri. Af ta
tsh tsaye daga kasan datake burgima jikinta
yayi bududud yayin da fskrta ta hadu ta
damule,bayan hawaye da yayi face-
face,idanuwan da fskr dk sun kumbura
luhu-luhu. Ta kade jikinta ta dubi yayanta
tace,yaya ina da magana dakai. Saita suce
daki, ya biyo ta a baya. Ta jawo jkrta ta
binciki,sai ta damko himilin kudi ta mika
masa har naira dubu goma sha takwas. Ya
karba cike da mamaki ya tmby,af waye ya
baki wadannan makudan kudi? Ta matse
hawaye tace, dr s ne ya bani dubu ashirin
wancan satin da yazo. Ya kalmashe ya zura
a aljihu yace,ki nutsu ki hada muku kayanku
a tsanake ni bance miki abida ta mu2 ba.
Ta fashe da kuka tace,haba yaya nima fa
musulma ce,kuma mai hnkli nasan
tawakkali. A gabana babana ya mutu ba a
dade ba uwata ta mutu,me yasa zaka boye
min mu2war abida? Yace,ni dai bance miki
ta mu2 ba. Ya ficce yabarta a drksh ta jawo
wayarta da sauri ta kira lmbr goggo
mahaifiyar abida taji a kashe. Ta kira
lambobin mutanen gdnsu har su 3 babu
mutum 1 data samu,dk sun kashe waya.
Wannan ya tabbatar mat abida ta rasu.
Saita kira kanwarta munawwara a lagos taji
muryar knwrta rangadau cikin fara'a take
magana. Af cikin kuka tace,baku da labarn
mu2war abida ne? Sai taji munauwara ta
kwalla ihu ta wurgar da wayar tana salati.
Aisha farisa ta tabbata lbrn mu2war bai isa
garesu ba. Ta kira yaya yahya sai tci sa'a
bugu daya ta shiga,nan da nan ya amsa. Ta
rushe da kuka,tace, yaya ka fada min
gsky,abida ta rasu ko. Hello,hello kawai
yake cewa,kasancewar yana cikin hayaniya
baya jinta. Yace aisha zan kiraki bana jinki.
Saiya katse wayar. Ta mimmike kafa ta ske
bude wani sabon shafin kuka. Kukan dako a
mu2wa iyayenta batayi irinsa ba. Bata
manta da ambaton innalillahi wainna ilaihi
rajiun ba. Babu anda tafi 2nawa sai irin
gudunmuwar da abida ta bata wajen yakin
neman soyayyar dr s. Allahu akbar,allah mai
yadda yaso,ga dr shuraim ya samu ita kuma
ta tafi. Tace a ranta, tabbas rabuwa da dr s
shine kwanciyar hankalina 2nsa babu abida,
muddin na kasance da shuraim babban
fami zai dinga yimin ina tunowa da ita.
matan gida suka biyo ta daki suka zagayeta
suna bata naki, su ma sun shiga rudani
kasancewar husaini yace bata mutu, to idan
bata mutu ba mai yasa xai tashi tfy a yau,
gashi kuma yana rusa kuka shima uwani ta
matse hawaye, tace AF tashi ki hada muku
kayan kafin yayanki ya dawo don ya tafi ya
samo mota" AF ta girgixa kai , tace"baxan
iya ba ku kyaleni kawai" taci gaba da rusa
kuka baji ba gani. nan matan gida suka
shiga hada musu kayayyakinsu suna durawa
a jakunkuna da buhuhunan kama daga
kayan sawarsu takalmansu da kwanukansu.
faruk ne yake ta jawo akwatinan mamansu
da babansu daga cikin dakinsu yana fitowa
dashi tsakar gida,matan suna ta harhadawa.
himilin kaya dauri dauri aka kawo zaure aka
himila, katifu ne kawai basu dauka ba
amma babu abinda ba'a harhada ba. ha
yanzu AF na zaune a daki ta hada kai da
gwuiwa, kukan da takeyi yaki ya kafe sai ita
tasan abinda takeji a cikin zuciyarta,
kuna ,suya da tafarfasa duk sun tabbata a
kirjinta. ta fada a baiyane" Abida.....abida
mutunce. muyane nagari basu cika dadewa
a duniya ba. sai yanzu na cika marainiya
nayi rashin yar uwata garkuwar jikina. dama
in mutu a yau in huta da takaici rayuwa.
bani da sauran farin ciki a rayuwata
kuma....
U.khairi ta rushe da kuka ta durkusa a
gaban af tace,ki yafe min, abida ta yafe
mana abubuwan da muka dinga yi muku a
zamanmu daku a gidan nan,hakika mun
zalunce ku,kullum muna cikin gulmarku,yi
muku kazafi,makirci kala2 ku baku sani ba.
Allah ya jikan abida mace mai hkr,sai a
zageta a gabnta ta juyo t kallemu tayi
mrmshi ta wuce ba zata rama ba,kuma
bazata tabayin gaba damu ba. Ban san
abida idan ta tafi ba zata dawo ba, dana
nemi gfrarta a ranar da za tafi da ita.
Farida, ki yafe min koke ma idan kin tafi kin
tafi ba zaki sake dawowa kano ba. Tabbas
nice nayita hada makirci a wajen mahaifiyar
musbahu dn kada ya aureki. Laure,uwani
yaya ku kayi shiru bayan daku mukeyi musu
komai. Suma sai suka gyara zama sukace
haka ne farida ki yafe mana, mun zalunce
ku, mun zalunci kanmu. Zazzafan hawaye
ne ya dinga tsattsafowa daga idanuwanta.
Ta tsura musu ido tana kallonsu kawaita
kasa furta kalma 1 sbd tsananin data ke
ciki. Kalamansu tmkr ruwan wuta suke fesa
mata,saita daga hannu ta dakatar dasu.
Tace,ya isa, dn Allah kubar fada min, dk
nasan abunda yake frauwa,kuma abida ta
fada min komai. Naji abnda kukace,kuma
na yafe muku,na tabbatar abida ma ta yafe
muku,dn bata taba kwana da wani a ranta
ba.
Su dukka suka cigaba da koke. Muryar yaya
hussaini suka jiyo a zaure dashi da maza
suna ta jidar kaya a zaure ana kaiwa mota
ana lufgawa. Har sai da aka kwashe kayan
tatas ya leko dakin yace aisha farida da yara
su fito su tafi. Sai da su uwani suka daga ta
tsaye wannan tana taro mata zaninta zai
fadi, wannan tana gyara mata hijabi.
Takalmi silifas sai da aka tura kafarta a ciki
don ta manta yadda yake sawa saboda
tsabar kidimewa. Wayarta ce kawai a
hannunta don ko kofofin dakunan sai da
yaya hussaini ya datso, kanta tsaye ta fice
ba tare da ta iya waiwayowa baya ba. Bata
iya amsa adduoin ta'aziya da fatan Allah Ya
kiyaye hanyar da jama'ar gida da makota
suke yi mata ba. Tafiya take tamkar kwai ya
fashe mata a ciki. Bata ma san inda take
jefa kafarta ba, 'ya'yan abida na nanike da
ita, idan ta kalle su sai taji wani gagarumin
tashin hankali ya sake taso mata.
"Faridah!!" Tattausar murya taji a gefenta
don haka ta waiga da sauri. Musbahu ta
gani idanuwansa sharkab da hawaye, itama
sai hawaye ya fara kwaranyo mata. Tayi
sauri ta sunkuyar da kanta kasa ta dinga
tafiya wurin mota. Yace Allah Ya jikan abida,
naji ance kun kwashe kayan ku kakaf kun
kaura shagamu. Yanzu shikenan ba zan sake
ganinki ba? Ki sani har abada ba zan daina
sonki ba, babu yadda zanyi ne. Sai ta sake
rushewa da kuka, shima haka yana biye da
ita har ta shige mota ita da 'ya'yanta. Yaya
hussaini ya shiga gaba shi da direba, su
kuma a gidan baya. Kaya kuwa suna can
baya irin motar nan ce mai kama da na 'yan
sanda bayanata kamar a kori kura.
Cincirindon mutanen unguwa ne suka firfito
yara da manya, maza da mata suna ta daga
musu hannu har suka ja motar suka tafi.
Sabon kuka ne ya sake sarkewa aisha
farida. Sun fita daga kano kenan sai dr
shuraim ya kirata, da farko tayi kamar ba
zata dauka ba, sai dai ta daure ta amsa.
Magana yake cikin shaukin soyayya. My
love kin tashi kalau? Jiya kuma muna
magana sai kikayi bacci ki ka barni ko? Ta
runtse ido dan tsananin tashin hankali yayin
da hawaye ya dinga tsartuwa daga
idanunta. Bata iya bashi wannan amsar ba.
Yayi murmushi yace banji kinyi magana ba
tun dazu, ko baki jina ne? Tayi magana cikin
sansanyiyar murya tace dr muna hanyar
shagamu. Abida ce ta mutu. Innalillahi wa
inna ilaihir rajiun dr shuraim ya sake
maimaitawa har sau uku. Yayin da kuka ya
barke mata. Dai dai lokacin kuma yaya
hussaini ya hasala ya juyo a fusace ya fizge
wayar, ya murtsike ya kashe ya rufe ta
bambamin fada. Waye yace miki mutuwa
tayi har kike yadawa a waya? Wai ke wace
irin yarinya ce mara jin magana? Cikin kuka
tace haba yaya me yasa kake boye min
mutuwar anti abida? Ya ja dogon tsaki ya
girgiza kai ya juya ya cigaba da kallon haya,
ya saka wayar ta ta a aljihunsa. Dr shuraim
yayi ta gwada kiran aisha farida ji wayar a
kashe , sai hankalinsa ya kara tashi matuka.
Yasan duk inda take yanzu bata cikin
hayyacinta, kuka kuwa yau ko kogin maliya
sai haka. A gigice ya tashi zaune ya fizge
bargon da ya lulluba ya diro daga kan
gadonsa yafito falonsa ya zauna ya cigaba
da kiran wayarta a kashe.
Ya kira dr lukman shima har sau uk bai
amsa ba ,sai na hudun ne ya dauka yana
magana cikin magagin bacci. Dr shuraim ya
fada a dimauce, lukman ka wartsake daga
baccin nan ka saurareni. Farida ce take
cikin wani hali gashi kuma na rasa ta waya.
Ka kira yayanta yahaya umar ka tambaye
shi dan inji halin da take ciki. Dr lukman
yayi firgigit ya tashi zaune yace ban fahimce
ka ba, meya samu farida? Yace yanzu na
kira ta tana kuka ta shaida min suna hanyar
shagamu Allah Ya yiwa antinta abida
rasuwa, mara lafiyar nan. Dr lukman ya
zabura ya dauki doguwar salati yace kashe
wayar ina zuwa barin kira yahaya umar.
Bayan mintuna 15 dr lukman ya kira dr
shuraim yace ka kara hakuri dai zuwa
anjima don yanzu nayi ta kira ba dauka ba.
Daya dauka ma sai naji shi a cikin hayaniya
yake, yace na kashe zai kira ni anjima. Kaga
kenan suna makabarta ko wajen zaman
makoki. Dr shuraim ya dafe kai ya cije lebe
yace halinda farida zata shiga shine babbar
matsalata. Idan ka duba yadda kullum take
kuka saboda rashin lafiyar nan inaga idan ta
mutu? Lukman yaya za'ayi kenan? Dr
lukman yayi ajiyar zuciya yace babu abinda
sai dai muji ra zuwa anjima muji ta bakin
yayan nata tukunna. Nayi maka alkwari
yana kirana zan kiraka kaji halin da ake ciki.
Dr lukman yayi godiya suka kashe wayan.
Har yanzu kiran wayar aisha farida yake yi
taki shiga. Sai ya tuno yana da lambar yaya
hussaini don haka ya cire kunya ya kirashi.
Yaci sa'a kuwa yana kira ta shiga, nan da
nan yaya hussaini ya amsa. Ya ambaci
sunan shi tangararau dr shuraim ne? Caraf
aisha farida ta dago ta dubi yayanta. Dr
shuraim yace sannu yaya, ya akaji da
hakuri? Sai yaya hussaini ya gallawa aisha
farida harara yace af! Kai ma ta fada maka
anyi mutuwa ne? To wannan fadarta ne
kawai, ni dai nace ta shirya mu tafi shagamu
sai ta dau kuka da ihu.
Dr shuraim ya cika da mamaki kafin yace
wani abu yaya hussaini ya mikawa aisha
farida wayar. Tayi ajiyar zuciya tayi sallama
cike da sansanyar murya. Dr shuraim ya
fara magana cikin tattausar murya. Yace
farida meyasa kike da rudewa ne haka? Ga
yayanki yyace bai fada miki ta mutu ba. Ta
fashe da kuka tace haba dr nifa ba karamar
yarinya bace nagane komai, meyasa za'a
boye min? Ni nasan anty abida ta rasu, ko
an fada min me zanyi, dole in dangana.
Yaya hussaini ne ya sake yi mata tsawa yace
kada ya sake ji tayi maganar rasuwan nan.
Ta rushe da kuka mai tsanani, hankalin dr
shuraim ya sake tashi ya shiga damuwa,
yace yi shiru baby, kiyi hakuri duk mai rai
mamaci ne , dukkanmu nan zaman jiranta
mukeyi. Kiyi mata addua Allah Ya yi mata
rahama. Ki kunna wayarki mu dinga
magana. Tace wayar bata wajena yaya ya
karba ya kashe tundazu da muke magana.
Dr shuraim yayi yace to anjima zan kiraki a
wannan layin. Idan anyi bakwai zaku dawo
ko? Ta girgiza kai kamar tana gabanshi, ta
zubo da hawaye masu yawa. Tace dr
shuraim ina ganin wannan wayar da muke
da kai itace rana ta karshe da zaka a duniya
ballantana ka ganni. Kuka ya barke mata.
See Translation
 KYAN TAKALMI 3* 7
Yayi zumbur ya mike tsaye ya dafe kirji
yace farida me kike so ki fada min? Kina so
kice min zaki kashe kanki ne saboda anti
abida ta mutu? Ta girgiza kai tace bazan
kashe kaina ba, saboda nima musulma ce.
Rashin anti abida babban ciwo ne a zuciyata
wanda bazan taba warkewa ba har abada,
kuma duk sanda na ganka ko naji muryarka
zaka zama min fami a wannan ciwon nawa.
Ba lallai bane ka gane abin da nake nufi
yanzu ba, kuma ba zan iya fada maka yadda
zaka gane din ba. Ni kadai nasan abin da
nake nufi da hakan. A sanadiyyar anti abida
nasan ka, da ba zaka sanni ba ma balle ka
fara sona, nima haka ba donn yakin da tayi
ba da tuni na manta da shuraim a
rayuwata. Abida itace silar hada
soyayyarmu, naso ace abida na raye ta
ganmu tare. Ta mutu ba tare da burinta ya
cika ba, komai ya fita a raina tunda babu
abida. Ya daka mata tsawa domin ya gigice
gaba daya da jin kalamanta. Yace farida kin
kuwa san abinda kike fada min? Anya kuwa
kina cikkin hayyacinki? Ta fashe da kuka
tace nasan abinda nake fada likita. Nayi
sallama da kano ko hanya bana so ta biyo
dani ta kano , tunda babu abida. Kayi hakuri
ka yafe min, nasan irin ciwon da zaka ji a
zuciyarka saboda nina fara shiga ciwon so
kafin ka shiga. Sai ta mutsike wayar gaba
daya ta rike a hannunta ba tare da ta
mikawa yaya hussaini ba.
Ya juyo ya dube ta cike da mamaki ba tare
da yasan abinda zai fada mata ba. Dr
shuraim yayi ta gwadar wayar, ya kira yaji
an kashe mudik , sai ya sulale ya zauna
akan doguwar kujerar falonsa yana sosa kai.
Yace innalillahi waiinnna ilaihirajiun.
Meyake shirin faruwa dani ne? Dama
wannan shine cutar son da ake fada a gari?
Ashe ban taba sanin so ba sai yanzu?
Inama zan iya hakura da son farida in huta.
Ya jawo wayarsa a sanyaye ya kira dr
lukman. Cikin sanyin murya yace abokina
kazo muyi magana ka bani shawara , don
ina cikin masifa wacce zata iya kaini da
kamuwa da son zuciya. Farida tace in kyale
ta bazata iya cigaba da son ba saboda babu
ran abida. Dr lukman yayi tsaki yace
wannan ai shirme ne, zafin mutuwa ne ya
shige ta, zata dawo hayyacinta ta neme ka.
Dr shuraim ya girgiza kai yace a cikin
hayyacinta take magana ba zafin mutuwa
bane. Na kasa gane abin da suke nufi.
Yayanta yace min bata mutu ba, ita kuma
tace min abida ta mutu. Abin da na
fuskanta boye mata yake yi don yaga ta
damu. Ga shagamu da nisa kar ta sume
masa a hanya. Dr lukman yace nima na fi
yadda ta mutu don yanzu yahaya ya turo
min sako a waya ta yace inyi hakuri yana
cikin mutane zai kira ni anjima.
Dr shuraim yace idan ba zaka zo ba gani
nan zuwa gidan naka muyi shawarar, don
bansan yadda zan iya yini a cikin wannan
halin ba. Dr lukman yace naga ka damu da
yawa abokina, bari nayi wanka inzo tunda
gidanka babu kowa zaifi dadin magana. Dr
shuraim yace don Allah kazo da wuri ina
jiranka. Suka kashe waya. Dr shuraim ya
kame a zaune ko yatsarsa baya iya dagawa
balle ya tashi yayi wani abu. Shi kansa yana
tausayin kansa da kansa, halin da zai shiga
idan ya rasa aisha farida. Ya rasa yadda
akayi ya zurmuka cikin ramin kaunar ta
wanda yayi zurfin da ya kasa fitowa. Ya fada
a bayyane lallai karshen namiji a karkashin
mace yake. DUK KYAN TAKALMI a kafa ake
taka shi. Sai ya zubo da wani zazzafan
hawaye daga idanuwansa. TABBAS DUNIYA
RAWAR 'YAN MATA CE, NA GABA SAI YA
DAWO BAYA IDAN AKAYI WANI JUYIN.
ASUBA TA GARI LIKITAN AISHA FARIDA!!!
BABI NA GOMA SHA BAKWAI Mako guda
kenan dai-dai da tfyr su aisha misalin karfe
5 na yamma. Dandazon maza tsofaffi ne
suka cika a majalisar hirarsu ta 2ntuni,wato
kfr gdnsu aisha farida. Mahaifin abida shine
ya gaji kujerar tsohon af shine kadai yake
zaune akan kujera sauran dukka a zazzaune
suke akan tabarmi a gefensa. Af ita kadai
ce mace a cikinsu,tana zaune akan kujera,
sauran dukka a zazzaune suke akan tabarmi
a gefensa. Af ita kadaice mace a
cikinsu,tana zaune akan dakali ta lanqwashe
kafa,sanye take da bakr riga abaya ta yafa
dankwalin a kanta. Ta jima tana kallon
tsofaffin nan daya bayan daya,sai ta 2na da
a lkcn da mahifinta yake raye,mahaifin
abida ya juye shi sak! Kmrsu 1 a yanzu
shine babba a cikinsu. Tabbas abida da
mahifinta tayi kama sak! Sai taji hawaye ya
cika mata ido ta grgza kai dn tausayi. Tace a
ranta, Allah sarki, wata rana sai a shafe
kowa kmr ba a taba yin mu2m a doron
k'asa ba. Haka ake tfy daya byn daya. Baba
iliyasu ne ya dubi aisha farida yayi mrmshi
yace, kai girman dan mu2m babu wuya,
kmr ba 'yar yarinyar nan bace, 'yar karama
aisha, yanzu ga yadda ta girma. Af tayi dry
tace,kaima aika tsufa inda zaka san an dade
kenan. Sai suka hau hirar 2na baya,abun
tausayi a jajanta,abn dry a kyalkyace
Tsayuwar wata tsaleliyar mota baka mai
duhun gilashi ce ta katse hirar,sai hnklnsu
gaba daya ya koma kallon motar. Mazaje 4
ne suka bude kofofin moyar guda 4 suka
fito. Af ta cika da tsananin mamakin data
kasa boyewa,sai cimak ta mike tsaye, yayin
da aka hau kallom-kallo a tsakaninsu. Dr s,
Dr Lk, Dr Dayyab da yahya umar ne suka
nufo inda su af suke. Suna isowa sai su
duka suka zube a gaban tsofaffi suka kwashi
gaisuwa. Nan da nan suka matsa musu waje
suka umarce su dasu hawo kan tabarma su
zauna sosai.
Bayan kowannensu ya zauna sai af ta
durkusa ta gaishe su ckn sanyayyar murya.
A lkc guda suka amsa, yayinda Dr S ya kafa
mata ido yana kallonta, ko ba a fada ba
ansan yayi kewarta,sati guda kenan bai
ganta ba. Cikkin kunya kanta a sunkuye a
kasa ta yunkura zata tsh ta shige gida.
Yahya umar yace ta daawo ta zauna zaiyi
magana. Sai taji zuciyarta ta harba, a ckn
ranta ta hau addu'a ALlah yasa alkhairi zai
fada. Numfashinta ya fara cikewa,yayin da
da babu abnda tafi bukat irin ta shige gida
kada ayi maganar nan a gabanta,tasan
koma dai me za a ce ya shafe ta. Ta fada
cikin ladabi,ruwan sha zan kawo muku.
Yahya yace munan ea kika ganmu a koshe
muke,su kuma basa shan ruwan randa irin
naki, sunada ruwansu na rba a mota. Sai
dukkansu sukayindariya. Af ta dawo jikin
dakali ta rabe kmr marar gsky. Ahya
yagyara zama ya dubi tsofaffin yace, baba,
wadannan gudaukun da kuke gani baki
netun daga kano,kuma gaba dayansu likitoci
ne a asibitin aminu kano. Sai tsofaffin
sukasuka hautsine da maganasuna cea,
likita bokayen turesai,ai da ga gani babu
tmby gasu nan a nutse kowanne cikin
kyakkyawan shiga. Wasu shaddoji ne suka
saka masu kyau,kowacce tsasaddiya ce sai
daukan ido takeyi. Farare sol sol anyi musu
dinkin surfani dinkin boda,rigar iya gwiwa.
Su shuraim dai dry kawai sukeyi. Yahya ya
cigaba da byani,ya nuna DR LK yace
wannan sunansa dr lk, babban abokina ne
tun. Una yara a yobe tare mukayi
sakandire. Ya nunaDR S yace ga shuraim
babban liktan fatar da akeji dashi a kano
shima aminin lukman ne, kuma shine yake
so r AIsha FArida. Sai gaba daya suka juyo
suna suka dubeta,tayi sauri. Ta sunkuyar
kkasa yayi akwakalra tsg aito m da y
yanaa,tmakr lma. Tana tmbyr zuciyarta
''ANya kuwaa mafarki nakeyi ba,yau
shuraim ne ya fara mgnr aure na. Allah mai
ikobabu abndaya gagari ubangiji.
Dr shuraiam har yanxxu kallon aishaa f
yakeyi kasa kasa yana soyaga yanayinta da
taji mgnr aurensu. Ya fusknci ta cika da
mamkikuma yaga annuri a fskrta yya karu,
dn haka ya sake csamun kwari. Gwiwar
tana sonsa. Tsofafi sai suka shiga jan
dogayen addu'oi. B.Sule ya dubi farida
yace,ja'ira ashe kin ruso miji kyakkyawa daa
kano haka kikeboyewa. Yanzun nan ika
gama cewa bakidasaurayi. Sai su dukka
suka tintsire da dry,harda ita. Yahya umar
ya nuna dayyan yazxe,wannan sunansa DR
Dayyabu shima a sibitin m. Aminu kano
yake aiki sunaji dashi ko kuma ma ince a
arewa anaji dashi. Reumatologist ne,likitan
daya shafi ciwon cikin kashi da jijyoyi. Shine
likitan daya shafi ciwon abida,dn haka nema
suka tzho dashi. Sai gaba daya suka zabura
suna kalonsa,musamman ma aisha f.
Mahaifin abida ya grgza kai, yace, ciwon
abidaaiba naasibiti bane kada ma ku
wahalar da kanku. Dr lk yayi gyarsan murya
yace, baba ni babu waniciwo da za'a ce
babu maganinsa a asibiti. Kada ku hana shi
gwadawa,abunda ya karanata kenan,aikinsa
ne shiyasa muka tahho dashia. Baban
abidaya grgza kai yaxe, me likta zaiyi mata,
yarinyar da htta gashin knta ya kde
dukka,kan nan kmr anyi mata kwal-kwal,I
wannan aikin kowa yasan iska ne.
KYAN TAKALMI 3* 8
Dr dayyabu yayi murmushi yace ciwon ya
gaji haka, yana zubar da gashi, yana saka
ciwon ido, yana sa mutum yayi ta zabura,
kuma da kumburin gabobi, wani lokacin da
yawan jin sanyi. Idan ciwon ya tsananta zai
iya taba dukkan kayan cikinta kamar koda,
zuciya, mahaifa da kuma kurajen baki. Allah
dai Ya kiyaye. Nan da nan tsofaffi suka fara
gamsuwa da bayanan dr dayyabu, domin ya
zano duk abubuwan da abida take ciki. Ya
kara da cewa kurajen suna iya feso mata a
kirjinta, baya, wuya, da kuma fuskarta. Na
fuskar zai zagaye kumtunta da kuma kan
hancinta. Zai yi siffar malam buda mana
littafi a turance muna kiransa butterfly
rashes. Aisha farida ta dafe kirji tace likita
wannan wane irin ciwo ne? Yaya sunan
ciwon? Kuma me yake kawo shi? Dr
dayyabu yayi dariya har sai da kyakkyawar
wushiryarsa ta bayyana. Ya girgiza kai yace
bazan iya tantancewa ko me yake damunta
ba har sai anyi gwaji. Gwajin ciwon kuma
ba a yinsa a kasar nan, sai a south africa ko
a beiruit. Aisha farida ta dafe kirji yayin da
kake iya ganin gigicewa a fuskarta. Tace
likita yanzu dai sai an kaita can sannan a
gano ciwon? Sai ta fara hawaye saboda
tunawa da tayi basu da wannan gatan.
Dr shuraim yayi sauri yace kada ki fara koke
koken nan. In Sha Allah komai yazo karshe
tunda kika ganmu da likita. Sai ki shekara a
AKTH baki samu damar ganinsa ba, amma
gashi mun kawo muku shi har gida. Kuma
zaiyi mata duk abin da ya kamata har sai ta
ji sauki in sha Allah. Dr dayyabu ya girgiza
kai yace ba sai an dauke ta an kai ta south
africa ba, za dai mu tura jininta wani lab a
abj su zasu aika jinin can idan anyi gwajin
sai su turo mana da sakamakon online.
Idan na duba sai in tantance takamaimain
matsalarta, sai in bata magani. Amma
bayan wancan gwajin mu ma anan akwai
gwaje gwajen da zamuyi mata kala kala
muga ko akwai matsala a cikin jikinta kamar
su koda, zuciya, hanta da dai sauransu.
Kowa yayi tagumi yana kallon bakin dr
dayyabu zuciyarsu cike da fargaba da
tausayin abida. Yayi murmushi yace kada
ku damu, ba wani abu bane na daban.
Anayi kuma ana warkewa sai dai don masu
irin ciwon basu da yawa ne a duniya. Yaya
hussaini ne ya fito daga cikin gida, baba
ahmadu yace yawwa hussaini zo ka zauna
kaji da kunnenka, likitoci ne suka zo daga
kano suna bayani akan ciwon matarka. Yaya
hussaini cike da mamaki yake kallonsu, bai
san sauran biyun ba amma ya gane dr
shuraim. Yazo ya mimmika musu hannu
suka gaisa, ya samu waje ya zauna ya
cigaba da sauraron bayanin dr dayyabu. Dr
dayyabu yace daga yadda yahaya umar ya
min bayani yadda ciwon nata yake yayi min
kama da Systemic lupus erythramatosis
(SLE). Sai kowa ya gyara zama suka mika
tunaninsu gaba daya kan likita dayyabu.
Yaya hussaini yace me kenan? Me yake
kawo ciwon? Dr dayyabu ya lankwashe kafa
yace SLE ciwo ne wanda yake samuwa jikin
wanda Allah Ya dorawa. Lupus is an auto
immune disease characterised by acute and
chronic inflammation of various tissues of
the body. Auto immune disease are illness
that occur when the body tissues are
attacked by its own immune system.
Bansan yadda zan fassara muku ba, amma
dai ba a gado, kuma ba'a daukar ciwon.
Ciwon yafi ga 'yan america bakaken fata
(africam americans) da kuma 'yan chinese
da japanese. Anfi samun SLE a jikin mata
fiye da jikin maza. Kuma yafi kama masu
shekaru ashirin zuwa arbain da biyar.
Malam ahmadu yayi dariya yace likita bokan
turai, ai ni wannan bayanin naka kamar
tatsuniya nake ji, mu nan 'yan chinese ne
da zai zo ya kama 'yarmu? Ai ciwon abida
sammu ne, daman ance tana da makiya a
kanon nan, musamman da awararta tafi
kowacce dadi suka jefe ta. Aisha farida ta
girgiza kai tace a'a baba ahmadu, ka bari ku
bari ya bata magani. Yau wata nawa kuke
yin na sammun amma babu alamar sauki
sai ma ciwon gaba yake ci. Yahaya yace
gaskiya fa tunda yazo a dakatar da duk wani
hayaki a zuba masa ido. Da yawa daga cikin
tsofaffin suka kushe maganin asibitin har da
mahaifin abida. Kadan ne suka goya bayan
likita. Daga karshe yaya hussaini yayi
magana yace ya yadda likita yazo ya duba
abida ko Allah zai sa a dace. Gidan su abida
da gidan su aisha farida babu nisa, don haka
aisha farida, hussaini, yahaya, da likitocin
guda 3 suka dunguma gidan su abida. A
zauren gidan aka iskesu an daukota tamkar
tsumma , wata mata mai maganin gargijiya
ta shafe jikinta sharkab da man shanu ta
tilo mata itatuwa a leda tace ayi ta jika
mata a sabuwar kwarya. Hankalin likitocin
ya tashi da ganin irin wannan kwabe
kwaben. Yaya hussaini yayi wa surukarsa
bayanin likitocin, tashin farko taki
amincewa ita da mata mai magani, tace
ba'a hada aikinta da na asibiti. Yaya
hussaini dai ya takura sai likitoci sun duba
matarsa. Mahaifiyar abida da mata mai
magani suka yi fushi suka bar wurin a
fusace daya ta shiga gida, mai magani ta
fice dauke da buhunta a kai.
Hakika abida tana jin jiki matuka, kamar ba
ita ba, gaba daya halittarta ta sauya, yanzu
ko magana bata iya yi saboda azaba. Sai
gyada kai, sai hawaye kawai zaka ga yana
zuba saboda tsananin wahalar da take sha.
Aka kawo musu tabarmi suka zazzauna
yayin da dogon turanci ya hautsine tsakanin
likitocin uku, likitan fata, likitan kwakwalwa
da likitan kashi da jijiyoyi. Dr dayyabu ya
bude jakarsa (brief case) ya jawo allurar
intramuscular injection wacce ake kira
dexamethasone 8mg start. Ya umurci aisha
farida tazo ta juya masa ita. Yayi mata
allurar sannan ya debo wasu magungunan
kala kala har kala biyar ya mika ma
maigidanta yace lallai a dinga bata
magungunan nan, kuma akan lokaci har
tsawon sati biyu za aga canji In sha Allah
kafin a gama gwaje gwajen jininta, idan an
gama tantance takamaiman ciwon. Dr
dayyabu ya dubi aisha farida yace matso
kusa nayi miki bayanin yadda za a dinga
bata maganin. Ga prednisole nan ta sha
kullum guda uku HOQ daya da safe, daya
da dare, calcium kuma kullum tasha daya.
Sai kuma methothroxate ranar asabar zata
sha 10ml. Ranar lahadi kuma ki bata folic
acid guda 2. Yanzu zan dauki jininta kashi
kashi in tafi dashi, wasu a kano zamuyi
gwajin wasu kuma a abj zamu aika lab suna
harhada jinin mutane da yawa, su tashi
mutum a kai south africa a gwada. Yaya
hussaini ya langabar da kai yace nawa ne
kudin maganin? Kuma nawa ne zamu bada
na wannan gwaje gwajen naji har da wanda
za aika kasar waje. Dr dayyabu yayi
murmushi ya girgiza kai yace kada ka damu
da wannan, abokina shuraim ya gama
shirya komai. Dan yanzu ma lagos zanje in
hau jirgi cikin dare in isa abj in bada
wannan jinin, kwana goma zaiyi sannan ya
fito, to sauran gwaje gwajen ma sai inyi a
national hospital abuja don yawo da jini
babu dadi, duk dr shuraim zai biya. Gwajin
jinin wanda za'a aika south africa ma dubu
sittin za a biya, yace shi zai biya.
Sai aisha farida ta fara hawaye haka itama
abida hawaye ya fara kwaranyo daga
idanuwanta dan tana jin duk abin da ake
cewa. Yaya hussaini ya hau godiya yana shi
albarka. Dr dayyabu ya zaro sirinji da
kwalabe ya zuzzuki jinin abida ya ciccika. Ya
dauko wata 'yar akwati ya jera su ya mayar
ya rufe. Suka mike suna yiwa abida sannu
da fatan Allah Ya bata lafiya. Aisha farida da
yaya hussaini ne suka kinkimi abida suka
shiga da ita cikin gida. A take yaya hussaini
yace aisha farida ta dibo ruwa ya bata
magani, bayan ya bata ta sha sai yace aisha
farida ta boye maganin a wurinta. Sanda
zata sha tazo ta bata kada ta barsu a fili
goggo ta zubar dan bata yadda da maganin
asibiti ba. Yaya hussaini ne kadai ya dawo
wurin su dr shuraim suka dunguma zuwa
kofar gidan su aisha farida wajen tsofaFfi.
Babu abinda yaya hussaini da yahaya umar
sukeyi sai godiya da shi albarka. Yaya
hussaini ya yiwa tsofaffin bayanin duk
abubuwann da ya faru da irin zunzurutun
kudin da dr shuraim ya kashe da wanda zai
kashe nan gaba. Sai suka kacame da yi
masa godiya da shi albarka, shi da
abokansa sauran likitoci.
Hussaini ya gyara zama ya dubi tsofaffin
nan ya nuna shuraim yace shine mai son
farida, da farko naki amincewa saboda ko
ba a fada ba shi ba sa'an aurenta bane, mu
talakawa ne kuma baki. Toh a haka muka
rabu. Yahaya umar yace kayi kuskure
hussaini tunda kayi wannan tunanin, ai
al'amarin soyayya ba a ayin ta don kudi, shi
ya ganta yana so, itama tana sonsa kayi
garaje da ka tarki raba su. Ba 'asan inda
rana zata fadi ba, haka baka san wanda zai
yi maka amfani a rayuwa ba. Ga shi dai
yanzu ya taimake mu a lokacin da bamu
zata ba, kuma bamu da matsayin samun
wannan. Dr lukman ya fada min komai
daga haduwarsu har zuwa tahowar aisha
farida. Naji ra'ayin shuraim akanta alkhairi
ne kuma aurenta yake so yayi. Yanzu
wannan tahowar da sukayi sunzo dan su
duba abida su bata magani kuma su nemi
auren farida ayi magana daya. Hussaini
ance ka kauro gida kacokan zaka bar aiki, to
zamanka a shagamu ba zai yiwu ba, ko ba
dan aisha da shuraim ba, kuma ba dan
karatun 'ya'yanka ba , don lafiyar matarka
da rufin asirinka aikinka sai ka koma kano
don abida yanzu dole ta kasance kusa da
likitanta dr dayyabu yawan yawan bincikar
lafiyarta. Yaya hussaini yayi shiru yana
gyada kai don ya gasgata maganar yayansa.
Can ya dago ya dubi yahaya yace tabbas ka
fadi gaskiya, dama ni ban gama tsayar da
shawarrar barin aikin ba, na dauko hutu ne
na shekara. A cikin hutun ne dama nake so
naga yadda halin zaman namu a shagamu
zai kasance idan na samu abinyi sai in
zauna. Idan ban samu ba in koma kano
iyalina in barsu a nan. Yahaya yace to
iyalinka ne ma zaman a kano ya kamasu
saboda lafiyar matarka, wannan likitan da
kake gani babu inda zakaje a kasar nan ka
samu iirinshi , su biyu ne kadai
rheumatologists , daya na kudu shi yana
arewa. Saboda masu irin ciwon basuyi yawa
ba. Saboda haka hutunka na karewa ko bai
kare ba ka hada su ku koma dan naji yace
sati biyu zai gama hada sakamakon gwaje
gwajen sannan ya gano kan ciwon. Yaya
hussaini fadi yake gaskiya in sha Allahu
zamu koma nagode.
Tsofaffi ma suna bayan yahaya, shawara
suka ci gaba da bawa hussaini su hada su
koma kano. Dr lukman ya gyara zama yace
toh mu dai yanzu munzo a shirye tafi da
gidanka mukayi, ma'ana muna neman
auren aisha farida. Yahaya ya dubi tsofaffi
yace toh me za a jira tunda gaku kacokan
kun hallara? Mutumin nan sananne ne
tunda ga lukman nasan gidansu yasan
gidanmu. Farida na son shuraim shima yana
so, ayi magana kawai. Dr shuraim ya
sunkuyar da kai kasa yace saboda rashin
lafiyar nan ne ta abida bamu san yadda
zamu tarar da jikin bane yasa bamu taho da
iyayena ba. Amma tunda komai yazo da
sauki idan an amince mana sai mu bada
kudin aure, sai kuyi magana da mahaifina a
waya ya lamunce in nemi auren. Su dukka
suka ce babu damuwa ai. Dr shuraim ya
dakko wayarsa ya kira tsohonsa , bayan sun
gaisa ya shaida masa gashi a gaban iyaye da
kakannin aisha farida kakaf sun hallara ,
kuma sun amince zasu karbi kudin aurensa.
Abban shuraim yace masa ya basu wayar,
daya bayan daya abban shuraim ya dinga
gaisawa dasu suna yi masa fatan alkhairi,
shima yana yi musu har suka kashe wayan.
Dr lukman ya tashi yaje mota sai gashi ya
dawo da bakar jakar leda yazo ya zauna, sai
ya mikawa yahaya umar. Yahaya ya bude
yaga damin kudi dauri biyu 'yan naira dubu
daya-daya. Kowanne dami dubu dari ne,
dami biyu dubu dari biyu kenan.
Dakata yahaya. Inji baban abida. Kowa yayi
carko carko yaji abin da zai fada. Yace ba
himilin kudi ba, haka ba wayar da mukayi
da tsohonsa bane aure. Shin an tambayi
yarinya tana sonsa? Don idan yayana umar
yana da rai zai iya yiwa kowacce 'yarsa
auren dole banda aisha farida. Don yana
matukar sonta, baya son abinda zai bata
mata rai. Hankalin dr shuraim ya tashi, sai
yayi ta zungurar dr lukman wai yayi
magana. Hussaini yayi murmushi yace
wallahi tana son shi, matukar so kuwa. Don
nine shaida saboda ni ta tara tace min ina
kokarin raba ta da shuraim, to in sani
kamar ina kokarin raba tane da rayuwarta,
don tanayi masa tsananin son da zata iya
rasa rayuwarta. Babu wanda bai kyalkyace
da dariya ba a cikinsu, yayin da dr shuraim
yayi ajiyar zuciyar jin dadi. Salati goma ga
annabi (SAW) suka fara kawowa, sannan dr
lukman ya fara warware kudade yana
bayani. Naira dubu 100 shine kudin na gani
inaso, naira dubu 50 gaisuwar uwa da uba,
sai naira dubu 50 kudi ne kyauta a
rarrabawa dangi , wani a siya alawa da goro
shaidar an bada ita. Sai tsofaffi suka rike
haba don mamaki da jin wadannan
makudan kudi tunda suke aurar da
'ya'yansu da jikokinsu babu wacce ta taba
yin tsadar da farida tayi. Sai wasu suka
barke da kukan dadi don ko naira ashirin
babu a aljihunsu. Wasu kukan tunawa da
mahaifin farida sukayi. A lokacin malam
sule ya shiga yiwa farida kirari irin wanda
baban yake yi mata tun tana karama.
"Aisha sarauniyar mata, fara mai farar
aniya, kinfi mata dubu". Kowa yana ta
adduar fatan alheri da fatan ayi auren cikin
sa'a da zaman lafiya. Dr dayyabu ne zai tafi
a yau, dr shuraim da lukman zasu kwana sai
washe gari zasu koma, da mota suka taho
don haka yahaya zai raka su masauki. Wani
tsadadden hotel zai kaisu, sai suka yi musu
sallama suka shiga mota suka tafi.
HAUSA Novels BOOK
DUK KYAN TAKALMI 3* 9
Aisha farida tana zaune a gefen katifar
abida tayi shiru tana sauraron bambamin
fadan da goggo keyi, saboda an kawo
likitoci sunzo sun korar mata mai magani da
suka kashe kudi sannan ta yadda tazo. Tana
shiga tana fita, ta na fada ita kadai, babu
wanda ya tanka mata a cikin gidan saboda
ranta yayi matukar baci. Ko hakuri aka bata
sai taji tamkar an zage ta. Abida ta dubi
aisha farida tayi dan murmushi yayin da
itama ta dube ta tayi murmushin. Abida ta
yi magana a hankali sai da aisha farida ta
dora kunnenta a kusa da bakin abida
sannan taji abinda take cewa. Cewa tayi
allurar nan da akayi min naji dadinta, yadda
kika san yawo takeyi kusurwa kusurwa duk
inda ciwon yake tana wanko shi. Gashi ina
iya daga hannaye sama. Dadi ya rufe aisha
farida tayi dariya tace mungode Allah, Allah
Ya karo sauki. Abida tace amin, naga
shuraim, Allah Ya sa ayi auren nan. Aisha
farida tayi dariya tace samun lafiyar ki shine
fatan mu , kafin ayi wata magana
antina......bata rufe bakinta ba saiga
maimuna ta fado cikin dakin budik! Ko
sallama babu kai kace jeho ta akayi. Sai haki
take daga gani tasha gudu. Cikin sheshekar
gudu ta rirrike aisha farida tace albishirinki?
An bada ke, yanzu aka kawo kudin aurenki
dubu dari biyu. Kallon rashin fahimta aisha
farida da abida sukeyi wa maimuna.
Aisha farida ta rike baki da daya hannun ta
dafe kirji ta dinga fadin Allah mai iko, Allah
abin godiya. Wai nice yau ake maganar
aurena da dr shuraim? Maimuna ta fice ta
barsu suna mamaki. Wayarta ce ta hau
karan sai tayi sauri ta duba ta zaci rabin
ranta ne, sai taga sunan barr muazzam ta
danna da sauri sai taji muryarsa cike da
farin ciki. Yace gani a kofar gidanku, na kira
wayarki taki shiga sai da na aika yara suka
fito suka ce min wai kun tashi, kun kaura
shagamu. Ance anyi muku mutuwa ko?
Yanzu yara suke fada min. Aisha farida tayi
murmushi tace kai dai bari yayana, tafiyar
ce babu shiri, a kidime muka taho jikin anti
abida ne ya matsa har ta suma an zaci ta
mutu ne shine muka dungumo, muna nan
dai a shagamu har zuwa wani lokaci. Kafin
muga yadda Allah zaiyi damu. Amma yanzu
an samu rabin warakar ciown, tunda an
samu likita da ya gano matsalar. Barr
muazzam yayi ajiyar zuciya yace har naji
sanyi a raina, ai tuni hankalina ya tashi da
naji ance anyi mutuwa. Sai na kawo anti
abida ce, Allah dai Ya bata lafiya. Albishir
nazo miki dashi sai gashi ba kya nan banji
dadi ba.
Aisha farida ta rike baki da daya hannun ta
dafe kirji ta dinga fadin Allah mai iko, Allah
abin godiya. Wai nice yau ake maganar
aurena da dr shuraim? Maimuna ta fice ta
barsu suna mamaki. Wayarta ce ta hau
karan sai tayi sauri ta duba ta zaci rabin
ranta ne, sai taga sunan barr muazzam ta
danna da sauri sai taji muryarsa cike da
farin ciki. Yace gani a kofar gidanku, na kira
wayarki taki shiga sai da na aika yara suka
fito suka ce min wai kun tashi, kun kaura
shagamu. Ance anyi muku mutuwa ko?
Yanzu yara suke fada min. Aisha farida tayi
murmushi tace kai dai bari yayana, tafiyar
ce babu shiri, a kidime muka taho jikin anti
abida ne ya matsa har ta suma an zaci ta
mutu ne shine muka dungumo, muna nan
dai a shagamu har zuwa wani lokaci. Kafin
muga yadda Allah zaiyi damu. Amma yanzu
an samu rabin warakar ciown, tunda an
samu likita da ya gano matsalar. Barr
muazzam yayi ajiyar zuciya yace har naji
sanyi a raina, ai tuni hankalina ya tashi da
naji ance anyi mutuwa. Sai na kawo anti
abida ce, Allah dai Ya bata lafiya. Albishir
nazo miki dashi sai gashi ba kya nan banji
dadi ba.
Aisha farida ta dafe haba tayi dariya tace
albishir din meye? Yace alewar saka aurena
da janan na kawo miki. An bani ita har an
kai kudi da kayan sa rana , nan da wata uku
za a sha biki. Alewarki ta musamman ce,
bounty na kawo miki har jaka biyu saboda
matsayin ki a auren nan, sai gashi ba kya
nan. Ko 'ya'yan yayanki suna ciki a kirawo
mun su na basu? Aisha farida tayi dariya
tace Allahi abin godiya, amma na taya ka
murna yayana. Kuma na gode da
karramawar da kayi min. Babu kowa a 'yan
gidanmu, dukka muka taho. Nima kuma
yanzu zan zankado maka nawa albishir din.
Dr shuraim yana shagamu yazo da likita an
duba anti abida, ya siya mata magunguna ,
ya biya makudan kudi za a kai jininta kasar
waje a gwado. Sannan daga karshe ya
kunso kudin aurensa ya kawo yanzu yanzun
nan nima labari yazo min, suna can a kofar
gida shi da yayyena da tsofaffin maza. Barr
muazzam ya cika da farin ciki da mamaki,
ya kyalkyale dariya yace ikon Allah, Allah
mai yadda yaso. Wato auren namu ma tare
za'ayi kamar yadda muka fara nema tare.
Na taya ki murna kanwata. Baraka ma
komai ya daidaita, ita da mijinta suna cikin
farin ciki, ya rabu da nafisa , hankalinsa
kacokan akan baraka. Ciki ne ma da ita, sai
ririta cikin yake yi. Tace in gaishe ki da
kyau, kuma tana matukar yi miki godiya,
tana so ta ganki a rayuwarta. Tace in
gayyato ki suna idan ta haihu. Aisha farida
tayi dariya tace Allah Ya kaimu , idan dai ina
kano zanje. Sukayi sallama ya kashe waya.
3 missed calls din dr shuraim ta gani a
wayarta a lokacin da take waya yake kira,
sai ta fara kokarin kiransa, shima ya kirata.
Ta amsa sallamarsa cikin nutsuwa kafin ta
gaishe shi ya jero mata tambayoyi guda
uku, ta rasa wacce zata fara amsawa a
cikinsu. Farida da wa kike waya nayi ta kira
har sau 3 naji call waiting? Meyasa da kika
shiga gida dazu baki fito ba mun gaisa har
na tafi? Meyasa kwana biyun nan naga
alamar kin daina damuwa dani? Sai ta
lumshe ido tayi ajiyar zuciya sannan tayi
murmushi. Tace bari na fara amsa maka
tambayarka ta uku, sannan a gangaro ta
biyu, sai in gangaro ta daya. Zancen na
daina damuwa da kai wallahi ba haka bane,
tunda ina tuna ka a rana sama da dubu.
Sannan tambayarka ta biyu ina shiga gida
na bawa anti abida magani sai na zauna ina
saurarom fadan da goggo keyi mana ni da
yaya hussaini, wai mun kawo likitoci sun
duba ta sun bata musu aiki. Yaya hussaini
ya wuce ba dadi, nima na fita. Sanda
nagama zan fita aka ce min kunja mota kun
tafi. Tambayarka ta farko kuma wanda nake
waya dashi wani ne sunansa barr muazzam ,
bansan kai kira ba da na bashi hakuri na
katse wayarsa na amsa taka. Amma kayi
hakuri. Sai ya tashi zaune daga kwanciyar
da yakeyi yace waye barr muazzam? Na
fahimci dalilin da yasa yanzu bana gabanki,
kinyi min kishiya, laifin me nayi bansani ba?
A ina na kuskure in gyara? Taji tausayinsa
ya kamata sannan tambayar ta daga mata
hankali. Tayi ajiyar zuciya tace Allah sarki
my love , sai naji kamar zanyi maka kuka da
ka jera min wadannan tambayoyin. Nagode
ma Allah da Ya sa duk abubuwan da ka
tambaya bai zamo gaskiya ba. Yaya shuraim
kai kadai ne a raina, ko a gaban idonka, ko a
bayan idonka kai nake so. Baka taba yi min
laifi ba balle naji haushi na canza ka. Haka
baka kuskure ba, balle nayi tunanin wani.
Barr muazzam wani bawan Allah ne da Allah
Ya hada ni dashi a kano, ya taimake ni a
lokacin da na shiga ukuba, sai muke
gaisawa. Ya kawo min alewar bikinsa da dr
janan bai same ni ba, shine yake shaida
min a waya. Dr janan sunusi? Shuraim ya
tambaya cike da mamaki. Aisha farida tace
kwarai kuwa itace, dan ya taba bani tarihin
rayuwarsa da ita. Wacce kwanakin baya ta
shiga matsala har aka tsare ta ko? Dr
shuraim yace tabbas ta dade ana shariar
nan wacce aka ce ta nemo izzudden taki
nunawa. Nasan janan, kawata ce ai. Kwarai
Kwanaki tayi min waya ta fada min zatayi
aure, ashe kin sansu? Aisha farida tace ban
taba ganinta ba, sai dai mijin da zata aura.
Dr shuraim yace shikenan ba matsala. Ki
bani labari mai dadi mana wanda zai sani
inyi bacci mai dadi tunda lukman yayi mun
bakin ciki yau bazan ganki ba. Yace ya gaji
anjima ba zai rakoni in ganki ba. Aisha
farida tayi dariya tace zanso nima ka
kwanta ka huta don kun sha hanya. Sai na
biyu ina so in mika doguwar godiyata a gare
ka bisa dawainiyar da kake yi mana da jinin
jikinka da kuma dukiyarka, Allah Ya saka da
alkhairi. Sai labarin da yafi kowanne dadi,
yau farida ta zama ta shuraim, shima ya
zama nata. Sai ya kyalkyale da dariya yace
bani labarin me ya faru? Haka dai suka
cigaba da hirarraki masu dadi cike da so da
kauna har tsawon awa guda. Abida na
kwance ta kafawa farida ido sai murmushi
takeyi, tana murna a zuciyarta tamkar ta
mike tayi rawa don babu hali ne. Tana
adduar Allah Ya tabbatar da alheri a yi
auren nan ko bayan ranta. ASUBA TA GARI
AISHA FARIDA!!!
BABI NA GOMA SHA TARA! Abu kamar
wasa karamar magana ta zama babba.
Auren farida da shuraim sai kankama yake
sake yi. 'Yan lungu yanzu sun gasgata, don
da jita jita akeyi ko kuma ana ganin abin ba
mai yiuwawa bane, wahalar da kanta kawai
zatayi, yaudararta zaiyi ya tafi don ba ajinta
bane. Sai gashi idan da a sati sau daya ake
ganinsa , yanzu a sati a kalla yazo sau biyar.
Ba sai an fada ba, rayuwa da tukunyar su
aisha farida ta canja gaba daya, sun fara
bankwana da talauci, dr shuraim ya tsaya
musu. Tun ba a yi auren ba ma har ta
kidime ta canza salo da yanayi, kai kace ba
wannan faridar bace ta da. A yanzu farida
ta zama gangariyar 'yar gayu. Komai nata
mai tsada ne (high class) , kama daga
suturunta, takalmanta, da jakunkuna,
mayukan shafawarta da kayan kwalliyarta.
Sai ta canja tafiya, ta canja magana ta kuma
canja tsarin rayuwarta. Bata wulakanta 'yan
lungu amma bata cika shiga cikinsu a yita
wasannin banza ba da surutai barkatai.
Zama da dr shuraim ta koya nutsuwa ga jan
aji , magana ma sai an daidaita baki. Haka
ba a cika dogayen jimla da hausa ba sai an
tottoshe da turanci. 'Yan lungu sunyi
gulmar, sunyi zumden, sunyi yaficen, abin
ya wuce tunaninsu. Sai cigaba suke gani
kala kala musamman da suka ga ta fara aiki
ya daukar mata mai adaidaita sahu ya kaita
ya dawo da ita.
DUK KYAN TAKALMI 3* 10
Abida na tsakar gida tana kallon bakinsu
bata ce musu komai ba suka gaji, har takai
ta kawo ma sun zo sun same ta don suji
wani labari game da wannan aure na farida,
sai ta nuna musu ba lallai sai dr shuraim ba,
duk wanda yafi alkhairi a farida shi zata
aura. Basu ankara ba sai suka ji tashinsu,
sai ana gobe zasu koma sabon gidansu suka
fada musu. Mamaki ya rufe jama'a, 'yan
rakiya mata lodi lodi suka bisu don su
ganewa idanuwansu. Gida mai kyan gaske
babu abinda ba'a zuba ba, tun daga gadaje
a dakuna uku da kujeru a falo duk shuraim
ya siya, gida gini bulo da bulo sama da kasa
duk tiles. Rayuwa sabuwa ta tabbata a
gidan hussaini, farida bata rasa kudi. Dr
shuraim yana bata, ta dauki albashinta
kuma. Babur ta fara siyawa yayanta, kuma
ta canja wa 'ya'yanta makaranta ta kudi
anan court rd, mai adaidaita ya kaisu ya
dauko su. Sun koma sabon gida ba dadewa
aka saka ranar kawo kayan sa rana da na
lefe gaba daya. Kudin mota baiyiwa su
aisha farida wuya ba, suka turawa
magabatansu a shagamu, mata bakwai
maza uku suka shigo mata suka zo kano
don karbar kaya. Abida bata mance da
kawayenta na tsohon gidansu ba, fiye da
bus uku suka ciko suka zo don su ganewa
idanuwansu. Tunda kan 'yan uwan shuraim
kallo ya fara kafin a bude kayan lefe. Masha
Allah! Tabarakallah! Kaya sun yi kyau.
Akwatuna shida da kit biyu. Da saitin
sarkokin gwal da awarwaraye hudu manya.
Wata uku kacal aka saka ranar bikin, kowa
yana sam barka tsakanin dangin amarya da
dangin ango, har aka watse.
An sha dauki ba dadi a bangaren dr
shuraim kan maganar aurensa, 'yan uwansa
mata da yawa basu son auren, kasancewar
sun iske dangin amarya basu da hali. Cece
kuce kala kala sukayi tayi amma shuraim bai
damu ba , tunda mahaifansa sun yadda,
sunyi masa fatan alkhairi , don haka suje
suce duk abin da zasu ce. Da farko dai
mahaifiyarsa taki yadda, amma da yake
tana jin maganar mijinta, kuma kaifi daya
ne, duk abin da ya fada ya zauna a gidansa
dole a bi. Amma a sanda guguwar rigimar
ta buso daga bangaren matar shuraim wato
faiza sai ta kore ta danginsa saboda tafi
karfi. A sanda shuraim ya shaida mata a
waya cewar zai kara aure aure cikin
lallabawa da tattausan kalamai, sai ta hasala
tayi ta zage zage har da koke koke wai bata
yadda ba. Ya shaida mata aikin gama ya
gama, saura wata uku, kuma ba zai fasa ba.
Haka aka tashi dai baram baram a wayar,
shi ba dadi, ita ma ba dadi. Bayan sati guda
da wayarsu sai gata a Nigeria ita da
mahaifiyarta. Ba sulhu ne ya kawo su ba,
rigima ce tsantsarta. Mahaifiyarta tace sai
dai ya saki 'yarta , dama can ita ba son
auren take yi ba. Tunda yace zaman nigeria
zaiyi tasan zai cuce su. Ta gangaro kan
mahaifansa tace dama sun tsani 'yarta faiza,
sune suke hadasu fada. Da kyar rigiman
nan ta lafa, su dai mahaifan shuraim ba su
rama ba, amma 'ya'yansu sun rama musu,
akayi ta cece kuce. Shuraim ne yayi ta bada
hakuri har aka samu hayaniyar ta sauka,
zuciyar kowa ta dan lafa aka zauna taro a
babban falon mahaifinsa aka fara bayanai
da yadda za'a gano bakin zaren. Kiri kiri
matar shuraim ta fada wa mahaifiyarta tana
son mijinta, ba zata iya rabuwa dashi ba.
Mahaifin shuraim yace to ki kwaso kayanki
kizo ki zauna da mijinki da 'yarku a
gabanku. Karatun fa? Inji mahaifiyarta ta
fada a fusace tana harararta. Tace saura
'yan watanni na gama, zanje na gama na
dawo na zauna. Ta sha adduoin albarka a
wajen mahaifin shuraim da shuraim din
kansa, gami da danginsa. Yayin da ta
sacewa mahaifiyarta gwiwa don ba haka
taso ba. Ta fusata tace to ko sau daya kada
kizo kice an miki wulakanci, kije can ki
karata.
A daddafe ta bari sukayi kwana uku sannan
suka koma london. Kafin su tafi kullum kuka
faiza take yi wa shuraim tana cewa baya
sonta yanzu tunda zai auri wata. Ya iya
dadadan kalamai masu kwantar da hankali,
gami da bayanai masu ma'ana ya hada da
yi mata alkawari zaiyi musu adalci a
tsakanin su. Sai taji sanyi a ranta, ta kuma
yadda da duk abinda yake fada mata.
Rabuwar lafiya yayi da matarsa, uwar ce dai
ko sallamarsa bata amsa ba a airport.
Hankalinsa ya kwanta a wannan bangaren
kuma bashi da sauran rigima. Duk dauki ba
dadin da suka yi aisha farida bata sani ba,
bai bari ta sani ba. A bangaren ta matsala
kadan ta samu daga musbahu, a inda ya
tayar da hankalinsa, ba ci ba sha da yaji
abar kaunarsa zatayi aure ta barshi. Ya hada
kayansa zai bar garin, zai shiga yawon
duniya a rasa shi har abada. Tunda ya rasa
farida, to shima mahaifiyarsa da matarsa sai
sun rasa shi. Hankalin 'yan gidansu da
mahaifiyar sa ya tashi, mahaifiyarsa da
kanta tayiwa aisha farida waya ta shaida
mata halin da musbahu yake ciki kuma suka
roke ta tazo ta bashi baki ko zaiji. Sai kawai
ta fashe da kuka ta kashe wayar. Abida tazo
ta iske ta tana kuka ta tambaye ta suka
zauna suka yi shawara. Ta bata shawara ko
bata je wajensa ba, ta saka kati a waya ta
kira ta bashi hakuri akan yayi tawakkali , ya
daure ya karbi kaddararsa , zai yiwu shi ba
alkhairi bane a gareta, itama haka. Ya zauna
kada yace zai gudu, baisan inda zai fada ba.
Kuma Allah Zai barshi da gudun tunda bai
yadda da hukuncin da Ya yanke masa ba.
Haka aisha farida tayi, sai bayan kwana biyu
ta kira shi a nutse tayi masa nasihu masu
ratsa zuciya. Har sai da yaji ba zai tafi ba,
ya fasa. Yana kuka, tana kuka, tanayi masa
fatan alkhairi da godiya. Shima irin
wadannan adduoin ya dinga zuraro mata
har ta kashe wayar.
Banbancin bikinta da na barr muazzam sati
uku ne, don haka sanda taje dinner party'n
bikinsu a tahir guest palace da daddare ta
tafi musu da katin bikinta ita ma. Barr
muazzam yayi farin ciki da ganin farida da
shuraim a wajen bikinsu. Da farko ma bai
ganeta ba, saboda kyan da tayi ta goge, ta
waye ta tsatso da wani kyau na daban. Duk
da dandazon taron nan kowa yana kokarin
ya gaisa da ango da amarya, sai da
muazzam ya taso ya tare su ya kamo
hannun amaryarsa ya gabatar mata da aisha
farida da ya dade yana bata labarinta.
Daman ta san shuraim har ta gayyece shi
bikinta, shuraim ma ya gabatar mata da
farida a matsayin amaryarsa. Daga karshe
muazzam ya kaisu wajen barr nuruddin suka
gaisa, suka zauna a kurkusa. Tabbas daga
gani babu tambaya, nuruddin yayi mamaki
da ganin farida, shi bai taba tunaninta ba
tun wacccan ranar, sai ya dinga tuno
wulakancin da yayi mata a baya, yana jin
nauyinta. Ya sake yin mamaki da yaga
matarsa ma ta santa, sun kebe sai hira suke
yi kuskus suna ta tuntsira dariya kamar sun
saba. Ya kalli shuraim ya sake kallonsa, ya
tabbatar ya hadu, Allah Ya tsara halittarsa a
nan ko ba'a fada masa ba yasan akwai kudi
da ilimi, kuma ita zai aura. Ya tara
tambayoyo jifgi guda a zuciyarsa yana so ya
samu muazzam ya jero masa su akan
farida. Baraka ta dubi aisha farida tayi
murmushi tace ina ta jin labarin aisha farida
kullum, sai yau Allah Ya nuna min ke. Babu
abinda zance miki ni da muazzam a duniya
sai dai godiya, kin ceci rayuka. Ni da na zata
ma soyayya kukeyi da barr muazzam, sai
daga baya na gane jininku ne ya hadu, ya
bani labarin ki da likita, kuma naji dadin
ganinku a tare. In Sha Allah kuma zanzo
bikinku duk da watan haihuwana ne
wannan. Farida tayi dariya tace nafi kowa
farin ciki da dukkanin mu Allah Ya amsa
adduar mu , Ya bamu wadanda muke so.
Ina nafisar ta sa take? Yaya suke a yanzu?
Baraka tayi dariya tace ai ko zancenta ba
yayi, ko kiransa tayi sai ya katse. Baya son
abinda zai bata min rai, yanzu duk abinda
nake so shi yake min.
DUK KYAN TAKALMI 3* 11
Tunda bikin farida da shuraim ya rage saura
sati guda basu zauna ba, daga ango da
amarya har danginsu. Sai shirye shirye
akeyi kala kala. Bayan yinin biki da
kowanne bangarorin biyu zasuyi, akwai
shagulgula har guda biyu da dangin ango da
amarya zasu hadu a waje daya ayi. Daya da
yamma za'ayi a tahir guest palace sai
dinner a Chinese dragon da daddare za'ayi,
kowanne kuwa sai da aka fitar da anko.
Kayan fitar bikin ango da amarya daban aka
dinka musu yadda zasuyi shigar kala iri daya
tsadaddun gaske. Asabar ce yau misalin
karfe biyar na yamma n shuraim ya sauke
aisha farida a kofar gidan kawarta khadija
sani dake sokoto td don ta mika mata katin
gayyatar bikinta ta fito su tafi. Saboda
akwai wurare da yawa da zata kai kafin
magriba ya mayar da ita gida,saboda dokar
da yaya hussaini ya saka mata cewar duk
inda taje ta dawo gida kafin magriba ko da
kuwa tana tare da shuraim ne tunda ba a
daura aure ba. 'Ya'yan abida dukka hudun
ne 'yan rakiya suna zazzaune a bayan mota
sunyi dai dai da kayan ciye ciye da shuraim
ya dau nauyin tulo musu. Suci biskit su kora
da alewa, sai su dora da ice cream da
shawarma. Ehm! Dadi kan dadi wai kunama
ta harbi gyambo, abinda basu taba ci ba a
yau gashi sun samu. Kada ki shiga ki zauna
kiyi ta labari fa a ciki. Shuraim ya fada a
lokacin da ya kashe mota dai dai wani bakin
gate. Ta dube shi tayi murmushi ta gyara
farin gilashin fuskarta tace bazan zauna ba
yayana, yaya za'ayi in iya zama inyi hira
alhali nasan kana jirana? Ina mika mata zan
fito. Ta juya ta dubi yara tace ku zauna
yanzu zan fito ba sai kun bini ciki ba.
Ta bude mota ta fito, takawa take a nutse
kafarta sanye da wani cogen takalmi mai
tsinin gaske, launin baki da bakar jakarsa.
Sai ya kara mata tsawo. Doguwar rigar
jikinta (gown) da aka dinka mata a jikin
super holland purple da baki ta sake fitowa
da kyauwn dinkin. Dr shuraim ya bita da
kallo saboda kyauwnta da yake gani, ji yake
tamkar zai hadiyeta don kauna. Tana shiga
gidan khadija ta iske ta a falo ita kadai tana
kallon MBC action, bayan ta amsa
sallamarta ta nuna mata kujera ta zauna,
sannan ta sake kallonta sosai, sai a lokacin
ta gane aisha umar ce. Khadija ta zabura ta
mike tsaye, ta jawo dogon salati ta dire, ta
rike haba tare da dafe kirji. Tace aisha
umar dama kece na kasa gane ki? Ikon
Allah kece kika zama haka? Daman maryam
ahmad tace idan na ganki yanzu ba zan
gane ki ba. Saboda kin sauya gaba daya kin
zama 'yar gayu. Dariya kawai farida ke
kyakyatawa, khadija ta matso kusa da ita ta
zauna ta shafa jikinta, ta sake nanikarta don
ta tantance kamshin turaren da take ji a
jikinta , tabbas designer ne. Kudinsa ba zai
gaza dubu ashirin ba. Ta janye dankwalinta
don taga gashinta. Sai taga waccan
cunkusheshen gashin na farida mai tauri da
ba a shamfo sai kitson zane kullum yanzu
ya sha mai (relaxer) yayi yalo yalo kamar na
larabawa, baki sidik da shi, ya warware ya
mike daman can mai yawan gashi ce da
tsawo, don haka ya wuce kafadarta. Babu
abinda khadija ke kira sai ikon Allah! Aisha
umar yaushe kika zama haka? Aisha farida
tayi sauri ta gyara daurin dankwalinta ta
mike tsaye tana dariya tace Khadija bana
son wulkanci, wane irin tonon silili kike yi
min haka? Ke dai wani labarin zamuyi shi
idan muka hadu, yanzu sauri nakeyi na bar
shi a kofar gida. Katin bikina na kawo miki,
rana ita yau yini da party. Ta zaro wasu
hadaddun katina guda biyu ta mika mata
daga cikin hadaddiyar jakar dake rataye a
kafadarta. Ta juya da sauri ta fara tafiya.
Khadija sani ta watsar da katunan akan
kujera ta biyo bayanta da sauri. Tace ke
aisha umar ko ruwa ba zaki tsaya ki sha ba?
Dan mai adaidaita sahu ba sai ki sallame shi
ba sai in mayar dake anjima da daddare
ba? Ko angon ne ya fara hana ki kaiwa dare
a waje? Lallai kina ji da wannan angon naki,
ance mai kudi ne shi ya tsaya miki, ance
yana sonki tamkar ransa. Auwal dan ajinmu
yace min a likita zaki aura , rannan na hadu
dashi auwal din a ministry of health yace
min tare kuke aiki. Wai meye gaskiyar
maganar? Aisha farida dai har yanzu dariya
take yi, tace khadija don Allah ki ajiye
tambayoyin nan naki sai mun nutsu zan
amsa miki su. Daidai lokacin khadija ta tura
kofar gate din suna kokarin fitowa, ta daga
kai ta dubi dankareriyar motar da aka kawo
aisha farida a ciki, sai tayi ajiyar zuciya kafin
tayi magana. Sai ta daga kai ta hango
santalelen saurayin da yake tsaye a jikin
motar. Ya kalle ta, ta kalle shi, ta daka
tsalle ta koma cikin gida da gudu, ta labe a
jikin gate din tana salati. Aisha farida ta
firgita itama tabi bayanta da sauri ta rike ta
tana tambayarta lafiya? Khadija ta rike kirji
tace aisha umar kamar dr shuraim nake
gani a kofar gidana? Lafiya ya biyoni? Ba dai
asirin da nayi masa bane yanzu ya fara
cinsa ya biyo ni har gidan mijina? Yaya zanyi
yau?
Aisha farida tayi dariya tace ta yaya dr
shuraim zai san gidanki har ya biyo ki? Wa
ya fada miki asiri yana ci? Tabbas sihiri
gaskiya ne amma bai cika kama wanda yayi
imani da Allah ba. Dr shuraim ni ya kawo,
don ni yazo gidannnan, shine angona.
Khadija ta bude ido da baki gaba daya tana
duban aisha farida, mamaki marar
misaltuwa zaka gani a idanuwanta. Tace
aisha umar yanzu dr shuraim zaki aura
shine baki fadawa kowa ba? Ashe daman
kema kina sonsa a lokacin da muke sonsa
kika boyewa kowa? Ta ya kika same shi? Ke
kuwa wane irin asiri kikayi masa haka?
Aisha farida ta girgiza kai tace babu asiri
acikin lamurana, sai dai addua. Addua na
rike, ita ta kaini ga matsayin da ban taba
zato ba. Khadija nayi alkwawri idan na
samu nutsuwa zan fada miki dalla dalla
yadda muka hadu da dr shuraim har ya
zama mallakina. Sai anjima, sai kinzo bikina,
adireshin wuraren duk suna jikin katin.
Aisha farida ta juya ta tafi, yayin da ta bar
khadija a sankare a tsaye, baki a bude don
gigicewa da mamaki. Daga gidan khadija,
gidan maryam ahmad suka wuce dake
unguwar sallari. Irin wannnan mamaki da
figici da ya samu khadija sani shi ya fadawa
maryam ahmad. A lokacin da ta fito har
mota don su gaisa da angon kawarta, ta
iske dr shuraim ne. Sai da aisha farida ta
tare ta don ta kusa faduwa don tsorata. Ta
shiga yiwa farida rada tana cewa ke dr
shuraim ne wannan ko kaninsa? Aisha umar
ina kika same shi har zakuyi aure? Labarin
yana da tsawo! Amsar da ta bata kenan ta
shige mota suka ja suka tafi ta bar maryam
a sankare a kofar gida.
Aisha farida ta sake kyalkyalewa da dariya
tace tunda kace Allah ai ka gama daure min
jijiyoyin jikina. A lokacin tabbas nima
mutum ce kamar kowa, kuma mace yadda
suke mata. Naji abinda suka ji a raina,
amma sai na fisu hakuri da tawakkali. Na
sama raina har abada ba zan same ka ba
gara ma kada in jefa kaina cikin wahala.
Don haka ban cusa kaina ba, ina gefe ina
addua, Allah masanin komai, sai Ya bani kai
a lokacin da ban taba zata ba. Dr shuraim
yayi murmushi ya lumshe ido yace na
fahimce ki, kuma na gamsu da bayananki.
Amma maiyasa kika tsorata baki zo kin
gwada sa'arki ba? Kika sani ko kici nasara ki
same ni? Ta girgiza kai tace karfina ko
wayona da kwarkwasata ba zasu amfana
min komai ba. Saboda naga 'yan mata da
suka fini komai basu same ka ba. Yayi
dariya yace kin taba sanin kina da kyau
kuwa? Kyawun da tunda nake ban taba
ganin wacce ta yi min kyau kamar ke ba.
Tun ranar da na fara ganinki a duniya na
tabbatar kina da kyau , da zan iya samunki
da naji dadi. Sai aisha farida ta dafe haba ta
bude baki tayi ajiyar zuciya ta langwabar da
kai gefe. Tace shikenan my dear tunda har
abin ya zama ba'a. Dr shuraim ya juyo a
hankali ya dubi kwayar idon abin kaunarsa
yace na taba yi miki karya ne? Toh ki yadda
da magana ta, kina da kyaun da ba a ko ina
ake samunsa ba, babu kantin da za'a iya
samunsa a saya.
DUK KYAN TAKALMI 3* 12
Yace,na taba miki karya? toh ki yarda da
maganata,kina da kyan da ba a koina ake
samunsa ba,babu kantin da za a iya samun
irinsa a saya saboda dalilaina masu zuwa.na
daya kina da kyakkyawar fata irin ta 'yan
kasar itiofiya,mai hasken duhu(chocolate
color).na biyu,kina da gashi mai kyau,irin
na asalin Africa mai gazar-gazar da baki,irin
wannan gashin shine a girarki da fatan
idonki.na uku,kina da kyawun kwayar ido
dara dara,farare sol!idan kina kallon mutum
sai yaji wani yarr a jikinsa saboda kina da
idanuwan nan da ake kira sexy eyes.na
hudu,hancinki bashi da tsayi sosai,haka
bashi da fadi ya dace da fuskarki.na
biyar,bakinki dan karami,kina da hakora
farare sol,ga 'yar siririyar wushirya a
tsakiya.ga ki da fara'a idan kika yi dariya sai
gefen kuncinki su loba dukka biyun,na
shida,Allah yayi miki wata irin murya mai
dadin gaske,wacce ko yar uwarki mace taji
muryarki sai ta waiwayo balle da na
miji.dadadan lafuzzanki su suke karawa
muryarki dadi.na bakwai,Allah ya miki kirar
jiki mai kyau,a dire kike,baki da kiba,ba ki
da rama.sannan bakiyi gajarta ba,ba kiyi
tsawo zalolo ba.amma duk wannan bai jaa
hankali na na fara sonki ba,sai da na gama
karantar halayenki na tabbatar kina da
hankali,kirki,t awakkali,sannan kina da aji.
Abubuwa biyu ne suke tafiya da tunanina a
wajen mace,shine,idan mace tana da aji da
kuma kamun kai wacce ba yar iska ba.kin yi
sa'a kina da duk wadannan.aisha farida tayi
hamdala a zuciyarta,tayi murmushi a
sarari,ta dube shi tayi fari da ido.ta ce,nayi
sa'a da nayi dace na sameka.Dr shuraim
hakika kana da kyau babu inda Allah ya
rage ka tun daga halittarka,ilimi da
dukiya.duk wadannan basu dameni ba,sai
na dinga lura da halayyarka.na shiga halin
damuwa alokacin da ka gwada ni cewar
zaka tafi da ni gidanka ko ba kayi bayani ba
na fahimci abun da kake nufi,sai na kudiri
niyyar rabuwa da kai har abada,kyawunka,
dukiyar baza su taba burgeni ba,tunda kake
sabawa Allah.sai daga baya na tabbatar ba
haka kake ba,kai mutum ne mai tsoron
Allah da tausayi shine na saki jikina na
tabbatar nayi dace da miji nagari.su dukka
sukayi dariya a lokaci guda.
Dr shuraim yace kin cika mai hankali mai
zurfin yunani,kuma ba zakiyi da na sani ba
tunda kika farga kika san kyau da kudi ba
komai bane in dai mutum bashi da hali na
gari.matsalar da ke damun yanmatan
zamanin nan ke nan,shi yasa ake samun
matsala a zaman aure,sakin aure ya yawaita
a kasar hausa.hirar so da kauna da fahimtar
juna suka yi tayi,har suka isa kofar
gidansu.yayin da yaran suke baya suna ta
hidima da kayan dadi,sai ci suke tayi,ya ki
ya kare saboda ledoji da yawa ya ciko
musu.aisha farida tayi godiya suka fito daga
motar suka shiga gida,dr shuraim yana daga
muau hannu,su ma suna daga masa har ya
tafi.su dukka suka ji kamar kada su rabu da
juna,sai kuma gobe idan Allah yaa kaimu zai
dawo don yanzu ba ya fashin zuwa wajen
farida.ASUBA TA GARI LIKITAN AISHA!!!
BABI NA ASHIRIN BIKI!BUDIRI! BIREDEDE!
Rana bata karya sai da uwar diya taji
kunya.tun ranar laraba aka fara gudanar da
shagalin bikin farida da angonta dr
shuraim.akayi kamu laraba,alhamis akayi
kunshi,jumaa akayi sisters eve da
yamma.ranar asabar aka daura aure da
misalain karfe goma sha daya na safe abisa
sadaki mafi kankanta don neman albarkar
aure,kuima a ranar akayi yinin biki.dangin
farida sunzo da yawa maza da mata daga
shagamu,tun sanda biki ya rage sati guda
suka fara zuwa don su taya ta murnar biki.a
ranar asabar da daddare akayi hadadden
party a hotel din tahir guest palace,wanda
mutane da dama suka halacci wajen.
Manyan likitoci abokan ango da kawayen
amarya,da yanuwaansu da abokan arziki
kowa yazo.makada kala kala sunzo kamar
mai dawayya,dan asharalle,yaron saadu
bori,fati niger,rabi mustapha,kowannensu
an bashi fili ya cashe.wannan yayi sai ya
matsa ya baiwa wani fili.babu abun da ake
kira sai likita shuraim angon sista
farida.barista muazzam da amaryarsa
janan,barista nuradin da uwargidansa
baraka su ma sun hallara.yan unguwansu ta
da duk sun zo babu wanda yasan adadin
wadanda suka zo,saboda yawansu.taro yayi
taro har amarya da ango basu iya gane
wadanda suka zo da wadanda basu zo
ba.kallo daya zaka yi wa ango da amarya ka
tabbatar suna tsananin murna.idan ka kalle
su zaka san maauratan nan suna tsananin
son junansu.sun ba wa kowa shaawa sosai
saboda sunyi kyau matuka,shigarsu ta
burge kowa,kowacce rana akwai kalar
kayan da zasu saka kala daya.
Kawayen amarya su ma sunyi nasu
ankon,dangin ango da irin nasu ankon
daban.'yan shagamu ma da irin nasu ankon
daban.masu daukar hotuna da bidiyo suna
ta aikin dauka,sai yau mutane da yawa suka
gasgata shuraim yayi saar mace mai
kyau,don kyawunta ya fito kamar ba ita
ba.ana daf da za a tashi sai ga uwar gidan
shuraim faiza ta shigo fili,ta yi wa kowa ba
zata ita da kawayenta guda biyu hafsat da
halima su ma mazauna london ne,tare suka
zo daga can.don da shuraim yayi yayi tazo
bikin tace baza ta zo ba,toh ashe ta taho
bai sani ba.ta danne kishinta tayi ta musu
kari da daloli sai a lokacin aisha farida ta
fara ganinta,ita ma haka,don ko a hoto ma
bai taba nunawa ko wacce ba.kyawunta bai
tsorata aisha farida ba ko kadan,don bata
fita kyau ba.fari kawai zata nuna
mata,tsayinsu daya,har farida ta fita tsawo
da yawan gashi.faiza ce ma ta tsorata da
ganina aisha farida saboda tayi mata ba
zata,ba ta zaci ta hadu haka ba,don 'yan
gulma sun tsegunta mata yar talakawa
ce,baka mummuna,ashe abun ba haka yake
ba.
Faiza ta kudiri aniyar zama na kishi,ba
kishin dokedoke da zage zage ba sai dai
zata nuna mata ruwa ba saan kwando
bane.wayewa da gogewa a cikin wayayyun
duniya tabbas abun da ta sani farida bata
sani ba,kuma ba zata taba sani ba.zata san
tayi garajen aure mata mili,don mai karbar
shuraim ahannunta sai yayi shirin yaki sosai
DUK KYAN TAKALMI 3* 13
Sai dr shuraim yaji dadi da ganin faiza ta
saki ranta,suka gaisa da farida sosai,har da
baby yarsa mai kama da uban kamar an
tsaga kara.babu wacce ta fi jin mamaki da
ganin aisha farida ita ce amarya sai
kanwarsa da suka hadu da ita a asibiti.suna
ganin juna suka shaida kansu,suka gaisa
cike da farin ciki.
Washegari ranar lahadi da yamma akayi
walima da yamma a farfajiyar gidansu
farida,aka zuba kujeru da yawa da manyan
dardumai.mata ne zalla da kananan yara sai
amarya da ta sha alkyabba,kawaye nta suka
zagayeta tana kan darduma a zaune daga
gabagaba.
mata guda uku ne suka yi waazi a wannan
waje,dukkaninsu akan falalar bin miji suke
magana.saboda yadda aazin ya ratsa
zuciyoyin mata,sai kowacce jikinta yayi
sanyi har da masu zubar da hawayen
imani.daga karshe abida ce ta karbi
lasifikata hau kujerar malamai ta dubi
dandazon matan da suka taru a
wajen,yawansu ya kai yadda baza su kirgu
ba,yara,manya,yanmata da tsofaffi.sai tayi
murmushi tayi musu sallama,sannan tayi
bismillah,ta dubi aisha farida. Like · 2 · 9
April 2013 Hajara Haruna Mahmud Ta
ce,nasiha zanyi miki ya ke kanwata farida
game da zaman aure.na farko iani miki
nasiha da ki bi mijinki domin aljannar mace
tana karkashin tafin kafar mijinta.yake
kanwata,ki fi shi farin ciki idan yana farin
ciki,sannan idan yana bakin ciki ki fishi
bakin ciki.ki kwantar masa da hankali.ya ke
kanwata aisha,ki lura da lokacin cin
abincinsa,domin mayunwaci mafadaci
ne.duk lokacin da kika lura lokacin cin
abincinsa yayi toh ki tanadar masa kafin ma
ya iso.idan ya shigo gida bayan kinyi masa
tara irin ta darajawa,toh ki gabatar masa da
abinci ba sai yace ina abincina ba?don idan
bari ma ya tambayi abinci to ransa ya baci
ma kafina a kawo masa abincin.wani ma sai
yaji baya shaawar abincin,sai yaji gara ya
tafi hotel ya ci mai dadi,duk ranar girkinki
sai yaki dawowa yaje yaci awaje.
Ya ke kanwata ki lura da lokacin da mijinki
yake jin bacci,ki bar shi ya kwanta ya huta
saboda wadansu matan sai sanda mijinsu
yake jin barci zasu tayar da shi su ce suna
da magana,yayi-yayi ta bar maganar sai da
safe tace wlh sai ka saurareni.daga lokacin
da kike hana mijinki yayi bacci a lokacin da
yake jin barcin to kina haddasa kakkaurar
gaba ce wacce ba zata gushe a tsakaninki
da shi ba. ya ke kanwata ki zauna a shirye
ki nunawa mijinki koda yaushe kina
bukatarsa.duk wani yanayi na kwarkwasa ki
dinga nuna masa.duk lokacin. Da kike
zaune da shi. Ki dinga shafar dukkanin
sassan jikinsa yadda zai yi farin ciki. Ya ke
kanwata ina horarki da yin ado ki lura da
ina yake fara kallo a jikinki da zarar ya shigo
cikin gida. Wani mijin fuskar matarsa yake
fara kallo,wani mijin da ya shigo kirjin
matarsa yake fara kallo,wani bayanta yake
fara kallo. To ki nutsu ki gane inda naki yaje
fara kallo. Idan fuska ce ki kula da lokacin
dawowarsa kafin ya shigo sai ki gyara fuskar
ki wanke ki saka hoda ki saka jagira,jan
baki,eye shadow da dai sauransu yadda
fuskar zata yi kyau sosai. Da ya zo sai ki yi
kokarin nuna masa fuskar kina murmushi.
Idan kirjin yake fara kallo to ki tanadi bra
mai kyau,irin mai karfen nan mai gyara
kirji. Tunda kin san kirjin yake fara kallo to
ba zai so kirjin ya ragwargwabe ba. Ko
bayan kin haihu sai ki bi duk hanyar da za ki
bi kada ki bari ya tamule,don wasu matan
su suke kwararraba kansu da zarar kin
haihu sau daya yaga kin tsufa sai ya fara
sha'awar ya auro wata budurwar mai kirji a
cike. To amma idan kika iya kula da
kanki,ba ki lalace ba ba zai tunanin neman
wata ba
In a gargajiyance ne akwai abunda larabawa
suke yi kirjinsu ba ya tamulewa,alkamadin
nan da kuka sani tana da amfani. Da zarar
kin sa rananr da zaki yaye danki kamar sati
uku kafin ranar da zaki yaye shi sai ki dinga
yin kunun alkama da nono ko
madara,madarar fulani ba yar kanti ba. Ki
sha kofi daya da safe kofi daya da yamma.
Bayan kin yaye yaron ma sai ki sake yin sati
uku kina sha,sati 6 kenan. Sannan randa
kika yaye yaron kuma sai ki saka bra wacce
ta matse ki sosai to wannan zai hana shi ya
zube duk da gyara ba zai yi kamar kari ba.
Ya ke kanwata ki lura da wuraren da mijinki
yake sa ido a jikinki in bayanki yake fara
kallo to akwai bukatar ki koyi tafiya idan
yace miko min buta sai ki juya kina
jujjuyawa ki wuce gaba yana biye da ke kice
za ki kai masa har bandaki. Ya ke kanwata
kada ki yarda mijinki yaga abun ki a jikinki,
ki kiyaye hancin mijinki kada ki yarda hancin
sa yaji wani karni,doyi ko bashi a jikinki to
duk lokacin da ya shigo dakin ki ko baby
warin sai yaji kamar da warin ba zaki taba
yin farashi a wajensa ba,kin zubar da ajinki
a wurinsa.saboda dauda ta dade tana kashe
aure sai a dauka wata aljana ce take zuwa
ta raba aure nan kuwa alnakiya ce kawai.
Ya ke kanwata ki kyaye kunnen mnki kada
ki yarda ya ji mummunar magana daga
bakinki. Ya zamanto duk abinda zai fito
daga bakinki zuwa kunnen mijinki to
magana ce ta girmamawa,jan hankali ko ta
tayar da sha'awa. Misali da na ganka sai
naji jikina ya yi wani zim don dadi (haha)
yake kanwata a lokacin da mijinki yake
kwance dake ki nuna tunda kike a duniya
ba a taba dadada miki ba irin a wannan
lokacin domin wannan zai sa kullum ya yi
sha'awar kasancewa tare dake. Ya ke
kanwata magana ta karshe da zan fada miki
ki guji bakin kishi,kishin da zai sa ki kasa
zaman lafiya da mutanen gida. To wannan
kishin zai saka tsana a zuciyar mijinki,kishin
da mace za ta yi shine wanda na fada a
baya,ya zamanto ba ya ganin wata mace a
duniya sai ke.duk abunda zaki yi ya
zamanto idan yana rumfar kasuwarsa ko
office ke yake tunawa.amma kishin da zaki
sa mijinki,abokiyar zamanki ko makotanki
cikin fitina to wannan kishi ne na lalatar
zamantakewa na aure. Allah ya nuna mana
ladubba na aure babu laifi mace taci abinci
tare da mijinta.ta bangaren maza kuma
addini ya nuna kada ango yaje dakin
amaryarsa haka hannu ba komai ya nemi
dan wani abu da zasu lasa kamar dan
nama,lemo ko dan cincin ya tafi da shi
dakin amarya.
Da farko yayi mata sallama ita kuma wajibi
ne ta amsa ba wai ta dinga noke-noke ba
wai sai an sayi baki. To bakin dukka ya biya
tunda ya biya sadaki. Bayan nan sai ya
shiga dakin da farko ya kama gashin
madigarta ya rike sai yayi addua yana tsaye
a kanta. "Allahumma inni as'aluka min
khaira ha wa khaira ma fiha wa khaira ma
jabaltaha alaihi wa'auzubikha min sharriha
wa sharri ma fiha wa sharri ma jabaltaha
alaihi. Ma'ana "ya Allah ina rokonka
alkhairin wannan amaryar tawa da alkhairin
da ka halicce ta akai kuma Ya Allah ina
neman tsarinka daga sharrinta da sharrin da
yake tare da ita da sharrin da ka halicee ta
akai" saboda wata ballagazar daga ya kai
hannunsa kanta sai ta buge hannun ta ce zai
murde mata kai. To iyayenta basu taba
fada mata ba ko malamanta. Ko da ya
manta to ki cire dankwalinki ki mika masa
kai,ki tuna masa idan ma bai sani ba ki fada
masa yadda zai yi idan ke kin sani. Kuma ba
amrya kawai ba ko da wani abu kika siya
kamar gida,mota ko dabba kafin ka fara
amfani da abin ka yi wannan addua. Idan
dabba ce an ce ka dafa bindin kamar kaza
sai ka kama bindinta ka yi wannan addua to
ba za ki ga wani abun bakin ciki game da
wannan dabbar ba. Haka idan sabon gida ne
ya dafa saman gidan yayi wannan addu'ar in
mota ya siya ya daga saman motar yayi
wannan adduar. Bayan ya yi wannan adduar
to sai ya zauna a kusa da ita su rungumi
juna su yi godiya ga Allah da yasa suka
zama halal ga junansu sannan ya gabatar da
wannan dan kayan makulashen da ya shigo
da shi su ci,ana ci ana hira ta sha'awa da
bege.
Amma an fi so kafin ciye- ciyen su fara
gabatar da sallah raka'a biyu nafila,kai ne
daman liman sai ka daga hannu ka yi muku
addua,Allah ya raba ku da sharrace-sharac
cen makiya,ya baku zuria ta gari,amarya
tana cewa amin.in duk sun kammala
wannan suka shiga kwanciya miji ya kusanto
matarsa sai yayi wannan addu'ar yace
bismillahi Allahumma jamnibnashaidan a wa
jannabul shaidana ma razaktana. Ma'ana,da
sunan Allah,ya Allah ka nisantar da shaidan
daga garemu,kuma ka nisantar da shaidan
daga abunda ka azurtamu da shi. Manzon
Allah (S.A.W) ya ce idan Allah Ya azurta su
da da a wannan saduwar da suka yi to babu
rabon shaidan a jikin wannan dan. Ba zai
iya cutar da shi a jikinsa ba ko a zuciyarsa
ba. Ba ranar angonci kadai ba duk randa
zaku sadu miji yayi wannan addua idan ya
manta ki tuna masa. Ba amarya kawai
ba,babu wacce bata karu da nasihohin
abida ba. Kuka yayi mata face-face a ido
kafin ta gama kamar yadda ya yiwa aisha
farida. Ta tabbatar yau abida ta cika amanar
da ta dauka ta rike ta tun tana karama har
zuwa wannan ranar data aurar da ita,ranar
da za ta damkata a hannun mijinta. Aisha
farida ta taso da sauri tana kuka ta
rungume abida suna ta kuka.kanwar
amarya manauwara ita ma ta taso ta zo ta
rungume su suna kuka.yayin da yan'uwa da
sauran jama'ar dake zaune a wajen suka
dinga fashewa da kuka don tausayinsu.
Aisha farida ta dago ta dubi jama'ar dake
wajen ta sharce hawaye. Tace" aunty abida
ta yi min komai wanda uwa da uba suke yi
wa yarsu. Tun ina karamata har izuwa ranar
da zata raka ni gidan mijina. Alllah shi ne
gatana abida ita ce jigo kuma jagorar data
kaini ga samun nasarar komai da na samu a
rayuwata.karatuna,zama da jama'a,farin
cikina da mijin da na aura. Abida ta hana
dan cikinta abu ta bani dan uwana yana
hana ni abu ita ta ba ni.anti abida bata son
taga damuwata,balle ta ga kukana. Ina yi
mata fatn Allah ubangiji Ya saka mata da
gidan aljanna,Ya raya mata 'ya'yanta Ya yi
masu albarka ko bayan ranta.Allah ka bani
ikon cigaba da yi mata biyayya da amfani a
rayuwa duk da nasan ba zan iya biyanta ko
da rabin2 abun da tayi min ba. Aisha farida
ta rushe da kuka sai jama'a suka dauka
gaba daya suna shi albarka suna gasgata
bayanan Aisha farida,musamman yan
uwansu yan shagamu.sannna aka watse
daga wurin walima domin ana ta kiran sallar
magriba.
Bayan sallar isha'I aka sake cancada
kwalliya kawayen amarya ne kawai da
abokan ango babu yara babu tsofaffi.
Hadaddiyar dinner ce za'a yi a royal
tropicana daga can za'a wuce da amrya
gidanta da yake ahmadu bello way,sai su
hadu da sauran mata da tsofaffi yan rakiyar
amarya a can, duk da daman wasu tunda
yamma suke can suna ta jere. Dr shuraim
ya kawata sabon gini a sabon gida wanda ya
tsantsara shi tamkar a turai mai dauke da
bangarori biyu iri daya sak. Kowanne ya
kunshi dakuna uku,faluka biyu,dinning
area,katafaren kicin da bandaki guda biyu.
Dakuna biyu!falo daya kicin da dinning area
dr shuraim ya zuba kaya gaba daya yan
waje ne,carpet da labulaye da fenti duk sun
yi iri daya,kalolin purple da pink. Ita kuma
amarya suka zuba nasu kayan a daki daya
da parlour daya ta roke shi da kyar ya yarda
ya bar musu don da ya ce komai ma su bar
shi. Tana gudun surutun danginsa saboda
an daukaki alada,haka gara ma sai da
danginta suka mata. Adashi yaya husaini
yayi abida da ita kanta faridar. Yan shagamu
ma sun taka rawar gani wajen hado kudade
aka hada da kudin aure da sadaki aka siyo
mata komai dai-dai karfinsu. Sai a yau su
uwani su ummulkhair suka sake gasgata
maganar abida da tace su zuba ido su ga
mijin da aisha farida zata aura. Yau sun gani
kuwa da idanuwansu. Tun daga gate din
shiga gida zuwa farfajiyar gidan ma abar
kallo ce don an kayata da shuke-shuke da
tsuntsaye,liluka,swimming pool kamar ba a
kano ba. Cikin gida kuwa ba ya kwatantuwa
aisha ta haye a rayuwar duniya dai,yadda
bangarenta yake haka bangaren kishiyarta
faiza yake,bambancin kala ce kawai ita
komai nata shudi ne da baki.
Gidan iyayen ango aka fara wucewa da
amrya,abban shureim yayi mata nasihohi
akan ta zauna ta bi mijinta lafiya,nasihohin
da yayi mata masu ratsa jiki ne.daga can
aka zarto da ita gidanta,bangaren kishiyarta
fa'iza aka wuce da ita suka iske falon nan
nata a cike dankar da hadaddun mata kai
kace su suka zabi kyawu da kudi sannan
Allah Ya basu. Kawayenta ne da kawayen
mahaifiyarta,danginta da wasu daga cikin
dangin dr shureim masu bin bayanta.wasu
sunyi musu faram-faram.wasu kuwa ban da
hararta da kallon banza babu abinda suke yi
musu,kai ka ce su aka yi ma kishiyar. Faiza
kuwa na zaune ko uffan ba ta iya cewa har
aka gama bayanai saboda tsananin kunar da
zuciyarta ke yi mata. Dangin farida ne masu
bayani har suna kiran ga 'yar su
amana,farida bata da matsala tana da
ladabi akwai bin na gaba ga hakuri da
kawaici. Suka yi kidansu suka yi rawarsu
suka fito. Hankalin aisha dai ya fara tashi
taga alaamr ko faiza na da niyyar su zauna
lafiya wadannan matan da suka baibayeta
zasu iya zuge ta ta burkuce. Koma dai me
ye ba ta damu ba ba abun da ya kawo ta ba
kenan. Kuma zata yi iya kokarinta don ta
cika burinta. Ita ma kanta ta ga kyawu da
tsarin gidanta sai ta ji kukan dadi ya rufe
ta,ta yi ta godewa Allah a zuciyarta. Babu
abin da jama'a suke cewa sai addua da shi
albarka da fatan nemar musu zaman
lafiya.Allah ya sa gidanta ne sai dai mutuwa
ta raba. Sai kuka ya sake kece mata a
lokacin da ta ga duk sun watse an barta ita
kadai,fiye da awa biyu sannan abokan ango
suka rako shi. Bayan su dr lukman sun
gama yi masu tsiya da barkwanci suka tafi
suka barsu. Aisha ta iske angonta mai ilimin
addini ya aiwatarda duk addu'o'I da
nafilfilin daya kamata ango ya yi shi da
amaryarsa a daren farko. Ya cika da
tsananin farin ciki mai dimbin yawa,so da
yarda ya karu akan amaryarsa a lokacin da
ya same ta cikakiyar budurwa wacce ta kare
kanta daga wasu mazan kafin ta yi aure.
 KYAN TAKALMI 3* 14
Kuskuren da wasu yan matan zamanin nan
ke tafkawa kenan a rayuwa,daga inda suke
fara jawo tsana,zargi,ras hin yarda har
karshen auren,kuma babu inda auren yake
zuwa ake rabuwa idan suka bari wani da
namiji ya fara saninsu a waje. Don haka
dole 'yan mata su yi yaki da zuciyoyinsu su
yi taka tsan-tsan da mayaudaran samarin
zamani ko da kuwa zasu aure su ne to a
guji zina har sai bayan an daura aure. Allah
yasa mu dace.
Satin ango guda a dakin amaryarsa kamar
yadda shari'a ta tanada.sati guda nan da
yayi ya fiye masa shekaru hudun da yayi da
aurensa a baya,don ya sami nishadi.
Lallausan lafazai,ladabi da girmamawa
bayan abinci masu dadi daga wajen
amaryarsa. Ya yi wa Allah godiya da ya sami
farida a matsayin matarsa. Ya kudiri niyyar
cure ta ba zai bari ta subuce masa ba a
rayuwarsa. Sai yaji bambarakwai da ya
koma bangaren fa'iza saboda rayuwar hutu
ta iya.sai sha biyun rana take tashi daga
bacci. Kafin ma ayi maganar abun karin
kumallo kuma ba ita zata yi ba.kofa zata
budewa masu aiki su shigo gidan daga can
bangarensu.kuku ya shiga kicin,mai shara
da wanke- wanke da goge-goge ta
fara.wanka kawai zata yi ta ci ado da riga
da wando ta zauna a falo tana game ko
kallo. Anci sa'a dai tana sallah da zarar
lokaci ya yi sai ta tashi,bayan wannan bata
san a yi wa miji wahala ba. Da zarar ya bata
mata rai zaka ji tana ce masa 'you are very
stupid' su a can karamar kalma ce wannan
dan mace ta furtawa miji. Sabanin abin da
ya ga farida na yi. Tunda asuba take tashi
ta shiga hidimar miji da kalkale gida,ta ce
ba ta bukatar masu aiki.ko cokali zata ba
shi sai ta durkusa har kasa,haka idan ya kira
ta. Sai yake jin kansa yana fasuwa tamkar
ya zama sarki,sarki da ake girmama shi a
fadarsa. Hutu ya dauka daga wajen aikinsa
yayin da ya sa farida ta rubuta takardar
barin aiki saboda ba ya bukatar ta yi ta
wahala saboda dan albashi. Ya yi mata
alkawarin zai bata babban aiki da zarar sun
kammala ginin katafaren asibitin da suke
ginawa shi da mahaifinsa a zoo road. Shi dai
ba zai bar aminu kano ba zai dinga shiga
lokaci2 amma zai fi ba wa asibitinsu
muhimmanci. Kafin nan faiza ta kammala
karatunta ta dawo gaba daya ita ma sai ya
sakata a asibitin a bangaren data karanta
wato acct section. Watanni biyu faiza tayi
tare da farida kafin lokacin jarabawarta yayi
don sun kusa fara jarabawar karshe.
Shureim yayi kokarin samarwa aisha visar
london,kamr ta sa har ta tsawon shekaru
biyar duk sanda suke son shiga sai si shiga
kawai. Don haka shuraim,farida da faiza
tare zasu tafi su yi zaman wata biyu har sai
ta kare su kauro gaba daya. Takaici ya
cikawa faiza zuciya don bata so ba shuraim
yace zai taho da farida,da ta so su tafi su
biyu abar ta saboda a fara zame mata
barazana wajen dauke zuciyar mijinta. A
cikin watannin nan biyu data yi Aisha ta
gama da mijinta,ta gama da iyayensa,ta
gama da danginsa kowa yana sonta saboda
da'arta,kyauta, ladabi,iya karbar baki dss.
Har wasu na tunanin ko da wani baki. Asiri
ta shigo ta asirce gida gaba daya, yayin da
masu hankali suka lura tsabar kirkinta ne da
iya zama da mutane ya jawo mata duk
wannan.
Abida tayi mata nasihohi masu ratsa jiki a
lokacin da ta je ta yi mata sallama zasu tafi
london su zauna har tsahon wata biyu.
Aisha farida tayi mata alkawarin yin amfani
da duk abunda take fada mata,kudi mai
dimbin yawa ta tulewa abida da mijinta a
gabansu har sai da suka tsorata da ganinsa
suka tambaye ta in da ta samu. Ta shaida
musu shureim ne yake bata kyauta wani
ragowar na cefane ne don kudi mai yawa
yake ba su kullum har ya fi karfin na
cefanen. Sannan mahaifin shureim ya ba su
kudi(dollars) mai yawa da zasu yi wannan
tafiyar kadan ta dauka ta canza musu
sauran. Ta umarce su da su cika su sayi fili
a unguwa mai kyau a hankali zata gina
masu. Kafin ta tafi sai da ta turawa
kanwarta munawwara kudi dubu hamsin ta
fara yin jari kafin ta dawo. Wannan shine
karo na farko da aisha ta fara hawa
jirgi,suka hay daga bab zuwa lagos daga can
suka hau zuwa london. A katafaren gidan
mahaifin shureim suka sauka sai dai su
kaiwa mahaifiyar faiza ziyara.babu irin
kallon banza da wulakancin da yan'uwan
faiza basa yi mata idan taje gidan,har
shuraim ya fara jin haushi ya fara kin son ya
kaita,ita kuwa sai tayi ta rokonsa sai sun je
tare saboda tasan kishi ne kawai ke
damunsu. Da suka zauna da ita sai suka
fara gane halin aisha tana da kirki suka fara
sakar mata fuska,haka baby yar gidan faiza
ta shaku da ita sosai koda yaushe suna tare
duk inda zasu je. Aisha tayi kallon duniya
da abunda ke cikinta kyau da tsari a garin
london ba'acewa komai. Sun zagaya koina a
birnin har sun shiga kasashen da suke
makwabtaka dasu don bude ido sunyi
siyayya sun shakata su dukka ukun.
Watanninsu biyu a london faiza ta gama
zana jarabawarta ta karshe ta kammala
degree,sannan suka dinguma suka wuce
saudiyya,ya zo daidai da lokacin aikin hajji
suka sauke faralli,duk da su shureim ba
hajjinsu ta farko ba ce.farida ce ta farko. Ta
nutsu ta yi hajjinta yadda Allah yace,sannan
ta yi addu'oin nemam zaman lafiya da
kwanciyar hankali a aurenta,da rayuwarta ta
duniya da lahira gaba daya. Tayi wa Allah
godiya da ya bata wanda take so a duniya
shi ma yana sonta kuma yana kula da
ita.suka dawo gida kano aka bude sabuwar
rayuwa zama ne na din3. Aka samarwa
baby makaranta mai kyau a akno ta shiga.
Bayan an kammala ginin asibitin aka saka
masa suna imran memorial hospital,ya
samarwa kowacce a cikinsu ofishinta a cikin
asibitin da albashi mai tsoka.
DUK KYAN TAKALMI 3* 15
Af mai kula da dukkan nurses da leburorin
asibitin, yayin da fa'iza ce mai kula da duk
kudin da yake shigowa asibitin, abban
shuraim shine mai kula da duk likitocin da
suke asibitin, shima yana zama ya kula da
masu matsalar fata kudine sosai ake biy
kafin a ganshi. Dr lukman yana zama a
asibiti duk ranar litinin da laraba, dr
dayyabu yana zuwa duk ranar alhamis da
yamma. dr janan mu'azzam likitar mata
(gynae) duk ranar juma'a sda asabar da
yamma. Dr muhd lktr tiyata yana zuwa duk
ranar talata da laraba.dr ruqayya lktr yara
tana zuwa ranar lahadi da juma'a da
yamma bayan likita daban daban da suke
asibitin na dindindin. barr. mu'azzam shine
babban lauyan asibitin shima da ofishinsa a
ciki don haka duk wani mai isa da kudi da
mulki a kano koma ince a kasan nan ya
bude file a asibitin nan saboda iya aiki
tsafta da tsari. makudan kudi suke samu a
kowacce rana wanda yake isarsu su biya
duk wani ma'aikaci hakkinsa dakuma karo
kayan aiki daga kasar waje. bayan shekara
1 dr.s ya dauki nauyin karatun AF don ta
karo ilimi abangaren nurse, tayi amfani da
takardunta suka bata shekara 1 n half zata
sami shaidar degree akan nursin.Hutu
kawai take zuwa nigeria kuma da albashinta
take zuwa bayan kudin abinci da shuraim
yake aika mata.kan ka ce kwabo AF ta
rikide gaba daya ta zama yar gayun gaske,
haka kyakkyawa har kamar sai an wanke
hannukafin a taba ta.
haka naira da pounds sun zauna mata, tuni
ta kaftarawa su yaya hussaini gida mai
tsananin kyau a unguwar jan bulo, ta siya
musu motar hawa. ta canza masa aiki ta
samar mas a asibitinsu a matsayinsa na mai
kula da masu gadin asibitin suma da
ofishinsu. kan ka ce kwabo rayuwar hussaini
ta canza dashi da iyalansa tayi kyau, ya saka
'ya'yansa a makaranta mai tsada, shima
kansa da abida har suna iya taimakon
danginsu na shagamu ba sai sun jira AF ta
aiko musu ba. Allah bai bawa AF haihuwa
da wuriba har sai da ta kammala karatunta
ta dawo gida, sannan ta samu ciki don a
lokaci faiza ta sake haihuwar mace mai suna
fadila har ta yayeta. santalelen jariri AF ta
haifa mai kama da shuraim aka saka masa
suna imran, sunan mahaifin shuraim. yadda
abba yake ji da imran kai kace bai taba yin
jika ba a duniya sai a kansa. wannan kauna
ta samo asaline da kaunar da yakeyima
uwar dan
wato AF a sanadiyyar kula da girmamawan
da take masa. idan kaji abba yayi kukan
yunwa tabbata AF bata kasan don da
tananan gida ko office xata aiko masa da
abinci kala kala kamar kunun gyada,
tsamiya, kanwa, dalayi da sauransu. idan a
bangaren abincine dambu, danwake,
kwadon zogale, rama, masa, sinasir, wainar
'yar tsala, farfesun kaza ko naman rago
amma dahuwardadawa na gargajiya shi
yafiso. haka take yiwa mahaifiyarsa
hidimomi na dafe dafe da ladabi da
biyayya. komai takeso kan tace tayi har tayi
mata, don haka suke son AF ba don faiza
taji haushi ba sai don bazasu iya boyewa
ba. ita kanta faiza baza ta iya cewa AF tayi
mata laifi ba sai dai kawai tayi kishi da ita
don ta aure mat miji,amma babu wata
kyautatawa da girmamawa da bata yi mata
ita da 'ya'yanta. a dole Faiza ta fara
canzawa tana kwaikwayon wasu
abubuwanda AF keyi duK da bazata iya yin
duka don bata saba da wahala ba.
yau falon AFa cike yake da kawayenta kai
kace hada baki sukayi a rana daya suka
kawo mata ziyara har su hudu kowacce
kuma da ban tazo. hidima kawai AF take
tayi masu da kayan abinci, lemo da kayan
marmari kalakala. maimuna kanwar abidace
ke zama a gidan tana taimakonta da
hidimomin gida kuma take rike mata yaro.
suka jera musu kayan dadi kalakala babu
wacce bata cika tumbinta ba a cikinsu har
suka bari. bayan ciki ya dauka sai murya ta
washe sannan falo ya hautsine da hira.
hoton shuraim da AF khadijah sani isma'il ta
kafawa idanu tayi ta kallo,can tayi ajiar hrt
tace "ikon allah ashe dr.s mijinkine, mukayi
ta wahalar da kanmu a kansa? maryam
ahmad tayi ajiyar hrt ta sake rungume
danta tana jijjigawa tace " matar mutum
kabarinsa kana taka allah na tasaa.gashi
nima na auri miji mai sona ina jin dadin
zama dashi. rakiya musa tace, "nifa da gani
nayi kamarAF ta tsani dr.s basa shiri kwata
kwata." ummi yasar tace" ai ni yau takanas
zuwa nayi in dauki darrussa akan
zamantakewar aure. yanzu yasar ya dan
fara yabawa da hankalina shiyasa ya mayar
dani gidansa sai dai kash! har yanzu
kishiyata surayya ta fini fada a wajensa duk
da haka dai muna zaune lfy da ita da
surukata da facalata. yanxu so nake in
samu in sake shiga hrt dinsa ba da neman
gudunmawa daga bokaye ba kamar yadda
nayi imanin bakya bin bokaye amma kika
sami shuraim. kin zama abar kwatance a
cikin mata. kece babbar malamata wacce
tayi min silar canza rayuwata daga
gurbatacciyar hanya zuwa hanya
madaidaiciya. ada na sha wuya a sanadiya
bacewar basira na sabawa mahaliccina"
A.f tayi tagumi tana kallonsu 1by1 har suka
gama maganarsu. murmushi kawai takeyi
yayin da dadi ya kamata tana farinciki da
suka gane komai. ta gyara zama tace
"nagodewa Allah daya ganar daku, nadode
da kyautar da Allah yayi min a duniya wacce
zata zamemin hanyar shiga aljannah a
lahira. dan daga lokacin da mace tayi dace
da samun miji ngari addininta ma ya gyaru.
mace dakinta guda2 ne gidan mijinta sai
kuma na2 kabarinta, na shiga gidan mijina
ba fita inshaAllah sai kuma kabarina ne ya
rage
nabi ta hanyar data dace na auri masoyina
da nake yimasa soyayya saboda Allah,
narike kissar matar nan data debo nonon
'bauna ina lallashinsa muna zaune lafiya
sannan na rike nasihohin nan guda goma
wanda Abida tayimin a ranar walimar
aurena wacce uwa ya kamata tayiwa 'yarta
a ranar da za'a kaita gidan miji. na haddace
su a kwakwalwata kuma ina yin amfani dasu
ina ganin falalarsu. a yau shureim baya
kallon wata mace a duniya sai ni AF, baya
son ya jiyo muryar kowacce mace sai tawa,
bashi da wani tunani sai nawa kuma babu
boka ba mallamai sai tsabar kyautatawa
shima kuma bashi da buri a duniya irin ya
kyautata min. wannan kishin da mata
sukeyi da kishiyoyinsu baya gabana bantaba
saka mata ido ba inga abunda takeyi balle
inji haushinta haka bani da burin in koreta,
burina kadai in zauna da mijina
lafiya.shureim yana da adalci a tsakaninmu
baya bambamtamu. a halin yanzu na
mallaki komai a duniya daidai gwargwado,
motocinmu na hawa na zamani guda
bibbyu babu ta kasa da million4
suturuna masu tsadar gaske, mayukan
shafawa da kayan kwalliya masu tsada
(designers), abinci sai wanda na zaba
zanci.shureim baya dannewa iyalansa
hakkinsu tsakanina dashi sai addu'ar
Alkhairi da fatan yazi gaba da samun budi a
rayuwarsa ta duniya da lahira.yayimin
komai sannan yayiwa 'yanuwana dan yanzu
dangina 'yan shagamu sunyi sallama da
wannan dankararren talauci da muka sha
fama. na dauki nauyin 'yan sakandire da
yawa harsu gama,na dauki nauyin masu
shiga jami,oi
DUK KYAN TAKALMI 3* 16
na dauki nauyin taimakawa iyaye da suka
tashi aurar da 'yan mata da kayan daki ko
samarin da suke hada lefe.kanwata
Munauwara ta rabu da turmutsitsi da
wahalar zaman haya na siya mata gida a
shagamu mai kyau na siminti, na bawa
mijinta motar haya bus yana tuki yana
samun na cefane, na biya mata makka taje
ta sauke farari ta dawo na hada mata jari
tana 'yar sana'a a cikin gida tana samun na
batarwa,ita da 'ya'yanta suna saka sutura
masu kyau suna makaranta mai kyau.
Musbahu tsohon saurayina kuma tamkar
dan uwana yanzu shima nayi masa rana don
na bashi dubu saba'in ya kama shago na
siya masa computers 3 da injin photocopy
ya bude business center tasa ta kansa ya
daina aiki a karkashin wasu. sai ga mamarsa
data tsaneni da matarsa an rakosu gidan
nan tana ta kuka tana neman gafara a bisa
tsana da cin mutuncin data yi min a
baya.harda cewa dama ace baya zata dawo
mana data bar Musbahu ya aureni ashe ina
da mutunci haka.tayita kallon gidana tasan
nayi musu zarra,
kyauta ta ban girma nayi musu na suturu da
kudi mai yawada zasu tafi kadan kenan
daga irin rahamomin da Allah yayi min duk
a sanadiyyar shureim bai rageni da komaiba
dan nima ban rageshi da komai ba.khadija
tayi ajiyar zuciya tace"ai ko baki fada ba
Aisha umar kallo 1 za'ayi miki mu2m yasan
kina cikin daula,jikinki ya nuna kuma muma
shaidu ne don babu abinda bakya yi
mana,kici gaba da godewa Allah sai ya kara
miki"Ummi tayi ajiyar zuciya tace"shiyasa
nazo daukar darasi kibani dama indinga
zuwa
kullum har tsawon wata guda inji ina ganin
abubuwan da kikeyi ni ban iya komai ba.AF
tayi dariya tace"zaki iya zuwa kullum amma
banda ranar weeEnd don mijina yana
gida"Ummi tace to, a wata zan zo sau
KWANA ASHIRIN DA HUDU. Saboda naga
alamar har yanzu GANGAR JIKINSA NA
AURA, zuciyarsa na wurin amaryarsa
surayya. gara inkoma kacokan indinga koyi
da abinda YARENA ADDININA, yazo mana
dasu.duk wanda na tara na fada masa
abunda Yasar yakemin sai yace INA RUWAN
WANI, dan abaya anyi min shaidar tsiya
as sanni da bin bokaye. nakan cewa Yasar
KAI KAFI CANCANTA' ka lura da cewar na
canza yanzu bana bin bokaye irinna da bai
cika kallonaba ma balle yasan nayi kwalliya
tsabar yariga dayayi min shaidar kazanta
abaya.sai Ummi ta fashe da kuka.Khadija ta
tabe baki tace wannan shi ake kirada ADON
DAWA'kenan kinyi kwalliya abanza don
baya lura"AF tayi murmushi ta dafa kafadar
Ummin Yasar ta girgizata tace"kwantar da
hankalinki kawata,sannu ahankali zaki gane
kan mijinki.Yasar zai zama takalmin takawa
tana rufe bakinta sai ga Dr.shureim ya
shigo, ya dubesu 1by1 yayi murmushi. yace
Farida, hakika ni takalmin kafarki ne, nayi
miki lamuni ki takani kije duk inda kikeso
dani 'DUK KYAN TAKALMI' a kafa ake
takawa......................**
*************** ***************
*************** *********ALHAMD
LILLAHI karshe
DUK KYAN TAKALMI 4
Aisha farida tayi karfin hali tace ba
damuwa, ai laifina ne dan banyi kama da
mai kamun kai ba, tunda ba'a tambaye ni
ba nazo na fara yi muku surutu, nasan ba'a
son mace marar kamun kai. Barr muazzam
ya girgiza kai yace zuwanki nan ba laifi bane
dan kin zo kin zauna a kusa damu, kujeru
ne a jejjere kowa zai iya zuwa ya zauna. Da
kika zo kika same mu kinyi mana sallama
duk da tun kafin mu amsa har kin zauna.
Daman kamata yayi ki gabatar mana da
kanki kuma kinyi hakan sai dai kika zarce da
bamu labari shine abinda ya daure mana
kai kenan. Kallon junan da kikaga muna yi
ina tunanin ya sanki ne, shima yana tunanin
ko na sanki ne. Aisha bani labarin
takamaiman abinda ke damunki, muma nan
da kika ganmu matsala ce take addabarmu,
ki saki jiki ki fada mana mu dake sai mu
taimaki juna da shawarwari. Barr
nuruddeen ya fusata ya mike tsaye ya dubi
abokinsa yace malam in ka gama kazo ka
same ni a cikin mota mu tafi, dan ba zan
iya zama ina sauraron wannan shirmen
naku ba. Bansan sanda ka zama marar aji
ba, daga haduwa da 'yar tasha sai ka hau
hira da ita kai ma kana baza sirrinka, idan
taji matsalar ka me wannan zatayi maka?
Itama bata san yadda zatayi da kanta ba
balle ta bawa wani shawara. Kada ka sake
ka ambaci sunana a cikin labarinku kai dai
ka fadi taka matsalar. Ya juya a fusace ya
tafi bai daina fada ba yana tafe yana
magana yana wurwurga hannu har ya fice
daga cikin gate din. Aisha farida da barr
muazzam suka bishi da kallo har sai da suka
daina hango shi. Ta sunkuyar da kanta kasa
sai hawaye ya fara zubowa daga
idanuwanta. Kada ki yi kuka aisha, ki mayar
da komai ba komai ba. Kece fa kika gama
bani labarin cewa zaki iya zama da
kowanne irin mutum a duniya. Inji brr
muazzam. sai tayi murmushi ta shiga goge
hawayenta tace ko kusa ban damu ba, banji
haushi ba. Kawai dai abokinka yayi min
kallon ballagar mace, 'yar tasha, 'yar club,
karuwa kenan. Shine mutum na farko a
rayuwata daya taba jifata da wadannan
munanan sunaye, saboda bai sanni ba, sai
dai ina fatan ya sanni nan gaba. Barr
muazzam yace yi hakuri kanwata, ki cigaba
da bani labarin rayuwarki, ina jin dadin
sauraronki.
Haqiqa Aisha farida,labarinki yakai maqura
gurintausayi,nayi kuka sosai,rabena da
irinkukannan yaukimani wata takwas
kenan.tunrasuwar yayata,ayau nafisa
mamawa kinsani cikintausayin
ki,maganardanakeyi yanzuhaka nakasa
tsayarda hawayendake zuba'a idona.
kitaimaka kibani lbrin cigabanki da
daukakardakikasamu kozansamisukuni
yau...wallah nafisa natausayamiki sosai.
BABI NA BIYU Da na karasa makarantar
primary sai yaya hussaini ya kaini wata
makaranta a wajen sabongari na zana
jarabawar common entrance ta shiga
makarantar federal. Allah cikin ikonsa sai
naci jarabawa aka turani makarantar da na
zaba wato FGC kano. Yayi min sayayya iya
karfinsa ya kaini, ya bibbiya dukka kudaden
makarantar da aka bukata, ya dawo gida ya
barni a can. Nayi kuka saboda rashin sabo,
gashi bansan kowa ba a makarantar amma
daga baya na saba da dalibai 'yan uwana sai
na fara jin dadin rayuwar makarantar.
Jama'a na sona saboda yadda nake da
fara'a, ladabi da son aiki bana kiwa don
haka kowa yana son ya jani a jiki saboda ina
da matukar tsafta. Na yi suna a makarantar
nan da nan malamai ma suka sanni saboda
kwazona da wayo, ga iya magana.
Na gama aji uku hutun da zamu shiga aji
hudu aka cireni, abu ya ci tura hidimomu
sun karu, yayana ba zai iya cigaba da yi min
siyayya ba da biyan kudin makaranta ba
kasancewar shima ya hayyayyafa. A jejjere
ba kakkautawa abida take haihuwa,
'ya'yanta na farko ma 'yan biyu ne maza
abubakar da umar, sai ta haifi mace
mas'uda ga wani cikin a jikinta ko yaye ta
goyen bata yi ba. Ga kudin haya ya karu,
cefane ya karu, farashin abinci ya karu,
gashi an kara kudin makaranta ya kusa
ninka na da ma. Daman duk sanda zan
koma makaranta sai ya ciyo bashi kafin ya
harhada ni in tafi. Ya kira ni daki ya zaunar
da ni yayi min bayanin halinda ake ciki, sai
ya bani hakuri cewar zai mayar dani
makarantar gwamnati ta ;yan mata dake
shekara. Dole na koma makarantar shekara
naci gaba da karatu, daga aji 4 na fara, sai
na zama zakaran gwajin dafi nafi kowa
kokari saboda dana sami horo a FGC a
wajen yaran kabilun da basa jin hausa da
yaran hausawan da suka sami horon turanci
tun daga primary. Ajin kimiya na shiga
(science class) har Allah ya kaini aji shida
aka bani shugabar dalibai, duk wata gasa ko
muhawara ta turanci tsakaninmu da wasu
makarantun ni nake tsayawa
makarantarmu, idan bana nan babau abinda
yake tafi dai dai. Shugabar makarantar mu
tana alfahari dani, kullum tana kwatance
dani saboda kokarina. Da muka gama
makarantar ita da malamai sai da sukayi
takaicin rashina saboda ba'a sami madadina
ba.
Bayan gama makarantata da wata uku
yayana ya harhada 'yan kudadensa ya bani
kudin mota da guzuri na zuwa shagamu,
saboda duksanda yake zuwa shi da matarsa
da 'ya'yansa ina makaranta ba'a zuwa dani.
Tsofaffin abokan hirata har sun gaji da
tambayata wasu ma sun mutu, haka wasu
daga cikin yayyena sun murmutu duk banje
ba. Ina samun wasikun kanwata
munauwara akai akai duk sanda ta sanda ta
sami mai zuwa sai ta bayar an kawao min,
ta shaida min cewar an cire ta daga
makaranta tana secondary aji 3 anyi mata
aure saboda rashin kudi. Ni kadai yaya
hussaini ya saka a mota zuwa shagamu,
dana isa garin shagamu a tasha na hau
acaba zuwa gidanmu, ban manta hanya ba.
Da yawan 'yan gidanmu basu shaida ni ba
sai daga baya suka gane ni, sunga na girma
nayi kyau. Duk da rashin wadatar da muke
ciki a kano sai naga na fisu kyawun gani,
cikakkiyar lafiya da gogewa. Na zagaya
dangi na kusa dana nesa har sai da naji
kafafuwana zasu gutsire saboda yawansu.
Na ziyarci gidan kanwata dake agege a
lagos anan take aure, rayuwarta abin
tausayi, gida ne irin na haya mai dauke da
dakuna fiye da ashirin, yare kala kala kamar
hausawa, yarbawa, igbo, da wasu yaruka
daban daban. Bandaki daya ne kacal, tunda
asubahi ake fara layin shiga bandaki. Mijinta
iliyasu shima dan shagamu ne amma a lagos
yake facin taya, ita kadai ce sana'arsa.
'Ya'yansu biyu a lokacin. Saboda tausayin
halinda na same ta kusan dukka kayana na
sakawa na bata kyauta, sannan na hada
mata mayafai, sarkokina, takalmana, guda
dai dai na rarrage. Duk kudaden dana samu
na bata dukka kudin mota na komawa ta
kano kadai na ware. Muka sha kuka tare da
nazo tafiya, kukan da muke na tunawa da
iyayenmu ne da kuma kukan rabuwa, don
munsan zamu dade kafin mu sake haduwa.
Na dawo kano jakata kwalam babu komai
duk na rabar da kyana kuma da masu kyan
na tafi dasu. Tsummokaran, tsofaffin,
yagaggun kadai na bari a gida. Haka nazo
na dinga karancin kaya duk sun ragargaje
dan haka na daina zuwa taron biki ko gidan
kawayena. Abida tayi ta min fada tace nayi
garaje ai ba'ayin haka tun da nasan ban
ajiye wasu ba a lufge kuma bani da mai
dinka min wasu ai bai kamata in rabar ba.
Idan fita ta kama ni dole sai dai in ari kayan
abida in saka inje, ina dawowa in cire mata.
Abinka da cakudi, zaman saka ido, kowa
yana kula da shige da ficenka. Gulmammaki
iri iri bayan zumde da yafice zaka ga anayi
mana, abin ya kai har su dinga kiran 'ya
'yan abida suna bugun cikinsu suna
tambayarsu wai ina kayana suka ga ina arar
na abida? Irin wannan gutsiri da tsomar sai
da ta wuce kan matan gida ta koma wajen
mazansu, su kuma suka tseguntawa yayana
hussaini, suka ce masa bai dace in dinga
arar kayan abida ina fita kofar gida ina
tsayawa da samari ba, ina yawo da
kawayena a gari. Idan ba an lura ba in a
duhune sai a zaci abida ta fara bin maza.
Sukayi ta zuba masa bayanan da dole
hankalinsa yayi matukar tashi, ransa yayi
mummunan baci.
Ya shigo dakina ransa a bace ya iske ni a
kwance yace min in kira abida itama ta
shigo nan dakin yana da magana da ita.
Mukazo muka durkusa a gabansa muna
karkarwa saboda yadda muka ga ransa a
bace gashi mutum ne mai zafin zuciya. Ya
umarci abida ta fada masa gaskiya kada ta
kuskura tayi masa karya akan abinda zai
tambayeta, haka nima ya gargadeni kafin ya
yi mana tambayoyin. Muka yi masa
alkawarin zamu fada gaskiya, ba zamuti
karya ba. Cike da fargaba mai tsanani
muke sauraron abinda zai fada mana. Ya
cewa abida da gaske ne aisha farida tana
aron kayanki ta saka ta fita yawo a gari? Sai
abida ta dafe kirji tace Innalillahi wainna
ilaihir rajiun! Ya daka mata tsawa mai
firgitarwa yace baki bani amsa ba. Nan da
nan ta fara hawaye, jikinta na karkarwa tace
eh haka ne. Sai ya kai mata mari har sai da
ta fadi kasa, ya fada cikin fushi yace to ta
hada kayanta ta tafi gidansu.
Na rushe da kuka na dinga rokarsa ya yafe
mata ba laifinta bane nice na tambaye ta.
Nima din ya yafe min na daina daga yau.
Sai ya rufe ni da duka yana duma, yana
tattaka ni da kafa tamkar zai kashe ni.
Munafukan matan gidan ne suka zo suka
kwace ni dakyar, ransa yayi matukar baci
sai fada yake yana zaginmu wai sai mun
harhada kayanmu mun bar masa gidansa.
Ana bashi hakuri tamkar zuga shi akeyi
dakyar ya haukra ya kyale mu amma tun
daga lokacin baya raga mana, komai mukayi
sai ya hantare mu, sai harara koda yaushe.
Sai na daina fita koina , koda yaushe ina
fama da dinkin yaga da zare da allura.
Abida ta iske mijinta a dakinsu ta ajiye masa
abinci sannan ta durkusa ta gaishe shi. Ya
amsa dakyar cikim fushi, bata damu ba ta
zauna a kusa dashi ta dauko muhuci ta fara
yi masa firfita. Sai yayi mata tsawa yace ta
bari baya so, ta tashi ta fita ta bashi waje.
Cikin lallausar murya tana zubar da hawaye
tace ka yafe mana laifukan da muka maka,
munyi kuskure, fushin da kake yi damu ya
hanamu sukuni, bama jin dadin rayuwarmu,
rayuwa tayi mana kunci. Dan ban fada
maka bane halin da ake ciki kada ranka ya
baci, ashe dana fada maka ma zaifi sauki.
Aisha farida ce ta rabar da kayan sakwarta
kakaf a shagamu saboda tausaya musu da
tayi, ta gansu cikin tsumma, shine ta dawo
bata da kaya sai yagaggu. Dan haka bata iya
fita wajen kawayenta shine nake bata aron
kayana ta saka tana dawowa take cirewa,
bansan abinda 'yan gulma suka fada maka
ba har ya jawo ranka ya baci ka dauki
mataki cikin fushi.
Sai yayi shiru yana sauraronta can yace ai
duk laifinki ne, meyasa ba zaki fada min
halin da ake ciki a cikin gidana ba har sai da
wasu suka fada min a waje? Kinsan irin
zaman da mukeyi da 'yan gidannan, zaman
saka ido ne, duk shige da ficen mu akan
idonsu. Ashe gaba daya lungunnan gulmar
ku ake yi shiyasa raina ya baci. A take ya
bata naira dubu biyu yace ta bani inje in
sayo atamfofi guda biyu 'yan naira dari
takwas takwas inyi dinkin dari bibbiyu.
Abida mace mai hakuri da tsananin wayo,
ta iya zama da mijinta duk zafin zuciyarsa,
tabbas macen da bata da hakuri da wayo
ba zata iya zama dashi ba, sai gashi da
kansa yayi nadamar aninda yayi mana, sai
yaji kunya yazo yana lallaba mu.
DUK KYAN TAKALMI 5
Saurayina guda daya nake kulawa mai suna
musbahu, lungun mu daya dashi kowa
yasan mu tare, yana sona sosai nima haka
saboda yana kula dani. Tun sanda na gama
sakandire yake so ya aiko gidanmu ayi
zancen aure sai aka sami matsala daga
gidansu, mahaifiyarsa bata sona 'yar
kanwarta take so ayi musu auren gida, shi
kuma ni yake so ya aura.mahaifiyarsa ta
tsane ni haka kawai, ko a hanya na gaishe
ta bata amsawa shiyasa na daina zuwa
gidansu don da ina zuwa wajen kanwarsa
jamila kawata ce ajinmu daya a shekara.
Musbahi ma yaji labarin duka dana sha
saboda aron kaya, sai naga ya siyo min leshi
guda daya da atamfa ya hada min da naira
dari biyar kudin dinki, sannan yayi min fada
in daina boye masa sirrina saboda yadda
yake sona a ransa, matsalata ai matsalarsa
ce. Yace duk sanda na shiga matsala in fada
masa ko bashi da kudi zai ciyo bashi yayi
min komai in dai baifi karfinsa ba. Yaci gaba
da bani hakuri akan halinda yake ciki shi da
mahaifiyarsa, ita ta hana shi ya turo
gidanmu zancen aurenmu. Ya umarce ni da
mu dage da addu'a Allah Ya karkato da
zuciyar mahaifiyarsa kaina taji tana sona ayi
auren dani.
Sakamakon jarabawar mu na sakandire ya
fito naci credit takwas, geography ne kadai
naci pass shima dan a ranar da muka yi
jarabawar bani da lafiya. Sai misbahu yace
idan ya sami kudi zai saya min form din
jamb in wuce jami'a. Sai nace ba zan iya
karatu a jami'a ba saboda 'ya'yan masu
kudi ne sukeyi, bani da mai bani kudin
mota da kudin sayan handout, gashi dole
sai an saka sutura masu kyau. Sai shima ya
gasgata zancena yaga shima bashi da halin
da zai dauki nauyin duk wadannan sabida
dan abinda yake samu ba mai yawa bane.
Duk da wasu lokutan sukan sami ayyuka da
yawa suna samun kudi a business center
yake aiki, suna typing a computer, suyi
kalandu ko meme. Sai yace to zai samo
min management in fara, nan ma nace
bana so nafi son inyi schl of nursing saboda
ba ruwana da neman kayan sakawa, suna
da uniform, sai yace shikenan zai binciko
yaji duk yadda akeyi a shiga amma in fara
jin ra'ayin yayana. Yayana ya amince da
shawararmu kuma yaji dadi musamman da
musbahu yazo har kofar gidanmu ya sa
akayi masa sallama da yayana hussaini ya
kara yi masa bayani. Yace zai taimaka min
da wata dawainiyar kudin makarnatar sai ya
amince yayi masa godiya. Musbahu da
yayana ne suka hada gwiwa suka bani duk
kudaden da ake bukata na shiga
makarantar koyar aikin jinya ta malam
aminu kano dake unguwar court road.
Karatun shekara uku ne a shekara ta uku ne
muke zuwa asibiti koyar aiki don haka
karatu na yi tayi haikan, ban taba samun
matsala ba cinye jarabawata nake yi koda
yaushe.
A asibitin malam aminu kano ake horar
damu koyar aiki (attachment). Ina zuwa
kkullum daga unguwarmu sharifai zuwa
court rd akan acaba saboda idan nace zan
hau bus zan bata lokacina zanyi in makara.
Kudin acabana kit da kit babu canji wata
rana ko purewater zan sha sai dai
kawayena su saya min. Duk da idan za'a je
sayan abinci ko shan lemo sai in gudu bana
binsu saboda kullum sai dai su saya min, ni
kuma na fara jin kunya sun gane bani dashi.
Kawata khadija sani ismail kadai wacce bata
gajiya da taimakona kuma duk sanda tace
muje cin abinci naki zuwa ko na sulale na
gudu sai ranta ya baci, har tayi fushi dani.
Sai inyi tayi mata bayanan karya in kirkiro
uzurin dana je nayi ba guduwa nayi ba sai
ta ki yadda tasan karya nakeyi. Ba ita nake
ji ba, sauran kawayenmu nakeji don suna
nuna min bakin hali daga baya kuma in
dinga jin kananan maganganu cewar na cika
san banza kullum bana fitar da kudina ina
sayawa kaina abu balle in sayawa wani, sai
dai ni kullum a saya min. Rashin sani yafi
dare duhu, kallon kitse sukeyi wa rogo.
Hakika ni mai yawan tsafta ce in kula da
fararen kayan makaranta ta, kullum tsaf
dani, ina kalkale jikina tas a wanke ga karin
guga. Gani nafi duk 'yan ajin mu kokari
yawanci ni nake basu amsa. Khadija bazata
iya rabuwa dani ba dan bata da kokari sai
dai gata, tunda iyayenta suna da hali. Duk
wasu manyan littattafai na karatu (text
book) babanta yana saya mata duk
tsadarsu, sai nafi morarsu don ni ce mai
hazakar karatun ba ita ba.
Da taimakon Allah da taimakon khadija sani
nake cin jarabawa dan ba zan iya sayan
littattafan nan masu tsada ba. Badan Allah
Ya sa na iya kitos ba ina yiwa makwabta, da
wata rana ma ba zanje makaranta ba
saboda duk ranar da yaya hussaini ya tashi
bashi da kudi sai yace in hakura kada inje
makaranatar randa ya samu naje. Ni kuma
bana so inyi fashi, da kudin kitson nake
harhadawa in tafi duk da kitso a unguwar
bashi da tsada, kan manya naira talatin ko
arba'in, na yara kuwa naira ashirin ko goma
ne. Ban taba fadawawa kawayena sirrina
ba, duk da yawan kawayen da nake dasu a
ajinmu mata da maza, sai dai ayi hayaniya
wasa da dariya a watse, ina taka tsantsan
da harshena a koda yaushe. Babu wanda a
cikinus ya san yadda gidanmu yake, basu
taba zaton haka nake rayuwa ba, sai dai sun
fahimci wani abu akwai wasu matsaloli
wanda ba zasu boyu ba. Suyi ta zargi da
sake sakensu a ransu su kadai, ni dai bazasu
ji daga bakina ba kuma ba zasu iya tara ta
su tambaye ni ba. Ni daman bana zuwa
gidan kowa balle azo gidanmu, mu hadu a
abkin gate ne mu rabu idan an tashi.
Bana jin dadin rayuwata a wannan
bangaren saboda bani da wata
takamaimiyar kawa ko masoyin da zan
amayar musu da radadin da zugin
matsalolin da suke addabata. Kawata guda
daya, itace aminiyata, yayata, masoyiyata
wato matar yayana abida. Muna zama ni da
ita mu raba dare ko mu yini muna tattauna
matsalolinmu, koda yaushe ina samun
nutsuwa da kwarin gwiwa idan abida ta
bani hakuri akan talaucin da na tsinci kaina
da shawarwari, sai inji sanyi a raina,
tawakkali ya kama zuciyata sai inji ta tuno
min da nasihohin da mahaifina yayi min a
baya. Idan nayi haka sai in dawo da
walwalata, ni burina guda daya ne shine in
gama karatuna in fara aiki in taimaki kaina,
in taimaki 'yan gidanmu. Babbar matsalar
ma da tafi damuna shine zaman cakudi a
gidanmu, cikin tsagoron kazata da cinkosa,
babban burina ba wuce inga mun bar gidan
nan da umguwar mu canja gida ko haya ce
dai mu kama gidan da muke mu kadai.
Dakina daya da yara, ga dakin dan karami
mun cunkushe gashi su dukka yaran abida
fitsarin kwance sukeyi dan haka sun ruba
katifar sai zarni take dan haka na hakura da
katifar na bar musu. Na koma kwana akan
tabarma, idan na tashi da safe sai inyi salla
akai in nada in jingine a lungu sai zan sake
yin wani sallar sannan in shimfida. Har
yanzu kayana a jakar bagco yake a gefen
shimfidata, rayuwata ba irin na 'yan matan
'yan boko bace, tamkar a kauye nake ba'a
birni ba. Ko inyi tunanin shiga hanyar
banza, ban taba sha'awar makalewa gidan
kawaye ba ko arar kayan kawa, na rike
talaucina na kama kaina bana sha''awar
kayan wani. Daga makaranta sai gida, a
gidan ma nafi zama a daki kullum ina
karatu. Idan kaga na fito aiki nazo taya
abida, wankan 'ya'yanta , tsarkinsu ko aikin
girki. Sai 'yan gidanmu da sauran 'yan
unguwa suka shiga yimin shaidar girman kai
ne dani dan ni 'yar boko ce, basa ganin
fara'ar da nake yi musu. Kullum ina gaishe
su ko basu ganni ba, tabbas mutum ba'a
iya iya masa, saboda dan Adam ya kasance
mai butulci ne.
BABI NA UKU Wata rana ranar litinin da
misalin karfe daya na rana muna cikin a
sibiti, a bangaren marasa lafiya muke
wadanda aka kwantar dasu sakamakon
wasu kurajen da suka feso a jikinsu. Muna
biye da ma'aikaciyar jinya matron maryam
tana nunnana mana yadda ake aiki, domin
neman karin bayani sai tace bari ta hada
mu da kwararren likita wanda ya kware a
bangaren fata. Ta tura wani daki ta shiga
muma muka bita a baya da alama dakin
daukan darussa ne sabida naga kujeru ne
zalla da allo makale a jikin bangon. Kamar
yadda naji ta ambaci sunansa, dr shureim
imran. Mun iske shi tsaye a tsakiyar ajin
tare da wasu daliban likitoci guda 3 maza
biyu, mace daya da alama sunzo sunyi
masa tambayoyi ne akan wasu abubuwan
da basu gane ba. Bayanai yake yi musu
cikin harshen turanci kai kace baturen
america ne, kalmomin kimiyyar (botanical
names) da yake ta ambato yana jerowa layi
layi da ka ba tare da yana duba littafi ba,
kai kace shine ya lakaba musu sunan don
ya haddace. Muna sake kutsawa cikin
ofishin yayin da zazzakar muryarsa,
daddada take sake shiga kunnuwanmu sai
duk muka kagu mu isa gabansa don mu kalli
fuskar mai muryan nan daddada.
Kasancewar kofar ta cushe muna shiga don
muna da yawa, ga dalibai likitoci nan suna
kokarin fitowa sun gama daukar darasin.
Kowa ya kagu yayi ido hudu da mai
daddadar muryar nan, keyarsa kawai na
fara hangowa daga nesa sai na tabbatar
bakar fata ne dan uwana saboda ban hango
jan kunne ba da farin gashi irin na turawa
ba. Bakin gashi ne tattaura irin namu na
hausawa, sai dai gashin a gyare yake yana
shekin mai kuma ya kwanto lambar zuwa
karshen keyarsa. Kansu babu hula, yana
sanye da bakaken kaya riga da wando
(suit), farar riga mai dogon hannu daga ciki,
ya daure wuyansa da jan kyalle wato
necktie. Dana matso ciki sai na fara hango
gefen fusakarsa, wata lafiyayyiyar fata na
fara hangowa mai dauke da launi mai
tsananin kyau. Irin kalar da take tsada a
duniya wato hasken duhu (chocolate color).
Ko dana sake samun daman na matso kuda
dashi sai ga gefen fuskarsa tar ina gani wato
idonsa daya da gefen hancinsa, sai kawai
naji wata mummunar fadywar gaba ta far
min ni ma bansan dalili ba har wadanda ke
kusa dani zasu iya jiyo karar ajiyar zuciya
danayi.
Tunda nake a rayuwata ban ta ba ganin irin
wadannan dara daran idanuwan ba masu
tsananin haske daga ciki, da bakar kwayar
ido mai tsananin baki, aka zagaye idon da
wasu gashin ido da gashin gira masu yawa
da tsananin baki, ya gyara su sunyi kira mai
kyau suna sheki. A nutse ya waiwayo da
kyakkyawar fuskarsa gaba daya ya dube
mu, bani kadai ba duk wata 'ya mace da
take wajen sai dataji a ranta dama ace
wannan kadarar mallakarta ce. 'Yan uwansa
maza ma sai da suka raya a ransu dama ace
sune shi, ga kyau ga ilimi. Ashe a da dana
ke hango gefen fuskarshi ban hango komai
ba, kyau mai sunan kyau sai ka kalle shi
gaba dayansa daga kafarsa zuwa kansa.
Dogon mutum ne sosai ma kyawun sura,
bashi da kiba da yawa, haka bashi da rama.
Yayi kama da irin bakaken turawan nan da
ake kira african American, hukuncin da na
yanke masa kenan dan ko kusa baiyi kama
da 'yan nigeria ba! Tabbas ruwa biyu ne
suka hadu suka same shi bakar fata da farar
fata.

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *