Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, 17 June 2019

NIDA SHUGABAN KASA 2 COMPLETE hausa romantic novels

adsense here
NIDA SHUGABAN KASA 2 COMPLETE hausa romantic novels

Karanta cikakken littafin NIDA SHUGABAN KASA COMPLETE hausa romantic novels daga shafin gidan novels


"My first lady ba gaisuwa ne?
Nan ma shiru kake ji.
"Ok nasan kunya na kike ji pls ki gayamin a ina kika samu tarihin rayuwata?

"Namanta"
Ya mata wani irin kallo ta sunkuyar da kanta saboda baxata jure kallon ba.

"Ok naji! Now ki gaya min meyasa kika CeCe ni ta hnyar cewa mun Dade muna soyayya"

"Nayi hakan ne don bana son ka rasa kujerar ka"
"Idan na rasa mulki na ta ina hakan xai shafeki"

"Ko kadan bazai shafeni bah nayi hakan nan don bana son ka rasa aikinka saboda nice sila"

Yayi shiru yana nazarin maganganunta
"Kai kuma meyasa ka sharemin hawaye wancan lokacin?
Da Sauri ya daga kai yana mamakin tambayar tata

"Kada kiyi tunanin share miki hawayen da nayi yana nufin wai ina sonki ne no! Tausayinki naji shiyasa na share miki"
  Wani shuumin murmushi tayi tace

"Kana nufin kowace mace zaka Iya share mata hawaye kenan?
Ya jefa mata harara dakyar yace

"Ehhh haka ne"
Shiru sukayi ya rasa wace irin yarinya bace Sam bata jin tsoronsa shi da ko manyan mutane suna jin tsoron kallon idonsa su gaya masa magana Amma ita ko bata damu bah.
Ta sake kallonsa Suka hada ido ta kawar da fuska tana murmushi, bash ne ya shigo ya shaidawa mr President yayi baki suna son ganinsa shuairat ta yi karfin hali tace

"Baka gaya musu muna tare ba ne?
Ba bash ba har mr President yayi mamakin kalaman nata yayi irin ta maza yace

"Sorry bash ka gaya musu ina tare da.... Yayi shiru yana kallonta ta sakar masa murmushi wani irin Yarr..yaji daga tsakiyar kansa yace

"Ina tare da first lady su Dan bani lokaci kadan"
"Ok sir!
Bash ya fada yana kallon shuairat tana wani murmushn mugunta bash ya kai bakin kofa shuairat ta CE

"Uhmmm ...wait! Ka saukeni a gida, mr President don't wory next tym xamu karasa maganar"
Cak! Bash ya tsaya wani irin haushinta yake ji lallai yarinyar nan ta na wuce gona da iri Amma xaiyi maganinta nan shuairat ta tashi ta rataya Jakarta tayi ficewarta bash yabi bayanta mr President kam ya tsaya galala yana kallon ikon Allah daga nan ya wuce dakin da bakin suke jiransa.


.....muje xuwa๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜€akwai drama kenan!
*reefat*
[10/19, 7:28 PM] ‪+234 816 336 4516‬: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*24*
By *Reefat yahya*

Gidan baya ta sake shiga ta xauna ya shigo ya tada motar suna tafiya yana kallonta ta ckn mirror ta juyar da kai gefe se wani shan qamshi take

"Wai angaya miki ni driver enki ne"
Ko uffan bata CE masa bah

"Ina miki magana hajiya"
Nan ma shiru tayi yaja wani wawan birki ya tsaya a gefen titi

"Se ki fita ki nemi taxi ya kaiki gida don ni ba drivernki bane"

"Eyya ...da tun farko ka gayamin ai xan sanar da mr President kaga kuwa akwai mototci da dama sai wacce na xaba , Amma ynxu din ma is not late let mi just call him ya turo min wata motar "
Ta cire waya tana faman danne danne a dole wai tana Neman layin mr President
Yaja motar Suka cigaba da tafiya yana harararta wani guntun murmushi ne ya bayyana a fuskarta.

"Look baby nifa yayanki ne dole kiyi respecting dina "
Bata CE masa komi bah tana danna wayarta da alama chatting take tana faman murmusawa , yana kallonta yana jin haushin abunda take masa wato sunyi nisa da soyayya haka har xata Iya xartar da hukunci ba tare da mr President yayi gardama bah toh a ina Suka hadu? Yaushe Suka fara soyayya? Yana mamakin wannan alamarin har Suka kai gida babu wani kalman da ya fito daga bakin shuairat.

*********  A can bangaren mr President kuwa baki yayi daga kasar waje suna tattaunawa dangane da harkokin siyasa har sun gama xasu masauki sannan daya daga cknsu ya juya yana tayasa murnar samun santaleliyar budurwa a matsayin matar da xai aura.

"Yaushe ne zamu sha biki mr President"
Mutumin ya fada ckn harshen turanci ga kuma yan news a xagaye dasu

"Nan ba da dadewa bah da yardar Allah"
Ya bada amsa kai tsaye se kuma yana mamakin ya akayi maganar ta fito daga bakinsa.

************
Haka Rayuwa ta kasance shuairat da yayanta sun share mako 2 basa magana duk abunda yake faruwa iyayensu basu sani bah don basu ga alamar hakan bah, shirye shiryen bikin bash da shukrah akeyi babu kama hannun yaro ynxu ya rage sati2 ayi bikin. Ya gama hada lefe akwati set daya da kaya kala 45 a ciki , lefe kam yayi kyau sai San barka mama da baba sai shirin bikin suke shuairat kam ko a jikinta kawai ta dinka anko nasu na kawayen amarya kuma ita ta zabi kalar kujerun da xaa xuba a falon amarya, suma sun canza nasu kujerun an sake wa gidan sabon fenti yayi kyau sosai ynxu kam se shirin xuwa mubi don gabatar da bikin.
        Tana kwance a daki tana karanta novel din "behind our Lov" na miemie bee๐Ÿ˜˜
Novel din ya burgeta sosai hnklinta ya tafi ga karatun dama a watsap ne aka tura a grp din *gidan gyara*๐Ÿ˜Šteemah ashaka CE ta tura musu...wayarta ya fara ringing bakuwar lamba CE ta ja tsaki ckn jin haushin katse ta aka yi

"Hello! Ta amsa kamar bata so

"First lady ina son ganinki ynxu"
Yana fadin haka ya katse wayar toh waye shi? Oh mr President kenan? Tasan dai shi kadai yake kiranta da wannan sunan toh a ina ya samu num ta ? Hmmm shine wai ina son ganinki ynxu wato ma har wani gadara yake mata...mtsswww se shegen girman kai ๐Ÿ˜
Bata motsa ba ta cigaba da karatunta ckn kwanciyar hnkli kofar dakinta aka bude bash ne ya shigo tare da sallama tayi banxa dashi tmkar bata San ya shigo bah

"Baby magana xamuyi but muje mr President na son ganinki first "

"Bani da lokacin magana da kowa"

"Look am serious about it pls" ya fada yana kallonta ta daga kai Suka hada ido tayi saurin dauke kanta nan kuwa ta soma kuka a hnkli, ya taka ya xo kusa da ita ya jawota jikinsa ya fara magana a hnkli

"Am sorry pls nasan nayi laifi baby kiyi hakuri kin ji koh my baby"
Ta cigaba da kukan da take Mara sauti

"Sorry yaya bai kyauta miki bah but am sorry now plss....
Ta tura baki ckn shagwaba tace

"Ba kaine bah wai kana fushi dani baka tsaya ka saurari me xan gaya maka bah

"Naji is ok now ynxu nagane ba laifinki bane sorry koh

"Uhmm"
"Toh tashi ki shirya idan mun dawo sai muyi maganar koh"
Haka dai ya lallabata sannan ya koma falo yana jiran fitowarta.

Wani dankareren lace ta saka green da touches din wyt n golden ta saka yan kunne cika wuya golden masu uban kyau ta fesa turare masha Allah tayi kyau sosai.
      A gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta ba karya ta hadu Iya haduwa..ynxu kwalliyan nan tayi shi ne don mr President?
No! ta bawa kanta amsa kawai tayishi ne don kar a Reina ta kuma a matsayinta na budurwar mr President she have to look unique always.light make up tayi a gurguje sannan ta fito falo yayanta ya sakan mata murmushi yace

"Wow! My sisy is looking cute"
"Tnx" ta fada daga nan Suka dau hanya ...


๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜tnx 4ur support my fans Lov u all
*Reefat ce*
[10/19, 7:29 PM] ‪+234 816 336 4516‬: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*25*
By *Reefat yahya*


Mr President yana xaune a filin hutawarsa yayi shiru daga gani yayi nisa ckn  tunani ta karasa tare da sallama baima San ta iso bah xama tayi a gefensa qamshin turarenta ne yasa ya juya don ganin ko wayene ido ya kura mata babu ko keftawa
Wani kunya ne ya lullubeta ta sunkuyar da kai dakyar ya saita kansa sannan yayi gyaran murya ya fara magana

" first lady ko xan Iya sanin dalilin da yasa kikayi wannan kwalliyar kodai kin kamu da son tsohon neh๐Ÿ˜‰"
Ya fada yana kallonta ta daga idonta Suka fada ckn nasa lallai mutumin nan

"Ko kadan Aisha bello bazata auri tsoho ba kuma tana da saurayi mai sabon jini me xatayi da tsoho ?
 Yayi murmushn yake yace

" wa ya sani Abu a hudu kuma waya San inda rana xata fado"

" mr President kenan ai kowa yasan cewa a yaMma rana take faduwa "

" shikenan...ynxu na nemeki ne saboda kisan halin da ake ciki
Kin rabani da ya'ta ynxu haka tana fushi dani kuma kin hadani da iyayena kinsa mahaifina yace lallai xai xo nema min aurenki "

๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณta xare ido ckn tsananin firgita shima kallonta yake

"Yes! First lady, kina tsammanin cewa maganan xe wuce haka kawai ne? Dama saida na gaya miki kin tafka kuskure gashi ynxu outcome din kenan, kuma duk duniya an baza kunne ana jiran ranar aurena da ke"

Me shuairat xatayi in ba kuka ba๐Ÿ˜†๐Ÿ˜†๐Ÿ˜† mr President yayi shiru yana kallonta tun tanayi a hnkli har ta fara da karfi wani security ne ya leka don jin muryar ta yana son ganin ko lfy daga ganin mr President a gefe yayi saurin komawa bakin aikinsa.
Mr President ya tashi ya koma kusa da ita har suna jin hushin juna.

Ya kai hannu xe share mata kwallan da ya bata mata fuska tayi saurin kawar da fuskan gefe yana murmushi yace

"Toh ai laifinki ne my first lady, kefa kika fito kika gayawa duniya cewa mun Dade muna soyayya koh?
Harara ta galla masa tace

"Kai de kace kaga Ya'r budurwa kana so shine ka gayawa dad naka amma ka daina labewa da wani magana daban"
Dariya sosai ta basa yace

"So? Toh ai ni bansan wannan Kalmar bah kuma ban taba yinsa ba a rayuwata , xancen aure kuwa tunda na rasa matata ban taba tunanin sako auro wata bah don haka ki kwantar da hnklinki ni bansan wani Abu wai shi so bah"
Tana kallonsa ckn mamaki sannan tace

"Y not ka gayawa dad naka gaskian lamarin"

"Ban taba masa gardama kuma baxan fara a kanki bah amma idan xaki Iya fuskantarsa ki gaya masa da zan fi kowa jin dadin hakan"

"Me xan gaya masa?
"Oho!duk abunda kike so"
Sunyi shiru kowanne da tunanin da yake can ya daga kai yace

"Kije kiyi tunani a kai ko ki fito ki fadi gaskiya ko kuma ki yarda da auren kaddara da xai fado kanki nan ba da jimawa bah"

Yana kawo nan a xancensa ya tashi ya tsaya ya mata wani irin kallon da ta kasa gane maanar sannan ya koma ckn gida ya barta tana xaune ta shiga duniyar tunani...
Me abin yi????????

Hmmmm muje xuwa dai,
Lov u all๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
[10/19, 7:30 PM] ‪+234 816 336 4516‬: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*26*
By *Reefat yahya*


 Bash ne ya katse mata tunani
"Sis ya naganki haka?
Kuka ta fashe masa ya jawota jikinsa
"C'mon let's go home  ki share hawayenki pls ga securities suna ganinmu tashi mu tafi "
Nan ya Suka tashi bayan ya share mata hawaye tana gaba yana biye da ita a baya Suka fada mota ta tadata Suka hau hanya, bayan sunyi tafiya mai nisa yayi parking a gefen titi

"Now tell me me yasa kike kuka?
Nan ta kwace labarin komi tun daga farkon haduwarta da mr President har xuwa hirarsu na karshe ta shaida masa yayi shiru yana naxarin maganganun can ya nitsa yace

"Sisy kinyi Abu mai kyau da kika kare mutuncinki da na mr President but ynxu problem din shine mahaifinsa..dama iyayensa sun jima suna mishi maganan aure baya sauraransu kinga ynxu dole hnklinsu ya kwanta n 2b frank I tink mr President likes u a lot cos tunda nake dashi ban taba ganin ya xauna yana hira da wani har da dariya ba sai ke, idan kinga yana magana da wani dai toh bai wuce maganar siyasa ba se kuma yaransa su kadai yake sakewa fuska"

"And so wat yaya! Kana nufin na auri tsoho kenan?

"Baby ina son ki gane cewa aure mukaddari ne daga ubangiji kuma matar mutum kabarinsa n mr President mtumin kirki ne bashi da matsala ta kowane bangare, kuma idan kika amince da auren nan tmkar jihadi ne don kin rufawa musulmi Dan uwanki asiri.idan har baki auresa ba xaa fara jita jita kuma xai xama wata magana mai girma"

"But yaya...
"Baby kiyi adua Allah ya xaba miki mafi alheri kawai daz final kuka da duk wani bacin rai ba naki bane"

Daga nan ya tada mota Suka koma gida.
Bash yana kwance a dakinsa yana lissafin yadda aurensa xe kasance wayarsa CE ta fara ringing umaima ya gani akan screen yana murmushi ya daga
" hey best friend ina ka shiga ne?
"Friend ina nan aikine ya min yawa"

"Kullum aiki baka hutawa ne?
Murmushi yayi yace

"Hutu ai se manya irinku"

"Hmmm.xolaya koh"

"No! Daz d fact"

"Naji toh yaushe xaka xo mu fita "

"Yaushe kike so?
"Ko ynxu ma am ready"

"Kiyi hakuri xuwa gobe kinji my dear"
Ta lumshe ido tana jin wani farin ciki tace

"Shikenan ina jira Allah ya kaimu"

"Ameen bye"
Tare Suka ajiye waya umaima ta rungumi tabbas ta fada tarkon son bash Allah ne kadai yasan adadin son da take masa๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณhmmmm...umaima kin shiga tarko amma kash!!! Ance rashin sani yafi dare duhu bata San cewa saura kiris๐Ÿ‘Œ๐Ÿขash ya angwance bah***********
Mr President kuwa yana xaune a falonsa yana tunanin hnyar da xaibi ya sasanta da umaima yrinyar Sam taki bashi fuska bash ne ya fado masa a rai tabbas shi kadai zai Iya shawo kan matsalan.
se kuma shuairat ta fado masa a rai yana murmushi shi kadai yarinyar akwai shagwaba kam maybe ita kadai iyayenta Suka Haifa da alama dai Ya'r gata CE ko su waye iyayen nata oho!

Se ynxu ya tuna baima San gidan nasu bah, idan dady yaxo yace su je tare fah?
Lallai dole ya nemo gidansu Amma wannan duk aikin bash ne..ya zaiyi da umaima bayan ya auri shuairat ? Ya zaman nasu xe kasance?
Shuairat xata amince da auren ne ko aa?
Idan tace aa'a me zai gayawa dadynsa ? Me mutane xasu dauke shi?Ku biyoni don jin amsar tambayoyin๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
~reefat~


[10/20, 8:18 AM] ‪+234 903 484 0427‬: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*27*
By *Reefat yahya*


Mr President yana xaune a ofishinsa bayan sun gama ganawa da vice dinsa akwai xasuyi tafiya xuwa China don kula da harkar kasuwanci tsakanin najeriya da china .
     Bash ne ya shigo masa da wasu files ya ajiye xe fita
" a moment pls"
Bash ya juya ya dawo a tsaya a gabansa mr President ya nuna masa kujera ya xauna wato alamarin da ya bashi mamaki kenan saboda tunda suke mr President bai taba masa hakan bah.

"Basheer wani taimako nake so ka min"

"Ina jinka mr President"
"Wato lura kusancinka da yata yayi karfi har nake ganin cewa xata Iya aikata duk abunda ka umarceta, basheer ina so ka bawa yata hakuri akan maganata da Aysha bello pls"

"Don't worry mr President xan mata magana insha Allah "

"Nagode" bash ya tashi har ya kai bakin kofa mr President yace

"N I want to know about Aysha bello"

"Ok sir! Ya bashi amsa sannan yasa kai fice.

A falonsu ya sameta da masu aiki suna mata gyaran farce tana waya, ya shigo tare da sallama
Fuskarta ne ya fadada da murmushi nan kuwa ta kashe wayar

"Aboki se yau"
"Yes my kawa" ya maida mata martani sannan ya samu kujera da yake kallon nata ya xauna nan ta sallami masu aikin bayan ta umarcesu da su kawo kayan motsa baki.

"Ya'r gatan dad ya kike"

"Lfy ya aiki"
"Alhamdulillh ya hutawa"

"Ya kadaici dai koh"
Sun Dan taba hira bash yace

"Kawa me yake damun dad naki ne kwanan nan duka naga yana ramewa"

"Oho! Maybe ya bata da budurwarsa"

"No! It can't b ki dai bincika ki gano matsalar he is ur dad after all"
Tayi shiru tana naxarin maganganun nasa kenan dad dinsu ya rame saboda tana fushi da shi? Dama haka ya damu da ita? Lallai bata kyauta masa bah, kamar yadda take fama da kadaici shima hakan yake fama amma meyasa tayi haka?
Hawayene Suka gangaro a fuskarta nan ta sunkuyar da kai kasa ta fara magana

"Laifina ne na daina kulashi ya bani hakuri har ya gaji ban saurareshi bah"
Nan kuwa ta fara kuka tamkar ranta xe fita

"Me kika masa umaima?

"Akan maganar wannan yarinyar "

"Haba umaima a ina kika taba jin anyi fushi da iyaye? Shin baki ganin irin biyayyar da dad dinku yake nunawa iyayensa ne? Meyasa baxakiyi koyi da halayensa ba?
Ta cigaba da kukanta ba kakkautawa bash kuma ya cigaba da magana

"Tabbas kinyi kuskure Amma is not late kije gun mahaifinki ki nemi gafararsa idan har baki son fadawa ga halaka ". Nan ya kwace labarin komi dangane da alakar shuairat da mr President ya gaya mata cki kuwa har batun aurensu jikinta ya mutu sosai ynxu ne ta gane cewa dad bashi da laifi ko kadan.
 Bash ya mata nasiha me ratsa jiki sannan ya tashi ya tafi.

Mr President yana xaune ya buga uban tagumi a hnkli aka tura kofar umaima CE ta shigo tamkar barauniya.sum sum ta karasa kusa dashi

"Dad....
Se kuma hawaye sun taru a idanunta .
Hannu ya bude mata ta fada jikinsa tana kuka yana rarrashinta dakyar ta daina kuka tace

"Dad am sorry ka yafe min sharrin shaidan ne"

"Is ok baby, idan har kin fahimceni dai shikenan "

"Dad I understand ba laifinka bane kuma itama taimakonka tayi "

"Am happy dat u know  ynxu me kuke bukata cos gobe ko jibi xan tafi China"

"Bana bukatar komi dad Allah ya tsare ka ya dawo da kai lfy"

"Ameen my baby"
Haka Suka kasance suna hira ckn farin ciki da jin dadi ya kalli fuskarta yace

"Baby kodai an samo min suruki ne"

"Laa...dad babu fah"

"Are u sure? Wat of basheer?

"Dad! Ta fada tana dariya bash da yake bakin kofa yayi murmushi sannan ya juya ya bar wajen.๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜to u my fans
[10/20, 8:18 AM] ‪+234 903 484 0427‬: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*28*
By *Reefat yahya*


Karfe 5dai dai bash yayi parking a kofar gidansu na mubi yaran anguwan ne Suka tayasu shigar da kaya ckn gida.
   Mama da baba Suka fito ana musu maraba da xuwa tuni shuairat kuwa ta kama hanyar gidan mutuniyar tata ckn xumudi ta shigo tare da sallama.
Inna tana tankade gari shukrah kuwa tana shara aikuwa sun kankame juna ckn jin dadi bayan sun gaisa da inna dakin shukrah Suka shige tare da sauke labule
( ni kuma nace baxaa barni a baya bah ..lolx)
" kai bestie kin ga hasken da kikayi kuwa? Se shining kawai kike yi"

  "Ya'r rainin wayo na kaiki ne, ke amarya ce fah ansha gyaran jiki ana ta shinning"
" ya gida ya hanya ya su mama"
  "Lfynsu lau ya shirye2"
Shukrah ta harareta ckn tsigar wasa tace
   "Wane shirye shirye"
"Oh! Wa yaga su bestie amarya"
   "Kya ji dashi ya'r nema"
   "Oho dai! Ana so ana kaiwa kasuwa , yawwa baki ban labarin haduwarku da yaya bah kince masa I love u ko ya?

" munafuka ai shuairat kina fama wallhi"
  "Lolx muna fama dai"
Haka Suka kasance suna hirar yaushe gamo shukrah ta kawo mata dambun xogale ta ci tayi hamdala har magarib sannan ta tashi ta kama hNyar gida shukrah tana mata rakiya shuairat ta juya ta kalleta tana murmushi tace

"Anti shukrah ki koma se munxo xance to nyt" shukrah ta kai mata duka suna dariya Suka rabu.

Hakan ko akayi bayan sallar isha bash ya shirya ckn kananan kaya se qamshin turare ke tashi a jikinsa yayi sallama ya tafi shuairat ta yi masa tsiya har ta gaji yana dariya ya tafi.
     Bayan kwana biyu aka kai lefe jamaa na ta yabawa nan aka fara shirye2n biki ba kama hannun yaro su shuairat kirjin biki itace kan gaba a kowane bangare. babbar kawa kuma kanwar ango, sun shirya xasuyi kauyawa day da walima se kuma kamu night"


**********
A can birnin tarayya kuwa mr President ya tafi China don gudanar da harkokinsa
  Umaima kuwa gidan ya mata fadi gashi ta nemi layin bash baya shiga kuma ta tambaya ance mata yayi tafiya sultan ne abokin hirarta se kuma watsap da Facebook, gashi makarantar su ana hutu .
  Tana kwance a falonsu yau taji shaawar shiga watsap dinta ta bude kenan mssgs Suka fara shigowa anyi adding dinta a wani grp din *Gidan gyara* mata ne xalla a GRP din, batasan wacece admin din bah kawai ta ynke shawarar yin magana a grp din ta rubuta "salam" ta tura bayan minti2 Meenat da esha Suka amsa mata๐Ÿ˜Š "wslm"
"Pls wacece tayi adding dina a wannan grp din? Bayan wani Dan lokaci mssg ya shigo from *Reefat* tace "nice nayi add din ki" Mmn Ummul ta tura novel din *tana tare da ni"* kamar da wasa umaima ta fara karanta novel din se kuma taji grp din ya burge tah anata hira a grp din so lively haka, tun tana sharewa har ta fara contributing ta Dan saba da yan grp din har magariba tayi sannan kowacce ta tashi don yin sallah.

    Bayan umaima ta idar da sallah ta sake daukan phn din ta shiga grp taga anyi posting din wasu pre-wedin pix kala2 batayi download bah ta cigaba da karanta novel din *yar Riko* da aka tura, chan an sake tura wasu pix din se a kasan aka rubuta

"Matan gidan nan u r invited auren yaya nah  gobe kamu night"
Cmnts aka fara aikowa
"Wow couples din sunyi kyau"
Su Rabi Oga da su momi Ummi da zaheeda da sauransu duk sunce xasu je auren.
Haka nan umaima taji tana shaawar bude hotunAn tayi download daya yana buduwa
๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ dam....dam....xuciyarta ta buga guess wat?
Hoton shukrah CE da basheer sunyi kyau sosai nan take wani jiri ya fara diban umaima
๐Ÿ˜ณtoh fah....hmmmm"
Wani xaxxabi ne ya rufeta haka ta kwanta akan sallaya idanunta na fitar da wasu xaxxafan hawaye

 ๐Ÿ˜ฅ๐Ÿ˜ฅeyya umaima nah...

Lols Ku biyoni

*Reefat*ce๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜


๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*29*
By *Reefat yahya*


Karfe 7 katon multipurpose hall din Adamawa state university mubi, ta cika makil da jamaa ga yan mata samari manyan mata da dai sauransu can na hango amarya tare da kawayenta dai Kelli suke ansha kyau.
Decoration din hall din ma abin kallo ne anyi decorating da purple n silver se fulawas masu kyau abun dai se Wanda ya gani.
       Kawayen amarya na sanye da purple head da material ash colour n silver wyl amarya kuwa ta saka purple material da silver n ash colour head tie sunyi kyau sosai an fara program sannN ango ya shigo da tawagarsa ckn fararen kaya masu kyau sai shinning suke.
Anfara gabatar da taro su shuairat anyi rawa har an gaJi ga abinci da drinks kala kala anci ansha an xuba kudi kamar ba gobe su Rabi Oga tun daga Jada aka tashi aka je auren๐Ÿ˜œ ga su nan dai matan gidan gyara birjik anyi ta kashe pix xaa canza dp.nima dakyar nasamu nayi pix 2 da amarya da kuma shuairat...
Bayan angama taro aka watse kowa ya kama hanyar gida.


A can Abj kuwa umaima aka kwantar a asibiti in banda kuka ba abunda take a waya aka hadata da mr President tmbayar duniyan nan ya mata Amma Sam tace xaxxabi ne ke damunta...( Kutt...Ashe dama she is in love wit yaya bash eyya poor umaima๐Ÿ˜ฅ๐Ÿ˜ฅ....lolx๐Ÿ˜œ)
Bayan an bata magunguna aka sallameta Suka koma gida tare da masu kula da lfyarta, yan uwan mamanta se kira sukeyi suna mata sannu haka nan iyayen mr President ma sun kirata sun gaishe ta.

****†

D next day da yamma su shuairat Suka hada walima na mata xalla anyi nasiha sosai akan hakkin aure shukrah ko har kuka se da tayi shuairat na tsokanRta
BayN wani lokaci Suka raba Qur'an da handfan da kuma memo daga nan aka raba abinci sannan akayi adua aka watse.

Ran jumaa aka daura auren shukrah Abubakar da Basheer Bello maiha daurin auren ya samu jamaa sosai.da dare aka kai amarya gidan mijinta.
D next day akayi fansar amarya da ango sannan da dare aka sallami kawaye shikenan jamaa kowa ya watse.
       
    Shuairat CE tare da aminiyar tata tana bata yan shawarwari ynda xata xauna da mijin nata bash ne ya shigo tare da sallama shuairat CE ta amsa ya kalleta yace

"Ke me kike jira baki tafi gida bah"

   "Ho...yaya korata xakayi yau"

"Ehh mana ba dole bah
"Hmmm...lallai gashi nikuma se nayi 1week kafin....

"1me? Tabdi ba dai a nan gidan bah, idan kinji haushi kema ki shirya a daura muku ke da wancan tsohon"

"Yaya....tsoho fa kace! Se na gaya masa kuwa"
Yana dariya yace
"Yi hakri ur Excellency kada a dakatar da salary nah na 1month"
Haka dai Suka cigaba da tadinsu ckn xolayar juna shukrah de bata sa musu baki bah daga karshe shuairat ta musu sallama Yayan nata ya ajiyeta a gida shukrah kuwa se hawaye take ๐Ÿ˜ni Reefat nace ki gama kukan munafurcin ki bada kai bori ya hau


Ku biyoni ku sha labari๐Ÿ˜œ

*Reefat* CE .....love u alll๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
Hop kuna manage da hausar tawa๐Ÿ˜œ

[10/20, 8:19 AM] ‪+234 903 484 0427‬: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*30*
By *Reefat yahya*


Bayan sati daya da auren shukrah da bash Suka dugunxuma xuwa Abj shukrah tayi kukan rabuwa da iyaye da yan uwanta sosai.
Baba da mama flight Suka bi sannan bash shukrah da shuairat kuwa Suka bi hanyar mota.

Da yamma Suka iso garin shukrah ma tana kalle-kalle har Suka shiga gidan nasu bangaren yaya bash ta wuce sannan shuairat kuwa ta shige bangarensu.bayan sunyi wanka sun huta shukrah ta share bangaren tas ko'ina se Kelli yake ta kunna turaren wuta nan take qamshin ya gauraye gidan bash kuwa yana sauke baccin gajiya , shuairat CE ta shigo musu da abinci tare Suka ci nasu bayan ta ajiyewa bash nasa.

Bayan sallar magrib gaba daya Suka hallara a falonsu mama ana hira har da shukrah ta sake sosai a gidan bata daukesu a matsayin surukai ba, wayar bash ne ya fara ringing "umaima ! Ya gani a rubuce kwata2 ya manta da ita se kuma yaga be kyauta ba saboda be taba kiranta bah kuma bai gaya mata xaiyi aure bah.
Yayi picking tare da sallama ckn sanyin muryarta ta amsa tare da cewa
"Ina son ganinka yanxu"
Tana gama fadin haka ta kashe wayar.ya kurawa wayar ido sannan ya tashi yace
"Baba ana nema na a gidan mr President "
A dawo lfy Suka CE masa daga nan ya ficeTana xaune a falonta ita kadai sultan yayi bacci ta shigar dashi daki tana xaune ta buga uban tagumi ya shigo tare da sallama sanye yake ckn kananan kaya yana ta qamshi se shinning yake, suna hada ido ta fashe da kuka ai kuwa ya rikice ya xo kusa da ita ya xauna ya marairaice yace
"Umaima am sorry nasan ban kyauta bah na tafi ba tare da sallama ba"
Ta daga idanunta suna kallon juna se kuma ta sake sunkuyar da kai ta cigaba da kukanta har ckn ransa yana jin kukan Amma ya xaiyi? Ya lallabata amma taki dainawa.

"Umaima I said soryy naa kiyi hkri pls bana son jin kukan nan naki don Allah"
"Bash! Farkon haduwarmu da kai u promised dat xaka kula dani xaka xame min kadangar da xan jingina a kai ashe ba haka bane?
Bash har xaka iya aure baxaka sanar dani ba?
Damm...gabansa ya fadi, toh ya akayi tasan yayi aure?

"Kana mamakin ya akayi na sami labarin aurenka koh? Ba abin mamaki bane amma gskiya banji dadin hakan bah

"Am sorry umaima"

"Sorry 4wat? Sorry dat kayi aure ko sorry dat ka tafi baka sanar dani bah? O sory dat ka kasa cika alkawarin da ka dauka?

Carab! Suka hada ido, hawaye na diga tace

"Y basheer? U knw dat I kia a lot meyasa zaka min haka? But....

Kuka ne yaci karfinta ta kasa karasar da maganan da take a hnkli ya jawota jikinsa๐Ÿ˜ณ๐Ÿ™Š.....
Gam ta kamkameshi tana kuka me ban tausayi.
     Dakyar ya rarrasheta ta sagaita kukan

"Kiyi hakuri umaima auren ya xomin unexpected ne iyaye na Suka hadani da yarinyar wllhi ba wai...
Se kuma yayi shiru toh wai meyasa yake kokarin kare kansa ne?.

Shiru sukayi na Dan wani lokaci a hnkli ya daga kansa ga mamakinsa umaima har ta fara bacci haka Suka xauna har sunkai 1hr a xaune sannan ya xame jikinsa a hnkli ya kwantar da ita a saman kujerar 3str sannan ya fita ya shige motarsa ya kama hanyar gida.
    A hanya ma yana tuki yana tuna kalaman umaima da kuma halin da ta shiga toh meya bata mata rai? Kuma yaga alamar damuwa a tattare da ita ko meyake damunta ne
Oho! Nima nace oho!


๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜lov u alll
[10/20, 8:19 AM] ‪+234 903 484 0427‬: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*31*
By *Reefat yahya*


Shukrah ta gama shirin kwanciyarta ta hau gado ta kwanta bash ne ya shigo dakin tare da sallama ta amsa cki-cki a dole fushi take ya karasa kan gadon inda take kwance yana murmushi yace
" my wife fushi kike dani"

Ko uffan bata CE masa ta kirkiro wani guntun murmushi

"Am sorry kiyi hakuri "
"Uhmm..ba komai"

"Sure"
"Uhmm"

"Toh ki danyi murmushi mana"
Hakan kuwa ta sake masa murmushi yana dariya yace

"Daz my wife, tashi mu ci abinci toh"

"Na koshi"
"Pls mana " ya marairece hmmm bash akwai iya salo..lolx
Nan ta tashi ta xauna nama ne da exotic mai sanyi ya CE shi xai shiga wanka ta fara ci daga nan ya wuce dakinsa ya watsa ruwa tare da sa kayan baccinsa ya dawo ya sameta a inda ya barta.
Yana lallabata tana ci tana yauki๐Ÿ˜†๐Ÿ˜†  kamar bata so har Suka gama Suka kora da juice nasu se kuma Suka dawo falo ya kunna musu wani series film *walking death* suna kallo.

Shuairat kuwa 11pmta tashi daga bacci dama tun suna hira ita ta shige daki ta kwanta . falo ta nufa don yunwa take ji sai kuwa tayi saa foil pepa ta gani tana budewa taga nama a ciki nan ta hau ci se da ya isheta ta sha ruwa sannan ta koma dakinta xama tayi a carpet saboda bata jin bacci ta rasa me zatayi sai ta kunna data dinta watsap ta shiga mssgs Suka fara shigowa new number ta gani an tura mata hi"
Ta shiga ta ga num na online
"Helo!
Babu bata lokaci aka mata rply da
"Hw u"
"Fine alhamdulillh n u"

"Same"
"Eyya waye ne"
"New friend dinki ne princess maimah daga grp din gidan gyara "

"Aw Ayya am Ayshah"

"Nice meeting u"
"U too "
"Will like 2b ur kawa idan baxaki damu bah"

"Aww..really ! Naji dadi sosai u r welcm"

"Tnx ya gida yasu mum n ya yayanki da amaryarsa "

"Lfynsu lau..amma nayi fushi bakizo auren bruh bah"

"Eyya sory wllhi bana Adamawa ne daz y"

"Ok wane gari kike"

"Ina kd"
"Wow..daz gud"

"Ki ban labari toh" shuairat tayi murmushi tana jin dadin chat nasu da alama dai princess bata da girman kai sai tayi rply

"Me ya hana princess bacci ko dai tunanin prince ne๐Ÿ˜œ

"๐Ÿ˜ƒ๐Ÿ˜ƒlaaahh...wa ya gaya miki? Nayi bacci fah ynxu na farka shiyasa"

"Aww...just like me wllhi"

"Baxaki ban labari ba koh"

"Toh princess wane irin labari kike so"

"Ur love story"

"Lolx...wllhi ban taba yin soyayya bah "

"Ar u serious Ayshah? Nima haka wllhi"

"Meyasa toh"

"Babu fah kawai ban taba bah kuma Wanda nake so din yayi aure"

"Allah sarki๐Ÿ˜ฅ naki tausayin ki sorry"

"๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Štnx"
"Amma ya akayi kika bari yayi aure ko kun bata ne?

"๐Ÿ˜Šis a long story"

"Ok hard luck"

"Tnx" haka Suka cigaba da hira har 1 sannan Suka rabu kowacce ta kwanta .

Asuba ta gari first lady๐Ÿ‘๐Ÿผ๐Ÿ‘๐Ÿผ


Love u all๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
[10/20, 3:33 PM] ‪+234 814 884 9338‬: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*34*
By *Reefat yahya*


Ta xauna dirshan a kasa wani irin bakin ciki take ji bash ne ya shigo yana mata murmushi ta kawar da fuskarta gefe handkerchief ya fara mika mata ta karba ta share hawayen sannan ya tashi ya bude fridge ya dauko mata ruwa mai sanyi nan ma batayi gardama ba ta karbi goran ta shanye tana sauke numfashi a hnkli nan kuwa taji hnklinta ya kwanta

"Umaima kiyi hakuri I know hw u feel"

"Hakurin me xanyi basheer? Nasan laifi na ne ni nafara nemanta da fada but...
Kuka ta fara yi bash ya cije lebe yana tunani halinsu iri daya da shuairat se saurin hawaye ga Neman magana koda yake mata ma dukkansu suna son kuka

"Bash baxan jure ganin dad da wata bah a matsayin matar da xai aura, it always reminds me of my mom"

"But umaima ya xakiyi? Allah ne ya kaddara hakan y not kiyi hakuri ki xuba musu ido"

"But na kasa bash! I can't baxan jure ganinsu bah wai ma dad har soyayya yake da wannan yarinyar?

"Umaima...
"No bash! Kasan me yake bata min rai? Tun ynxu fah idan ta fadi Abu dad baya tsallakewa idan sunyi aure fah?

"Umaima don't worry kiyi hakuri komi xai daidaita , nide ki rage yawan fushin da kike yi pls kuma ki daina disrespecting din dad naki pls"

"Ok "
"Pls promise me dat baxaki kara fushi da dad bah"

"Ok I promise"
"_gud girl daz y I like u"

Murmushi take ita kadai tasan abunda take ji, haka bash ya xauna yana debe mata kewa daga karshe ya mata sallama ya tafi.waya ta cire ta kira wata yar mamanta bayan sun gaisa take shaida mata cewa dad nasu xeyi aure haka anty kadi ta bata hakuri akan cewa ta kwantar da hnklinta dama dole wata ran xeyi aure ko ba ynxu ba.


***********

Shuairat CE tare da shukrah suna xaune suna hira a falon shukrah ya shigo tare da sallama shukrah ta karbe jakan hannunsa shuairat ma ta masa sannu da dawowa yace

"Baby I don't like wat u did today"

"Yaya ba laifina bane"
"I know but da kin kyaleta kawai"

"Haba yaya ya xaayi...
"Baby kada ki manta aure xakiyi ki koma a gidan bai dace Ku fara samun matsala tun ynxu bah"

"Yaya kasan baxan taba barinta ta mare ni ba koh"

"Yes na sani kuma ki rage nuna gadara da iko a gaban mr President he deserve som respect , duk da bansan limit na soyayyarku bah"
Shiru sukayi suna kallon kallo shukrah CE ta fito daga ckn daki tana kallon halin da suke ciki tace

"Lfy? Meke faruwa?
"Ba komai bash ya bata amsa sannan ya tashi tayi shigewarsa daki ya barsu ta juya gun shuairat tace

"Bestie menene?

"Ki tamabayi mijinki "
Nan itama ta fice ta koma bangarensu dakinta ta shiga ta fada gado ta rike kanta
"Ya Allah Kaine gata na ka xabamin mafi alheri tsakanina da mr President " ta lumshe idonta nan ta fara tuna fuskar mr President farine Sol dogo mai matsakaicin jiki yana da saje da dimple gashin kansa baki mai laushi yana da shanyanyun idanu farare gashi nan so cool bai iya fada bah baya son hayaniya duk abunda tayi se ido kawai yake xuba mata baxai furta komai bah
"He is too young 4his age"
ta furta a hnkli se kuma tayi murmushi .

Hmmmmm *Reefat* tace
"Shuairat ar u in love???
Hmmmm muje xuwa


๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
[10/20, 3:34 PM] ‪+234 814 884 9338‬: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*33*
By *Reefat yahya*


Shuairat tana xaune a ofishinsu bodyguards Suka shigo Suka sanar da ita cewa mr President na bukatar ganinta ba tare da bata lokaci ba Suka fice tare.

     Yana xaune a dakin hutawarsa ta shigo tare da sallama ya amsa ba tare da kalleta bah yana rike da wani Dan karamin cup black coffee ne a ciki yana sha a hnkli , waje ta samu ta xauna shiru sukayi babu Wanda yayi magana har tsawon minti 10 shuairat CE ta gaji da xaman nasu tace

"Mr president ka aika a kirani ina aiki n u din say anytin"

"My first lady yaushe xaki koyi gaisuwa ne? Ko baki iya respecting magabatanki"

Wani irin kunya ne ya lullubeta amma bata son ya gane hakan tayi gyaran murya tmkar Mara gaskiya tace

"Emm...uhmmm sorry about dat actually...

"Is ok! Neva mind , anyway na kira ne saboda ina son sanin hukuncin da kika yanke ko kuma in CE shawarar da kikayi batun maganar da mukayi som few weeks ago"

Ya tare numfashimta tare da kura mata ido

"Mr president I don't knw wat to say about it"

"Look Ayshah lokaci yana tafiya ya kamata ki fito fili ki gaya min cos my dad is on his way soon kuma xancen auren ne xe kawo shi"

Shiru sukayi kowanne da tunanin da yake yi ckn sanyin murya shuairat tace
"Mr president idan nace baxan aure ka bah wat will b d outcome"
Murmushi yayi yana girgiza kai yace

"Funny girl! Me a ciki ? Kawqi ki fito ki gayawa yan jarida da sauran jamaa cewa karya kikayi tun da can ba abunda yake tsakanin mu kinyi hakan ne....
" mr President ya xakayi da ...

Hannu ya daga mata yace
"Don't worry about me, kawai ki fito ki gaya musu gaskiyan idan xaa cireni akan mulkin ma fine I don't kia n xanyi tunani akan abunda xan sanar wa mahaifina so kada ki sa damuwa a ranki"

Ta rintse ido ya ilahi wannan wace irin jaraba CE? Shin ya xatayi? Ta amince da auren ko kuwa ? Toh idan ta fito ta fadi gskiya tabbas jamaa xasu mata kallon mutuniyar banxa daga ita har mr President yanxu me abun yi? Muryan mr President ne ya katse mata tunani

"Ayshah u don't have to worry about me"

"About u? Mr President dis is about us ya shafeni ka gane koh?
Murmushi yayi yace

"Nasan ma kina son auren kina wani nokewa pls feel free Ayshah"
Ta daga idanunta Suka fada ckn nasa ta murguda masa baki tare da cewa

"Meyasa xan so auren tsoho ? Kawai de kai kafi bukatar auren ba ni bah"
Tana gama fadin haka ta juya tabar masa falon yana murmushi shi kadai.

A waje Suka ci karo da umaima kallon kallo Suka tsaya yi daga karshe shuairat tasa kai xata wuce umaima ta fisge hannunta da karfi
"Ina xaki je munafukar karuwa kawai kin xo kin like wa mahaifina daga ganin arxiki koh"

Wani shuumin murmushi shuairat ta sakar mata tare da cewa
"Karuwancin ma iyawa ne wata idan tayi ta samu kudi wata idan tace xatayi duka xata sha"

Hannu umaima ta daga da niyyar Marin shuairat cas ta cafke hannun tana murmushi ta nunata da yatsa
" yarinya kinyi kadan wannan fuskar ba kowane mahaluki bane xe iya taba shi ba kingane koh, n don't 4get saura kankanin lokaci na xame miki uwa "

"Har abada Baxaki taba xama matsayin uwa a gareni bah"
Nan kuwa umaima ta fara hawayen jin an ambaci sunan uwa ta tuna da mahaifiyarta shuairat ta sake mata hannu ta juya xata tafi umaima ta sake Jan gyalenta da karfi ta juya suna fuskantar juna tace

"Ke umaima kike ko wa ki shiga taitayinki ni ba Saar yinki bane da mahaifinki nake dealing ba da ke ba , so ki kiyaye"
Bash ne ya hangosu ckn Sauri yaxo ya shiga tsakaninsu umaima ta fashe da kuka dai2 nan mr President ya fito don ganin meke faruwa shuairat ta juya ta kakkabe gyalen ta fara tafiya sai kuma ta juya ckn gadara tace

"Mr president I tink ya'r ka bata da tarbiya yana da kyau ka sanar da ita cewa aurenmu yana nan xuwa bada dadewa bah xan dawo gidan nan da xama she shul learn how to respect me "

Mr President da bash baki Suka bude suna kallon shuairat wacce ta wuce direct gun mota aka bude mata ta shiga umaima kuwa ta fashe da sabon kukan bakin ciki dad nata ya juya xai mata magana ta daga masa hannu alamar cewa bata bukatar jin komi daga garesa , wani dogon numfashi yaja sun hada ido da bash ya masa nuni da ido akan yaje ya mata magana hakan kuwa akayi umaima ta koma bangarenta bash yabi ta baya.


๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜lov u all
[10/20, 3:34 PM] ‪+234 814 884 9338‬: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*35*
By *Reefat yahya*


Alh Mohammed mahaifin mr President ne yake saukowa daga benen jirgi ga nan jamaa da dama ciki kuwa harda mr President ga yan jarida birjik se daukansa hotuna suke mr President ya karasa ya rungumi mahaifin nasa ckn farin ciki ya rike shi a kafada suna dariya Suka wuce filin motocin da aka tanada musu convoy na motocin Suka dau hanyar xuwa gidan mr President.

       "Daddy nah I miss u so..much"

"I missed u too my boy"
Suna dariya bash ma yaso yin dariya Amma ya danne sarai mr President ya gane hakan se ya juya gun mahaifin nasa yace

"Daddy kaga wai kirani boy shine yake basu dariya"
Mahaifin nasa ya juya yana murmushi ya kalli bangaren da bash yake a gaban mota yace

"Yes! He is my boy cos shi kadai Allah ya bani kuma har ynxu ganin karamin yaro nake masa"
Murmushi sukayi haka Suka kasance har Suka karasa gida.
Umaima da sultan Suka fito da gudu Suka fada jikin kakan nasu yana dariyar jin dadi ya rungumesu sosai yaran na basa tausayi musamman idan ya tuna irin shakuwarsu da mahaifiyar tasu bayan sun shige katafaren falon mr President nan masu aiki Suka cika dinning da abinci kala2 ga yan xuwa barka da xuwa nan birjik bayan jamaa sun da tsagaita ne Suka wuce dinning table don cin abinci.
Mr President yana xaune kusa da mahaifinsa umaima kuwa tana gefen bangarensa na hagu sultan ne gefenta anyi serving dinsu kowa ya fara cin nasa, Alh Mohammed ne ya fara magana

"Son am so happy batun auren nan naka ka farantamin rai sosai"
Mr President ya fara tari daga nan ya dau ruwa yana kurba a hnkli sun hada ido da umaima ta kawar da fuska gefe.ya cigaba da cewa

"Dama naxo ne xancen auren naku , gobe xanje mu gana da iyayenta mu sa rana"

"Daddy y not...
"Boy bana son musu pls"

"Ok daddy Allah ya tabbatar da alkairi "

"Yawwa haka nake son ji.ynxu in banda abinka shkru nawa da rasuwar matarka amma ka kasa samun wata ko don yaran nan naka baka tunanin suna bukatar wacce xata debe musu kewa da rashin mahaifiyarsu?

Se ynxu umaima ta sa baki
"Granny mu bamu da matsala idan sultan ne kuwa yana da nannies masu kula dashi ba sai ya auro wata ya kawo bah"

"Oho! Ynxu nagane me  yake hanaka aure wato wannn ja'irar ya'r taka ce bata son kayi aure koh? Toh karya kike umaima aure kam dole sai yayi kuma nan ba da dadewa bah"

"Daddy pls..
"Rufemin baki, baka da abunda xaka gaya min.Amma ka bani mamaki wallahi "

"Daddy plsss...
Fuu..umaima ta tashi ta bar falon ta tafi bangarenta Alh Mohammed ya juya yana kallon Dan nasa yace

"Boy! Irin tarbiyar yaranka kenan? Gaskiya nayi mamakin ganin haka a ckn gidanka son.kai kadai Allah ya bamu mun dauka son duniya mun dora a kanka amma hakan bai hanamu baka tarbiya mai kyau bah but y?

"Daddy am sorry wllhi umaima bata jin magana na ban....

"Quiet! Boy...kai ka haifeta ko ita ta haifo ka? Which one? Tell me!

"Daddy am sorry"
Mr President ya marairaice tmkar xeyi kuka nan kuwa mahaifin nasa yaji tausayinsa yasan sarai Suleiman be iya fada bah he is too cool shiyasa umaima take yin abunda ta ga dama can yace

"Ok son! Gobe insha Allah xan gana da mahaifin yarinyar xaa saka ranar aurenku nan ba da jimawa bah, aurenka na fari ni na xaba maka matar da ka aure n dis tym ka kawo wacce kake so dole xan jajirce don ganin na cika maka burinka.Allah ya bada xaman lfy insha Allah wannan yarinyar xata xame mana alkairi xata kawo farinciki a rayuwarka believe me son"
Yana magana yana kallonsa bayan ya gama ya tashi yayi shigewarsa dakin da ya saba sauka duk lokacin da ya kawo musu xiyara.sultan yabi bayan kakan nasa  aka bar mr President shi kadai a xaune yasa abinci a gaba yana tuna kalaman mahaifinsa "shin da gaske Aysha xata kawo farinciki a rayuwarsa? How? Meyasa daddy ya fadi haka?

Hmmmmm..... Ya xata kaya tsakaninsu?
Muje xuwa

๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
[10/20, 3:35 PM] ‪+234 814 884 9338‬: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*36*
By *Reefat yahya*


Mr President ne xaune a falonsa yayi nisa ckn tunani bash ya shigo tare da sallama

"Mr president sir!
Firgigit ya motsa a hnkli yace

"Ehmm...basheer pls ina son ka kai daddy na gidansu Ayshah Bello"
Jim bash ya tsaya yayi shiru se kuma yace
"Ok sir!
Daga nan yayi waje wayarsa ya fitar yayi dialing din numbar mama ckn kankanin lokaci ta daga tare da sallama

"Mama ya gajiya"
"Lfy ya aiki"
"Alhamdulillh, dama mahaifin mr President ne zaizo Neman auren baby ynxu haka xamu taho tare shine nace bari na sanar daku"

"Tohh! Ikon Allah , dama shuairat ta daidaita da shugabankasa shine bata gaya mana bah?

"Mama kada ki sa damuwa a ranki kawai ki sanar da baba gamu nan xuwa yanxu"
Ya katse wayar a dai2 nan daddy ya fito yasha many an kaya se uban qamshi ke tashi bash ya fara soshe 2 kamar Mara gaskiya daga nan aka bude musu mota Suka dau hanyar kubuwa xuwa gidansu shuairat. Bash ya turawa matarsa text akan ta tanadi kayan motsa baki danginsu snacks da fruits se kuma lemuka masu sanyi ya sanar da ita gasu nan a hanya yana tare da manyan baki.

Baba da mama suna xaune a falo mamakin alamarin sukeyi domin basu taba tunanin cewa mr President xe auri ya'rsu bah suna nan xaune suka ji dirar motoci a kofar gidan bash ne ya sauka da sunan zeyi sallama don a basu ixinin shiga ya tura kofar gidan a hnkli yasa kai a ciki (basu San cewa gidansu bane lol) bayan kankanin lokaci  ya fito ya shaidawa daddy ya fito nan Suka shiga har falon baba yana xaune shi kadai daga nan bash ya bar musu falon...
Bayan sun gaisa nan Suka fara hira tamkar sun Dade da sanin juna daddy ya shaidawa baba kan cewa shi Dan jahar Adamawa ne haka nan shima ya gaya masa shi Dan Adamawa ne sosai sunyi hira harda dariya tamkar sun saba da juna tun asali
Shukrah CE ta shigo tare da sallama ckn ntswa ta gabatar da kayan motsa baki bayan sun gaisa ta sa kai ta fice ta koma bangarenta bayan wani Dan lokaci mama ta fito Suka gaisa da daddy sannan ta koma ckn daki daga nan daddy ya gabatar da bukatarsa na Neman auren shuairat baba yayi shiru can kuma yace

"Alh da zaka bani lokaci zan...

"Haba Alh bello ai anzama daya, kuma yaran nan suna son juna tunda sun fito fili sun bayyana hakan.kuma shi yaron matarsa ta Dade da rasuwa munyi iya bakin kokarinmu ya kara aure amma Sam yaki, don haka ina rokonka ka taimaka ka bamu ya'rka tunda de sun daidaita suna kaunar juna"

"Alh Muhammad bawai zan hanaku bane, kasan shaanin yara"

"Haba Alh..Suleiman fah ba yaro mana shekarunsa 40 da doriya na tabbata xai rike ya'rka bisa gaskiya da amana , nidai burina ka amince mu sanya musu albarka kuma in son samu ne a daura auren nan da sati 2 masu xuwa"

"Ahhh..abun ma da wuri haka ne?

"Ehh mana..burina shine ka amince batun wani shiri koma menene bai taso bah ba se ansiya mata komai ba ni xanyi kayan daki da duk wani abunda zaa bukata na auren"

"Haba Alh Muhammad bazaayi haka bah"

"Alh bello bazaka gane farinciki da nake ciki bah, Suleiman shi kadai Allah ya bani a duniya burina shine naga ya tara min jikoki dayawa se kuma Allah ya kaddara matarsa ta haifi yara2 ta bar duniya.don haka nake son ayi wannan auren da wuri ko Allah zaisa da rabo a ciki"
Baba yayi shiru yana naxarin kalaman daddy

"Kayi shiru Alh bello, kada ka manta yanxu mun xama yan uwan juna fah " ya fada yana dariya baba yace

"Shikenan Allah ya tabbatar da alheri ya basu zuria ta gari masu albarka"

"Ameen yanzu naji magana! Nagode sosai ALh bello Allah yabar xumunci ya saka da alheri" nan ya xare bundir na yan dubu sabbi fil har bandur 3 ya ajiye a gaban baba

"Me wannan Alh Muhammad? Kaga abunda bana so kenan, ni ban nemi koda sisi ba daga gareku don Allah ka maida shi kuma auren nasu idan yazo bana son almubazzaranci a kimanta komi a yishi  dai2 gwargwado nasan kuna da kudi amma ni bana son hakan"

"Alh Bello jahar mu daya da kai kasan al-adunmu na Adamawa idan anzo Neman aure da goro ake xuwa , nikuma ban siyeshi ba saboda ina marmarin xuwa don haka wannan kudin goron Neman aurene ba komai bah"

"Nasan da hakan Amma na yafe"

"Aa'a bazamuyi haka da kai bah alada CE dole sai anyi , batun almubazzaranci kuma insha Allah bazaayi bah na maka alkawarin hakan"

Baba ya xare bandir daya ya maida sauran yace

"Allah yayi albarka ya sanya alheri nagode"

"Sauran kudin fah Alh"

"No! Wannan ma yayi yawa kawai bana son gardama ne"

"Toh nagode sosai Alh bello se a fara shirin daurin aure nagode sosai"
Nan sukayi musabaha baba ya rakashi har bakin mota sukayi sallama driver ya ja a yayinda bash yake zaune a gefe Suka dau hanyar gidan mr President.


Hmmmmmm.muje xuwa
[10/20, 3:35 PM] ‪+234 814 884 9338‬: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*38*
By *Reefat yahya*


Mr President tare da daddy da sultan suna cin abincin dare a dinning table na bangaren mr President umaima kuwa taki xuwa a dole wai tana fushi daddy ne ya fara magana

"Boy u ar lucky wallhi surukinka mutumin kirki after ol Dan Adamawa ne"

"๐Ÿ˜ณ ..uhmmm ehh dad namanta ne ban gaya maka cewa shi Dan Adamawa ne ba "
Lallai shi da bai taba xuwa gidan surukan nasa bah ina zai San halayensu...

"Boy kana ji nah"
"Ehh..ina jinka daddy"
" idan na koma zanyi magana da momsin ka batun hada lefe xatayi magana da sakeena ya'r wanta wacce take business na kaya zaa hada komai a kawo daga nan sai a kai gidan nasu koh"

"Ok daddy nagode but da nace kudi zan bata ta siya da kanta"

"No! Mu zamu siya komai kuma babanta yace baya son almubazzaranci saboda haka komai dai2 gwargwado zaayi"

"Ok daddy nagode Allah ya kara tsawon rai "
"Ameen! Auren naku nan da 3weeks ne"
๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณwani tari ne yaxo masa wani bugun xuciya yaji...damm

"Boy ar u ok!
"Ehm..umm.am ok daddy am am fine"
Gub...gub haka xuciyarsa ya cigaba da bugawa innalillahi kawai yake maimaitawa can yaji muryan daddynsa na cewa
"Sultan tashi muje muyi hiranmu koh kasan gobe jirgin 7 zanbi insha Allah"
Daga nan Suka tafi aka barshi shi kadai nan ya fada duniyar tunani ....yanxu da gaske aure zaiyi? Ya zasu kaya da umaima? Ya zaman nasu zai kasance? Shuairat zata zauna lafiya ta rike masa sultan ? Anya xai iya kallonta a matsayin mata? Wace irin rayuwa zasu yi? Hmmm lallai yana da babban aiki a gabansa...haka dai ya cigaba da tunane tunanensa..****************
Shuairat CE xaune a gaban dressing mirror tayi jugum tana tunani wai ynxu da gaske aure zatayi? Mr President xata aura? Ze iya bata romantic lyf da ta Dade tana mafarkin samu? Zai iya kallonta a matsayin matarsa? Zata iya zama da umaima da sultan? Ya rayuwarta zai kasance? Ya.....
Bude kofar dakin da akayi ne ya dawo da ita daga kogin tunanin da take mama CE rike da waya a hannunta ta mika mata

"Hajiya mairo xata miki magana"

"Ok" nan ta sa hannu ta karba ta kara a kunne tare da sallama
"Ina yini anti"
"Lfy my baby ya kike ya aiki"

"Lfy alhamdulillh"
"Baby nah magana xamuyi ta fahimtar juna"

"Ok anti ina jinki"

"Mama ta gaya min halin da kike ciki Amma ina son ki kwantar da hankalinki ki gane cewa aure nufi ne na Allah kuma matar mutum kabarinsa ki daure ki amince da zabin da Allah ya miki alkairi ne insha Allah, ki sake ranki ki cigaba da activities dinki kinji?

"Ok anti nagode"

"Ki kwantar da hankalinki munyi magana da yayanki zai sama miki ticket ki bi flight gobe kixo Kano gida kinji"

"Ok anti tnxx"

"Yawwa my baby takkia sai na ganki koh"

"Ok anti bye"daga nan ta mikawa mama wayar ta kashe ta juya suna fuskantar juna mama tace

"Ki shirya kayanki gobe jirgin safe zaki bi ki tafi Kano "

"Ok mama "
"Batun events kuma walimah kadai ya wadatar ko kuwa akwai program da zaki yi"

"Walima is ok "
"Toh shikenan ki fara shirya kayanki yanxu"
"Ok toh" daga nan mama ta bar dakin shuairat ta hada kayanata kala10 a travelling bag bayan ta gama se ta shiga watsap mssgs Suka shigo dama ta kwana2 bata shiga bah. Mssg din princess maimah ta gani

"Hi dear fren ya kike
"Fyn " ta mata reply tana online dat tym se ta tura
"Wia have u bin shiru 2days"

"Ina nan just busy ya gida n evrtin"

"Fine alhamdulillh kawai gt a little prblm wit dad ne"

"๐Ÿ˜ณur dad? Haba y?

Nan ta gaya mata abunda ya hadasu shuairat tace

"Haba kawa ba kyau fushi da iyaye"

"Ok tanx xan kiyaye next tym"
murmushi princess tayi a dayan bangaren a xuciya tace she is just like her bro.haka Suka cigaba da chat nasu har na tsawon lokaci sannan sukayi sallama.Ku biyoni....๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
[10/20, 3:35 PM] ‪+234 814 884 9338‬: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*37*
By *Reefat yahya*


Shuairat tana xaune a ofishinsu ta buga uban tagumi wayarta CE ta hau ruri numban mama ta gani ckn mamaki ta daga sabida mama bata taba kiranta ba muddin tana wajen aiki
"Hello mamana"
"Baby kizo gida yanxu"
"Lfy dai koh?
"Kizo ina jiranki"
Ta kashe wayar tayi jugum se kuma ta tashi ta fara harhada takardunta bayan ta gama tayiwa Sarah sallama akan cewa ana nemanta a gida carab Suka hada ido da Mahmud yayi sauri kauda fuskarsa gefe taku biyu tayi ta karasa inda yake

"Mahmud ina son yin magana da kai"

"Sorry am busy"

"I knw but maganar is very important"
Ba gardama ya tashi Suka fita waje

"Mahmud wane laifi nayi to deserve dis?

"Bangane bah ! Wani Abu ne ya faru?

"Mahmud pls ka gaya min me namaka plss...

"Shuairat baki min komai bah"yana gama fadin haka ya juya ya koma ciki ya barta nan tsaye tsaki taja ckn jin haushin kanta wato ma har wani rigima yake mata mtswww...
Nan ta tare taxi ta kama hanyar gida.

Mama CE zaune a dakinta tayi shiru tana tunannin kalaman aminiyarta Hajiya mairo
"Amina ki godewa Allah da irin kyautar da ya baki ki kwantar da hankalinki , ai wannan shine arxiki na binka kana gudunsa idan ba haka ba waye xaiki amincewa da auren shugabankasa? Kawai ki nusar da shuairat ki gyarata sosai ki koya mata dabarun xama da miji ba wani batun ya tsufah ki manta da zancen shekaru ki tashi tsaye ki nemawa ya'rki hanyar da xatabi ta zauna da mijinta lfy wannan shine abunda ya dace kiyi tagumi ko tunani ba naki bane"....shuairat CE ta katse mata tunani ta shigo tare da sallama ta fada jikinta tana juyi

"Oh mama! Kin tsoratani I tot wani Abu ne ya sameki tank God u ar fine"
Murmushi mama tayi tace
"Lfy ta kalau na kiraki ne ina son muyi magana"

"Go ahead ina jinki"
"Dazun nan mahaifin shugabankasa ya bar nan, ya zo Neman aurenki"
Dumm...xuciyarta ta buga nan ta tashi xaune

"Waat? Neman aurena? Me baba yace masa?
"Me zai fada kuwa an saka ranan auren nan da...

"No! Mama it can't b nikam baxan auri tsoho bah"

"Aww really? Bazaki auri tsoho ba kika fito gaban dubban jamaa kika bayyana cewa kuna soyayya? Kiyi amfani da hankalinki shuairat ke fa kika amince masa ya turo iyayensa me kika maida mu?

"Haba..mama kinfa San komai akan alamarin nan na gaya miki yanda abun ya faru kuma wllhi bamu taba wani xancen soyayya dashi bah ..ni ..ni"
Se kuma ta fara kuka
Mama ta tabe baki tace
"Kanki ake ji yarinya da can wani ne ya turaki kika CE kuna kaunar junanku? Ko a wancan lokacin baki San shi tsoho bane se yanxu? Bazaki maidamu mutanen banza bah bari kiji gara ma ki saita kanki kisan abunda kikeyi"
Nan mama ta tashi ta bar mata dakin shuairat ta nemi hawayen ta rasa๐Ÿ˜†๐Ÿ˜† da can ta dauka mama xata rarrasheta ne aikuwa ta tashi ta nufi bangaren shukrah a falo ta sameta tana buga game
"Yadai mutuniyar"

"Mtswww...wato kina xaune ckn kwanciyar hnkli baki damu da halin da nake ciki ba koh"

"Me ya faru bestie" shukrah ta fada a yayinda take ajiye wayar hannunta ta gyara xama
Shuairat ta tura baki tace
"Kina ji wai daddyn mr President yaxo neman aure nah"

"๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณkai ...dama shine yaxo gun baba dazun nan?

"Mstsww...ke ana serious kina wani mtsww

"Yi hakuri bestie dama kina soyayya da mr President ne baki taba gaya min bah"

"Allah na! Shukrah! Haba try to understand mana haaa da muna son juna xan damune ?๐Ÿ˜๐Ÿ˜

"Okkk...calmdown n tell me meyake faruwa"
Nan shuairat ta kwashe labarin kaf ta gaya mata murmushi shukrah tayi tace
"Trust me kuna son junanku just dat Baku fahimci hakan bane but wit tym...

"Hey hang it girl! Ar u kidding me? Ya zan fara soyayya da tsoho ne ..yurk! U know I can't "

"Babe baki gane ....
"Pls bestie stop it! Shi tsoho ne bai San me ake cewa love bah n shima ya gaya min bai taba yi bah"

"Tsoho? Ya kai 80 ne?
"Ahh..haba he is 40+"

"Hmmm bestie he is still young u can handle it, waima lemmi ask u salman khan na Indian film shekarunsa nawa?
"40+"

"Wat of sharukh khan?
"40+"
"Akshay kumar fah?
"๐Ÿ™„๐Ÿ™„๐Ÿ™„ shima haka"
"Me zasu nunawa mr President? Kyau? Ilimi ko arziki? Hey girl wake up! Mata nawa suke neman mutanen da basu kai mr President bah? About 1000+ n duk fadin duniya babu macen da zata ki auren mr President but y bestie? Kiyi aiki da brain naki pls ke da kanki kika CE he is so cool..meyafi hakan toh namiji kyakkyawa ga ilimi ga hankali ga tausayi ga arixizi ga ga ...komai ya tara me laifinsa? N tell me ke din kintaba son wani namiji? Maza nawa Suka so ki Amma baki sauraresu bah kinga kenan Allah ne ya hadaku shi bai taba soyayya ba kema haka kiyi tunani akai shuairat u can do it u can handle it after all u ar a lady ni kaina ke kika koyamin wasu abubuwa da dama y not kiyi amfani da su? Ki zauna da kyau kiyi tunani"
Daga nan shukrah ta tashi ta shige kitchen ta bar shuairat da dogon tunani akan kalamanta...Hmmmmm
[10/20, 3:35 PM] ‪+234 814 884 9338‬: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*39*
By *Reefat yahya*


A airport mr President yayi sallama da mahaifinsa yana rike da hannun sultan suna dagawa daddy hannu har sun juya xasu tafi daddy ya sake dawowa gun mr President yace

"Boy is gud kaje ka gaida surukinka"

"Ok daddy xan samu lokaci"

"No! Son xanso ace yau xaka je"

"Ok insha Allah zanje"
"Ok gud na tafi sai munyi waya"

"Safe trip a gaisheda momsi"

"Ok zata ji" daga nan mr President ya ja hannun sultan Suka shiga mota Suka kama hanyar gida.
     Da yamma misalin karfe 4:30 mr President yasha manyan kaya se qamshin turare ke tashi an jera motoci bash na gidan gaba tare da driver a yayinda mr President ke xaune a gidan baya hannunsa rike da magazine yana karantawa , a kofar gidansu shuairat akayi parking na motocin dama can baba ya San da xuwan surukin nasa batare da bata lokaciba Suka shiga ckn gidan bodyguards Suka tsaya a waje bash na gaba mr President na biye dashi.baba na xaune a falo Suka shigo tare da sallama bayan sun gaisa an jerawa mr President kayan marmari iri2 Amma ko ruwa bai iya ya sha bah saboda kunyan baba yake ji, basuyi wani dogon hira bah shiru Suka yi tamkar babu kowa a falon chan baba ya daure yace

"Duk da naji cewa kana kaunar ya'ta amma don Allah ina rokonka ka riketa bisa gaskiya da amana bana son wani Abu ya sameta"

"Insha Allah baba na dau alkawarin kula da ita babu abunda zai taba ta "

"Nagode! Allah ya Baku zaman lafiya da zuria mai albarka"

"Ameen" mr President ya amsa ckn jin kunya daga nan mama ta fito Suka gaisa ta koma ciki ta barsu, haka nan sukayi sallama mr President ya tafi sannan bash ya shigo da bandir din kudade ya ajiyewa baba shi kuma se fada yakeyi wai akan me bash xe karbi kudin bai sauraresa ba yayi ficewarsa saboda ana jiransa a waje xasu koma gidan mr President.


*******************
Shuairat CE zaune a dakin da aka sauketa a can Kano ta ajiye kazar da ta sha hadin magunguna a gaba ta rasa ya xata fara cinsa gashi ta taba ta jishi ba dadi anti mairo CE ta shigo tare da sallama

"Lalala..baby har yanxu baki cinye bah? Gaskiya xamu bata dake"
ta tura baki tare da yatsina fuska tace

"Allah anti ba dadi bazan iya ci bah"

"Baby ki daure haka ki ci if not xamu bata oya ..now "
Haka tasa shuairat a gaba dole ta cinyeshi tass tana maida numfashi dakyar.bayan ta huta kadan mai gyaran jiki ta fara tata aikin haka Suka yini ranar gaba daya se gyarata ake yi har dare bata huta bah wani hadin tsimi aka bata dole ta shanye.
     Misalin 9:00pm ta watsa ruwa tayi shirin bacci kenan ta kwanta a gado dama dakin ita kadai CE a ciki ta bude data mssgs na watsapp dinta Suka fara shigowa se kuma wayar ta fara ringing sabuwar num ne kuma special har ya kusan tsinkewa sannan ya daga ta kara a kunne tare da sallama

"Hey reporter ina kika je ? Wato baki xaman gida koh?

"Pls who is on d line?
"Baki ban amsa bah"

"Mr president?
"Baki xaman gida ina kike xuwa?

"Mr president ko kamanta cewa am a reporter so I have....

"Luk Ayshah daga yau nayi banning duk fitanki har xuwa ranar daurin auren"

"Aww..da gaske?
"Tambaya kike? Dont u have som respect?

"Umm..am sorry"
Shiru sukayi dukkansu biyu kowannensu ya rasa abun fada daga karshe ya kashe wayar.daga can bangarensa tunani yake meyasa ma ya kirata? Kuma idan tana fita ma meyasa zai damu? Daya bangaren xuciyarsa yace of coz matata tace dole na damu, no! I don't have too" shiii...ya sunkuyar da kai yana tunani ya kasa samun amsa ko daya.shuairat ma haka abun ya kasance mata ta kurawa wayar ido tana tunani daga karshe ta share maganar kawai ta shiga watsapp dinta Suka fara chatting da princess maimah da kuma shukrah.


Ku biyoni....
Love u all ๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
[10/20, 3:36 PM] ‪+234 814 884 9338‬: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*40*
BY *Reefat yahya*


Bayan sati daya aka kawo lefen shuairat mata biyu ne kacal Suka xo anyi musu kyakkyawar tarba an karbesu ckn mutunci akwati set 2 ne cike makil da kaya masu kyau Wanda bazan iya siffantasu ba sai dai masu karatu su kimanta da kansu๐Ÿ˜œ daga karshe sukayi sallama Suka tafi bayan an cikasu da snacks da drinks kala2.shukrah kam se santin kayan take xubawa aikuwa tayi snapping ta tura a instagram da watsapp cewa ga kayan lefen aminiyarta amma bata bayyana cewa mr President ne xai aureta. Shuairat ma ta yaba da kayan sunyi kyau ba karya , shirye shiryen biki ake Amma mr President ya hana duk wasu programs da zaayi ciki kuwa har fansan amarya yace bayaso sabida yasan yan gulma zasu cika wajen shuairat CE zatayi walima shikenan.


****************

"Umaima lfynki kuwa? Yarinya kin dau karan tsana kika dora akan mahaifinki bayan kinsan Allah ne ya hallata masa auren kin isa ki hana ne?

"Wllhi anti khady wannan cin amana ne yanxu shekaru nawa ne da rasuwar mom amma har ya manta da ita? Se kuma ta cigaba da kukanta anti khady ta sake baki tana kallonta sannan ta cigaba da cewa

"Nidai baxan goyi bayanki ba umaima wannan ai rashin gaskiya CE , Allah ya halasta masa auren mata 4 ke kice baki so yayi auren? So kike ya kare rayuwarsa haka?

"Anti kinga yarinyar karamace fah wllhi tun bata shigo ba ya daina kulamu kuma...

"Ki bude kunnuwanki kiji abunda zan gaya miki, ki tashi ki koma ki bawa mahaifinki hakuri ki rungumi kaddara ki xauna lafiya da matarsa Allah ne ya kaddara baki isa ki hana bah "

"Gaskiya nikam baxan iya bah, ynxu dama duk son da yakewa mom ya...

"Dakata umaima bari kiji labarin da baki taba ji bah, dad da mom dinku auren xumunci aka hadasu dad naku ba shi ya nemi auren mom naku bah biyayyace ta sa ya amince ya aurota har Suka xauna tsawon xaman da sukayi.dad dinku bai taba yin soyayya a rayuwarsa bah kuma....

"Wait..an..anti kina nufin duk xaman da sukayi babu soyayya a tsakaninsu?

"Bansani ba umaima Allah shine masani nidai nasan dad mutumin kirki ne yana da kara sosai har gobe baraa sami yaro mai biyayya irinsa bah a duk fadin danginmu"
Shiru umaima tayi tana tunani kanta ya kulle kwakwalwarta ya to she anti kady CE ta dafata a kafada tace

"Kiyi hakuri ya'ta nasan kina taya mom naki kishi but koda ace tana raye itama bata da ikon hana wannan auren kiyi hakuri ki shirya ki koma gun mahifinki"

"Zan koma amma ba yanxu bah, sai bayan bikin nasu "

"Shikenan xan kira dad na fada masa kada ya tada hankalinsa gun nemanki "

"Ok anti nagode"
Haka ta cigaba da xubda hawaye tana jin wani radadi a ckn xuciyarta.


*********
Shuairat CE a gaban dressing mirror tana kallon kanta tabbas ta canza ba kadan bah fatar jikinta se sheki yake ga gashin kanta da ya sha gyara se kuma dadaddan qamshin da yake tashi a jikinta murmushi tayi a yayinda ta cigaba da kallon fuskarta tana admiring din kanta lallai mr President yayi dace๐Ÿ˜€๐Ÿ˜€tunaninsa ne ya fado mata a rai fuskarsa ta hango , kyakkyawan karshene ita kanta tasan da hakan kuma yana da karamin ruwa idan bakasan shrkarunsa xaka CE Dan shekara 32 ne ta lumshe ido tana tuna farkon haduwarsu yana magana so cool yana da class sosai kuma yana da tausayi musamman idan ta tuna ranar da ya share mata hawaye lokacin da take kuka, shin zata iya soyayya dashi? Anya kuwa? Hmmmm ko kadan bata taba mafarkin cewa taxa auri babban mutum kamarsa bah sai kuma rayuwarta na baya ya fara dawo mata a kwakwalwa.....


Muje xuwa....
*Reefat*
[10/20, 3:36 PM] ‪+234 814 884 9338‬: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*41*
By *Reefat yahya*


*wacece shuairat*???

Alh Bello mamman hafaffen garin maiha ne na jahar Adamawa su hudu ne a gun iyayensu Ahmadu Salihu bello da kuma zainabu a can garin maiha aka haifesu duka amma shi bello ya koma garin mubi da xama gun wan mahaifinsa a can yayi primary da secondary sannan ya wuce jamia ta bayero Kano a can ya karanta bangaren education, bayan ya gama ya dawo gida a Yola yayi bautar kasa a wannan lokacin ne ya hadu da Fatima ya'r layinsu mahaifinta ne limamin unguwarsu a can karamar hukumar maiha ta jihar Adamawa.
          Bayan ya gama bautar kasa akayi aurensu da Fatima shi kuma ya samu aikin koyarwa a makarantar secondary na technical school a can mubi.Bello da Fatima suna son juna sosai kullum suna cike da begen juma haka Suka xauna ckn rufin asiri , sun share sama da shekara 6 Allah bai basu haihuwa bah amma duk da haka bello bai taba nuna damuwarsa bah, Fatima tayi2 ya kara aure yaki sauraranta har ta gaji don kanta ta daina kawo masa xancen.kwatsam Allah ya bata ciki sunyi murna sosai hKa Suka kasance ckn farin ciki har Allah yasa ckn ya cika wata9 da yan kwanaki Fatima ta haifi kyakkyawan danta fari tas babu inda ya bar fuskarta cki kuwa har hasken fata saboda Fatima fara CE sosai, ranar suna yaro yaci suna Basheer.

Haka Suka cigaba da rainonsa har ya girma yayi wayo aka sashi makarantar firamari har ya gama Allah be kara basu wani rabon bah , basheer ya gama primary ya shiga secondary har ya kai ss1 sannan Allah ya bawa Fatima wani ckn batun murna kam baa magana basheer duk yafi xumudi akan cikin kullum hirarsa be wuce xancen a haifa masa kanwa ya'r kyakkyawa.
Bayan wata9 ciff Fatima ta haifi kyakkyawar ya'rta wacce tayi kama da bello tamkar anyi kaki an tofar yarinyar baka CE Amma ba sosai bah tana da Dan hasken fatA , haka aka saka mata suna Aisha ana kiranta shuairat.
   Shuairat ta tashi ckn gata gaba da baya koina sonta ake musamman yayanta basheer baya barin kowa ya taba ta, a wannan lokacin Alh bello yana koyarwa a jamiar federal university of technology Yola. Daga kan shuairat haihuwa ta tsaya musu cak da wannan lokacin ko bari Fatima bata sake yi bah, haka Suka rungumi yara biyun da da Allah ya basu.bash ya gama secondary dakyar ya yarda ya tafi jamia wai shi baya son ya tafi ya bar kanwarsa dakyar aka lallabashi ya tafi jamiar  Ahmadu bello zaria bayan ya kammala ya dawo yayi bautar kasa sai kuma aka daukesa aiki da state security service , shekaru sun gabata Alh bello yayi retire ya koma gida yana hutawa se kuma dansa ya samu canjin aiki xuwa fadar shugabankasa a wannan lokacin ne shuairat take Jin karshe a federal polytechnic dake can mubi har ta samu ta kammala inda ta karanta bangaren mass communication...
Wannan kenan shine takaitaccen tarihin rayuwarta.

A hnkli ta ja wani gauron numfashi kamar a mafarki take ganin duk abubuwan da suke faruwa a rayuwarta "ikon Allah kenan"
ta furta a hankali ynxu matsalarta shine ya xata fara nunawa mr President so? Anya zai kulata kuwa? Wane irin zama zatayi da umaima? Tabbas tana da aiki a gaba idan batayi da gaske ba xata fuskanci matsala a gidan wayarta ta hau ruri sunan shukrah ta gani nan ta daga
"Matar Yayan"
"Amarya bakya laifi ko kin kashe Dan masu gida"

"Lallai sai dai idan baa kashe din bah , ya kike ya gidan"
"Lfy lau yaushe zaki dawo"

"Umm..kinyi missing dina ne "
"Bani kadai ba harda angon mah"

"Bangane bah"
"Ehh..mana wai dama baki gaya mishi zakiyi tafiya bane?

"Y? Meyasa xan gaya masa?
"Hmm...dazu ya tura bodyguards wai yana son ganinki"

"Uhmm..yayi kyau"
"Munafuka kina so kina nokewa"
"Ehh..sai akayi yaya"

"Nidai ki dawo da wuri kan a buga mana news paper cewa mr President yana Kano"
"Wannan kuma maysalrku "

"Uhmmm..in tayi tsami ma ji"
"Babu abunda zakuji"

"Se anjima toh "
"Ok bye sai na kira "
"Ok takkia"
Tare Suka katse wayar shuairat tayi jugum tana tunani lfy mr President yake Neman ganinta?
Oho!


Nima nace oho! Ku biyoni

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *