Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, 17 June 2019

Tudun Dafawa Complete hausa novels world

adsense here
Tudun Dafawa Complete hausa novels world

Tudun Dafawa Complete hausa novels world


[11/30/2016, 5:07 PM] Ummieejaafar
    *TUDUN DAFAWA*


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar  
                   *01*

"Dan Allah kiyi hakuri Umma,wallahi ba da sani na ya fashe bah",Bilkisu take cewa cikin shesshekan kuka..
   Wacce ta kira da Umma kuwa sai zabga mata bulala take yi ba kakkautawa,"Wallahi sai na ci uban ki yau da uwar ki da ta ke kwance a dakin can,shegiya 'yar iska,ki fasa min tulu sannan kice ba da sanin ki ba!,ja'ira kawai",sannan ta daina dukan ta sai huci take faman yi kaman zaki kana ta shige dakin ta ta bar Bilkisu a wurin..

 *Bilkisu
Yarinya ce 'yar kimanin shekara goma sha biyu a duniya.Baka ce amma irin _'black beauty'_ din nan neh..Tana da suma mai dan tsayi da kuma idanuwa fici fici kanana...
     Sunan mahaifinta Mal. Idrisu Maikwano,mahaifiyarta kuma Malama Lami Madaki,sannan da uwargidan baban su, Jummai(Umma)wacce dalilin rashin haihuwan ta,Mal ya auro maman Bilkisu...
      Suna da zama ne a kauyen Gurmana dake Minna,Niger state...Mahaifin ta yana sana'ar kera kwanuka neh shiyasa aka fi sanin sa da Mal. Idrisu Mai kwano..Mahaifiyarta kuwa tana yin cin cin neh na siyarwa a da kafin ta fara rashin lafiya bayan ta haifa Bilkisu,tana haifan ta ta fita hayyacin ta,ba ta cewa uhm bare uh'uhm,kullum tana kwance a daki,Mal. ne mai tallafa mata har Bilkisu ta danyi wayo a hannun kishiyan ta,Umma sannan Bilkisu ta fara renon mahaifiyarta da kanta...
     Tunda aka haifo ta baban ta ya tsane ta amma shi bai san Umma tana Muzguna mata ba..abinci sau daya take bata a rana, ga duka da aiki kullum kamar jaki...
     Bilkisu ta rasa *TUDUN DAFAWA*,da wanne zata ji,da mahaifiyar ta da bata da lafiya,ko kuma mahaifin ta da ya tsane ta ko Umma da take muzguna mata..๐Ÿ˜ฐ.Kullum cikin tashin hankali ta ke..

*Cigaban Labari✍๐Ÿป*
Da kyar Bilkisu ta iya mikewa daga wurin tana hawaye,dakin da mahaifiyar ta ke ciki ta wuce kai tsaye.Tana shiga,jikin Maman ta ta fadi kai tana shesshekan kuka,"Mama ki tashi ki taimake ni, Mama kiyi min magana ko naji sanyi a raina"..
     Maman ta sai kallon ta take yi amma komi baza ta iya tabukawa ba,wani kuka mai ratsa jiki Bilkisu ta soma yi kuma,"wayyo Allah kai ne gata na,Na san kai kadai ke so na,Allah ka ba wa mahaifiya ta lafiya saboda na san itace zata so ni bayan kai ya Allah, way...",kafin ta karasa maganar taji muryan mahaifin ta akan ta,"toh munafukar yarinya tashi daga jikin mata ta,muguwa wacce ta illata mahaifiyar ta" ya fadi cikin tsawa..Da gudu ta fita daga dakin tana kuka mai kona rai..
     "Shegiya mayya kawai,ki karata can ke da uwar ki,Umma ta fadi yayin da Bilkisu ta gitta ta gaban ta..Da gudu Bilkisu ta fita wajen gidan tana jin dama ba a haifo ta duniya bah.......Ni kam nace Allah sarki Bilkisu 'yar karama dake amma har duniyan ta ishe ki ..........


Tana fita waje ta samu wuri ta zauna ta cigaba da shesshekan kuka har kawarta kuma yarinyar makwabtan su tazo gittawa..Da sauri Bilkisu ta goge hawayen ta don karda ta gane cewan kuka take yi...
     "Haba Bilkisu,mai yasa kike son boye mini damuwar ki,iyye??๐Ÿ˜”sai kace ba kawar ki ba"..cewan Fatima...
     Share guntun hawayen da ya karasa sauko mata tayi..."kiyi hakuri,na san halin da kike ciki,kullum ni da umma ta sai munyi zancen ki,karda ki damu komai zai wuce in shaa Allah,baban ki zai so ki,mamanki kuma zata samu lafiya kinji".
     Gyada kai tayi alaman eh taji.."toh ni na wuce kawata,sai anjima sannan ta mike ta wuce gida..'Yar albarka!,'ya ta ina kike!,da sauri Bilkisu ta mike taje amsa kiran Umma saboda haka take kiran ta idan Mal na nan don ta tunzura shi..Kwata kwata Mal baya son yaji an kira Bilkisu da 'yar akbarka,ya kan ji tamkar ya fashe...
    Karasawa gaban Umma tayi ta gan ta rike da ciki tace je ki gayawa Mal cewa yazo ciki na yana ciwo.. Da sauri Bilkisu ta juya zata dakin shi sai taji ta bangaje mutum..Wani mahaukacin Mari ya dauke ta dashi,tuni ta tsuguna ta fara kuka wiwi.."Muguwar yarinya,wato kina son ki karasa ni yadda kika karasa Maman ki koh?toh wallahi baki isa ba,kur wata kur mayya kawai"inji Mal...ni kam nace o'oh duk ita kadai ๐Ÿค”๐Ÿ˜ฐ
..
     Goggo kuwa tana gefe tana jin dadi Ana bari ta na jin haushi,daman ta ga Mal a bayan Bilkisu di gan gan tace wa Bilkisu taje ta kirawo Mal..Tana ganin ya jiyo kanta,ta Fara wani murkususu kana tace "haba Mal ka daina yawan yi wa yarinyar ga fada man...",kin ga ba ruwan ki,karda ki kuma abinda zai bata min rai"cewan Mal..
    "Toh yi hakuri Mal, kaga ciki na yake matukar ciwo, dan Allah na shirya muje kilinic ( _clinic_)?,"toh shirya mana ina jiran ki"sannan ya juya zai tafi,da sauri  Umma tace 'yar albarka zo ki taimaka min na tashi..Da sauri Mal ya juyo ya hankade Bilkisu dake shirin mikewa,"karda ki kuskura ki taba min mata,bace min da gani a nan.. Da gudu ta tashi ta wuce dan karamin dakin ta kamar akurkin kaza..
    Umma kuwa wani dadi taji yayin da Mal yayi fam kamar zai fashe..suna fita Bilkisu ta fita da gudu ta je dakin maman ta,ta rungume ta tana kuka,a haka ta sami nutsuwa har bacci Mai dadi ya sace ta..๐Ÿค“UWA UWACE,KO A WANI HALI TAKE,RAHAMA CE A GARE MU...
     Mal kuwa suna isa clinic tayi musu bayanin yadda take ji..suka karba fitsarin ta da sauran abubuwan da za a bukata na gwaji..Bayan Awa daya, _lab attendant_ yazo ya sanar dasu cewan cikin wata daya ne gare ta kana ya taya su godewa Allah..Murna wurin Mal da Umma kam ba ya misaltuwa, ace mutum shekara goma sha biyar da aure,amma sai yau Allah ya azirta su da abinda suke ta nema ido rufe,ikon Allah kenan,Mal kuwa saboda tsabagen jin dadi har alkawura yayi mata na cewan duk abinda take so shi za ayi....Haka suke ta tafiya suna hira cikin nishadi har suka isa gida..
    Haka su Umma ake ta laulayin gaskiya da karya, Bilkisu kuwa na jin jiki in mal baya nan..in yana nan ta kan dan ji sa'ida ta fannin aikace aikace da yunwa saboda Umma na nuna wa Mal cewa tana son ta...Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa a gidan Mal kullum cikin takura wa Bilkisu'yar albarka☺ har wata tara suka cika....


*Toh Ku biyo ni don jin wani jinsi Umma za ta sambado..๐Ÿ™‹๐Ÿป**_Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜_*
[11/30/2016, 5:07 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป                  Na
                   
           Ummiee Ja'af
                   *03*

Umma ta sambado 'yar ta fara mai kama da ita sak.Murna a wajen Mal da Umma ba a iya cewa komai..

Bilkisu ma tayi murna da zuwan kanwar ta,a tunananin ta zata samu kawa,abokiyar hiran cikin gida in tayi wayo.Amma bata san cewa wannan yarinyar zata zamo annoba ba ne a gare ta...

Duk da murnan da take yi,Mal ya hana ta zuwa kusa da Umma ko jaririyar a cewan shi karda ya shafa musu bakin jini..Makwabta kuwa sai shigowa ake yi ana masu barka..

Ana haka wani dan kasuwa da ya dauki Abba aminin sa yazo masu barka.. Bayan ya dauki jaririyar ya sa mata albarka, ya Kira Bilkisu tazo ta karba jaririyan.

Mallam na ganin haka ya tsuke fuska yayi sauri ya mika hannu ya karbi yarinyar tare da watsa mata harara.Jiki a sanyaye Bilkisu ta juya ta wuce..
 
"Haba Mal ina zaton kace min kana kula da yarinyar ka yanzu,meh yasa kayi mata haka,kaji tsoron Allah fah,All...","kaga Alhaji ya isa haka,ai ita zaka cewa taji tsoron Allah,don ita ta nakasar da mahaifiyar ta garin haihuwa,ehhe"...

"Haba Mal ya kake magana kamar jahili,to gaskiya ni in baka daina ba zanzo na dauke ta na kaita gida na","wallahi je ka,ka rabani da annoba ne ma",inji Mal..Alhaji yace "Allah ya shirya,zan dawo na dauke ta in mun shirya da Mai daki na,sai anjima"..ko Kala Mal bai ce ba,ji yake tamkar ya fashe idan ana zancen Bilkisu....


*Bayan sati daya*

Alhaji Uthman yazo daukar Bilkisu..Bilkisu yarinya mai hankali tace fafur ita baza taje ko ina ba,Umma ma ta dage saboda wasu dalilai nata,na daya baza ta samu 'yar aike bah,sannan kuma bata son Bilkisu taje birni idon ta ya bude tazo ta rama abinda take yi mata..
 
Mal ne ya jajirce yace wallahi ko ta halin qaqa neh sai ta bi Alhaji,ya gaji da ganin ta a nan gidan..Shi dai Alhaji neh ya lallaba ta har ta yarda kana yace wa Umma tayi hakuri kuma Bilkisu zata dinga zuwa masu hutu a man..

"Wa? Allah wadai,meye maraban dambe da fada,nace ka wuce da ita kace zata zo wani hutu, meye amfanin wucewan ta toh,ka ga ko fuskan ta bana son na kara gani,ehhe"๐Ÿ˜ ,Mal yace tare da hada rai kamar tsummar tsohuwa ๐Ÿ™Š๐Ÿ˜‚...

"Hmm,Mal kana bani mamaki,lafiyan ka kuwa?",inji Alhaji.."Garau nike Alhaji,ku dai je Ku,Allah ya kiyaye hanya",Alhaji yace ameen,'ya ta zo mu wuce..

Da gudu Bilkisu ta ruga dakin Maman ta,"kaga munafuka,ke! Karda ki kuskura kije kusa da mata ta",Bilkisu koh jinsa bata yi,haka take ta ruzgar kuka har Alhaji yazo ya bambare ta a jikin Maman ta yana mai takaicin hali irin na Mal.

Umma kuwa data cika  fam da takaici ta dau jaririyar ta ta shige daki.Haka Bilkisu tabi Alhaji tana mai kukan rabuwa da mahaifiyar ta...๐Ÿ˜ฐ ............


*✍๐ŸปAllah sarki Bilkisu,ban ga laifin ki bah,ba abinda ya kai rabuwa da mahaifa tausayi musamman rabuwa da mahaifiya๐Ÿ˜ช๐Ÿ˜ข*


*_Yar autan mama,Ummiee Ja'afar_*
[11/30/2016, 5:07 PM] Ummieejaafar
  TUDUN DAFAWA                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar
                   *04*

*Billionaires quarters*
"Assalamu alaikum",Alhaji yayi sallama ya shigo rike da hannun Bilkisu.."Wa alaikumussalam, Alhaji bakuwar tamu ke ga?"Hajiya ta tambaye sa..
     "Eh itace","Allah sarki 'ya ta karaso mana",cewar Hajiya..Sum sum take tafiya har ta kai gaban Hajiya, ta durkusa"ina wuni Anty"..."kul da bakin ki, karda ki kara Kira na da Anty, ki dauke ni a matsayin mahaifiyar ki,oya yanxu meh zaki kira ni?? 
    "Mami",Bilkisu tace a hankali don taji wai ana kiran Mama, Mami a birni.."yawwa that's my girl",inji Mami,"Mami bani da gyale fah"Bilkisu tace.ni kam kyalkyalewa nayi da dariya,ina ruwan Bilkisu anji girl wai gyale ๐Ÿ™Š๐Ÿ˜‚..Da sauri Mami ta kalli Alhaji da yake musu dariya,
     "Alhaji daman yarinya ga basu sa ta a sch ba da wayon ta haka,"ta tambaya fuskarta cike da mamaki.."ah ya kike magana tamkar kin manta dalilin da yasa na dauko ta nan,wacce ake treating kamar bare a gidan su,ina taga ta schooling"Alhaji ya fadi tare da mikewa,"Toh anyi baby an manta da Mai gida"...
   "Haba ya zan manta da oga,bari na gana da 'ya ta,ina nan shigowa",Mami ta amsa tana dariya...Bilkisu dake tsugunne a wurin taji ana zancen sch,lallai tana ganin yaran makota a garin su suna zuwa,ba ma dai kamar gidansu Fatima kawar ta ba,amma kirikiri ita Umma ta hana ta zuwa...
     "Toh,'ya ta zo na kai ki dakin ki,anjima yayan ku zai zo ya kai ki ku siya kayan sawan ki sannan gobe za a miki register a makarantar boko da ta islamiya" Mami tace tare da riko hannun Bilkisu,"Nagode Mami"...."shhhh"....

*Alhaji Uthman Barwa*
Wani hamshakin dan kasuwa ne,yana da shagon _accessories da jewelries_,sannan da shagon kwanuka wanda ta dalilin haka ne suka zamo aminai da Mal. Idrisu..
    Matar sa daya ce,wato Hajiya Sa'adart amma an fi kiran ta da Hajiya *Adart*,tana aiki ne a hukumar Lura da hakkokin iyali dake nan garin Minna..Ita bagwariya ce yayin da Alhaji Uthman bahaushe ne tsantsa...
    Yaran su guda uku ne kuma dukka mazaje..Ja'afar shine dan su na farko,sai Ramlan,sannan Sultan wanda ya kasance autansu..
     Ja'afar ya gama makarantar sakandire kenan yana jiran _admission_ a Ibrahim Badamasi Babangida _University_ Lapai inda yayi _applying_ ma _business administration_, yana da kimanin shekaru 18 a duniya kuma yayi walimar saukan Qur'ani a lokacin shekarar sa 14 kasancewar yana da hazaka sosai,shi mutum ne mai son kowa da kuma dauka kowa nashi..
     Ramlan yana ss1 neh a makarantar Bilal bn Rabah dake London street,Minna..yana da kimanin shekaru 14 a duniya,shi yake ba su Alhaji ciwon kai a duk family din saboda girman kai da rashin ji da ya sa wa kan shi,gashi babu cigaba a karatun shi na boko da islamiya,kullum sai ci baya...
     Sultan kuma yana jss2,yana da kimanin shekara 10 a duniya,kuma ya kusa yin walimar saukan al-Qur'ani saboda shima yana da kwazo..shi da Ja'afar ne suka biyo Maman su sak,Farare kuma kyawawa kamar fillo,kasancewar Mahaifiyar su ba a barta a baya ba wajen kyau........
   
*Cigaban labari......*

Mami ta Kai Bilkisu dakin ta,Bilkisu na sa kai a dakin kawai ta sulale a kasa ta fadi sumammiya........... 

*Ni kam nace toh? Wata sabuwa......๐Ÿ˜ณ,mu hadu a shafi na gaba,don jin me ya sanya Bilkisu ta suma๐Ÿ™๐Ÿป*


*_Yar autan mama,Ummiee Ja'afar_*
[11/30/2016, 5:07 PM] Ummieejaafar
    *TUDUN DAFAWA                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar
                   *05*

Abin ya matukar firgita Mami,da sauri ta dibo ruwa a bathroom na dakin...tana yayyafa mata ta tashi za tayi waje da gudu Mami ta rikota.."wai lafiyar ki Bilkisu?, nice fa Mamin ki...."wayyo Mami ina ne nan?ta fadi tana rike Mami....

Nan Mami ta dago cewa tsoro dakin ya bata ,ta kyalkyale da dariya..."Kai Bilkisu a kwai wauta daman saboda dakin kika suma",kada kai tayi alamar eh..Mami ta dafa kafadarta kana tace,"in ban da abinki,ai bazan kai ki inda zaki cutu bah,nan dakin ki ne,matso nan"..

"Kinga wannan,wurin kunna fitilar dakin kenan, wannan kuma na fanka, wannan kuma na A.C mai sa daki sanyi"..Haka Mami take tayi mata bayani game da abubuwan dake dakin..Bayan ta gama,sai ta fita..
 
Bilkisu dai bin dakin take yi da kallo..Komai na dakin pink ne harda fentin kuma da gani bai dade da akayi fentin ba..Zama tayi kan lallausan gadon tasa hannu tana shafa bargon da aka shimfida kai.Hawaye na ga ya zubo mata kan fuska.Ni kam nace ko meh ya sa take hawaye? ๐Ÿค”

Sai naji tace "ya Allah ka ba wa mahaifiya ta lafiya,ya Allah ka ganar da mahaifina gaskiya,kasa ya so ni,kasa ya gane ina bukatar soyayyarsa a matsayin mahaifina,ya Allah kasa zama na a gidan nan ya kasance alkhairi a gare ni,Allah ka saka musu da alkhairi, ma tausaya musu yadda suka ji tausayi na,ameen...

Bilkisu yar baiwa,karamar yarinya amma ga kaifin tunani da basira...Mikewa tayi ta shiga bayi,ta bude shower yadda Mami ta nuna mata,ta watsa ruwa kana ta bude famfo tayi alwala ta fito...

Gaban mirror taje ta dauki _hair conditioner_ ta narka wa jikinta,sai walkiya take yi...kana ta dauki riga da hijabin da ta gani kan gadon ta sanya sannan ta shimfida darduma..Tana son tayi sallar azahar amma ta kasa gane alqibla,haka dai tayi sallan..

Bayan ta idar,mikewa tayi ta bi lafiyar gado,barci mai dadi ya dauke ta a sanadiyyar AC dake ratsa ta ta ko ina..anjima kadan Mami ta leko ta, ta ganta ta na narkar bacci,tayi wani baje2 ta bararrake kan gadon..Murmushi Mami tayi ta rufo kofan ta na Mai cewa "Allah sarki 'ya ta...

Mami na isa falo naji ta ce"toh kanwar taku ma barci take yi abin ta,anjima kwa gaisa.."Toh Mami Allah ya kaimu anjiman"a cewar Ja'afar.."mtssssw,haka kurin an kawo wata bare tazo ta dinga takura wa mutum a gidan nan"inji Ramlan..

"Kul da bakin ka ko nasa yayan ka yayi ma dukan tsiya yanzu,wai kai wani irin yaro ne iyye,toh ka jira Abban ka ya dawo sai ka gaya mai ya kore ta,kai ka ma je ka Kore ta yanzu in kai ke da gidan,yaro da tsiwan tsiya,Allah ya shirye ka",Haka Mami ta cigaba da bambamin ta,karshe ma mikewa Ramlan yayi ya wuce abin shi a zuciyar shi yana cewa" _I will make your life miserable_ shegiyan yarinya kawai"...

Ja'afar ne ya bawa Mami hakuri da yaga har muryan ta ya fara sarkewa alamar kuka zata yi,yace "Mami dan Allah karda ki zub da hawayen ki kan Ramlan,kin san zub da hawayen iyaye wa yaran su in sunyi abu marasa dadi bashi da kyau..Mu cigaba da yi Mai addu'an Allah ya shiryar dashi"..

"Toh Ja'afar nagode,Allah shi yi maka albarka","ameen Mami, bari naje na huta,yau na sha _huzzling_"ya karasa maganar yana dariya,"je kaci abinci tukun my son",cewan Mami.."Toh Mami na", ya fadi tare da mikewa ya wuce _dinning area_..Mami kuma ta mike ta wuce daki tana mai gode wa Allah da ya bata da mai share mata hawayen ta......

Zuwa la'asar Bilkisu ta tashi daga barci,tayi addu'a sannan ta mike ta shiga bayi,tayi tsarki sannan ta dauro alwala ta bada farali..Tana idarwa ta nannade sallaya sannan ta fito daga dakin domin taje wurin Mami...Ji kake tummmmm!!..........


*Toh,ko wa ya fadi haka,kuma meye sanadiyyar faduwan wannan,๐Ÿค”,ku biyo ni don samun amsoshin ku*


*_Yar autan mama,Ummiee Ja'afar_*
[11/30/2016, 6:27 PM] Ummieejaafar
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar
                 *06*
Ji kake tummmmm!!,Bilkisu ce ta fadi sanadiyyar kafa da Ramlan yayi mata..Kokarin mikewa tayi amma sai ta kuma jin saukan mari, a razane ta mike ta shiga dakin da gudu ba tare da taga fuskan wadda ya mare ta ba...

Ramlan kuwa wani dogon tsoki yayi sannan ya shiga dakin ta,"hey you local champ!!kadan kenan kika gani,wallahi sai na sa rayuwar ta kasance a very miserable one!! Ya karasa zancen shi tare da bugo kofar da karfi yayin da ya fita.. 

_*"Allahummak fineehim bima shi'eta"*_,shine kawai abinda Bilkisu take fadi tare da kuka mai cike da tausayi,"Umma na kin gani koh,shiyasa nace miki ba zan zo birni ba,amma suka tursasani,Umma babu mai so na,ya zanyi da rayuwa ta???"...

Sai da tayi kuka mai isan ta,sannan tayi a mahaifiyar ta addu'an samun lafiya..Bandaki ta shiga ta wanke fuskar ta saboda bata son Alhaji da Mami su gane tayi kuka saboda ta san su tsakani da Allah suke son ta..

Amma waye ne wannan da ya zabga mata wannan rashin mutuncin daga fitowan ta,meh tayi masa da har yayi mata irin wannan muguntan??tambayoyin da take ta jefa wa kan ta kenan wacce tasan bata da amsoshin su...

Fitowa tayi daga dakin ta sauko kasa domin yamma yayi,tana son taje ta taya Mami aiki a kicin..Gashi bata san ina ne kicin din ba..Dudduba wurare ta fara yi tana addu'a a zuciyar ta karda ta hadu da mugun da ya mare ta...Ni kam nace Bilkisu karamin yaro ne fa kamar ki,karda kiji tsoron shi amma kamar na kara ingiza ta ne ma....

"Ke ce kanwar tamu?",da sauri ta juyo saboda jin muryar shi da tayi a bayan ta...Ja'afar ne ta gani a tsaye yana mata murmushi..Daga kai tayi alamar "eh".Murmushi ya kuma yi kana ya ce "sannu da zuwa kanwar mu, shin mene ne sunar ki?","Bilkisu",ta amsa a takaice..

"A'a,toh?,kice min su Bilkisu Mai gadon zinari ce ashe?? Maganar tashi ya bata dariya har ta dan murmusa.."ni kuma sunana Ja'afar"...Murmushi kawai tayi..Nan Ja'afar ya gane ita ba mai yawan surutu ba ce,unlike others.."Toh ina zaki je?","Mami nike nema,ban gan ta ba"....

"Toh in banda abin ki,ai dakin ta zaki je ki duba","ban san dakin ba",cewan Bilkisu.."toh muje na kai ki"...Sadaf sadaf take bin shi a baya har suka kai dakin Mami..........


_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar*_
[11/30/2016, 7:30 PM] Ummieejaafar
   *TUDUN DAFAWA                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar 
                  *07*
Daidai bakin kofar dakin Mami ya tsaya yayi knocking tare da yin sallama.Daga ciki Mami ta amsa sannan ya shiga Bilkisu na biye dashi."Surprissse!!!",yace wa Mami yana murmushi sannan ya matsa domin taga abin da ya boye a bayanshi wato 'Bilkisu'...

Dariya Mami tayi kana tace "kai Ja'afar, Allah ya shirya min kai"..Da sauri yace"ameen,gashi na kawo miki 'yar ki,a falo na gan ta wai tana neman ki"...Dariya Mami ta kuma yi sannan tace " 'ya ta zo ki zauna oh,'yar albarka har kin farka daga bacci ashe"....."eh Mami"...

"Toh wannan shine yayan ki Yaya Ja'afar, shine zai kai ki makaranta gobe domin ayi miki rijista".."Su yarinyan Mami za a makaranta",inji Ja'afar.."kai,karda ka takura min 'ya fa","haba Mami,ni a wa?wai dan wake a super market",dariya sosai Mami tayi har Bilkisu ma sai da ta murmusa.Ja'afar kuwa tamkar bashi yayi maganar ba...

"Kai Ja'afar ba zaka kashe ni da abin dariya ba,you're so funny my child,"dan Allah ka kula min da 'ya ta,she is like a daughter to me,ka san yadda nike bala'in son Allah ya bani diya mace,gashi kuma Allah ya kawo min har gida,dan Allah karda ka bari Ramlan ya muzguna mata,haka zalika karda ka bari Sultan ya raina ta,ka taimaka mata da abubuwan da take bukata musamman ta fannin makarantar boko da islamiya"cewar Mami....

"Karda kiji komai Mami, in shaa Allah zan bata kulawa tamkar kanwa ta, ta jini,anything for you Mami".."yawwa, that's my boy...ina alfahari da kai,Allah ya kare min kai,ya Kara maka wadatar zuci..ke kuma Bilkisu, ki ba wa yayanki girman shi,banda rashin kunya kuma kisa ido a karatu sosai domin nan gaba zai amfane ki,sannan ki rage sa damuwa a zuciyar ki,duk lokacin da kika tuna iyayenki,ki dinga yi musu addu'a ne,kin ji koh 'ya ta"...

"Eh naji Mami, nagode,Allah ya saka da alkhairi".."shhhh,oya tashi muje ki ci abinci kafin na girka na yamma","a'a Mami ba zan ci komai ba,da muke hanya Abba ya siya min abinci naci".."toh shikenan,Ja'afar in baka da wani _schedule_ da yamman ga,ka dauke ta a mota kuje yi yawo domin ta ga yadda garin yake",inji Mami....

"Ok Mami, muje koh 'yar lele?",cewan Ja'afar... Mikewa Bilkisu tayi suka sallami Mami,dawowa Ja'afar yayi kuma"Mami nace ko na kai ta shopping gabadaya?","eh lallai kam kayi tunani mai kyau tunda bata da kayan kirki na sawa,bari na dubo ma credit card dina"ta fadi tare da mikewa...

"A'a Mami ki bar credit card din nan,ina da isasshen kudi a hannu na wanda Abba ya bani last week,zai ishe mu in shaa Allah".."oh Allah Sarki,Allah shi yi maka albarka dana,maza jeka yamma na kara yi,please karda kuyi dare fa"...

"Ok Mami",sannan ya je falo ya jira Bilkisu da taje dauka silifas dinta..tana fitowa ya bude mata kofan falo suka fita zuwa parking lot,wata farar mota mai kyau ya ciro ya bude mata kofa ta shiga sannan ya sa mata seatbelt bayan ta rufe kofan kana yaja motar suka fita daga gidan.......
 

_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[11/30/2016, 8:04 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                 *08*
_Bomaz supermarket_ ya kai ta bayan sun gama zagaya anguwar su...Wurin kayan mata suka shiga,ya fara zabo mata kaya masu bala'in kyau,su English wears,jallabiya,Arabian gowns,Indian wears,atamfa,lace da shadda kala uku uku....kaya dai bila adadin ya siya..

Sannan suka shiga bangaren takalma,ya daukan mata guda takwas da na makaranta guda hudu,ya Kama goma sha biyu,sannan suka shiga bangaren kayan ado,dankunne da sarka kala biyar ya daukan mata da wrist watch uku sannan da make up kit da mayukan jiki da su turare....

Kai komai da ya kamata mace mai irin shekarun ta tasa,sai da ya siya mata hatta underwears..Sannan suka jibgi kayan zuwa mota bayan ya biya kudin kayan.Bilkisu kuwa tsoro ya Kama ta,irin wannan kashe kudin...hmmm nan da nan ta tuna Maman ta,ta fara kuka a hankali,da yake Mami ta bashi labarin komai game da ita, sai ya fara lallashin ta har tayi shiru sannan suka je _Safara foods_ ya siya mata ice cream da cupcakes sannan suka wuce gida....

Mami da Abba sunji dadi matuka ganin yadda Ja'afar ya kashe wa diyar su kudi,suna ta suburbuda mai albarka..Mami ta jera mata kayan da kanta a daki tare da yi mata bayanin yadda zata dinga amfani da su shampoo,man shafawa,kayan kwalliya da sauran su sannan ta kwashe su atamfa,lace da shaddan domin ta bawa telan ta...

Zuwa karfe shida Sultan ya dawo daga islamiya,"Assalamu alaikum, _Mami I'm bacmkk!!_..ya fadi tare da shiga kicin.Turus yayi ganin wata a gefen Mamin shi.." _Mami who is she??_","yayan ka ce sultee na"inji Mami.."okkaayy!itace wacce kike bamu labarin ta wai zata so?".."Eh Sultan"..

"Oh..sannu da zuwa yaya"..murmushi ta sakan mai kana ta rungume shi,haka kawai taji dadin ganin tsaran ta a gidan..Sultan shima yaji dadin samun sister saboda duka abokanan shi suna da sisters,saboda haka shima ya shiga layi...Jakkan shi ya dauka zai tafi daki ita kuma don yaranta ta bishi,suna kai wa daidai bakin kofar dakin Sultee...Aka daka mata tsawa..."kee!!!"...a razane suka jiyo.........._*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar*_
[12/2/2016, 5:00 PM] Ummieejaafar
   *TUDUN DAFAWA*                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                 *09*
Ramlan ya daka mata tsawa,"ke dawo nan,ina zaki je"!!..."Bro raka ni zata yi"cewan Sultee.."raka ka?,yau ne ka fara zuwa daki kai kadai,c'mon get in!!",da sauri Sultee ya shiga daki yana kuka..Bilkisu itama ta juyo da sauri zata koma kasa ya finciko ta _"where do you think you are going to??!"_..Bilkisu dai kuka take yi har da kakkarwa....

Dakin shi ya shiga da ita sannan ya zauna a bakin gado,"oya ki fara frog jump",inji Ramlan.Tsayawa tayi tana kallon sa saboda ko kashe ta za ayi, bata san meh yake nufi da wannan yaren ba..Tsawan da ya daka mata ne yasa kukan ta ya tsanan ta..

"Kalli nan,durkusa,mike,durkusa,mike...."haka zaki dinga yi ko na zabga miki belt din nan",ya nuna mata wani skin belt,haba wa da sauri Bilkisu ta fara yi,tana yi tana kuka,tayi shame shame da majina abin tausayi..Ni kam nace karamin yaro amma sai masifan tsiya,just 14yrs amma sai girman jiki....

Ta kai kusan minti talatin tana abu daya, sannan yace tayi tukin babur (shima punishment ne).."Dan Allah kayi hakuri,ba zan kuma ba"...tassss! Kake ji,karan belt da ya watsa mata,take ta saki wani irin Kara...

Da karfi aka budo kofan dakin dayake bai rufe ba..."innalillahi wa inna ilayhirraji'un",abin da Mami ta fadi kenan tana ganin ta'addancin da Ramlan keyi wa Bilkisu.."Ja'afar!! Ja'afar!!!,zo kaga abinda yaron ga ke yiwa 'ya ta",ta karasa maganar cikin shesshekan kuka..

Ja'afar na isowa ya shiga dakin,"subhanallah!! _Are you stupid_, _are you insane!_, _are you...."_wani lafiyayyen mari ya sauke meh a fuska.."kai wani irin yaro neh,meh tayi maka?, _what did she do to you,answer me!!_"..

Shiru Ramlan yayi kamar ba dashi ake yo ba saboda ya san halin yayan nashi.."dazu fa take tare dani muna aiki a kicin,shine Sultee ya dawo ta bishi,ina ta ihun sunan ta amma naji shiru ashe tana nan tana shan ukuba..Allah ya shirya min kai,'ya ta taso mu tafi"...amma shiru bata amsa ba,lokacin suka lura da fitar numfashin ta..Da sauri Ja'afar ya sunkuce ta sai mota yayin da Mami ta biyo su a guje da hijabin ta,ta shiga baya in da ya kwantar da ita... Da gudu ya ja motar suka Kama hanyar asibiti da ita yayin da take kwance lamo tamkar matacciya a jikin Mami...

*hmmm..Allah sarki Bilkisu, Allah zai saka miki๐Ÿ˜ž๐Ÿ˜”๐Ÿ˜ช*_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[12/6/2016, 8:10 PM] Ummieejaafar
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar  
                 *10*
Suna isa Nurses suka zo suka karbe ta,sai ER..In banda salati babu abin da Mami keyi,"mai zan ce wa Alhaji in abu ya sami yarinyar nan??"...
      Ja'afar kuwa sai zuwa da dawowa yake yi,duk hankalin shi a tashe,zuciyar shi kamar zai faso don tsabar bacin rai da yake ji...Bayan awa daya likita ya fito,da sauri Mami da Ja'afar suka karasa kusa dashi..."Doctor lafiya,'yata ta farfado??",Mami ke tambayar sa a rude..
      "Eh ta farfado amma Ku biyo ni ofishi na domin mu dan tattauna",inji likita...Ya juya,yana tafiya Mami da Ja'afar suna biye dashi..Bayan sun shiga,yayi musu nuni da kujeru dake gaban teburin shi yace su zauna..Zama suka yi sannan likita yayi gyaran murya ya soma magana...
     "Toh a gaskiya 'yar ki tana da wani dan matsala da bai kamata ace tana dashi ba don qarancin shekarun ta..Don haka shine nike son na san musabbabin hakan,shin me ake yi mata ne da ya kai ga sawa 'yarki hawan jini?.."Hawan jini??!!",Mami da Ja'afar suka fadi lokaci daya.."eh hawan jini take da wanda kuma bai kamata ace tana dashi ba saboda karancin shekarun ta"..
    "Inna lillahi wa inna ilayhir-raaji'un!, ayya 'ya ta ai dole ki samu hawan jini ko don ja'irin da ya muzguna miki ba tare da kinyi masa komai ba,in shaa Allah likita zamu kiyaye,baza mu dinga barin a bata mata rai ba",cewan Mami."Toh madalla,sannan a raba ta da duk abinda yake firgitar da ita saboda firgici ne yasa ta suma,please a kiyaye",likita ya fadi...
    "Toh in shaa Allah, mungode likita",Ja'afar yace..."yawwa Ku gode wa Allah,ga wannan magungunan a siya mata,wannan"ya fadi yana nuni da sunan wani magani,"shi za dinga bata kowani lokaci jinin ta ya hau kafin Ku kawo ta asibiti".."toh Allah saka da alkhairi, zamu iya tafiya da ita yanzu?"inji Ja'afar..
     "Ameen,eh zaku iya tafiya da ita, babu matsala in shaa Allah","toh sai anjima likita"suka fadi tare da mikewa bayan ya kira wata nurse cewan ta kai su inda Bilkisu ta ke..Suna isa suka ganta zaune a kan gado tana hawaye.."ya ta kiyi hakuri,ki yafe ni ki yafe ni ki yafe min",Mami ta fadi tare da rungume ta tana hawaye..
    Rungume Mami tayi tana kuka mai karyad da zuciya.Ja'afar da sauri ya juyar da fuskarsa saboda saukan hawayen da yaji akan kuncin sa,ya bala'in tausayawa Bilkisu, karamar yarinya kamar ta amma wai tana da nawan jini??..hmmm,yayi ajiyar zuciya kana yace da Mami su zo su wuce gida,isha'i ya gabato..gashi ko maghrib basu yi ba..
    Hannun ta Mami ta riko suka fita zuwa wurin da ake fakin motoci,suka shiga motar su,Ja'afar ya tuka su zuwa gida..Suna isa daidai ana sallame sallar isha'i,kai tsaye dakin ta Mami ta kaita sannan ta sauko zuwa dakin ta itama..Ja'afar shima yaje dakin shi don bada farali.
    Bilkisu dai gode wa Allah tayi,domin tana tunanin lokacin mutuwar ta ce yayi,ba ta son ta mutu ba tare da ta neman wa mahaifiyar ta lafiya ba.Mikewa tayi ta tube kayan ta,ta shiga bayi ta wanke kanta fes sannan ta dauro alwala ta fito,bayan ta shafa mai, ta ciro wani jallabiya mai shigen rigar bacci ta saka,sannan ta dau hijabi ta sanya taje dakin Mami domin har yanzu bata gane ina ne alqibla ba.
      Tana isa daidai Mami tana tada kabbara,sai ta yi maza ta tada kabbara ita ma.Suna idarwa suka yi addu'a sannan Mami ta juyo tana kallon ta da murmushi shimfide a fuskarta,'ya ta,ya jikin ki?",Mami ta tambaye ta tare da shafa kuncin ta,"alhamdulillah garau nike jin kaina Mami",cewan Bilkisu.."toh masha Allah, Allah shi albarkaci rayuwar ki Bilkisu na","ameen Mami, nagode da kulawar ku, Allah ya saka muku da alkhairi","ameen 'ya ta,ai da na kowa ne,oya tashi muje muci abinci"..Mikewa suka yi zuwa kicin..
     Kulolin abinci suka kwaso,suka jera a kan dinning table sannan Bilkisu ta koma ta kwaso plates da robunan wanke hannu..Kana Mami ta bata abincin baba maigadi ta kai me..Zama suka yi kan kujeran dinning suna jiran Alhaji da sauran yaran..Ja'afar ne ya fara saukowa,sai Alhaji da Sultee suka y sallama suka shigo da alaman yanzu suka dawo daga masallaci..Ramlan shine na karshen fitowa..Kowa ya hallara a dinning kana Mami ta tashi zata yi serving,Ja'afar yayi saurin mikewa ya karba,murmushi Mami tayi ta bar mai,shi yayi serving kowa,suka ci suka koshi..
     "Rabin rai,ina kuka je ne wai,da na dawo Sultan kadai na cimma a gida,yace shima ya fito daga daki ne bai gan Ku ba",cewan Alhaji.."hmm,asibiti muka je","asibiti??!,waye bashi da lafiya?",nan Mami ta labarta wa Alhaji dukkan abinda ya faru.Wani irin kallo Abba(Alhaji) yayi wa Ramlan,"kai wane irin yaro ne wai fisabilillahi!,meh yarinyar ga tayi ma?...meh tayi ma nace??!!.."Ab..bba..dakin Sultan fa na..na..naga zata shiga fa!,"dakin Sultan din dakin uban ka ne!,nace dakin uban ka ne!!?,"a'a Abba amma..","will you shut your mouth up!,ace yaro yayi laifi ayi masa fada ba za ya karbi laifin sa ba,kai wane irin yaro ne?",Ramlan ya wani murtuke fuska kamar hadarin kaji ala ana mai fada kan bare..
    "Toh yau shine na farko kuma na karshe,in ka kuskura ka bari na kara jin ko da tsinke neh ka taba ta,sai ka yaba wa aya zakin ta,stupid kawai!",/"Abba kayi hakuri",cewan Ja'afar.."kai baza kace Abba yayi hakuri ba koh?!"..."Abbo yakuri",Ramlan ya fadi ciki2.."Allah ya shirye ka",Abba ya fadi yana mai takaicin halin yaron sa...
    "Bilkisu na,zo nan",mikewa tayi jiki a sanyaye taje wurin Abba,bata ji dadin fadan da aka yi wa Ramlan a gaban ta ba.."kiyi hakuri kinji,ba zai kuma ba,kuma gobe zaki fara zuwa school in shaa Allah".."toh Abba nagode"....Mikewa Ramlan yayi ya wuce dakin abin sa,kowa ya bishi da idanu kana suka karkada kai lokaci daya........
      ***********************
๐ŸŽ“๐Ÿ‘” *Wednesday* ๐ŸŽ’

Washegari,Mami ta sa Bilkisu ta shirya tsaf cikin jallabiya da dan karamin hijab..Wuraren karfe bakwai suka gama breakfast,dukkan su suka fits parking space..Abba da Mami suka shiga mota daya inda Abba zai ajiye Mami a wurin aikin ta sannan yaje ya duba shagunan shi..Ja'afar kuma ya shiga motar shi,ya bude ma kannen shi kofa domin su shiga,yace wa Bilkisu ta zo mazaunin gaba.Nan fa Ramlan ya soma kumbure2 kamar kumurci ya zauna a mazaunin baya shi da Sultee...Sallaman baba maigadi suka yi sannan yaja motar sai Bilal bn Rabah Islamic School,London street..
     Suna isa, ya mika wa kowannen su #200,Ja'afar ya kasance mutum ne mai wadatan zucci." _thank you_ yaya",cewan Sultee."shh bana hana ka ce min thank you bah?","ohhh! Na manta neh,jazaakallahu khairan yaya"cewan Sultee..."yawwa my boy,a yi karatu fa,Ramlan a rage taurin kai",kwafa Ramlan yayi sannan ya juya ya wuce abinshi, Sultee ya bishi a baya...
     *_Galaxy international schools_* da ke chanchaga suka wuce kai tsaye bisa ga umarnin Abba, yace ba zai hada su a makaranta daya ba..Suna isa ofishin _headmaster_ suka nufa kai tsaye inda Ja'afar yayi masa bayanin ya kawo sabuwar daliba ne kuma yana son a sa ta a class da ya dace da ita...
    Jin yawan shekarun ta yasa shugaban makarantar yace za a sa ta a aji na 3(wato primary 3) zuwa nan gaba in tana da kokaro sosai,sai ayi mata tsalleken aji zuwa jss1.Sannan yace a saman mata _lesson teacher_ wacce zata dinga zuwa har gida domin koyar da ita abubuwan da aka koyar a ajujuwan da suka gabata..Godiya yayi sannan ya biya kudin makaranta da na litattafai da uniform a ofishin bursar dake kusa da na headmaster..Bayan ya gama,yayi sallama da principal da cewan Bilkisu zata fara zuwa sch washegari...
    "Kanwa ta,ina kike son muje yanzu tunda sai gobe zaki fara zuwa sch",a cewan Ja'afar da yaga shirun yayi yawa."uhmmm๐Ÿค”,nima ban sani ba yaya",Bilkisu ta amsa.."toh bari muje yawo ta G.R.A gidan kanwar Mami","toh"..Hanyar by-pass suka bi sai GRA dake gefen _government house_,gaban wani tamfatsetsen gate suka yi parking,sauka yayi daga mota bilkisu ta fito itama..Kulle motar yayi kana ya kwankwasa gate din,sai da maigadi ya dau kusan minti biyar sannan yazo ya bude gate din..
     "A'a Alhaji Ja'afar ne a gidan?",maigadi ya fadi yana washe baki,"eh nine fah,ya kwana biyu","lafiya lau,wace ce wannan kuma?","wallahi yarinyar aminin Abba ce,tana zama damu neh","oh...to..to..to..to,yayi kyau,yayi kyau,Ku karasa ciki suna nan,sannu yarinya","ina wuni baba",Bilkisu ta gaishe shi,"lafiya lau,Kin zo lafiya?","lafiya lau","toh madalli jeki,a fito lafiya"..karasawa suka yi zuwa falo, Ja'afar yayi sallama ya shiga sannan Bilkisu ta shiga itama..
    "Oyoyo bros,idon ka ke ga??",wata budurwa kusan age mate din Ja'afar ta fadi tana saukowa daga bene.."wallahi nine fah,ya naga baki wuce sch ba bayan Xahra ta gaya min kin samu admission?","eh,ka san nan FUT na Bosso campus zana dinga lectures,so I choose to stay at home kawai na dinga zuwa lectures daga gida tunda Mommy ta siya min mota kuma","uhm yarinyar Mommy kenan",inji Ja'afar..
    "Wace ce wannan kuma??"ta tambayi Ja'afar tare da yatsine fuska tamkar kashi ta gani.............................._*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar*_
[12/7/2016, 8:32 PM] Ummieejaafar
   *TUDUN DAFAWA                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar
                        *11*
"Asmee,wannan yarinyar aminin Abba ce,jiya ya kawo ta gida,she would be living with us",ya karasa maganar cikin harshen turanci.."ohh,I see..toh meye sunan ta?",inji Asmee.."Bilkisu",ya amsa a takaice..
    Kyalkyalewa da dariya tayi harda rike kirjin ta da hannu daya, dayan hannun kuma Samsung galaxy dinta ta rike dashi,"so funny!,'yan mata kika bari aka sanya miki sunan tsoffi?",ta karasa maganar tana dariyar iskanci.."please would you stop dt,its irritating!, ai kema sunan tsoffin gare ki,Assama'u","kai bros ka daina bana so Allah",tace tare fa shagwabe fuska."Toh ke ma ki daina bata so",ya fadi yana murmusawa..
    "Toh bros,Mallama wai baki iya gaisuwa ba neh?koh nayi kama da kanwar ki ko tsaran ki neh?",da sauri Bilkisu ta sunkuyar da kan ta,idon ta cike da hawaye taf,"ina wuni anty","hhhh,so smart harda anty?.."please ya ishe ki haka nan! Kanwa ta,taso mu wuce",Ja'afar yace..
     "Haba bros just kidding her n..","laaa bros kai ne a gidan mu yau?, wata yarinya tsarar Bilkisu ta sauko daga bene ta katse maganar da Asmee take yi.."Hey Zahratee baki je sch ba yau?,cewan Ja'afar,"a'a bros,wallahi bani da lafiya ne","subhanallah sorry Zahratee,Allah ya sawwaka Lil sister","ameen big bro,who is she bro,she is cute",ta tambayi Ja'afar yayin da taje kusa da Bilkisu ta tsaya tana mata murmushi..
      "Friend na kawo miki, kinga school dinku ma za ta but ita a primary 3 za a sa ta,her name is Bilkisu,yarinyar friend din Abba ce","primary 3??!,suka fadi lokaci daya,"wannan katuwar yarinyar?",cewan Asmee.."hmm..daga Gurmana aka dauko ta,so she is just a fresher a school","ok,yanzu naji zance,Bilikisu suna na Zahra,ni kanwar yaya Ja'afar ce",cewan Zahra yayin da ta miko wa Bilkisu hannun ta domin suyi musabaha..Murmushi Bilkisu tayi sannan ta maida wa Zahra da martani...
    "Toh lil sis sai kun hadu a sch gobe,mu zamu wuce kenan".."ok bro ka gaida min da Mami na",cewan Zahra.."Toh zata ji,nima ki gaida min da Mommy in ta dawo","toh zata ji,bye Bilkisu"..."oh ni baza a sallame ni bane?",cewan Asmee da ke tsaye a wurin tamkar zata fashe saboda sun share ta..."oh sorry na manta ki na nan,bye Assama'u",kwafa tayi kana taja tsaki ta hau bene abin ta su kuma suka fita daga falon..Zahra tayi musu rakiya har parking space,suka wuce.....
     

     *Ubay bn Ka'b Islamic school* suka zarce kai tsaye,inda ya siya mata form na islamiyar 2-6,wato bayan ta tashi daga makarantar boko,drive zai garzayo islamiya da ita, sai 6 ya dawo ya dauke ta...Fitowar su ke da wuya daga islamiyar,tace "yaya shin ni za a sa a wa'ennan makarantun?,tambayar ta bashi dariya sosai amma murmusawa yayi kawai kana yace da ita,"eh can da muka je dazun,shine school din da zaki dinga zuwa,wannan kuma na islamiya"..
     "Ayya Mami da Abba,ni ban san da wani baki zan yi musu godiya ba,sunyi min komai a rayuwa, yaya Allah ya saka muku da alkhairi, nima ina son ku yadda kuke so na",ta fad'i tare da share hawayen da ya gangaro mata akan kuncin ta..Tausayi ta bashi ainun,"ba komai kanwa ta,ke dai ki sa ido a karatu,kuma banda biye biyen kawayen banza",Toh zan kiyaye in shaa Allah yaya"...
     "Kanwa ta wai me yasa ba kya son yin magana neh?",ya tambaye ta yayin da yake tuki,"ina yi mana yaya",inji Bilkisu harda dan dariyar ta.."wow,yau ne rana ta farko da naga dariyar ki,I love it!",cewan Ja'afar..Dariya ta kara yi saboda yadda yayi far da idanu,daga nan hira ta barke a tsakanin su har take bashi labarin kawar ta, Fatima da ke kauye..Amma bata gaya mai komai game da muzgunawar da ake mata ba...
     *Alhaji Muhammad Isma'il*
 
Shine mahaifin su Zahra kuma mijin kanwar Mami,Hajiya Khadija..Yana aiki ne a CBN dake Abuja shiyasa baya samun zama a gida kowani lokaci..Kowani karshen mako yake zuwa duba iyalan sa kuma ba abinda zasu bukata da baya basu sai dai inda karfin shi bai kai ba..Yana da fara'a sosai,ga son talakawa da kuma taimaka musu.Shi amini ne ga mijin Mami.A bikin Abba da Mami, Alhaji Muhammad ya hadu da kanwar Mami....

*Hajiya Khadija*

Itace mahaifiyar su Zahra kuma mata ga Alhaji Muhammad sannan kuma kanwar Mami,wato mahaifiyar su Ja'afar..Hajiya Khadija kyakkyawa ce fara sol, ga ta da kyaun diri..Amma halin ta sai ita, idan tana son mutum,wallahi ko za a fadi aibun wannan ba zata ki shi ba,idan kuma ta qi mutum,ko za a fadi alkhairan sa so nawa ne,baza ta taba son sa ba..Gata da kyankyamin talakawa,a wurin talaka ba komai ba ne akasin Mami da ta dau kowa nata neh.Ita matron ce a asibitin gwamnati dake garin Minna.......

*Asma'u Muhammad*

Ita ce 'ya na farko ga Alhaji Muhammad da Hajiya Khadija. Ita fara ce amma ba sosai ba,tana da Kama da Daddyn su.Tana da kimanin shekaru 17 a duniya.Halin ta daya da na mahaifiyar ta,ga dagin kai da rainin wayo sai dai Allah ya jarrabce ta da bala'in son Ja'afar, shiyasa duk inda ta ganshi sai ta susuce ta zama tamkar wawiya..A shekaran ga ta samu _admission_ a FUT Minna inda zata karanta _Biochem_.....

*Zahra Muhammad*

Itace 'ya ta biyu kuma ta karshe ga Alhaji Muhammad da Hajiya Khadija.. Kammanin ta daya sak da na mahaifiyar ta sai dai ita halin mahaifin ta ta dauko.Akwai ta da son mutane da girmama na gaba,kowa nata neh..Tana da kimanin shekaru 12 a duniya,kuma tana jss3 a _*Galaxy international school*_.. Tana 9yrs tayi walimar saukan alQur'ani,yanzu hadda take yi a _Bilal bn Rabah_ kowani karshen mako..Wannan kenan!......

_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[12/8/2016, 7:48 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                          *11*

******** *Cigaban labari*


_''Hello,boy''_,cewan Ja'afar.."kai waye boy din ka,dan rainin hanks",cewar abokin shi,dayake Ja'afar yasa call din a _handsfree_ saboda yana tuki."Ashraf yane?", _"I dey oo steady!!_"ya su Mumcy da old man?,"lafiya kalau suke",inji Ja'afar.."mun samu admission fah!!","woah!!,yaushe ka duba mana??"cewan Ja'afar,"wallahi yau na duba,dukkan mu sun bamu courses da muke so harda su Ubaid da Sufyan"..
     "Oh alhamdulillah!, _congratulations to all of us_,gaskiya naji dadin wannan news din",cewan Ja'afar.."Ok then,za a fara registration mako mai zuwa,dukkan mu zamu hadu ranar Monday muje muyi harda su payment na school fees cox beginning of next month zamu yi resuming which is 3weeks away"cewan Ashraf.."alright,sai mun hadu in shaa Allah",inji Ja'afar.."ya mutumiya ta ne wai?"..
    "Tana nan dai yadda ka san ta,yanzu muka baro gidan su","oh my love,yarinyar nan tana birge ni sosai" cewan Ashraf."kai ba na son iskanci fah,ku karata can,bye"..Ja'afar ya yanke call din.."kanwa ta mu wuce gida ne ko na kai ki yawo kuma?","a'a ni dai muje gida,kila Mami ta dawo yanzu"..."toh as you say my sister".."A cuce waye yaya na?"cewan Bilkisu...
    Kyalkyalewa yayi da dariya ganin bata gane turancin da yayi ba sai yace"nufi na shine,duk yadda kika ce,haka za ayi"..dariya tayi har sai da dimples dinta ya lotsa.."asi say ma sita,koh?",ta maimaita..Dariya yayi kana ya gyara mata sannan ta dinga maimaitawa har sai da ta iya..
    "Bilkisu zan wuce makaranta nan da sati uku",dafe kirjin ta tayi kana tace "haba yaya?,tare zamu koh?,"ya zamu je tare kuwa,koh kin manta zaki fara zuwa makaranta neh?","wai har na manta,toh Allah ya bamu sa'a dukkanmu".."ameen kanwa ta,dan Allah karda ki sa muji kunya,kisa hankali a karatu sosai,be the best!!","be the best",ta maimaita maganar,yace"wow,kinyi kokari,kisa himma kinji koh?","toh in shaa Allah yaya"....Haka suka cigaba da surutun su har suka isa gida...
   

     *********************

   "Ke yaya wai meh yasa kike wa mutane haka ne?"cewan Zahra.."ke kuma asu wa da kike tambaya ta?"Asmee tace tare da watsa mata harara.."Allah ya huci zuciyar ki"Zahra tace tare da barin dakin.."mtsssw har Ja'afar ya dizga ni gaban village brat din nan,wallahi na sa mata karan tsana ta kenan,mtcchhhw",ta kuma yin tsaki kana tasa headphone dinta ta fara jin dabsy...
     " _Hello,anybody home_?",cewar Mommy da ta shigo babu ko sallama.Zahra na jin ta amma tayi cim, bata amsa ta ba.."ke,ashe kina nan kina ji na,shine kika ba wa iska ajiya ta koh".."oh,sorry ma naga ba sallama kika yi ba shiyasa",Zahra tace tare da tsuke baki.."iyye,har karamar kwaro kamar ki ce zata fada min abin yi koh?u are stupid!",Mommy ta karasa zancen tana gallawa Zahra harara sannan ta wuce dakin ta..
    Zahra dai halin mahaifiyar ta da yayan ta yana bata haushi amma ta rasa yadda za tayi.Mahaifin ta kadai ne gwanin ta kuma ba ya zama tare da su."Allah ya shirye ku",ta fadi tare da mikewa domin ta gabatar da sallar azahar...
    

      *Kauyen Gurmana*

"Allah da gaske kake yi wai zamu koma birni??"cewan Umma yayin da take sa wa *Saleema* kaya.."eh wallahi,kinga shiyasa nace tsinanniyar nan annoba ce a gare mu,ji fa duka duka kwana biyu kenan da Alhaji yazo ya wuce da ita,gashi har alkhairi ya same mu,gwamnati ce ta bada takardun gidajen ga hakimi cewan duk wanda yake son gida a farashi mai sauki ya same shi,shine da ni,da Mal Auwalu,da Mal Musa muka siya,nawa da na Mal Auwalu suna kusa da juna neh,zuwa sati in shaa Allah zamu tattara inamu inamu mu wuce".
     "Kai Mal amma naji dadin wannan zancen,sai dai wani hanzari ba gudu ba,wani aiki zaka cigaba da yi a birnin?","eh..toh,haka ne fah,zan yi magana da Alhaji ko da aikin masinja ne ya saman min"."toh madalli,amma dai a nan zamu bar waccan koh?",cewan Umma."waccan matar ka mana da bata da bambanci da......","kamar ya fa?ban gane ba.ke mai yasa idan ana zancen alkhairi sai kin dauko na sharri a ciki,haba meye laifin a wuce da ita can,'yar uwar ki ce fa.kuma lalura yasa take kwance haka nan,haba kiji tsoron Allah mana, mtccchw".Baba(Mal. Idrisu) ya karasa zancen da tsaki.Ni kam nace su Baba manya, har kana da bakin cewa wani yaji tsoron Allah, toh Allah shirya...
    Umma kuwa tun da ya fara magana taga ran shi a bace yake, ta sha jinin jikin ta,"yi hakuri Mal ,subutan baki ne".."ke kika sani dai"baba yace tare da mikewa zuwa dakin mahaifiyar Bilkisu.."ki taya ni murna Lami,Allah ya azirta mu da gida sanadiyyar wucewar yarinyar da ta zamo silar kasancewar ki haka,ba zan taba yafe mata ba!!"........


_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[12/9/2016, 8:10 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                        *13*

*A/N: Assalamu alaikum masoya na,amincin Allah ya tabbata a gare ku a cikin wannan wata mai albarka..Lallai ranar haihuwan manzon tsira,rana ne mai muhimmanci ga dukkan al'ummar musulmi.Azumi da salati ga annabi shine muhimmin abubuwan da ya kamata muyi a wannan rana mai tarin albarka..Mu tuna fa,karda garin yin gwanin ta mu zaqe mu wuce gona da iri,wato muyi abinda annabi bai yi wa kansa ba,ko kuma sahabbai da tabi'uttabi'una basu yi masa ba..Mu tuna fah!!Annabi yace duk wanda ya kago wani abu da bamu yi ba,toh baya cikin mu..ina fatan wannan guntun sakon nawa zai fadakar kuma ya wa'azantar..Allah ya ganar damu,ameen..Abu na biyu shine, nayi kuskure wajen numbering pages na novel din nan,last page da nayi posting shine page12...I'm sorry for d inconveniences my mistake might have caused,thanks Jidda(Xahra novels)for d observation๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜....thanks for ur prayers,ur support and everything...love you so so Much...Allah ya barmu tare!!ameen*
*Billionaires quarters, Thursday*

Bilkisu ce na hango sanye da riga da skirt na kanti sannan da dan karamin hijabi kamar na jiya dai.Tayi kyau sosai.Sch bag ne sakale a bayan ta sannan da farin safa da bakin takalmi a kafarta.Sultee ne biye da ita sanye da uniform dinsu da ya kasance kamar kaftan,kalar baki da ruwan toka sannan da bakaken takalma da sch bag.Biye da su shine oga Ramlan..lolzzz. Yana wani takun kasaita da gayu,sanye yake da uniform iri daya da na Sultee sannan da sch bag irin wanda ake sakalawa a kafada....
      Mami ce ta fito tana gyara saitin hijabin ta da gilashin ta a lokaci daya kasancewar sun makara har Abba ya riga ta fita..Ja'afar a gurguje ya fito shima ya shiga mota ya tayar..Ganin Bilkisu zata nufa wurin kofar seat na gaba,Ramlan yayi sauri ya shige gaban ta ya tsaya..Komawa baya tayi ta shige motar..Duk abinda ya faru kan idon Ja'afar aka yi amma saboda sauri suke yi,bai ce Kala ba duk da bai ji dadin abinda ya faru ba..Motar Mami ne ya fara fita sai na Ja'afar,kowa ya kama hanyar sa..
     Sai da ya kai su Sultee tukun sannan ya kai Bilkisu itama.Wajen auntyn ajin su ya damkata tare da yi wa auntyn baya ni a kan ta sannan ya sallame ta ya wuce..Tana shiga ajin taga duk kananan yara ne sa'oin kanwar Fatima(8yrs)sai wata kamar tsaran ta da ta hango ta kujera na karshe.."class kunyi sabuwar kawa,da fatan za ku zama abokanai da ita, sunan ta BILKISU IDRIS",(dukka wannan bayanin cikin harshen turanci auntyn ke magana).."sannu d zuwa Bilkisu",('yan ajin suka fadi a harshen turanci).Murmushi Bilkisu tayi saboda bata san mai suke cewa ba.
      "Ki bisu kuyi musabaha(handshake)",(Aunty Aisha ta fadi a harshen turanci tare da yi mata nuni da hannu)..Haka Bilkisu ta bisu daddaya tayi musabaha da su.Duk wanda tayi musabaha da,sai ya/ta fada mata sunansa/ta..Tana kaiwa wurin yarinyar nan,Aunty tace mata ta zauna a wurin.Zama tayi tare da yin musabaha da ita, yarinyar tace "sunana SAMEERAH NAJEEB".Murmushi Bilkisu tayi sannan suka maida hankali ga abinda Aunty Aisha ke rubutawa kan allo....๐ŸŽ’๐ŸŽ’๐ŸŽ’๐ŸŽ’๐ŸŽ’๐ŸŽ’๐ŸŽ’๐ŸŽ’๐ŸŽ’

*_Lokacin break 10:00am_*

Bilkisu ce zaune a wurin kujerun shakatawa da ke karkashin wata  bishiya tana kallon yadda kowa ke harkan sa..Sai ji kawai tayi an dafa ta,tana dagowa ta sake murmushi ganin wacce ta dafa ta..Zama tayi kusa da ita kana tace "Ashe da gaske bro yake yi,an kawo ki sch din mu",cewan Zahra..
      "Eh wallahi",Bilkisu ta amsa a takaice."kun kai gida lafiya jiya?,"lafiya lau Anty Zahra".."wooahh,karda ki kara kira na da anty bayan ni tsarar ki ce,Zahra ma yayi min",Zahra ta fadi rai a bace."Toh kiyi hakuri Zahra",cewan Bilkisu."haba ko ke fah?",murmushi Bilkisu tayi."kinyi break ne koh?",Zahra ta tambaye ta."a'a bana jin yunwa","are you sure?",shiru Bilkisu tayi tana kallon ta,lokacin Zahra ta tuna ashe fa bata gane turanci,sai ta murmusa tace"kin tabbata ba kya jin yunwa?",a nan Bilkisu ta gane ma'anar _'are you sure?'_."eh bana jin yunwa"."toh shikenan"..Haka Zahra take ta jan Bilkisu da hira har ta sake jiki da ita,Zahra tayi mata alkawarin koyar da ita abubuwan da aka yi a classes da bata yi ba,a kowani break...
     Suna zaune a wurin suna hira sai ga Sameera tazo ta zauna itama aka tsunduma duniyar hira da ita har Bilkisu ta ke basu labarin kawarta Fatima.Nan dai suka kulla kawance da juna dayake Zahra bata son 'yan ajin su saboda suna da jijji da kai,Sameera kuma yaran aji sun yi mata kanana..
     Kullum suna makale da juna lokacin break.Da lokacin tashiwa yayi kuma zaka gansu tare a bakin gate har sai direbobin su sun zo daukan su...Haka rayuwa ta kasance wa Bilkisu, da safe ta na school,da an tashi ta wuce islamiya.Yayin da Ja'afar ya zama kullum yana nan ya na can batun registration din su..Sultan kuwa shine abokin hiran ta kuma mai koya mata abu in ya shige mata,sam bata da girman kai..Ramlan kuwa sai abinda ya karu na muzguna mata amma bata sanar da kowa sai dai taci kukan ta in yayi mata abu..Aunty Aisha kuma tana zuwa gida kowane asabar da lahadi domin koyar da ita bisa ga magiyan da Abba yayi mata da kuma alkawarin biyan ta dubu biyar kowane karshen wata...

*Bayan sati daya*

Ranar juma'a tana dawowa ta shige dakin ta saboda babu kowa a gida,direba kuma ya je kwaso su Sultan daga makaranta.Tube uniform tayi wanda ya kasance riga kalar sky blue da skirt navy blue da karamin hijab shima kalar sky blue,sannan ta tube bakin takalmin ta da farin safa dake kafar ta..Tawul ta daura ta shiga wanka,tana cikin wanka taji karar ana bude kofan ta da kuma muryar mutum,amma bata gane ko muryar mace ce ko namiji ba.Da sauri2 ta karasa wankan,ta dauro alwala ta fito gaban ta na faduwa...... *Wa zata gani???!!*


 *ku biyo ni don jin kwakwam*

_~Love you always dearies~__*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar*_
[12/11/2016, 9:35 PM] Ummieejaafar
   *TUDUN DAFAWA


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar 
                       *14*

"Wayyo Fatima!!!",Bilkisu tace tare da rugawa da gudu ta rungume ta,da kadan towel dake jikin ta ya kwance..."Bilkisu kin gan ki kuwa??",cewan Fatima."zo zo zo,zauna, daga ina haka?",ta tambayi Fatima tare da karbar ledan da ke hannun ta.."Wallahi daga gida,ai mun dawo nan da zama mu ma,muna anguwar Bosso estate neh"."kai amma na taya ku murna,Allah ya sanya albarka a gidan, yasa ayi rayuwa mai alkhairi a cikin gidan,ameen"..
      "Baba ne ya kawo ni ma",cewan Fatima."oh Baba,bari na sa kaya muje mu gaisa",tace tare da mikewa tana shafa mai a gurguje."Baban ki nike nufi fah,kuma muna isowa ya juya ya tafi abin sa"..jikin Bilkisu yayi sanyi da ta ji wai baban ta ne ya kawo Fatima amma ko tsayawa bai yi bah domin ya gan ta.Duk da hakan dai, ta ciro wani rigar kanti gown ta sa sannan taje kicin ta zubo musu abinci saboda ita da Mami sai sunyi abinci kafin su fita...
     Tana kawo wa,taje ta dauko bottled water da kofuna sannan tazo ta zauna a gefen Fatima suka fara cin abincin."Shi baban meh yazo yi a birni,ko dai ke kika matsa mai ya kawo ki",cewan Bilkisu.."Ni? A su wa?!!,ai su ma sun dawo nan birni da zama,kuma gidajen mu na kusa da juna neh yadda muke a can dai,kar dai kice min ba ki sani ba??",cewan Fatima..
     "Hmm,Fatima ya zan sani kuwa?,sanin kan ki ne tun da na zo birni ban kara leko kauyen mu ba duk da bai da nisa da nan"inji Bilkisu.."Toh Allah shi kyauta,nima sai da na hada da magiya kafin ya yarda ya kawo ni"..."Bilkisu kin fara zuwa sch ne?",murmushi tayi kana tace "eh na fara.......",nan ta fara zuba tana ta bawa Fatima labarin sch dinsu har da kawayen da ta samu,da uwa uba Ja'afar kuma..........
     Mikewa suka yi,suka je suka yi alwala,Bilkisu ta sake wani alwala kuma..Bayan sun idar da sallah,Bilkisu suka cigaba da hira har sai da Mami suka dawo sannan suka sauka kasa,suka gaida Mami.Can Abba shima ya dawo.Sun yaba halayyan Fatima kwarai har yasa suka ce zasu bar Bilkisu ta dinga zuwa mata ziyara..
     ***********************************

*Bayan mako biyu*


Ranar litinin da yamma Ja'afar ya shirya tsaf,yaje falo sallaman su Mami da Abba. A yau ne zai wuce makaranta kasancewar ya gama registration kuma an fara lectures.Shi da abokanan sa zasu wuce,suna jiran sa a gareji..Ranan Bilkisu bata je islamiya ba.Taci kuka har ta gaji tamkar ba zata kara ganin shi ba.A karshe dai bayan iyayensa sunyi masa nasiha,suka ce da su Bilkisu su shirya su raka shi gareji...
    Kuka tayi sosai a gareji kuma,har abokanan sa suna ta mata dariya,Ubaid har da cewa ko za ta bishi neh?,tsuke fuska Ja'afar yayi kana dukkan su suka kama kan su..Haka dai suka yi sallama kowannen su rai wani iri.Ramlan kuwa tamkar ya zuba ruwa a kasa ya sha domin mai kare 'yar iskan ya wuce...Tun a mota ya fara yaba mata magana amma ta ki amsawa saboda ta san mai zai biyo baya in ta amsa shi...


Bayan sati daya da wucewan Ja'afar,Mami da Abba suka yi tafiya zuwa kauyen su Mami da ke paiko.Nan fa Ramlan ya samu garabasan gallaza wa Bilkisu.Akwai ranar da zasu je sch kuma sunyi latti,sai yace ta je ta dauko mai juice a firij,tana shiga ciki yace ma direba su wuce saboda Bilkisu tace zata hau acaba taje.Shi kuwa direba bai san wainar da ake toyawa ba,ya ja motar suka tafi...Tana fitowa ta ga wayam,mai gadi yace mata ai yanzu suka wuce.Tamkar ta zube a wurin ta dinga kurma ihu taji amma ta kasa,Allah yaso Abba ya bata kudi kafin su tafi...
     Fita tayi ta fara neman acaba,da kyar ta samu lokacin karfe takwas da minti ashirin,gashi ana basu punishment in sunyi latti.Suna isa ta biya dan acaba sannan ta karasa bakin get,manya2 buloli ne ta ci karo da,kamar ta ruga a guje ta koma gida,amma ya ta iya?,karasawa tayi ta shiga aka sasswade ta sannan tayi picking kana aka bar ta ta wuce class...
     Kuka take tayi lokacin break,su Zahra da Sameera suna ta bata hakuri,da kyar tayi shiru.Duk haka ta yini ranan ba dadi,Ramlan yana ganin ta ya kece da dariya sannan ya taka kafar ta da yazo gittawa..Sultan shi dai sai dai ya bishi da ido sannan ya bawa Bilkisu hakuri....
      
Kafin Mami suyi tafi,ta yi ajiyan kudade masu yawa a wardrobe, haka Ramlan yaje ya kwashe kudin nan tas, yaje ya kashe na kashewa shi da abokin sa Shareef.. Sauran kuma ya je wani mini market dake kusa da su,ya siya snacks irin packaged one din nan ya je ya ajiye a dakin Bilkisu ta inda baza ta gani ba sannan ya kuma diba cikin kudin yayi squeezing ya sa a wardrobe din ta..
     Mami ta dawo tana ta neman kudi amma wayam kudi tace dauke ni inda kika ajiye ni.Hauka kadai ya rage Mami bata yi ba ranan saboda kudin da aka bata ajiye ne a wurin aikin su na case din wata mata da za ayi running.Kudin da za a ba wa lauyan da zasu dauka kenan.Allah yaso lokacin Ja'afar yazo weekend a gida.Tuni Abba ya kira dukkan su falo..
     "Ni ba barawo ba ne,mahaifiyar Ku ba barauniya ba ce,ta ya na samu barawo a cikin 'ya'ya na,wa ya shiga dakin mahaifiyar ku ya dauki kudi?!,dim!! gaban Bilkisu ya fadi wadda itama bata san dalilin faduwar gaban bah.."ba kwa ji na neh?!, nace wa ya dauka kudin a cikin Ku?!,look at how your mum is crying,who the hell took the money among you??!!!",shiru suka kuma yi.."Oh ba zaku yi magana ba koh??!..ok"..
     Daki ya shiga ya dauko dorina,Ramlan yana ganin haka ya tsure,sai yayi saurin hada plan,"wallahi Abba kai ma ka San tunda muke nan gidan ba a taba yin sata ba sai yanzu,ple...","kai meh kake nufi??,kana son ka ce min Bilkisu ce ko meh, you're very stupid!!!..Bilkisu dai jikin ta sai bari yake yi."Ja'afar je ka duba dukka dakunan su",cewan Abba...
      Bayan minti talatin,Ja'afar ya fito da kudi a hannun sa zuciyar shi cike da rashin yarda da bacin rai."Ab..Abba gda wanda na gani",yace tare da mikawa Abba kudin da ke hannun shi."a ina ka ga wa'ennan,tabbas wannan shine kudin saboda ni ban ba wa kowa irin kudaden nan ba kafin na wuce,a dakin wa ka gani?"..
      "A..a..a dakin Bi..bi..Bilkisu na gan...",kafin ya karasa zancen Mami ta wanke shi da mari."har da kai za ayi wa Bilkisu sharri,yaushe ka fara biyewa Ramlan?!".."wallahi Mami a dakin ta na gani,kije ki duba yadda nayi scattering wardrobe din ta,a nan na gani"ya fadi hawaye na gangarowa kan kuncin sa...
     Mami ba ta yarda da zancen Ja'afar ba,wucewa tayi zuwa dakin Bilkisu,lallai kuwa a nan ya gani saboda wani rafar kudin ma yana ciki bai hango ba,zarowa tayi zata fita sai ta hango leda a can loko2n gadon ta,tana budewa ta ga snacks cike da ledan.Daukawa tayi kamar wacce bata da laka a jiki ta fita zuwa falo..
       Tim!! ta yar da ledan a gaban Abba,Bilkisu na gani ta fara zazzaro idanuwa,sai hawaye sharrr.Mami na zuwa dai2 wurin Bilkisu ta kwashe ta da mari. Ni kam nace hmm Mami rai ya baci, Bilkisun ki ce fa!."na dauke ki tamkar 'ya ta na ciki na amma kike neman ki tozarta ni a wajen aiki na?,meh zan ce musu,yarinyar da nike riko ta saci kudin da suka bani ajiya??,ban ga laifin mahaifinki ba da ya tsane ki,ke annoba ce!!"..Hmm Mami ta fita hayyacin ta ooo..
    "Wallahi Mami bani na dau....",ki yi min shiru!,ko wata biyu ba ki kai ba da zuwa gidan nan amma har kin soma nuna halin ki,you are no more needed here,ki tashi ki bar mana gida,daman iyayen ki suna nan kusa oya a bar mana gida kuma Allah ya isa amana ta da kika ci as small as you are!!!"..Bilkisu dai sai kuka take yi tana ba wa Mami hakuri tana cewa bata san komai gami da abubuwan nan ba amma ko a jikin Mami...
     "Please stop all this!!,meye haka wai??!",cewan Abba."ta bar gidan kawai that's all I know!!,sannan ta ja Bilkisu waje ta tura ta da karfi ta fadi.Ja'afar ya biyo bayan su yana hawaye,zuciyan shi na bashi cewan she is too innocent to do that..Hankade shi Mami tayi ta shige ciki..Ramlan kuwa wohoho dadi kashe shi.Ni kam nace karda kayi murna da yawa saboda in ka shiga hannu,baza ka ji da dadi ba..Sultee ma yana ta kuka ya ruga daki da gudu.Abba ya rasa nayi ma,da kyar ya ja kafafuwan shi ya zube a kushin..Duk jikin shi yayi sanyi,amma ya rasa nayi..
     "Tashi muje",Ja'afar yace mata tare da miko Mata hannu,da gudu ta rungumeshi tana kuka,"yaya wallahi ba ni ba ce,yaya na shiga uku,babu mai sona,na rasa TUDUN DAFA WA,ina zan je??kowa ya tsane ni,kace Mami tayi hakuri,wayyo yaya na shiga u.....","shhhhh,ya isa bari zan kai ki gida,zanyi wa baba bayani kinji kafin Mami ta huce"..Ja'afar ya san halin Mami,in tayi hushi sosai,loosing control take yi kwata2,ya san zata yafe mata amma shin waye yayi mata wannan sharrin?,tabbas ba zai wuce Ramlan ba neh,amma why does he hate her that much da har zai kulla mata irin wannan sharrin,he needs to be interrogated.................

*A/N:Allah sarki Bili na, Wallahi my heart hurts while typing this page,so young amma taga Rayuwa๐Ÿ˜”๐Ÿ˜ฐ*


_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar*_
[12/12/2016, 8:24 PM] Ummieejaafar
   *TUDUN DAFAWA                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                       *15*
 "Dakata dakata,meye haka?,nace ku dakata,meh annobar ga take yi a nan?",Baba yace a fusace.."Dan Allah Baba kwantar da hankalin ka nayi maka bay.....","kai Ku fita min daga gida!"cewan Baba."Ina son na ga Mama don Al...",amma bai bari ta karasa maganar ba ya hankade ta da karfi,"Ku fita nace"..."mallam lafiya?",cewar Umma da ta fito tana karkade zane...
      "Ayyo Bilkisu ce,zo mana'ya ta",cewan Umma.."ke nace Ku fita".."haba mallam ka bar....".."babu ruwan ki a zancen nan,koma daki".Sum sum sum ta shige daki gaban ta na dukan uku2 saboda ganin yadda Bilkisu ta murmure.."Allah ba ka hakuri,tashi mu je kanwa ta"...Tana mikewa ta fadi sanadiyyar kashin kafan ta da ya goce saboda faduwa da tayi kansa sau biyu.Hannu ya sa ya dago ta,ta soma tafiya ta na dingishi,suna kaiwa wurin kofa,ta bige kafar ta,wani ihu ta saka kana ta kankame shi,"innalillahi wa inna ilayhi rajiun,wayyo kafa na yaya"...Daga ta yayi suka fita sai mota. A bayan mota ya kwantar da ita, sai ihun azaba take yi.Da gudu ya figi motar,sai wurin masu gyaran kariya......

"Haba wifey,meh yasa kika dau hukunci tun ba ki yi bincike ba,yarinyar nan tana ta cewa ba ita bace ta dauk.....","Abban Sultan ya isa please!"Mami tace tare da daga hannun ta tana kuka..
    "Nima jiki na yana bani cewan ba ita bace,amma lokacin raina ya bace,I couldn't restrain myself, I was so stupid,na dau alhak...!!","shhhh,I understand, amma ki daina yawan yanke hukunci ba tare da kinyi bincike ba".."in shaa Allah na daina,gashi ban san inda yarinyar nan taje ba,na shiga uku,wayyooo Bilkisu na!"..Shiru Abba yayi kana yace "amma wane ne da wannan aikin??,someone must be investigated!",yace sannan ya fita..Ni kam nace, Ramlan! Sai ka yaba wa aya zakin ta,sai ka gwammaci kidi da rawa..


"Ya kafar yanzu?,"yana min zogi yaya",tace tare da share hawaye.Haka yake ta tuki duk jikinshi yayi sanyi yana tausaya wa Bilkisu..Daidai gaban get ya tsaya yana honk,tunanin abinda zai fadi yayi convincing Mami da Abba yake yi.Maigadi na bude get ya gaida shi yaja motar ciki.Bilkisu sai zazzaro idanu take yi,tana tunanin ina za ta je in Mami da Abba suka kore ta..
   Sallama yayi ya shiga falo tare da Bilkisu da ke goye a bayan shi.Mami da Abba da ke falo mikewa suka yi suna kallon su kana Mami ta karaso gaban su."Mami dan Allah ku yi hak.....",abinda Mami tayi ya sa ya kasa karasa maganar da yake fadi.Bilkisu ta cire daga bayanshi ta dora ta a kafadan ta ganin katon bandage dake kafar ta..Zama tayi a kujera da Bilkisu a kan cinyar ta sannan ta rusa kuka..
    "Ki yafe ni Bilkisu,ki yafe min,mene ne nayi haka,sanadiyya ta kika samu wannan ciwon,kaico na.kai....."."Mami babu komai,ba ki yi min komai ba amma please Mami ki yarda da ni ban dauka miki kudi ba"..ta karasa maganar tare da rungume Mami.Sai rizgar kuka suke tayi..Abba neh ya katse shirun,"kai Ja'afar jeka ka kira Ramlan da Sultan sannan kaje dakin Mamin ku ka dauko ledar da snacksa din nan ke ciki","toh Abba"...
     Bayan sun fito gaba dayan su kowannen su ya zauna harda Ramlan da bai lura da Bilkisu ba saboda yana chatting,gyaran murya da Abba yayi shi ya sanya Ramlan dago kan sa.Ido hudu yayi da Bilkisu,nan take jikin shi ya fari bari,zazzaro idanu yayi jin abinda Abba ya fada."Ja'afar je ka wurin Hamisu ka tambaye shi wanda yazo ya siya wannan a wurin shi"..Mikewa Ja'afar yayi,nan da nan gumi ya keto wa Ramlan,sai zufa yake ta yi...
    Bayan minti sha biyar ya dawo,saukan mari ya dawo da Ramlan duniyar da ya shiga."you are cruel,kai wani irin yaro neh?,meh ke damun ka,in iskokai kake dashi,to yau zanyi maka rukiyya da kaina",cewan Abba.Mami da Ja'afar da takaici ya cika su,shiru suka yi suna kallon su.."Kai Sultan je ka dauko min dorina a daki",da gudu Sultan ya ruga dakin mahaifin su."Abba kayi hakuri ba zan kara ba",yace tare da share zufan da ya jika fuskarshi.Ko kallon gefen shi Abba bai yi ba..Sultan na kawo dorina ya mike ya karba kana ya shiga da shi dakin horo dake gidan,kulle kofan yayi da sakata ta ciki..
    Ba wanda yace ko kala a cikin su.Bilkisu kuma sai jimamin abin take yi a zuciyar ta.Meh yasa Ramlan ya tsane ta ne har da yi mata sharri,kodayake ta saba da tsana da tsangwama tun tana karama..Habawa ihu kake ji mallam, Abba yana cire aljanun jikin Ramlan..lolzzz.. Sai da yayi mai isar sa sannan ya bude kofar ya tura mage ciki kana us rufo da padlock..Ramlan na bala'in tsoron mage,yana gani us fara ihu yana zufa yana kiran Mami amma ba Wanda yayi ta kan shi,asali ma mikewa suka yi suka bar falon..
     Can da dare Bilkisu tazo wucewa zata kicin,taji mutum yana cewa ruwa..ruwa,juyawan da zata yi sai taga Ramlan ne ta taga,duk ya canza ya zama wani iri... Kicin taje ta dibo mai ruwan gora mai sanyi ta kai meh, tana isa ya gan itace,jiki na bari ta mika mai, cafke hannun ta yayi kana ya watsa mata sauran ruwan da ya sha a jiki sannan yace,"mun zuba kenan ni dake,I will make sure you  hate life".................


*Hmm,ba Bilkisu kadai ba,har sai da nima naji gaba na ya fadi da irin threatening din nan๐Ÿ˜’*

_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar*_
[12/14/2016, 8:36 PM] Ummieejaafar
   *TUDUN DAFAWA                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar  
                      *16*
Bayan wata daya da faruwar hakan,Bilkisu suka fara midterm test.Wata malamar fine arts ta basu assignment akan suje suyi cardboard mat da kuma fure (roses) na paper..Tana isa gida ta sanar da Abba saboda ranar yana gida bai je duba shagunan ba.Nan da nan ya bata kudi yace ta siyo wajen Hamisu..Godiya tayi sannan taje ta zira hijabin ta ta fita siyo cardboard da water color....
 
Tana tafiya tana karatun Qur'ani dayake hadda da bita take yi a islamiya,sai ta hango motar gidan su,nan take ta sha jinin jikin ta saboda wanda ke cikin motar.Ba kowa bane face Ramlan...Sultee sai da yamma ake dauko shi saboda yana tsayawa a islamiya na sch wanda suke yi har alhamis..

Motar na kaiwa wurin ta,ta dauke idon ta da wuri,harara ya galla mata kana yace wa direba ya tsaya.Daidai inda take ya tsaya,"ke! Ina zaki?",yace mata yayin da yake saukar da gilashin motar."i....in..ina...ina son naje na siya cardboard paper neh",tace tana i'ina..

"Mtsssssw,mai ido kamar na aljanu kawai,Sule ja motar mu tafi",yace cikin isa babu koh girmama Sulen da ke da yaro sa'ar shi a gida...Sum sum taja kafs(lolzzz) dinta zuwa shagon Hamisu tayi siyayyar ta..

Tana isa gida,library ta shiga ta kama aikin weaving tabarma na cardboard paper.. Da kyar ta samu yankan yaje dai2..Awa uku taci tana hada shi,abin yayi kyau sosai da ta gama..A lokacin maghrib yayi sai ta fita taje ta gaida Mami a daki.."Abban ki yace kina nan kina assignment koh?",Mami ta tambaye ta..."eh Mami".."toh nima ayi min mai kyau in kun gama test,Allah shi baki sa'a,yayi miki albarka".."ameen Mami"..Daga bisa ni ta sallami Mami taje tayi sallah sannan ta koma library..

Sultee ta tarar a libraryn yana assignment.Ganin abinda take yi sai yaji sha'awar abin kana yasa hannu suka fara hada furen tare..Yayi kyau sosai.Bayan ta gama na assignment, sai tace bari suyi wa kowa da kowa dake gidan..Sultee yayi mata wani mai pink and light blue color, yayi kyau sosai sannan yayi wa Abba Red and green... Bilkisu kuma tayi wa Sultee dark blue and white sannan na yaya Ja'afar red and white,best color din shi kenan.Sannan tayi wa Ramlan Blue and black da ratsin white,maigadi kuma purple da white...

Raba ma kowa suka yi kana ta boye na Ja'afar a locker dinta yadda ba zai cikwuikwuye ba..Kowa na ta yaba kokarinsu amma banda Ramlan da yake ji kamar ya fashe don tsabar haushi..Can da dare ya tashi yaje library saboda ya gan Bilkisu a can ta bar assignment dinta..Zuwa yayi ya zuba duka paint din a kai kana ya yayyamutsa su sannan yayi murmushi yace "mutum sai iyayi"...

Washegari ta tashi confidently taje tayi aikin gida ta shirya,a lokacin ko waiwaya library bata yi ba.Sai da za ta wuce taje daukowa taga abinda kadan ya rage ta hadiye zuciya ta mutu..Tana fitowa taga sun wuce saboda ta tsaya tana kuka a ciki..Ranan a sch tun Anty nayi mata fada har ta gaji ta koma lallashin ta..A takaice ranan bata shiga shirgin kowa ba don takaici..Su Zahra ma da kyar ta gaya musu abinda ya faru..

Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa ga Bilkisu da Ramlan muguuu..

*A gurguje plzzz....*

*Bayan shekara biyar*

"Wayyo dan Allah kuyi hakuri karda Ku min fyade..Al...llahu..ma ajirni fi musee..ba..ba..bati,wakhlifny khairan minha",take ta fadi yayin da samarin suka yi sheqeqe,ko a jikin su.."Wayyo Ku bar min yaya na,meh tayi muku",cewar Saleema yarinyar Umma..

Saleema tana bala'in son yayan ta tun da ta dawo gida da zama.Umma ce ta tasa Baba a gaba har sai da yaje ya dauko ta..Mami tace Sam baza ta yarda ba,sai da Abba yasa baki yace 'yar su ce,ta bari ya wuce da ita...Umma bata son yadda yarinyar ta ta shaku da Bilkisu amma babu yadda ta iya....Soyayya mai karfi kuma ya kullu tsakanin Ja'afar da Bilkisu.. Hakan ba karamin dadi yayi wa su Mami ba..Haka tana aji na karshe 
Kenan a school yayin da Saleema take nursery 3..Ramlan yana IBB lapai inda yake karanta _Mass comm_.Sultee kuma yana zaman gida saboda ya gama school a 14yrs akace baza a iya bashi admission ba sai ya shiga 16yrs..Bilkisu da Saleema suna dawowa daga makaranta neh 'yan daba suka sace su zuwa wani gini da ba a gama ba a unguwar...

"Wayyo kuyi hakuri",cewar Bilkisu...B'arka mata vest yayi saboda sun cire long sleeve rigan ta sun cillar.."kai yarinyar akwai dukiya fa,ai dole mu cika aikin oga",wani cikin su yace yayin da yake kokarin cire wandon sa..daga bakin kofa suka ji wani yana cewa"kai! Ku dakata ni zan fara tukun"sannan yayo kan Bilkisu ya fizge skirt dinta cikin zafin nama sai ya.................


*Wayyo Bilkisu, Wa zai kawo mata dauki???*

*Ku biyoni don sanin wa ya aika ayi mata fyade kuma wa ke shirin yi mata fyade!!!*_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[12/17/2016, 6:14 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                     *17*
    Ja'afar yana karyo kwana cikin anguwar su Bilkisu ya hango wata kamar Saleema tana fitowa daga wani gini tana kuka.Honk ya fara busa mata tun daga nesa amma ina?? Ko tsayawa bata yi bah sai ya sauka a gaban ginin domin yaga ko lafiya take gudu?...
   "Allahuma ajirni fi musibatee,Bilkisu!!!!",ya Kira sunan ta tare da zubewa akan gwuiwansa ta gefen ta..Tana kwance jina jina,dukkan tsiraicin ta a waje... Wani kuka mai tsuma rai ya fara yi..
   "Why?,why?,me kika yi musu suka yi miki..."bai ma iya karasa zancen ba,ya rike hannun ta yana jijjiga ta yana kuka..
    "Kan uban can me zan gani haka??"
   Da sauri ya dago ya kalli Umma dake tsaye tana wani karkade jiki kamar budurwar tunkiya..
  "Umma kalli abinda suka yi wa...."
   "Kai ja'iri yi min shiru,kun gama jin dadin Ku sannan kace wani wai wai wasu,Dallah ke zo mu wuce"
    "Umma wasu n...
"Ke yi min shiru kizo mu wuce kuma sai babanku yaji zancen nan""
  "Wallahi Umma nima ban san wanda yayi..."bata bari ya karasa maganar ba ta ja hannun Saleema suka wuce..
   "Wato sharrin da Umma zata laqa min kenan,Allah gani gare ka"..Kallon ta ya kuma yi ya tuna cewan bata ko numfashi.Da sauri ya gyara mata sch skirt din ta sannan ya ciccibe ta zuwa mota...
   Da gudu ya figi motan sai kofar gidan su Bilkisu. Yana shiga ya ci Karo da Saleema.
  "Kanwa ta,je ki dauko min riga da zani da hijabin yayar ki"
    "Toh yaya",tace sannan ta juya taje dakin.
   "Anyi abin kunya ai dole ta kasa zuwa ta dauka da kan ta"cewar baba da ya fito daga dakin Umma.Umma tana biye dashi tana murgude murgude..
   "Wallahi baba ba.."
"Yi min shiru ai ba yau na saba ganin Ku tare ba,sai ka dauke ta kuje anguwa kuyi ta shashancin Ku koh??.,yau ka kasa hakura har...."
  "Baba ya isa! I can't take this anymore!,Saleema kawo min kayan nan"
   "Eh lallai fa,mallam ai dole ya daga ma murya,tunda 'yar ka ta bashi kan ta"
   "Yaya zan bika",cewar Saleema tare da gyara hijabin ta.Hannun ta yaja suka fita yayin da baba da Umma ke bin su a baya.
   "Ke dawo nan"
"Ka dauke ta domin kaje ka karasa iskancin da ita koh,ke don ubanki baza ki dawo ba?!",baba ya karasa maganar cikin tsawa.Koh ta Kansu Ja'afar be bi ba,motarsa yaja suka kama hanyar Dr. Wahab hospital....
   Da isar su aka basu gado a ER.Ja'afar ya rasa nayi,ya rike hannun saleema gagam.Saleema kuwa sai kuka take tayi tana cewa "yaya".Can ya zare wayar sa ya Kira Abba.
  "Hello Abba"..ni kam nace Ja'afar an manta da sallama yau...
  "Abba please kuzo Dr Wahab hospital yanzun nan"
   "Lafiya son? Me ya faru?"
  "Abba Bilkisu ce.sun..sun...kai Abba kuzo dai"
    "Toh sai mun zo,just keep calm kaji??"
 "Toh Abba",sannan ya katse kiran.
 
********
*_Bosso Estate_*

"Wallahi ba zai yiwu ba mallam,ka tashi muje gidan iyayen yaron nan"
   "Toh sawo hijabin ki muje",yace kana ya juya ya shiga dakin mahaifiyar Bilkisu.
  "Lami kin ga abinda annobar nan tayi koh?,tana so ta zubda mana da mutunci"
    "Lami kiyi hakuri amma dole na aurar da yarinyar nan kafin ta karasa ni nima",ya karasa zancen rike da hannun Mama a hannun sa..
   "Uh..uhm,mallam sai ka fito muje koh?",cewar Umma da ke matukar jin haushi in taga mallam yana magana da mahaifiyar Bilkisu.. Ni kam na ce mata hoo! Kishi harda wacce bata hayyacin ta,Allah ya ganar damu.
    Fitowa yayi ya burga babur dinsa da ya siya kwanaki,Umma ta hau bayan mashin din sai gidan su Mami..
   "Assalamu alaikum"
"Wa alaikumussalam, sannun Ku da zuwa",cewar Mami da take saukowa da hijabin ta a hannu..
   "Habeebee ga su Umman Bilkisu sunzo"

"Sannun Ku da zuwa cewan Abba da ke saukowa daga bene"
   "Yawwa Alhaji"
"Asibitin zaku kuma koh?",cewan Mami..
   "Oh ashe har sun kira ku?",cewan baba.
   "Eh",Mami ta amsa da sauri,"muje koh?"
  "Ai batun wucewa bai ma taso ba",cewar Umma..
"Toh,da fatan lafiya dai koh?",cewan Abba da yake kokarin zama.
    "Wallahi Ja'afar yaci amanar 'yar mu,fyade yayi mata fah",cewan Umma.
   "What?!",Mami da Abba suka ce lokaci daya..
 "Ke Mallama bama son rainin hankali fah,dan namu zaki yi wa sharri?",cewan Abba a fusace.
   "Alhaji ina jin kunyar ka fah,ka bari tayi maka bayani mana",cewan baba.

  "Bayanin banza,na san Ja'afar dina ba zai yi haka ba",cewan Mami da ta gama quluwa..
     "Yi shiru Wifey,bari tayi bayani"
   Zama Mami tayi kana Umma ta zayyana musu karya da gaskiya harda hawayen munafurci,har tana cewa da idanun ta biyu ta gansu a wannan yanayin.
   Baba shi dai bai ce komai ba..Yadda Umma ta bada kagaggen labarin ta,ko za a sa maka wuka a wuya ne mutum zai ce gaskiya take fadi...
    "Mu Ja'afar zai zubda wa da mutunci,toh in shi mutumin banza neh,mu ba mutanen banza ba neh,shi yasa ya kasa gaya min abinda ya same ta da na tambaye shi",Abba ya fadi a fusace tare da mikewa.
    "Wifey zo mu wuce asibitin muga halin da innocent girl din nan ke ciki",mikewa Mami tayi ta bishi,su Umma ma suka bisu a baya.Duk jikin Mami ya yi sanyi,ta kasa yarda da cewan Ja'afar din ta zai yi haka.
   *******
*_Dr Wahab Hospital_*

Suna isa suka hango Saleema da Ja'afar a bakin kofar shiga ER.Saleema tana hango su ta rugo da gudu tazo ta rungume Mami ta na kuka,
   "Mami su ne..su ne.."
"Ke don uban ki wato sai da kika biyo shi bayan abinda yayi wa yayar ki koh",cewan Umma da ta ga Saleema za ta tona mata asiri.
   Ja'afar da yaga Saleema ta ruga da gudu, sai ya kalli wurin yaga su Mami ne ke zuwa,sai ya taso yana share hawaye.
   Yana isa gaban su Mami ya bude baki zai yi magana kenan kawai sai saukan mari yaji..
   "Ashe kai dama yaron banza neh ban sani ba?"
 "Ab..b.baa",Ja'afar ya kira mahaifinsa da i'ina.
   "Meh tayi maka that you have to punish her this way??,why did you rape her??"..
  "Rape her!rape her!!rape her!!",maganar dake ta ringing a kunnen sa kenan..Kawai zubewa yayi a wurin sumamme.
   Mami na ganin haka ta kira nurses,Abba kuwa ko a jikin shi..Nurses maza suka zo suka dauke shi tare da baba da ya taimaka musu. ER suka wuce dashi shima,da yake sun san shi ya kawo Bilkisu,suna tsammanin mijin ta neh tun da sun gano cewan raunin da ta samu na saduwa neh,an shige ta sosai.Sai suka kai shi dakin da take itama..
    Mami kam in banda kuka da addu'a babu abinda take yi.Ya zata yi,yaran ta biyu a lokaci daya sun shiga wani mawuyacin hali. "Meh yasa bamu yarda mun aurar dasu ba lokacin da yace yana son ayi auren",cewan Mami a zuciyar ta..
   Abba kuwa sai basu baba da Umma hakuri yake yi yana kara jin takaicin abinda Ja'afar yayi.
   Sai da likitoci suka ci awa biyu a kan Bilkisu ana dinka ta saboda ba karamin rauni taji bah,da ta farfado sai ta firgita ta suma kuma.A na ukun ne bata suma bah,sai kuka take tayi tana fadin "ka yafe min"..Can anjima aka fitar da ita zuwa special ward meh gado biyu a ciki inda aka mayar da Ja'afar da dadewa saboda ya farfado kafin ita.
    Abba suna ganin an shigar da Bilkisu dakin,suka je su ma.Fashewa da kuka tayi da ta gan su Abba..Juyawa tayi ta bangaren Mami da Ja'afar.
   "Mami kice yaya ya yaf...."
  "Bilkisu zan kwatan miki 'yancin ki,bazan yarda Ja'afar yaci galaba a kan ki a banza ba",Abba ya katse ta.
   "Ab..bb.ba,ban gane ba",cewan Bilkisu.
   "Nufi na shine sanadiyyar fyaden da Ja'afar yayi miki,na yanke hukuncin daura meh aure da ke!!"        

"What!!!",cewan................


*_Toh masu karatu Ku biyo ni don sanin waye ne yayi wannan reaction din?!!!๐Ÿค“_*


_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[12/19/2016, 11:51 AM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                      *18*
*_Billionaires quarters_*

"Hello,yaya gamu a gidan Ku amma only Sultan is at home,wai ance mai kuna asibiti"

"Waye bai da lafiya?"

   "Ja'afar da Bilkisu?,toh Allah ya sauwake..bari mu garzayo can",Mommyn su Asmee ke waya da Mami..
     "Mommy wai meh ya same su?",cewan Asmee..
   "Bari dai sai mun je asibitin",cewan Mommy...
   Zahra kam duk hankalin ta ya tashi da taji cewan an kwantar da su Bilkisu a asibiti.
    Sultan ma mikewa yayi ya bisu..Suna is a Dr Wahab hospital suka shiga reception suka tambaya inda special ward yake aka kai su...
     Suna shiga dakin kenan Abba yake cewa,"............nah yanke hukuncin daura meh aure da ke!!"

          ***********

"What?!!",cewan Asmee yayin da ta karaso ciki da sauri..
    Lokacin Mami suka lura da isowar su.."A'a,har kun iso",cewan Mami.
"Eh wallahi, ya masu jiki?"
   "Toh jiki alhamdulillah",Mami ta karasa zancen tana shafa kan Ja'afar tamkar karamin yaro..
  Kowannen su suka gaida Su Mami, Abba,Umma da baba banda Asmee da take son jin karin bayani game da abinda kunnen ta ya jiye mata..
   "Ke baki iya gaisuwa ba koh",cewan Mami da take jin takaicin halin Asmee..
  "Ya zanyi gaisuwa bayan naji ana wani zance da ya tada min da hankali"
    Da mamaki Abba ya juyo ya kalle ta kana ya tambaye ta cewan''wani zance kenan Asma'u"
   Sunan da ya Kira ta neh ya kara kular da ita."zancen wai ko bros za a yi wa aure da wannan",tace tana wani murza idanu kamar mujiya..
   "Eh za a daura wa yayan Ku aure da Bilkisu neh,Do you have any problem with that?",cewan Mami..
  "Ya zaku yi min haka bayan kun san shi nike so,in fact shi nike jira shiyasa banyi aure bah",tace tare da sa musu kuka...
    Kallon ta kowa ya ke yi bama kamar Bilkisu da Ja'afar bah..Shi Ja'afar yaji dadin zancen auren su da aka yi amma tunani daya neh ya makale masa a kwakwalwa..Shin wanene yayi wa Bilkisu irin ta'addancin nan?,so wani ya riga shi sanin matan shi kenan...
     Bilkisu kuwa abubuwa da yawa ke yawo a kan ta?,daman yaya neh yayi mata fyade?kai bashi ba neh,suna da yawa fa,but would he accept me the way I am?,he doesn't deserve me.Na kasa kare mutuncin kai na..
   "Why me?,why,why.....",abinda Bilkisu ta soma fadi kenan tana kuka.
   "Shhhh..Bilkisu ke daina fadin haka nan kina nufin cewa *Allah bai isa dake kenan ba koh ko kuma kina da ja da abinda Allah ya nufa,Sam Sam wannan ba Kalmar da ya kamata ya fito daga bakin musulmi ba neh*",cewan Mami da ta rungume ta...
   Zahra ma zuwa tayi ta zauna a gefen Bilkisu ta rike mata hannu tana mai murnar Bilkisu zata zama Inlaw din su amma ita ta kasa gane sauran zancen da ake yi,amma ohho dai happy she!!
    Sultee shima zama yayi a gefen Ja'afar ya rike hannun sa.
   "Congrats bro,ashe ciwon so kuke yi a nan",murmushi kawai Ja'afar yayi wa Sultee..
   "Kai yi mana shiru ba ma son shashanci a nan,ke kuma Asmau idan munje gida zamu zanta da ke",cewan Abba da zancen Asmau da Sultee ya kara kular dashi..
   "Toh mu zamu wuce,kun san mun bar mahaifiyar ta a gida,anjima zamu dawo mu dauke ta",cewan Umma da kwata2 bata ji dadin zancen auren su ba.Ta so Abba ya kore Ja'afar neh sannan ya tsani Bilkisu amma ko kadan bata ga alamar cikan burin ta ba,amma babu matsala tunda ta samu abokiyar adawa da su,wato Asmee...
    "A'a ba sai kun dawo ba ma,zamu kai ta can gidan mu har taji sauki tunda sanadiyyar mu ta samu wannan raunin",cewan Abba..
   Baba bai so hakan ba saboda ya so ne yaci kaniyar ta in sun je gida amma ba yadda ya iya."Toh",yace kawai sannan ya riko hannun Saleema da take gefen Zahra..kuka Saleema ta Fara yi..
    "Ni dan caya da yaya.wayyo yaya Jara zan caya da yaya Bikitu neh",amma ina Baba ya finciko ta waje ya sata a gaban Babur,Umma ta hau baya suka yi gaba..
   Duk Mami tana Lura da take taken su musamnan Umma,bata yarda da matan nan ba..
     "Toh muma zamu wuce,sai mun leko Ku a gida",cewan Mommy fuska a daure..
   "Toh mungode Khadija,jazaakumullahu khairan,sai kun zo "..
   Ko amsa addu'ar basu yi ba,kofar fita suka nufa Mommy ta juyo ta kalli Zahra da koh motsawa bata yi ba daga inda ta ke.Watsa mata harara tayi kana ta ce,
  "Ke kuma yaya haka?"
"Ayya Mommy ki bari na tsaya da ita please"
    "Saboda kanwar uwar ki ce koh?"
"Aah Mommy meh yayi zafi haka,kiyi hakuri mu je",Zahra tace tare da sumbatar goshin Bilkisu ta sallame ta kana taje wajen Ja'afar shima ta sallame sa sannan ta sallame su Mami,Abba da Sultee.
   Finciko ta Asmee tayi suka fita daga dakin.Baki galala Mami da Abba ke ta kallon su har suka fita..
   Ja'afar kuwa dadi yaji da suka wuce saboda baya son irin kallon da Mommy da Asmee suke ta yi wa Bilkisu.Ajiyar zuciya yayi sannan ya juya ta daya bangaren ya fara barci..
   Bilkisu ma dadi taji da suka wuce saboda sun takura mata da harara.Kara gyara kanta tayi a jikin Mami yayin da Abba da Mami suka ce mata sannu lokaci daya..
   Mikewa Abba yayi yace zaije gidan kanwar sa da ke Farm center ya karbo musu abinci..
   "Uhm Abba,Mahneerah tace zata kawo in 20minutes time",cewan Sultee yana dan soshe soshen kai kamar mara gaskiya..Mami dai ta gano inda dan ta ya dosa,murmushi kawai tayi..
   "Ok ka sanar da su neh?",cewan Abba..
  "Eh",ya amsa da..
"Ok bari naje na ga Alhaji Muhammad domin muyi magana kan yarinyar nan,naji kince Mommyn su Zahra tace ya na gari"
  "Toh,a dawo lafiya",cewan Mami rai a bace.Ita dai duk da ta san yaron ta yayi laifi,amma bai kamata Abba ya yadda a hada shi da Asmee mara kunyar nan bah...


               **********

    Wata beautiful girl na hango tana tafiya tamkar dawisu..Kana ganin ta,ka ga yarinyar da tasha hutu amma.........da tarbiyya mai kyau.Sanye take da tiyobo hijab mint color sannan da black socks.Fuskar ta yasha ado..nikam nace da kin hada da niqabi ai..
    Tana da slim face,sannan idanuwan ta dara dara,kwayar idonta grey color ne da black Wanda yayi mugun fito da kyawunta.Gata da long eyelashes sannan da bakin gira da karamin madaidaicin bakin ta da yasha lip glow.
    Rike take da food basket tana shigowa ta reception din Dr Wahab hospital.A yadda na karance ta,shekarunta ba zasu haura 14 ba,sai dai tana da jiki mai kyau...
    *Mahneerah!!*,naji Sultee ya kira ta da yake zaune a wurin yana jirar ta..Irin murmushin da ta sake yasa waya na ta fadi๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜• tsabar kyawun ta da yayi min shoki.............hahha


*_Ku biyoni don sanin wacece Mahneerah…??๐Ÿ‘ธ๐Ÿป_*

*_A/N: assalamu alaikum masoya na..da fatan kuna lafiya?,ina son nayi using wannan medium din neh nayi kira zuwa ga 'yan uwa na game da fadin Kalmar "why me?",idan Allah ya jarrabce su da wata musiba domin jarraba imanin su.Sam Sam wannan ba dabi'a Mai kyau bace ga musulmi...Allah ya Riga ya bamu remedy na wannan abin,Allah madaukakin sarki yana cewa"Allazeena aswabat-hum museebatun Qwalu Inna lillaahi wa Inna ilaihi raaji'un"..Ma'ana: wa'enda muka saukar musu da musiba suna cewa Daga Allah muka zo kuma gare shi zamu koma!!..wallahi a'alam..Allah ya ganar da mu kuma ya bamu ikon kiyayewa daga kwafan koma menene na sharri da muke gani a films ko kuma a novels..ameen..Da fatan kun karu da wannan sakon nawa..Allah yasa mu dace,ameen..ina kaunar Ku har abada!!_*

~Taku har kullum~

_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[12/21/2016, 6:14 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                     *19*

*Mahneerah Sadiq*

Itace yarinyar kanwar Abba dake zaune a farm center..Itace only sister na Abba,Hajiya Rahma..Kyakkyawa ce sosai,kamanninsu daya da Abba sannan tana aiki a wuri daya ne da Mami..Mijin ta Alhaji Sadiq Sadauki shine CEO na Jap.made Cars Limited.
    Mahneerah itace only daughter na su kuma suna ji da ita sosai.Mummynta ta bata tarbiyya mai kyau duk da irin daulan da ta tashi a cikin sa..Ba abinda zata nema ta rasa a wurin iyayen ta amma wasu lokutan ana hana ta wasu abubuwan domain ta san ana rashi wani lokaci a rayuwa saboda,'yan Karin magana sunce ba kullum a ke hawa gado bah..
     Mahneerah ta kasance yarinya mai fara'a,sam2 bata kyamar talakawa saboda haka ta taso taga iyayenta,suna kyautatawa jama'a..Ga ta da kokari a makarantar boko da islamiyya saboda har musabaqa take zuwa da quiz competitions..She is so nice to be with!!

         *** *Cigaban labari* ***

"Ya Sultee",ta kirashi da funny voice din ta.Karban basket din abincin yayi daga hannunta sannan suka karasa cikin dakin da aka kwantar da su Bilkisu..
    Har yanzu Bilkisu tana nan tana kuka saboda duk lokacin da ta yi yunkurin mikewa,sai taji kamar gaban ta zai yanke ya fado don azaba.Mami kam sai bata baki ta ke yi har su Sultee suka shigo dakin..
   "Mahneerah ta,matso nan"
  "Ina yini Mami",tace cike da jin kunya.
  "Lafiya lau baby na,ya gida,ya Mummyn ki??"
 "Lafiya lau,alhamdulillah, Mummy wai tana gaishe ku, tace zata shigo anjima da dare"
  "Toh madalla,amma taje wajen aiki yau kuwa?"
 "A'a,itama tana gida,Mami ya masu jiki?"
"Alhamdulillah Mahneerah,Ja'afar ma yana bacci"
  "Anty Bilkisu,ya jiki??",Mahneerah ta tambaye ta tare da karasowa gefen ta.Daga mata kai tayi alamar da sauki..
    Zama tayi a kujeran dake gefen Sultee kana Mami tace musu tana zuwa,ta fita waje..


            ********
      Sai da Bilkisu ta kai sati daya a asibiti kafin aka sallame su da cewar zasu dawo a kwance dinkin.Ja'afar kuma yana nan yana zirga zirgan auren sa da Asmee saboda Abba yace tunda bai iya controlling din kan shi bah,za a aura masa Asmee da Bilkisu amma Asmee ce zata tare kafin Bilkisu saboda ba zai so ta kara jin rauni ba bayan na da.Ba yadda Mami da Ja'afar basu yi bah cewan Abba ya janye zancen aurensa da Asmee amma ya ce sam..
    Hakan ya sa Ja'afar da Bilkisu a cikin damuwa duk da Ja'afar bai sake wa Bilkisu fuska kuma saboda itace silar abubuwan da ya faru cikin dan kwanakin nan..Abin na matukar damun Bilkisu yadda ya juya mata baya a lokacin da ta ke bukatan mutum a kusa da ita..
    Zahra,Sameerah da Mahneerah suna zuwa wurin ta kullum,har Zahra da Mahneerah ma suka tattaro inasu2 suka tare a gidan Abba.Ba karamin dadi Mami ta ji ba saboda tana bala'in tausaya wa Bilkisu ganin Ja'afar ba ya kula ta..
     A bangaren Ja'afar kuwa ya rasa wurin da zai sa kan sa,kwata2 ya rasa *tudun dafa wa*..Kullum cikin addu'a yake Allah ya tabbatar masa da alkhairi game da bikin nan.Asmee uwar rawan kai kullum sai ta Kira shi fiye da sau ashirin kamar zautacciya,kodayake ta zauce akan soyayyar da take yi wa Ja'afar din ta...An sa date na biki nan da two months domin Bilkisu ta samu ta rubuta exams saboda Abba yace ba ita ba school sai bayan ta tare zata fara zuwa makarantar jami'a.A yanzu dai za a cigaba da yi mata lesson har ta rubuta external exams..


*Bosso estate* ***

"Wai mallam haka cigaba da zuba wa Alhajin nan ido har sai yasa an daura auran nan?"
   "Toh in bai aure ta bah,wa zai aure ta,haka kurum ya lalatata ya wuce?"
  "Ni kam bai dace bah,ya aure ta suje su cigaba da iskancin su,haba mallam ka Kara duba zancen mana"
   "Zancen banza zancen wofi,ba matar shi ba ce ko sunyi iskancin bare ai tsakanin mata da miji babu iskanci,bana son irin zancen nan"
    "Toh Allah ya baka hakuri",cewar Umma tare da shigewa daki tana maganganu..
  Mikewa Baba yayi ya shiga dakin mahaifiyar Bilkisu wato Mama."Lami kin ga 'yar ki koh,irin rayuwar da ta zabar wa kan ta ba mai kyau ba ne,saboda kwadayin kudi ta sake wa namiji jikin ta,ya lalata ta,kai yarinyar nan baza ta taba ganin haske ba a rayuwar ta",ya karasa zancen yana jin wani daci2 a zuciyar sa....

*One week kafin biki*

    "Hehhe Amaryar yaya Ja'afar kin sha kamshi",cewan Mahneerah..
  "Hmm,ke dai kyale,taji dadin ta,she is getting married @ 18,wallahi ance yafi dadi mace tayi aure at this age",cewan Zahra da ke gefe tana admiring yadda Bilkisu ta kara kyau tayi mulmul..
   "Please girls,Ku bar zancen nan",cewan Bilkisu da sam2 zancen su ba ya mata dadi saboda gani take kamar Ja'afar ba ya son ta, so baza tayi enjoying auren ba kamar yadda suke tsammani..
   "Hmm,ana so ana kaiwa kasuwa,mu dai a bar yin munafinci,na san Allah2 take yi taga kan ta in his arms dauke da dan babynmu a ci...",dukan da Bilkisu ta kai mata yasa Zahra ta kasa karasa maganar..
    "Wallahi sai na rama"..Nan suka fara bin juna a guje suna dariya sai ji kawai tayi ta ci Karo da mutum...
   "Tassssss!"kake ji kawai,karar saukan mari. Dagowa dukkan su suka yi a firgice domin ganin wanda yayi marin kuma wa ya mara... Ido hudu suka yi da Ja'afar da ke tsaye gaban Bilkisu yana huci...
   "Ke wata irin yarinya ce,kina abu kamar baki san kin girma bah iyye??,wato jin dadin ki ma yayi yawa har da guje2 kike yi,ni ina can ina shan wahala saboda bakin cikin da kika cusa min,da auren Asmee zanji da koh kuma da.....",da sauri ta sa hannu kan bakin shi domin karda ya karatsa sauran zancen saboda ko da wasa bata son Sameera da Zahra suji wannan zancen..
    A fusace ya cire hannun ta daga kan bakin shi sannan yayi nuni da ita yace "be careful!",sannan ya raba ta gefen su ya wuce...Zubewa tayi a wurin ta fara kuka mai tsuma rai.Su Zahra ma jikin su yayi sanyi,durkusawa suka yi a gefen ta suna bata hakuri..
    "Ke,Dalla can da kukan munafuncin nan,ai yaya ma yayi kokari da ya yarda da cewan zai aure ki",cewan Ramlan da basu ma san ya shigo bah..
"Haba,Ramlan,maimakon ka bata hakuri shine kake kara yi gaya mata magana mara dadin ji  ",cewar Zahra.
   "Please kiyi min shiru,ba ki san cin amanar da yarinyar ga tayi mana ba,second hand crap kawai!!"
   "Please Ramlan kayi min rai kayi shiru,karda ka fadi",cewan Bilkisu cikin shesshekar kuka.
   "Dan Allah Ku yi min bayani,kun samu a duhu,what's going on??",cewan Mahneerah.Sameera kam shiru tayi kafin tayi magana ya yaba mata magana...
  "Ki zo garden anjima da dare,i will tell you everything!",yace tare da yin wani shu'umin murmushi ya haye sama abin shi..Rike ta suka yi zuwa daki..Bilkisu kuwa hankalin ta ya tashi,bata son Ramlan ya fada musu halin da take ciki,dole ta nema hanyar bashi hakuri..
     Wuraren karfe shida na yamma taje ta roke shi cewan karda ya fada masu, ya rufa mata asiri cox itama bata san yadda akayi mata fyaden bah.Cewa yayi ya ji amma taje ta dawo anjima ta same shi a garden,zai yi wata magana da ita..
      Nan da nan tace toh,not knowing that akwai abu a kasa..Bayan an idar da maghrib yayi mata flashing alamar ta zo garden sannan ya kuma yi wa Zahra call itama..
   Da sauri ta fita daga daki taje, dai2 Zahra na fitowa daga kicin da coffee da yace tazo dashi..Tana isa garden tazo gittawa a gaban shi sai yasa mata kafa ta fado a jikin shi,dai2 Zahra tana shigowa da coffee din a hannu...
    "Bilkisu????!!",ta fadi tare da sake cups din coffee din a kasa ta juya da gudu. Kafin tayi yunkurin kwace kan ta,sai ga Ja'afar ya shigo..."Ramlan??Bilkisu??",yace tare da garxayowa inda suke cikin bacin rai....


*Toh fah,another wahala don come๐Ÿ˜Ÿ*


_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[12/24/2016, 9:06 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                      *20*

      Karasowa ciki yayi kana ya dago Bilkisu daga jikin Ramlan,ya watsa mai mari wanda zai sa mutum ganin taurare..
      "Wallahi yaya sharri zai yi min,I don't know how it happened na gan kaina a jikin shi",tace tana kuka..
     "Bro zaka yarda da ita neh,can't you see,kawai tana son tayi defending kan ta ne,she was seducing me.?",cewar Ramlan..
   Ja'afar da ya gama kulewa ya juya ta bangaren Bilkisu ya dago hannunsa da ya dunkula,duk idanunsa sun kada sunyi ja tsabar kunar rai da yake ji..."dummm!",da sauri na jiyo domin ganin wanda yayi wa kullin sai naga Ramlan a kasa yana zazzare idanu....
    "Ramlan I'm suspecting you,yaya ka san da zancen fyade da aka yi wa mata ta?,who the hell told you about it??",ya karasa zancen cikin tsawa...
    "Ni ban san komai ba fah"..
  "I swear I'll kill you and no one dare ask me the reason for that!"
   "I know nothing,kan karuwar ga ka daga hannun ka ka mare ni,you shall see. Wallahi sai na zamo ajalin ka!",Ramlan yace tare da mikewa a wahalce ya wuce..
    Juyawa yayi ta bangaren Bilkisu ya gan ta a tsugune tana kuka.."why,yaya why?meh nayi musu da suka yi min irin azabar ga,I kept myself for you but they deprived you of that,why???, yaya abinda yafi ci min rai shine ban san ko su waye ba neh",ta karasa zancen tana kuka mai ban tausayi...
    "I love you that way,ina ji a raina cewan Ramlan yana da hannu a case din nan saboda naji abinda yace miki a lokacin da na mare ki,I'm so sorry,I never meant to hurt you.Na rasa ta yaya zan gano wanda yayi miki haka neh shiyasa na dau shawarar da zuciya ta ta bani akan na aiwatar dashi duk lokacin da Ramlan ya dawo"...
    "Yaya ban san da wani baki zan gode maka bah,yaya ina jin kunyar ka I couldn't protect my pride for you,please ka duke ni son ranka duk da na san ba zai sa ka huce bah amma saboda ban san ta ya zan biya ka bah, I prom...."
    "Shhh its ok baby nah,miko hannun ki na daga ki"..
    Wani tingles suka ji yana bin jikin su a lokacin da ya riko hannun ta,kura wa juna ido suka yi suna ji kamar su rungume juna..Da gudu ta ja hannun ta ta gudu zuwa main house da taga ya rage kiris Ja'afar ya rungume ta..Lumshe idanuwa yayi yana jin son ta yana Kara ratsa shi..
   "I'll always be there for you kissy",sunan da yake kiranta da shi kenan..Fitowa yayi yaja ciki shima yana jin dadi matuka a zuciyar shi kuma ya dau alwashin dauka mummunar hukunci a kan duk wanda yake da hannu a fyaden da aka yi mata..


        ******######*****

Da dare tana zaune a daki bayan ta idar da sallah,sai tunanin abinda ya wakana a garden dazu take yi..Kafin ta ankara sai taji karar wayan ta alamar sako ta shigo,da sauri ta dauka ta duba..Sako ne daga HUBBIL KHAIR..
     _"Don't hate me,desert me,don't give up on me.I'm sorry if I've never counted on you,You are my one and only love..Sorry for all the times I've shunned you..ina matukar sonki my kissy...Have a stressfree night๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹"_

    Murmushi tayi har sai da kumatun ta ya lotsa.."ina matukar son ka nima",ta furta a hankali tare da kissing wayar...Qur'anin ta ta bude ta karanta Suratul mulk sannan ta mike ta nannade sallayan ta ajiye shi a ma'ajinshi..Rigar baccin ta,ta ciro ta saka sannan ta sa hula ta kakkabe saman gadonta,ta yi addu'a ta kwanta..Waya ta dauka ta Kira Mahneerah da Sameera ta san ko sun kai gida lafiya saboda anyi wa Mahneerah urgent call,Sameera kuma wai bro dinta zai dawo,shiyasa suka wuce..Bayan ta kammala ta tuna Zahra,tun da ta gan su a garden basu hadu ba kuma,"meh yiwuwa tana dakin Mami,gobe zan neme ta",cewar Bilkisu..
    Hoton handsome dinta ta bude tana kallo har bacci mai dadi yayi gaba da ita.. Ja'afar shima wayarsa ya bude ya shiga kissyfolder yana kallon pics din su har bacci barawo ya sace shi...A takaice wutar da Ramlan yaso yasa wa fetir ta juyo kanshi saboda sharrin da yaso ya kulla wa Bilkisu ya zamo sanadiyyar Kara rurin wutar so a zuciyar masoyan.
    *Bosso Estate*

"Wato mallam haka za ka sa ido su ajiye yarinyar nan a can koh,suna Kara tambadewa...."
   "Meh yasa kin cika surutu neh,don Allah ki bari naji da abu daya mana..mtssw",cewar Baba sannan ya mike ya shiga dakin sa..
   "Wallahi ni kam sai naga bayan yarinyar nan kafin mallam ya fara son ta....",tace tare da shigewa dakin ta itama.
   Baba dai Allah yana ta Kara musu budi saboda yayi modernizing kasuwancin kwanukan sa da taimakon Allah ta Abba,yanzu shaguna biyu gare shi,daya a can garin su wanda yaran aikinsa suke kula da wurin sai kuma na nan cikin gari...Ya gyara gidan sa,anyi wa gidan sabon fenti..Umma da Saleema kuwa sai sheki fatar su ke yi don jin dadi...Duk da wannan jin dadin amma Umma tana so taga bayan Bilkisu saboda tana tsoron idan mahaifin Bilkisu ya rasu,a bai wa Bilkisu kaso Mai yawa na gadon...Allah ya shirya!
     
                 *21*

         *Gidan su Mahneerah*

"Assalamu alaikum"
"Wa alaikumussalam, Mahneerah karaso ciki da wuri,Daddynki ne bashi da lafiya shine nake shirya shi muje asibiti"..Da sauri Mahneerah ta karasa ciki har tana cin tuntube.."Kira min uncle Babur (The brave or jarumi shine ma'anar sunan)yazo ya kai mu asibiti"..Juyawa tayi zata fita amma Daddynta ya rike ta gam yana kallon ta yana murmushi..
   Rungume shi tayi sannan ta dauki wayan ta ta Kira Uncle..Cikin minti sha biyar suka kai Daddy asibiti..Yana fama da ciwon diabetes kuma yayi tsanani sosai..Haka ake ta abu daddaya har da gari ya waye, rai yayi halin sa..
    Su Ja'afar da su Bilkisu,Mami da sauran dangi duk sun hallara..Kuka mai tsuma rai Mahneerah take yi..Irin kuka na masu hankali ba na hauka bah(mutum za iya yi wa dan uwansa kuka idan ya rasu amma ba kukan hauka ba,haka zalika zaman makoki har na kwana uku ya halatta,amma zancen sadakan uku bai samo asali daga Qur'ani ko sunnah bah.Allah yasa mu dace)...
    Sultee zama yayi kusa da Mahneerah yana zubda hawaye.Tabbas sunyi babban rashi.Daddy mutum ne Mai tausayi da son zumunci shiyasa a jana'izar sa yayi mutane musamman talakawa da ya tallafa wa a lokacin da yake raye.Kowa sai addu'a da fatan alkhairi suke yi mai da fadin kyawawan dabi'unshi..(Allah yasa mu cika dah imani.ameen)..


*****####*****

    Sai da aka daga bikin su Ja'afar da sati biyu...Basu so hakan ba amma ba yadda suka iya sannan ma yana son yayi amfani da dan lokacin da ya rage domin kawar da wata annoba da ta addabe shi..Asmee kuwa sai shige shige su ke yi,su je nan suje can har wurin wani malami suka je yayi mata sihirin mallakar mijin da zata aura da zarar ya kwanta da ita...Murna a wurin Asmee ba ya misaltuwa,at last zata mallake Ja'afar..
     Zahra kuma tun ranar da taga Bilkisu da Ramlan a garden ta wuce,bata Kara waiwayo ta ba kuma ko Bilkisu ta kira bata daukawa..Ita ta rasa dalilin da yasa take feeling wani iri,ko dai kishi neh??,a'a ina?,na rasa wanda nike so sai yaron nan,no it can't be!!.....
     Mahneerah kuma ta koma gidansu Mami da zama gabadaya saboda Momynta ta kulle gidan ta koma garinsu,bayan ta gama takaba itama zata dawo gidansu Mami da zama..Haka rayuwa ke ta tafiya masu har aka shiga makon da za a fara biki ..
     Ranar laraba suka je Ar-riyadh Saloon domin gyaran gashi da faratai...Gyaran gargajiya aka yi musu daga ita har Asmee sabody Mommyn su Asmee ta nace tare zasu to komai a tunanin ta kila Bilkisu zata je wurin boka cikin kwanakin da ya rage..Kitson karkashi aka yi musu,na Asmee yayi kyau sosai saboda tana da suma mai tsayi,na Bilkisu kuma average amma shima yayi kyau sosai saboda sumar ta baki ne wul...
    Bayan an gama musu kitso aka yi musu gyaran faratai da kuma lalle Mai dankaren kyau...Duk wanda ya gan su lokacin da suka fito daga saloon sai ya san Amare ne su..Bilkisu ne ta ja su zuwa store suka dan yi siyayya saboda Asmee tace sai dai tayi tuki,a tunanin ta ba za ta iya bah,bata san cewan Ja'afar yana ta koya mata manual ba,bare ma motar Asmee da ya kasance automatic..Sunyi siyayya sosai har ta siya wa Saleema wani ready made gown Mai kyau sannan suka ware gidan su Mami.Asmee ta koma mazaunin direba taja motar ta zuwa gida..*Ranar daurin aure*

Ranar juma'a bayan anyi sallah aka daura aure a babban masallacin garin Minna wato Central Mosque....Ango sai sheki ya ke yi da abokanan shi musamman Ashraf..Dariya sosai Ja'afar keyi tamkar ba shi za a daura wa aure da Asmee wacce ba ya so ba..
   Zahra ma tayi kyau sosai,Mommy ta tursasa ta cewan tare da yayan ta zata tsiya,in ba wawanci ba,ya zata je wurin kishiyar yayan ta bayan ga yayan ta.Ja'afar ya Kira Zahra yayi mata bayani game da abinda ya faru ran nan,shine ta kira Bilkisu ta bata hakuri..Su Asmee hoo,wai kishiya..Ni kam dariya nayi na kakkabe saratu na,sai anjima da dare zan dawo in za aje kai amare...๐Ÿ˜œ
    Da dare motoci suka jeru a cikin gidan su Mami.Umma ce ke tayi wa Bilkisu wa'azi kamar da gaske,Mami ma tayi nata sannan aka kai ta bangaren Abba,yayi mata nasiha ya sa mata albarka,abinda baban ta yace fafur shi bazai yi mata ba.Ya za ayi yasa wa wannan annobar albarka,ta karata can...
     Sai da jikin Abba da na 'yan rakiya yayi sanyi da suka ji maganar da Abba ya yaba wa diyarsa.Kowa nata Allah wadai da wannan halin.Bilkisu kam tayi kuka har ta gode wa Allah. Haka aka fita da ita zuwa wurin da aka faka motoci..Wani lafiyayyen ash color car aka saka ta ciki.Sameera da Mahneerah suna gefen ta,sannun su 'yan uwa da school mates dinta a sauran motocin..
    Can bangaren su Asmee ma Daddyn ta kadai yayi mata nasiha na kwarai,Mommyn ta da kawayen ta sai suburbuda mata hudubar shaidan suke tayi..Itama motoci neh jibge a gaban gidan su..Sallama tayi da 'yan uwanta da Daddy sannan ta shiga mota..Daddyn ta dai sai murmushi yake ta yi wanda daga ita, har su Mommy da Zahra basu san me ke tattare da murmushin nan bah..
    An kai amare lafiya kowa ya watse.Bilkisu dai tana dakinta ko ina shiru,babu hayaniya.Tana tunanin ko dai an kai Asmee wani gidan neh,amma da taji dadi saboda ita bata son tashin hankali..Asmee ma tana can tana tunanin inda Bilkisu take,in so samu ne ma ta hallaka ta amma taji wuri shiru...Sallama taji da wata bakon murya,shiru tayi bata amsa ba.Sai da ya kara maimaitawa sannan ta amsa..
     Karasawa ciki yayi ya ajiye ledoji."Sannu amarya",da sauri ta dago kai jin muryar wanda bata yi tsammani bah.."Ashraf!!,meh kake yi a nan,ina Ja'afar".."Calm down,nine angon ki!".."Never!,wallahi karya kake yi","Haba Asmee na,kin san yadda nike mutuwar son ki,ki tausaya min muyi zaman lafiya",yace tare da matsawa kusa da ita.Shiru tayi kamar maganar shi ya shige ta..Ya ajiye mata ledoji,yace taje tayi alwala suyi sallah sannan ya fita..
    Yana fita ta rufe kofa da key sannan ta zube a gado tana ta rizgar kuka,"wallahi sai sunyi nadama..dukkansu!!",ta karasa zancen tana bubbuga hannu akan gado.Ashraf ya dawo ya bubbuga kofa ta share shi,haka ya hakura yaje dakin shi ya kwana...
     Bilkisu tana zaune Ja'afar ya shigo bayan yayi sallama,amsa sallamar tayi ya shigo dakin.."amarya Kin sha kamshi",yace tare da yaye mayafin dake fuskar ta..Naseeha ya fara yi mata,kana tace masa ai ita da Asmee zai yi wa nasiha amma sai cewa yayi ai Ashraf ne angonta..kallon shi tayi da alamar tambaya, sai yace mata zaiyi mata bayani gobe.......


*Toh nima dai gobe zan koma domin dauko muku bayanin saboda na san kuma kuna son kusan yadda al'amarin ya juya........๐Ÿ˜œ*_Washegari_

Bilkisu na hango a kicin tana soya chips,duk kamshin chips da tea ya gauraye kicin..Tana kammalawa ta shiga dakin da ke gefen wanda suka kwana a ciki.Ita kunyar hada ido take yi da Hubbil khair saboda abinda ya wakana a tsakanin su daren jiya..
   "Hmm",ajiyan zuciya tayi yayin da ta rufo kofar dakin.Komai na dakin pink and maroon color ne,yayi kyau sosai.Tana bude durowa taga kayan mata neh a ciki,lokacin ta Lura da akwatunan ta dake sama.A nan ta gane cewan wannan dakin ta neh...
   Murmusawa ta kuma yi ta shiga bude wani akwatin ta da kayan ta na gida ke ciki domin cire tawul,sai da ta cire har zata rufe box din,sai ta zuge zip din da wuri ta bude wani karamin zip ta ciro wani paper rose flower..Sai da na ware idanu na da kyau,shine na gano cewan flowern da tayi masa ne lokacin da take school,koh me yasa bata bashi ba?,zamu ji dalilin nan gaba...
     Wanka tayi sannan ta fito ta shafa mai. Duk abin nan da take yi,Ja'afar yana dakin sa yana bacci.Tunda suka idar da sallah suka koma bacci,da wayo Bilkisu ta kwace jikin ta daga nashi lokacin da ta farga...
    Pink lace ta ciro daga kayan da ke wardrobe ta sa, sannan tayi make up daman ta zama gwana a make up tunda suka kulla kawance da Zahra da Sameera..Tayi kyau sosai da pink lipstick da ta sa a baki..Turarukan da ke kan mirror ta feshe ko wani lungu da sako na jikin ta yadda Mami tayi mata bayani..Sannan ta dauki sweet na freshening baki ta fara tsotsa,yana sa baki kamshi kuma bashi da side effect..
    Fitowa falo tayi sannan ta zauna a kushin ta na kare wa falon kallo da kyau...fentin falon shima yayi matching da komai na falon.. Karan footsteps taji alamar mutum yana dosar inda ta ke,da sauri ta saukar da kai kasa.......
     ******""""******

Abba da Mami ne zaune suna hira.."oh Allah sarki ina jin kewar 'ya ta",cewar Mami yayin da tayi murmushi..
   "Ji min wifey fah,kika kaini jin kewar ta?,she is my daughter too y'know"
   "Yawwa Habeebee ina son muyi wata magana if you don't mind please.."
   "Go on,ina jin ki"
  "Dama akan zancen Ja'afar neh nag......"
"Shhh,na san mai kike son kice,wallahi ni ban rike Ja'afar a raina ba kuma ni ban yadda cewa zai aikata wannan aikin bah ko saboda irin son da yake ta nuna mata fun tana karama,sai da aski ya kai gaban goshi sai ya kasa hakuri?,no way!I just played along,na san mutanen musamman matan,they are up to something but who knows??"...
    "Kai..amma naji dadi Habeebee yadda ka fahimci abinda nike zargi nima,in ka Lura bata bari Saleema tayi magana ba although the poor girl was trying to say something",cewan Mami tare da gyara zama..
   "Eh toh,na nuna musu bacin raina ne so that karda idan ma da hannun su a fyaden da aka yi mata,su sa ayi mata worse than that.."
   "Toh Allah ya shirya, gashi dai mun samu Mahneerah kuma,yarinyar tana aiki sosai,very nice to be with,lallai Hajiya Rahma da marigayi sun bata tarbiyya mai kyau despite itace only child na su"
    "Allah ya jikan shi"
Suka amsa da "ameen"
"Ina fatan da daya daga cikin su zai so ta,kinga sai muyi tuwo na miya na"
   "Ai Alhaji kai tsohon zance kake yi,na lura ita da Sultee are attracted to each other amma dai mu jira su kara girma muga ko da gaske son junan su suke yi saboda karda muyi amfani da assumption mu aurar da su in ba so a tsakanin su,kaga zai zamo auren dole kenan"
   "Haka ne,we shall not go into conclusion,Allah ya tabbatar da alkhairi","ameen"..
   "Yawwa wifey,kinga business sai bunkasa yake yi har na bar wa baban Bilkisu business na kera kwanukan,yanzu shagunan kayan kicin da na bude da kuma nasu accessories da nike da sai kara cigaba yake yi,so,ina son na bude babban kamfanin kera jewelries and accessories na gwalagwalai don na samu wani agent a India wanda muka shirya zai dinga aiko min da materials da muke bukata sannan na biya shi.."
    "Amma gaskiya wannan tunanin naka yayi,Allah ya taimaka"
    "Ameen,kin ga ba sai mun ringa siyar gwalagwali daga wasu guraren bah,sannan Ja'afar zan sa as manajan wurin,banda wannan kuma na yi musu visa na honey moon da na yi musu planning a London"
    ""Kai Abban Ja'afar don't know how to thank you,kana kokari wurin faranta mana, Allah ya bamu ikon faranta wa juna rai..Ameen",cewar Mami...
   "Ameen my dear".........


            *****************

"Ni yaya zata yi wa wannan rashin mutuncin,no wonder bamu ga Ja'afar a bangaren mu ba ranar bikin,so ta zabi bare a kan jinin ta,stop crying my baby Asmee,trust me,zanyi komai saboda ku, just take care of yourself,karda ki bare yazo koda kusa dake or else kinsan sauran..Yawwa that's my baby..toodles",dukkan maganar ga akan waya Mommyn su Asmee ke yin sa,Daga ji da Asmee take magana..
    "Wo...Mommy meh ya same teddyn ki",cewar Zahra da ke zaune a sofa tana chatting da Sameera..Nan Mommy ta zayyana mata komai,dariya tayi sosai although she was surprised yadda komai ya kasance..
    "Ke kina hauka neh??,da ma ban gaya miki bah"
   "Awwn! serves her right!"
   "Meh kika ce??!",Mommy ta tambaye ta fuska a murtuke..
   "Ban ce komai ba",sannan ta mike ta wuce daki abin ta yayin da take ba wa Sameera labarin da Mommy ta bata..Sunyi wa Bilkisu murna sosai,Allah ya raba ta da musiba...
    Mommy kuwa car keys dinta ta dauka,sai gidan su Mami ko mayafi bata yafa ba bare hijab..........

               **********

"Hello,guy how far, wallahi ba lafiya fah,bro na ya fara suspecting dina batun aikin nan da na sa boiz din mu,kai dai bari,so abinda nike so da kai yanzun nan shine ka tara su kayi warning nasu da kyau cewan karda su bari yar karamar yarinyar nan ta hadu da su ko a ina neh,eh ka san yara basa mantuwan abu da wuri,yawwa zan turo ma sauran balance din su yanzu before I think of the next step, har Mari na banzan nan yayi kafin bikin su fah saboda bitch din nan,don't worry sai min hadu",duka zancen nan a waya Ramlan ke yin sa..Tun ranar da Ja'afar ya mareshi ransa a jagule yake, har lokacin bikin ana ta tambayan sa ko lafiya?saboda babu ko digon fara'a a fuskar sa ko da na pretence ne..Mikewa yayi ya dauki key din motar da Ja'afar yake tukawa da saboda Abba ya siya wa Ja'afar wani as wedding gift,shiga motar yayi ya sa mata key da dabsi kamar motan zai yi tsalle don irin sautin da ke tashi a cikin sa,sannan ya fita a guje har tayar motan tana wani kara"kiiiiiiiiiiii".................*********

"Amarya kin sha kamshi",cewan Ja'afar tare da rungumo ta ta baya yana shinshina wuyan ta da su kunnuwa..
    Shiru tayi tana jin wani irin tickling sensation yana bin jijiyoyin jikin ta..Zagayowa yayi ya zauna a gefen ta tare da sa hannu a haban ta ya dago fuskar ta,da sauri ta lumshe idanu tana wani shagwaba fuskan ta..hakan ba karamin birgesa yayi ba..
   "Masha Allah my kissy kinyi kyau fah amma kunyar ga da kike yi ya bata show",ya karasa maganar tare da lakutar hancin ta...
   "Ina kwana yaya",tace a kunyace..
  "Lafiya lau my kissy,ya daren jiya?"
  Mikewa tayi zata gudu ya jawo ta ta fado kan kirjin sa,rufe ido tayi,da yaga da gaske take yi sai ya kyale ta..
   Tashiwa tayi ta dosa hanyar kicin,"kissy na zo ki taya ni wanka mana",da gudu ta shige kicin ta rufe.. Murmushi yayi kawai ya shige dakin sa..Har ga Allah yana jin son ta a kowani sassa na jikin sa..Wanka yayi sannan ya fito ya shafa mai yasa farin T-shirt da pink wando saboda yaga kalar kayan da Bilkisu ta sa kenan..Feshe sumar sa yayi da turaren kai mai kamshin gaske sannan ya feshe ilahirin jikin sa da turare kana ya fito,a dinning area ya same ta...
   Mikewa tayi ta jawo masa kujera ya zauna sannan ta fara serving din sa still kan ta a duke,shi dai Allah Allah yake yi ta gama,ya fara ci,gani yake Lamar first time dinta na dafa Mai abinci ke ga..Bayan ta zuba musu ta zauna a gefen sa,a natse suka karya sannan ta kwashe kofunan da plate taje ta dauraye sannan ta fito daga kicin..Tsayawa cak tayi ta rasa ko taje daki ne,ko ta tsaya a falo neh,toh in ma zata tsaya ina zata zau...?,kafin ta karasa zancen zucin ta kawai ji tayi an dauke ta cak sai kushin,yana zaune ita kuma ya kwantar da ita a jikinsa..
  Labarin yadda komai ya gudana ya fara sambado mata.lokacin ta daga kai tana  kallon sa..
    _Bayan an daga bikin su,Ja'afar ya fara neman hanyar da za ya bi ya rabu da batun aurenshi da Asmee.Ashraf ya tuna cewan yana matukar son Asmee.Gidan su Ashraf ya nufa ya gaya masa abinda ya kawo sa,he was so happy har kuka yayi don murna.Ja'afar yace masa su shirya suje gidansu Asmee shi zai yi wa Daddynsu Asmee bayani..Da sauri2 ya shirya suka wuce gidan su Asmee.Sunyi sa'a Daddy yana nan.Kai tsaye Ja'afar yayi wa Daddy bayani,a take Daddy ya amince saboda ya yadda koma waye Ja'afar zai kawo saboda Ja'afar yaro neh Mai hankali so,ya san ba zai yi yawo da mutanen banza ba.Kuma Daddy ya amsa batun auren Ja'afar da Asmee, shi baya son ya takura ma dan wani..Nan take Daddy ya Kira Abba yace zasu zo yanzun nan da su Ja'afar.. Suna isa aka sasanta komai,Mami ma taji dadin zancen sosai amma dai ta dake kuma Daddy yace karda su kuskura su bari Mommy ko Asmee su ji..Abba ma ya biya wa Ashraf sadaki sannan Mami ta bi shi gida suka zanta da mahaifiyar sa saboda baban shi ba ya da rai.Maman shi taji dadi sosai saboda itama ta kosa yayi aure saboda tana tsoron karda ya fada sharrin shaidan..A satin nan aka yi siyayyan su akwatuna sannan aka gyara mashi daya daga cikin gidajen gadon sa......Wannan kenan!_
    Ajiyan zuciya tayi bayan ya gama..."su kissy na hoo,sarkin kishi harda ajiyan zuciya"
     Dariya tayi tare da rufe fuskarta da tafukan hannayen ta..Hannu yasa ya janye hannayen ta kana ya soma sumbatar ta...hmm daga nan labari ya canza..............Karar waya ya dawo da su hayyacin su!.................

*~Muje zuwa dai๐Ÿ˜œ~*


_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[12/28/2016, 7:59 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                       *23*
"Assalamu alaikum,hmm Fateema kenan kin kyauta,daman haka zaki ce ai,I was expecting you a wurin biki na amma naji ki shiru,toh shikenan ya su mama da baba,toh ki gaishe su sai kin zo",cewar Bilkisu da ke waya da Fateema..
    Ajiye wayar tayi sannan ta gyara kwanciyar ta a kan jikin sa.Sunnah TV ya sa musu inda Sheikh KG yake yin wa'azi a kan ma'aurata.Inda ya ke cewa:
     _"mu musulmai min bar abubuwa da ya kamata mu yi a zamantakewar aure ma yahudawa.Zaka ga idan bayahude yana tare da matan shi,da sun dan motsa kadan yace I love you.Ko wurin aiki za shi.idan ya manta bai ce mata I love you bah,sai ya kira ta a waya ya gaya mata........."_
    Haka suka cigaba da sauraron wa'azin ya na yi yana ce mata I love you.Ita kuma sai murmushi take yi,itama tana mamakin irin son da Ja'afar yake mata,ace bai same ta da mutuncin ta ba amma ko mugun bai hada su ba tun jiya har yau.. A hakan bacci ya kwashe su,sun wani kankame juna kamar za a sace dayan su.....


                  ********

Knocking na hauka take yi.Mami na ji ta san cewa Mommy ce,daman ta san za a rina.Fitowa Mami tayi daga daki taje ta bude kofan,shigowa tayi ko sallama babu, duk a hargitse take..
   "Lafiyan ki zaki shigo mana gida a hargitse babu ko sallama?"
"Ina amfanin yin sallama a irin gidan nan,da munafikai neh a cikin sa!",ta karasa zancen tana karkada kugun ta..
   "Wato baki da kunya koh,ki zo har gida na kina zagin ni da iyalina?,meh muka yi maki?"
  "Oh meh kuka yi min ma kike tambaya na,da kuka yi duping din *NI DA 'YATA* ai dole ki tambaye ni meh kuka yi.Harda dan kwaron nan Ja'afar,shegen ya...."
   "Tasssss!",karan saukan mari na jiyo."jar uba!,saboda tsinannen yaron ki kika mare ni??"
  "Duk abinda zaki ce,ki ce amma karda ki kuskura ki shegen ta min yaro don a gidan uban shi na samu cikin shi na haife shi,'Yar ki dai yace baya so,don haka ba za ayi wa yaro na auren dole ba,so get out!"
    "Haba yaya ki ji kan 'ya ta,'yarki ce fah itama",tace tare da share kwallan da ya zubo mata a kan fuska saboda marin ya shige ta..
   "I said get out!!!!"
"Shikenan mu zuba mu gani tunda ba kya jin magiya,mtssssw,we shall see!",Mommy ta ce tare da banko kofar falo a fuskar Mommy.. 
    "Allah ya shirye ki wallahi",Mami tace sannan ta je upstairs inda Abba ke kiran ta yana faman cewa ita da waye ke magana..

                  #######

"Kai har kana zaton zaka samu wani kulawa neh a wurina,kazo kana wani kakkashe murya,don Allah ka rabu dani naji da raba ni da masoyi na da aka yi,mtsssw"
   "Haba yanzu ni fa mijin ki neh,ai ko saboda igiyan aure na da yake kan ki,ya kamata ki daraja ni,ki kwatanta min so da kauna ko da kadan neh daga cikin wanda nike yi miki, kin san.... "
    "Dan Allah jeka,ka ishe ni da surutu da sanyin safiyar nan,allow me to sleep"
 "Shikenan lokacin ki neh,amma ba zan zuba miki idanu kina min duk iskancin da kika ga dama bah,dare me!",ya karasa zancen tare da banging kofar dakin..
    "Mtchhhw,mutum kenan ba za a bari yaji da abinda yake damun shi ba kawai kazo ka tsaya min a kai ina breakfast,breakfast yana wajen uwar.......",haka ta cigaba da kundume kundumen ashar sannan ta ja comforter ta rufe jikin ta,ta cigaba da bacci....

                *********

"Alhaji!,Alhaji ka tashi muyi magana,yaya zaka yi min haka"
    "Haba Khadija, meh yasa kike yin abu kamar karamar yarinya wani sa'in"
  "Ai dole kace hakanan bayan da kai aka yi kulle kulle,aka ci mana fuska"
   "Kamar ya?,ni ban gane ba"
"Ohho,ka aurar da 'yar ka ga wani dan iska bayan ka san Ja'afar take so,sannan kana tambaya ta wai kamar ya"
   "Oh! ashe can kika dosa,nifa gani nayi cewan yaron nan Ashraf yana da halayya mai kyau,kuma yana son ta sosai don haka na san zai iya koya mata son sa,kuma"
   "Ka ga,ya isa haka nan,ya isa, tunda har baza ka iya ba wa 'Yar ka abin da take so ba,toh ni zan zamo gata a gare ta,I'll do what it takes to make her happy,daman kai ba son ta kake yi bah"
  "Meh zaku yi ne wai"
"Ba ruwan ka,wannan tsakanin *NI DA 'YA TA* neh"
   "Toh Allah shi kyauta",yace tare da mikewa ya shige bayi yayi brush.Sannan ya fito ya ga bata daki,dinning area ya nufa..
   "Good morning Daddy",Zahra ta gaishe shi tare da gyara mai kujera ya zauna.
  "Morning dear,kin tashi lafiya my baby?"
  "Lafiya lau Daddy,I prepared your best coffee da omelet"
"Allah shi yi miki albarka",lokacin ya Lura da Mommy dake faman zuwa da dawowa a tsakiyan falo, murmushi yayi ya girgiza kai..
    "Mommy ba za kici abinci ba?",Zahra ta tambaye ta tana dariya..
   "Abincin uwa ki na ce,zan ci kaniyan ki"..Dariya ita da Daddy suka yi,suka yi breakfast abin su,suka bar mata falon...
     

                    **********

"Gaskiya mallam ban ji dadin abinda kayi wa 'yar ka bah,ko tsanan ta ka yi bai kamata ka nuna hakan a gaban jama'a ba",cewan Abba..
   "Alhaji ba za ka gane bah,baza ka gane ba kawai"
  "Gaskiya nima Alhaji ban ji dadi bah da naji maganar a bakin mutane,bai kamata ba sam2",cewan Abban Fateema,kawar Bilkisu..
   "Atoh kaima ka taya ni fada,Allah ya shirya",ameen suka ce gaba dayan su sannan suka yi alwala suka wuce masallaci..

                          *******

"My kissy,kinji Abba wai yayi mana visa na zuwa London honeymoon",cewan Ja'afar da yake taya ta warming naman kaza a warmer..
   Murmushi tayi tace"Abba kenan,Allah ya bar mana su mu faranta musu rai yadda suke faranta mana"
   "Ameen my kissy,so zuwa next week Saturday zamu wuce,daga nan sai nayi ajiya na a nan",yace tare da shafa cikin ta.Murmushe tayi ta sunne kai a kirjin sa..Warin konewar nama ya dawo dasu duniyar da suka fada,da sauri suka karasa gaban warmer din Ja'afar ya sa hannu,da sauri ya cire yana tsalle kamar karamin yaro,handkerchief ta dauka ta jawo plate din sannan tazo ta fara hura masa hannu,daga nan suka Lula duniyar masoya...hihi๐Ÿค“...


*Toh fans din kissy da Ja'afar, sai mun hadu a airport,kowa taje ta samo visa muje kwaso rahoto...hihi๐Ÿค“*


_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[12/31/2016, 9:11 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                      *24*
_*Dubai*_

Jirgin su ya sauka a Dubai karfe 02:00pm.."toh kissy na, alhamdulillah mun iso".Murmushi tayi ta kara matse hannun sa a cikin nata.Suna karasa saukowa wani balarabe yazo ya karbi kayan su tare da fadin, "welcome to Dubai"...
     "Thank you",suka amsa a tare,sannan yayi directing din su zuwa inda motar da aka yi musu charter yake.....
     A Armani hotel ya ajiye su..Suna isa reception ya gaya masu suna da reservation a wurin..Sai da aka yi musu 'yan tambayoyi sannan aka basu dukka info. Da suke bukata,saboda har inda zasu je yawon shakatawa da siyayya yana kan booklet da aka basu..Dukka wannan aikin Abba neh.
     Wani daki mai bala'in kyau aka kai su.Falon yana da dan fadi,sannan ga HD TV a bangon falon da sauran kayan kallo..Kushins din su ma 'yan medium sizes..
    Rufo kofar Ja'afar yayi sannan suka karasa cikin dakin.Ko ina kamshi yake yi.Ga wuta da ya haskaka ilahirin dakin.Closet dake gefen mirror,Bilkisu ta ajiye akwatunan su a ciki kafin tazo ta jera kayan anjima..
    "Kissy na,ya kika ga dakin,yayi miki ko mu canja??",cewar Ja'afar.Duka na wasa ta kai mai sannan tace,"haba dai, ai ni zabin Abba shine zabi na"
   "Iyye masu Abba,toh ni mijin ki kuma ogan ki nace dakin bai yi min bah,so kizo muje wani room". 
   Marairaice fuska tayi kamar wacce zata yi kuka."Haba yaya,don Allah kayi hakuri mu zauna a nan,zabin ka ai nawa ne nima but please nan din ma yayi please,kaji?"
  "Toh zan yarda only on one condition",yace tare da riko hannun ta ya jawo ta kusa da shi."ok tell me the condition"..
     "Zaki daina Kira na yaya,call me with sweet names yadda nima nike kiran ki da Kissy"..Dariya tayi tace,"kai yaya har mene ne a sunan da baka so na Kira ka,"..
   "Toh shikenan kinga wucewa ta",yace tare da Kama hanyar fita daga dakin.Bata san lokacin da tace "YOU ALONE",bah.Cak ya tsaya ya kara jin ta maimaita abin da tace..
   A hankali ta tako har gabanshi kana tace,"haba you alone,wasa nake yi ma fah"
    "Gaskiya I love this name kuma in shaa Allah kema you alone ce a gare ni in shaa Allah",yace tare da manna mata kiss a goshi..Da sauri ta janye kan ta saboda ta san halin shi,daga nan zarcewa zai yi..
    Dariya yayi sannan ya bi ta zuwa bakin gado da ta zauna suka cigaba da hiran love dinsu kowannen su,zuciyar su cike da kaunar juna.


         ๐ŸŒฐ๐ŸŒฐ๐ŸŒฐ๐ŸŒฐ๐ŸŒฐ๐ŸŒฐ

    A yau neh Umma ta nema ganawa da Ramlan.Bayan sun cimma burin su ta farko na sawa ayi wa Bilkisu fyade.
    "Ke ya aka yi neh?",cewar Ramlan. Ni kam nace oh su Umma girma ya zube,har yaron da kika isa ki haifa sau biyu ko uku ya tsaya yana kiran ki da ke.Allah wadai!!.
    "Yawwa na Kira ka ne saboda naga yadda muka so abin nan ya kasance,ba haka ya zamanto bah"
   "Toh sai yaya?"
"Eh nazo mana da wata sabuwar hanya neh wanda na san baza su iya tsallake shi bah"
    "Ina jin ki"
"Yawwa naji ance sun tafi Dubai koh ko ina ne ma?"
  "Ni ina ruwa na da inda suka tafi,ke in zaki yi maganar straight forward kiyi,bana son dogon zance!"
   "Toh daman cewa nayi ko zaku samu wata ko wani a can da za ya/ta shiga tsakanin su yadda kwata2 baza su jitu ba a zaman da zasu yi a can?"
   "Eh toh,kin kawo harka mai kyau.Amma sai dai wani hanzari ba gudu bah.Ba zai yi sauri da yawa bah?ai kamata yayi mu bar su su dan shana",cewar Ramlan tare da yin wani shu'umin murmushi..
    "Ai bai yi sauri bah tunda baka riga ka samo wanda za a bai wa aikin bah"
"Eh toh,in dai wannan neh babu matsala,akwai wata babe dina da ke can. Ita zan ba wa aikin tayi mana,amma ita Bilkisu'n ya za ayi da ita?"
    "Kai ka barni da ita kawai..Naka dai ka sa su rasa sukuni a duk inda su ke!"....
   "toh shikenan an gama",cewar Ramlan yayin da yake makala no respect din sa a idanu.
   "Yawwa zamu yi maganar kudin idan aikin yayi kyau"
  "Toh Allah ya sa,ko kuma nayi sanadin mutuwar ki".."hmm"kawai tace sannan ta juya ta fita daga uncompleted building din ta wuce.Bayan ta wuce da minti biyar shi ma ya fito ya shige motar sa,ya wuce.....


         ๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป

_*Shu'uma*_

Itace babbar yarinya da ke tashe a Dubai.Ta kasance tantiriya tun a secondary sch..Ta hadu da su Ramlan neh a wajen rubuta exam.Tun lokacin suka zama friends saboda halin su ya zo daya. 
    Ta rasa mahaifiyar ta tun tana karama,don haka bata samun kyakkyawan tarbiyya bah kasancewar mahaifin ta dan siyasa neh.Baya zama a gida,kuma ko meh take so yana yi mata.A yanzu ma ta kai shekara biyu kenan da zuwa Dubai saboda wai ita kasar najeriya ta ishe ta..Wasu 'yan iskan mata ta hadu da su a nan,duk ta Kara tabarbarewa.Duk club din da kaje,kana cewa S.H an san ta..Sunan ta Sumayya Hashim wacce zan dinga kira da Shu'uma har karshen novel din nan...Wannan kenan!!
    "Hello,watsup,yeah na gane ai,Real guy koh,okay ya 2days?.Toh that's good,OK ina jin ka..uhhum wannan ai karamin aiki ne a wuri na,I can do it free for you so,karda ka damu da zancen payment,yeah never mind.Ka turo min pic din su da every details about them so that inyi studying na su da kyau kafin na fara,aha take care..!",dukka zancen nan kan waya Shu'uma ke yin sa,daga ji da Ramlan ta gama magana..
   "Hey babes mun samu wani work fah"
"Ok muna jin ki,mun san duk wanda zai baki aiki toh bana wasa ba neh",cewar kawayen ta,Jumy da Shola.
  "Yawwa ina jira a turo pic dinsu tukun,wai couples neh ake son na raba su",ta ce tare da yin katkat da chewing gum din ta.Karar wayar ta taji,alamar notification neh ya shigo a messenger din ta...
    Sai da ta karanta dukka details din a bayyane domin kawayen ta su ji,sannan ta mika musu wayar,su ga hoton."wow",suka fadi lokaci daya..
   "Cute couples,amma meh ya sa yake so a raba su??!",cewar Jumy.
   "Ke forget kawai,all I know is that,guy din nan nawa neh,no one dares to come close to him.Ku barni dashi kawai,kuje Ku samo min details din su,Suna Armani hotel,room 15.."
   "Ok,let's go",suka ce tare da mikewa suka shige arniyar motar su...sai Armani hotel.

   
   *ARMANI HOTEL*

  Su Shu'uma na isa hotel din daidai lokacin Ja'afar da Bilkisu suke fitowa.Sunyi shirin larabawa,shi yasa jallabiya itama sanye take da jallabiya sai dan karamin hijab da ya rufe mata kirji..Sun yi matukar kyau.
   Nan take Shu'uma taji wani irin kishi,ita ina koma yaya neh,dole ta mallaki fine boy din nan.Su Ja'afar kuwa hankalin su kwance suka shige mota ba tare da sun lura da su Shu'uma dake kallon su bah tunda kowa harkar gaban sa yake yi.
      Wani madaidaicin pick up van suka shiga ya kai su *DUBAI SAFARI*. A nan ne inda city da concrete na Dubai yazo karshe,daga nan sai desert din dake wurin..
   Suna isa,wani mai land rover yazo ya dauke su bayan ya bukaci ko sune Mr and Mrs Ja'afar suka ce mai eh..Nima da sauri 2 na sauko daga pick up da ya kawo ni har ina cin tuntube,ina isa na shige wani land rover nima,ina ciki na hango su Shu'uma suma a cikin nasu landrover'n sai wani shan kamshi suke yi irin bad girls din nan.
   Gaskiya wani wurin idan kaje sai ka tambaye kan ka cewan Anya duniya kake?.. Wurin yayi ne kawai.Muna kaiwa can karshe sai ga wani oasis setup inda na hango barbarque yana wani irin welcoming dina, duk yawu na ya gama tsinke wa...hahha
    Wasu belly dancers na hango wai suna rawa abin su da yake d yamma suke fara rawa sai dare ake gamawa.Inda Bilkisu da Ja'afar suka zauna,nan nima naje na zauna domin kwasan rahoto..
    Mutane na sai zuba love suke tayi ni kuwa ina murmushi a gefen su ina con barbaque dina. Ina hada ido da Shu'uma ta watsa min harara,tuni na kama kai na,na daina yin murmushi.Haka nike ta zaman banza a wurin yayin da masoyan suna love,Shu'uma kuma sun hana ni sakewa..
    Sai can da daddare direbobin land rover'n suka mayar da mu inda muka sauka a farko.Pick up kuma ya kwashe mu zuwa Armani hotel kuma.Dukka abinda dai suke yi,Shu'uma da kawayen ta suna biye da su,har booking daki suka yi a hotel din.Dakin su Ja'afar na nufa abina ina sanda don karda su jiyo shigowa na...
     "Washhh! Gaskiya na gaji you alone",tace tare da cire hijabin ta sannan ta ciro towel.
  "Wallahi nima I'm so tired kissy na,muyi wanka sai muyi sallah mu kwanta koh??"
  "Eh wallahi",tace yayin da ta daura towel sannan ta cire jallabiyar jikin ta da su undis ta zuba a closet.
   "Toh bismillah nima a cire min"
"Kai yay..wai you alone,ka cire da kan ka mana"
   "Ni kam in ba ke zaki cire min bah toh na fasa yin wankan",yace tare da langabe kai irin na shagwaban nan.
   Ba magiyan da bata yi mai ba,yace sam sai dai ta cire mai,harda cewa tare zasu yin wankan.Haka dai ta hakura,suka yi wankan tana wani noke2 sannan suka dauro alwala..Dauko ta yayi tamkar wata jaririya,ya shirya ta sannan itama ta shirya shi bisa ga umarnin shi..
   Suna kammalawa ya tada iqama da yake daman akwai dadduma a wurin da kuma alamar inda zasu yi facing wato alqibla..
   Suna idarwa suka yi addu'a sannan ya dauki waya yayi order'n coffee.Cikin mintuna kalilan aka kawo,shi ya tashi ya karba sannan ya rufe kofan da doorlock..Bayan sun sha kowa yaje ya kurkure  bakin sa sannan suka yi kwanciyar su.Ni kam tun ina jin hirar su har bacci barawo ya sace ni...... *Asuba ta gari Loverbirds*....*Toh Ku biyo ni domin jin ta inda Shu'uma zata bullo musu*๐Ÿ‘น_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[1/1, 7:38 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                       *25*
_*Bayan Kwana uku*_

A lokacin su Shu'uma duk sun gama observing Ja'afar da Bilkisu sosai,saboda haka suka fara shirin afka masu..
     Sun hadu da su a rana ta biyu a Burj khalifa har suka gaisa da Bilkisu saboda shigar mutunci suka yi don haka ita bata kawo komai a ran ta bah.Har nombar ta suka karba kafin Ja'afar ya same ta a wurin mota.
   A rana na uku ne suka shirya afka masu..Ja'afar da Bilkisu sun shirya cikin English wears sannan Bilkisu ta sa abaya a saman kayan ta da yake rigar jikin ta bai kai cinya da kyau ba kuma wando ta sa saboda yau Dubai ski za su..
    Suna isa wurin,suka sanya woolen coats da thermal caps din su wanda zai yi keeping din su warm a wurin.Da farko Bilkisu ta ji tsoro ganin irin wurin da zasu yi skiing kai,amma da Ja'afar ya rike ta ya fara moving sai tsoron ya dan ragu..
   "Kissy na ki rike ni da kyau fah!",yace da karfi.
 "Toh ai wannan ya zama dole you alone"
   "Wow! Yeah! Wow! Wayyo Allah na!",shine abinda suke ta fadi suna faman zuwa da dawowa.Gwanin sha'awa abin su.
   Duk abinda suke yi,hankalin su Shu'uma ya na kan su amma su basu ma san da mutane a wurin ba.Anjima kadan Bilkisu ta saba sai ta fara yi da kan ta,sai ihu take yi na jin dadi.
    Bayan kamar awa daya, Ja'afar yace mata yana zuwa ya samo abin motsa biki tunda ita ta ki ta raka shi.Yana juya baya,su Shu'uma suka karaso,abin nema ya samu.
   "Hey friend!",cewar Shu'uma yayin da ta karaso ta inda Bilkisu ta ke.
  "Hey ya kike",Bilkisu tace ba tare da ta kawo komai a rai bah.
 "Lafiya kalau,na ga kina jin dadi abin ki,I'm I welcome to join you?"
  "Sure!",cewar Bilkisu tare da murmusawa.
"Mother fucker!",Shu'uma tayi murmuring a hankali.
   "Let's go!!!",cewar Bilkisu da take kara jin son skiing ke shigan ta.
   Sun yi round daya, biyu lafiya.A na uku neh Shu'uma ta fara buge ta.A round na hudu su Jumy da Shola suka yi joining.
   A farko ta dauki abin as mistake.Da ta Kara na biyu,na uku sai Bilkisu tace,"ouch! that hurts.!"
   "Oh yi hakuri dear!",bata karasa zancen ba ta Kara buge ta.Bilkisu na dagowa ta sake mata wani irin murmushi.Haba wa ba sai suka fara rough skiing da ita bah.Wannan ta bige ta,wannan ta hankade ta.
   "Its okay please!,zan je na jira miji na a can",tace tare da yin nuni da wani resting place tana haki..
  "No ai yanzu muka fara,the game has just began!",cewar Jumy.Bilkisu tana dagowa ta ga irin kallon da suke mata ta juya da sauri zata wuce su ka jawo ta baya...
    Suna jan ta,tana ihu amma mutane basu lura da hakan ba,gani suke duk cikin jin dadi neh..Cikin 'yan mintuna suka dagula mata lissafi sai ji kake fummm ta fadi a kasa.
   Kinkimar ta suka yi kamar zasu ba ta taimako,suna wucewa Ja'afar ya dawo.Zubar da ledar hannun sa yayi da yaga ko inuwar kissy'n sa bai gani bah.
   Gashi kowa yana harkan gaban sa ne bare ya tambaye su amma dai ya maze ya na ta tambaya.Duk wanda ya tambaya suce no basu gan ta ba.Har yayi loosing hope zai je ya zauna yayi figuring yadda zasu yi sai ya hango su Shu'uma.
   Da sauri ya karasa wurin su yana haki.Shu'uma na ganin shi ta san yes hakan ta zai cimma ruwa.Daman sun zauna a wurin neh domin ya hango su.Gyara zama tayi ta langabar da kai tana jiran sa. 
   ”Hey..hey please did you...did you help me see my wife a nan wurin",bai ma san da wani yare zai tambaye su."calm down,tare Ku ka zo nan",cewar Shu'uma.
   "Eh naje siyo abu ne na dawo ban gan ta bah.."
  "Oh sorry,toh ka zauna bari muje mu dubo ta"..Shine magana ta karshe da Ja'afar ya ji saboda tana gama fadi ya juya zai wuce sai ta dafa shi ya juya ta fesa mai wani abu a wurin shima ya zube.
   Ciccibar shi suka yi zuwa motar su,suka wuce.Ni kam nace Allah kadai ya san mai zasu aikata wa bayin Allah nan...
    *************

_*A Gida Najeriya*_

"Wai ke ba kya da aikin yi neh kullum sai kallace kallace da chatting?iyye"
  "Mtsssw kan ka ake ji"
"Ni kike yi wa tsaki don kinga ina barin ki?"
  "Toh meh zaka yi?in ka gaji ka sake ni mana, na ce bana son ka,dole neh?"
  "Toh wallahi yau sai na karbi hakki na,Ba zan yi azumi don kare kaina daga zina ba bayan gani da mata a gida!"
  "Lallai ma,in your dreams"
  "Wallahi yau ba zan hakura ba sai na biya bukata ta"
  "Wallahi baka isa bah,mutum daya na tanada wa budurci na kuma..."
   Tasssss# ya wanke ta da lafiyayyen mari. Kinkimar ta yayi,tana ihu tana bugun shi amma ina bai ma san tana yi bah.Abinda yafi bashi haushi shine yadda take sa tsirarrun kaya tana zama dashi.
    Kiciniyar tube mata kaya yake yi.Da kyar ya samu ya cire kayar..Ita kuwa sai ashar take ta kundumawa harda kiran shi dan iska,zai yi iskanci da ita. Shi kuma yace tunda da matar shi zai yi,toh wannan bai shafe shi ba..
    Kai a takaice fyade yayi mata.Ya sha yakushe2 da cizo amma sai da ya cimma burin sa.Ita kuwa ta sha azaba saboda sai da ta jigatu sosai ya bar ta.
   Yana gamawa yaji duk yanayin shi ya canza,duk yaji kanshi wani iri.Wani irin tausayin ta da kaunar ta ya shige shi da ko da tace mai kashe kan ka,zai iya yi in dai har zai faranta mata rai.
   "Ka cuce ni,ka cuce ni,Allah ya isa, shege..mugu..wayyo Mommy na"
  "Haba amaryata kiyi hakuri na sa...."
   "Fice min daga daki!"
Sum sum ya tashi har ya Kai bakin kofa zai fita sai ta kuma cewa,
"Shege dawo nan ka gyara ni,wallahi ka shiga uku kenan".Da sauri ya juyo jikin sa na rawa yazo ya na kokarin taba ta,cikin zafin nama ta watsa mai Mari.
  "Wawa ruwa zaka hada min"
  "Toh nagode,bari na hada miki",yace tare da shigewa bayi.
   "Ai ka zama kuku na kenan tunda ka shiga hurumin da ba naka ba...wayyo Allah ya isa!!"...Haka dai take ta bala'i shi kuma tamkar yaron ta,sai jujjuya shi take yi.Ni kam nace oh Bilkisu da Ja'afar Allah ya raba Ku da dambe.Ashraf kuma Allah ya tsamo ka daga duniyar da ta tsunduma ka ciki..

              ########

"Alhaji naji yaran ga shiru,yau ba su Kira ba yadda suka saba"
  "Haha,suna nan suna jin dadin su,kin manta lokacin da muka je mu ma",dariya tayi kana ta ce,
  "Kai Alhaji har ka tuna min da baya.Ko zamu je ne kuma??"
   "Hahha watarana zamu in mun yaye yaran nan"..kyalkyalewa da dariya suka yi kana Mami ta mike ta shige kicin domin duba abincin da ta sa a wuta.Ita dai tana ji a jikin ta cewa akwai abinda yake faruwa.Addu'a tayi wa 'ya'yan ta gaba daya sannan ta cigaba da aiki...._Next page in shaa Allah_

*Cin karo yayi da ita daidai zai fita neman ta kuma wuraren karfe goma na dare.Wani Gardi ya rike ta tana tafiya tana tangadi,da gani ta bugu neh.*
  *"Ga matar ka,she made my day a romantic one",yace tare da murmusawa ya juya ya wuce..*
  *"Ya anka yi neh you alone..hihi....ghoooor",ta karasa zancen tare da gyatsa mai cike da warin giya..Fizgar ta yayi zuwa daki sai faman huci yake yi...An tabo jealousy din sa!*
_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[1/3, 8:51 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                      *26*

   Wani club su Shu'uma suka kai Bilkisu.Karamin daki da yake gefen bar din suka shigar da ita. Lokacin ta soma bude ido tana cewa,
   "Ruwa,Ruwa..."
  Da sauri Shu'uma ta karbo kwalbar giya guda daya ta zuba a 'yar karamar kofi ta kai mata shi a baki,ta kwankwade shi tas..
   "Meye wannan?",take tambayarsu yayin da take Kara shan wani giyar.
  "Sha yarinya zaki ji dadi",cewar Shola..Haka ta cigaba da sha har ta bugu.Wani gaye suka kira daga dance floor..
  "Shayo what's up now, wani dan aiki zaka yi min",cewar Shu'uma.Shayo shi ma dan Najeriya neh. Iyayen shi sun turo shi Dubai domin harkar business da su ke running a nan kasar Dubai..
   "Ok, ya aka yi"...Nan ta zayyana mai abinda take so yayi mata.Cewa tayi ya kula da Bilkisu, karda ya bari kowa ya zo kusa da ita har sai lokacin da za su dawo,warning ta bashi sosai cewar karda yayi mata komai,yace toh..
    Jan motar su suka yi sai Armani Hotels inda suka bukaci dakin da Ja'afar ya sauka.Ganin su da aka yi tare da shi,ya sa aka basu makullin dakin suka wuce ciki...
    Rufe kofar suka yi sannan Shola ta ciro camera'n su Ja'afar da ya fadi a kasa yayin da suke ciccibar sa.Tube masa kaya suka yi suka fara jajjagula shi,kowane style suka yi,sai Shola ta dau hoton amma fa basu yi lalata da shi bah.Haka kurum Shu'uma take jin tausayin su ganin irin halin da ta sanya su ciki.Dukka abinda suke yi,Ja'afar bai sani bah saboda ba ya hayyacin shi.
    Wuraren takwas na dare ya fara farfadowa,da gaggawa suka bar masa dakin da short note a gefen sa,
     *_"I will be back soon you alone"_*

   Yana farfadowa mike wa yayi da sauri yaji jiri na kwasan shi,sai ya koma ya kwanta.A hankali ya bude idanuwan sa domin ganin inda ya ke.Ya akayi yazo daki,shine abinda yake ta dawowa masa a kwakwalwa.
   Yana tunawa,zumbur ya mike amma ina maganin da ta fesa mai yayi bala'in saukar mai da kasala.Kwanciya ya kuma yi yana tunanin ina zai ga Kissy'n sa.Sai wajajen karfe 9 ya dan ji karfin jikin sa ya mike yana dafa bango yaje ya watsa  ruwa kana ya dauro alwala ya zo ya biya sallolin da bai yi ba dazu.
    Yana idarwa ya daga hannu yana rokon Allah ya bayyanar masa da ita. Wuraren karfe goma ya fito daga dakin.
     Cin karo yayi da ita. Wani gardi ya rike ta tana tafiya tana tangade,alamar a buge ta ke.
   "Ga matar ka,she made my day a romantic one",yace tare da murmusawa ya wuce abinsa(Shayo kenan,kuma karashen aikin sa kenan da su Shu'uma).
   "Ya anka yi neh you alone..hihi....ghoooor",ta karasa zancen tare da gyatsa cike da warin giya.
   Fizgar ta yayi zuwa daki sai faman huci yake yi.Yana isa daki ya cillata kan gado.
   "Meh nayi maaaah",ta tambaye shi tana lullumshe ido.
"Ina kika je??"
    "Ni..ni..ni ba tare muka fi..fita bah...ji.ji..tambaya fah..ghooor",ta kuma yin gyatsa.
   Mikewa yayi ya cakume ta a wuya.Tana son tayi magana amma ta kasa.
   "Yaushe kika fara shan giya,when?when? Bilkisu when?tell me!",Kara makure ta yayi.
    "Ke kika ajiye min note sin nan koh?kika fita da wannan gardin bayan ina ta Neman ki hankali a tashe"
  "Eh..a'a..ni..na..na...",don tsananin haushi da kishi bai san lokacin da ya kwada mata mari a fuska bah.Firgigit ta dawo hayyacin ta.
   "Wayyo yaya wani ya mare ni",tace cikin muryar kuka yayin da ta rike shi.
  "Ke matsa min a nan!",ya daka mata tsawa,bata san lokacin da ta cire hannun ta daga jikin sa ba,tsabar tsoron da ya kamata..duk idanun shi sun kada sunyi ja tsabar kishi..........Toh fah!!


*Ku biyo ni a next page don jin yadda karashen honeymoon zai kasance*

*Sorry for the short chapter..wallahi I'm too busy kwanan nan..hope baza Ku gaji da ni bah.....love you always, fans!๐Ÿ’‹*
_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[1/4, 8:47 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                      *27*
_*Najeriya*_

"Ka gama wanke wanken?"
  "Eh na gama",ya amsa da sauri yana goge tafuka hannayen sa.
  "Toh ni zan je gidan hajiya ta,karda ka kuskura na dawo naga ba abinci a dinning,kana ji na??"
   "Eh..toh..amma.."
"Amma meh"Asmee ta katse shi.
  "Don Allah so nake ki bar ni na je wajen Hajiya ta"
  "Uhmmm.toh,zaka iya zuwa amma bayan ka kammala aiki fah!"
  "Toh toh nagode",ya karasa zancen kamar wanda zai yi kuka don murna.
  Rabon shi da ganin mahaifiyarshi tun bayan biki da tazo ganin ko lafiya,saboda basu kawo mata gaisuwa ba as usual. Rashin mutuncin da Asmee ta yi mata ya sa bata kara stepping ko da gate din gidan ba.
    "Yawwa kuma karda ka kuskura ka ci abincin idan ka dafa.... Kuma karda ka ci a wajen hajiyar ka"..cewar Asmee a bakin kofa.
    Kada kai yayi alamar eh sannan ya mike ya karasa sauran ayyukan da zai yi sannan yaje kicin ya fara dafa abincin.
   Shi karan kanshi yana tausaya wa kan sa amma ya rasa mai ke damun sa.Kullum cikin addu'a yake Allah ya taimake shi.
   Asmee ta mayar da shi kukun ta,dan aiken ta,mai yi mata wanki da sauran su..Ga ta da yawon tsiya kamar wacce ta ci kafan kare.Amma shi a su wa?ba ya iya musa mata ko kadan bare ma yace karda ta fita sai dai ita ta hana shi fita.
   A takaice da zamar da shi mijin tace cikin mako daya da auren su...


                   *********

"You alone,meh ya faru?,why are you mad at me?",cewar Bilkisu tana hawaye.
  "Oh tambaya ta ma kike yi?ina kika jeh bayan da naje siyan abin motsa baki mana"
 "Kamar ya ina naje? I was standing there waiting for you!"
   "Please save me that bullshit!,ki yi min shiru!ok kina jirana kika ce,ya aka yi na dawo kafin ke?!"
 "Uhm..uhm..ni..ni"
"Ke..ke meh?!,na ce ke meh?!" 
    Shiru tayi hawaye sai ambaliya yake yi a fuskar ta..
  "That means abinda yace gaskiya ne..You were cheating on me!,bayan taimakon da nayi miki na aure ki,na danne zuciya ta bayan wasu sun riga ni... "
   "Please ka daina maganar nan please,ka san ban san kowa ba a nan,in fact no one knows me better than you,so plea...."
"Ya zaki ce na daina maganar, bayan kin san gaskiya nike fadi! Did I marry you as a vir...."
   "Stop it!! Na ce ka daina!",ta daka masa tsawa yayin da ta sa wani irin kuka mai tausayi.
   "How dare you shout at me?!",yace tare da wanke ta da mari kuma.(jama'a kun ga laifin sa?..duk cikin kishi neh,so ku yafe mai... #smile)
   Faduwa tayi saboda gravity na marin, daidai kan cameran da su Shola suka ajiye ta fadi tare da sakin kara mai cike da tsananin azaba.Wani kara ta ji daga inda take a kwance.
   A hankali ta dago ta dauka......


*********

Saleema ce tayi sallama ta shiga cikin gidan su.Dakin Umma ta nufa ta gaishe ta yayin da ta ajiye jakkan makaranta ta fito.
   Dakin baba taje ta gaishe shi sannan ta wuce dakin Umma'n Bilkisu saboda ta shaku da ita duk da bata motsi.Kullum tana ganin baba yana zuwa shiyasa ita ma take yin hakan..
   Da sallamar ta ta shiga,zama tayi kusa da Mama sai ta ga alamar hannun mama yana motsi.Da gudu taje dakin Umma..
   "Ke lafiya zaki shigo min daki da gudu??"
 "Umma,mama ce ta tashi..."
  "Ke matsa can da shirmen ki dallah"
  Fita tayi taje dakin baba,tana zuwa ta shige jikin sa tana ajiyar zuciya.
  "Ya aka yi Saleema ta?"
 "Baba,mama tana motsi"
  "Meh kika ce?",cewar baba yayin da ya mike tsaye.
  Kara maimaita abinda ta fadi tayi.Da sauri ya riko hannun ta suka shiga dakin...Zama yayi a gefen ta yace"mata ta Lami",sai ya ga ta juyo da kan ta a hankali,tana kokarin daga hannun ta......


*********

"Assalamu alaikum",cewar Ashraf yayin da ya shigo falon mahaifiyar sa.
  "Wa alaikumussalam. Ashraf kai ne a gidan ga yau?",ta fadi mamaki kaf a fuskar ta..
  "Ni ce mama,ina yini"..Kuka ta soma yi ganin yadda yaron ta ya canza cikin mako daya. Duk ya kode ya zama wani iri.
 "Meh ya same ka Ashraf,meh yake faruwa? Da na San haka rayuwar auren ka za ta kasance da ban takura maka da cewan kayi aure ba"
   "Umma ba laifin ki ba neh,kawai ki sani a addu'a.Nima na rasa mai ke damu na",yace tare da share hawayen da ya gangaro kan kuncin sa..
  "In shaa Allah zan cigaba da yi ma.Allah ya kare min kai,ya warware ko ma mene ne yarinyar nan tayi ma"
  "Ameen, nagode Umma"..Hira suke tayi na dan abinda ba za a rasa ba amma hankalin shi yana gida.Ya na tsoron Asmee ta dawo,baya gida.Sai kace ba ita ta ce ya je bah...
   Minti talatin yayi ya wuce gida.Umman shi dai addu'a take ta yi masa har ya wuce...

         *******

Daukawa tayi a hankali ta kai duban ta zuwa ga abinda ke playing.Wani rikitaccen kuka ta fara yi kuma.
    "Ke Mallama lafiya??",
  Mika masa tayi.Da karfi ya fizge daga hannun ta.Addu'oi ya fara jerawa yana salallami.Ga dai mata biyu a kan jikin sa amma shi bai ga fuskan su bah.
   Cillar da camerar yayi kan gado ya rike kan sa da ke sara mai.Wannan wani irin al'amari neh?.
   "Ni na yarda da kai,na san baza ka ci amana ta bah.Na san cewa wannan sharri neh aka yi maka amma meh yasa ka kasa yarda da ni?,nima ban san meh ya faru bah,ban san meh ya same ni ba.."
   "I'm so sorry,nima kishi neh yasa na kasa sauraren ki..I'm so sorry,ban san meh zan yi miki ki yafe min bah,na san...."
   "Shhh..ya isa haka.Ba komai ni na yafe maka. I understand you,kayi hakuri I never meant to shout at you",tace tare da zaunawa kusa da shi a kushin.
   Tsananin mamaki ya lullube sa da yaga bata yi hushi da shi ba.Kai amma I'm such a fool,shine abinda yake fadi a ran sa.Ya kasa trusting matar sa..
   "You alone mu koma gida gobe please saboda wanda ya hada abin nan,na san yana nan yana bibiyar mu har yanzu..please mu koma gida gobe",tace tare da kwanciya a jikin sa..
    "Shikenan zamu koma gobe in shaa Allah, amma kin gama siyayyar da zaki yi ko kuma zamu je mall mu karasa da safe?"
   "A'a mu dai mu wuce gobe da safen please"
  "Toh shikenan kissy na.I Love You so much!"
  "I Love You more!",peck tayi masa sannan ta mike ta cire kayan ta,ta shige bandaki domin watsa ruwa da kuma yin alwala don gabatar da sallolin da bata yi ba..A takaice cikin farin ciki suka kwana,har dan Dubai ma an samu Ina gani....hihi...
    Wato abinda Shu'uma ta fesa musu ya sa sun fita hayyacin su har suka manta da abubuwan da ya gudana bayan ya je siyan abincin...
     _Washegari suka shirya wuraren karfe goma suka kai airport.10:30am daidai jirgin su ya daga zuwa Najeriya....Ni dai fata na Allah ya sauke mu lafiya saboda a wurin injin jirgi na zauna๐Ÿ˜œ__*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[1/8, 8:01 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
   
_*A/N:Assalamu alaikum my sweet and lovely fans..na san nayi falling hands din ku cikin 'yan kwanakin nan,abubuwa suka yi min yawa shiyasa amma in shaa Allah zan kokarta na dinga turo 2pages kullum daga gobe domin na kammala novel din da wuri saboda nayi resuming sch so things will be difficult for me..Again,bayan wannan novel din,I'm afraid I'll have to drop writing novels aside saboda nayi concentrating a makaranta..Na san baza ku so nayi failing ba a makaranta koh?I know d answer is yes☺so,chill as you read this mind brightening chapter! Love you all๐Ÿ˜..*_

                   *28*
    Mun sauka a airport na Abuja,Najeriya lafiya.Direba yana jiran su Ja'afar already.Kayan su ya karba ya zuba a bayan motar.
   Sun iso Niger state wajajen karfe biyu na rana.Daidai gaban gidan su yayi parking.Ya kwashi kayan su zuwa falo yayin da Ja'afar da Bilkisu suka riko hannun juna suna tafiya ciki suna dan hirarrakin su...
   "Wow home,sweet home kissy...we are back!",yayi exclaiming yayin da ya zube a cikin kushin..Zubewa tayi a jikin sa itama tace "and no place like home....you alone I.....",murmushi tayi ta kasa karasa maganar..
    "Gaya min ko kuma.....",rufe masa baki tayi ta kyalkyale da dariya.A nan suka fara wasannin su har suka wuce daki domin watsa ruwa....

               *****

_Asibiti_
"Haba mallam,ya zaka yi wa diya ta haka,diya daya kankat da Allah ya bani a doron kasa kafin na fara wannan rashin lafiyar..uhm mallam?",cewar mama(mahaifiyar Bilkisu)..
   "Saboda ke nayi haka.Sanadiyyar yarinyar nan kika shiga halin nan shiyasa na kasa yafe mata tsawon shekarun nan..",baba ya karasa zancen yana share hawaye..
     "Haka Allah yaso mallam,amma ka daura laifi ka sa wa 'Yar ka da take bukatar ka,har tsawon shekaru goma sha takwas ka yi da yarinyar ga amma kace min ko kula ta baka yi..mallam baka kyauta min ba,ai wannan ba so bane"
    "Ki yi hakuri maman Bilkisu",cewar Mami da ke zaune a gefen ta..
    "Toh in ban yi hakuri bah Hajiya ya zan yi..Na gode wa Allah da ya ba wa 'ya ta suruka kamar ki..Nagode da halaccin da kuka yi wa 'ya ta Alhaji,Allah ya saka da alkhairi..."
    "Ameen ameen.. ki daina yi mana godiya Mallama,ai da na kowa neh,baka san ko na waye zai rike ka nan gaba ba..Mu dai muna godiya wa Allah da ya karbi addu'ar mu ya baki lafiya...Bilkisu za tayi murna sosai...",cewar Alhaji.
      "A'a ai dole na gode muku,Allah ya bar zumunci"...karar wayan Abba neh ya sa tayi shiru.
   "Laaa Ja'afar neh,wa alaikumussalam my son,kun dawo neh?..ayya welcome back..lafiya kalau..eh toh muna asibiti...but karda ka gaya mata,Ku dai zo kawai..yawwa sai kun zo.."
   "Ja'afar ne koh?"
"Eh shi ne,Mallama 'Yar ki ta na nan zuwa in shaa Allah",cewar Abba..
   "Toh nagode,nagode,nagode..uhm"
    

                  ****
"You alone bismillah koh?"
   "Meh yasa kike zumudi neh kissy na,ki bari muje gobe mana",yace tare da zaunar da ita a kafar shi...
    "A'a zuciya ta tana raya min cewa wani abin alkhairi zan tarar wajen Mami na,please ka tashi mu je, na dau tsaraban su ko..",tace tare da mikewa tana kokarin daga sa.
    "Hahha..ji min 'Yar babyn ga, ni din zaki daga?",dariya yayi sannan ya mike tare da manna mata peck a kumatu..Hannun ta ya rike suka jera zuwa motar shi,ya ja su sai asibiti.
    "A'a you alone,ina zamu kuma,wajen waye zamu je a asibiti"..
   "Koma waye neh zaki gani in mun isa"...
 "Please kar dai kace min wani bai da lafiya.."
   "Hey kissy calm down mana, ki aminta da ni,zaki ji dadin abin da zaki gani"..
"Toh shikenan you alone, I love you"..
   "I love you more and more sweetheart!"..Dariya tayi saboda yadda yayi stressing maganar..
    Bakin asibitin suka yi parking motar sannan suka je reception suka tambaya inda dakin patient Lami Idris ya ke.
  Nan take Bilkisu taji wani iri a jikin ta,wace ce wannan mai sunar Maman ta.Nomban dakin aka gaya musu, ya ja hannun ta suka wuce dakin.
    Da sallama suka shiga dakin,ganin Mami da Abba da Baba da tayi yasa gaban ta ya fadi.Allah dai yasa ba mamar ta ba ce a ka kawo asibiti..
    "A'a Ja'afar har kun gama honey moon din kenan?",Mami tace tare da mikawa Bilkisu hannun ta tana murmushi.
    "Uhm..ina yini Mami".tace tare da karasawa gefen Mami tana murmushi...Juyowan da zata yi..idon ta ya hadu da na mahaifiyar ta...
    "Maa.mam..maama?",cewar Bilkisu tare da karasowa kusa da ita kana ta taba ta domin tabbatar wa kan ta da cewar ba mafarki take yi bah...Sulalewa tayi ta fadi kasa sumammiya da mahaifiyar ta ta Kira ta da sunan ta....
     Da gudu Ja'afar da Mami suka karasa wurin ta amma kafin su ankara sai ji suka yi an bangaje kofar dakin da karfi...
    "Ina matacciyar???!!!"*Ku biyo ni a next two pages da zan yi updating gobe in shaa Allah don jin........ehhe kun gane ai*

                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar  
                      *29*

     Shu'uma ce ke tafe da kawayen ta a airport na Dubai.Bayan sun samu labarin cewa su Bilkisu sun dawo Najeriya,shine ta shirya domin dawowa itama saboda ji take tamkar baza ta iya rayuwa babu Ja'afar bah so zata yi nata deal din da Ramlan,tunda ta cika mai aikin sa,dolen sa shima ya taimake ta.. _its pay back time!_

*****

"Ina matacciyar",cewar Umma da ta shigo.Sam sam ba ta hayyacin ta.Ya za ayi ace matan da ta hada ta da bakin aljani tun haihuwar Bilkisu ace ta samu sauki?,
    "Ina? Ba zai yiwu bah!",tace tare da karasowa ciki.
  "Ke ba kya da hankali ne,za ki shigo wa mutane daki babu ko sallama sannan kina wasu maganganu da ban gane bah",cewar Baba..
    Mama dai bayi ta shiga ta dibo ruwa ta shiga yayyafa wa Bilkisu har sai d ta farfado.Maman Bilkisu ta kura wa 'yar ta ido tana meh jin tausayin ta.
   "Yaya ba zan shigo ba sallama ba,ace duk aikin da nayi ya bi ruwa,don Allah Ku matsa min na karasa ta",cewar Umma yayin da tayi wani kukan kura ta zo gab da gadon mama.
   "Ja'afar Kira mana police ya zo ya dauki azzalumar ga!",cewar Abba a fusace.. 
   Umma na jin anyi zancen station,tayi faking cewa ta haukace.Ta fara maganganu na fitar hankali yadda duk wanda ya gan ta sai ya zata haukan gaske take yi.
   Bilkisu kuma tana rungume da mahaifiyar ta,sun kasa cewa ma juna uffan..Kuka suke yi sosai,daga Mami,baba,kai har ma da Ja'afar.Abba ma ya maze neh kawai shiyasa bai yi bah.
  Umma tana ganin basu kulata bah,ta tashi tana soshe soshe ta fita daga dakin.."Sai na dawo a Karo na biyu",ta fadi tare da yin murmushin mugunta...
    "Mama na gode wa Allah da ya cire ki daga taskar azzalumai da shaidanu,ban san Mai zan yi na nuna godiya ta ga Allah bah,mama na Dade ina jiran wannan ranar,ban taba tunanin zaki tashi har ki fara magana bah,nayi rayuwar maraici duk da kina raye, bani da kowa sai Allah sai kuma baba,Abba,Mami da miji na da kawaye na,mama ban....",kasa karasa maganar tayi saboda kuka da yaci karfin ta.
   Kara rungume ta mama tayi tana kuka..Da sauri Abba ya share hawayen da ya digo masa a kunci.Tabbas Bilkisu da mahaifiyar ta ababen tausayi neh,ace an raba mutum da 'yar sa na tsawon shekara goma sha takwas,ita ba matacciya bah,ita ba motsi ba..oh duniya...ina zamu je??!!
    "Mallam ka ga abinda nike ta gaya maka, duk abubuwan da kake tayi wa Bilkisu bai dace bah,tun yarinya tana karama,baka taba fadin ko da Kalmar so daya a gare ta ba,ka dauki tsanan duniyar ga ka sawa yarinyar ka,ka manta cewar Allah yake kaddara komai yadda ya so,wacce kake ji da ita, matar ka,gashi ta watsa maka kasa a ido, gashi itace sanadiyyar salwantar da rayuwar Ku gabadaya...Hmm Allah dai ya kiyaye na gaba mallam",cewar Abba..
   "Nagode sosai Alhaji, ban san ta ya zan gode maka bah,na san nayi babban kuskure a rayuwa ta,na sawa yarinyar da bata san komai ba karar tsana har ta girma, ban damu da koh ta ci abinci bah ko kuma bata ci bah,ban damu da lafiyar ta bah,ban san ta ya zan fara Neman gafarar Ku bah...Lami ki yafe min,ban kula da 'yar mu ba a lokacin da take bukatar mu..Bilkisu ki yafe min..ki yafe min,na san ban kyauta miki bah...."
    Tasowa tayi ta rungume mahaifin ta tana kuka.."baba na yafe maka, Allah na gode maka da ka nuna min wannan ranar.na dade ina jiran ranar da ko da rike hannun ka zan yi sai gashi har rungume ka na yi yau..sai yau na san yadda ake ji idan mutum yana farin ciki,Allah karda ka sa wani ya kuma shiga tsakani na da mahaifa na..Baba na karda ka kuma bari na kuma..",ta karasa maganar tana kara rungume shi.Shi ma rungume ta yayi.Ja'afar dai ya rasa wani yanayi yake ciki,ta wani bangaren yana taya Bilkisu'n sa murna saboda yanzu zata samu kulawa da so na iyayen ta, ta daya bangaren kuma yana tausayin ita da iyayen ta,sai kuka suke yi...
    Bayan sun yi mai isar su,Mami ta yi breaking silence din..
   "Wai ina tsarabar mu neh mutan Dubai ko kuma za ayi mana rowa neh??"..Dariya suka yi gabadaya yayin da Bilkisu ta mike tana cewa,
   "Haba Mami mun isa?,mun bar shi a mota neh amma bari na dauko muku"..
  "A'a ki bari muje gida tukun mana",cewar Abba..
"Uhm uhm..ni a nan zan nuna wa kowa na sa.",dariya suka yi saboda yanayin yadda tayi maganar..
   Mikewa Ja'afar yayi ya bita a baya.Suna fita ya rike mata hannu yana murzawa."Kissy na na taya ki murna sosai,yanzu hankalin ki zai kwanta koh??"
   "Sosai ma you alone,thank you so much for everything,you are the reason behind my smile..I love you"
  "Love you more kissy,please karda a ajiye so na a gefe oo saboda Mama is back on her feet"
  "Ni a wa?na isa?, soyayyar ta daban,taka daban,trust me",ta karasa zancen tana bude murfin motar.Zama yayi a seat na direba kana ta jawo ta ciki...Kiss na tsawon minti biyu suka yi kana ya kyale ta.
   "Ni fa zan rama,irin wannan unexpected kiss din fah?",tace tana murguda baki..
    "I love your lips...hope nima an dawo min da tsaraba ta?",yace tare da shafa cikin ta.Dariya tayi da ta gano in da ya dosa ta kwashi bags din da tsaraba ke ciki ta fita daga motar.
   "In ka gama sai ka fito,ka ga tafiya ta"..Murmushi yayi ya rufo kofar sannan ya bi ta da sauri ya karbi jakkunan.
    "I'm at your service my kissy",yace tare da kashe mata ido daya.
   Jan kumatun shi tayi sannan suka cigaba da hirar su cikin nishadi har suka kai dakin da Mama su ke..
    Ta ba wa kowa tsarabar shi harda mama,saboda ta diba cikin na Mami ne ta bata.Sun ji dadi sosai,sai suburbuda musu albarka suke tayi..Can likita ya shigo yayi musu bayani game da progress din jikin Mama kana yace za a sallame ta Nan da kwana uku..
    Haka Ja'afar suka yini a asibitin sai da yamma Ja'afar ya wuce gida da su Mami,Abba da Baba domin su huta.Bilksu kuma za ta kwana da mahaifiyar ta neh...

*Bayan kwana uku*

Gida aka wuce da Mama, alhamdulillah jiki yayi karfi saboda drips da ta sha da magunguna.Maganin kara karfin jiki kawai ake ta bata da yake ciwon sihiri ke damun ta ba na asibiti bah...
      Soyayya mai karfi ya kullu tsakanin Bilkisu da mahaifan ta.Ririta ta suke yi a kowani lokaci tun tun da Mama ta Lura da cewar 'yar ta na da juna biyu.Sai kiba take yi tana kara haske.
    Watarana ta tashi da laulayi.Tace dole da faten tsaki za ta yi breakfast.Sai da Ja'afar ya kira Mami ta hada mata faten sannan hankalin ta ya kwanta.Da rana tace garaugarau na kasuwa zata ci...Abin ya bashi mamaki matuka,ya za ayi mutum na da abinci a gida amma tace garau garau zata ci?..Anya?..
   Yana siyowa ta hau ci,sai da ta cinye tas har da sude kwanu.Ba ta kai ko minti biyar ba da cin abincin ta fara kwarara amai.Duk ta bi ta rikice,yana gama gyara inda ta bata ya dauke ta sai asibiti..
   Sakamakon test da aka yi mata ya nuna tana da shigar ciki na sati daya. Murna a wurin Ja'afar da su Mami ba ya misaltuwa.Kullum laulayin sai karuwa yake yi.Su Mama da Mami ke dafa mata dukkan abinda take so..Ga su Zahra,Sameera da Mahneerah da ke zuwa mata yini.Dukkan aikin gida,su suke taya ta...
    Haka rayuwa ya cigaba wa su Bilkisu. Kullum suna walwala suna nishadi har cikin ya kai wata biyar..
      Ranar wata lahadi suna zaune da su Zahra suna hira sai ga text message yana shigowa wayar su a lokaci daya.I.v neh na auren Fateema da saurayin ta Yahya nan da wata daya.Kiran ta suka yi a waya suka taya ta murna kana su Zahra suka yi mata alkawarin zasu zo domin fara shiryeshiryen biki......
*NEXT PAGE*
*Inna lillahi wa Inna ilaihi raaji'un,ya mutu Abba!!*
 


_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[1/9, 9:35 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                      *30*

*A/N:Umma ta gudu da Saleema so,ba zan dinga ambaton ta ba for now..2,Maman mahneerah ta dawo,zan dinga kiran ta da Momma.....story continues.....*


*Bayan watanni uku*

Ashraf sai kara susucewa yake yi.Ya zama tamkar bashi bah.Kowa ya dauke kafa daga zuwa gidan musamman Ja'afar.
   Akwai ranan da Ja'afar yace,Asmee tayi seducing din shi,da kyar ya iya kwatan kan sa kana yayi warning din ta cewa karda ta kuskura ta kara yi Mai abu kwatankwacin haka...
    Abin ya matukar bata haushi,sai da ta Kira mahaifiyar ta,ta gaya mata.Gidan wani boka suka je domin fara sabon aiki....


******

"Mahneerah ina kike?",cewar Momma.
   "Ga ni Momma",tace tare da fitowa daga daki tana gyara daurin zanin ta..
  "Ki shirya zan aike ki gidan Hajiya Hassana Maman Farhan,zaki karbo min sako neh..."
   Dadi taji sosai jin an ambaci gidan su Farhan saboda tana matukar son Anty Ablah..At least za ta je su ga juna kuma..da sauri2 ta shirya ta fito..
    "Yar gidan Ablah kenan,toh in kin je kin karbi sakon, ki biya wajen Ablah ki gaishe min da ita..ki yi hankali da Shamsiyyar nan fah..",Momma ta ce tare da rike kunnen ta..
  "Haba Momma trust me...bana son abin da zai hada ni da ita mah,sai na dawo.."
"Toh a dawo lafiya baby nah"...
   Tana fita suka ci Karo da Sultee a bakin gate yana shigowa.Murmushi suka sakar wa juna.
   "Chuchu ina zaki haka?"
"Wallahi Momma ta aike ni,will you escort me please?"
   "Uhnmm.kiyi hakuri please,da kwai dan abinda zan yi,next time kin ji?"
"Toh shikenan sai na dawo"
   "A dawo lafiya chuchu na,take care please.."
    "OK dear!",kallon juna suka yi tamkar suna tunanin abu sannan kowannen su ya juya,kowa ya bi hanyar sa..
    Yana shiga ciki ya gaida Momma sannan ya leka dakin Mami ya ga tana bacci.Hawa stairs yayi,za shi dakin shi kawai ya jiyo murya daga dakin Ramlan.
   Mamaki ya ji sosai saboda shi dai ya san Ramlan ba ya gida so,wane ne ke magana a dakin sa.Yana sa hannu zai murda handle sai yaji wannan yana magana..
    "Toh karda ki damu,zamu kulla wata sabuwar deal,yanzu ina kike?,madalla,karda ki bari yarinyar ki ta kuskura ta gaya ma wani abu game da fyaden da muka sa aka yi wa Bilkisu,kin san yara sai a hankali..in har kika bari asirin mu ya tonu toh a bakin ran ki..."
   Yana kai wa nan Sultan ya bude kofar,ganin Ramlan yayi yana kokarin ajiye wayar.
   "Kai ya haka?ka wani shigo min daki"
"Haba yaya,daman kai kasa aka yi wa matar bro fyade?why?,meh tayi maka neh,what did she do to deserve this from you??!"
   "Kai babu ruwan ka a zancen nan..just keep your mouth mute and pretend as if you never heard anything!"
   "I can't! Wallahi sai na gaya wa Mami cewar da sa hannun ka aka bata sunan yaya!...watch me...",cewar Sultee yayin da ya fita daga dakin yana huci.
  Ramlan yana ganin ya fita ya bi shi a baya da sauri.Tura shi yayi da karfi,sai gib..gib..gib.gib kawai kake ji.Karan fadowar Sultee daga stairs,tun kafin ya kai last step din,numfashin shi ya dauke..
   Zubewa yayi a wurin kamar gawa.Ramlan na ganin haka,ya sauka da sauri ya taba shi ya girgiza shi amma shiru,no respond..
    Hankalin shi in yayi dubu ya tashi...Da gudu ya hau stairs ya dauki jakkan shi a daki ya bar gidan.
   Bayan da Sultee ya gaisa da Momma ta tashi ta shiga kicin.Fitowar ta kenan ta gan shi zube a wurin stairs.Sake plate din fruits dake hannun ta tayi tana salallami.
   Dakin Mami taje ta taso ta.Suna zuwa suka girgiza shi amma shiru still no respond.Da gudu Mami ta dauko hijabin ta da takalmi dabbare dabbare ta fito..ciccibar shi suka yi zuwa mota sai asibiti.
   ER aka shiga da shi kana Momma ta Kira su Abba da Ja'afar domin Mami ta gama rudewa.Ba a fi minti talatin da shigar da shi bah,su Abba suka iso, daidai likita yana fitowa daga ER...
    Sallama yayi da su Abba kana ya fara jawabi kamar haka..
   "Toh kamar yadda muka sani, Allah shi yake bayar wa kuma shi yake karbe abin sa..Kuma duk wanda yayi hakuri da duk abinda ya rasa,Allah zai musanya masa da mafi alkhairi.......",ajiyar zuciya yayi sannan ya cigaba da magana,
   "Hakuri zaku yi,mun yi iya kokarin mu amma mun kasa ceto ran sa,kuyi hakuri mun rasa shi...rai yayi halin sa...innalillahi wa Inna ilaihi raaji'un",juyawa yayi ya shige dayan ward din...
   Wani irin kuka Mai tsuma rai Mami ta fara yi lokacin da taga ana fitowa da gawar Sultee, Sultee dan albarka.Yaro Mai hankali,Mai girmama na gaba da shi,mai fara'a....tabbas dole Mami taji mutuwar autan ta...
   "Innalillahi wa Inna ilaihi raaji'un,ya mutu Abban sultan... D'a na ya mutu,Allah ya karbi abin sa..uhmm..a'a bai mutu bah,Ku bari na tashe shi..ai na san wasa yake yi mana..",tace tare da karasawa gaban gawar da ke lullube a kan gado..
   "My son wake up please,karda kayi wasa da mutuwa ka ji?",shiru babu amsa..
  "Bude idanuwan ka mana,ka tashi ka ce karya suke yi kana da ran ka...please wake up",still taji shiru...Kuka ta fara yi tana jijjiga shi a hankali tana sambatu..
   "Don Allah ka tashi,ina son in ka girma na hada ka da mahneerah ta,ka tashi ka ji d'a na.....ka tashi..",ta karasa maganar tana kuka..Rike ta nurses suka yi aka ja gawar zuwa mota...Abba dai hawaye yake tayi saboda yana jin son Sultee deep down his heart.....I couldn't stand the scene, juyawa nayi na samu wuri na labe domin nayi nawa kukan da addu'a ga Sultee...
     Suna isa gida,mahneerah tana shigowa.Kowa na ganin ta suka fara nonnoke wa.kowa ya san yadda take da Sultee.. Basu da courage da zasu gaya mata abinda ya faru..
    "Momma sannun Ku da gida,ya na gan ku haka?"
  "In...in..Ki zo mu shiga ciki kin ji??"...
   Bin mahaifiyar ta tayi,tana waigowa.Can ta kasa zama ta fito wajen motar..Tana zuwa daidai Mami tana fitowa daga motar tana hawaye..Lekawa tayi ta gan mutum a lullube cikin motar..
   Da sauri ta kalli Mami,Abba da Ja'afar sannan ta bude lullubin..Ihu tayi ta koma da baya,sai ganin ta nayi a kasa tana juye2 kamar tababbiya...Su Abba na rike ta,ta cillar dasu har sai da Abba ya bugu da motar..Ashe iskokai ne gare ta...
    Sai da ta tada hankalin kowa a gidan..chain aka sa Mata sannan aka Kira malamin da zai yi mata rukiyya kafin ta dawo hayyacin ta...Tayi kuka sosai na rashin dan Uwa kuma masoyi a gare ta...   
   Kai har sai da kowa ya koma Ana tausayin ta..Kafin ka ce kul..gidan ya cika da jama'a..Su Asmee da Hajiyar ta ma sun zo.
   Asmee sai bin Bilkisu take yi da idanu hankali a tashe,ganin ta da tsohon ciki da tayi..Haka ma Mommyn ta..Sai kuma bakuwar fuska da ta gani wato Maman Bilkisu...
    Bilkisu ta zo gittawa gaban Asmee sai ji kake.."tummmmm!"..........*Abeg waye ya fadi??!!..mu hadu a next page in shaa Allah๐Ÿƒ๐Ÿฟ๐Ÿƒ๐Ÿฟ*

_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar  
                      *31*
    Hotel de peacock shine sunan hotel d Shu'uma ta Kama ita da kawayen ta.Sai da suka huta sannan ta dau wayar ta ta Kira Ramlan. Ringing biyu ya daga wayar..
    "Hello,sup...kalau..ba komai what are friends for?.. Kana MX neh?...yawwa in ka shigo,you let me know please..ina son muyi wani dan magana neh..OK...bye!",sannan t katse wayar..
    "Jay I'm coming for you soon...kai nawa neh!",ta karasa zancen tare da yin pecking hoton sa da ta mayar a wallpaper'n ta.
   A rayuwa,Shu'uma bata taba son wani namiji ba sai akan Ja'afar.. Ta sha alwashin ko ta halin qaqa neh sai Ja'afar ya aure ta!....

******

   Ramlan yana type b quarters Abba ya Kira sa a waya cewar ya dawo gida yace toh..
    Ba akai awa biyu da Kiran sa ba sai gashi ya shigo yana wani mutsutssuke ido kamar wani kamili..Duk idanunwan shi sun yi ja.
   Tabbas ya ji mutuwar dan uwan sa,musamman ma da shin neh sanadiyyar mutuwar sa shiyasa yayi wa kan sa alkawarin sai yasa Bilkisu ta rasa farin ciki a rayuwar ta..
     Yana shigowa dai dai Bilkisu tana gittawa gaban Asmee.dummmmm!,karar faduwar mutum aka ji,kowa ya kai duba zuwa ga inda aka ji karar...
    MAHNEERAH ce ta fadi!..iskokai sun yi sallama kuma.ihu ta fara yi Mai razanarwa sannan ta mike tana sambatu...
   "Wallahi sai mun kashe shi..sai mun kashe shi...wayyo...har ya isa ya taba mu!!....",Ramlan na ganin haka,ya raba cikin jama'a ya shige dakin sa..
   Babu wanda ya gane abinda yake faruwa saboda su dai sun ga shigowar shi kenan,basu san meye dalilin ta na cewa sak sun kashe shi bah...
   Yana shiga daki ya zauna yana kuka."why!..why me!!...Sultan I'm sorry,I never meant to kill you..sai da na gaya maka karda ka sa bakin ka a zancen nan..amma..amma...gush!!",ya karasa maganar yana buga kan shi a gado..
   "I'm such a failure! Ban so rayuwa na ya kasance haka bah.how did I become so bad like this? Na kashe kani na da hannu na..ka yafe min..Mami Ku gafarce ni!"..Kuka sosai ya ke tayi.
    Ko jana'izar ma bai je bah saboda tsoro.Gani yake kamar Sultan zai tashi ya damqe shi. 
   Ana dawowa daga jana'iza Ja'afar ya shigo dakin,ganin shi yayi a kwance yana kallon silin,daga ganin sa ka san hankalin sa baya jikin sa.
   Firgigit ya tashi da Ja'afar ya taba shi..
  "Haba bro,sai ka ce ba namiji bah..he is your kid brother,amma ko bankwanan karshe baka yi masa ba..raka shi makwancin sa shine gatan da zaka yi ma sa amma you were nowhere to be found...."
   "Yaya I couldn't take it...mutuwar shi yaxo min unexpected.. Allah sarki Sultee..he was my little companion....",kasa cigaba da magana yayi saboda muryar sa da ta shaqe....
    "Its ok.. Addu'a za ka yi mai ka ji??"...kada kai yayi alamar eh..
   "Toh bari naje falo domin taya Abba karbar gaisuwa,take care of yourself ka ji??"
  "No please,karda ka bar ni...ka tsaya da ni please....",cewar Ramlan yana kaduwa...
   Zama Ja'afar yayi kusa da shi,ya rike mai hannu yana ta bashi baki har ya zo ya daina kuka yayi bacci.
   Abin ya matukar ba wa kowa mamaki musamman iyalan gidan Abba da suka san halin Ramlan,amma yau gashi ya nutsu sanadiyyar mutuwar dan uwan sa..
   Zazzabi yayi sosai saboda yawan mafarke mafarken da yake yi da Sultan.sai da yayi sati biyu ana jinyar sa kafin ya murmure..
   Mahneerah ma sai da ta rame tayi kashi kashi da ita... Kullum tana cikin daki a kulle tana karatun alqur'ani in ta dawo daga makaranta..
    Ana nan ana ta zaman makoki har sati uku...
 
 ****

A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah... Cikin Bilkisu ya cika wata tara...
   Ana tsaka da bikin Fatima ta fara naquda..Su *Ummieekhaleel* uwar zakwadi ta je ta kira Ja'afar a waya. Kafin ka ce meh, Bilkisu ta gama birkicewa.
   Su *Leemcy,Dimples, UmmieeRilwan,Fiyya da Sha'awa* suka runtumo a guje.. *Anty Billy (Maman Nu'aiym) da Aunty Fauxah mb* na ga suna fitowa daga motar Ja'afar.
   *Salmerh da Zeenaseer* neh suka dauke ta zuwa mota yayin da *Khadija Alnur da Momyn Sultan* suke damben shiga gidan gaba..Sai da mutan gidan *precious writers forum* suka sa baki,Khadija ta hakura Momyn Sultan ta bi su.
    *Motan Xarah novels members* na shige ina yi wa *Momyn Cyama* gwalo saboda an rakube ta a ciana'r mutan gidan *Amalfansclub*...
    Muna isa asibiti direba ya juye mu sannan yayi parking a waje.Kana ganin mu zaka ce biki muka zo yi a asibiti,ba su san haihuwar *'YAR GATA CE* bah..Muna tsaye a wurin sai hayaniya ake yi,da masu addu'a da masu kuka da masu gulma dai kowa yana na shi.
  Can motar *Professional writers da Dimples novels* ya iso.A nan na hango *Asmeebae* tana gyara gwagwaron ta da ya karkace,da gani dambe tayi kafin ta samu shiga motar. *Jidda da Xeebae* suka biyo baya sai *Mrs Fulani da Anty Cute Xahra tare da Jumping๐Ÿ’* din ta...
   Duk wanda ya gan mu,sai yayi dariya saboda yadda muka cika gaban asibitin kamar za a raba mana kudi.
     Bayan minti arba'in da biyar *Dr. Harisa* ta fito tana murmushi.Magana tayi da *Maman Nu'aiym* sai ganin Maman Nu'aiym nayi tana kwasan shoki...hahha...Rangada guda *Fiyya* tayi yayin da *Anty Badeesocial* ta bada announcement cewar Bilkisu ta hankado tika tikan twins...
   Kamin kace kwabo, *Leemcy da dimples* iyayen rawa sun fara kwasan rawa a tsakiyar asibiti sai da security ya bude musu idanu sannan suka dai na...
    *Babynurse* ce ta fito tare da *NurseFaizah* dauke da twins din.Ja'afar ya fara daukan su yayi musu addu'a yayin da *Sha'awa* keh jin dama ace baba ya bar ta tayi aure ta zankado twins haka itama..Magana yayi da nurses cewan su mayar da yaran ciki saboda ya lura zamu iya hallaka Mai yaro in aka bamu shi...
    Da muka jira muka ji shiru,kowa ya kakkabe saratu'n sa yayi gaba..
   Abba,Baba,Mama da Mami kai har ma da Momma sun yi murna sosai da haihuwar 'yan biyu'n nan..Sai da aka gyara Bilkisu aka bata magunguna da zata bukata sannan aka sallame su...
   Gatan yau daban,na gobe daban,na jibi daban..Su mama na kula da ita da yaran sosai..Mami ki kulawa da ci da gyaran jiki na Bilkisu,yayin da Momma da Mama ke kulawa da 'yan biyu..
   Ranan suna aka rada wa yaran sunan Abban Mahneerah (Sadiq,Abba karami) da Sultan (Sultan junior).Abba sunji dadi sosai da karamcin da 'ya'yan suka yi.. musu..Ba ma kamar Momma bah da sunan mijin ta sukutum aka sa wa Hassan...
    Yara sun sha kyauta.Akwati daddaya na kaya 'yan *HAMA GEE novels* suka mawo.'yan gidan *Maryerm novels* kuma suka kawo set na sweater bibbiyu. *Home of novels* kuma suka kawo packet din pampers...
     Mun ci mun sha mun koshi har na rago wa mutan gidan *Ummieejaafar novels* kasussuwan kaza saboda a nan muka fi auki๐Ÿ˜œ.....Allah shi raya *Abba karami da Sultan junior*..............*Welcome to the duniya twins....sai mun hadu a next page*_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[1/11, 8:11 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                      *32*

Zaune take tana shayar da Junior yayinda Abba karami yake bacci abin sa.Ja'afar neh ya bude kofan ya shigo a hankali.Da ganin shi,zaka san a boye ya shigo..Kyalkyalewa da dariya tayi,da sauri2 ya zauna a gefen ta yace "shhhh",sannan yayi mata peck.
   Magana ya soma yi mata cikin rada.
  "How is my baby mama doing?"
  "Alhamdulillah dear."
"Yara na fah?,wallahi ina son na tayaki raino amma Mama sun tasani a gaba.."
  "Hakuri zaka yi you alone,its just for sometime, muna cika forty days zasu wuce.."
  "Ohshhh,har forty kissy na?,I really missed you a lot!",yace tare da rungume ta yana kallon baby junior da bacci ya dauke shi..
  "I miss you too dear!",tace yayin da tayi relaxing kan ta akan kafadarshi da kyau...
    Yana kokarin kai mata kiss kenan,Mami ta leko.."toh marar kunya sai ka fito koh."
   "Haba Mami mutum da matar sa amma sai anyi masa iyaka da ita"
 "Ni dai ka tashi ka fita daga dakin ga kafin na bata maka rai",cewar Mami tare da nuna mai hanyar fita.
   Sunkuyar da kai Bilkisu tayi cike da jin kunyar sirikar ta,shi kuma gogon ya wani tamke fuska ya fita.
  "Ke kuma ki dinga biye masa kinji koh?"..
   "A'a Mami"...
"Ohho dai, kya ji dashi in aka sambada miki wani",cewar Mami tare da rufe kofan.
   Bilkisu bata ji dadin yadda Mami tayi wa you alone dinta bah.Kwantar da junior tayi sannan ta mike a gadon itama.
   Wayar ta neh ya soma ruri.Tana dubawa taga Ja'afar neh.Murmushi tayi sannan ta daga call din.
   "Wa alaikumussalam ya hasken zuciyata,please kayi hakuri,nima ban so haka ba amma ya muka iya,haba you alone I can't,please kayi hakuri just some weeks ya rage fah,please...don Allah karda ka......",katse wayar yayi Kafin ta kuma yin magana.
   "Haba ya zanje dakin sa,gaskiya hakuri zai yi,bana son ya ja mini wani abin kunya kuma".
    Text ta tura Mai Wanda yake kunshe da kalamai masu dadi. Sannan ta ajiye wayar tayi kwanciyar ta....


*****

"Mommy gaskiya ba zai yiwu bah,ni fah ya kamata ace Ja'afar ya aura na hayayyafa Mai 'yan biyu din nan..mum I'm eager please,wani plan kike hadawa neh",cewar Asmee muryar ta kamar wacce zata yi kuka.
  "Karda ki damu baby nah,sai kace kin manta wace ce uwar ki,zan dau mataki nan ba da dadewa ba,kin san I'll do anything for you"
   "Yes mum,love you so much"
"Love you more my baby"
   "Uh..uhm a kulla alkhairi dai",cewar Zahra dake fitowa daga kicin tana hawan stairs.
   "Ke uban waye tsaranki a nan..kiyi iya bakin ki ko nazo na gyara miki shi..wawiya kawai" ,cewar Asmee..
   "Ohho dai... Carry go!",cewar Zahra yayin da ta shige daki tayi banging kofar da karfi.
   "Wai Mommy ba zaki gyara wa marar kunyar ga zama bah"
"Ke dai rabu da ita, ban da lokacin ta tukun,jira nake ta gama school of nursing din inga uban waye zata kawo min"..
    "Ni gani nike kamar Ramlan kanin Ja'afar shi take so"
"Koma wane ne,ina nan tare da ita, sai ta kawo shi zan bata mamaki"
   Kyalkyalewa da dariya Asmee tayi."gaskiya Mommy kina birge ni,ba kya kyaliya..toh Mommy ni zan wuce,idan na samu wani plan din zan sanar dake"..

******

"Yawwa guy ya batun zancen da nayi maka, naji ka shiru neh",cewar Shu'uma.
   "Hmm..gaskiya babe,bana tunanin zan iya yi miki hanya a wurin shi..its not easy as you think"
    "Koh nawa neh kake so zan baka, please just help me".
  Wani dariyan shakiyanci yayi sannan yace,"gaskiya bana son nayi miki alkawarin abinda na san ba zan iya ba,deal din dake tsakani na dake, ya kare tun a Dubai, I never asked you to fall in love with him"
   "Ok then,watch it as I do it my own way!",tace tare da juyawa tana tafiyar kasaita.
  "Good luck but my hands are clean!",ya fadi da karfi saboda ta dan yi nesa dashi sannan ya shige motar sa yayi gaba.Daman zai koma school neh..
    

*****

Asmee tana isa gida ta kira kawar ta Shola(Kawar Shu'uma).Bayan sun dan taba hira neh shine ta zayyana wa Shola komai game da auren ta da kuma taimakon da take nema daga wurin ta.
   Sai da ta dan yi Jim sannan tace wa Asmee ai faduwa tazo daidai da zama ne saboda harkar su ke nan.But zata sanar da ogar su,wato Shu'uma kenan saboda recently ta cika irin aikin da Asmee take bukata.
   Sosai Asmee ta ji dadi,bata san *BABBAN KUSKUREN DA TA TAFKA* kenan bah.Hotunan couples din tace Asmee ta turo mata..Cikin dan kankanin lokaci ta tura mata hotunan kana Shola tace mata zata Kira ta,ta bata feedback.
   Tana gama wayar taje kicin domin dauka juice din da ta ajiye a fridge.Tana shiga taga Ashraf yana shan abu cikin kofi.
    "Kai meh kake yi?",ta daka masa tsawa.
  Kaduwa ya fara yi Kamar wanda yaga mala'ikar mutuwa.
  "Ba da kai nike yi bah??"
 "Uhm..uhm..hajiya ta ce ta..ta zo dazun..shi..shine..ta..ta..ta kawo min ruwar..addu..addu'a wai na sha",yayi maganar yana i'ina.
   "Iyye,kutumar uba,wato ita Mai da koh...Ni da uwar ka wace ce ta fi daraja a wurin ka?"
    "Keh",ya amsa jiki sanyaye.
"Kace wa?",yace "keh"..
   "Toh miko min kofin"
 Mika mata yayi ta karba ta juye a sink sannan tayi masa quoting warning cewa karda ya kuskura ya kara shan duk wani abu da mahaifiyar shi zata ba shi..Sannan ta fice daga dakin.....

*****

Haka Bilkisu suka yini a gida,Ja'afar yana wani shan kunu saboda tace ba zata je dakin shi bah..
    Bayan sun ci abinci da dare ya tashi ya wuce dakin sa.Hira take yi da su Mama amma hankalin ta baya wurin su tunda ya tashi. Da Mami ta tambaye ta,sai ta fara inda inda,karshe tace zata je ta duba su Abba karami.
   Tana shiga taga sun farka daga bacci sai mutsu mutsu suke yi a shawl din su.Madara ta hada musu ta ba su.Nan da nan cikin su ya dau suka koma bacci kuma.
   Wuraren karfe goma,taji falon shiru,alamar su Mama sun shige dakin su.Mikewa tayi ta watsa ruwa sannan ta fito ta shafa mayukan ta masu kamshi,ta dau riga da wando ta bacci ta sa,sannan ta sa hula.
   Leka falo tayi domin ta tabbata ko su Mami sun shige daki.Tana lekawa taga wayam, babu kowa a falon. Twins ta dauka kowanne a kafadan ta,ta wuce dakin Ja'afar.Tafiya take yi sadaf sadaf har ta kai dakin shi.
   Knocking tayi da kafa a hankali saboda yaran dake kafadun ta.Bude kofar yayi ta shige dakin sannan ya rufo.
   Kala bai ce mata bah har ta kwantar da yaran.Juyowa tayi ta bangaren shi tace,
   "Haba you alone,hushin ya isa haka mana,I don't like it when you're angry with me,gashi na zo,kayi hakuri ka ji?"
    "Na ji..",yace tare da kwantawa.
  "Haba Hon..I'm sorry",tace tare da hura mai kunni.Jin shi yayi kamar cakulkuli sai ya kyalkyale da dariya ya rungumo ta..
    Shikenan oo zance ya canja,farantawa junan su rai suka yi sosai har sai da suka ji daidai sannan suka liqe wa juna sai dreamland....

*****

"Bae gashi mun samu irin deal da muka yi a Dubai fah,sai dai na ga kaman the same couples neh da muka yi aiki kan su"..Shu'uma na jin haka tace bani wayar na gani.
   "Wow...su neh!...wani aiki tace ayi mata",cewar Shu'uma.
   "The same aiki da na Dubai da muka yi"..
  "Wow this is extremely good! Wannan hausawa kece wa 'faduwa ta zo daidai da zama,kinga garin yin deal din sai na shigar da kaina a registar zuciyar shi'",ta fadi tare da yin wani shu'umin murmushi..
   "Abeg ooo,na fa san Asmee,please karda ki sani a case din ku, she can do anything to anybody who betrays her"..
   "Naji,daman ai nice master mind na komai,so don't worry baby,zanyi komai da kai na..Kira min ita"...
   "Alright then,my hands are clean,Allah ya bada sa'a",tace tare da dialing nombar Asmee..
   Bayan ta dauka ta mikawa Shu'uma suka shirya kan amount din da za ta biya ta,sannan Shola ta jaddada wa Asmee cewar she has no business with them.Don haka zata turo wa Asmee da nombar Shu'uma su dinga communicating....

****

  Asmee tana kammala wayar,ta fara jin zuciyar ta yana tashi.Kafin ta mike ta shiga bayi ta fara kwarara amai.Da gudu Ashraf ya shigo dakin, ganin halin da Asmee take ciki yasa ya rude.
   Sai da tayi amai sau uku da yammacin nan.Duk jikin ta yayi weak.Karshe ta ce Ashraf ya kai ta asibiti.Shi ya taimaka mata ta shirya sannan suka wuce asibiti.
   Suna isa tayi musu bayanin yadda take ji.A take aka yi mata pregnancy test.Ita dai gani take yi kamar suna shirme neh,sai da result ya fito,likita ya mikawa Ashraf yana murmushi.
   "Congratulations sir,your wife is 2months pregnant!"
   "What!!!!"*Ku biyo ni a next page....Love you all๐Ÿ˜˜*


_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[1/13, 4:55 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                      *33*

   Zaune take ta rasa yadda zata yi.Ya za ayi ace tana da ciki whereby tana using roban kwororo wajen saduwa da Ashraf..Gaskiya ita baza ta iya renon yaro ba at her young age, dole ta zubar da cikin nan.
    Wayar ta ta dauka ta yi dialing nombar Mommy. Bugu biyu ta dauka,
    "Hello baby na,ya kike"
"Mommy ba lafiya fah"
  "Toh ya aka yi,hope ba wani cin mutuncin aka yi maki bah"
 "A'a wallahi..uhm..uhm Mommy daman..daman"
  "Daman meh?"
"Mommy jiya neh na fara dan karamin zazzabi sai nasa Ashraf ya kai ni asibiti..sai.sai"
   "Sai meh? Ba dai ciki kika hambaro ba koh?",Mommy ta fadi da karfi a wayar da yake a loudspeaker ta sa.
   "Shine Mommy"
"Lahaula wala quwwata illa billahi,iyye Asama'u,tarbiyyan da ba baki kenan,kije ki bi maza a waje har su d'ama miki ciki.?!"
  "Haba Mommy, trust your girl,wallahi cikin shi ne"
  "Toh ta yaya tunda na san ba bashi fuska kike yi bah?",Mommy ta tambaya unbelievably.
   "Mommy kin san abin ne da dadi idan kayi shi for the first time,so wani lokacin na kan biye mai mu yi amma ina amfani da kororon roba",Asmee tace kamar wacce tayi abin arziki.
   "Kororon robar uban ki na ce,tunda ke kika ja wa kan ki,count me out!"
  "Hello..hello Mommy..oh shit! Ta kashe",cewar Asmee tare da ajiye wayar.
   Juyowan da zata yi sai ta hangi Ashraf tsugune a bakin kofar ta kamar wani maraya.A harzuke tace,
   "Kai mallam lafiya ka wani zo ka rakube min a bakin kofa?"
   "Dan Allah, don son annabi karda ki zubar da cikin nan,its all I've got now"..tun bayan da ta mayar dashi mijin hajiya,sai yau yayi speaking english a gidan..
   "Kaji min ja'iri,har kana da bakin cewa karda na zubar da cikin ka,yaushe ka fara jayayya da decision dina, toh gwara karda ka fara saboda zan mugun saba maka",tace tare da mikewa.
    "Don Allah nace fah please"
   "Watch me as I do it!",tace tare da hankade shi a bakin kofa ta wuce kicin abin ta domin neman madaci da aka kawo mata...
    

*******

Kiran sallar asuba ya fargar da ita. Tana mike jiki tare da yin addu'ar tashi daga bacci ta tuna ba a dakin ta ta kwana bah.Da kyar ta kwace kan ta daga jikin shi bayan ya bude ido sannan ta Mike ta kwashi yaran ta.
    Lekawa tayi kafin ta fito yana tafiya sadaf2 kamar munafua.kuwa tayi sa'a su Momma suna daki amma tana jin Kara a dakin nasu kamar sun farga daga bacci.
   Tana shigewa dakin ta,ta yi wani ajiyar zuciya sannan ta rufe da kafar ta.Kwantar dasu tayi sannan ta shige bayi tayi wankan ibada sannan ta fito. *(Ba dole ne ba idan kika yi wankan ibada,ki kuma yin alwala bah,saboda shima wankan ya wadatar...Wankan tsarki nike nufi da ba wankan soso da sabulu bah...wallahu a'alam)*.
    Shafa mai tayi sannan ta dau jallabiyar ta na yin sallah ta sa sannan ta sa hijabi a sama,shimfida darduma tayi sannan ta tada iqama.Rak'atanul fijr ta fara gabatarwa *(wato sallar.rak'a biyu da ake gabatarwa kafin sallar asubahi.tana da falala mai dimbin yawa! Allah ya bamu ikon yi.)*
     Bayan ta idar da sallah tayi azkar sannan ta mike,ta Ciro hand dryer din ta domin tayi drying sumar ta. Tana cikin drying din sumar neh Mami ta leqo,
   "Sannu Bilkisu,kin tashi lafiya?".Har ta tsargu sai ta maze kawai tace,
  "Lafiya lau Mami, ya gajiya da ni?"
  "Gajiya ya bi jiki,ya kwanan jikokai na?"
 "Alhamdulillah, gasu nan sai bacci suke yi.."
 "Toh madalla,wannan drying sumar da sassafe na lafiya?"
   "Uhm..uhm wanka nayi sai na hada da suman na wanke gaba daya saboda yayi datti".
  "Toh yayi kyau",Mami ta ce sannan ta rufe kofar.
   Ajiyar zuciya tayi sannan ta cigaba da drying sumar,tana gamawa ta kulla shi a ribbon bayan ta kwaba Mai a suman sosai.
   Wani shadda Mai kyau ta cire cikin wanda Mama ta dinka mata tasa.Sannan ta fita zuwa dakin su Mami domin yi musu ina kwana.
   Bayan sun gaisa neh ta wuce kicin domin hada wa oga breakfast saboda Momma ta hada musu kunun alkama da shinkafa koh.
   Plantain ta soya sannan ta hada masa kunun gyada da yaji kayan kamshi sannan ta juye su a flask.Diba kunun alkaman tayi taje ta zauna a falo, tana kallon SUNNA TV tana kurban kunun a hankali.
     Karfe bakwai da rabi ya fito daga daki sanye da English wears.Momma da take shirya su Sultan junior ya gaisar sannan ya wuce dakin su Mami ya gaishe su.Yana fitowa yayi mata alama da idanu cewan tazo dinning area.
   Sum2 ta mike kamar munafuka taje dinning din.Bayan ta gaishe shi tayi serving abincin sannan ta koma falo. Bayan ya kammala karyawa ya sallame su cewan zai leka company yau.
   Rarraba idanuwa Bilkisu take tayi har abin yaso ya ba wa su Mama dariya.Momma ce tace,
  "Tashi kije ki sallami mijin ki mana"
  Mikewa tayi cike da kunya ta fita waje. Har ya shige motar sa,zai rufe kofa yaga tana zuwa sai ya bar kofar a bude.
  "Ina zaton ba za ki sallami you alone dinki ba neh"..Far tayi da idanu sannan tace,
  "Na isa??,kunyar su Mami dai nike ji shiyasa kaga nayi hesitating"
  "Gaskiya ni na gaji da wannan takura,mutum da gidan shi amma ba zai wala da iyalin sa bah",yace tare da murguda baki.
    Kyalkyalewa tayi da dariya har tana shidewa saboda yadda yayi da fuska.
   "Kayi hakuri its just for some time Nawan",tace tare da yin dariya kuma.
   "Toh leqo in gaya miki wani abu",yace tare da mika mata hannu.
    Dariya tayi saboda ta dago manufar shi sarai,sannan tayi yadda yace.Sumbatan ta yayi na wasu 'yan mintuna sannan yayi mata peck a kumatu kana ta rufe mai kofar mota tayi waving dinsa yayin da yake fita daga haraban gidan.
    "Sannu baba",tace wa maigadin su sannan ta wuce ciki.Sadda kai tayi a kasa kamar Mara gaskiya ta wuce dakin ta........

*****

"Oh ni Asmee ya zan yi,tun jiya da dare na sha wannan madacin amma wannan shegen cikin yaki fita",cewar Asmee yayinda take karasa cinye madacin da ya rage.
    "Dole na kira Mommy na roke ta ta taimaka min,I really want to get rid of this pregnancy don ni cikin Ja'afar kawai zan iya daukawa"..
   Daukar wayar ta tayi,ta kira Mommy amma taki dagawa.Sai da ta Kira kusan sau hudu kafin ta daga,
   "Wai ke lafiyar ki kuwa,kin wani ishe ni da kira!"
  "Haba Mommy, kiyi hakuri ba zan kuma bah please,I really need your help"
 "Gobe ma ki kuma ja'ira kawai"
   "Yi hakuri Mommy, yanzu ma na ci madaci amma yaki zubewa,please ki taimaka min da wani abin da zan sha"
   "Toh zanyi miki wani hadi in ba Zahra ta kawo miki"
 "OK Mommy,thanks love you!",tace sannan ta katse call din.
   Sallama ta jiyo daga falo ta mike taje ganin ko waye neh.Hajiyar Ashraf ta gani tana washe hakora kamar wacce aka yi wa albishiri da aljanna.
    "Mallama lafiya kin shigo min gida baki ce Kala ba sai wani washe hakora kike yi".Kasa magana tayi,wato haka rashin mutuncin Asmee ya kai.
    "Haba..uh..uhm hajiya ta ce fah"
  "Dalla can,bace min da gani,je ka gyara min daki kafin na gama jin meh ya kawo gyatumar ka".Sum2 ya wuce daki.
   "Nazo neh na taya Ku murna saboda karuwan da aka sa..."
  "Ya isa haka nan,wato yaron ki ya kira ki ya gaya miki koh,toh ki saurare ni da kyau..wannan cikin ba zan haifo shi bah,kin gani ma madaci nike ci..."
   "Don Allah karda kiyi mana haka Asama'u"
"Gush..the name she calls me irritates me the most..Mallama ki fita min daga gida"
   Hajiyar Ashraf kuwa idan hankalinta yayi miliyan ya tashi.Wanga ake cewa an ga samu an gan rashi.Ita da take rokon Allah ya nuna mata jikokan ta kafin ya dau ran ta,shine addu'ar ta na shirin karbuwa wata zata kawo mata cikas.
   Rike kafar Asmee tayi tana rokon ta tana hawaye amma meh Asmee zata yi,cire kafan tayi,tayi ball da surukar ta.hmm Asmee kenan.Haka hajiya ke ta rokon ta,ta tura ta waje ta rufe kofan,ta wuce daki abin ta.....


******

"Peep.peep..peeep",yake ta honk amma taking bashi hanya da zai shiga company din sa.
   Fitowa yayi yana huci."ke Mallama lafiyar ki zaki wani tsaya min a gaba,idan na bige ki fah",cewar Ja'afar a fusace.
  "Please I'm sorry sir,babu yadda na iya neh,in bqn tsayar da kai a nan bah babu yadda zan yi na shiga saboda an ce maigadi ya Kore ni,please help me sir",cewar Shu'uma.
  "Meh ya kawo ki nan kuma bayan....wait kin sani tuna abu ma...follow me to my office!",yace tare da shigewa motar shi,yana kaiwa wurin maigadi yace,"mallam Illu ka bari waccan ta shigo",sannan yaje yayi parking a parking lot.........*Sai mun hadu a next page... Muaah๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹*


_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[1/14, 9:30 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                      *34*

"Ke Zahra zo na aike ki wajen yayar ki",cewar Mommy.
  "Kai Mommy ina da lecture fah by 2 kuma kin ga yanzu 1pm yayi"
"Xaki je ko kuwa?"
   "A'a zanje,kawo sai na yi mata dropping daga nan sai na wuce school".
  Ciro kullin maganin tayi ta mika mata kana tace,
  "In kin ga dama kuma kije kiyi mata rashin kunya ta mammazge ki"..
   "Ohho dai",cewar Zahra yayin da ta dauki makullin mota ta fice abin ta...


*****

Ajiyar zuciya yayi bayan ya gama jin dukkan bayanan ta.
   "Amma ke mai yasa ki yin hakan,wani ne ya sa ki aikata hakan? tell me the truth".
  "Uhm..uhm..a'a,wallahi sharrin shaidan neh,tun da na gan ku tare kuka birge ni,shine naji dama ace nice haka nan,shine...na"
   "Please ya isa haka nan,yanzu ma da nike magana da ke,na shirya da mata ta tun ranar da abin ya faru coze trust each other so,babu Wanda ya isa ya raba mu,stick that into your dumbhead next time idan sharrin shaidan din ya motso miki"..
    "Wallahi na tuba sosai,ina kan turban neman rahamar ubangiji na neh.ka yafe min,zanje wajen matar ka na nema gafarar ta itama please",cewar Shu'uma tana wani kukan munafunci.
   "Ni na yafe miki so,there is no need kije wajen matata saboda idan har nq yafe miki tamkar itama ta yafe miki neh,so?"
   "Uhhum,one more thing please,I want you to be a like a brother to me"
  "What?! Saboda meh, wato ba ki tuba ba kenan,kina son kiyi playing pranks da ni koh?!",yace a fusace.
  "I'm serious please,kaga ni marainiya ce,I lost my mum tun ina karama kuma ni kadai ce yarinyar su,I don't know how it feels to have a sibiling,don Allah shine alfarma na karshe da nake nema a wajen ka,ka zamo tamkar yaya a gare ni so that ka sani bisa ga turba Mai kyau.."
   Hmmmm..ya ja wata doguwar ajiyar zuciya.
  "Zanyi tunani kai kuma karda wannan ya baki guarantee na zuwa office Dina anyhow,you may take your leave"..
   Mikewa tayi tare da yin murmushin 'na kusa cin nasara' sannan tace,
  "Nagode sosai,please ka rokar min madam,itama na san she'll accept me as a sister ko ba komai musulunci ya....."
  "Please take your leave",ya katse ta saboda yana ganin tana so ta wuce gona da iri.Ficewa tayi daga office din tana Mai jin dadin kammala first mission dinta,wato ta nuna mai cewan ta tuba har ya yarda da ita..
   Ta Lura yana matukar son matan sq,so watarana zata yi amfani da ita to get Ja'afar. Ita bata son ta bata kyakkyawar alakar shi da matar shi amma she wants to be his wife too.......


*****

"Assalamu alaikum, babu kowa a gidan neh",cewar Zahra da tayi sallama taji shiru.
   "Wa alaikumussalam a'a hajiya Zahra ke ce a gidan namu yau?",cewar Ashraf da ya fito yana goge hannu da alama abinci ya ke yi.
   Baki ta sake galala tana kallon sa
  "Uncle Ashraf ince dai ba abinci kake yi bah"
  "Uh.uhm..eh wallahi abinci nike yi,kin san yayan taki bata ji dadi bah"..
  "Ohh Allah ya sawwake,ina take?"
 "Tana dakin ta"
   "Toh sannu da jinya"
"Ihhi..yawwa sannu",tare da yin dariyar da bai kai ciki ba..
   Tana shiga daki daidai tana fitowa daga bathroom tana goge baki,saboda amai da yazo mata.
   "Sannu ya jiki"
"Dallah mika min sako na"
  "Dadi na dake kenan ba a taba yi maki abin arziki",cewar Zahra tare da mika mata ledar.kallon yayan ta take yi yadda take abu kamar Mai ciki sai tace,
  "Kardai nace someone has been put into the family way?",
 "Uban ki neh ya sani a family way din marar kunya,dallah tashi ki fita min daga daki"
   "Hhh ai ko baki Kore ni bah wucewa zanyi,school zani shins Mommy ta bani wannan banzan aiken,if not me zan zo yi a akwalar gidan ki,mtchww kinga tafiya ta...",tace tare da sabula handbag din ta,ta wuce.......

*****

"A'a su Ramlan neh a gidan har kun dawo hutu kenan",cewar Momma a lokacin da Ramlan ya shigo falon su Ja'afar.
   "Eh wallahi mun samu hutu,ina yini"..
   Bayan sun gaisa neh ya bukaci ganin babies din,dakin Bilkisu Mama taje ta dauko su kana ta gaya wa Bilkisu Ramlan ne ya zo..Sai da gaban ta ya fadi jin an ambace sunan sa,ita tama manta da kwai mutum Mai existing irin sa!..
   Babban mayafi ta ciro ta yafa sannan ta fito falon.
   "A'a sannu da zuwa mutanen IBB",tace tare da zuwa kicin ta ciro mai drink din Chapman da snacks na suna da ya rage..
   "Yawwa sannu,na same Ku lafiya?"
  "Lafiya lau,ya sch"
"Toh mungode Allah"..Haka dai suka gaisa sama2 amma na ciki yana ciki.
   Shi kuma yazo da manufa biyu neh,daya yaga takwarar kanin sa,na biyu kuma ya nema hanyar daukar fansa.
    Wata biyu kadai gare shi for vengeance saboda hutun school din su two months neh.
  Mikewa tayi ta shige daki,ita dai bata yarda da wannan zuwan nashi bah.
   Bayan minti talatin ya sallame su tare da ajiye dubu hudu,acewan sa shi student neh suyi maneji...


******

Da dare suna zaune a falo da kissy'n sa saboda su Mami sun shige daki da wuri yau shine yake bata labarin abin da ya auku tsakanin sa da Shu'uma..
     Nan take kwalla ya cika a idon ta."haba you alone,wai meh na aikata ne a rayuwa da yasa duk inda nike sai na samu makiya?",tace tare da goge guntun hawaye da ya zubo a fuskar ta...
    "When people do not hate or talk about you,then you are nobody,kin mallaki wani abu neh da suka kasa mallaka shiyasa,but please karda ki bari su fi karfin ki kissy na",yace tare da rike hannun ta.
    "So,yanzu meh zaka ce mata?"
"Meh kuwa,hakuri zan bata kawai saboda bana son nan gaba ta rikida zuwa halin ta na da"..
   "Hmm ba komai you alone,ka yadda da bukatar ta kila ka zamo *WANI HASKE* a rayuwar ta,tunda ta zabi ta bar halayen ta na da,kaga bai kamata mu juya mata baya ba idan tazo neman taimako daga gare mu".
   "Gaskiya zanyi tunani kai still,ba zan amsa request din ta ba kwasam sai nayi wasu bincike"..
   "Gaskiya kissy na ke ta daban ce,samun mace irin ki sai an tona"..
  "You alone you're the most lovely person on earth to me,I can't imagine my life without you..",tace tare da kwantar da kan ta bisa kafadar sa.
     "Kissy na,Allah ya jarrabce ki tun kina 'yar kankanuwa,baki tashi cikin gatar iyaye bah,abubuwa da dama sun faru a rayuwar ki amma kin daure Kin bar wa Allah komai,gashi kina cin moriyar hakurin da kika yi yanzu,Allah ya barmu tare uwar ya'ya na",ya karasa zancen tare da hada fuskokin su,yana shakan dadaddan kamshin dake fita daga wuyan ta.
    "Allah ya bar min kai you alone",matsowa da lips dinta tayi zata hada da nashi sai ji suka yi ance,
  "U..uhm sannun ku",cewar Mami..
   Wayyo Bilkisu ji tayi kamar kasa ya bude ta shiga don kunya.Kwata2 sun manta a falo suke mah, da sauri ta janye jikin ta daga nashi.
    "Oya mallam bi nan...",tayi masa nuni da hanyar dakin sa.Mikewa yayi yana dan Susa kai ya wuce dakin sa yayin da Mami ke cewa,
   "Ka zo ka tsare ta a nan,yara na can suna kuka,sannu loverbirds,haba ke Ku...",juyowa tayi taga wayam Bilkisu ta shige daki koh...Murmushi tayi sannan ta shige daki itama.Tana jin dadin zamantakewar 'ya'yan ta sosai,kullum cikin yi musu addu'a take cewar Allah ya kare su daga sharrin mahassada......


*SHAFI NA GABA*
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*Innalillahi wa Inna ilaihi raaji'un,Mama sun sace min Bilkisu nah!*
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*Wallahi tallahi ni ban san da komai ba game da kidnapping din ta da aka yi bah!*
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*Ya samu matsala neh a kwakwalwar sa,matsawar abinda yake so bai dawo masa bah,toh I'm afraid haka zai cigaba da rayuwa!!*
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
_Sai mun hadu a next page in shaa Allah_...mai kaunar ku๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹


_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[1/15, 7:14 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                      *35*

*_Inna lillahi wa inna ilaihi raaji'un!!Ya Allah kai ka bamu shi,kuma ka karbi kayan ka.Allah ya jikan shi,yasa ya zamo Mai ceton iyayen sa...Ameen..Please accept my condolence Ummiee Khaleel๐Ÿ˜ฐ_*

         ๐ŸŒฐ๐ŸŒฐ๐ŸŒฐ๐ŸŒฐ๐ŸŒฐ๐ŸŒฐ๐ŸŒฐ๐ŸŒฐ
_*Bayan Wata hudu*_

A kwana a tashi,twins suka cika wata hudu da haihuwa.Abubuwa da dama sun fara tsakanin watannin nan harda dawowar Mahneerah gidan su Bilkisu da zama domin ta taya ta rikon yaran kafin next year,ta wuce school.
    Asmee kuma tayi tayi ta zubar da cikin amma ina yaki fita. Kwata2 ta rasa *TUDUN DAFA WA*,saboda har gan Allah bata son cikin nan.Har wurin likitoci daban2 ta je amma suka ce gaskiya akwai hadari wajen cire cikin nan,kawai ta hakura ta haifo yaron kawai.Tun daga lokacin tsana da tsangwamar da take yi wa Ashraf da mahaifiyar sa ya karu.Sai rashin mutunci kala2 take zuba mai.
    Hajiyar Ashraf kuwa kullum cikin tashiwa nafilan dare take yi,tana mika kukan ta ga Allah. Tabbas ta san yaron ta ya fada a cikin wata rayuwa mai ban tausayi,ace mutum da yaron sa amma matar sa ta raba ku..Hmm...
    Shu'uma kuma ta zama 'yar gida.Saboda Ja'afar yazo ya yadda da request din ta,har wurin mahaifin ta ta kai shi a matsayin her new founder brother.Kawayen ta sun yi matukar mamakin yadda ta canza,har kayan ta ta kwashe karkaf ta kona,sannan ta koma gidan mahaifin ta da zama...
   Su Mami suna son ta sosai saboda kirkin ta.Tana kyautata masu harda su iyayen Bilkisu ma.Wannan ake kira *Classic bribing*..hhhh.Saboda duk ta siye zuciyar su akan cimma manufar ta guda daya, wato *sai ta auri Ja'afar*.Idan Asmee ta tambaye ta sai tace ai sai ta shige su sosai,sun yadda da ita kafin ta karasa deal din su...

******

Ranar wata laraba,Mahneerah da Bilkisu suna hira a falo abin su,yayin da twins ke kwance a baby cot din su.Sunyi bul bul da su,zar sha'awa.
    "Eh wallahi ina jin shan faten acca. Ji nake kamar zan mutu idan ban sha ba",cewar Bilkisu.
 "Wayyo Anty na karda ki mutu oo,I can't imagine how brother would be,bari naje na dafa miki faten,kinga sai mu sha shi as abincin rana koh?"..
   "Eh my dear,shiyasa nike son ki..oya je ki dafa,sai nazo nayi miki rating dinshi",tace tare da mikewa da kyau a cikin kushin.
    Dariya suka yi kana Mahneerah ta wuce kicin,Bilkisu kuma ta mike taje ta dauko mp3'n Qur'anin da take kunnawa wa su twins.A rayuwa tana sha'awan ta ga yaran ta sun zama hafizai shiyasa a ko da yaushe zaka ji Qira'a yana playing a cot din su sai dai idan an samu mishkila.
    Tana fitowa taji Ana knocking a kofa.
   "Anty ana knocking fah",cewar Mahneerah daga kicin.
  "Eh naji,I'll go and get the door",tace tare da komawa daki ta yafa babban mayafin ta sannan ta fito ta bude kofar.
    Minti biyar,minti goma ya wuce amma shiru.
    "Anty in sa curry a faten?",cewar Mahneerah daga kicin still.
  "Anty kina ji na?",amma shiru.Murmushi tayi tace,"kai Anty kenan da son bacci,kila tayi bacci neh,bari na zuba kadan dai karda yazo yayi yawa".
    Sai da ta gama dafa abincin tas har da hada lemon drink sannan ta fito daga kicin tana murmushi.Bayan ta jera abincin a dinning din sai ta shigo falo amma wayam babu Bilkisu sai ma twins dake cot din su,suna kuka.
    "Anty where insin you,the baby his crying",tace tana kwaikwayon muryar Jennifer tana dariya.Amma meh tana shiga dakin taga wayam.Shiru tayi koh zata ji karar saukan ruwa daga cikin bayin ta amma ko karan digon ruwa bata ji bah.
    "No,its not possible,anty da na bari a falo just thirty minutes ago?"
   "Anty dan Allah ki bar wasan nan ina kika shiga..Anty..Anty...",tace tana leka dakin Ja'afar,shima wayam babu kowa.Da gudu ta fita taje waje, abinda ta gani yasa gaban ta ya fadi,baba maigadi ta gani a daure an saka Mai tsumma a baki.
   Da gudu ta karasa wajen shi ta cire mai tsumman.
   "Baba mai ya faru? Ina Anty na..Baba yi magana mana",tace tana jijjiga shi amma da yake he was short of oxygen,sai ya zube a wurin sumamme.
    "Inna lillahi wa inna ilaihi raaji'un na shiga uku,wayyo Allah wa ya dauke min Anty na,please ka tashi ma gaya min..meh zan ce wa yaya idan ya dawo..he'll kill me...la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zaalimin..Antyyy...",ta mike da gudu ta koma falo,ga twins sai kuka suke yi kamar ana Kara tunzura su ne suyi.
     Rudewa ma tayi ta rasa da meh zata fara.Wayar Bilkisu ta dauko saboda nata ya samu matsala ta far neman nombar Mami saboda bata san yadda zata yi facing Ja'afar da wannan zancen bah.
    Bugu biyu Mami ta dauka da sallama amma shiru ba'a amsa bah.
   "Maman biyu lafiya?",cewar Mami daga daya bangaren.
   "Mami Mahneerah ce",tace cikin shesshekar kuka.
   "Lafiya Mahneerah?ita Bilkisu'n fah"..Toh anzo wurin.Kara fashewa tayi da sabon kuka.
   "Ke lafiya,wani abin neh ya same ta?..kiyi min magana kina faman kuka".
   "Mami ta bude,sun dauke ta".
  "Ta bude sun dauke ta kamar ya?kin sani a duhu,yi min bayani mana".
    "Mami sun sace anty Bilkisu,sun kashe baba maigadi".
  "Inna lillahi wa Inna ilayhi raaji'un,yi shiru kinji gamu nan zuwa",cewar Mami a sanyaye sannan ta katse wayar.
   Wani babin kuka ta bude kuma taje cot din su twins ta ciro su,sai kuka suke yi tamkar sun san uwar su ta bata.Kwata2 ta manta suna shan madara.Haka ta tasa su a gaba,suna kuka tana kuka har su Abba da Mami da Momma suka iso.
    Ganin Maigadi suka yi kwance a bakin gate.Abba yace da su Mami su shiga ciki,shi zai kai baba maigadi asibiti sannan ya biya office din Ja'afar.
     Da kyar twins suka yi shiru bayan sun sha madara.Mami da Momma suka goggoya su a baya.Mahneerah kuwa tuni zazzabi ya kama ta.ace kana tare da mutum yanzun nan sannan ace ya bata.Kai its unbelievable!.Sai faman kuka take yi,ala yau Ja'afar zai so ya kashe ta saboda da ta fito lokacin da ta kira ta taji shiru da kila basu samu sun ci nasara bah.
    

*****
"Mommy zanje gidan su Ja'afar,yanzu Mahneerah ta Kira ni tana kuka wai Bilkisu ta bata".
   "Ayyuriri,ahayye nanaye. Annoba ta bata shine kike rawar jiki zaki je can saboda gaki munafuka koh"
  "Haba Mommy in ce dai Bilkisu'n matar dan Uwa na ne kuma kawa ta ce,don haka dole ne na damu"
  "Ai sai kije,maimakon ki taya 'yar uwar ki murnar cikan burin ta na samun auren Ja'afar din shine kike wani besty stuff, toh in har na isa da ke,babu in da za ki".
     "Haba Mommy ko saboda jariran da ta bari ya kamata ki tausaya mata,Mommy don't allow me to suspect you!,kin ga tafiya ta",cewar Zahra tare da dauka jakkar ta ta fice daga falon.
    "Jama'a yau ga ikon Allah, *NI DA DIYA TA* amma ban isa nace mata yi kaza tayi ba,kya dawo ki same ni"..Daukar wayarta tayi tana murmushi, nombar Asmee tayi dialing.Bugu daya ta dauka.
   "My darling baby ya kike?",cewar Mommy tana murmusawa kamar Asmee tana gaban ta ne.
   "Wallahi I've a very good news for you"
   "Mommy wani good news bayan kullum cikin bakin ciki nike tashiwa da wannan shegen abin da ke ciki na",cewar Asmee.Mommy tasa wayan a loudspeaker saboda akwai network problem.
    "Hmm kwantar da hankalin ki 'ya ta,abokiyar gaban ki ta bata"..
   "Wa,Mami ba dai Bilkisu bah!",tace excitedly.
"Ita fah,kinga aiki yazo da sauki kenan.No need inje wajen malamin".
   Dariyar jin dadi Asmee tayi sannan tace,"kai amma Mommy you made my day da wannan sweet news din,sai nazo celebration Mommy. I love you..muaah!"..
   "OK darling,sai kinzo",sannan ta katse wayar.
   A bangaren Asmee kuma she was like,"wow Ashe Shu'uma'r nan tana wuta,aikin ta na manya neh,she did everything in such a way that babu wanda zai yi suspecting dina, dole na saka mata da wani alkhairi yanzu"..
    Mobile transfer ta shiga,tayi wa Shu'uma transfer din naira dubu dari kana ta tura mata message kamar haka.
   _Aikin ki yayi kyau,the more kina gyara min hanya,the more ina sake miki kudi yarinya..keep it up!_
   Sannan taje ta ciro champagne tayi popping harda sa disco a falo.Shi dai Ashraf zuba mata idanu yayi yana kallo saboda bai san ko menene dalilin ta nayin murna bah.Wa ya sani ma ko taci nasarar zubar da cikin shi neh.......

******

"Inna lillahi wa inna ilaihi raaji'un Mama sun sace min Bilkisu nah!",cewar Ja'afar da ya shigo babu ko sallama.
   Gaban Maman Bilkisu ya zube yana faman kuka wiwi kamar karamin yaro.
   "Wallahi yau zan kashe ko ma waye neh yake da hannu a cikin bacewar mata ta!",yace a fusace tare da mikewa ya fita.Mami suna kiran sa amma ina?ko ta kan su bai yi bah.Ji yake kamar zai iya shake koma waye yazo kusa da shi a lokacin.
   Gidan su Shu'uma ya wuce direct.Babu ko sallama ya shiga gidan,daidai tana call da mahaifin ta tana murmushi.Ganin shi da tayi a hargitse yasa ta katse call din.
    "A'a bros lafiya na gan...",kafin ta karasa maganar ya shake ta,sai bubbuga kirjin shi take yi saboda azaba amma ina idon shi yayi jaa,ji yake kamar yana da bindiga ya kade ta lahira.
    "Sai da nace mata tuban mazuru kika yi but she didn't believe me,I know you were back to destroy our relationship! Ina kika boye mata ta!"..
   Kasa magana tayi saboda yadda ya shake ta."Na ce ina take?!!!!",yace tare da cilla ta a gefe.Daidaita numfashin ta tayi sannan ta soma magana.
   "Wallahi ni ban san da komai bah game da kidnapping din ta da aka yi bah",tace tana haki saboda ya mugun shakure ta.
   Wani kuka ya sake yana fadin,"No!!! This can't be,kice min mafarki nake yi please!!,ba zan iya rayuwa babu ita bah,in kece kika boye ta ki taimaka min ki fito da ita"...
   Tausayi ya bata amma har ga Allah ita bata san da zancen bah.Kokarin taba shi tayi da niyyar lallashin shi,kamar jiran ta yake yi ya tashi ya fara fasa masu appliances yana sambatu.Shikenan fah Ja'afar ya fara hauka tuburan..
    Wayar shi ta ciro da kyar ta Kira Abba ta sanar dashi.Cikin dan kankanin lokaci Abba suka zo suka dauke shi zuwa asibiti shi da daddyn Asmee.Shu'uma kuwa sai kuka take yi,meh yasa sai da ta kusa cimma burin ta wani ya ruguza...
    Bayan awanni,likita ya fito yace musu hakuri za ayi a kai Ja'afar psychiatric hospital saboda ya kamu da cutar hauka.
   "Ya samu matsala ne a kwakwalwar sa saboda over thinking da yayi cikin dan kankanin lokaci,kuma mun gano cewar tunanin shi yana zuwa ga abu daya neh,mai yiwuwa shi wannan abun shine dalilin sa shi over thinking, kuma matsawar abinda yake so bai dawo masa bah,toh I'm afraid haka zai cigaba da rayuwa.."
   "Inna lillahi wa inna ilaihi raaji'un,Abba meh yasa zasu yi min haka?why???,wallahi koma wane ne yayi wannan abin sai naje *DAUKAR FANSA*..
   Su Abba ma basu iya cewa ko kala bah,jikin su yayi sanyi da bayanin da Dr yayi musu,ga Shu'uma kuma da ta tasa su a gaba da surutai.
   "Yawwa kuma please yana bukatar kulawa sosai a can,so Ku saman mai special ward..Zaku iya tafiya dashi..thank you",yace tare da juyawa ya wuce.
    "Daddy don Allah Ku bar ni na kula dashi,ba zan iya rayuwa babu shi bah..please".
    Ana wata ga wata,Wannan kuma wani zance take yi?.toh kawai suka ce mata sannan suka je suka biya kudin duba shi da aka yi sannan suka dauko shi zuwa mota saboda anyi masa allurar bacci.Wucewa suka yi sai *ASIBITIN MAHAUKATA*..........._*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[1/17, 8:00 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต


                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                      *36*

❤๐Ÿ’” *_I dedicate this page to you mu beloved unforgettable mum!,any moment I hear of someone's death,it breaks my heart to remember that you're gone.every time I come across your belongings,I wish time could be reversed so as to see you once again! I wished I gave you the last hug before Allah who loves you must took you away...I love you forever and ever my sweet mommah๐Ÿ˜ฐ๐Ÿ’‹_*
*_Bayan watanni bakwai

Abubuwa da dama sun faru,ciki harda auren Sameera kawar Bilkisu da abokin Ramlan,Ubaid.
    Sun hadu ne daman a wajen bikin Bilkisu inda yayi proposing dinta ita kuma ta yadda.
     Asmee kuma ciki ya tsufa,haihuwa yau ko gobe amma shiru ta kasa haihuwa sai wani azababben ciwon mara da take yi kullum.Abin yazo har ya soma ba wa Mommy da kowa ma mamaki saboda yadda cikin ya hura ta,ya maida ta kamar balan2,babu ko kyawun gani.
    Ja'afar kuwa sai abinda ya karu a ciwon tabin hankalin da ya Kama shi,kullum Shu'uma na yini neh a asibiti dashi har ya kai ga su Abba suka yanke shawarar daura masu aure da Shu'uma saboda kulawar mata yake bukata bana iyaye bah,kuma tunda sun yarda da tarbiyyar ta da kuma irin familyn da ta fito,Mami suka amince su ma.Mama da Baba ma duk sunyi murnar jin cewa za a aura wa surukin su wata mata,a daya bangren kuwa kewa da tausayin 'yar su suke yi.Kullum addu'ar su shine Allah ya bayyana masu 'Yar su.Shi mahaifin Bilkisu ma har Bp'n shi sai da ya hau saboda rashin 'ya'yan sa biyu,Bilkisu da Saleema..
    Zahra da Ramlan kuwa sun kusa kammala karatun su na jami'a.Iyayen su suka tasa su a gaba da su fidda wadda/wacce zasu aura.
    A lokacin Zahra ta aminta da abinda zuciyar ta ke raya mata,wato she's in love with Ramlan.Bata bata lokaci ba ta sanar da mahaifinta saboda karda a yi mata irin na yayar ta da Ja'afar.
      Daddy yayi murna sosai yayin da Mommy tace sam bata isa bah.Ita baza ta hada jini bah da munafukai.Sai da Daddy ya tsawata mata sannan taja bakin ta tayi shiru.
     Daddy yaje wajen Abba ya gabatar da abinda ya kawo shi.Bai nuna musu cewar Zahra tayi Mai magana bah,cewa yayi yana son su hada auren zumunci ne tsakanin 'yarshi da Ramlan amma in har Ramlan ya yarda.
    Ana kiran Ramlan aka sanar da shi,take ya yadda a wurin saboda bashi da choice.At least zai iya manejin ta tunda tana da kyau da ilimi.Nan da nan aka tsai da ranar auren su akan nan da wata uku....
   Asmee kuwa tayi bakin ciki sosai da auren Shu'uma da Ja'afar.Amma abin bai wani dame ta ba tunda Ja'afar din ma bashi da hankali kuma.Sai dai sai da ta sa Shu'uma ta biya ta dukkan kudin ta karkaf sannan ta kyale ta...


"Kissy...kissy na...uhm.uhm ni ke nake so..kinga babyn mu..yeee suna min dariya...ina kike?ki dawo,wagga tana taba ni",cewar Ja'afar da yake sambatu a kan gado yayin da Shu'uma ke goge mai jiki da ya bata garin cin abinci.
   "Yi hakuri kaji ka ci babyn Bilkisu,ba zan taba ka ba kuma",cewar Shu'uma tana share hawaye.Rayuwar Shu'uma ya matukar canzawa daga sharri zuwa alkhairi musamman da ta gane duniya ba komai ba neh.Da wani zai ce mata Ja'afar zai sami tabin hankali da ta ci kaniyar sa amma yau ga Ja'afar da take muradi amma bashi da bambanci da karamin yaro.
     "Ka san ni,ni wace ce?",tambayar da take yi masa kenan kullum with the hope that watarana zai ce eh ya gane ta amma sai dai yace,Kissy kadai ya sani. Wannan dai ake cewa *GANGAR JIKIN SA NA AURA*,ruhinshi yana tare da abar kaunar shi.
    Soyayya kenan Mai canza bawa.Ji yadda soyayya ta canza Shu'uma farat daya.Dukkan koman ta ta basar saboda soyayyar Ja'afar da ke dawainiya da zuciyar ta,bata damu da tabin hankalin ba.Ita dai addu'ar ta a kullum Allah ya bayyanar da Bilkisu domin ta san matsayin ta saboda ta san muddin Ja'afar ya warke to zai sake ta ne saboda ta san da yana da lafiya ba zai taba yadda ya aure ta bah..Amma Allah ya zaba mata mafi alkhairi shine addu'ar ta..
    Yau ma kamar kullum dakin Bilkisu ta shiga.Tana 'en neme nemen ta ko zata ga wani abu Mai muhimmanci ma shi da Bilkisu ta kai meh ko zai dawo hayyacin sa.
    Tana cikin duba wardrobe kawai rose flower'n data taba hada masa tana ss2 ya fado.Da sauri ta dauka ta duba,sai ta ga an rubuta,'from Bilkisu to my lovely bro,Ja'afar',dadi taji at least ta samu wani abu da zata kai Mai yau saboda ita a zaton ta ya san da flower'n.
    Duk kamshin sa ya Kama mata hannu.Dakin da Ja'afar yake ta shiga ta ganshi ya kura wa hoton Bilkisu idanu kamar yadda ya saba. Kuma su Mami sai da suka hana Shu'uma ajiye masa hoton amma ya ta iya,she can't watch her love and her hubby suffer,shiyasa take ajiye Mai abinda yake sa shi nishadi.
    Zuwa tayi ta bashi tana cewa,
  "Inji kissy tace a baka"
Mikewa yayi zumbur ya karba yana sambatu yana kissing fulawar,kuka neh ya kubce wa Shu'uma ta ruga falo da gudu tana ta kuka.
    Yanzu haka rayuwar ta zaya kare idan har Bilkisu bata dawo bah,gashi tana matukar son Ja'afar da zata iya rasa ran ta idan har ta rabu da shi.Kwata kwata ta rasa *TUDUN DAFA WA*,ni kam nace ki dafa tudun hakuri da tawakkali da ubangijin ki,baza ki taba tabewa ba....
     

*****

Wasa wasa cikin Asmee ya shiga wata goma amma shiru babu haihuwa babu dalilin sa.
   Hankalin ta da na Mommy in yayi dubu ya tashi,anje asibitoci amma suka ce sam su basu ga wani cuta tattare da ita bah,lafiyar ta kalau.
   Nan Mommy ta yanke shawara komawa wajen bokan da yayi musu aiki.Tana isa ya hau ta da fada,ya za ayi ta kwana da wanda bashi ne aka yi mata magani saboda shi bah.
   Yace sanadiyyar barin Ashraf da tayi neh ya kwana da ita ya jawo hakan don haka dole a kwance asirin da tayi wa Ashraf idan dai ana son ta haihu nan ba da dadewa bah.
    Kiran Asmee tayi a waya ta sanar da ita.Nan Asmee ta shiga rabka uban kuka,babu yadda ta iya dolen ta ta cewa Mommy a kwance asirin.Duk hankalin ta ya tashi saboda azabar ciwon da take ji da kuma yadda Ashraf zai kalle ta idan ya warke.
   Mommy tana gayawa boka abinda Asmee tace,nan da nan yayi wasu tsafe tsafe ya ciro gaban kaza ya barbada mata abu sannan ya yanka ta ya cillar.
    Daidai yana cillarwa,Ashraf yana zaune a falo yayi tagumi,ya rasa mai ke damun sa,sai ji kawai yayi kansa yana juyawa,sai tim!! Kake ji,ya fadi sumamme a kasa.
    Asmee kuma tana daki,daidai lokacin da ya sume,ruwan haihuwar ta ya fashe,nan fa ta fara jin wani sabon azaba,wayar ta ta dauka ta Kira mahaifiyar ta.Cikin minti talatin ta iso gidan.Ko ta kan Ashraf bata yi bah,in ban da Zahra da ta yayyafa mai ruwa tana mamakin yadda aka yi ya sume.
    Yana mikewa,ya tambaye ta ina Asmee? Nan ta sanar dashi yanzu suka fita waje da Mommy tana nakuda,"nakuda"?,ya maimata zancen disbelievingly.
   Dakin shi ya shiga,ya fara Neman key na mota,da kyar ya gani ya fito daidai mommy tana fita da motar ta,motarshi Zahra ta shiga suka bisu a baya....********

"Allahummak fi ni him bima shi'eta",shine naji wata tana maimaitawa.Juyawan da zanyi na hangi Bilkisu rakube a gefen gadon wani lafiyayyen daki.Sai kuka take yi tana addu'a,tayi kashi kashi da ita.
   "Ke dalla can,gwara ma kin daina kuka,ace mutum watannin sa takwas da barin gida amma har yau kin ki sakin jikin ki da ni",cewar wani da yake tsaye ya juya baya ta bangaren da na labe.
   "Meh nayi maka, meh nayi ma da ka raba ni da 'yan Uwa na har watanni takwas,ka raba ni da 'ya'ya na,ka raba ni da hasken rayuwa ta",ta karasa maganar tana kuka Mai tsuma rai.
    Tunda aka sace Bilkisu, sai yau ta farfado saboda karfin maganin da aka yi mata using dashi.Anyi mata allurar da zata yi losing memory na ta amma ina da alamar basu ci riba ba koh tunda tana tuna gida still.
   "Tunda na kusance ki kina budurwa na rasa sukuni har wayau,shiyasa na sha alwashin mai dake nawa komi daren dadewa...so,ki cira rai daga ganin su,saboda baza ki taba komawa gare su ba!!"....
_*'Yar autan mama Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[1/21, 9:13 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต

                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                      *37*
*~Sadaukarwa ga Bily Galadanchi's novels~*

Asmee ta haifi santaleliyar 'yar ta wacce tayi Kama da hajiyar Ashraf.
   Yarinyar ta matukar shigan ran ta amma saboda shaidananci irin na Asmee,ko daukar yarinyar ta ki yi.
   A cewar ta,da babyn Ja'afar ce ta haifa da zata shayar da ita tana Mai murna,amma wannan bad luck din(kamar badluck din naufal@NI DA DIYATA),ta rugurguza mata plan din ta.
    Mommy ma da yake jirgin ta daya da diyar ta,haka ta karbi jaririyar kamar kashi tana kallo.
  Amma can karkashin zuciyar ta,jaririyar ta mata kyau.Waya ta dauka tayi dialing nombar Ashraf tace su shigo.
    Shi da Zahra suka shigo.Sai wani biribiri yake yi,suna shigowa gaga Mommy da baby a hannun ta,tana kuka.
   Mika mai yarinyar tayi.ihun murna yayi yana hawaye a lokaci daya.
   "Alhamdulillah, alhamdulillah, Alham..." 
   "Kai ja can,ba hamdalar ka muke so ba,ka wani zo ka cika mana kunne",cewar mommy yayin da take katse shi daga yin hamdala.
   Juyowa yayi ya kalli Mommy da mamaki karara a fuskar sa,ita kuwa ta murtuke fuska kamar wacce aka kawo wa sakon mutuwa.
   Jikin Zahra yayi sanyi saboda abinda Mommy tayi wa Ashraf amma sai ta dake kawai,taje kusa dashi ta karbi yarinyar.
   "Masha Allah, tabarakallah,yarinya kyakkyawa haka,kamannin ta sak dana hajiyar ka.."
   "Ba dole ba,mugun jini ai daman karfi gare shi,jaririya sai kace..."
   "Haba Mommy ni fa ban son haka,ai a hakan mahaifanta suke son kayan su,ko sister? Karbe ta ta shaa nono"..
   "Wallahi in kika kuskura kika kawo annobar nan kusa da ni wallahi sai na...."
   "Ya isa! Na ce ya isa!, Zahra mika min 'ya ta in yi mata huduba,kuma nonon nan sai Kin bata ta sha",cewar Ashraf a harzuke.
    "Eh,lallai yaro ka samu wuri,har a gaba na zaka ce dole 'ya ta,ta shayar da 'yar ka,toh baza ta shayar ba,nace baza ta shayar din bah banza shashasha!"
    Ko Kala bai ce mata ba,sai da ya gama yi wa 'yar sa huduba sannan yaje gaban Asmee ya tsaya yana mika mata Rahma(sunar da yayi mata huduba dashi kenan).
    Juyawa tayi kamar bata san abinda yake nufi bah.Dago ta yayi da hannu daya, ya watsa mata harara.
    "Karbe ta ki shayar da ita nace",yace yana mika mata yarinyar.ya kai koluluwa wajen bacin rai,ji yake kamar ya shake ta.
    Shi fa koman wulakancin da zata yi Mai,bai damu bah amma karda tayi wa 'yar shi.
    "Oh wato Kama raina ni,nace baza ta shayar da ita bah amma kai sarkin rawan kai kaje kana wani zazzare mata idanu..kai ka shayar da ita mana!" 
    "Mommy babu ruwan ki a zancen nan,she's my wife.I'm talking to her not you!"
   "Cabdi to zan ga yadda za ayi ta shayar da yarinyar nan,dan iska kawai",tace tare da karasawa gefen Asmee ta zauna.
     Ji yayi kamar yayi kuka tsabagen haushin da yake ji.Ficewa yayi daga dakin a fusace da jaririyar a hannun shi.
   Kokarin bin shi Zahra tayi amma Mommy ta hana ta.Zahra kuwa in ban da haushin Mommy da Asmee da take ji,ba abinda ke ran ta.Tsaki tayi ta zauna.
    Ashraf yana fita,nurses suka fara tambayar sa lafiya amma ko amsa su bai yi bah,ya shige motar sa.Bai zarce ko ina bah sai gidan hajiyar sa.
   Kallon kallo suka yi tukun kafin ya karasa kusa da ita ya ajiye mata babyn.Hawaye ne ya gangaro kan fuskar ta,tana tunanin anya is this real?.
   Shi kuma yana ganin haka,yace Mama ni ne Ashraf din ki,wannan kuma jikar ki ce.Shi a ganin shi kamar ya kwashi shekaru bai ga mamar sa ba,kila shiyasa take kallon sa haka nan.
   "Tabbas yanzu na Kara yarda cewa sihiri ne ke ta dawainiya da kai,nayi rashin ka d'ana,ji bi duk yadda na rame",tace tana kallon jikin ta.
   Hawaye neh ya gangaro masa shima.Ya sauko daga kushin ya zauna a kasa yana share mata hawaye dake zuba kan kuncin ta.
   "Yanzu wannan jaririyar ce jika ta?,Allah Mai iko,babu yadda Asama'u bata yi bah don ta zubar da cikin ga, har gida na tazo ta ci min mutunci,sai gashi da ikon Allah sai da ta haifo ta..ina bakin ciki da wannan yarinyar da ta kasance matar ka Asharaf".
   "Mama wallahi ban san da cewan tayi miki hakan nan ba amma sai na gyara mata zama wallahi..."
   "A'a ka bita a hankali d'a na,Allah ya kare min kai",tace tare da kai duban ta zuwa ga jaririyar.Murmushi tayi kana tace dashi,
  "Sai na ga kamar da ni yarinyar ga tayi Kama da"
    "Nima hakan na gani,yawwa Mama dama na kawo miki ita neh don ki kula da ita.....",nan ya zayyana mata dukka rashin mutuncin da suka yi masa a asibiti.
   Mama kuwa sai Allah wadai take ta cewa da halin su.Anya lafiyar Asma'u,ace 'yar da kika haifa amma kinki ko da shayar da yarinyar neh,Allah shi kyauta.
  "Toh shikenan in shaa Allah ni zan kula da ita har lokacin da Allah zai baka wata mace ta gari ka aura".
   "Ameen",yace sannan ya fada mata zai kawo kayan baby anjima,dasu madara,kafin su fara tsare tsaren suna!.....

***********
Shu'uma ce zaune a kan bedside drawer na gadon Ja'afar.Kallon shi take yi cike da so da tausayawa.
    A yau ma yana kwance a kan gado yana surutan sa kan Bilkisu as usual.
    Wani sa'in ya kan dawo hayyacin sa,yayi shiru yana kallon ta. Amma yau da ganin shi,ka san abubuwan suna kan sa.
    Sallamar su Mami da Momma ta ji.Da sauri2 taje ta bude kofan tayi masu sannu da zuwa tare da karban Abba karami daga hannun Momma.
    "Ya kike,ya dawainiya da marar lafiya?",cewar Mami.
   "Toh,alhamdulillah".
    "Allah ya ba shi lafiya,Allah kuma ya biya ki my daughter,bamu san ko da meh zamu saka miki bah sai dai muyi miki fatan alkhairi",cewar Mami.
    "Ameen nagode,bismillah muje daga ciki Ku gan shi".Mikewa suka yi suka shiga dakin.Arba suka yi da kayan Bilkisu kala2 a kasa,da turarukan ta,hoton ta da sauran su.
   Gashi sai sambatu yake yi,yana faman cewa, "Bilkisu ce?,yawwa miko min Sultee junior..hihi kinga yana murmushi koh..uh..uhm ni shi zan dauka,haba kissy na..."ya karasa maganar yana wani juya idanu.
    Kallon Shu'uma Mami tayi,haba wa kamar jira take Mami ta kalle ta,ta fashe da kuka ta ruga falo.
    Duk jikin su Mami yayi sanyi su ma.Wannan wani irin musiba ce?a ce ga matar ka a gaban ka,amma hankalin ka yana wajen wacce ta bace, ba a ma san ko tana raye bah.
    Sun ga ma kokarin ta da ta iya auren shi kuma ta yadda ta zauna dashi a cikin halin nan.Tabbas da bata son shi da baza ta iya zama dashi har tana kawo Mai kayan abokiyar zaman ta ba,ko don bala'in kishi da mata suke da.
    Falo suka bita, tana zaune a kushin sai faman zubar da hawaye take yi.Zama Momma tayi kusa da ita ta rungumo ta,ta soma lallashin ta..tana yi tana bata baki har tayi bacci.
   Allah sarki,abinka da wacce bata bacci,sai da ta sha baccin ta sosai kafin ta tashi lokacin sallar magriba yayi.
    Rabon ta da ta yi irin bacci Mai dadi haka,tun tana gidan baban ta,kafin ta aure Ja'afar..Sai bayan magrib Mami suka wuce lokacin su Abba karami sunyi bacci,sun sha wasa sosai da rana.... 

*******

"Waya na kika dauka koh?",cewar wani gardi yayin da yake nufar inda Bilkisu ta ke.
    Kuka ta fara yi tana rokar sa da yayi hakuri amma yana kaiwa gaban ta,ya dauke ta da mari sannan ya d'are kan ta........

*sorry for this page,please bear with me,ban ji dadi ba neh yau,kuma na dau alkawarin turowa yau neh,so zaku ga pg din nan wani iri.wish myself a quick recovery in shaa Allah..*

   
  

_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[1/24, 9:17 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ©ExีฆสŠษจsษจtษ› OีผสŸษจีผษ› Wส€ษจtษ›ส€s
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต

                     Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                      *38*

  D'are wa yayi a kan ta.Tana ihu tana kuka,tana rokan sa amma yayi mata kunnen shegu.
   Barka mata rigar ta yayi.Ita kuma sai kuka take yi tana ja masa Allah ya isa.
    Sai da ya lallasa ta son ran shi ya mike domin karasa tubewa.A lokacin dukkan jikin ta yayi weak.
    Ita ba ma tsoron abin ta ke ji bah,a'a tsoron Allah ne ke dawainiya da ran ta,ya za ayi tana matar aure wani gardi Dan iska zai kusance ta.
     Mafita ta fara nema,can ta hango wani kwalba da ke gefen gadon,Tana yunkurin mikewa sai ji tayi ya kuma danne ta...
    Ihu ta fara yi tana yi masa magiya.
   "Wayyo don Allah kayi min rai,ni fa matar aure ce,meh yasa ba Ku da imani?"tace tare da Kara sautin kukan ta.
    Shi kuwa gardin ko a jikin shi,shi dai ya matsu ya ji kan shi a cikin ta.
    Yana kusa da afka mata kenan,sai ji kake "gbushh!",karan naushi.Da sauri ya dago saboda ya ji zafin naushin sosai.
    Wani kukan kura dayan gardin yayi ya finciko shi daga jikin ta.Tuni ya fara jibgar sa.
   Bilkisu tana ganin haka ta fara mustering courage da za ta mike.Sai da ta jero addu'oi ta dan ji karfi ta mike.
    "Dan Tasha kawai,wallahi yau zamu ci kutumar uban juna,daman ina Lura da take taken ka,tun ranar da nace zan dandana ta,naga ka fara wasu games...toh yau ko ni ko kai?"..
     "Har kai waye da zaka mola ta kai kadai,yau sai na aika ka lahira saboda ba tun yau ba kake shiga sabgata!"
     Suna cacan baki suna kai wa juna duka har Bilkisu ta samu ta dauki kwalbar ta ruga a guje,da yake kofar a bude yake.
    Tana rugawa hankalin su ya dawo jikin su...
   "Wallahi,idan ta gudu,na san sai oga ya aika mu lahira,duk kai ka jawo mana",cewar gardu na farko.
    Bin ta suka yi a guje,can suka hango ta ta kusa kaiwa corridor da zai fitar da ita tsakar gidan..
    Kara guru suka yi har suka kamo ta dai2 tana shirin sauka daga lungun da ta fito.
    Juyowa tayi tana haki,tana kuka."wallahi in kun zo kusa Dani sai na kashe kai na,ko na kashe ku mugaye kawai marasa imani"
    "Duk abinda kike fadi ba zai yi tasiri a zuciyar mu ba yarinya,ki dai ajiye abin wasan nan na hannun ki saboda ko kadan bai firgitar da mu ba",cewar gardi1.
    "Karda Ku kuskura Ku matso",cewar Bilkisu tana kuka yayin da suke karasowa wurin ta suna dariya.
    Buga kwalbar tayi a kasa sannan ta rike sharp place din.Daidai2 suna karasowa.
   Rufe idanu tayi ta caka wa gardi1 a gefen cikin sa.Wani irin ihu yayi ya rike wurin.
    Tana ganin haka ta juya wurin dayan shima ta bashi rabon shi a ciki shi ma.Tana yi tana kyarma duk gumi ya keto mata.
    Yar da kwalbar tayi ta ruga hanyat gate a guje,tana isa tasa hannu a handle tana turawa,amma yaki bude wa.
   Buga kofar ta soma yi da karfi da ta ga gardi1 ya nufo ta yana kyalkyala wani irin dariya Mai firgitarwa.A take ta sake wani irin fitsari..(irin fitsarin tashin hankalin nan)!***********

Yau dai Ja'afar ya tashi cikin wani irin yanayi neh.Duk ya zama abin tausayi,yayi wani iri da shi.
   A gefen shi kuma Shu'uma ce zaune tana shafa Mai kai kaman karamin yaro.Tunani kala2 take yi.Daga cikin tunanin shi ne,Anya Ja'afar zai yarda da ita bayan ya warke bayan ya san halayyar ta na da?! Ni kam nace amsar tambayar ki sai ma'aiki.
      Suna a haka ne taji yana magana a hankali.sunan Bilkisu yake furtawa as usual. Goge hawayen ta tayi,tana kallon shi.Wannan wani irin rayuwa ce?
    Haka zan karasa rayuwa babu farinciki?ko da yake wani farin ciki nike bukata da yafi na ga kaina da bawan Allah'n ga rumfa daya na raya sunnar ma'aiki?..  
    Haka dai take ta sake sake har bacci barawo ya sace ta....


************

Asmee ce kwance duk abin duniya ya ishe ta.Kullum itace cikin zafin mama, kan Maman ta ya dinga yi mata ciwo.
    Ta sha magani har ta gaji da sha.Ashraf kuwa ya canza kwata2.In bai jibge ta da safe ba toh zai yi da rana ko kuma da dare.
    A bangaren Ashraf kuwa yana matukar son Asmee amma da ya tuna irin cin mutuncin da suka yi mai da mahaifiyar ta, sai ya ji haushi matuka.
     Baya sanin lokacin da yake hawan ta da duka.Wani sa'in kuma fyade yake mata idan ya nema biyan bukatar sa ta ki.
   Duk duniya ya juya mata upside down cikin kwanaki.Mommyn ta da ke goya mata baya ma ba ta,saboda tun da Zahra ta gaya wa mahaifin su abinda ya faru,ya Kira ita da Asmee ya ci masu mutunci.
       Tun ranar ta cire hannun ta a harkan ta.Kuma daddy ya kai ta gidan su Mami ta roke su gafara.Abin yayi wa Zahra dadi sosai,ta zamo kullum da ta dawo daga makaranta,dakin mommy ne first place da take xuwa.
      Tare suke shiga kasuwa domin yin siyayyar bikin 'yar auta.Ko da Zahra tayi zancen Asmee sai mommy tace ba ruwan ta,da Zahra kadai zata kasuwa...
    Toh Asmee dai idan tana da hankali ya kamata ta tuba saboda taga rayuwa cikin 'yan kwanakin nan bare ma kuma idan ta mutu.Bata da kowa sai kuka,kuka kadai ke debe mata kewa.
    Har Zahra ma Daddy ya hana ta zuwa wajen Asmee a cewar sa horo yake mata don ta shiga taitayin ta....


*******

"Haba lami wai ke kullum cikin kuka iyye? Ince kukan dai bai dawo da ita ba,ai addu'a kadai take bukata a duk inda take",cewar baba.
   "Haba mallam yaya ba zan yi kuka bah,ita ce 'ya daya tilo a gare ni,yaushe2 muka san juna da ita,amma wasu azzalumai sun raba NI DA DIYA TA(na Ayna'u Dimples)kuma kuma...",kasa karasa maganar tayi saboda kukan da yaci karfin ta.
    Duk jikin baba ya sanyi amma yaya zai yi.Tabbas shi yafi mama jin rashin Bilkisu saboda ita ta rage Mai tunda bai san inda Umma da Bilkisu suke bah amma sai dai ya mika Kukar sa ga Allah, shine Mai maganin komai.
    Maganar mama ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya shiga..
    "Duk kai ka jawo abin nan.uhm..ace yarinya tunda take karama ba ka taba yi mata bakin alkhairi ba sai na sharri,gashi yanzu a lokacin da kake bukatar ta, Allah ya jarrabce ka saboda mugun bakin da kake tayi mata ne..."...
     "Ki daina maganar nan Lami,na san nayi kuskure am a bisa ga rashin sani ne,yanzu ina nadamar abubuwan da nayi mata a baya....",kasa karasa maganar yayi saboda wani yanayin da ya tsinci kanshi a ciki,mikewa yayi ya wuce daki yana share kwalla.
   Mama tana ganin haka,jikin ta yayi sanyi,ta dau maganar da zafi da yawa, amma ya za tayi dole taji haushi saboda a tunanin ta shi ne sanadiyyar faruwar hakan ga 'yar su.
     Mikewa tayi jiki a sanyaye ta je daki domin ta bashi hakuri a kan yadda tayi mai magana....


*********
Ramlan na hango zaune a gindin bishiya da abokin sa Rayyan.Tunani yake yi sosai saboda bai ma san da zaman Rayyan a wurin ba.
    Tunanin irin abubuwan da yake ta aikatawa a da yake yi.Ga wannan case din batar Bilkisu, ga haukar da Dan uwan sa yayi.
   Duk abubuwa sun bi sun cude mai.. A da ya tuhume Shu'uma sosai gami da batar Bilkisu amma daga baya ya gano wanda yake da hannu a abin ba daya daga cikin su ba neh.
   Taba shi Rayyan yayi,firgigit ya dago ya kalle shi,babu yadda Rayyan bai yi dashi da ya gaya mai abinda ke damun sa ba amma yace ba komai.
    Karshe ya tashi ya sallami Rayyan ya shige keke napep sai gidan da yake renting...
     Yana cikin tunani ne zahrata bugo,murmushi yayi ya dauka.Daga nan suka fada login soyayya......


*Ni dai sai munzo shan Biki๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ**Next page*

*Dama kai ne kake da hannu a case din nan?,Allah ya isa!!!*๐Ÿ˜ณ

*wayyo meh tayi maka?? What did she  do to you to deserve this??!! I hate you!*๐Ÿ˜ฃ


_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[1/25, 8:24 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ©ExีฆสŠษจsษจtษ› OีผสŸษจีผษ› Wส€ษจtษ›ส€s
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต

                     Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                      *39*

     *SECOND TO THE LAST PAGE*
     *~In dedication to Dimple's novels~*"Yawwa anjima ina son muje gidan su Bilkisu kuma,ko an ji labarin ta",cewar Sameera.
   "Uhm..toh..babu komai anjima sai ki shirya mu je my baby",cewar Ubaid,mijin Sameera.
     Mikewa tayi ta shiga kicin domin zubo Mai peppered fish da tayi hade da kunun aya Mai sanyi.
    Wayar sa da ke kan center table ya fara ruri.Da sauri ya daga call din kamar Mara gaskiya,yana amsawa yana waige2.
   "Gani nan zuwa",shine abinda ya furta kafin ya shige daki.Fitowa yayi dai2 Sameera tana fitowa daga kicin.
    "Hun ina zaka je bayan gashi na debo ma abin motsa baki",ta ce fuska a marairaice.
  "Sorry durling,yanzu zan je na dawo,it's urgent shiyasa",yace yana gyara hular sa.
   "Toh wajen wa za ka tunda na san ba a fara batun NYSC din Ku ba koh?"..
   "Uh..uhm ke dai sai ns dawo",yace tare da ficewa daga falon da sauri domin gudun karda ta tambaye sa kuma.
   "Anya kuwa,wannan yana da gaskiya??",tace zuciyarta cike da zargi.Tun kafin auren su,ta lura da shi,kullum cikin waya ko kuma yin abu da za ayi suspecting din sa.
     Da gudu ta shiga daki ta kwaso hijabi ta sa,ta na fitowa dai2 ya tada mota yana fita daga gidan.
    "Hun zan bika",tace a shagwabance.
  "Yanzu ba time na wasa ba ne,nace I'll be back soon,wani muhimmin abu ke son kubuce min,I need to go",yace tare da daga glass din motar sa,ya wuce.
   "Ai kuwa sai na bi ka wallahi",tace tare da rufe kofar falon,ta fita a guje...
     Tana fita ta hangi wani Mai keke napep yana ba wa wata canji,da sassarfa ta karasa wajen shi.
    Ko explanation bata tsaya yi mai ba,kawai cewa tayi da shi ya bi motar can da ta wuce zata bashi ko nawa ne yake so.
   Abinka da mai neman kudi Ido rufe,nan da nan ya yarda,ya ja keke sai hanyar da Ubaid ya bi......

*******

"Don Allah don son annabi na tuba,ka yafe ni miji na",cewar Asmee da ke durkushe kan guiwar ta bibbiyu tana rokan Ashraf da ya gama jibgar ta.
     Wayar sa ya cigaba da latsawa kamar ba da shi take yi ba,asali ma haushin ta yake ji.Kullum kenan sai yaje restaurant ya siya abinci saboda abincin ta kamar a wanke kan tsohuwa.
     Yau ma stew da ta hada ba shi da bambanci da dayyan tumatirin gwangwani.Kuma gashi ya kwaso yunwa daga office,ya samu aiki a wani private school inda yake koyarwa for the main time.
      "Please na tuba ka yafe min, Allah zan je na koya yadda ake abinci just for you",tace tare da rike kafafun sa.
   Mikewa yayi ya shure ta sannan ya fice daga gidan zuciyar sa tana masa radadi,in ba haka yayi mata ba,ba za ta bar shi ya ji sakat ba.
    Gidan hajiyar sa ya nufa.Yana shiga ya tarar da ita tana ba wa Rahma madara tana murmushi.
   Shima murmushin yayi ya zauna a kujera,ya gaida ta cike da girmamawa.Da fara'ar ta ta amsa sannan ta mika masa jaririyar.
    "Ga ta nan sai shusshure ni take yi,ya Mai dakin ka?"..
    "Um..um..Tana lafiya",cewar Ashraf yayin da yake sosa keya.
   "Kai yaron nan,ka ji tsoron Allah, har ni mahaifiyar ka zaka yi wa karya,wato har yau baka yafe wa yarinyar nan ba duk da nace maka na yafe mata",cewar mama a fusace.
   "Ki yi hakuri mama, nan ba da dade..."
    "Yi min shiru dalla,yau din nan zaka sauya halin ka,dan ni Ashraf dina ba mugu ba ne,abinci ne kace bata iya ba,ka kai ta inda za a koya mata mana'..
   "Toh naji Mama zanyi in shaa Allah, kiyi hakuri..Nima shaidan ke zugani shiyasa,in ba haka ba ta shiga hankalin ta sosai".
    "Toh shikenan,Allah shi yi maka albarka,ya Kara shiryar da ita"..........

******

"Yeeey Momma zo kiga angon ki zaman sa ya fara nuna,ya raga Sultee na",cewar mahneerah da take wasa da twins.
    Dariya Momma tayi tace "ai dole ango na baya daukan last",cewar Momma.
    "Ni kuma dana ya dai ba Ku chance ne,if not kowa ya san Sultan dina jarumi neh,Dan Lele na ",cewar Mami da ke fitowa daga daki tana murmushi.
    "Yawwa Mami na ki gaya mata,our Sultee is always the best",sannan tayi shiru da ta tuno Sultee din ta.Hawaye ne ya cika a idon ta haka ma Mami.
    Lallai sun shiga wani yanayi cikin Dan kankanin lokaci amma sun yarda da kaddara kuma sun yi imani cewa Allah zai sawwaka masu komai.
    Tusa Sultee yayi mai kara,abin sai ya basu dariya sosai.
    "Kai Mami kin ji yadda Abba karami ya sake algaita",cewar mahneerah tana dariya.
    "A'a karda kiyi wa miji na sharri,ba wanin nan,na san junior yayi",cewar Momma .
    Dariya suka yi gabadaya dai2 Abba yana shigowa.Wuri ya samu ya zauna suka y masa sannu da zuwa yayin da mahneerah taje kicin ta dauko mai juice Mai sanyi da Kofi.
    "Yawwa mahneerah ta,sannu",yace tare da bude drink din.
    "Ya naga kuna ta dariya ne?",cewar Abba yayin da ya kai kofin juice a bakin shi.
   "Wallahi Abba mutumin ka neh ya yi burrrrnet",cewar mahneerah tana dariya tana kallon yadda Momma tayi kicin2 da fuska.
    "Toh mahneerah mene ne burrrnet kuma?"
   "Wai fa Sultan junior ne yayi tusa shine suke lakawa maigida na",dariya Abba yayi sannan yace,
   "Ni dai na san aboki na baya yi".
"Hehhe Abba waye kuma abokin naka"..
    "Ba sai kun sani ba,yawwa Ramlan wai yana nan dawowa yau".
    "Toh Allah ya dawo da shi lafiya",cewar Mami da Momma..
    Haka suka kasance cikin nishadi abin su.tun bayan bacewar Bilkisu suka rasa walwala.Karshe dai addu'a suka yi cewa Allah ya bayyana ta ko da ran ta,ko babu sannan suka watse daga falon...******

"Wayyo na shiga uku,Inna lillahi wa Inna ilaihi raaji'un",cewar Bilkisu yayin da take bubbuga gate da karfi,gashi gardin yaja daf da Kama ta.
    Tana kokarin bugawa ne kuma,kofan ya budu,ji tayi an buge ta tim, har sai da ta fadi a kasa saboda gravity din dukar.
    Mantawa yayi bai rufe gate din ba saboda tsananin rudu.Shi da yake ganin ya kusa cimma burin sa shine take son ta kawo mai cikas.
    Kukan kura yayi ya hau kan ta.Sai ihu take yi tana rokan sa,yana daf da sa mata cello tape a baki shine aka hankado kofar gate din..
    "Ubaid?!!! Bilkisu??!!",cewar Sameera cike da mamaki karara a fuskar sa.
   Dagowa yayi a hankali yana kallon ta.Bilkisu na ganin hankalin sa bai wurin ta,ta lalubo kwalbar ta inda ta bar ta saboda gardawan sun shige ciki bisa ga umarnin shi.
    Marin Sameera yayi a zuciye.."ba nace miki karda ki biyo ni ba wato saboda ke ga ki karamar 'yar iska shine kika biyo ni ko?".
   "Ubaid daman kai ka sace Bilkisu?",cewar Sameera yayinda hawaye yake gangarowa akan kuncin ta.
     Fizgo ta ciki yayi yana huci ya rufe gate din.Wani mari ya kai mata kuma,ya hau ta da duka.
   A lokacin Bilkisu ta samu ta dauki kwalbar ta nufi kofar corridor din tayi locking da key,sannan ta cire key din ta cillar.
     Karar key din ya dawo da shi ta bangaren ta.Gadan2 ya nufo ta,bai lura da kwalbar da ke hannun ta bah.
    Yana zuwa ta buga mai shi a kai da dukkan karfin ta,sannan ta fara ja da baya ganin ya rike kan sa alamar kan yana juya mai,sai zubewa yayj a kasa yana gurnani.
    Kasa motsawa Bilkisu tayi,duk hankalin ta in yayi dubu ya tashi.
   A hankali Sameera ta mike saboda ta jibgu itama sosai,jikin ta duk yayi weak.A hankali ta karaso ta ja hannun Bilkisu sannan ta dan fara sauri2.
   Daidai wajen gate din suka tsaya,kofan a rufe yake.A rude Sameera ta juya ta koma wajen Ubaid domin zaro key daga aljihun sa.
    Still yana rike da kan sa.Hannu tasa tana zaro key din taci sa'a kuwa yana kusa.Har ta cire zata juya ya sa mata kafa ta fadi a wurin key din ya fadi.
   Hankalin Bilkisu ya Kara tashi gashi gardawan suna ta kokarin bude kofa...
    Karasawa tayi ta fara Neman key din yayin da Sameera ke kokarin kwace kan ta..
   "Bilkisu ki ta wuce wa,I'll be fine!",tace tana kuka amma sam juyowa Bilkisu tayi ta wurin ta,ta fara jan ta,ai kuwa tayi sa'a ta janye ta.
    Daga ta tayi da kyar saboda dukkan su,sun galabaita.Gashi gardawan sai Kara buga kofar suke yi...
    Suna kaiwa gate suka bude,fitowa suka yi don tsananin rudewa basu rufe gate din ba sai ma yadda key da suka yi.
    Hanyar empty babu mutane kan hanyar saboda wurin bayan gari ne.Wayar ta ta zaro ta fara neman nombar Zahra saboda ita kadai take tsammanin zata taimaka ta,gashi Bilkisu ta fara aman jini.
    Ta Kira sau daya, sau biyu,amma ba a dauka bah.Karshe ma taji wayar a kashe.
    Hankalin ta bai gama tashiwa ba sai da ta hango gardawan nan sun fito daga gidan suna neman su.Rike juna suka yi gagam suna gudu suna waigawa yayin da Sameera kuma take kokarin kiran layin 'yan gidan su.
    Waigawan da zasu yi suka ga gardawan nan na zuwa a guje har sun kusa kamo su.Kara dialing nombar baban ta tayi amma sai wayar ta ya dauke saboda cajin ya kare...*Toh fah!!...Ana yin ta!!...Ku biyo ni a last page don jin yadda za a kaya... Zasu tsira ko dai mutuwar su ta zo kenan? Shin Ja'afar zai samu sauki ko dai haka zai cigaba da kasancewa har karshen rayuwar sa...Ku biyo ni don samun amsoshin wannan tambayoyin*
    
    _*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
[1/28, 9:11 PM] Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜: ©ExีฆสŠษจsษจtษ› OีผสŸษจีผษ› Wส€ษจtษ›ส€s
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต
   ๐Ÿƒ๐Ÿป *TUDUN DAFAWA*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต๐ŸŒต

                  Na
                   
           Ummiee Ja'afar๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป๐Ÿ™‹๐Ÿป  
                      *40*

*~Sadaukarwa ga Xaษฆส€a aีผษ– Uสสษจษ›ษ›สaaส„aส€ novels~*

       *Sษฆaส„i ีผa ากaส€sษฆษ› (tษฆษ› ส€ษ›tสŠส€ีผ ึ…ส„ BษจสŸากษจsสŠ!)*

"Zahra ina kike?,wayar ki yana ta ruri tun dazu",cewar Mommy da ke duba zannuwan da suka siyo daga kasuwa.
   "Bari na duba naga ko waye",cewar Zahra yayin da take karasowa ta inda Mommy ta zauna.
    "Oh Sameera ce! Kila zata zo ne shiyasa ta kira,bari na Kira ta"..Shigowar call din Sameera neh ya katse ta kuma.
    Tana dai2 da daga wayar,wayar ta mutu sanadiyyar rashin caji.
    "Yaa salaam!,gashi wayar ta mutu".
   "Ai daman ke in akwai wuta baki cajin waya, sai ya mutu kiyi tsuru2 da idanu,yanzu in ma zuwa za ta yi,ta ya zaki San time da zata zo har kiyi mata tanadin abinci?".
    "No problem ai Mommy,ita ma 'yar gida ce,ko ta zo,ita zata girka da kan ta coz I'm so tired",inji Zahra sannan ta kishingide a kujera tana kallon zannuwan da Mommy ke jera mata a akwati.
     Ita har ga Allah zuciyar ta bai raya mata komai ba game da kiran da Sameera tayi mata bah,so bata damu ta ara wayar Mommy ta Kira ta bah.
    Haka suka cigaba da hira da Mommy har bacci barawo ya sace ta...

********

"Wa nike gani kamar yaya jummai??",cewar Fatima (kawar Bilkisu da tayi aure).
    "Ni ce Fatima",cewar Jumy tana share hawaye daga kan lotsatsen kumatun ta,duk kamannin ta ya canza.
    "Ikon Allah,yaya ina kika shiga tun shekara da shekaru,dukka hankalin kowa ya tashi,tun muna tunawa da ke har muka so muka manta da ke,yaya meh ya same ki haka kuma ya kika gane gida na?"..
   "Haba ki bani waje na zauna mana,sai jero min tambayoyi kike ta yi",cewar Jumy da ke rike da kwankwason ta dake mata ciwo.
     Matsawa tayi daga bakin kofar,Jumy ta shigo.Ta nuna mata wurin zama.
    Gidan Fatima dan karami ne madaidaici babu laifi.Daga falo mai dan girma sai daki biyu da kicin da bathroom.Kuma gidan kan su neh.Mijin ta ya kasance yana aikin tiles kuma yana samu sosai daga aikin,sannan kuma shi malamin makaranta ne.
    Fatima ta murmure abin ta walillahil hamdu sai dai abu daya da ke damun ta shine rashin sanin inda Bilkisu ta ke.
    Sai gashi yau Allah ya turo mata yar ta da ta ma manta da ita.
    Kicin ta shiga ta ciro goran kunun aya mai sanyi saboda suna samun wuta sosai a unguwar.Kofi ta dauka a dayan hannun sannan ta fito ta ajiye mata a karamin tebur dake gefen kujeran.
     Zama tayi tana kallon Jumy yayinda take kora kunun ayar ta na lumshe idanu alamun jin dadin abinda take sha.
   Sai da ta shanye tatas sannan ta juyo ta fuskanci 'yar uwar ta da kyau kana ta soma bata labari kamar haka.
   _"Tun ranar da na bar gida saboda baba yace ba zani aura Alhaji Tagoma bah na shiga wani irin rayuwa da nike da na sanin sa yanzu.Daren ranar da na gudu, Alhaji Tagoma ya dauke ni muka wuce gidan sa,a cewar sa zai kaini wajen 'yan uwan sa in zauna kafin ya nemo wanda zai wakilci iyayena a bikin mu.Ni kuma da na riga nayi nisa bana jin Kira,na bishi sai gidan shi da yake Shango.Muna isa, muka shiga gidan,sai naga Ashe shi kadai ke gidan sabanin yadda yayi min bayani.Nan hankali na ya tashi na fara tambayar sa,ina 'yan uwan na sa.Hakuri ya soma bani sannan kuma ya bani tabbacin babu abinda zai yi min.Nan hankali nah ya kwanta na dan saki jiki.Ba da dadewa ba ya shiga kicin ya fito da drinks da kuma naman kaji.Da kyar na iya cin abincin shima sai da ya bani tabbacin babu komai a cikin sa.Ni dai a iya sani na,amare neh suke cin wannan a daren auren su.Amma tunda yace na kwantar da hankali na,sai na sake rai naci naman sosai sannan na sha drink din.Zama nayi a takure a falon yayinda muke kallon TV.Cikin Dan kankanin lokaci,sai na fara ganin wuri dishi2.Kafin na san meh yake faruwa sai ganin kai na nayi a hannun sa,ya ciccibe ni zuwa daki yana murmushi.Ina ji ina gani ya raba ni da budurci nah,sai sambatu yake tayi,ni kuma na kasa yin komai saboda jiki na yayi weak...."_,dakatawa tayi da maganar saboda kuka da ya ci karfin ta.
   Mikewa Fatima tayi ta zauna a gefen ta,tana lallashin ta har ta dan tsagaita kukan.
    _"Washegari ya bani makudan kudi sannan yayi min alkawarin in har zan tsaya da shi,toh zai biya min dukkan bukatu na,da na tambaye shi zancen auren na mu fah,sai yace in dakata tukun,na kwantar da hankali na,zamu yi aure.Tun ranar na zama farkar sa,dani yake tafiye2,har Dubai muna zuwa tare.Kuma koh meh nike so ya nayi min.Na kasance tare da shi har tsawon shekara uku muna zaman haramun.Daga baya nazo naga baya satisfying dina, sai na fara biye2n young millionaires ina kwana da su.Da na tara kudi da yawa, sai na gudu na koma Dubai da zama saboda ina tsammanin ko na dawo gida,babu Wanda zai kula ni.Isa na Dubai, na samu wani tamfatsetsen gida na siya,ina ta rayuwa ta a ciki.Ba na sallah bare azumi sai zuwa clubs da aikata alfasha.Kowa ya sanni a club saboda na fi dukkan 'yan matan wurin iya rawa da harka. Da Jumy suka san ni a can.Ina nan ina harka na ni kadai har na hadu da wata friend a can,muna kiran ta da S.H.Itama gwana ce a filin rawa,nan da nan muka kulla kawance,daga baya wata Shola tayi joining din mu.Haka muka cigaba da cin karen mu babu babbaka sai dai na dai na kwana da mazaje saboda S.H tace ba abin yi bane sai na daina...Haka muke ta holewar mu na ma manta da wani Alhaji Tagoma sai da muka samu wani aiki through S.H.."_.Nan ta ba wa Fatima labarin abinda ya wakana tsakanin su da Ramlan har izuwa dawowan su Najeriya,da kuma auren Ja'afar da Shu'uma.
    Baki sake Fatima take ta kallon ta,"ashe har rashin hankalin Ramlan ya Kai haka da yake son a raba Bilkisu da Ja'afar?",cewar Fatima cikin takaici.
   "Au dama kin san su neh?"...Nan Fatima tayi wa Jumy kwatancen Bilkisu har ta gane ta.Kara fashewa tayi da kuka,tana da na sanin abubuwan da tayi wa 'yar uwar ta.
    _"bayan mun samu labarin S.H ta auri Ja'afar,kowa ya Kama gaban sa inda Shola tace zata koma garin su saboda ta ga babu riba a irin rayuwa da muke yi.Nan take nima na yanke hukuncin yin hakan.Bakin titi muka fito domin neman taxi.Bayan shola ta samu ta wuce,na rage ni kadai a wurin sai ga wani mota yazo ya wuce ni.Reverse da direban yayi neya dawo da hankali na wajen su.Wasu gardawa naga sun fito daga motar sannan wani ya ciro wheel chair.Sai ga Alhaji Tagoma an sa shi a wheel chair din.Ina ganin shi na ji gaba na ya fadi.Kafin na ce zan ruga sai ji nayi an fara bugu na kamar ana ruwan sama.Bayan sun gama ne yace sanadiyyar cin amanan shi da nayi ne ya zamo haka.Ya bani dukkan abinda nike so amma na butulce masa na gudu,ya shiga tashin hankali har stroke ya kama shi,don haka wannan shine sakamakon abinda nayi masa. Sannan ya basu order suka dauke shi suka mayar da shi mota suka watsa min kuran titi...Da kyar na iya mikewa na lalubi kudi na bar kayana a wurin,na nema taxi.Ina isowa Minna,na shiga mota sai garin mu.Ina isa gida naga wasu mutane daban ke ciki inda suka yi mini bayani cewan ai kun bar gidan da dadewa amma ga adireshin ku. Ban ko tsaya ba na juyo zuwa Minna kuma,na nema anguwar,naci sa'a Mai mashin din da na tsare ya san wurin.ina isa na duba lamban gidajen har na ga Wanda yaxo daidai2 da adireshin da aka bani.Sallama nayi tare da kwankwasa kofar gidan,can mama tazo ta bude.Tana budewa na kalle ta na fashe da kuka.Tambaya ta soma yi ko ni wace ce.Nan take na ce mata nice Jummai.Ai kuwa kamar yadda na zata,nan ta wanke ni tatas da masifa sannan tace na bar gidan tun da dadewa kafin baba ya dawo.Ina fitowa na ga wata mata makwbciyar ku na ce don Allah ina neman Fatima 'yar gidan nan neh,shine tace min ai kin yi aure, nan na roke ta ta bani adireshin ki shine ta bani kenan na zo.Don Allah Fatima ki taimaka min ki taya ni rokon su Mama.Ku yafe min,gashi na fara ganin sakayyar bijirewa umurnin mahaifa na bana son rayuwata ta karasa gurbacewa..ki taimake ni....."_,ta karasa zancen tana kuka mai ban tausayi.
    "Karda ki damu in shaa Allah zan sasanta Ku.Na yafe miki yaya"..cewar Fatima tana kuka itama,suka rungume juna....


*******

Gardawan na daf da kamo su,sai ga wata mota ta zo gittawa.Tsayar da motar suke yi amma bai nuna alaman tsayawa bah.sai da Sameera ta hau kan titin ta tsaya a gabar motan.
    Birki ya taka da karfi.ji kake "kiiiiiii".da gudu taje wurin window tana rokar sa,tana nuni da gardawan.Kai ya kada mata alaman su shigo.
   Da sauri ta riko Bilkisu suka shiga motar da wuri, bata gama rufe kofar ba,ya ja motar saboda cikin gardawan yakai wurin motar,rike kofar motan yayi yana binsu.
    Haphazard driving ya fara yi har gardin ya fadi sannan ta rufe kofar.Kuka take yi sosai.Sai da mutumin yayi nisa,ya tsaya a hanyar shiga cikin gari.
    Tambayar ta ya soma yi cewa ina zai kai su.Da kyar ta saita kan ta,tace a kai ta Morris.Suna kaiwa unguwar tana ta nuna Mai inda zai bi har suka isa gidan.
   Bilkisu kuwa ta dade da sumewa.Harabar gidan ya shiga yayi parking,ya taya Sameera ciccibar Bilkisu suka shiga gidan.Suna shiga falo, Mami ta na kokarin shiga daki.
    Juyowa da zata yi,idanun ta yayi arba da mutum kamar Bilkisu a hannun wani,murza idanun ta ta kara yi amma dai still Bilkisu'n ta gani.
    A lokacin ta lura da Sameera da ke kuka,duk ta fita hayyacin ta.Da sauri Mami ta sauko,harda sassarfa.Tana karasowa ta kwala wa Momma kira, nan suka fito dukkan su saboda kiran ya razanar da su.
    Cirko2 suka yi ganin Bilkisu a hannun wani."Bilkisu??!!!",cewan Abba da karfi.
   Da sauri ya karasa gaban su.Tambaya ya fara jerowa bawan Allah,da kyar yayi calming na sa tare da nuna mai Bilkisu bata numfashi.
    "Alhaji mu kaita asibiti karda ta mutu",cewar Mami da ta gama rudewa.
    "Je ki kwaso min key toh",inji Abba sannan ya karbi Bilkisu daga hannun mutumin,dai2 Ramlan yana shigowa.
   Ganin Bilkisu da yayi yasa gaban shi ya fadi."Bilkisu?! Abba ina aka gan ta",yace ko sallama babu.
    "Yawwa thank God ka dawo,juya asibiti za mu,je ka dauko key na motar ka",cewar Abba yayinda yake fita da Bilkisu.
   Sameera,mutumin da Momma na biye da su a baya.Can Ramlan da Mami suka fito,Mahneerah da twins na gidan su Ja'afar a lokacin,bayan sallar azahar Abba ya kai su.
   A motar Abba ne aka sa Bilkisu,Mami ta shiga baya ta zauna da ita. Sannan Momma ta bi Ramlan,Sameera kuma ta bien wannan mutumin.
   Dr Wahab hospital suka je. Suna isa aka karbe ta sai ER.Da yake suna da kokari sosai a asibitin,nan da nan aka fara aiki a kan ta.
   Bayan sun dan nutsu neh,Abba ya tambaye su for the thousandth time yadda aka yi suka ga Bilkisu.
   Nan Sameera tayi mai bayanin komai.A harzuke Abba ya ciro wayar sa ya Kira police yayin da Mami da Momma suna ta suburbuda wa mutumin godiya.
   Kwatancen wurin yayi musu sannan yace Ramlan ya dauke ta a mota su je. Duk jikin Ramlan yayi sanyi jin Ubaid ne ya sace ta.
   Jiki lakas ya ja motar Sameera na gefen sa zuwa can bayan gari.
  Suna isa polisawa na isa,suna shiga gidan suka ga wayam babu shi.Tatas aka duba gidan amma ba a gan shi ba.
  Har sun fito zasu wuce sai suka ji kamar mutum yana nishi a cikin kwalbatin gidan.
   Suna budewa,suka ganshi kwance a wurin sai fitar da nishi yake yi da kyar.Ciccibo shi suka yi suka saka shi a black maria'n su.
   Ramlan ko kwakkwaran motsi bai iya ba saboda ya san kashin shi ya kusa bushewa.
   Sameera kuwa sai kuka take yi.Allah ya gani tana bala'in son Ubaid sosai amma baza ta iya yafe masa ba saboda abinda ya yi wa Bilkisu.
    Suna wucewa dashi Sameera suka koma asibiti.
   Bayan wasu awanni Bilkisu ta farfado aka mayar da ita special ward.Sai ajiyar zuciya take yi,tana bacci.
    

****

"Durling ki yi hakuri da abubuwan da Nike tayi miki kwanakin baya,ba da son raina nike yi bah,kece kika kaini bango",cewar Ashraf yayinda yake share wa Asmee hawaye.
    Kullum kuka take yi saboda da na sanin abubuwan da tayi.
   "Ni ya kamata na baka hakuri,na cutar da kai yayinda kai kake nuna min kauna.Na cutar da rayuwar ka,na jefa ka a halin kakani kayi.Ka yafe min miji na",tace tare da kwantar da kanta a jikin sa.
   "Na yafe miki my dear,Allah ya yafe mana gabakidaya",wani kukan dadi ta fara yi,ta kankame shi sosai tana jin son sa a kowani loko na jikin ta.
     "Za ka kai ni na roke Umma don Allah",tace tare da kallon sa ido cikin ido.
   Wani yarrr suka ji lokaci daya.Wato so da kaunar juna a aure daban yake da auren da babu so ko kauna.
   "Toh je ki shirya yanzu muje",da gudu ta je daki ta danyi kwalliya sama2,ta sanya hijabin ta ta fito.
   Jin dadi take yi yau zata ga babyn ta.Rike hannun ta yayi suka shige mota sai gidan hajiyar sa.
   Suna sallama ta amsa masu saboda kusan kullum a falo take zama.Fadada murmushi ta tayi ganin Ashraf tare da matar sa.
   "A'a su Asma'u ne  a gidan yau?",tace fuskar ta dauke da fara'a.
   "Eh Umma ina yini",tace tana jin kunyar abubuwan da ta aikata a baya amma gashi matan nan sai dariya take yi da ita. Gaban Umma ta je tayi kneel down.
    "Umma nazo na roke ki neh,bisa ga abubuwan da nayi miki a baya,ki yafe ni,na tuba",gyaran murya Umma tayi sannan tace,
   "Hmm,ni ban rike ki a zuciya ta bah,na san harda kuruciya ke deban ki. Amma abinda nike son ki sani shine,ki san yadda za ki dinga yin mu'amala da mutane,yau mu ne watarana ba mu ba ne.Gashi kafafuwan da kika shure ni dasu rannan,dashi kika tsunkuya min,gwiwoyin da na sa a kasa,yau gashi kema kin sa naki gwiwoyin a kasa kina roka na,mu dinga tunani kafin aiwatar da abu.Manzon Allah yace"Kama tadeenu tudaani..duk abinda kayi wa wani, shi za ayi maka...",amma ni ba na yi miki irin fatan nan,na yafe miki diyata,ga 'yar ki nan,ki kula da ita, kulawar mahaifiyar ta take so ba nawa bah",cewar Umma sannan ta mika mata Rahma.
    Tana kuka ta karbi 'yar ta,lallai yanzu ta yadda da cewa tqyi shiririta.Kallon yarinyar tayi tana share hawayen ta."why did I punish this innocent soul?"ta tambayi kanta.
    Gashi ko sunar ta bata sani bah kuma tana jin kunya ta tambaya. Ashraf ya Lura da hakan sai yace mata sunan ta Rahma.
   "Allah shi raya Rahma,mai Kama da Maman mu"..
   Dariya suka yi gabaki dayansu.Haka suke ta hira cike da nishadi daga baya suka wuce gidan su Mommy.
   Mommy da Zahra sunji dadin ganin ta.Nan da nan aka yi entertaining din su.Sai da suka Dan yi hira sannan da shiga cikin falon Abba ta roke shi shima ya yafe mata.
   Sallar la'isar suka yi sannan suka ce zasu gidan su Ja'afar.Suna isa Asmee na ganin Ja'afar ta fara kuka.Nan ta nema yafiyan Shu'uma kan threatening dinta da take tayi sannan ta dauki twins tayi wasa da su.
    Mahneerah tace zata bisu su sauke su a gida suka ce toh.Suna isa gida,maigadi yace ai anga Bilkisu suna asibiti.
   Abba mahneerah ta Kira ya gaya mata inda suke.juya ka motar yayi sai hanyar Dr wahab hospital.
   Mahneerah sai ji take yi kamar tayi tsuntsuwa taje asibitin.
   Suna isa ta fita a guje,ta ma manta da twins a bayan motar.Su Ashraf suka kwashi twins din suka bi bayan ta.
    A lokacin Bilkisu ta farfado,suna shiga mahneerah ta ruga da gudu ta rungume ta tana kuka.Juyowa Bilkisu tayi hawaye na gangaro mata tasa hannu ta shafa kan Mahneerah.
    Kuka kowa keyi a dakin yayinda aka bata twins daya bayan daya saboda kuka Mai tsuma rai da take yi.
    An raba ta da 'ya'yan ta da basu san meye duniya ba.Amma Ubaid ya cuce ta.Haka dai suka yini a asibitin kafin Abba ya kwashe su suka wuce gida.Sameera,Mama, Mami da Momma aka bari a asibitin.
   Mama tayi kuka sosai ganin 'yar ta cikin wannan halin.Amma ta gode wa Allah da ya sa komai yazo da sauki,bata ji rauni sosai va.
   Sai da suka yi kwana uku a asibiti kafin aka sallame ta.Ta sha tambayar ina Ja'afar ya ke amma sai ce mata ake yi,yayi tafiya.
    Ranan da aka sallame su gidan su dake Bosso estate aka kai ta saboda su Mami basu san yadda zasu yi mata bayanin auren Ja'afar da Shu'uma bah.
     Bayan sun je can,Mama ta zaunar da ita tayi mata nasiha sosai sannan tayi mata breaking news din.
   Sharrrr hawaye ya fara zuba daga idanun ta.....*An zo karshen labarin amma wani hanzari ba gudu bah,Ku biyoni a epilogue na wannan LABARIN coz da sauran tonon asiri a kasa!!!*
_*'Yar autan Mama Ummieejaafar๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜*_
     
                    Na
                   
           Ummiee Ja'afar
                      
*~Sadaukarwa ga Hama gee,professional writers,Amalfans01 and phateeBabyZahra novels~*"Toh kamar yadda kuka sani, abubuwa da dama sun faru a cikin watanni da suka wuce,ciki kuwa har da batar Bilkisu, da rashin lafiyar Ja'afar,da kuma auren sa da Sumayya kum.....".
    "Auren waye da Sumayya?!!!",cewar Ja'afar da ya katse mahaifin sa.
   "Kwantar da hankalin ka mana, zaka ji komai da sannu a hankali",cewar Abba.
    "Haba Abba, ya kuka aura min wannan tantiriyar,'yar iska,shasha,...".
   "Kai za kayi shiru ko kuwa??!!",cewar Mami da attitude din Ja'afar ya mugun bata mata rai.
   Shu'uma kuwa in ban da kuka babu abinda take yi.Mama ce ta jawo ta a jiki ta rungume ta,tana faman lallashin ta.
   "Daman na san akwai ranan kin yin dillanci",cewar Shu'uma a hankali.Wannan ne ranar da ta ke ta jin tsoron zuwar sa.
    "In ma wasa kike yi,gwara kin daina,tunda wuri ki ce a fasa auren nan or else zaki yaba wa aya zakin ta...mtssssw",yace sannan ya fita daga falon a fusace ya je garden.
    Alama Mami tayi wa Bilkisu da ta tashi ta bishi garden din.Sum2 ta mike kamar mara gaskiya ta fita.
    "Mami don Allah Ku bashi hakuri,ni din yanzu ba daya nike da na da ba,na canza halayya ta saboda shi, don Allah Ku tausayin min Ku fahimtar da shi..idan ban same shi ba,zan iya rasa farin ciki a rayuwa ta...",kuka ne yaci karfin ta.
    "Ke don Allah daina kukan nan,ki gaya mana meh ya faru,kun samu a duhu",cewar Alhaji Hamisu, mahaifin ta.
   Ramlan kuwa yayi tsuru2,gumi ke keto masa ta kowane bangare.Shikenan kashin sa ya bushe yau.Gashi asirin sa zai tonu a gaban kowa,ciki kuwa har da masoyiyar sa,Zahra.
     Gyara zama Shu'uma tayi tana share hawaye kana ta soma magana kamar haka,
   _"Daddy tunda mahaifiya ta ta rasu na shiga wani kuncin rayuwa wanda kake ta kokarin ganin ka faranta min amma A DALILIN GATA'n da ka bani,sai na shiga wani irin rayuwa, rayuwar bariki...."_,nan ta basu labarin dukkan abubuwan da ya faru da ita har izuwa wannan lokacin.
    "Kin cuce ni,kin cuce ni Sumayya.Dukkan gatan da na baki Ashe kina zuwa kina min fentin kashi ne a farin kyalle,what did I do to deserve this?"...
    Tasss! Suka ji karar saukan mari. Mami ce ta mari Ramlan bayan ta gama jin bayanin Shu'uma.
   "Wato rashin imanin ka bai tsaya tun kuna yara bah,har auren yarinyar nan ka so ka ruguza..Anya kai dana ne kuwa???...Allah ya I......",da sauri Momma ta rufe mata baki tana kuka.
    "Kiyi hakuri Maman Sultan,karda ki tsinewa Dan ki,kiyi hakuri don Allah",Momma ta karasa maganar tana zubda hawaye.Wannan wani irin AL'AMARI ne haka?!.
    Nisawa yayi ya matsa ta bangaren Abba ya rike masa kafa yana kuka.Abba ma kasa motsawa yayi daga inda yake don takaici.Bai san haka kiyayyar da Ramlan ke yi wa Bilkisu ya kai haka ba.
    "Abba wallahi believe me,na san nayi abubuwa da dama a rayuwa ta amma don Allah kuyu hakuri Ku saurare ni,karda Ku tsine min....",yace yana kuka.
    Daddyn Asmee ne ya ce mai da yayi magana,suna jin sa.Labari ya basu daga kan makircin da yake ta kulla mata har izuwa ga hada kai da Umma da suka yi sannan da bayun fyaden da suka sa ayi mata saboda karda Ja'afar ya aure ta.
     Zahra ce ta mike ta shige daki da gudu ta na kuka.she couldn't take it anymore.
   Bata taba tsammanin rashin imanin Ramlan ya kai level din nan bah.Abba da yake ta karfin hali sai da ya fashe da kukan takaici.
    Ba abinda yafi daga mai hankali kamar abinda ya kuma jim Ramlan yana fadi wai shine sanadiyyar mutuwar Sultee.
    "Enough!!,wallahi kana kara magana zan tsine maka",cewar Abba a tsawace.
    "Ki bar ni da Dan iskan nan,murderer.Allah ya I....".
   "Haba ya kuke abu kaman marasa ilimi",cewar Mama da ke rungume da Shu'uma still yayin da Momma ke rufewa Mami baki.
    Mahneerah ce ta mike,sai ji aka yi tana dukan Ramlan ta ko ina kamar an aiko ta.
   Abin ka da mara gaskiya,kasa ko da motsa kafan sa yayi daga wurin.Daddyn Asmee da Shu'uma ne suka mike domin taimaka mashi amma inaa,watsar da su tayi a katsa,ashe iskokan ta ne suka taso.
    Sai da tayi mai isar ta sannan ta koma tana fizge2.Da kyar aka samu aka rike ta.Duk ta ji wa kanta ciwo,sai kuka take yi tana Allah ya isa,ita a bar ta ta kashe shi itama ta huta.
    Kai...duk Wanda yake wurin nan,sai ya kuka saboda tausayi.Dukkan ilahirin falon gunjin kuka ake ji.
    

*****

"You alone,mai yasa kayi wa su Abba rashin kunya,you walked out on them!",cewar Bilkisu rai a bace.
   "Baki ji meh su ke cewa bani,wai ni Ka aura wa banzar can..kum..."
   "And so what?!,karda ka zama butulu mana, she choosed to stay with you a lokacin da kake bukatar kulawa ta...ta tsaya da kai yayin da baka cikin hayyacin ka...ta canza halayen ta saboda kai,just give her a chance ta nuna maka how sorry she is...".
    "Wato kema tayi brainwashing dinki kenan koh,toh idan ta iya d Ku,ni ba za ta iya da ni bah..Kinga tafiya ta!",yace tare da juyawa zai bar garden din.Riko hannun shi tayi,babu shiri ya dakata.
    "Haba you alone,ka manta fadin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,da yace karda mu saka wa sharri da sharri sai dai alkhairi, bare kai alkhairi tayi maka fah.Haka zaka saka mata?...come to think of it,da ace bata yarda ta aure ka bah,Mami ba za ta iya baka dukkan kulawan da kake bukata bah hakazalika Abba... Ni na yarda na amince da auren ka da Sumayya.Tayi min abinda har in mutu bazan iya biyan ta bah,for taking care of someone who means a lot to me!,please consider her...",haka ta cigaba da lallashin sa har yazo ya yarda da kyar da sharadin zaman kan ta zata dinga yi a gidan.
    Sai da taga hankalin sa ya kwanta sannan ta ja sa suka koma cikin gida.Suna shiga falo suka ga atmosphere'n ya koka na kuka.
   Maganar da suka ji Mami tana ta nanatawa neh yasa hankalin su ya tashi.
    Gaban Ramlan Ja'afar yaje ya tsunkuya ya cakume kwalar rigar sa.
    Kasa aiwata komai yayi,sai fashewa da kukan da yayi.
   "Amma ka cuce mu....daman kai ka kashe mana Sultee"..
  "A'a wallahi yaya mistake ne....na tuba..tun lokacin da abin ya faru na dinga da na sanin
..ban ma yi da na sani sosai ba,sai da aka nema Bilkisu aka rasa inda take.... Tunani na fara yi,idan har ta mutu ta yaya zan nema gafarar ta.....wallahi yaya bani na sa Ubaid ya sace ta ba,tun bayan da na sa su suyi mata fyade,ban Kara bashi wani aikin bah..."..
    Ja'afar na Jin Kalmar fyade kuma Ramlan yasa aka yi mata,ya zube a kasa sumamme.
   Nan sun Mama suka yo kan shi,Mami na cewa in har Ja'afar ya mutu to sai dai Ramlan ya bishi,ta huce takaici.
    Kusan lokaci daya Shu'uma da Bilkisu suka je suka dauko ruwa.Cirko2 suka yi ganin kowaccen su da ruwa a hannu.
   Alama Bilkisu tayi mata da taje da nata sannan ta juya jiki a sanyaye.Dole ta bar wa Shu'uma wasu responsibilities saboda itama mijin ta neh.
    Ajiye Nata tayi sannan ta karasa ta zauna a gefen sa yayinda Shu'uma ke shafa Mai ruwan a fuska.cikin mintoci kalilan ya farka.
    Kuka ya cigaba da yi,yana yi yana nuni da Ramlan da ke kuka shi ma,kasa magana yayi ya sadda kan sa a kasa yana kuka.
   Daddy ne yayi gyaran murya,yace musu kowa ya zauna sannan Mahneerah taje ta kira Zahra daga dakin Bilkisu.
    Zahra na fitowa ta fara magana tana kuka,"wayyo meh tayi maka, what did she do to you to deserve this?,ni na fasa auren,ba zan iya auren azzalumi macuci irin ka ba..ka ci amanar 'yan uwantaka,ko mutuwa zaka yi ba zan aure ka ba"..
     "Please karda ki yi min haka,na tuba please believe me.Don Allah karda Ku Bari tayi min haka",yace yana rike kafafuwan Daddy'n ta.
     Ganin za su bata masu lokaci ne yasa Daddy ya tsawata ma Zahra shine tayi shiru ta zauna kusa da Bilkisu.
    "Toh alhamdulillah da Allah ya......"
   "Assalamu alaikum",wani murya suka ji tana sallama tana shigowa."Umma?!",cewar Bilkisu yayin da ta zaro idanu ta dafe kirjin ta.
    Duk ta susuce ta zamo tamkar tsintsiya,baba yana biye da ita,bai ji dadin jikin sa ba shiyasa bai samu halartan meeting din ba sai gashi Umma ta so da sabon zance.
   Tana rike da Saleema da tayi baka ta rame.Saleema tana ganin Bilkisu ta ja hannun ta daga na Umma ta ruga sai wajen Bilkisu.
     Rungume juna suka yi su na kuka yayinda Abba yayi wa Umma nuni da wani bangare a falon da ta zauna.
     Bayan an natsu,Abba ya tambaye ta meh ya kawo ta.Nan ta fara shedding crocodile tears,ganin zata bata masu lokaci shine baba ya gaya musu yadda ta zo ta same shi a gida ta yi mai bayani,shi kuma yace ai ba yafiyar sa xata nema ba.Taje wajen wa'enda ya kamata ta nema gafarar su,shi yaso suka zo nan.
     Jinjina zancen kowa yake tayi.Ashe ita tayi wa Mama asirin da bayan ta haihu ta fita hayyacin ta.Sannan kuma da halin kakanikayi da ta shiga bayan ta gudu daga gidan.
    Zaman gidan bariki tayi tana masu ayyuka.Da tazo kudin baya isan ta,sai ta fara yi musu sace2.Har rannan wata ta gano ta,suka taru suka nada mata na jaki sannan suka kore ta.
    Daga nan ta fara bara a titi saboda basu da kudin da zasu ci abinci.Bayan watanni biyu shine ta yanke hukuncin dawowa gida ta nema gafarar mijinta,kishiyar ta da kuma Bilkisu.
    "Toh alhamdulillah da Allah ya nuna mana wannan ranan da zamu ga hasken al'amuran da ke ta gudana a gidajen mu.Abu na farko da nike son na fara magana a kai shine zancen Sumayya saboda labarinta ne makasudin tonuwar asirin sauran mutanen.Kai Alhaji Hashimu kayi sakaci.Saboda uwar yarinyar ka ta rasu,ba shine zai sa ka sangar ta ta ba,lokacin ne ya kamata ka bata tarbiyya Mai kyau yadda mahaifiyar ta zata yi alfahari da kai da kuma ita,Amma daga labarin 'yar ka,I'm very sure ko dan zama da ya kamata mahaifi da d'a suyi once in a while bama yin ta,kaga ba abin duniya muhimmanci fiye da rayuwar ta.Yi wa yaro duk abinda yake so ba shine gata ba,a'a koya masa akwai samu akwai rashi,akwai jin dadi akwai rashin sa and many more shine gatan da zaka iya ba wa yaro.Give them your time,ka zauna da su ka saurare su,know there problems ba wai kullum a Kira su a waya ba ace hope all is fine?...Alhaji kaji naka sakacin kenan kuma alhamdulillah Allah yasa soyayyar da take wa Dan mu ya canza ta although ba saboda Allah ta fara son sa ba da amma sai Allah yayi amfani da wannan Ya sa ya zamo sanadin shiryuwar ta,shiyasa turawa suka ce never underestimate the power of love....",sai da ya dan nisa sannan ya cigaba.
    "Ku kuma naku laifin shine yawan scolding din Ramlan da kuke yi.Na sha magana da kai Alhaji uthman amma baka ji,bashi da kyau yawan scolding yaro ko da baya jin magana.Addu'a shine abinyi da kuma Jan sa a jiki,amma the moment ka fara scolding din sa sannan kana yawan yabon 'yan uwan sa a gaban shi,sai ka haifar da hassada a tsakanin su kamar yadda Ramlan yayi wa Ja'afar har Bilkisu da bata hada alaka da Ku ba.Sannan kuma kamata yayi Ku dinga yawan zama dashi kuji problems din sa,wannan yana rage irin problems dinnan shima saboda at least he will feel that someone cares for him.Batun mutuwar Sultan da ya zamo tsautsayi ga Ramlan kuma ina son Ku yafe Mai,already haka Allah ya nufa kuma babu Wanda ya isa ya canza hakan",yace yana kallon kowa daya bayan daya, sai kada kai suke yi kamar kadangaru,alamar maganar da yake yi tana shigar su.
    "Kai kuma Ja'afar kamata yayi ka karbi Sumayya hannj bibbiyu saboda ita ta rike ka bayan da ka shiga wani mawuyacin hali na rashin matar ka,ta bar komai na ta saboda kai.Shin kai baka ji dadi ka zamo WANI HASKE a rayuwar ta bah,sanadiyyar son ka Allah ya shiryar da ita.The only way da za ka saka mata shine kayi accepting dinta as your wife yarda ka rike matar ka Bilkisu.Kaji tsoron Allah kayi adalci a tsakanin su..."
    Kada kai Ja'afar yayi jiki sanyaye alamar ya gamsu da bayanin Daddy'n su Asmee.
    "Asma'u kuma alhamdulillah itama Allah ya bani ikon tankwasa ita da mahaifiyar ta da yanzu sun zarce tunanin kowa a rashin mutunci,kin ma ci sa'a Ashraf yana son ki saboda da wani ne,da ya sake ki koh...Ku daina wulakanta dan Adam sannan ki tuna Wanda kike ta yin haukan domin sa,yanzu yana da mata har biyu so gara ki kwantar da hankalin ki,ki rungumi mijin ki,Allah ya yi muku albarka"..Ameen suma amsa gabadaya.
     "Kai kuma Ramlan tunda ka tuba,there is no such to say to you sai dai nace Allah ya Kara shiryar da kai,sannan ka cire damuwa daga zuciyar ka,haka Allah ya kaddara komai kuma on shaa Allah we will always be here for you,kana jina ko?",kada kan sa yayi shima alamar eh.
    "Ke kuma Zahra,in har kin fi karfin yin kuskure ne a rayuwar ki,sai ki fasa auren tunda ke perfect aka halicce ki,Ramlan dai yayi kuskure kuma ya tuba so,its left for you ki san nayi..."
    "Gare ka mahaifin Bilkisu.kai ne makasudin komai da yake faruwa da Bilkisu tun haihuwar ta har izuwa yau saboda mugun kalamai da kake fadi a kan ta.Ba zan taba manta Kalmar da aka ce ka furta ba ranar auren ta,cewar ba za ta taba jin dadi ba a rayuwar ta,shin tunanin bai zo maka cewa bakin ka yake bin ta bah duk da bata yi maka komai ba,fata na dai Allah ya kiyaye na gaba amma yi wa yaro baki ko da da wasa ne,bashi da kyau,don haka iyaye a kula....".
    "Ke kuma Maman Saleema tabbas Kim aikata babban sabo,kinyi shirka,kin hada Allah da boka amma gashi da Allah ya tashi Kama ki,sai ya Kama ki ta hanyoyi da dama, ciki kuwa har da warkewar mahaifiyar Bilkisu.Don haka ina son ki san wannan,duniyar ga da kike gani,karamin  ne,idan kika gina ramin mugunta,watarana zai karkato ta wurin ki ki fada a ciki.Allah ya sa mu dace".Suka kuma cewa ameen.
   Haka dai Daddy yayi musu naseeha Mai ratsa jiki daga karshe yace a yafe wa juna.Dukkan su suka ce sun yafe banda mutum daya da kila sai ta ga azra'ilu shine zata tuba wato Umma.
    Rufe taro aka yi da addu'a sannan aka watse,Mahneerah dai ta nace ita a wajen Bilkisu zata tsaya tayi musu kwana daya.
   Bayan sun wuce neh Bilkisu ta tashi ta shiga kicin don girka masu aabinci.tana cikin wanke shinkafa,sai ga Sumayya(Shu'uma) ta shigo kicin din.
    "'Yar Uwa da meh zan taimaka miki?".
   "Laaa karda ki damu,ai hutun amarci zaki yi..".
  "Kai ni fa babu ruwa na fah",tace tana dariya.
    "Yawwa Sumayya ina son na Kara gode miki da kulawa da miji na,wai mijin mu da kika yi...babu abinda zan iya saka miki dashi face nace Allah ya saka miki da aljanna fiddausi".
   "Kema haka Anty,ba kowace mata ce zata iya sharing mijin ta da wata bah especially me da na yi yawon bariki.Nagode sosai da kika amince da na zama abokiyar zaman ki,I'm ready to follow you sau da kafa,Allah ya bami zaman lafiya"..
    Haka suka cigaba da hira suna aiki gwanin sha'awa.D Ja'afar ya tattakure amma ganin su da yayi suna hira cikin kwanciyar hankali,sai ya samu relief.
   Tare suka ci abinci a dinning.suna yi suna Satan kallon juna.Mahneerah dai sai dariya take yi musu.Gida ya zama happy home kamar da.
   Dare nayi labari ya sha bambam inda Ja'afar ya nace shi wajen Bilkisu zai kwana.Da kyar ta lallabashi ya je dakin Sumayya.
    Sannan ita da mahneerah da twins suka kwana a dakin ta.Duk da tana jin kishin wai yau mijin ta yana nan tare da wata mace da ba ita bah,still ta danne zuciyar ta,tayi adduo'in bacci ta shafa wa dukkansu sannan ta kunna kira'a ta kwanta.Nan da nan bacci yayi awon gaba da ita.
    A can bangaren su Ja'afar kuwa babu abinda ya shiga tsakanin su face tashiwa da tayi da dare ma tana sallah,Ja'afar ya farga daga bacci ya ganta.
    Yaji dadin ganin ta a haka,nan ya yadda cewar lallai ta canza daga Shu'uma ta koma Sumayyar ta.Mikewa yayi shima yaje yayi alwala yayi joining dinta.....


                      **********

Toh masu karatu,haka rayuwa ta kasance wa su Ja'afar. Komai ya dawo normal,kuma suna zaman lafiya sosai a gidan Ja'afar.
   In ka ga Bilkisu da Shu'uma wani lokacin kaman twins saboda hadin kai.Twins ma kowace ta dau daddaya.Abba karami ke wajen Sumayya sannan sultan junior ke wajen Bilkisu.
    Ja'afar kuma kullum yana cikin godewa Allah da wannan iyalin da ya azurta shi da shi...
    A kwana a tashi har Ramlan sun kammala degree program dinsu.Nan da nan aka fara zancen bikin su.in no time,lokaci ya gabato.
   Anyi biki kuma biki yayi albarka sai dai muce Allah ya basu zaman lafiya.
  Sameera kuma ta koma wajen iyayen ta da zama kuma ta ki yin aure,a cewar ta no man can he trusted...
    Shi kuma Ubaid an yanke masa hukuncin daurin rai da rai saboda he was found guilty of dukka allegations da aka yi a kansa.
    Fatima kuma ta kai Jumy gida sun sasanta da mahaifan su da sharadin ba zata ka ra cin amanar su ba...
    Karshe dai dukka family din suna ta rayuwar su cikin nishadi sai dai dan rikicin duniya da baza a rasa ba wani sa'in....

"Wayyo....wallahi sai barauniyar nan ta bar min gida",cewar Umma da ke ihu a tsakar gida.Ko ta kan ta baba da Mama ba su you bah.Dama ance halo zanan dutse,kuma sun Saba da halinta.Addu'ar su a gare ta kullum shine Allah ya shiryaar da ita.

*Nima UmmieeJa'afar,addu'ar da zanyi wa masu irin halin nan kenan....*

*TAMMAT BI HAMDULLAHI*

*INA MIKA GODIYA TA GA ALLAH DA YASA NAA KAMMALA WANNAN LITTAFIN LAFIYA.KUSKUREN DA NAYI A CIKIN SA,ALLAH YA YAFE MINI. WANDA NA FADI DAIDAI,ALLAH YA BAMU LADAN SA.ALLAH YA BAMU IKON AMFANI DA FADAKARWAR DA NAYI MUSAMMAN TA KARSHEN WANNAN LITTAFIN.....ALLAH YASA MU DACE..AMEEN*


GODIYA TA MUSAMMAN ZUWA GA:
-Exquisite Online Writers
-Billy Galadanchi's novels
-Dimple's novels
-Xahra Bukar Novels
-Hama gee novels
-Amal01fansclub
-Afirst novels
-Professional writers group
-Maryerm G novels
-PhateeBabyZahra novels
-Isnarf novels
-Ummieejaafar novels
-Writers Planet
-Mata masu Aji
-Home of novels(Raheem)
-Home of novels(General Hassan)

Da sauran groups da ban samu na lissafi bah..Nagode sosai da kulawar Ku da kuma kaunar Ku..I cherish it so much. Allah ya barmu tare.Allah ya bar zumunci.


*Ba zan taba mantawa da ke ba,Ummiee Rilwan,my source of inspiration.Ta dalilin ki na fara rubuta novel.nagode sosai..Allah ya barmu tare*


*Love you so much my funny didi, Anty Ayna'u Dimples the anonymous writer,Maman Nu'aiym uwargijiya ta,Ummi khaleel, Khadija Achiba,sis Zainab and Hafiza my naughty friends,Dr.Fateema,Fiyya,Sha'awa,Leemcybae,Sis Lubna,Zeenaser,Jidda,Khadija al-nur,Asmeebae,Xeebae,Dr. Harisa,Ferteemerh,Maman Useey,Aminatou,Zailumy,Hanny,Ummujaafar,Momyn Sultan,Momyn Cyama,Mjaybae๐Ÿ˜‹,xeemee,stargirl...kai harda masu bina a private domin na turo musu book,duk da ban san Ku bah,I still want to let you know that I love you guys so much......**Jazaakumullahu khairan....ma'assalam*
   


_*Yar autan mama,Ummiee Ja'afar

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *