Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

RASHIN GODIYA(1 to End)complete

Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
        (admin
   Arewa hausa novels
       Novels villa
     Duniyan novels
   Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
          And
Cool novel, makeup and cooking)

      WHATSAPP NO:
    +2347039625239
RASHIN GODIYA
RASHIN GODIYA ✂ 1
BISMILLAHIR RAHMANIR
RAHIM
Rana ta take sosai duk wanda ka gani a cikinta
dole ce ta fito dashi daga gida. Tana zaune a
bayan bus ita kadai kamar mayya saboda babu
mai zama kusa da ita...karnin da take yi yasa
ake gudunta. Daidai asibitin tace da kwandastan
akwai na nan. Bai ji abinda tace ba saboda
karar horn daga motocin da ke sintiri akan titin.
Ai kuwa mutanen ciki kamar hadin baki suka
fara cewa akwai na nan, kai baka ji ne ana yi
maka magana akwai mai sauka. Kusan duk
mutanen bus din fitowa suka yi suka bata hanya
ta wuce. Wata dattijuwa ta rike hanci...wai!
yarinya a rinka wanka don Allah. Kwandasta
yayi dariya ai irin matan nan masu gayu da
kazanta suna da yawa. Amma dai gaskiya
yanmata idan kika dore a haka sai dai kiji ana
biki a makota amma ba naki ba. Aishatu bata ce
komai ba har aka bata canjinta tayi gaba.
Wani daci ne ya tokare mata wuya ta kasa
hadiyar yawu saboda radadin da zuciyarta ke yi
mata. Inda sabo ya kamata ta saba da kyamar
da mutane ke yi mata a dalilin ciwon da take
fama dashi. Hawaye ne suka sauko mata tayi
saurin gogewa da kasan hijab dinta sannan ta
karasa gate din asibitin. AMC....Assalam
Medical Centre. Tabbas shine asibitin da Anti
Lawisa ta kwatanta mata. Daga kanta tayi tana
karewa ginin kallo, a rayuwarta tana son gida
mai kyau, ba don lalura ce ta kawota ba da ta
bawa idanunta hakkinsu.
Tana shiga ciki reception ta wuce ta tarar da
mata biyu tsaye. Sallama tayi musu suka amsa
tare. Daya daga cikinsu ta kalli dayar, ke
Jummai warin me nake ji haka, ko jiya a nan
kika bar flask din abincinki ne? Bana son
wulakanci ta bata amsa a harzuke, kila ma
shegen cover shoe dinki ne da baya samun iska.
Ta kalli Aishatu ke baki ji karnin bane don
Allah? Ai gara wari akan wannan silent bala'in.
Ita dai Aishatu bata ce komai ba don tasan ita
ke fitar da wannan abin kyamar. Likita zaki gani
ne taji an tambayeta. Eh ta amsa amma ina
neman wata nurse ne Risikat. To wanne zaki
fara? Likitan ko Sis Risikat din. Daga baya
Aishatu taji ance gani meye ake kiran sunana.
Hmmmm kai Jummai yau anyi shara kuwa? An
fitar da bola da wanke toilets? Wurin nan has a
terrible odour. Aishatu suka nuna mata, ga
wadda take nemanki. Risikat na matsowa ta
tabbatar daga ina warin yake sai tayi shiru don
a matsayinta na maaikaciyar lafiya bai kamata
tasa mara lafiya yaji ba dadi ba. Haka ta daure
ta matso kusa da Aishatu, gani how can I help
you?
Dan murmushi tayi tace Anti Lawisa ce ta turo
ni. Tuni Risikat ta washe baki Ahh kece yar
yayarta ko? Ai ta fada min zaki zo. Kinyi saa Dr
Rano bai dade da zuwa ba. Sai dai zaki sami
layi ta fada tana nuna matan dake zazzaune a
wurin da aka yi domin zamansu suna shan sanyi
AC. Ina fata dai akwai kudi ko. Zaki bude file ki
biya consultation fee. Nawa ne ta tambaya tana
kokarin bude jaka. Jummai tace dubu biyu kudin
file sai dubu da dari biyar na ganin likita.
Sai da ta gama biyan kudin Risikat tace ta
zauna zaa kira ta. Idan tana bukatar wani abu
tayi mata magana. Kinsan farkon zuwana
unguwar mu Lawisa ta taimake ni sosai. Bana
manta alheri so feel free to ask idan kina son
wani abu. Godiya tayi mata sannan ta kara
shafa yar jakarta ta tabbatar kudinta yana nan.
Sai da babanta ya sayar da tumaki hudu aka
bata kudin don ance mata irin lalurarta tana cin
kudi sosai.
Kusan mintuna talatin tana zaune saura su biyu
a wurin taji ance Aishatu Yusuf. Gabanta ne yayi
mugun faduwa ta mike kamar an tsikareta.
Yanzu ta yaya zata yiwa likita bayanin ciwonta.
Gaba daya ta rude don saboda irin wannan
kunyar ta kasa fadawa kowa tana da ciwo har
sai da ya bayyana kansa.
RASHIN GODIYA ✂2
Sallama tayi tare da kwankwasa kofa taji muryar
namiji ya amsa daga ciki. Hantar cikinta ta sake
kadawa da ta shiga taga mutumin ba wanni
babba bane. Sai da Aishatu ta kwashi rabin
minti a tsaye...malama ki karaso mana akwai
taji ya fada yana danne dannen computer.
Aishatu ta karaso gaban table din ta zauna kan
kujera. Zumbur Dr Rano ya mike yana
kallonta...sorry wani wari nake ji,ina zuwa.
Karkashin kujerarsa ya duba da bayan labule.
Har wurin gadon da marasa lafiya ke kwanciya
ya duba su duk sai da ya leka yana yi yana dan
kallonta. Ko dai tusa tayi masa ne tana shigowa
ya tambayi kansa. Ganin irin kallon da yake
mata yasa ta galla masa harara. Ya dan shafa
kansa yana dawowa wurin zamansa tare da
karfafa zarginsa na cewa iska ta sakar masa
mai wari.
Yana zama ya jawo file din gabansa, Aishatu
Ja'afar ko. Kai ta gyada masa kawai. Ya dauko
biro ya dora kan wata takarda. Aishatu
shekarunki nawa?
Ashirin da hudu.
Kina da aure ne?
Eh...har ya rubuta tayi saurin cewa a'a.
Cikin rashin fahimta ya kalleta. Bangane ba?
Tace wata bakwai kenan da rabuwarmu da
mijin.
Sai da Dr Rano ya gama rubuta bayanan da
yake da bukata ya ce to me ya sameki?
Kasa dago kai Aishatu tayi tana wasa da wani
zobe a hannunta tace kuraje ne suka fito min
suna yin ruwa sannan ina fitar da wani ruwa.
Ganin daga nan bata da niyar kara yin wani
bayani ga lokaci yana tafiya yasa ya danna wani
abu a jikin bango. Ba jimawa wata nurse ta
shigo. Gani doctor. Ya tashi daga kan kujerar sa,
zan duba patient dinnan ne idan kuma kina wani
aikin ki kira wata tazo muyi tare.
A bisa tsarin asibitin idan lalura ta bukaci likita
namiji zai duba mace a jikinta sai ya kira nurse
mace ta tsaya a wurin saboda kare mutumcin
su.
Gadon nurse din ta nuna mata, taso ki kwanta.
Aishatu ta dan zare ido a ina? Dama dai Anti
Lawisa ta fada mata da wuya idan ba sai likita
ya duba wurin da kansa ba. Shiyasa ma ta jima
da ciwon bata yi yunkurin zuwa asibiti ba.
Daga dan guntun bayaninta Dr Rano ya dan
gane inda ta dosa. Nurse tana rike da file din ya
cigaba da yiwa Aishatu tambayoyi game da
abinda idanunsa suka gani a jikinta. Haba dole
yaji wari mana. Ita kanta nurse din don bai
kamata ta nuna kyamar patient bane amma sai
da ta kawar da kanta gefe.
Dr Rano yace Aishatu tun yaushe kika fara
ciwon nan?
Wata shida kenan ta amsa daga kwance.
Muryarta har rawa take tana magana. Yana
kallo ta share hawayen da suka dade cikin
idonta tana hanasu sauka.
Tijjani ya cuceta tunda a dalilinsa yau ita ce
kwance ana kare mata kallo cike da kyankyami.
Dr Rano ya katse mata tunani...banda kurajen
da discharge akwai wurin da ke miki ciwo ne?
Eh marata tana ciwo kuma idan zanyi fitsari da
zafi wani lokacin ta amsa idanunta a rufe jin an
tura mata wani dogon abu. Bata san nurse din
ce ma a kanta ba ba likitan ba. Nurse din tana
gamawa tace da Aishatu ta tashi an gama. Dr
Rano yace ki kai sample din lab ga request form
dinta ki hada dashi.
Wani rubutun yayi sannan ya bata takardar da
zata kai wurin ba da magani. Ga wadan nan ki
fara sha kafin ayi test din. Ki dawo nan da
kwana uku.
Har ta tashi yace Aishatu ki dena sakaci da
lafiyarki kinji ko? Rashin zuwanki asibiti da wuri
yasa ciwon ya kamaki haka, banda haka da tuni
kin manta dashi.
Dan murmushi tayi nagode doctor. Zan kiyaye in
sha Allah.
Aishatu na rufe kofa ya dauki wayarsa wadda ta
jima tana vibrating lokacin da yake duba
Aishatu...sunan Fadila ya gani ta kira sau goma
sha hudu. Allah gani gareKa yace don yau kam
gidansa bazai masa dadi ba.
RASHIN GODIYA ✂ 3
Shopping yaje yayi mata na tarkacen kayan
kwadayi kala kala duk na toshiyar baki. Idan da
kayan zaki zaifi jindadin bata hakuri.
Har ya shiga gidan bai ganta ba, yaransa biyu
Aliya da Aliyu kadai ya gani suna wasa tare da
mai aiki. Da murna suka tare shi ya basu tasu
tsarabar...Aliya ina Mamanki? Tana daki ta
amsa masa tana barewa kaninta sweet.
Da sanda ya shiga kamar barawo ya tarar da ita
a kwance tana kuka. Motsi kadan yasa ta juyo
tana kallonsa idanunta jazur sun kankance. Fitar
min daga daki munafuki.
Zai yi magana ta hana shi ta hanyar daga masa
hannu...wallahi nayi regretting aurenka
Huzaifa...ka cuce ni.
A kan gado ya ajiye jakarsa da white coat
sannan ya zauna. Yau kuma me nayi Fadila?
Meyasa kike son tadawa kanki hankali a banza?
Kin san yanayin aikina tun kafin ki aure ni amma
ke kullum zuciyarki bata kitsa miki komai sai
zargi. Ta ce to ka rasa abinda zaka zama sai
likitan mata sai kace wani namamajo. Indai ba
tsabar son mata ba meye na specializing akan
cututtukansu eyye?
Ledojin da ya shigo dasu ya tura mata. Fadila
kiyi hakuri don Allah. Ban taba tunanin cin
amanarki ba. Lokacin da kika kira ni dazu ina
duba patient ne. Kinga its against dokar asibiti
ace kana duba mara lafiya kana waya. Ledojin
da ya ajiye ta janyo tana lekawa daya bayan
daya...to ai kaine Huzaifa sai ka rinka kula duk
wata mace nurse ko patient. Ta dan gutsiri
chocolate kaga ai dole na rinka zarginka. Amma
komai ya wuce.
Ajiyar zuciya yayi ya tashi zai shiga wanka.
Fadila ta bishi har kofar toilet din...Abban Aliya
don Allah kada kaci amanata. Ina tsananin
sonka shiyasa nake kishinka da yawa. Gefen
fuskarta ya shafa tare da daga mata
gira..soyayyar da kike min ce ta hana ki ce min
sannu da zuwa dana dawo? Sunkuyar da kanta
tayi kasa kayi hakuri bazan sake ba. Yanzu ma
sharrin shaidan ne. Yayi murmushi haka kika iya
ai.
Aishatu kuwa bayan ta karbi magangunanta gida
ta tafi. Mamanta Hassana ta gani tare da wasu
mata biyu sun zo taya awakin da suka yi mata
saura. Da faraa ta shiga gidan ta gaishe su. Sun
gama daidaitawa akan dubu shahudu zasu sayi
guda hudu. A dole Mama ta amince suka bata
kudin suka kada awakin. Duk abinda suke yi
Aishatu tana gefe tana kallonsu tana share
kwalla. Suna fita tace Mama meyasa kika sayar
dasu. Su kadai suka rage fa. Hassana ta yi dan
murmushi to Shatu idan bamu yi miki ba waye
zaiyi miki? Duk halin da kika tsinci kanki
qaddara ce amma laifinmu ni da Babanku.
Saboda haka ni dai ina sake baki hakuri ki yafe
mana kada mu hadu da fushin Allah. Shatu tace
ni ki dena cewa na yafe muku. Kamar yadda
kika fada qaddara ce kawai.
To naji yanzu ya kuka yi a asibitin? Kinga likitan
da Lawisa ta ke fada. Eh Aishatu ta amsa
sannan ta bata labarin yadda suka yi.
Kwana biyu da fara shan magungunan da Dr
Rano ya rubuta mata taga kurajen sun fara
motsewa da kansu. Hakan yasa kaikayin ya fara
raguwa. Babanta Mal Sa'id Jaafar yana ta
fafutukar wani abokinsa ya biyashi bashin da
yake binsa abin yaci tura. Dan pansho din da
ake bashi ma na tsohon malamin makaranta
wata na uku kenan shiru. Duk ya damu saboda
kanwar matar sa Lawisa ta fada masa ciwo irin
na Shatu yana bukatar kudi. Shi kuwa tunda
shine yayi silar kamuwarta da ciwon dole yayi
iya yinsa don yaga ta sami lafiya. Mashin dinsa
ya bugar ya bata wani abin abu a cikin kudin,
sauran kuma ya ajiye saboda bukatun gida.
Bayan kwana uku ta shirya ta koma asibitin.
RASHIN GODIYA ✂ 4
Aishatu sammako tayi saboda kada ta tarar da
layi,amma duk da haka akwai wurin mutum
takwas a gabanta. Hira suke yi abinsu ita kuwa
seat din layin karshe taje ta zauna saboda kada
a fara gudunta yadda aka saba. Tana nan zaune
tana duba wani littafin addu'o'i daga Quran da
Sunnah wata mace da a kalla zata bata shekaru
goma tazo ta zauna kusa da ita. Kayan jikinta
ma abin kallo ne. Kana ganinta kasan akwai
wadata. Aishatu na ganin haka ta tashi tsam ta
koma wata kujerar nesa da matar. Ga
mamakinta sai taga ta taso tazo kusa da ita ta
zauna. Aishatu ta sake mikewa sai matar tace
haba yar uwa me nayi kike guduna haka. A dan
kunyace tace yi hakuri ba gudunki nake ba. Baki
ji wari ba da kika zauna kusa dani? Yar dariya
matar tayi har hakorin makkanta ya
bayyana...kinga yi zamanki nima irin lalurar dake
tare dake gareni. Aishatu ta dan gyara zama wa
ya fada miki? Risikat matar ta nuna mata. Cewa
tayi mu zauna tare tunda duk Dr Rano zamu
gani. Aishatu tace au..amma ke banji kina wari
ba.
Dariya matar ta zake yi. Ni sunana Sauda ke
fa? Sunana Aishatu
Sannu Aishatu. Kin dade da ciwon ne? Kafin ta
bata amsa nurse tace Aishatu Sa'id.
Tashi tayi ta tafi room 3 inda Dr Rano yake.
Bayan ya amsa sallamarta a bakin kofa ta tsaya
taki karasowa. Fuskarsa ba faraa sosai
sakamakon fadan da sukayi da Fadila kafin ya
fito.
Ganin da yayi ma Aishatu kamar a tsorace take
da dashi yasa ya dan saki fuska. Zo ki zauna, ya
dan kalli file din Aishatu ko? ya jikin?
Da sauki Alhamdulillah.
Kina ganin canji da kika fara shan magani?
Eh ina gani
Yayi Bismillah kamar yadda ya saba idan zai
fara duba mara lafiya ya dauko result din test
din da aka yi mata. Kinga infection kika samu
wanda yake barazanar taba miki mahaifa
sakamakon rashin zuwan ki asibiti da wuri.
Mahaifa likita ta fada a dan tsorace, yanzu
bazan haihu ba?
No ba haka nake nufi ba, da kinzo da wuri dai
bazai kai haka ba.
Wasu magungunan ya rubuta mata sannan yace
ina bukatar duk panties dinki ki zubar dasu. Ki
sayi sababbi kamar shida. Su ma zaki rinka
wankesu da ruwan zafi da dettol.
Sai kuma ki rinka amfani da pad saboda
discharge din. Kiyi amfani da atleast hudu
kullum. Ki yawaita tsarki da ruwan dumi ko da
bakiyi abinda ke bukatar hakan ba.
Kanta a kasa saboda kunya ya dan rage murya
kina jina kuwa Aisha? Tana dago kai suka hada
ido.
A daidai lokacin aka banko kofa da karfi sai da
suka mike gabadayansu.
Fadila ce ta shigo a harzuke da wata farar shirt
a hannunta...Huzaifa meye wannan? Ta nuna
wani jan shati a jikin rigar. Janbakin wace
shegiyar ne haka? Da so kayi ka rufe ni ko, to
Allah Ya kamaka. Ina hada kayan wanki
naganta. Wallahi idan baka nuna min yar iskar
da take neman hanani zaman lafiya ba sai na
tara maka jama'a.
Aishatu sai ta kalleshi ta kalli matar. Idanunsa
sunyi jawur ya rike karfen kujera da
hannuwansa. Da gani kasan daurewa yake kada
ya karasa gabanta ya shaketa.
A hankali yake magana yanzu Fadila da izinin
wa kika fito? Kuma wurin aikina ne kika ga ya
dace muyi wannan zancen. zata sake magana
ya kama hanunta ya kalli Aishatu idan zaki iya
ki dawo karfe biyar, sai in ganki a lokacin. Ya ja
hannun matarsa suka fita.
RASHIN GODIYA ✂5
Aishatu ta dade a tsaye tana mamakin wannan
al'amari da ta gani, wannan matarsa ce ko
budurwa? Nurses din da suka ga fitowar Dr
Rano suka sami abin gulma. Ba karon farko ba
kenan da Fadila ke zuwa. Ita dai Aishatu fitowa
tayi a sanyaye ta koma wurin zamanta ta zauna.
Shaf ta manta da Sauda sai da tace mata har
kin gama? Tace a'a likitan ya fita ne amma yace
zuwa karfe biyar zai dawo.
Sauda ta tashi to ai gara mu tafi gida. Yanzu fa
sha biyu da kwata ai kinga akwai zama. Aishatu
ta gama yanke shawarar zama a asibitin don
kudin hannunta take tsoron yiwa gibi kada ta
kasa siyan magani. Sauda ta dan tafa hannu
tunanin me kike yi ne? Tashi mu tafi mana.
Uhmm ba komai ki tafi kawai ni zan jira har
biyar din.
Sauda tace ko gidanki da nisa ne? Eh Aishatu ta
amsa ta dan gyara zama. Kudin da zata kashe
daga yan kaba zuwa gwammaja gidansu ai ba
kadan bane. Gara kawai ta jira ta gama
gabadaya.
Sauda tana ta kallon yadda Aishatu ke zama
lost in her thoughts tace kinga layi biyu zaki
wuce tsakanin asibitib nan da gidana. So ki zo
muje ko don yin sallah. Da farko Aishatu taki
yarda sai da Sauda tayi ta roko da magiya.
Wata farar benz taga Sauda ta nufa. Suna shiga
ta kunna AC din motar ta ja suka tafi. Basuyi
tafiya mai nisa ba suka je gidan Sauda. A ranta
Aishatu tace tsabar gata yar wannan tafiyar ma
sai an shiga mota. Wani dattijo ya taso ya bude
musu gate, Sauda cikin ladabi ta gaishe shi
sannan ta shiga tayi parking din motarta.
Yara biyu ne duk yan mata wanda babbar bata
wuce shekaru goma ba suka taho wurinta da
gudu suna mata sannu da zuwa. A tare suka
durkusa suka gaishe da Aishatu ta tambayesu
sunayensu. Babbar tace sunana Sajida wannan
kuma ta nuna kanwar sunanta Islam. Wadda aka
kira Islam ta suma kuka Umma kinga ta fadi
suna na bata jira na fada ba ko. Aishatu ta
durkusa a gabanta tana rarrashinta ni banji me
ta fada ba ma. Islam tayi wa Sajida gwalo Allah
Ya kara bata ma ji ba. Sajida tace Umma kin
ganta ko. Anti sunana Aisha amma Islam
Ummana take kira na. Aishatu tayi murmushi
ashe ma sunanmu daya. Islam sai murna ta rike
hannun Aishatu. Sauda tace to kaji ya isa haka
fadan kun tsare min bakuwa a waje.
Falon gidan Sauda ma abin kallo ne ga Aishatu.
Bayan sunyi sallah Sauda ta kawo musu abinci.
Da kyar Aishatu taci kadan saboda ta kasa sakin
jiki da Sauda. Suna gamawa Sauda tace naga
baki kira mijinki kin sanar dashi ba kada yaji
shiru. Aishatu ta dauko yar motsatstiyar wayarta
da tasha salatif, batir din wayar ma ana ganinsa
don bata da cover din baya. Mama ta kira ta
sanar da ita. A dan zaman da suka yi Aishatu
ta fahimci Sauda tana da kirki shiyasa ta dan
saki jiki da ita. Sauda tace mijinki yana karbar
treatment kuwa? Don idan ke kadai ke shan
magani indai yana da infection bazaku warke ba.
Aishatu ta ce auren ya mutu.
Ba dai dalilin ciwon ba ko. Allah sarki. Kinga ni
na kawo mana ciwon nan gida gashi watan mu
na uku kenan da fara neman magani kuma
Alhamdulillah sauki ya fara samuwa. Musamman
bayan mun fara ganin Dr Rano.
Aishatu tace ai naga kamar yasan abinda yake
yi. Nima kwana na uku da fara zuwa amma
kinga kaikayin ma ya ragu sosai.
Haka suka zauna suna ta hira. Har Sauda ta
bata labarin yadda ta sami ciwon ta. Wato
Aishatu duk macen da bata da godiyar Allah
komai kudi komai rashi to tana tare da matsala
babba a rayuwa. Ni kinga Baban Sajida babu irin
abinda baya min na jindadin rayuwa. Duk kasar
da yaje saboda yanayin aikinsa sai ya yi min
tsarabar sutura mai yawa. Allah Ya hada ni da
wata makociya mai rokon tsiya. Itama fa mijinta
nada rufin asiri amma roko tamkar a jininta
yake. Kuma aron na kaya ne. Daga hijab zuwa
mayafi ta fara. Kafin na ankara mun fara
exchanging kaya. Ta karbi nawa taje taro nima
na karbi nata. Duk abinda akeyi maigidan bai
sani ba. Sai wata rana naje gidan zamu biki tare
na fara period duk na baci. Kawai ta dauko min
pant a cikin kayanta ni kuma ganin mun zama
daya kawai na saka. Wallahi Aishatu sai da
baban Sajida yayi kusan wata uku baya fita
saboda irin kurajen da muka rinka yi. Ga wani
ruwa mai wari...nayi kuka nayi dana sani sosai,
baki ga yadda na rinka bashi hakuri ba don na
zata saki na zaiyi wallahi. Kinga sai ya gaggauta
gama gininsa muka dawo nan don ya raba mu.
Shiyasa yanzu ladabin da nake masa ko kadan
nasan banyi rabinsa ba ma da.
Aishatu ta jinjina labarin tace amma Anti Sauda
gara ke sau dubu akai na. Ni da kika ganni
namiji duk kyansa akai kasuwa. Sauda tayi
dariya haba kanwata ayi haka kuwa...Aishatu
tace ai anyi ma.
Labarin Aishatu Sa'id Jaafar
RASHIN GODIYA ✂6
Iyayen Aishatu duk yan garin Getso ne a jahar
kano. Babanta Mal Sa'id yayi karatu har NCE
yayi. Bayan ya gama ya sami aikin koyarwa a
makarantar gwamnati sannan ya auri Hassana
mahaifiyarsu. A Gwammaja ya ke zaune tare da
iyalinsa Allah Ya azurta su da 'ya'ya hudu.
Aishatu ce babba sai kannenta maza uku Sadiq,
Nurain da autansu Mahmoud. Iyayensu suna
zamansu lafiya. Hassana tana kiwon awaki da
tumaki sannan tana sayar da zobo.
A haka yaransu suka yi karatu. Aishatu tana aji
biyar a secondary school ta hadu da Fahad sun
tare da iyayensa a kusa da gidansu. Tun da ya
ganta yake sonta idan yayi mata magana ko
kallo bai isheta ba saboda tana ganinsa da su
Garzali daya daga cikin fitinannun unguwar.
Babban burinta a rayuwa ta zama lawyer.
Lokacin tafiya teaching practice Fahad ya
nemi makarantar su Aishatu. Nan fa yan mata
da yawa suka nuna mishi so saboda dan gayu
ne na ajin karshe. Kullum kayan jikinsa sai kaga
karin guga ya saka turare yana baza kamshi.
Lifan dinsa kuwa kafin a tashi sai yasa maigadi
ya kara wanke masa shi. Duk abinda yake yi
don Aishatu tayi noticing dinsa ne, ita kuwa ko a
jikinta. Karshe ma tunda ya rinka nunawa kamar
kanwarsa ce ita tunda su makota ne sai ta biye
masa. Duk yarinyar dake sonsa sai ta rinka
kamun kafa da Aishatu.
Duk hanyar da Fahad zai bi don ya sami kan
Aishatu yayi amma abin ya faskara. Karshe
Fahad dai mahaifinsa yasa yaje gidansu Aishatu
nema masa aurenta. Mal Sa'id ya yaba da
karamci irin na gidansu Fahad da yadda suka
fara tuntubarsa kafin ma yayi magana da
yarinyar. Wannan dalilin yasa ya yi alqawarin
bawa Fahad auren Aishatu bayan ta gama
WAEC. Amma da sharadin zata cigaba da karatu
bayan anyi auren.
Tunda Babanta ya sanar dasu Mama ke ta
murna. Ko ba komai yaron yana da nutsuwa a
ganinsu. Duk kawaici irin na Aishatu sai da ta
nuna bata so har ta sanar da iyayenta irin
abokansa na unguwar. iyayenta suka ki yarda da
maganarta, a ganinsu samun dan mutumci
kamar Fahad a irin wannan zamanin sai an tona.
A haka Fahad ya rinka bibiyar Aishatu da dukkan
kyautatawa tana wulakanta shi son rai. Idan
yazo sai Mama ta fattattake take fita.
Wata rana yana mata hira a soron gidansu ta
hade fuska. Ita ko kadan bata son Fahad, taki
jinin namiji mai ji da kansa kawai don yana da
kyau. Wannan kuwa halin Fahad, suna zaune sai
juya wayarsa yake yi. Sabuwar model ce don sai
da ya sayar da tv din dakinsa ya cika ya saya.
Duk yadda yaso ta nuna tayi noticing wayar ma
taki. Can yar karamar wayarta tayi ringing taga
sunan dan wan babanta Kamal. Da sauri ta
dauka harda kara kashe murya don Fahad yaji
haushi. Nan ta rinka magana cikin jan hankali
har Kamal sai da yayi mamaki. Kusan minti
ashirin yana son ajiyewa tana sake jan hirar.
Iyakar kulewa Fahad yayi don shi mutum ne mai
tsananin kishin abinda yake so.
Tana gama wayar ta dan kalle shi ni zan shiga
gida sai da safe.
Tasss taji ya dauke ta da mari, ni zaki yiwa
wulakanci Aisha? Don kinci saa nace ina sonki.
Duk masifar da yake mata bata fahimta saboda
yadda marin ya shigeta. Hawaye ne kawai yake
wanke mata fuska. A zuciyarta ta kudire bazata
taba yarda ta aure shi ba.
RASHIN GODIYA ✂ 7
Ihunta yasa Mama ta fito soron da gudu.
Aishatu me ya faru? Ta kalli Fahad ..me ya
sameta Fahad. Aishatu zata yi magana ya
durkusa har kasa gaban Mama sai ga hawaye a
idanunsa kamar famfo, Mama cewa tayi ko zan
mutu na dawo bazata aureni ba. Nace ta manta
iyayenmu sun riga sun shiga maganar. Shine ta
soma kuka ita da ta aure ni gara ta mutu. Ran
Mama yayi matukar baci tunda tasan dama
Aishatun ba son Fahad take ba.ta dubi yarta da
ta rike kumatu kin kyauta Aishatu tunda ke kike
da iko akan ki ba mu ba. Bari babanki ya dawo
zan sanar dashi gara ayiwa tufkar hanci mara
kunyar banza.
Wallahi Mama sharri yake min. Mari na yayi
Wani marin taji daga mahaifinta da ya shigo
gidan a lokacin kuma duk yaji abinda suka ce.
Wato ke ban isa da ke ba ko. Da ina miki kallon
saliha ki rinka mikil mikil da ido kamar
mutuniyar kirki.
Fahad ya durkusa a gaban Mal Sa'id yana bashi
hakuri. Baba ni na janye gara a bari ta zabi
wanda take so. Baba yace ai bazaayi haka ba
Fahad, ka turo min Alhajin gobe muyi magana
asa lokacin biki. Sai nayi maganin wannan
rashin kunyar taki.
Mama tace kayi min daidai, suka shige gida
suka bar Aishatu da baki a bude. Fahad ya yi
mata wani kallon banza..kadan ma kika gani
Aisha. Ni din nan nafi karfin mace ta wulakanta
ni. Macen ma irinki wadda bata gama wayewa
ba. Yana gama magana ya fice abinsa.
Daren ranar Aishatu tasha kuka. Mama na jinta
duk tausayinta ya kamata amma ta share.
Yarinya alkhairi na bin ta tana sa kafa tana
shurewa. In ba haka ba meye aibun Fahad.
Iyaye maza sun hadu an tsayar da biki wata
biyu. Hakan yayi daidai da gama jarabawar
qualifying da Aishatu zata yi. Ba karamin tashin
hankali ta shiga ba jin cewa ko SS3 baza tayi
ba. Wan babanta ba yadda baiyi ba amma Mal
Sa'id yaki hakura. Tun wan nasa Alh Dalhatu
yana fada har ya koma nasiha saboda yasan
kafiya irin ta kaninsa. Suna zaune a dakin
mahaifiyarsu a Getso, Alh Dalhatu yace wai
Sa'idu shin yaron nan ko iyayensa sun maka
wani abu ne da ka kafe sai ka bashi 'ya.
Gwaggo Juma tace banda lalacewa ma ai dan
uwanka ya dace ya bada ita ba kai ba. Baba
gyara zama ni dai kuyi hakuri amma yarinya
karama bata isa na rinka sa'insa da ita akan
maganar aure ba. Jiya fa a gabana ta kare
masa tanadi da yazo. Har tana cewa shi makiri
ne. Yaya kaji fa, dama ya fada min a makaranta
ake hure mata kunne. Shiyasa nake son cireta
kowa ya huta. Duk shawarar da aka bawa Baba
sai ya kawo uzurinsa. Dole suka kyale shi da
matarsa suka rinka shirye shiryensu na biki.
Lokacin kamar yasan Aishatu gudunsa take ya
rinka sauri. Ranar larabar da suka gama
jarabawa akayi kamunta. Kawayenta sunyi
mamaki sosai don babu wanda ta fadawa.
Mamakinsu ya karu da suka ga Uncle Fahad ta
aura. Daga masu tayata murna sai yan hassada.
Kyakkyawan mutum kamarsa ya kare da
Aishatu. Ba wai bata da kyau ba amma kyale
kyalen rayuwa basu dameta ba. Ranar asabar
aka daura aure da yamma aka kaita dakin
mijinta.
 RASHIN GODIYA ✂ 8
Aishatu zaune gaban kakarta Gwaggo Juma, tayi
kuka har ta gaji. G.Juma ta kawar da kanta gefe
ta share yar kwallar da ta taho mata. Ba don
Aishatu yarinya ce mai kyaun hali ba da ba zata
damu ba saboda irin abinda Baba yayi musu na
nuna musu iyakarsu akan yarsa. Kiyi hakuri
Aishatun Nabiyy, wadda kika gaji sunanta uwa
ce ga dukkan mumini kuma duniya ta shaida
mace ce ta kwarai. Aishatu cikin kuka tace ni
Gwaggo Allah idan aka kaini guduwa zanyi.
Kowa yaki ganewa amma Fahad mugu ne ga iya
sharri. G. Juma ta rufe mata baki da hannunta
wanda yasha jan lalle gabadayansa, kul kike irin
wadannan maganganun. Ya riga ya zama
mijinki. Kuma idan har na isa dake zaki yi
amfani da shawarar da zan baki. Ki rike Allah ki
tsayar da gaskiya a dukkan lamuranki. Kiji tsoron
Allah kada ki tarwatsa rayuwarki kawai don ba
kya son mijin da Allah Ya rubuta zaki aura. Duk
matan da suke guduwa ko kashe miji saboda
kiyaya wallahi komai dadewa sai sunyi dana
sani. Ki auri mijin da ba kya so ma ai jarabawa
ce. Idan kika yi hakuri kuma kika dage da
kyawawan halaye sai kiga Allah Ya daidaita ku.
Idan ko har babu alkhairi a auren to da sannu
Allah zai warware shi Ya baki rabonki. Duk
abinda hakuri bai baki ba to rashinsa ma bazai
baki ba. Ni so nake ko bayan babu ke idan ana
kwatancenki ace ke mace ce mai biyayya ga
Allah. Shiyasa kika bi mijinki sau da kafa.
Aishatu ta dago kanta ta kalli fuskar kakarta
nagode Gwaggo. In Sha Allah zanyi amfani da
shawararki. G. Juma da sauran yan uwansu
suka tashi suka tafi dama motocin kawo amarya
suka biyo.
Fahad da kansa ya shigo gidan ya tarar da yan
kawayenta uku da basu tafi ba yace su fito kada
su rasa mota. Daya daga cikinsu tace haba
ango ai baka sallame mu ba. Dari biyu ya zaro
daga aljihunsa ya mika mata, gashi nan ku shiga
mota. Allah Ya bamu alkhairi. Ganin yadda ya
hade fuska babu wadda ta sake magana suka
da uko jakunkunan su suka fice.
Duk muguwar niyar Aishatu na cusguna masa
shawarar G. Juma tasa ta watsar. Shiyasa da
ya shigo dakin da sallama ta amsa masa fuska a
sake. Wuri ya samu ya ajiye ledar hannunsa.
Kaza ce guda daya gasashshiya sai juice mai
sanyi. Kitchen ya tafi ya dauko plate ya zuba
kazar gaba daya ya dan barbada yaji a kai ya
fara ci ko kallon Aishatu bai yi ba. Ba dai tace
bata son shi ba. Zata gane bata da wayo don
yana da mugun riko. Gidan da suke sama da
kasa ne da babansu yake ginawa yaransa. Kasa
yayansa ne Khalid da matarsa Maryam da
yaransu biyu. Saboda riko irin na Fahad ya dena
kula wan nasa saboda ya hanashi aron mota.
Aishatu tana ta kallon ikon Allah sai da Fahad
ya cinye naman gaba daya ya shanye juice
dinsa. Dama karamin kwali ne daidai shan
mutum daya. Yana gamawa ya shiga toilet yayi
wanka ya fito ya nemi wuri ya kwanta. Da tana
sonsa ba karamin haushi zata ji ba amma yanzu
dariya ya bata. Tana nan zaune taga da gaske
dai bazai kula ta ba sai ta tashi ta dauki wata
doguwar riga da hijab ta shiga toilet ta canja
kaya. Da hijab din ta fito a jikinta ya dan tabe
baki meye kike ta wani rufe jiki kamar abin
arziki ne a ciki. Ita dai bata ce komai ba ta
shimfida abin sallah ta tayar. Kafin ta idar yayi
nisa a baccinsa. Itama tana idarwa bacci ya
dauketa akan abin sallar.
Mafarki takeyi wai kunama ta harbi babban dan
yatsanta na kafa wani irin zafi har tsakar kanta.
Tayi saurin bude ido da salati ta ga Fahad tsaye
a kanta yasa kafa ya take mata dan yatsan
kafa. Tayi saurin janye kafar lafiya Fahad taka ni
fa kake yi. Karfe nawa yanzu kina kwance kina
baccin asara. Ba sallah ba girki bare na ganki
kinyi wanka. Tayi sauri ta tashi tana shafa dan
yatsanta. Kayi hakuri in sha Allah bazan sake
ba. Ki wuce akwai dankali da kwai ki soya kuma
kada ki bata lokaci don yunwa nake ji.
Sallah kawai Aishatu tayi ta shiga kitchen din.
Dankali ta gani dan kadan an zube a kasa sai
kwai gudu biyu a cikin farar leda da bread.
Zama tayi ta kirga dankalin, guda ashirin ne cif.
Ikon Allah lallai Fahad mutumcinsa ragagge
ne...sai tayi saurin rufe bakinta da hannunta
Astagfirullah...lallai Fahad mutumin kirki ne.
Ta soya dankali da yayi kukut a plate da kwai
guda biyu ta hada da bread din duk ta dora akan
tray. Sannan ta zuba ruwan zafi a flask ta kai
masa falo. A gabansa ta ajiye komai ya share
dankalin da kwai ya rage mata bread. Bata nuna
bacin rai ba ta hada tea ta sha da sauran bread
sannan ta dan yi gyare gyare a gidan.
RASHIN GODIYA ✂ 9
Dayake aikin ba wani mai yawa bane bata dade
ba ta gama tayi wanka. Duk da ita ba mai yin
kwalliya bace amma yau ta bata lokaci sosai a
gaban madubi. Addua take Fahad ya dena
fushin da yake da ita har ta sami damar rokonsa
ya barta ta cigaba da karatu.
Riga da skirt ta saka dinkin yayi mata kyau
sosai. Jikinta yasha turare kala kala ta fito falo
ta same shi zaune yana duba wasu takardu.
Wata kujerar ta samu ta zauna Fahad zan sauka
kasa mu gaisa da matar Yaya Khalid. Ko kadan
bai nuna alamun ya ji ta ba bare ya bata amsa.
Fahad magana nake fa...Aisha shiru nake fa ya
bata amsa. Tasowa tayi ta durkusa a
gabansa...don Allah kayi hakuri da dukkan
abinda ya faru kafin muyi aure. Na gane
kuskure na kuma in Allah Ya yarda zan gyara. A
hankali ya dago suka hada ido....ko baa fada ba
Fahad kyakkyawa ne sai dai kuma kyan dan
maciji gareshi tunda bashi da halin kirki. Aisha
kenan daga kwana daya har kin rissina, ko dai
kazar da na ci jiya ban baki bace kike neman
yin rigakafi? To bari kiji in fada miki, na so ki
sosai da farko amma yanzu kin sire min. Auren
ma don na nuna miki kinyi kankanta ki ja dani
ne. Duk da ta tsorata da kalamansa bata karaya
ba ta rinka bashi hakuri. Kafa yasa ya shureta
ya fice.
A haka suka yi sati uku da aure ko matattakalar
benen yace Allah Ya isa idan taje. Tana daga
sama kamar tsuntsu sai dai ta ji hayaniyar yaran
shima ba sosai ba. Wata ranar litinin da safe
Fahad yana ta sauri zai je makaranta don a
lokacin yake level 4. Lectures gare shi karfe
takwas na wani malami mara kirki irinsa. Sai
sauri yake kamar zai tashi saboda ya makara.
Sai da ya gama shiryawa ya nemi assignment
dinsa da ya kai karfe ukun dare yana yi ya rasa.
Ga takardu da sauran books dinsa amma babu
paper din da yayi aikin. Aishatu tana goge
kitchen ya shigo rai a bace..to yar mara
mutumci ina paper din da kika sace min?
Kallonsa tayi ta watsar ta cigaba da aikin ta. Ya
daka mata tsawa Aisha ba magana nake miki
ba? Lokaci ya kure wallahi idan har ya shiga ajin
bazai karba ba. Nan ma shiru yaji ba magana.
Fizgota yayi cikin fushi idan na makara jikinki ne
zai fada miki. Naga yana miki kaikayi saboda
ban taba dukanki ba. A nutse ta yi masa
magana..ni ban taba maka komai naka ba.
Gudun kada wani abu ya faru ma yasa ko falon
ban gyara ba na bari sai ka fita.
Idan baki taba ba ubanki ne ya dauka?
Ba dai ubana ba ta bashi amsa tana kokarin
kwace hannunta da ya murde.
Idanunsa kamar garwashi jin agogon falo yana
kara alamun karfe takwas din tayi. Hannunta
yaja har falo yayi wurgi da ita akan kujera.
Goshinta ya bige da kujerar ta kwala ihu. Bai
barta haka ba ya soma dukanta.
Kofin tea din da ke hannun Khalide ne ya fadi
da yaji wani gigitaccen ihu da Aishatu ta saka.
Mikewa yayi da sauri sai ga Maryam ta fito da
gudu. Kaji ihun amarya ko? Don Allah kaje ka
duba kada ya kashe musu 'ya. Khalid yace
maryam kamar baki san Fahad ba. Yaron nan
bashi da kirki ko kadan yanzu ina zuwa sai ya
hada ni da Alhaji, shi kuma baya son laifinsa.
Matar ma ko sau daya bata shigo nan ba fa.
Maryam tace kaima ka biye masa ka hanani
hawa saman ba. Wani ihun suka ji tana bashi
hakuri ba shiri suka hau saman. A kwance take
ya daga kafa zai bige ta Khalid yayi saurin janye
shi. Ita kuma Maryam ta daga Aishatu wadda
goshinta ya tashi saboda buguwa ga jini a
bakinta. Tana kuka ta kankame Maryam tace
Fahad Allah zai saka min kuma in sha Allah sai
kayi carryover.
Khalid ya kalli kaninsa cike da takaici me tayi
maka haka kake dukanta. Yaya ba ruwanka da
iyalina,idan ba rainin hankali ba in zauna har
karfe ukun dare ina aiki ta dauke takardar don
mugunta. Khalid yace ka duba ko ina baka gani
ba. Na duba mana yana magana ya dauko
jakarsa kinji dadi tunda kin hanani zuwa
makaranta zan zauna a gidan muci uwar da
zamu ci dake. Kayan jakar ne gaba daya suka
zube a kasa saboda zip din a bude yake.
Papers dinne suka fara fadowa ya daukosu cike
da farinciki...Subhanallahi ashe da na gama a
jaka na saka don kada na manta su a gida. Duk
su ukun yaga suna masa kallon tuhuma yayo
wurin su Maryam. Don Allah Aisha kiyi hakuri
wallahi tsautsayi ne. kukanta kawai take taki
kallonsa. Daga yau na amince ki rinka zuwa
wurin Anti Maryam hira idan na fita. Nan ma
bata ce komai ba da yake bashi da kunya yace
Yaya ku tayani bata hakuri mana. Shi Khalid
ficewa yayi yana sauka ya kwalawa Maryam
kira. Aishatu ta kalle shi a tsorace kada ya
sake dukanta.
RASHIN GODIYA ✂ 10
Matsowa yayi kusa da ita yaja hannunta suka
zauna a bakin kujera. Kana ganinta kasan a
tsorace take. Hankici ya dauko daga aljihunsa
ya soma goge mata lebenta da ya fashe. Kiyi
hakuri Aisha nasan ban kyauta miki ba. Ina da
saurin fushi ne da riko amma zanyi kokarin
canjawa kinji. Kai kawai ta daga don bakinta ya
kumbura. Ya yi dan murmushi kinga bakinki
kuwa kamar an cusa fanke. A wahale tayi
murmushi yace ko ke fa. Ki daure mu gina
rayuwa mai kyau mu manta da dukkan abinda
ya wuce. Kin hakura? A yadda ya tsareta da ido
ai dole tace ta hakura ko don kada ya sake
dukanta.
Tun daga ranar Fahad ya koma lallabata. Sunje
gidan iyayenta da nasa sun gaishe su sannan ya
barta tana zuwa wurin Maryam ko ita ta zo ko
yaranta. Zaman su abin shaawa a lokacin
saboda Aishatu ta iya zama da mutane. Kuma
ladabin da take masa yasa ya kara sassauta
mata.
Matsalar da suka fara fuskanta ta fara daga
abinci da suke ci tare. Kullum suka zauna cin
abinci ita ce karshen tashi. Tun baya magana
har abin ya soma damunsa. idan ta fiye cin
abinci kiba zata yi, shi kuma baya son tayi kiba.
Dan jikinta a yanzu yayi masa shiyasa ko ciki
baya son tayi sai an kwana biyu tunda da
kuruciyarta. Wata shawara ya yankewa
zuciyarsa washegari ya fara amfani da ita.
Dama idan bashi da lectures kasuwa yake tafiya
wurin babansa. Ranar zai tafi kasuwa sun gama
breakfast tana fitowa daga kitchen taga ya kulle
kofar yasa key a aljihunsa. Lafiya ka rufe
kitchen din Fahad? Lafiya kalau, kawai na fi son
sai na dawo zaki rinka dora abinci sai muci a
alokacin. Likitoci sun ce yafi lafiya. Tohhh idan
naji yunwa fa ko nayi baki? Kada ki damu zan
saka fridge a falo sai a cika shi da ruwa. hannu
ta zira a aljihun rigarsa inda ya sa key din...kaga
bana son wasa Fahad ka bani don yau sinasir
zanyi har da su Anti Maryam nake son aikawa
kaga gara na fara da wuri. Hannun nata ya
kama ya matse tare da zaro key din Allah da
gaske fa nake. Wannan shegen cin da kika tsira
kwana biyu kamar gara bazan jura ba. Salon kiyi
muni kisa na fara kallon sirara a waje. Abu
kamar wasa sai ga Fahad ya fice da key din
kitchen. Haka ta koma girki biyu a rana. Daga
na safe sai na yamma bayan laasar. Shima da
kansa yake auna mata abinda zata dafa. Shi
kuwa a waje zai take cikinsa. Babu wanda tayi
yunkurin fadawa sirrin gidan ta. Kullum addua
take Allah Ya sa ya canja hali. Wata daya da
fara horon yunwar da Fahad yake mata ta rame
sosai ta kara haske. Anti Maryam tace kanwata
ko dai ciki gareki. Dariya kawai tayi ina ciki zai
shiga ana fama da yunwa??? Cikinta taji ya fara
murdawa saboda tsabar yunwa. Lipton kawai
suka sha yau da wani guntun bread. Da farko
daurewa ta rinka yi, a hankali abin ya fara
tsanani har Maryam ta lura. Aishatu ya dai me
ya sameki...jini ta gani yana bin kafar Aishatu ta
kamata da kyar suka shiga toilet sai ga wani
gudan jini kato ya fado. Anti Maryam ta ce
Aishatu bari kika yi fa. Dama ciki ne da ke?
Jikinta duk a mace tace ban san dashi ba anti.
Anti Maryam ta kira Khalid a waya yazo ya
kaisu asibiti lokacin Aishatu ko tsayawa bata iya
yi. Likita na dubata yace da Khalid ai dole tayi
bari. Mace da ciki ga yunwa tana neman yi
mata illa. Ai baa biyewa mata idan suna laulayi
mai hana cin abinci. Ko yaya sai a basu wani
abin da zai zauna. Shi khalid mamaki ne ya
kamashi wai yunwa! A gidan Fahad din? Lallai
dole Alhaji yaji wanan magana.
Sai da aka gama komai na asibitin aka sanar da
Fahad yazo. Iyayensu da sauran yan dubiya na
fita Fahad ya matso kusa da gadon ya rikewa
Aishatu hannu. Meyasa baki sanar dani kina da
ciki ba Aisha? Hawaye suna zubo mata tace
nima ban sani ba. Share mata hawayen dena
kuka kinji dama ni ba son haihuwar nake yanzu
ba. Sai na gama makaranta nayi service sai ki
haihu. Ashe shiyasa kika rinka shegen cin nan
kwanaki kamar ahalin yunwa. Kada ki damu zan
karbar miki maganin planning. Khalid da ke jikin
kofa yana jin abinda kaninsa ke fada yayi tsaki.
Allah wadaran halin yaron nan.
RASHIN GODIYA ✂ 11
Kwananta biyar aka sallameta. Kulawa kam tana
samu a wurin Fahad sai dai kullum dare kafin su
ci abinci zai bata kwayar magani. Lallabata yayi
yace maganin zai hanata daukab ciki yadda zata
samu damar komawa makaranta tayi WAEC da
NECO. Sai dai lokacin yanayi ya tsiri abinda zai
hadasu fada yadda bazai biya mata kudin ba sai
wata shekarar. A haka suka zauna har yayi
jarabawarsa ta karshe. Da murnarsa yaje
makaranta duba result. Abin bakin ciki yana da
spillover a course din da Aishatu tayi masa
addua ranar da yayi mata duka. Da bacin rai ya
nufi gida yau jikin Aisha zaiyi tsami ya fada a
ransa. Muguwar yarinya ashe da gaske tayi
masa wannan adduar.
A tsorace ta fito daga bandakin da PT strip a
hannu, Anti Maryam kin gani layi biyu ne.
Maryam ta rungumeta tana murna Alhamdulillah
Aishatu Allah Ya raba lafiya. Aishatu kuwa
jikinta har rawa yake tace na shiga uku na yau
me zan fadawa Fahad? Bangane ba Maryam ta
tambayeta. Abin arzikin ne kike cewa me zaki ce
masa? Karar babur dinsa ta ji yana turo shi cikin
gate din. Cikinta yayi wani mugun murdawa don
tsoro. Sosai Fahad yake jaddada mata rashin
son haihuwa a yanzu. Gashi ta dan samu saukin
irin yadda yake zama da ita. Ta fara zubar da
hawaye ba kakkautawa Maryam ta rike
hannunta suka zauna. Aishatu ko planning kuke
yi ne? Ita dai bata bada amsa ba ta tashi ta hau
sama a sanyaye.
Irin kallon tuhumar da yake mata yasa ta kara
tsorata kamar yasan abinda ya faru. Suna shiga
falo ya kama kofar ya kulle ya zaro belt din
wandonsa. Akan gwiwarta ta durkusa tana bashi
hakuri. Wallahi Fahad bansan haka zai faru ba.
Tsautsayi ne kayi hakuri.
Bai ko saurareta ba ya fara tsula mata. Har ni
zaki yiwa cuta irin wannan. Ta bude baki zata
kara magana yace rufa min baki makira. Dama
nasan har yanzu ba sona kike ba ahiyasa kike
min muguwar addua. To burinki ya cika na sami
carryover saboda haka kema haihuwarki ta kara
nisa. Sai na gama makaranta kamar yadda na
fada miki nayi service kuma sai na sami aiki. Ai
fadan da taji yana yi yasa ta fasa fada masa
tana da ciki. Gara tayi shiru kawai idan ya fito
idonsa ya gane masa.
Tun daga ranar aka koma gidan jiya. Ga rashin
wadataccen abinci ga wulakanci kala kala. Ko
kadan bata fada masa tana da ciki ba.
Wata alhamis ya dawo daga kasuwa a gajiye ga
yunwa bazai iya jira ya auna abincin da zata
dafa a lokacin ba. Indomie biyu ya dauko mata
yace ta dafa masa. Tun da ta dora amai yake
taso mata tana daurewa. Da kyar ta gama ta kai
masa ya bata guda daya yace ta dafa tace ya
kula jikinta ya fara budewa. Tana mikewa amai
ya kwace mata ta rinka kwarawa a wurin. Ya
tashi a fusace wai me kike nufi dani ne Aisha?
Ya zaki rinka min amai don ki haramta min
abinci. Abba dan maryam yana bakin benen ya
jiyo kakarin amanta ya ruga wurin mamansa.
Anti Aishatu zata yi amai Mummy. Da sauri ta
hau saman ta bude kofar falon. Aishatu ta gani
tana amai tana gyara wurin da ta bata. Duk tayi
kaca kaca da wurin. Maryam ta harare shi
amma kai dai Allah wadaran halinka. Mace na
fama da ciki kana kallo ka zuba mata ido tana
wahala. Ya kalli Aishatu da ta tsure ya kalli
Maryam. Ciki kuma??? Garin yaya? Me yasa baki
fada min ba. Baki na rawa zata yi magana
Maryam tayi saurin gyara zancen...dama
surprise zata maka to kuma yadda kayi mata
yanzu ne ya bani haushi shine na fasa kwan.
Sai da ta gyare wurin ta sauka a ranta tana
fargabar abinda zata jawowa Aishatu. Ai kuwa
taba fita sabanin ya nuna fushi sai ya nuna
kamar yana murna da cikin. Ai da kin fada min
da wuri saboda zuwa asibiti. Wata nawa ne
yanzu. Kai a kasa tace nima ban sani ba. Amma
ina jin zai kai uku. Masha Allah sannu kinji.
Sai dare yace ta dauko masa maganin da yake
bata na planning. Ya duba ya tabbatar bata
fashin shan maganin. Dan murmushin yake yayi
yana tunanin yadda zaiyi yasa cikin ya zube. Ina
shi ina 'ya'ya yanzu. Kuma sai ya rama abinda
tayi masa na muguwar addua. Ita kuwa Aishatu
ta gama saka rai da abinda ke cikinta. Duk
abinda Fahad ke yi mata bata damuwa burinta
ta haihu lafiya. Su Mama sai murna da ganin
cikin wanda har ya kai wata hudu. Fahad na
kwance akan gado lokacin ya rasa me ke masa
dadi don mamansa tace ya bawa Aishatu dubu
hamsin ta fara siyan kayan haihuwa. Sassaken
maganin daya karbo ya dauko yana kallo.
Gaskiya bazai iya bari ta haihu ba. Baya kaunar
'ya'ya yanzu ko kadan. Falo ya bita ya mika
mata jikon. Aisha ga wannan kisha saboda
saukin haihuwa. ta karba da hannu biyu nagoda
Allah Ya saka da alkhairi. Amin, bari na dauko
miki cup. Da kansa ya zuba ya bata. bata kawo
komai a ranta ba ta shanye shi tas. Cikin dare
suna kwance cikinta ya soma murdawa. Ta dan
taba shi Fahad cikina ciwo...wani murmushi ne
ya kwace masa yayi wata munafukar mika
sannu ko inyi miki tausa ne? Tana yunkurin
tashi daga kan gadon jini ya balle mata.
RASHIN GODIYA ✂ 12
Kuka Aishatu tasa masa Fahad don Allah ka
taimakeni kada na rasa wannan ma. Tasowa
yayi kamar gaske duk a rude. Bari na shiga toilet
gani nan zuwa. Bandaki ya shige ya bata lokaci
sannan ya fito. Zuwa lokacin Aishatu har ta fara
fita hayyacinta. Kinkimarta yayi kasa ya
bugawa su Khalid kofa Yaya don Allah ka
taimaka ka zo muje asibiti Aishatu ce ba lafiya.
Su ma duk sun rude haka Khalid yazo ya fitar da
mota suka tafi asibiti. Kafin su karasa Aishatu
tayi karamar haihuwa tayi barin cikin wata hudu.
Likitoci sun bata dukkan taimako don har wankin
ciki aka yi mata. Sai gabanin asuba ta farka
taga Mama da Hajiyan su Fahad a dakin. Suna
hada ido da Mama ta fashe da kuka. Hajiya ta
zo ta rungumeta...yi hakuri Aishatu qaddara ce
wadda bawa ba yadda zaiyi da ita. Ita dai
Aishatu kuka take yi kawai Mama tana bata
hakuri. Sai dare Fahad ya shigo...Hajiya ta fara
masa fada yace Hajiya ni bazan iya ganin
Aishatu a wannan yanayin ba. Duk mun gama
sa rai...sai hawaye sharr kamar yaro. Har kudi
na hada zan bata ta fara siyayya ashe ba
rabonmu bane. Mama tace haba Fahad kaine ya
kamata ka bata hakuri. Ku karfafi zuciyarku.
Haka suka yi ta basu baki. Baban Aishatu shima
yaji tausayin Fahad sosai don abinci ma baya ci
a cewarsa duk jikin matarsa ke damunsa.
Kwanaki uku da kwanciyar Aishatu tana bacci
dakin shiru Maryam ta tafi gida dama mata
kunu. Su Mama basu karaso ba sai ga Fahad ya
shigo. Ganin tana bacci ya hakince akan kujera
yana waya da Audu Kulli mai magani. Audu yace
mutumina kuma sai naji ka shiru ko maganin
baiyi bane.
Fahad yace inaaa mutumina ai gamu a asibiti
ma magani yayi kyau. Wallahi a ranar ma cikin
ya zube da daddare. Ai wannan karon allura
zansa ta rinka yi don naga maganin baya hana
daukar ciki. Da su na taho ma zan mayar da
sauran.
Sai da ya gama maganarsa Aishatu ta tashi rai
a bace. Allah Ya isa Fahad kuma wallahi sai na
fadawa su Hajiya. Ni ba karatu ba ni ba ga
haihuwa ba. Wace irin rayuwa ce wannan? Gara
ka sake ni in huta.
Mama ce ta bude kofar ta shigo...Aishatu ashe
baki da hankali har yanzu? Har yanzu baki
kwantar da hankalinki a gidan mijinki ba shine
kike cewa ya sake ki. Hajiya da ke bayanta tace
Hassana baki san halin Fahad ba. Allah kadai
yasan me yayi mata. Cikin kuka tace Hajiya
magani ya bani cikina ya zube.
Laaaahhhhh haba Aisha kada ki tona sirrinmu a
wurin nan. Mu bar zancen nan kawai bana son
abinda zai hada iyayenmu. Mama tace ko meye
Fahad ka fada don a gyara idan ma matsala ce
da ku ai gara kowa ya sani a daidaita ku. Ba
komai fa mama rigimarta ce kawai. Aishatu da
tayi saroro tana kallon Fahad don ta rasa inda
ya dosa. Hajiya ta ce kaga ba sa'anninka a
wurin nan ka fadi me ya faru ko mu fita mu
barka da matarka.
Hannunsa yasa a aljihu ya fito da maganin
planning da yake bawa Aishatu. Wanda ya
dauko ma har ya kusa rabi ya mikawa Mama.
Dazu da zan dauko mata kaya naga maganin.
Ashe shi take sha don kada tayi ciki. To da
Allah Ya kawo kuma shine suke zubewa. Ya fara
kuka....tace bata sona bazata yarda ta hada
zuria dani ba. Aishatu tasa ihu wallahi karya
yake min. Mama ta bige bakinta rufe min baki
mutuniyar banza. Duk abinda kika fada naji kafin
na shigo. Mungode tunda kin nunawa duniya
bamu isa ba. Hajiya ma bata ji dadi ba amma ta
daure kiyi hakuri Hassana mu bita a hankali.
Fahad yace banso fada ba don Allah kada baba
yaji zancen nan. Zamu daidaita a tsakaninmu.
Zance dai bai kare ba har aka sallameta. Kowa
ya juya mata baya banda Khalid da matarsa.
Har fadawa Alhaji abinda yaji Fahad na fadawa
Aishatu game da hana haihuwa yayi aka karyata
shi a gida. Sai da akayi mata fada sosai sannan
ta koma gidanta. Haka ta koma cikin rayuwar
kunci da bacin rai don wulakancinsa yafi na da
saboda goyon bayan iyaye da ya samu.
Wata shida da dawowarta yanzu ko abincinta
baya ci. Idan ya dawo gida zai auna mata
abinda yaga dama ta dafa taci sauran taci da
safe. Duk ta kara ramewa ga rashin kwanciyar
hankali. Wata rana tana zaune tana jin radio taji
ana bada labarin wata mata da ta zane mijinta
saboda baya bata abinci. Tayi dariya sosai taji
ina ma ita ce ta zane Fahad. Ai kuwa daren
ranar ya auna mata wake wai ta dafa taci da
mai. Yanzu don Allah a daren nan zanci wake?
Kaga fa tara da kwata idan naci cikina zai baci.
Daki yayi shigewarsa idan bazaki dafa ba ki
barshi mana. Nan take dabara ta fado mata,
tana jin alamun ya fara wanka ta tsala ihu iya
karfinta. shiru bai fito ba ta kuma yin ihun ga
maciji nan zai shigo bandakin ka fito Fahad.
Bata rufe baki ba ya fito jikinsa duk kumfa.
Akan kujera ya ganta a tsaye tana tsalle. Yana
ina ya rinka waige waige. Karkashin kofar daki
ya shije. Ni dai bazan kwana a nan ba kasa
zani. Ke bana son shirme bari na nemo maza a
waje su kore shi. Tace kai ma namiji ne...sarai
tasan ko a tv aka nuna maciji canja tasha yake
saboda ya taba saransa yana yaro a yadda ya
bata labari. Duk inda yaga abu a dan murde a
kasa ko tsumma ne ya rinka fada kenan.
RASHIN GODIYA ✂ 13
A baibai ya saka doguwar riga jikinsa duk yayi
jirwaye saboda kumfa da ta fara bushewa ya ce
ke ki tsaya a nan zan nemo masu taya ni fitar
dashi. Tace nima sauka zanyi, ko ka tsaya ka
fitar dashi kawai. Sai dai naga kato ne jikinsa
har sheki yake. Tsawa ya daka mata don a
tsorace yake yana ta waige waige...malama kiyi
min shiru kuma ban yarda ki sauka kasa ba, ya
fita da sauri. Tana jin ya sauka kasa ta
kyalkyale da dariya. Amma Fahad ya shahara a
keta, shine zai barta ita kadai da gaske ne ma
sai dai ya cutar da ita. Dakin ta shiga ta lalubu
keys din kitchen da yake fita dashi kullum ta
shiga toilet ta dauki sabulun wanka ta manna a
jiki yadda shatin key din zai fito a jikin sabulun
sannan ta mayar da key din inda ta dauko shi.
Wani bakin mayafinta ta dauko mai ratsin ja ta
murde shi sosai sannan ta jefa karkashin kujera.
Bayan ta gama ta ta koma falo ta cigaba da
ihun maciji.
A haka suka dawo suka tarar da ita. Ku shigo
tace hanyar daki yayi. Maza biyu ne bai damu
ba ya nuna musu hanyar dakin ya haye kan
kujera ya tsaya kamar yadda Aishatu tayi yana
bada umarni. Ku duba har karkashin gado da
cikin toilet din kunji ko? Ba kyauta zaku min ba
zan biya wallahi.
Dariya ta rinka cin Aishatu tana ta gimtsewa.
Can ta sauko kaga kamar gashi nan a kasan
kujera. Tana mika hannu ya sona ihu ki barshi
su zo su dauke kar ki taba. Ko sauraronsa bata
yi ba ta janyo mayafin tayi cilli dashi kansa. Ihu
ya kwalla tare da faduwa kasa a sume. Mazan
da ya kira kira suka fito tace ai ya fita ta taga
amma sai da ya fado masa a jiki. Suka taimaka
mata aka kai shi daki ta yayyafa masa ruwa ya
farfado. Tun daga ranar ya wani kara hade rai
kada ta raina shi, a nata bangaren kuwa dariya
yake bata sannan ta kai an yanko mata irin key
din kitchen da rana tana diban abinci kadan
yadda bazai gane ba ta dafa ta ci. Lokacin
horon yunwa ya kare.
Haka Aishatu ta rinka cin karenta ba babbaka
har na tsahon sati uku. Ranar alhamis da tsakar
rana tana zaune tana cin shinkafa da mai da yaji
ya shigo gidan ba ko sallama dama bai fita da
wuri ba duk yunwa ta isheta ga fushin ya hanata
zuwa Getso duba G. Juma. Tana cin abincin
tana mita ita kadai sai ganinsa tayi a gabanta.
Kallon da yake mata ba karamin tsorata ta yayi
ba. Cikinta ya dori ruwa....ya kalleta sai ki fada
min gidan uban wa kika sami abincin nan? Bara
kika fara ko roko, ko kuwa aljanu sun fara ciyar
dake? Nan take idea tazo kanta ta yi wani
murmushi sannan ta cigaba da cin abincinta.
RASHIN GODIYA ✂ 14
Ya sake cewa Aisha ba magana nake miki ba.
Nan ma bata kula ba ta cigaba da cin abinci
harda fara 'yan wake wake. Rai a bace ya kai
hannu zai dauke plate din ta fizge. Dama kanta
ba kitso sai kawai ta jefar da dankwalinta ta
canza murya. Tunda bazata iya yin ta maza ba
sai ta kara rage ta ta...idan ka taba mata abinci
zamu tabbatar munga bayanka Fahad. Dan ja
yayi da baya don idanunta ta kafe a kansa ita a
dole aljanu take yi. Ya danyi ta maza ke ni zaki
yiwa aljanun karya? Lallai tunda rashin kunyarki
har ta kai ga haka dole zanyi maganinki mara
kunyar banza. Aishatu dama ta samu! ta cakumi
wuyansa ta kwada masa mari wanda yayi
matukar shigarsa. Kumatunsa ya rike da kyau
idanunsa sunyi ja ya rasa tantacewa gaske ne
ko gangan. Sai dai Aishatunsa matsoraciya ce
bazata taba iya yi masa haka ba. Yarinyar da
sai yadda yayi da ita kuma ta kasa fadawa
kowa a gidansu. Baya ya kara matsawa Aishatu
tana kallon yadda jikinsa ke bari tace mu sittin
ne a jikinta. Munzo kwatar mata 'yanci ne
saboda irin cutar da kake mata. Ka zubar mata
ciki har sau goma...bakinsa na rawa yace
wallahi biyu ne kawai kiyi hakuri. Ta sake make
murya kai ni namiji ne ba mace ba. Kuma bazan
hakura ba sai ka gyara halinka. Idan ba haka ba
zamu dawo Fahad,idan muka dawo rayuwarka
zamu nema. Wayar chaja ta dauko ta rinka
zambada masa yana ihu har waje ana jinsa.
Tana jin takun Maryam ta dena dukansa ta
samu daidai kan kujera ta kwanta tana fitar da
wani irin sauti. Maryam ta shigo a tsorace
Fahad ihunka naji. Me ya faru? Jiki a sanyaye
yace Anti ashe aljanu gareta. Ji yadda ta rinka
duka na. Ki dauke ta kawai ku sauka kasa. Anti
maryam ta samo ruwa ta tofa addua ta shafa
mata. Ka kaita daki ka kwantar da ita ina jin
abin ya sauka. Amma me ya faru har suka
tashi? Yace daga yi mata wasa fa...abinci take
ci nace zan dauke plate din shikenan. Aishatu
tana kwance tana jin yadda yake karya. Kadan
ma ka gani ta fada a ranta. Daki aka kaita bata
dade da kwanciya ba sai bacci. Tana farkawa
Mama ta gani a kanta da Anti Lawisa suna mata
sannu. Har ta ma manta abinda tayi da farko ta
dan kalle su Mama me ya faru? Anti Lawisa
tace kwanta abinki sannu. Allah Ya kara sauki.
Mama dai bata yi magana ba sai kallon Aishatu
take tana tausaya mata.
Jinya sosai tayi har sati biyu. Abinci da kayan
kwadayi kala kala Fahad yake kawo mata
saboda yan uwanta da ke zama a gidan kullum.
Anti Maryam ma tana nata kokarin sosai.
Shi kuwa Fahad tsoronta yake ji don baya
yadda su kadaice a daki.
Ya dawo gida a gajiye ya nufi kitchen dibar
abinci don yanzu baya yadda ya takura ta.
Ciwon karyar ya sake tashi cikin dare ta masa
duka shiyasa ya fita harkarta. Yana kofar
kitchen din ya ji muryarta tana waya da kaninta
sadiq da baya gari tana fada masa abinda
tayiwa Fahad harda zancen macijin karya. Shi
kadai take iya fadawa sirrinta, tana magana
yana dariya. Kofa taji an taba ta juyo. Fahad
yaji duk yunwar da yake ji ta tafi ya ce mata ta
shirya su je gidansu gaida G. Juma yaji ance ta
shigo kano. Murna ta kama ta suka tafi ko
abincin bai ci ba. Gidansu Fahad suka fara shiga
yace da iyayensu su biyo su zasu gaishe da
kakarta.
Suna zazzaune a falo Baba yace ni fa bangane
wannan tara mu da kuka yi ba Fahad. Me yake
faruwa ne? Fahad yace babu abinda ke faruwa
ina so in sanar daku na saki Aishatu saki uku!!!
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Hajiyan Fahad
tace ka fara shan kwaya ne? Saki uku kamar
baka da hankali. Aishatu bata san lokacin da
tace Alhamdulillah a fili ba. Mama ta magareta
baki ji sakinki yayi ba kike hamdala? Iyayensu
babu wanda yaji dadin abinda ya faru. Fahad
dan sarkin kuka ya fara hawaye. Ashe Aishatu
ba aljanu gareta ba, na karya tayi kawai don ta
doke ni. Kwanaki ma macijin karya ta jefa min
na suma. Babu abinda bana yi mata amma
yarinyar nan na fuskanci rayuwata take nema.
Kowa yayi mamaki amma tunda ansan ba sonsa
take ba sai suka yarda. Aishatu kamar an cire
mata kaya tace ni bazan taba tona maka asiri
akan irin abinda kake min ba,amma idan na
cuceka Fahad Allah zai saka maka idan kuma
ni...Baba ne ya rufe ta da duka bata gama
magana ba. Ke dai anyi mutuniyar banza. Ki
dawo gidan sai muci abinda muke ci tare.
RASHIN GODIYA ✂ 15
Iyayen Aishatu sam sun ki fahimtarta. Bata da
wani sukuni indai ba tana tare da yan uwanta su
Nurain ba. A haka ta gama iddarta cikin kunci
da tsangwama. Mama har hantarar take idan
tayi magana, a dole suna bayan Fahad.
Da kyar da sidin goshi Baba ya biya mata kudin
WAEC. Ta dukufa karatu sosai saboda
shekararta uku rabonta da makaranta gashi ko
aji shida ma bata yi ba. Lokacin da result ya fito
tayi saar samun credits takwas da pass a
history. Baba duk abinsa yayi murna amma dai
ya kafa mata sharadin bazata cigaba da karatu
ba sai ta sake aure. A haka Aishatu ta kwashi
shekara daya da rabi babu abinda take yi sai
zuwa islamiyya da yin zobo da meatpie wanda
almajiri yake sayar mata tana biyansa. Shi kuwa
Fahad watansu biyu da rabuwa ya sake aure.
Matarsa yar kanin Alhaji ce wai nan anyi masa
auren huce haushi tunda Aishatu ta ki shi.
Yahanasu amarya dai bata da matsala da yan
uwansa. Hatta anti maryam da basu dena
mutumci da Aishatu ba suna zaman lafiya da
ita. Da yake ya saba da keta lokacin da ya fara
kokarin kwatanta mata irin zamansu da Aishatu.
Ranar da ya kulle kitchen yana fita tasa tabarya
dama turminta a baranda yake tayi rugu rugu da
kofar. Da ya dawo zai fara fada tace kar ma ya
soma idan ba yana so ta fada a gida bane. Irin
kayan ciye ciye da yake shigowa dasu da ya
cinye gaban Aishatu kuwa da karfi take kwata.
Tun yana hakuri har aka fara jin kansu. Bata
shiru yana fada tana fada. Karshe ma Alhaji ta
fadawa karya da gaskiya akan Fahad to sai tayi
rashin saa son dansa ya rufe masa ido yaki
yarda. Wata rana suna fada ta biyoshi har kasan
bene da tabarya saboda yaki siyo mata naman
miya. Da rarrashi Khalid ya samu ta hakura ya
aika aka siyo mata naman. Suna zaune a
falonsa Fahad ya dora kankara akan
kumburarren goshinsa Khalid ya rinka masa
nasiha. Fahad rayuwa fa bazata taba tafiya a
haka ba. Banda keta da hada sharri baka iya
komai ba. Hakika Allah SWT Yayi gaskiya da
Yace idan muka gode Masa zai kara mana, idan
muka ki kuma to azabarSa mai tsanani ce. Ka
fini sanin tun bata sonka Aishatu aka tilasta ta
aure ka har ta kwantar da hankalinta don ku
zauna lafiya amma kiriri ka rinka cutar da ita.
Ko sau daya bata taba fada min abinda kake
mata ba amma ai ina da idanu. Duk ta rame
kamar wata kazar mayu. Shiyasa idan ka fara
wannan kukan ko kadan bana yarda da kai
tunda tun muna yara ka iya wannan sharrin.
Fahad ya dan harare shi yana magana da kyar
saboda ciwo yace yanzu dai Yaya me kake son
cewa? Khalid yace abu daya ne kawai. RASHIN
GODIYA ga Allah akan ni'imomin da Yayi mana
komai kankantarsu masifa ne a garemu. Ya baka
mace tagari mai hakuri da sannin hakkin aure
amma sai da ka kaita bango ta yi maka bore.
Sau nawa kake dukanta da yin abubuwan da
zasu saka ta a cikin matsala da iyayenta? Duk
ta shanye saboda ka iya toshe duk wata kofa da
zata yiwa wasu bayani su fahimta. Bansan
cikakken abinda ya faru ba amma nayi imanin
laifinka yafi nata. Abinda kayi mata ne Allah Ya
baka mace irin yahanasu wadda bata barin ta
kwana. A sanyaye fahad ya tashi don ya san
gaskiya dan uwansa ya fada masa.
Cikin ikon Allah sanaar Aishatu tayi albarka dan
kudin da take samu ta ke tarawa a banki.
Sauran kuwa gidansu take taimakawa da kanta
duk da iyayenta basa gani bare su yaba. Maza
suna ta neman aurenta saboda yadda ta
murmure tayi kyau. Lokacin shekarunta ashirin
da biyu. Wani ma bazai yarda ba idan aka ce ta
taba aure. Rannan ta kira Maryam a waya su
gaisa khalid ya dauka yace suna asibiti ne anyi
mata aiki ta haifi mace. Aishatu tayi murna
sosaita tambaye shi asibitin don bazata iya
zuwa gidansu ba saboda surutun mutane.
Atampa tasa mai kyau wanda aka yiwa riga da
wrapper skirt sai mayafi babba da ta yafa.
Fuskarta kwalliya tayi kadan tasa takalmi mai
dan tudu sai yar purse dinta da ledar kayan
barka. Tayi kyau sosai ta fito tayiwa Mama
sallama zata fita...tabe baki tayi haka dai aka
iya sai yawon tsiya an kasa aure. Koda yake
waye zai auri mai dukan miji. Zuciyarta ba dadi
ta fita ta tafi. Sun sha hira sosai da maryam.
Suna zaune Khalid da Fahad suka shigo tare da
Yahanasu tayi wa maryam girki. Yaran maryam
na ganinta suka rungumeta suna murna.
Yahanasu ma sun gaisa lafiya ta gaishe da
khalid tare da dauke kanta daga Fahad tayi
musu sallama ta fice. Tunda Fahad ya ganta
gabansa ya fadi. Gaba daya ta canja ta kara
kyau. Fita yayi yabi bayanta yana kiran sunanta.
Kamar yana magana da dutse bus na tsayawa a
gabanta ta haye ba ko waige. Daga ranar Fahad
ya soma wani tashen sonta, zance kadan sai ya
sakota. Abu kamar wasa sai gashi bashi da wani
sukuni idan baije gidansu ba duk da bata fitowa.
Da baba yayi masa magana ma cewa yayi saki
uku cikin fushi ai a matsayin daya yake. Baba
yace abu daya zaisa ka kuma aurenta sai idan
ta auri wani ta fito. Shi dai yana kaunar Fahad.
Duk da baya son ya ganta da kowa dole ya karbi
shawara. Ganin bata sauraron kowa Fahad ya
tura mata kanin abokin shi Audu mai suna Tijjani
suyi auren kisan wuta ba tare da ta sani ba.
Anyi saa ta damu da rashin karatu babu wani
bincike iyaye suka shiga maganar duk da ba
wani sonsa take ba ta amince aka yi aure
saboda su baba sunce idan ta wuce wannan
shekarar ba aure zasu yi fushi da ita. Duk
abinda ake Baba da Fahad suke shawara yasan
auren kisan wuta ne. Amma idonsa ya rufe shi
dai a mayar da aurenta da fahad musamman da
yaga kudi sun fara zauna masa har ya sayi
mota. Anyi aure ita dai Aishatu tana zaune ne
kawai saboda biyayyar iyaye. Bayan wata daya
Fahad ya hurawa tijjani wuta ya sakota tare da
infection din da ya sa mata. Tana gama idda
Fahad ya dawo. Sai dai kafin ta bashi amsa
ciwo ya bayyana a jikinta. Hajiya tace bazata
yadda a mayar da aurensu da fahad ba. Da
kansa yace ai shi ya jawo mata har ma ya fadi
duk irin zaman da suka yi a baya duk don a bari
ya aureta. Shi da gaske yanzu sonta yake. Su
baba sunji kunya sosai tare da tsanar fahad.
Shiyasa duk yan kudin su da nata a neman
lafiyarta suke karewa domin sunyi nadama.
Alhaji da Hajiya ma sun bata hakuri sannan
Alhaji yace idan ya kuskura ya saki yahanasu
zaiyi fushi da shi.
Aishatu ta numfasa ta kalli Sauda wannan shine
labarina wanda da zan buda miki sosai sai mun
kwana a nan. Fahad yasa na tsani maza saboda
muguntarsa da tsantsar iya sharri. Sauda tace
Aishatu tabbas kinga rayuwa Allah Ya baki
wanda zai zama haske a rayuwarki.
RASHIN GODIYA✂ 16
Sai da suka yi sallar laasar suka koma asibitin.
Sajida da Islam basu so Aishatu ta tafi ba har
gate suka bisu suna daga mata hannu. Sun
zauna har shida saura babu Dr Rano babu
dalilinsa. Karshe Sauda ta ce mata gara su tafi
gida, nurse suka tambaya tace sai wani satin
ranar talata zai shigo. Suka yanke shawarar
dawowa ranar. Har phone number suka yi
exchanging.
*
Tamkar wata jaka haka Huzaifa ya rinka jan
hannun Fadila har suka shiga dakinsa ya bude
drawer din da yake ajiye kayan wanki. Wata
farar leda ya dauko ya bude ya fito da wando da
safa wadanda duk suke da digon ja a wurare
daban a jikinsu. Saboda bacin rai da kyar yake
iya magana ita kanta fadila ta gama tsorata da
yanayinsa..ba a nan kika dauko rigar ba. Kai ta
daga masa a hankali. Ya ce saboda kin gama
ginawa zuciyarki zargi baki dauko sauran kayan
ba kika fito da shirt din ita kadai ko. Sabo mai
wanki ne ya fada min ya jika su da wasu kayan
masu zuba wadannan sun baci shine na hadasu
a leda zan bayar. Idan baki yadda ba na yarje
miki ki dauki wayata ki kirashi ki tambaya. Yana
gama magana ya fice daga dakin ya koma falo
zuciyarsa na kuna ta rufe idanunsa.
Hasbunallahu kawai yake karantawa don a
yadda yake ji idan Fadila ta shigo hannunsa zai
iya yi mata rauni da duka.
Inda ya barta haka ta tsaya kusan minti goma
ta kasa fitowa daga daki. Wani irin so take yiwa
Huzaifa wanda bazata iya hada shi da komai ba.
Shiyasa take tsananin kishinsa. Duk irin yadda
mata suke nuna sonsa musamman abokan
aikinsa bai taba tunanin biye musu ba. Idan har
zai kula mace sai ya tabbatar aurenta zaiyi. To
bai tashi aure ba tunda ko shekara biyar baiyi da
auren fari ba shiyasa yake kama kansa. Hakuri
yake sosai da Fadila saboda irin yadda take
yawan zarginsa da yi masa rashin mutumci idan
abin ya motsa. Falon ta biyo shi ta durkusa a
gabansa tare da rike masa hannu. Abban Aliya
don......daya hannun nasa ya daga ya dakatar
da ita. Kada ma kice don Allah don baki san
girmanSa, isarSa da buwayarSa ba. Fadila ba
kya gode masa duk abinda ya baki sai ki rinka
hangen wani abun daban kawai don ayi ta zama
cikin tashin hankali. Bakin gwargwado ina
kokarin kyautata miki amma na rasa dalilin da
yasa ba kya kyautata min zato. Ko dai kin taba
ganina da wata a zahiri, waya ko text? A'a
wallahi duk sharrin shaidan ne kayi hakuri. Yace
ke zan bawa hakuri tunda kice aka yiwa laifi.
Abu daya nake so ki sani wallahi idan kika kaini
bango bazan nemi matan banza ba amma sai na
cika gidan nan da matan da suka fiki komai.
That is a promise. Baki bude ya barta a zaune
ya dauki key din motarsa ya fita.
Gidansu ya tafi ya shiga dakin Umma
mahaifiyarsa ya tarar tana sallar laasar. A kan
kafet ya zauna ya jingina bayansa da gado yana
jira ta idar. A nan bacci ya dauke shi saboda
gajiya da tension da suka yi masa yawa. Tana
idarwa ta kalle shi cike da tausayinsa. Filo ta
dauko zata gyara masa kwanciya yayarsa Kubra
ta shigo. Aurenta ne ya mutu ta dawo gida suna
ta rigimar wanda zai rike 'ya'ya ita da mijinta.
Sauri tayi ta karbi filon ta saka masa ya gyara
kwanciya ya cigaba da bacci. Tace yanzu
Umma wannan katon magidancin kike gyarawa
kwanciya sai ya karasa ki. Umma tace ina
ruwanki, danki ko nawa?
Wai ina ni ina wannan zabgegen dan kalen
hanjin. Nasan bazai wuce yar banzar yarinyar
nan bace ta bata masa rai. Kina ganinsa kinsan
bashi da kwanciyar hankali. Mtswww ina ma ya
saketa kowa ya huta. Umma ta harareta ke
bana son rashin hankali don kin kaso naki auren
sai na kowa ma ya mutu. Yaya Kubra tayi dariya
umma kinsan dai ba laifina bane. Umma ta ce
haka kuke fada ke da mijin naki magulmata
kuna so kuna kaiwa kasuwa. Dariyar Yaya kubra
ce ta sa Huzaifa ya farka. Yana tashi ya gaishe
su Umma tace autan umma yau ba aiki ne ka
dawo wuri? Wallahi umma akwai, wata yar
matsala ce ta....idanunsa ne suka kai kan
agogon dakin ba dai biyar da rabi ce zata yi ba?
Yaya Kubra tace ya lafiyar idon ne likita. Da
sauri ya tashi yana saka takalmi zan dawo ko
zuwa gobe ne umma yau na kusa karya alqawari
. Yana tuki yana adduar Allah Yasa yarinyar bata
jira shi ba. Sai yanzu ya tuna ma a gabanta
Fadila tayi wannan tsiyar. Karshenta ma ta
gama baza labarin kowa ya ji a asibitin. Wani
tsakin yayi ya cigaba da tukinsa.
A bakin gate ya ganta tana kokarin tare mota ga
wata mata daga cikin motarta suna hira. Har ta
samu za ta shiga yayi saurin tura maigadi ya
tsayar da ita. Kafin ya karaso ta shige mota ita
ma Sauda taja tata motar ta tafi. Hannu ya
buga kan sitiyari duk Fadila ce ta ja masa. Allah
kadai Ya san patients nawa ne suka tafi da
haushinsa a rai.
RASHIN GODIYA ✂ 17
Magungunanta na farko ta cigaba da sha sannan
ta rinka yin yadda likita da Anti Sauda suka bata
shawara. Ita kanta taji dadin jikinta kuma
wannan karnin ya ragu sosai ga kurajen duk sun
mutu. Mama sai washe baki take don murna
'yarta ta fara samun lafiya. Da yamma tana
sharar tsakar gida yaro ya shigo yace wai Aisha
tazo inji Fahad. Sai da gabanta ya fadi don
rabonta da shi zai kai wata shida. Daga bakin
yan unguwa taji wai aiki ya samu a Abuja.
Likafa ta cigaba ta fada a ranta. Ta san dole ya
karo wulakanci. Da can ma yana fama da lifan
ya aka cika. Mama tana daga daki tayi saurin
fitowa ta kalli dan aiken, kaje ka fada masa
babanta yace duk ranar da ya sake zuwa kofar
gidan nan hukuma ce zata rabasu. Dan banzan
yaro ga karyar tsiya. Aishatu ta kwashe da
dariya kai Mama sirikinki ne fa Fahad. Ni
gaskiya ki barni inje. Biyota tayi da maficin
hannunta tana cewa kaniyarki Shatu. Ita kuwa
daki ta ruga tana yiwa Mama dariya don ba
karanar tsanarsa tayi yanzu ba. Yadda yake iya
tara hawaye a idonsa ya fadi karya da gaskiya
yasa Mama tace ita tsoronsa ma take ji.
Yaro ya maimaita sako yadda aka fada masa
Fahad yace to nagode. Kofar gidansu ya koma
ya zauna har ya hango Mal Sa'id ya dawo zai
shiga gida. Sauri yayi ya tarar da shi suka gaisa
fuskar nan ta Baba a hade. Har mamakin kansa
yake yadda ya tsayawa Fahad akan Aishatu
kamar wani wawa. Yarinya duk tabi ta motse
amma a lokacin gani yake kamar ita ta jawowa
kanta. Fahad yace Baba don Allah kuyi hakuri
ku bari nayi magana da Aishatu ita ma na
roketa tayi hakuri.
Ba sai ka ganta ba inji Baba, zan fada mata
kuma tunda yarinya ce yar albarka nasan da
gudu za ta yafe maka. Kai ka sawa ranka ta
yafe amma wallahi ka nesanta kanka da gidana.
Duk irin magiyar da zaiyi yayi amma sam baba
yaki amincewa. Karshe ma dai shigewa cikin
gidansa yayi ya bar fahad a tsaye.
Sunyi waya da Anti Sauda har sau biyu. Mama
ma tayi mata godiya saboda yadda ta ke nuna
kulawa ga Aishatu. Ana gobe zasu koma asibiti
ta sake kira tayi mata tuni. Aishatu tayi mata
godiya sosai.
Sai karfe tara na dare ya dawo gida a gajiye.
Shopping din kayan abinci da sauran kayan
bukatun gida yayi. Boot din motarsa a cike har
seat din baya. Shi da maigadin gidansa suka
rinka jidar kaya suna shiga dasu store. Motsinsu
yasa Fadila fitowa da doguwar rigar bacci.
Huzaifa yayi mata muguwar harara saboda tana
ganin maigadi amma taki komawa ta sa ko da
mayafi ne. Sai da suka gama ya ce cikin fada
yanzu don Allah Fadila kin kyauta kenan? Ki fito
gaban M. Bala da irin wannan shigar ba ko baki
da aure ai kinsan tsiraici haram ne. Zumbura
masa baki tayi to ba gidana bane. Duk wanda
ya kalla yayi wa kansa, ta wuce shi ta shiga
kitchen. Tsaki yayi ya bi bayanta ga kaya nan ki
jera yadda ya kamata. Kinyi min papper soup din
kuwa? Dan tsaki tayi banyi ba wani film ne ya
dauke min hankali yanzu aka gama. Nayi tunanin
za ka yi aikin dare ne shiyasa ban yi ba. Huzaifa
girgiza kansa yayi kawai yace to ki fito da kazar
daga fridge ta dan saki kafin ki dafa.
Ai ban saka ba ma, ni tunda ka fita ban shigo
kitchen din ba. Yace a takaice dai kina nufin
tana cikin sink tunda na ajiye miki da azahar.
Bata kula shi ba ta dauko tukunya zata dora
yace ta barshi ya fasa zai sha tea kawai. Tace
to babu bread mantawa nayi ban kira ka ba.
Fadila what is wrong with you, me Aliyu zai ci
gobe? Kinsan baya cin komai sai bread da safe.
A hasale ya fita don ya gama kulewa.
Haka yasha tea da madara ya shiga wanka.
Yana fitowa wayarsa na soma ringing. Lokacin
shadaya saura. Kafin ya dauka Fadila ta riga
shi. Tana dubawa taga ansa lady K tasan mace
ce ta dauka ta fara masifa....to kadangarun
bariki masu hana matan aure sakewa da
mazansu. Me zaiyi miki da tsohon daren nan
kike kiransa. Muryar Yaya Kubra taji tace Fadila
rashin da'ar taki har yazo kaina? To tun wuri ki
shiga taitayinki ko na saba miki, shashashar
kawai. fizgar wayar taji yayi yana magana yana
harararta.
 RASHIN GODIYA ✂ 18
Daren ranar damuwar Fadila tasa da kyar bacci
barawo ya dauke Huzaifa. Gari na wayewa tun
bakwai da rabi ya fice. Fadila tana tambayarsa
ko zaiyi breakfast bai kulata ba ya tafi.
Sai da ya gama ward round a asibitin sannan ya
shiga office wurin karfe goma. Lokacin Aishatu
da Sauda suna zaune a baya suna ta hira. Yau
Sauda aka fara kira, bayan sun gaisa ya
tambayeta progress din da ake samu game da
jikinta ta sanar dashi. Yace to ya akayi baki zo
ba last week. Ko lafiya ta fara samuwa zaki fara
wasa da ita. Murmushi tayi haba Dr ai kasan ina
kulawa. Nazo last week kana cikin duba Aishatu
sai ka fita ita ma baka gama dubata ba. Mun
dawo around 5 muka jira shiru sai aka ce sai
yau za ka sake zama. Dafe kansa yayi da yake
masa ciwo, ta fada muku dalilin fitar da nayi
ko? Sauda tace eh to, cewa tayi kace idan zamu
iya mu dawo karfe 5. Sai da ya gama yi mata
tambayoyi ya kara mata wasu maganin ya ce ta
turo next patient. Har ta je bakin kofa taji yace
ita dayar kin santa ne? Sauda tace ai tana nan
ma muna tare. Na dai riga ta zuwa ne kawai.
Mutum uku ya gani bayan Sauda kafin Aishatu
ta shigo. Yau sai yaga tayi fes ba kamar
zuwanta na farko ba. Fuskarta dauke da
murmushi tayi sallama. Bin ta ya rinka yi da ido
har ta zauna bayan ya amsa sallamar. Dr ina
kwana
Ajiye biron hannunsa yayi sannan ya amsa lafiya
kalau. Ya jikin ina fata kina samun sauki.
Alhamdulillah da sauki. Yace to yanzu me yake
damunki? Yadda ta sunkuyar da kanta bata iya
bashi amsa sosai saboda kunya yana burge shi.
Gata kyakkyawa sai yau yayi noticing....she
looks so innocent.
Zafin bai tafi ba.
Kamar daga sama yaji muryarta a kunnensa. Sai
a lokacin ya dawo hayyacinsa. Ya kama zancen
zuci..amma Fadila kin cuce ni, ace daga ganin
patient na fara wasu irin tunani a kanta.
Hmmm kika ce zafin bai tafi ba ko? Eh ta amsa.
Allurai ya rubuta mata da wani magani na
shafawa. Ki cigaba da shan wadancan har su
kare. Wayarsa yaji an kira sai ya share ya
cigaba da bayani don yayi tunanin Fadila ce.
Godiya tayi masa ta tashi zata tafi aka sake
kiran wayar sai ya dauka. Abokinsa ne Abdul
wanda shi kadai Huzaifa ke iya sanarwa
matsalolin gidansa. Alama yayi mata da hannu
kada ta fita.
A yadda yake kallonta kamar wadda batayi
karatu ba sai kawai ya rinka magana da turanci
yana bawa Abdul labarin irin kuncin da yake ciki
a dalilin Fadila. Duk maganar da yake idanunsa
basu bar Aishatu ba. Ita kuwa kasa take kallo
amma tana tausayawa likitan da baiyi dacen
mata ba. Ko da yake samun wuri tayi. Ita idan
taga mace na yiwa miji iskanci har mamaki
take. A hankali taji ya ce Abdul i need a second
wife. Bata san me abdul din ya fada ba amma
dai ta ga Dr Rano ya sake kallonta yayi
murmushi.
Ajiye wayar yayi...kiyi hakuri na bata miki lokaci
sosai ko. Dama ina son baku hakuri ne game da
abinda kika gani wancan zuwan naki.
Murmushin da ya soma jindadin gani a fuskarta
tayi masa sannan ta mike tsaye. ba komai Dr
nan gaba dai ka dena hirar sirri a gaban
patients don da yawanmu muna jin yare daban
daban. Ba shiri ya tashi yana kiran sunanta ta yi
gaba. Maimakon yaji ba dadi sai ya sami kansa
cikin nishadi. Sai da ta fita ya tuna ashe kansa
na ciwo kuma yana jin yunwa.
Kai Aishatu kamar bazaki fito ba. Ina jin matan
can suna korafi wai ko hira kuke yi. Aishatu tayi
dariya ko daya Anti Sauda bari na karbo magani
mu tafi.
RASHIN GODIYA ✂ 19
Suna wurin karbar maganin suka ga sauran
likitoci da nurses duk suna ta tafiya hanyar
consultation rooms din da suka baro. Wata
nurse ta leko wurin mai bada maganin wanda
tuni dama ya tashi daga kan kujerar sa yana
kokarin fahimtar abinda ya kawo rudu haka a
asibitin. Tace masa Huzaifa ne yayi collapsing
yana cikin duba wata mata. Saurin tura
kujerarsa yayi baya yace da su Anti Sauda dake
tsaye jikin window ina zuwa don Allah. Da gudu
suka fice Aishatu ta kalli Anti Sauda da fuskarta
ta nuna alamun damuwa kin san wanda suke
fada ne? Eh likitan da muka gani ne. Aishatu
tace Huzaifa naji ance fa Anti ba Dr Rano ba.
Anti Sauda tace sunansa kenan ai. Amma kinga
bai kamata mu tafi ba ace daga fitowarmu wani
abu ya same shi. Duniya àbin tsoro, irin haka ne
sai kiji ana yanzu fa muka rabu. Aishatu tace ai
tunda bamu karbi magani ba dole mu jira.
Wuri suka samu suka zauna suna kallon yadda
ake ta kai kawo akan Dr Rano. Matar da yake
dubawa bayan fitar Aishatu sai bada labarin
abinda ya faru take. Yana cikin tambayata me
ya same ni sai naga ya rike kansa. Yayi kokarin
tashi kawai sai naga ya fadi kasa. Aishatu na jin
haka ta fara bawa Anti Sauda labarin da taji
yana yi a waya. Har cewa yayi rabonsa abinci
sosai tun shekaranjiya. Anti Sauda ta rike baki
wasu matan basu da godiyar Allah. Irinsu ya
kamata Fahad dinki ya aura. Uhmm uhmm
Fahad dinsu dai Aishatu ta fada tana dariya.
Sai bayan wurin minti talatin likitoci suka fito
daga emergency inda ake saka masa ruwa suka
koma bakin aikinsu. Sai ga patients suna shiga
da kadan kadan suna duba likitansu. Anti Sauda
ta ja hannun Aishatu tashi muje mu duba shi.
Mata uku ne a dakin suna fitowa suka shiga.
Yana ganin Aishatu gabansa ya fadi. Zaune
yake akan kujera ana masa karin ruwa. Sis
Risikat tace lallai Dr Rano ka tsorata mata irin
wannan yan dubiya haka..to gaskiya kowa ta
shigo mana da kaji da lemo sai mu san kun
damu da Dr dinku. Anti Sauda tace harda dawisu
ma. Dr Allah Ya sauwake. Risikat ta kalle
Aishatu kece niece din Lawisa ko? Ya jikinki
kuwa kwana biyu bamu hadu ba. Jiki yayi sauki
all thanks to Dr Rano. Tana magana yana
kallonta yarinyar nan ta gama sanin sirrinsa
tunda yayi waya a gabanta. Anti Sauda ta ce mu
zamu tafi Allah Ya kara sauki. Amin suka amsa
shi da Risikat.
Kofar dakin aka turo da karfi Fadila ta
shigo...idanunta kan Sauda da Aishatu suka
tsaya Risikat wadannan su waye? Me ya kawo
su dakin da aka kwantar da mijina?
Anti Sauda tace dazu ya gama duba mu kafin
mu karbi magani aka ce yayi collapsing shine
muka zo duba shi. Huzaifa ta kalla da tun
shigowarta ya rufe idanunsa don yasan sai tayi
wani abin da zai kara bata masa rai. Kaga irin
abinda bana so ko, idan nayi magana ace na
fiye kishi da zargi. Idan ba haka ba meye
dalilinsu na zuwa dubiya. Anti Sauda ta ce kiyi
hakuri fita ma zamuyi. Wasu matan ne biyu suka
bude kofar zasu shigo Fadila ta daka musu
tsawa suka koma ba shiri. Aishatu sai kallonta
take yi. Wace irin mace ce wannan da kishi ya
fiye mata akan lalurar mijinta. Risikat ta nuna
mata bakin gado zauna duk fita ma zamuyi Allah
Ya kara sauki Dr. An duba shi dai stress ne da
yunwa suka masa yawa. Fadila ta watsa mata
harara to na tambayeki ne uwar kinibibi. Dama
ance haka kuke yarbawa da shigewa mutane
jarababbu. Huzaifa hakurinsa ya kusa karewa ya
bude idanunsa da suka yi masa nauyi a
hankali...Fadila don Allah kiyi shiru. Risikat da
fuskarta ta kwabe kamar zata yi kuka ya kalla.
Ko shi ta girme shi bare Fadila. Aishatu ta tare
shi kafin yayi magana kiyi hakuri, ku zo ku tafi.
Fadila daga zaune tace umma ta gaida Aisha.
Risikat tace ni fa na fada miki ne don ki sa shi
dole ya rinka cin abinci kada yunwa ta sa masa
wani ciwon. A tsiwace Fadila tace ai ban
tambayeki ba. Ku kuma tsayuwar me kuke yi ne
haka, a tafi mana. Anti Sauda har ta bude kofa
Aishatu ta dawo ciki ta dan durkusa a gefensa.
Tun kafin tayi magana Fadila ta miki kamar an
tsikare ta. Aishatu ta wani kara rage murya
baby bari naje gida inyi maka kunu don ruwan
nan kadai bazai dauke maka yunwa ba. Ko
akwai wani abin da kake so? Zo ku ga idanun
Fadila...baby? baby fa ta kira ka Huzaifa. Shi
kansa da su Anti Sauda fuskarsu ta nuna
mamaki sosai suka tsaya kallon ikon Allah.
Aishatu ba kula ba don itama a tsorace take
kada Fadila ta rotsa mata wani abin a kanta.
Amma wani haushinta ne ya kamata tana zuba
iskanci an rasa mai nuna mata kurenta. Ganin
ya kasa magana tace baby ko jikin ne? Anti
Risikat ki fadawa dr azo a sake duba min shi.
Hawaye ta soma yi a hankali bana son ganinka a
wannan yanayin..ina ma ciwon ya dawo jikina.
Kifta masa ido Aishatu tayi don yasan wasa
take yi. Fuskar Fadila ya kalla. Ta gama hade
rai sosai ga hawaye kamar famfo a idanunta.
Sai kawai ya biyewa Aishatu. ki dena fadin haka
idan kika kwanta ciwo ya zanyi. A kasalance
yake maganar ki tashi ki je gida kinji Aish amma
da gaske ina jiran kunun kafin su Umma su zo.
Ta mike a hankali sai na dawo baby na. Yaya
Fadila ki kular mana dashi sosai. wani irin riko
taji fadila tayi mata tana ta zuba ashar irin
wanda kunne bai kamata yaji ba. Ni zaka yiwa
karya kace min baka da budurwa. Ke kuma yau
sai naga abinda kike takama dashi. Hannu ta
daga zata mari Aishatu wadda ta gama
kidimewa sai Anti Sauda ta rike ta. Idan kika
taba mij kanwa ni bazan kyaleki ba. Banza
wadda ta rako mata duniya. Kanina sai anjima
ta fada suka fita ita da Aishatu. Dariya sosai
suke yi Sauda tace dama haka kike? Aishatu ta
share hawayen idonta na dariya ke kuwa zama
da Fahad wasa ne. Kawai ji nayi gara in dan
nuna mata yadda ake tarairayar miji. Anti Sauda
ta yi murmushi dama na bari ta dan mareki. Ai
nasan bazaki fara ba. Don bakiji yadda cikina ya
kada ba da naji ta damko ni.
Fadila kuwa dirar wa Huzaifa tayi da masifa da
zagi yaci amanarta budurwarsa tayi mata rashin
mutumci yana kallo. har waje ana jin muryarta
saboda fada na cinta ko sau daya tunda ta shigo
bata ce masa ya jiki ba. Sai da ta gaji don kanta
ta dena. Kuma ba inda zani wallahi zan gani
idan zata dawo. Kunun ma in ta kawo sai nayi
mata wanka dashi. Tana cewa baby kana kiranta
Aish. Tayi kwafa wallahi har yau baka sanni
bane. Kuma sai na fadawa Daddy.
Huzaifa rufe idonsa yayi tana ta fadanta ita
kadai saboda bacci dake dibarsa yana
murmushi. Who is Aishatu ita ce tambayar dake
yawo a zuciyarsa.
RASHIN GODIYA ✂ 20
Anti Sauda ki gaishe min da su Sajida ni zan
wuce gida, Aishatu ta dan yi gaba. Bangane zaki
gida ba Sauda ta fada tana rike mata hannu.
Kizo muje gida ki dama kunun, anjima da kaina
zan kaiki gida mu gaisa da Mama.
Kunu kuma Anti Sauda, wane kunun?
Au har kin manta yanzu kika gama kiran mijin
wata baby har kina masa alqawarin kunu.
Dariya sosai Aishatu ta rinka yi. Amma dai Anti
Sauda ba kya sona. Wato na koma wannan
matar tayi min duka kenan. Ai ni ina tunanin
daga yau na dena zuwa asibitin nan don nasan
da ganinta za ta sa ayo mata farauta ta. Sauda
ta dage ita dai sai sunje an dama kunun..kika
sani ma ko daga nan abin arziki ya tabbata.
Aishatu ta girgiza kai rufa min asiri ina fama da
wari ko ta ina. Ni da aure ai munyi hannun riga.
Sauda bata hakura na tayi ta insisting ita so
take taga yadda Dr Rano zasu kwashe da
matarsa. Karshe dai Mama ta kira da wayar
Aishatu ta fada mata zasu zo gidan tare amma
sai sun fara zuwa nata. Mama ta ce to ba
matsala.
Aishatu dai a sanyaye ta bi Anti Sauda don ita
ko Huzaifan bata san da idon da zata kara
kallonsa ba. Su Sajida sunyi murnar ganinta
sosai. Anti sauda ta nuna mata komai na damun
kunun tace to sai ki dama yadda idan munje
kinga zanji dadin cewa ke kika yi. Cikin damuwa
tace ni dai Anti Sauda da mun bar wasan nan
haka kada shima yazo yana tunanin ko ni irin
matan nan ce marasa kamun kai. Anti Sauda ta
dafa kafadarta...Aishatu kinga dai bamu dade da
haduwa ba amma ina kaunarki tsakani da Allah.
Haka kawai naji ina sonki da Dr Rano. Auren
mazan da basa jin dadin matansu na gida yana
da riba idan kin iya takunki. Aishatu tace to Anti
me ya kawo zancen aure kuma. Zan dama
kunun amma bazan shiga asibitin ba. Ki kai
musu ki zo ki muje gida kawai. Anti Sauda tace
naji nagode.
Kafin ta gama Sauda ta shiga dakinta ta duba
kaya har kala biyar masu kyau da mayafai uku
duk masu kauri tasa a leda. Sai body spray kala
kala da turare mai kamshi har da panties
sababbi duk ta hada. A falo ta sameta su Islam
tana yi mata surutu. Korarsu tayi suka tafi suna
turo baki ta mika mata ledar. Aishatu ta duba
kayan da suke ciki ta bude baki tana kallon Anti
Sauda. Ni dai kafin kiyi tunanin na raina ki
wallahi duka kayan nan basu dade ba kuma ina
saka su. Sauran tarkacen kuwa duk sababbi ne
duba ki gani. Aishatu tace kada muyi haka dake
Anti Sauda. Ban baki don komai ba sai kawai
don na dauke ki kanwata. So nake ki gyara
jikinki muje asibitin nan...Aishatu ta daga gira
Anti kinki hakura da zancen Dr dinnan. Shine
kika hado ni da kaya, idan na saka naje gida
Mama zata yi fada. Anti Sauda tace zanyi mata
bayani da kaina. Kinga jikinmu kusan daya so
rigunan zasu miki daidai. Kuma duk wrapper
skirt ne don kada skirt din yaki yi miki daidai. Da
lallami da magiya ta samu Aishatu ta shiga
wanka. Irin kallon da ta ga Huzaifa na yi mata
tana fatan kwalliya ta biya kudin sabulu. Aishatu
ta sami sabulu mai kamshi tayi wanka ta gyare
jikinta sosai. ta fesa body spray kala kala
sannan ta saka daya daga cikin kayan da aka
bata. Falo ta fito Anti Sauda ta bita da
ido...kanwata Allah kinyi kyau sosai. Wannan
karon inajin rodi matar nan zata biyoki da shi.
Suka yi dariya sannan sauda ta kira mijinta ta
sanar dashi zata koma asibiti daga nan ta kai
Aishatu gida.Idan ya dawo kuma akwai labari.
Umma da Yaya Kubra sunyi sunyi Huzaifa yaci
abinci yaki wai bakinsa ba dadi. Ya Kubra ta
kira kanwarta Saddiqa tace ta taho masa da
kunu ko zai sha. Suna zaune suna taba hira
umma nayi masa fadan zama da yunwa. Fadila
dai bata yi magana ba don a cike take fam.
Ganin idon umma yasa ta dena masifar da take
masa. Daga baya ma ta fita waje yin waya.
Kwankwasa kofa akayi Yaya Kubra ta ce a
shigo. Anti Sauda ce ta shigo da dan kwandon
abinci wanda aka saka flask din kunu da cups
sai fruit salad da tayi mai sanyi. Ko baa fada ba
tasan dattijuwar da ta gani mai cike da kamala
babar Dr Rano ce. Sauda karasawa tayi gaban
Umma ta gaisheta sannan ta gaida Yaya kubra.
Harda dan sunkuyar da kai tace Dr ya jikin?
murmushi ne a fuskarshi ya amsa mata
Alhamdulillah da sauki. Hankalinsa duk yana kan
kofa ya ga ta inda Aishatu zata bullo. Sauda
tace ga kunun da kace kana so inji Aishatu,
Allah Ya kara sauki. Gidana nan kusa ne ko
gobe na dawo na dauki flask din. Mamakin
dawowarta yayi sosai Yaya Kubra tace baiwar
Allah bamu ganeki ba. Ni yayarsa ce ga umma
kuma mahaifiyarmu. Anti sauda tayi tsuro ta
rasa abin fada yau ake yinta...Aishatu na can
waje ita ana yi mata yar kure. Yadda tayi yasa
Huzaifa ya kusa dariya duk da bai yi tsammanin
zasu dawo ba. Ta fara cewa uhmm, uhmm
dama. Ya kubra tace ko dai karin aure zaiyi
dake. Ta firfito da idanu ni??? Da aurena wallahi.
Huzaifa yayi gyaran murya kanwarta ce ba ita
ba. Umma tayi murmushi Allah sarki yar albarka
shine ta aiko da kunu. Auta kace aure zaka
kara...kana ganin fuskarta kasan labarin yayi
mata dadi. Kara kawai take yiwa Fadila. Yaya
Kubra baki yaki rufuwa tace tana ina yanzu?
Anti Sauda tace waje....wai kunya take ji. Yaya
Kubra ta tashi muje mu shigo da ita su gaisa da
Umma. Huzaifa na tsoron kada karyar ta kara
gaba yace ki bari kawai zancen baiyi nisa ba.
Bata saurare shi ba suka fita. A cikin mota suka
ganta zaune, yays kubra tace kanwata fito mu
gaisa. Gaban Aishatu ya fadi taji ko'ina a jikinta
ya soma rawa. Kai karya ba kyau!
RASHIN GODIYA ✂ 21
A sanyaye ta bude kofar ta fito ta durkusa ta
gaisheta. Dadi ya kama Yaya Kubra ta kalleta,
dole Huzaifa ya so ki. Ina fata zaki rike min dan
uwa amana. Aishatu a rikice take kallon Anti
Sauda da ke faman kifta mata ido akan kada ta
ce komai. Ku zo muje ki gaisa da Umma,
mungode sosai da abinda kika kawo masa ba
irin wasu ba. Har sun kama hanyar komawa
Aishatu tace ammm don Allah tsaya kiji. Anti
Sauda ta rike mata hannu har tana matse shi
duk don tayi shiru. Aishatu ta girgiza mata kai
alamun bazata yi ba sannan ta sanar da Yaya
Kubra komai. Ji tayi ta rungumeta sosai. Allah
Yayi miki albarka Aisha. Kin yi min daidai
wallahi, ni da igiyar aurensa a hannu na take da
Fadila bata shekara a gidansa ba. Ba karamin so
yake mata ba, tun yana kau da kai har suka fara
fada sosai. Daurewa kawai yake da rabon
'ya'ya. Kuma Umma tana hana shi daukar
mataki. Duk kawaici irin nata baki ga farinciki a
fuskarta ba da taji zancen nan. Indai ba wani
gareki ba ki yarda kawai. Anti Sauda tace nima
haka na fada mata . Kuka kawai tasa musu, ni
fa ba cewa yayi yana sona ba. Ga lalura ina
fama da ita. Kuma bazan sake aure ba har
abada. Yaya Kubra tace kada ki kuma fadin
haka. Kuma ke da kike da lalura har akwai
wanda ya dace dake kamar likita ne. Suna ta
magiya ita dai jinsu kawai take har suka ja ta
zuwa dakin da aka kwantar dashi.
Mayafi tasa ta rufe fuskarta sosai. Ba umma ba
shima kansa kunyarsa take ji. Wani irin relief
yaji da ya gansu sun shigo tare. Ta gaishe da
umma shi kuwa ta kasa kallonsa ma. Yaya
Kubra tana dariya tace amaryar auta baki gaishe
da angon naki ba ko don kinga umma ne? Da
sun san yadda ta gama tsurewa babu wanda
zaiyi mata magana. Umma tace bari in fita naga
auta shima yau wai kunyata yake ji. Huzaifa
yayi murmushi cikin shagwaba haba Ummana
jira nake ta zuba min kunu in sha sai na farfado
sosai. La'ila ha ilallah. Sun gama rudata karshe
don maganarsa ta karshe sawa tayi ta fadi
zaune daga tsugunawar da tayi. Umma ta jefe
shi da mafici kuga min mara kunyan yaro zaka
sa taji ciwo. tashi tayi ta fita ta barsu. Yaya
Kubra tace to dan nema duk naji bayani daga
Aishatu amma ina so kuyi tunani kafin nan da ka
warke son mu san abin yi. Anti Sauda tace baki
ga da yadda na samu muka dawo ba. Huzaifa ya
dubi idanunta da suka yi ja fuskarta kamar zata
yi kuka yace Aish zo ki bani kunun soyayya
yunwa nake ji. Hawayen idanunta ne suka sauko
cikin kuka tace ni dai don Allah abar zancen nan
kada umma ta zata gaske ne. Na nawa kuma
inji Anti Sauda. Ai yanzu sai maganar sa rana
kawai. Huzaifa yace ai tunda kika kawo kanki
Aish kinzo kenan. Kubra ta mika masa hannu
yauwa dan gari. Zama suka yi suna ta rokonta
ta amince ta aure shi ko don Fadila ta dena
abinda take yi. Budar bakin Aishatu sai cewa
tayi ni ina da wanda zan aura. Anti kizo mu tafi
don Allah....Fadila ce ta shigo dakin rai a bace.
To munafukai har kun dawo? Ashe yarinya ba
kya son kanki da arziki. Flask din kunun ta
suntuma su Yaya Kubra suna mata magana bata
saurari kowa ba ta bude ta soma watsawa
Aishatu a jiki. Ihu tasa iya karfinta tana kuka.
Su Anti Sauda suka janyeta. Allah Yasa
mayafinta da girma jikinta bai kone sosai ba sai
kafarta. Huzaifa ya fizge drip din hannunsa ya
ture Fadila. Kina hauka ne zaki kona ta. Umma
ta bude kofar tare da wata nurse lafiya me ya
faru? Yaya Kubra tace kinga abinda Fadila
tayiwa Aishatu. Banda rashin mutumci irin naki
ko ruwa baki yi tunanin bashi ba tunda aka
kwantar dashi sai tsabar balai da yake cin ki.
Umma ta riko Aishatu da ke kuka rai a bace
tace Fadila na gaji da wannan halin naki. Ta
dubi Huzaifa shima ransa ya baci tace ka shirya
wallahi don daga nan gidansu yarinyar nan zani
na bawa iyayenta hakuri sannan zan fadawa
Yaya Babba yaje ya nema maka aurenta.
Fadila sai kuka wai shi da yan gidansu sun hade
mata kai idan ya gaji ne ya saketa kawai. Fita
tayi ta tafi gidan kawarta Wasila.
Ita kuwa Aisha tayi kuka tayi dana sanin shiga
sabgar da babu ruwanta. Sai da aka duba mata
wurin da ta kone aka bata magani sannan
Umma ta ce da Yaya Kubra ta ja mota su bi
bayan su Sauda sai gwammaja gidan Mal Sa'id.
RASHIN GODIYA ✂ 22
Aishatu kamar wadda tayiwa sarki karya haka ta
shiga soron gidansu tana ta rabe rabe. Anti
Sauda tana ta yi mata dariya tun a mota ta
dena kula ta wai duk ita ta jawo mata.
Su Umma suka fito suka shiga gidan tare.
Mahmoud kaninta ne ya fara ganinta jikinta duk
kunu. Yaya Shatu lafiya kinga jikinki kuwa?
Mama ta fito daga daki da sauri me ya faru?
Matan da ta gani ya dan tsorata ta. Wani abin
kika yi ne Shatu? Kuyi min bayani don Allah.
Fashewa Aishatu tayi da kuka ta rungume
mama. Yaya Kubra tace ashe ma raguwa ce ke,
har ta fara saki kuka tun yanzu. Umma ta ce da
mama ki kwantar da hankalinki babu abinda ya
faru sai alkhairi. Tabarma Aishatu ta shimfida
musu a tsakar gidan ta kawo musu ruwa sannan
ta koma cikin daki. Tana jin muryar umma tana
mata bayani danta ne yake son Aishatu yanzu
daga zuwa duba shi matarsa ta zuba mata kunu
a jiki. Ni dai nazo baki hakuri ne sannan in fada
miki wan babansa zai zo nema masa aurenta.
Mama gaba daya ta kasa fahimtar zancen, abu
daya ta kula da shi yadda Umma ta damu da
abinda aka yiwa Aishatu. To ni bani da abinda
zance muku yanzu. Idan babanta ya dawo zan
sanar dashi.
Sai bayan fitarsu Mama ta tsare Aishatu da
tambayoyi. Bata bata lokaci ba wurin labartawa
Mama komai...ta rike baki lallai Shatu ina ke ina
shiga irin wannan rigimar. Wallahi nima mama
nayi dana sani amma yayar nan tasa da Anti
Sauda sun ki yarda a fadawa Umman gaskiya.
Mama ta ce to kinsan babanki bazai yarda yayi
gangancin sake yi miki zabe irin na da ba. Kinga
ko zancen aure baya yi miki yanzu. Haka suka
yi ta tattaunawa har Baba ya dawo.
Kwana biyu a tsakani Huzaifa yaji sauki sosai
Umma ta takura masa da zancen Aishatu. Ga
Fadila tayi yaji daga gidan Wasila kawarta mai
bata shawarar mata basa zamewa mazansu
bayi. Dole miji yabi matarsa kuma ya kyautata
mata sosai. Gidansu ta tafi tana kuka wai su
Yaya kubra sun dake ta a asibiti. Ko kadan
babanta bai yarda ba don yasan halinta na
rashin bawa komai mahimmanci in ba kanta ba.
Maminta kuwa ta hau magana ta zauna suna
jiran Huzaifa yazo biko. Su Aliyu ma ya mayar
dasu wurin Umma kullum shima acan yake cin
abinci. Ya dawo daga asibiti umma ta takura
masa akan yaje Rano wurin wan babansa ya
fada masa zancen auren. Umma yarinyar nan fa
bamu gama daidaitawa da ita ba. Tana daga
kan kujera tace to kaje ku daidaita mana. Nifa
tunda naje na bawa iyayenta hakuri magana ta
kare. Duk da yana fata Aishatu bata da wani
tsayayye amma yana tsoron yadda abin zai
kasance. Umma ta katse masa tunani kaga auta
ka tashi ka shirya bayan magriba ka je gidansu.
Sannan gobe da rana Haj Rabi zata zo muje
bikon Fadila. To kawai yace ya tashi ya fita falo
inda sauran yayyensa mata suke zaune.
Babansu Dr Aliyu Ahmad Rano ya shekara goma
da rasuwa. Su biyar Haj Gaji ta haifa wadda
suke kira umma. Akwai Zainab, Kubra, Shukriya
sai Saddiqa wadda Huzaifa yake bi. Dukkansu
suna gidan mazajensu da yara banda Kubra da
suke ta rigima da mijinta akan babarsa da ta
takura mata. A halin yanzu yayi mata saki biyu
tana gidansu.
Wani sky blue din yadi yasa wanda yayi masa
kyau sosai. yasa hula da takalminsa yana fesa
turare yana tunanin yadda Aishatu ta kira shi
baby a gaban fadila. Murmushi yayi shi kadai da
ya tuna yadda fuskar Fadila ta canja saboda
kishi. Tabbas zai san yadda yayi ya auri Aishatu
don ya sami kan matar da yafi so banda
ummansa....FADILA.
 RASHIN GODIYA ✂ 23
Bai sha wahalar kwatancen da Yaya Kubra tayi
masa ba ya gane gidan su Aishatu. Wurin
parking ya nema sannan ya fito ya karasa kofar
gidan. Yana zuwa ya aika wani almajiri a fada
mata Dr Rano yana sallama da ita don bashi da
numbar wayarta.
Fahad na kofar gidansu tare da wani abokinsa
suna zaune kan boot din motarsa yaga lokacin
da motar Huzaifa ta wuce su har yana fadawa
abokin nasa kaga wannan motar ina sa ran
karshen shekarar nan irinta zan siya. Wannan
kuma sai na barwa Aishatu. Yahanasun kuma fa
ko ka siya mata wata ne? Bai kai ga amsawa ba
yaga wani kyakkyawan mutum ya fito daga
motar ya tsaya kofar gidansu Aishatu. Ita kadai
ce mace duk gidansu saboda haka ya tabbatar
wurinta mutumin yazo. Sauka yayi daga kan
motar yace kai ina zuwa ya karasa kofar gidan
ya tsaya. Huzaifa na ganinsa ya karaso gabansa
ya mika masa hannu suka gaisa. Kowa cikinsu
na ji da kyau da kudi ga shiga ta alfarma.
Sai da Mama tayi da gaske Aishatu ta gyara
jikinta ta fito. Mama tace kije don baki san inda
alkhairinki yake ba. Tunda yazo da kansa ai
kinsan ba da wasa yake ba. Ba a son ranta ba
ta kimtsa ta fita. Turus ta tsaya har sai da
gabanta sai da ya fadi. Huzaifa da Fahad ta
gani a tsaye. Fahad ya matsa mata sosai yan
kwanakin nan. Ba karamin so yake nuna mata
ba ga siyayya kala kala. Komai ya bayar mayar
masa take yi. Anti Maryam ma tazo kamfen don
tana son Aishatu ta dawo gidansa. Fahad din
yanzu dana da fa ba daya bane. Aishatu tace na
yanzu yafi cutata tunda ya jawo min wannan
mugun ciwon. Sai dai yau da gobe tasa kiyayyar
ta ragu har tana tsoron kada wata rana yaja
raayinta ta amince da aurensa. Tafi kowa sanin
Fahad green snake ne.
Wurin Huzaifa ta nufa yana jingine da motarsa,
Fahad ya biyo bayanta da sauri Aisha don Allah
ki tsaya. Ga mamakinsa dana Huzaifa sai ji yayi
tana cewa Huzaifa...baby na yi hakuri na barka
a tsaye. Ya kalli fuskar Fahad da ta canja lokaci
guda ya gano saboda shi tayi haka. Sai kawai
yace take your time my luv. Nasan kwalliya kika
tsaya yi min, and you look so beautiful. Tana
matsowa Fahad na binta a baya. Huzaifa yayi
kissing hannunsa yayi hura mata. Kunya taji
sosai tayi saurin rufe fuskarta. Tunda Fahad
yake baya jin ya taba ganin bacin rai irin
wannan. A fusace ya zo gabansu ke Aisha
iskanci kike a titi duniya na kallonki. Wane dan
iskan ne wannan yake biyoki har gida. Huzaifa
yace who gave you the right to insult my wife?
Fahad ya rinka kallonsu yace matarka kuma?
Wallahi Aisha as long as I live baki da miji sai
ni. Me zaki ci da wannan mutumin. Tace Fahad
ka fita harkata ko in hada ka da Baba. Huzaifa
ya dan bata rai yanzu ina kusa kike sa'insa da
namiji...haba Aish. Fahad ji yake kamar ya rufe
mutumin nan da duka sai dai yana tsoron kada
sauran chance dinsa na samun soyayyar Aishatu
ya rasa. Yace kaga malam yarinyar nan matata
ce so ka kyale mu muyi settling problems
dinmu. Tana daga gefen Huzaifa tace a da ba.
Saki uku ai ya yanke duk wata alaqa
tsakaninmu. Ran maza ya baci Fahad yayi kan
huzaifa yana neman suyi fada. Abokinsa ne
yazo ya janye shi da kyar yana ta zage zage wai
babu mai raba shi da matarsa. Suna tafiya ta
janyo mayafi ta rufe fuskarta. Ina zata kai
kunya a wurin Huzaifa. Yau ma ta sake
maimaita abinda tayi rannan. Kallonta Huzaifa
yake yi, tayi kyau sosai duk da ba wata kwalliya
tayi sosai ba. AISH!!! Yadda ya kirata yasa taji
wani iri a jikinta..
We need to talk, ina zamu zauna? Soron gidansu
ta kaishi don zance a cikin mota ba mutumcin
mata bane. Nesa dashi ta zauna kanta a kasa.
Shiru babu wanda yayi magana cikinsu. Can
yace ya jikinki ko akwai matsala? A'a ina shan
maganin da ka rubuta min. To kada kiyi wasa
dasu kuma duk wanda ya kare kafin ki sayi sabo
ki fara sanar dani. To kawai tace ta sake
sunkuyar da kanta. Aish kinga ta yadda Allah Ya
hada mu ko. Kin taimakeni nima na taimake ki.
Umma ta dage sai naje Rano na sanar da wan
baba maganarki. Aishatu ta dago kai ni dai
tsautsayi ne ya sa nayi abinda nayi. Ka bata
hakuri kawai ko kace ni nace na fasa. Its not
that easy Aish. Waye wannan mutumin da na
dazo? A takaice ta fada masa tarihin aurenta da
Fahad. duk da yaji haushin irin abinda yayiwa
Aishatu sai da yayi dariya sosai da tana fada
masa irin ramuwar da tayi. Kafin ta gama
labarin duk sun sake da juna. Shima nasa
labarin ya bata ta kara tausaya masa. Indai
bazaki damu ba Aish ki amince muyi aure. I
believe love will find its way idan muka fara
zama a matsayin maaurata. Ta dan kalle shi
saboda a hankali yake magana. Ta lura sam
baya son tashin hankali. To ka bari muyi
shawara da su Mama zuwa gobe. Ba damuwa
ya amsa mata, Ina wayarki? Kankame abarta
tayi don da kunya ta bari ya gani. Yayi yayi taki
bashi wai dariya zaiyi mata. Yace to shikenan
dama number dinki zan dauka. Tace bari na
fada maka a haka. yace naki wayon nima bazaki
ga tawa wayar ba. Sai goben zan dawo in sha
Allah. Tare suka tashi tana nade tabarmar duk
soron ya cika da kamshin turarensa yace Aish
kafin muyi auren zanso mu zama abokan
shawara. Tace ba komai mun zama ma. Har zai
fita ya waigo tana tsaye tana kallonsa. Saurin
kawar da kanta tayi yace baki ce goodnight
baby ba? Da gudu ta shige gida. Shima dama
tsokanarta yake. Cike da nishadi yaja motarsa
ya tafi gida.
RASHIN GODIYA ✂ 25
Kamar yadda ya fada a daren ranar yazo. mama
tana yiwa Aishatu kitso don yan unguwa sun
dena yi mata, nurain ya fada mata tayi bako.
Mama tace saura daya mu gama ka kai masa
tabarma soro tana zuwa. Tunda aka ce yazo
Aishatu ta kasa sukuni. Wani irin dadi taji a
zuciyarta. Ana gama kitson ta gyara jikinta don
yanzu ta dage wurin tsafta.
Kamshin turarensa wanda ta fara ganewa taji
tun kafin ta gama shiga. Da sallama ta shiga ta
samu wuri ta zauna daga gefe. Huzaifa ya bita
da kallo har ta zauna. Me yasa yarinyar nan
take affecting dinsa haka...ita ta fara gaishe shi
ya amsa sannan Mahmoud ya kawo ruwa da
kunun aya a jug. Kunun ya kalla zuba min
wannan Aish. Murmushi tayi ta kasa
kallonsa...ai da ka zuba da kanka. Why ya
tambaya yana kokarin hada ido da ita. Saboda
bani da lafiya mana. Ni banda yan gidanmu
babu wanda yake cin wani abu nawa. Aish! Ta
dago kai a hankali jin yadda ya kira sunanta. Ni
ba dan gidanku bane? Ta soma inda inda ba
haka nake nufi ba ai...yace to indai dan gidanku
ne zaki zuba ki miko min da kanki. Da ta mika
masa cup din idanunsa cikin nata ya shanye tas.
Wasu hawaye masu zafi ne suka sauko mata
yayi saurin ajiye cup din. Nayi wani abu da zai
bata miki rai ne Aish? Sai da ta gama kukan
tace tunda na fara ciwon nan banda yan
gidanmu kai da Anti Sauda ne kadai baku nuna
kyama gareni ba. Ta sa gefen mayafinta ta goge
idonta tana dan murmushi koda yake ranar da
ka fara ganina a asibiti....ya katseta kada ma ki
fara lokacin fa kina yar kazamarki ne. Tare suka
yi dariya sannan ya gyara zama. So what do you
think about us? Dan turo baki tayi a take yaji
wani abu a ransa sai ya wayance da dauko
waya a aljihu. Sai da ta rufe fuskarta sosai
sannan tace na amince. Alhamdulillah taji
yace...Aish na rasa abubuwa da dama a rayuwar
aure wanda sai mun zauna zaki fahimce su da
kyau. Amma a yanzu ina son kiyi min alqawarin
zaki yi kokarin zame min garkuwa a gidana. Ki
zama matar da babyn ki zai gani yaji dadi.
Kunya sosai ta rinka ji ta tashi zata gudu. Yace
dawo please ga wannan kuma kada kice min
bazaki karba ba. Ai kuwa kin karbar sabuwar
wayar da ya bata tayi. Yayi ta magiya amma
taki. Sai yace to ni gobe zani Rano muyi
magana da Kawu. Ina son inji muryarki kafin na
dawo. Wayarta ta mika masa wai ya sa number
dinsa ya yi ta dariya don baka ce tana amsa kira
ba. Tana kallo ya bude wayar ya zaro sim dinta
yasa a sabuwar wayar. A rikice tace Dr babana
zaiyi min fada fa. To ai bazan tafi ba ma sai
mun gaisa dashi. Ba haka kawai zan turo masa
iyayena ba bai sanni ba. Zan bashi wayar ya
baki da kansa. Ko an fada miki ke kadai ce
yarsa? Haka suka zauna suna taba hira har
Baba ya dawo ta tashi ta basu wuri.
Washegari da sassafe Huzaifa ya tafi rano.
Gidansu baban shi yaje, family house ne mai
dauke da barin duk 'ya'yan gidan harda na
babansa inda suke zuwa sallah a lokacin yana
da rai. Yanzu kuwa sai dai idan wani sha'ani ya
kaisu saboda kowa yayi aure. Umma kuma
bazata ji dadi zuwa ta zauna ita kadai ba. Gidan
nasu akwai hadin kai da zaman lafiya. Wurin
babban wansu ya fara zuwa ya sanar dashi
maganar aurensa. Matarsa Hajjo tayi murna
sosai ai gara ka kara aure ko ma cigaba da
zumunci da iyalinka. Aure shekara hudu amma
mu da matarka sai dai idan ta haihu. Kawu yace
mata iyayen zance kishiya indai ba taku bace
taje gidan kowa ma. Sun daidaita magana ranar
jumaa su kawu zaso zo kano. Huzaifa bai tafi
ba sai bayan laasar ya shiga sashen sauran yan
uwansa.
su umma sunje bikon fadila amma taki
amincewa ta koma. Yaya Zainab da aka je da
ita duk ta kule. Dama Yaya Kubra ta labarta
musu yadda ya hadu da Aishatu, Yayarsa
shukriya tafi kowa nuna son auren har da kubra
da aka yi komai a gabanta. Lefe suke hadawa
na gani a fada ko kwandala basu nema a wurin
autan umma ba. Su kawu sunje har Getso
neman aure Alh Dalhatu yaji dadin yadda dan
uwansa ya bashi girma wannan karon. G Juma
kuwa sai tsokanar baba take wai duk wanda ya
tuba don wuya ba lada. An tsayar da biki bayan
sati uku saboda dangin Huzaifa sunce basa son
a dauki lokaci sosai. Fadila ganin da gaske
auren nan ba fashi ta tattara ta koma gidanta
ganin mijinta ko waigenta baya yi ta yanke
shawarar maganin Aishatu idan aka yi auren.
Abinda bata sani ba duk abinda yake don ya
sami damar dawo da soyayyarsa da matarsa ne.
Kulawa dai sosai yana nunawa Aishatu kuma ko
da wasa baba yace kada ta taba nuna masa
Fadila tazo gidansu. Yace ai irin wannan zaman
iyawa ne Shatu. Bana so miji ya sanki da kai
kara tun yanzu. Kaji su Mal Said!!!
RASHIN GODIYA ✂ 24
Aishatu tana shiga gida ta fadawa mama duk
yadda suka yi da Huzaifa. To ke Shatu kin
tabbata kin amince da auren nan? Zaki iya zama
da kishiya? Aishatu ta ce ni dai Mama kuyi
shawara da Baba zuwa gobe. Basu bar wurin ba
ya shigo. Mama nayi masa bayani yace ba dashi
ba. Aishatu indai ba kina sonsa bane to bazan
yarda kiyi irin wannan auren ba. Ga ciwo a
jikinki yaje yana wulakanta ki ma. Bata nuna
masa damuwa ba, kullum adduarta akan zabin
Allah ne. Zuwa yanzu ta damu da lamarin
Huzaifa amma bazata iya yiwa baba musu ba
idan har yaki amincewa ta tabbatar babu
alkhairi. Sai dai tun da ta shiga daki take juyi
akan gado. Hirarsu da Huzaifa take tunawa ita
kadai tana murmushi.
Washegari da safe Mal Sa'id yana zaune a gefen
dakalin gidansa suna hira da wani makocinsa sai
ga mota ta zo kusa dasu da gudu har tana
watso musu kwata. Tare suka mike suna fada
matan dake cikin motar ko a jikinsu. Sai da tayi
parking suka fito. Kamar bata san abinda tayi
musu ba tace sannu baba ina neman gidansu
wata Aishatu ne. Baba yace ke mahaukaciyar
ina ce zaki bata mana jiki amma ki kasa bada
hakuri. Fadila ta yatsina fuska kaga malam
tambaya nake ka bani amsa idan ka sani. Wasila
tace ba kince kin biyo shi jiya ba kinga gidan da
ya shiga. Fadila tace ai kinsan dare ne ga uban
duhu. Ga gidajen kusan duk iri daya. Baba ya
kare musu kallo lallai yaran nan suna da
karancin tarbiya. Kofar gidansa ya nuna musu
ku shiga nan ne gidan su Aishatu. Hannafi
makocinsa yace ya ka nuna musu baka san da
me suka zo ba. Baba ya karkade rigarsa so
nake naga a inda shatu ta kwaso mana wannan
gayyar tsiyar. Bayansu ya bi shima ya shiga
gidan.
Mama na ta yiwa su Nurain fada sun ki tashi
daga bacci kosan da Aishatu ke soya musu na
safe ya soma hucewa. Fadila da Wasila suka
shigo gidan ba sallama. Aishatu na ganinta
jikinta ya fara rawa ai bazata taba manta fuskar
nan ba. Fadila ta kalli mama nazo baku shawara
ne ke da matsiyaciyar yarki. Kada tayi kuskuren
shiga gidana don kishi dani sai an shirya. Mama
tace to Allah Ya baki hakuri amma bazata aurar
miki miji ba. Wasila ta tabe baki an ga mai kudi
za a like masa. Ku siyawa yarku mutumci ku
bata miji daidai da ita. Aishatu sai basu hakuri
take Fadila na kiranta mara kunyar karya. Baba
yana tsaye a bakin kofa sai da suka gama
rashin kunyarsu suka wuce shi ko kallo bai ishe
su ba. Aishatu tana ta kuka don da gaske tsoron
fadila take. Baba ya yi gyaran murya...Aishatu
na ganinsa ta ce me ya sami kayanka? Bai bata
amsa ba yace da mama ku fara shiri in Allah Ya
yarda sai Shatu ta auri likitan nan. Har ni wata
yarinya zata yiwa fitsara don mijinta na neman
yata. Ya girgiza kai bata sanni bane wallahi
banda girma ya kamani da sai....
Mama tace yi hakuri malam. Aishatu tana
hawaye dob duk ita ta jawo wa kanta da
iyayenta wannan masifar tace baba kuyi hakuri
amma bazan yarda na aure shi ba tazo tana ci
muku mutumci. Baba yace ni bazan takura ki ba
kada a maimaita irin na da. Amma tunda ni naki
amincewa da fari yanzu na baki dama. Idan kin
amince ki sanar dashi ya turo iyayensa can
Getso gidan Yaya Dalhatu.
RASHIN GODIYA ✂ 25
Kamar yadda ya fada a daren ranar yazo. mama
tana yiwa Aishatu kitso don yan unguwa sun
dena yi mata, nurain ya fada mata tayi bako.
Mama tace saura daya mu gama ka kai masa
tabarma soro tana zuwa. Tunda aka ce yazo
Aishatu ta kasa sukuni. Wani irin dadi taji a
zuciyarta. Ana gama kitson ta gyara jikinta don
yanzu ta dage wurin tsafta.
Kamshin turarensa wanda ta fara ganewa taji
tun kafin ta gama shiga. Da sallama ta shiga ta
samu wuri ta zauna daga gefe. Huzaifa ya bita
da kallo har ta zauna. Me yasa yarinyar nan
take affecting dinsa haka...ita ta fara gaishe shi
ya amsa sannan Mahmoud ya kawo ruwa da
kunun aya a jug. Kunun ya kalla zuba min
wannan Aish. Murmushi tayi ta kasa
kallonsa...ai da ka zuba da kanka. Why ya
tambaya yana kokarin hada ido da ita. Saboda
bani da lafiya mana. Ni banda yan gidanmu
babu wanda yake cin wani abu nawa. Aish! Ta
dago kai a hankali jin yadda ya kira sunanta. Ni
ba dan gidanku bane? Ta soma inda inda ba
haka nake nufi ba ai...yace to indai dan gidanku
ne zaki zuba ki miko min da kanki. Da ta mika
masa cup din idanunsa cikin nata ya shanye tas.
Wasu hawaye masu zafi ne suka sauko mata
yayi saurin ajiye cup din. Nayi wani abu da zai
bata miki rai ne Aish? Sai da ta gama kukan
tace tunda na fara ciwon nan banda yan
gidanmu kai da Anti Sauda ne kadai baku nuna
kyama gareni ba. Ta sa gefen mayafinta ta goge
idonta tana dan murmushi koda yake ranar da
ka fara ganina a asibiti....ya katseta kada ma ki
fara lokacin fa kina yar kazamarki ne. Tare suka
yi dariya sannan ya gyara zama. So what do you
think about us? Dan turo baki tayi a take yaji
wani abu a ransa sai ya wayance da dauko
waya a aljihu. Sai da ta rufe fuskarta sosai
sannan tace na amince. Alhamdulillah taji
yace...Aish na rasa abubuwa da dama a rayuwar
aure wanda sai mun zauna zaki fahimce su da
kyau. Amma a yanzu ina son kiyi min alqawarin
zaki yi kokarin zame min garkuwa a gidana. Ki
zama matar da babyn ki zai gani yaji dadi.
Kunya sosai ta rinka ji ta tashi zata gudu. Yace
dawo please ga wannan kuma kada kice min
bazaki karba ba. Ai kuwa kin karbar sabuwar
wayar da ya bata tayi. Yayi ta magiya amma
taki. Sai yace to ni gobe zani Rano muyi
magana da Kawu. Ina son inji muryarki kafin na
dawo. Wayarta ta mika masa wai ya sa number
dinsa ya yi ta dariya don baka ce tana amsa kira
ba. Tana kallo ya bude wayar ya zaro sim dinta
yasa a sabuwar wayar. A rikice tace Dr babana
zaiyi min fada fa. To ai bazan tafi ba ma sai
mun gaisa dashi. Ba haka kawai zan turo masa
iyayena ba bai sanni ba. Zan bashi wayar ya
baki da kansa. Ko an fada miki ke kadai ce
yarsa? Haka suka zauna suna taba hira har
Baba ya dawo ta tashi ta basu wuri.
Washegari da sassafe Huzaifa ya tafi rano.
Gidansu baban shi yaje, family house ne mai
dauke da barin duk 'ya'yan gidan harda na
babansa inda suke zuwa sallah a lokacin yana
da rai. Yanzu kuwa sai dai idan wani sha'ani ya
kaisu saboda kowa yayi aure. Umma kuma
bazata ji dadi zuwa ta zauna ita kadai ba. Gidan
nasu akwai hadin kai da zaman lafiya. Wurin
babban wansu ya fara zuwa ya sanar dashi
maganar aurensa. Matarsa Hajjo tayi murna
sosai ai gara ka kara aure ko ma cigaba da
zumunci da iyalinka. Aure shekara hudu amma
mu da matarka sai dai idan ta haihu. Kawu yace
mata iyayen zance kishiya indai ba taku bace
taje gidan kowa ma. Sun daidaita magana ranar
jumaa su kawu zaso zo kano. Huzaifa bai tafi
ba sai bayan laasar ya shiga sashen sauran yan
uwansa.
su umma sunje bikon fadila amma taki
amincewa ta koma. Yaya Zainab da aka je da
ita duk ta kule. Dama Yaya Kubra ta labarta
musu yadda ya hadu da Aishatu, Yayarsa
shukriya tafi kowa nuna son auren har da kubra
da aka yi komai a gabanta. Lefe suke hadawa
na gani a fada ko kwandala basu nema a wurin
autan umma ba. Su kawu sunje har Getso
neman aure Alh Dalhatu yaji dadin yadda dan
uwansa ya bashi girma wannan karon. G Juma
kuwa sai tsokanar baba take wai duk wanda ya
tuba don wuya ba lada. An tsayar da biki bayan
sati uku saboda dangin Huzaifa sunce basa son
a dauki lokaci sosai. Fadila ganin da gaske
auren nan ba fashi ta tattara ta koma gidanta
ganin mijinta ko waigenta baya yi ta yanke
shawarar maganin Aishatu idan aka yi auren.
Abinda bata sani ba duk abinda yake don ya
sami damar dawo da soyayyarsa da matarsa ne.
Kulawa dai sosai yana nunawa Aishatu kuma ko
da wasa baba yace kada ta taba nuna masa
Fadila tazo gidansu. Yace ai irin wannan zaman
iyawa ne Shatu. Bana so miji ya sanki da kai
kara tun yanzu. Kaji su Mal Said!!!
RASHIN GODIYA ✂ 26
Shirye shirye ya kankama a gidansu Aishatu.
Zuwa yanzu Anti Sauda ta zama yar gida komai
da ita ake yi. Mal Sa'id ya dage karshe don yaga
ya fito da yarsa. So yake ya wanke duk abinda
ya faru a baya. Maimakon mama ta bata
shawara da kansa yake sa yarsa a daki yana
bata shawarar yadda zata tafiyar da sabuwar
rayuwarta. Sai ya gama kuma sai yace kiyi
hakuri Aishatu na bi son zuciya a baya na cutar
dake. Murmushi take yi tace babu komai. Kayan
kamshin jiki dana daki kala kala Anti Sauda ta
hada mata ga shi tana matsa mata taci abinci
sosai saboda jikinta ya ciko. Tace sauran sai
kin sami lafiya kanwata. A son ranta basai anyi
wani biki ba ita da zata yi aure na uku. Gidansu
Huzaifa suka ce basu yarda ba. Ko walima ne
ayi suna son gayyatar mutane kuma ya kamata
ango yazo suyi hoto. Har mai gyaran jiki aka
dauko ta dan gyara mata shima dai Anti Sauda
tayi alqawarin da lafiya ta samu jikin nan zai
kara shan gyara.
Iyayen Fadila ma sun yi mata fada tare da bata
shawara akan ta gyara zamanta da mijinta, ta
kiyaye maimaita abinda yasa shi neman aure da
wuri haka. Jinsu kawai take, da idanunta taga
yadda mijin wasila yake mata. Tamkar ma
tsoronta yake ji sannan baya kafa mata
takunkumi akan duk wani abu da ta bukaci yi.
Girki kuwa na masu aiki yake ci hankali kwance.
Ita dai tana son mijinta amma ko kadan bata son
aiki kuma ga korafi idan abu baiyi mata yadda
take so ba. A son ranta ta zauna suyi
soyayyarsu da mijinta amma ya dena expecting
wani abu daga gareta na daga aikin gida. Sun
riga sun gama shawara ita da wasila...yanzu ne
lokacin da zata nunawa kowace mace Huzaifa
bazai iya rayuwa babu ita ba. Ba karamin so
yake mata ba. Tasan da haka shiyasa take ta
tsiyarta son rai don tasan bazai iya sakinta ba.
Saura kwana hudu biki Huzaifa ya shigo gida da
kaya a wata karamar jaka. Sako ne daga yar
uwarsa Saddiqa da ta dinka musu shi da Aishatu
na fitar biki. Shadda ce tashi ash anyi mata aiki
mai kyau da silver zare sai wani hadadden ash
lace. Dinkin buba akayi da zani. Sai head da
wani silver mayafi. Hatta sarkar da Aishatu zata
saka Saddiqa ta hado a ciki don ita yar kasuwa
ce. Yawancin kayan lefen da suka kai akwati
takwas duk ita ta hado kayan. Ya tafi duba aikin
fetin gidan da akeyi Fadila ta zo ta dauki jakar
ta bude tana kallon kayan. Tabe baki tayi zaku
ci ubanku daga kai da amaryar taka. Wato har
anko zaku yi. Wata irin dariya tayi wadda tafi
kuka ciwo.
Huzaifa ya fito daga kitchen din da ake yiwa
Aishatu ya nemi jakar ya rasa. Dakinsa ya shiga
yaga Fadila ta saka kayan tana kokarin saka
sarka. Tana jin motsinsa ta juyu da sauri
fuskarta dauke da kayataccen murmushi tana
juyi a gabansa Abban Aliya nayi kyau??? Baki
bude ya tsaya yana kallonta. Fadila waye yace
ki taba min kaya? Gabansa tazo ta tsaya ta rike
masa hannu kayi hakuri Huzaifa da dukkan
abinda nayi maka. Kuma nagode sosai da kayan
nan. Nasan dai sai ranar biki zamu saka ko.
Thank you dear sai tayi masa kiss. Kasa
magana yayi har ta fita zuwa dakinta bari na
duba idan bani da matching shoe and bag sai
muje mu siyo wani anjima ko.
Tausayinta yasa ya kasa cewa ba kayanta bane.
Sai da ta fita ya fara tunanin yadda zaiyi don a
hanya har yayi wa Aishatu waya yana kwantanta
mata kayan. Saddiqa ya kira ya fada mata
abinda ya faru. Kin ga ita ma Fadilan abar a
tausayawa ce, baki ga yadda take kokarin
kyautata min ba yanzu. Tsabar takaici ya hanata
magana ta kashe masa waya tun bai gama
bayani ba. Fadila da ke labe a jikin kofa ta
toshe bakinta tana dariya. Sai ta nuna musu
itama mace ce.
Yaya Shukriya ta kira tana ta fada. Ke saddiqa
lafiyarki kuwa? Me ya faru kike ta masifa kamar
wadda ta zauce. Ta fadawa yar uwarta abinda
Huzaifa yayi. Sai kace wanda aka asirce Yaya.
Lace din dubu arbain ne wallahi na ajiye ma
Aishatu banda sarkar dana saka mata. Shima
tasa shaddar mai tsada ce ga kudin dinki. Haba
don Allah. Yanzu ma Yaya kubra zan fadawa.
Shukriya tace kada ma ki soma don sai taje
gidan ta karbo kayan. Kinsan halinta sarai. Su
biyu suka yanke shawarar yadda zasuyi. Kudi
suka hada suka kaiwa wani tela dinkin wani
lace din fari wanda yafi nada tsada da farin
yadi na maza shima mai tsadar gaske aka sake
dinkawa express. Kusan dubu tamanin suka
kashe sannan suka kira Huzaifa yazo ya dauka
a gidan Shukriya. Duk abinda suke ita dai
Aishatu bata sani ba. Godiya yayi musu sosai
akan irin yadda suke masa. Saddiqa tace Allah
idan ka sake bata Huzaifa sai na maka rashin
mutumci. A take ya kira Aishatu yace zai kawo
mata kaya da daddare amma farare ne. Tayi
amfani da light green shoe and bag saboda head
da sarkar light green din ne. Ita dai godiya sosai
tayi masa tace sai yazo. Lokacin saura kwana
biyu ayi bikin.
RASHIN GODIYA ✂ 28
Ran Huzaifa yayi matukar baci da ganin Fahad.
Hannun Aishatu ya ja suka koma wurin zamansu
yana ta bata rai. A haka dai taro ya tashi
zukatan maauratan babu walwala. Fadila tana
shaaninta amma tana lura da fuskokinsu. Dadi
ne ya kamata har suka fito zasu tafi tana faraa.
A bakin motarsa suka tsaya zasu tafi Kubra ta
taho rike da hannun Aishatu. Fadila tana saka
yara a mota zata shiga ita ma kubra tace ku
fito fadila sai ku tafi a motar Yaya Zainab.
Fadila ta hade fuska yaya bangane ba. Gida fa
zamu tafi. Huzaifa da ke gaisawa da abokansa
ya nufo su.. Fadila ta ce yaya kubra ce tace mu
koma motar yaya zainab. Na zata gida zamu tafi
yanzu. Kubra ta fara fada yau daya dai Huzaifa
kamata yayi ace kai kazo da Aishatu nan wurin ,
to tunda baka dauko ta ba ai sai ka mayar da ita
gida. Huzaifa ya tsaya yana kallon Yaya kubra
tana fito dasu Aliya daga motar. Ta ce muje
yaran albarka mu tafi motar Anti. Ba musu
yaran suka tafi suna murna saboda ga yan
uwansu a motar. Huzaifa ya kalli Yaya kubra ta
hade rai bai ga alamun wasa ba. Kuma shima
yana son tafiya da Aishatun. Aishatu tana kallon
yadda hankalinsa ya rabu biyu sai da ta ga
Fadila ta bude gaban motar zata shiga wai zasu
tafi da Aishatu su ajiyeta a gida sai su wuce,
har da yiwa Aishatu gwalo. Yamutsa fuska
Aishatu ta soma yi har Yaya kubra ta kula.
Lafiya dai Aishatu me ya sameki? Cikinta ta
nuna ta fara cijewa kamar dauriya take. Huzaifa
duk ya rude Aish sannu ya sata a bayan mota
ya taimaka mata ta kwanta. Fadila ki bisu su
ajiye ki a gida bari na je asibiti da ita. Yaya
Kubra tace idan muka ajiye yaran zamu taho
muma. ta leqa ta window Aishatu Allah Ya
sauwake. Tana soma tafiya fadila ta ce huzaifa
yarinyar nan fa kalau take. Tsabar iya barikanci
ne yasa take karyar ciwo. Hankalinsa gabadays
yana kan Aishatu yace kinga bana son surutu ki
bi su Yaya ku tafi. Nan ya barta a tsaye yaja
mota yayi gaba.
Basu yi tafiyar mintu biyu ba Aishatu ta tashi
zaune abinta tana kallon titi. Ba tare da ya juyo
ba yace Aish ashe kema kin iya rigima? Shiru
bata amsa masa ba. Yayi murmushi naga tunda
nazo ko magana baki min ba. Laifin me nayi?
Nan ma shiru ba amsa. Sai da yaje kofar
gidansu ta kama kofa zata fita taji ta a rufe. Ka
bude min na fita ta fada rai a bace. Ace ranar
aurenta har sai an fada masa abinda ya kamata
yayi mata, banda wulakancin da yayi mata na sa
kaya iri daya da uwargidansa kamar ba ita ce
amaryar ba.
Shiru yayi shima yaki kulata, ta soma dukan
kofar ni ka bude min sai kuka ya kwace mata.
Sai da tayi mai isarta fuska sharbe da hawaye
sannan ya fito ya bude mata kofa amma ya
tsaya ya tsare wurin fitarta. Gani tayi ya sake
cika mata ido kuma yayi matukar kyau. Sai ta
kawar da idonta don bazata juri hada ido dashi
ba. Aish kiyi hakuri don Allah nasan fushinki
harda na kayan dana saka da fadila ko? Ba
musu ta gyada kai. Kuma ciwon cikin ma na
karya kika yi don kawai ki rama ko? Nan ma kai
ta daga. Yayi ajiyar zuciya to kiyi hakuri haka
halinta yake. Duk abinda tayi don ta baki haushi
ne kuma tayi nasara tunda ko sau daya banga
fara'arki ba yau. Wayarsa ya dauko ya rinka
daukarta hoto tun tana turo baki har ta soma
dariya. Sai da ya tabbatar ta hakura yace to
bari na wuce gida kinga muna da tafiya Getso
da wuri gobe. Ta dan bata fuska ni fa abar
lallabawa ce yau tunda kayi min laifi. Ka bari sai
na ce ka tafi don kaina. Dariya yayi yana
mamakinta. Wani lokacin kunyarta har yawa
take. Wani lokacin kuma sai ta zama bold,
wanda hakan ma yana burge shi game da ita.
Rike kofar yayi har ta sauko ana jin hayaniyar
yan biki daga gidansu. Tace bari na karbo key
din nan, ta nuna masa kofar wani daki da ya ke
ta wajen gidansu. Bata jima ba ta dawo ta bude
masa. Dakin a gyare yake kuma dama don
hakan ta gyara shi. Bata jima ba ta dawo da
buta a hannu. Kayi alwala ga masallaci can a
kasan layi kaje kayi sallar isha. Ya dubeta da
kyau yau bazan tafi gida ba kenan. dariya kawai
tayi ta koma cikin gida. Itama sallar tayi kafin
ya dawo ta kai masa abinci. Tuwon masara ne
da aka kulla a leda da miyar kuka, ta sha wake
da naman kaza. Sai man shanu da yajin
daddawa. Tun kafin a fara shirin bikin tayi ta
ajiye saboda ta tuna a wata hirarsu ya fada
mata irin tuwon da yafi so. Ta hado masa da
ruwa mai sanyi sosai. A cikin gida ana ta
tsokanarta ta fice abinta tana dariya.
Yana dawowa dakin kofar a bude take sai labule
da ta saki. Ya shiga da sallama ya ganta da
kwanukan abinci. Wayarsa ta mika masa wadda
take ta ringing a cikin hularsa da ya bari a
dakin. Ya duba Fadila ce ta kira sau takwas.
Yana karba wani kiran ya shigo ya dauka yana
kallon fuskar Aishatu. Tuni ta gane ko waye mai
kiran sai ta dauke kai. Yana dauka yaji sautin
kukanta tana ta mita wai ina ya tsaya daga kai
Aishatu asibiti. Aishatu sai ta matsa kusa dashi
ta dan daga murya wayyo baby cikina. Sakin
baki yayi yana kallonta bai san lokacin da dariya
ta kwace masa ba. Yace Fadila kada ki damu
taji sauki na kaita gida. Dariya ya cigaba da yi
Aishatu ta kasa kallonsa, yayi nuni ga abincin
zuba min tunda yau rigimar fadila kike son ja
min. Tace rigima har ta wuce ta saka kayan da
kace za'a aiko min ranar bikina. Ya dan rage
murya kice kin fara kishina Aish...a'a ni ba kishi
nake ba. Murmushinsa ya kayatar da ita ta zuba
masa abinci yana ci suna yar hira yana mata
santi ya dade bai ci tuwo irin haka ba . Bai
ankara ba yaga karfe goma da kwata na dare.
Wayarsa da ya saka a silent yaga missed calls
din farida kusan dari. Kamar kada ya fita yace
Aish zanyi missing din rigimarki, da kunyarki da
wannan murmushin. Suka fita ta raka shi har
mota. Ya tafi yana zulumin tashin hankalin
fadila. Ita kuwa Aishatu a ranta tace Fadila kinyi
da yar halak. Kowa yaci bashina sai ya biya.
Duk da bata fada ba amma ranta yayi matukar
sosuwa da wulakancin da aka yi mata a wurin
bikinta don tasan bazai wuce sharrin fadila ba.
A haka zata taimaka masan yana biyewa Fadila
blindly?
 RASHIN GODIYA ✂ 27
Asibitinsu sun bashi hutun sati biyu yaje ya kai
musu invitation cards sannan ya wuce gida. Mai
kunshi ya gani ta gama yiwa Aliya ana yiwa
Fadila a falo akan karfet ko leda ba'a sa ba.
Ranshi ya baci sosai ya shige daki. Dama a
hannu daya aka yiwa Fadila tace da mai lallen
ina zuwa. Ledar da ya shigo da ita a hannunsa
ta nema ta rasa. Idonta tabbas ya gane mata
kamar kaya ne a ciki ta dan laluba wardrobe
dinsa bata gani ba. Jin motsin sa zai fito daga
toiley yasa tabar abinda take yi. Abban Aliya
sannu da zuwa...kin kula ta yayi ya dauko
jallabiya zai saka. Me nayi maka ne? yace ba
komai kawai. Wato bata ma san me tayi ba. Fita
tayi abinta ta koma aka cigaba da lallen. Idan ya
fita zata sake dubawa taga abinda ya boye daga
shigowarsa daki.
Ranar jumaa bayan laasar su Anti Lawisa da
sauda suka dauko mai kwalliya aka yiwa
Aishatu. Lallen kafarta da hannu ya fito sosai.
Mama sai kallon yarta take cike da kulawa. A
ranta tace Allah Yasa gidan zamanta ne.
Amarya tayi kyau har ta gaji. da yake ba fara
bace sosai kayan jikinta sun fito da ita sosai.
Tana ta kamshi...Anti Sauda da su Islam anko
suka yi suma duk sunyi kyau. Hudu da kwata
suka tafi wurin bikin. hall ne da yasha kwalliyar
da ta dace da kayan amarya da ango. A Jeep
din Yaya Zainab aka dauko amarya. Lokacin da
zata shiga mota Fahad yana kallonta daga kofar
gidansu ya yi sauri ya shiga mota. Gidansa yaje
ya saka farar shadda da light green din hula irin
kayan Aishatu ya dauko card din bikin wanda da
kyar ya samu daya ya shigo hannunsa tunda
bikin card admit ne ya fice. Huzaifa ya fito daga
wanka yana fesa turare Fadila ta shigo. Ba
karamin kyau tayi masa ba ya rinka kallonta har
tazo ta karasa fesa masa turaren a singlet
dinsa. Ya kalleta, uwargida ran gida. Kinga
yadda kika yi kyau kuwa? Ita dai dariyar keta
take masa a zuci. Jakar kayansa ya dauko
tunda ya riga ya kaiwa Aishatu nata. Ya bude
wandon yasaka ya bude rigar yaga wani abu
kamar miyar kuka. Meye wannan haka? Fadila
ta nuna tsoro ta ta karba tana kai rigar
hancinta. Kamar warin lalle fa. Ya fizge rigar da
sauri, lalle kuma? Me ya kawo lalle nan. Ya fara
kallonta cikin tuhuma Fadila wane irin wulakanci
ne wannan. Ban gane wulakanci ba. Wallahi bani
na taba maka kaya ba. Aliya ta kira suma duk
an shirya su sunyi kyau. Tace Aliya kece kika
bata kayan Abbanki da lalle? Aliya tace tsumma
ne fa Mummy na goge lalle dashi. A leda na
gani. Huzaifa ya kara harzuka yanzu Aliya
drawer din kayana ne wurin goge lalle? Ta kalli
mamanta sai ta soma kuka. Ita dai mummy ce
ta nuna mata ledar tace ta goge hannunta kafin
a wanke. Zata yi magana Fadila ta mareta tare
da korarta daga dakin. Huzaifa har yana hanata.
cikin bacin rai tace to yanzu wane kayan zaka
saka? Ya ce ina da fararen shadda da yadi bari
na duba. Sai dai ko daya bai samu ba Fadila
tace ni duk na hada su wanki jiya. Yanzu ma
naga yana shanya. Iyakar kulewa Huzaifa yayi
amma sai ya daure. Ta shiga duba kayansa wai
bari ta samo masa wani. Shi kuwa tunanin
fadan da zasuyi da Saddiqa yasa ya hakura yasa
ash. Zuciyar Fadila fes suka fito tare da mijinta.
Taro yayi taro amarya tana zaune ana jiran
shigowar ango sai gashi da abokansa sun shigo.
Wasila tasa Aliyu da Aliya daga gaba suma ash
din shadda aka dinka musu sunyi kyau sai
bayansu iyayensu ne Fadila da huzaifa suma
shigarsa iri daya. Sunyi kyau sosai sun kuma
burge mutane sosai. Aishatu tana hango su
hawaye suka cika mata ido...tabbas kayan da
ya kwatanta mata ne daga baya ya kawo mata
wasu daban. Hawaye taji ya taru a idanunta
suna barazanar fitowa. Hannu taji a kafadarta ta
dan dago kai. Saddiqa ce ta ke girgiza mata kai
alamun kada tayi kuka. Ita kuwa shukriya da tafi
kowa rauni sai da hawayenta suka sauko.
Saboda wulakancin da akayiwa Aishatu. Yaya
Kubra da yaranta suka zagayeta taca a hankali
sai kan uba. Amma Huzaifa sai na koya maka
hankali.
Har seat dinsa Fadila ta rako shi sannan ta
sauka ta zauna wurin kawayenta. aishatu
fuskarta ba yabo fa fallasa. Tun yanzu ta fara
sanin matsayinta...ana tsaka da taro aka bukaci
ango da amarya a filin rawa. Daga shi har
Aishatun da tunda yazo bata ce masa ko sannu
ba babu wanda ke rawar. Fadila kuwa ta cashe
tayi musu barin kudi sosai. Suna haka sai ga
Fahad from no where shima yazo yana rawa
yana kallon Aishatu. Sonta ke kara shigarsa
yana tunanin yadda zaiyi ko anyi auren ya
rabata da huzaifa.
RASHIN GODIYA✂ 29
Aishatu tana shiga gida ta kira Anti Sauda ta
fada mata yadda suka yi da Huzaifa. Yaba mata
tayi sosai tace ta cigaba kuma kada ta bari
tsoron fadila yasa ta dena abinda take yi. Shi
kuwa Huzaifa bai isa gida ba sai shadaya saura.
Ledojin biskit da robar lemo yayi karo dasu an
baza su a kasa. Fadila bata falon amma Aliyu
da Aliya suna zaune akan kujera suna kallo a
waya. A dan tsorace ma ya karaso ya gansu.
Suna masa oyoyo yace Aliya me kuke yi har
yanzu baku kwanta ba. Ya mika masa wayar
Fadila kallo mummy ta bamu muyi. Aliyu yace
sunan film din zaman auye. Aliya tace kai
zaman aure ake cewa. Ta cigaba da kallon
babanta, wata mata ce suka yi aure da wani
mutum tare ma suke kwana a gado fa abba. Ni
dai na fadawa Aliyu wuta zasu shiga. Karbe
wayar yayi hankalinsa a tashe ya kai su daki.
Kowa gadonsa daban yace su cire kayan jikinsu
don tun wanda suka je biki. Kunyi sallah kuwa?
Suka ce a'a. Zama yayi suka yi alwala ya nuna
musu suka yi magriba da isha. Aliyu yace
Abbana cikina yana ciwo, yunwa nake ji. Aliya
tace nima haka Abba. Lemo muka sha da biskit.
Zuciya ba dadi yace musu yana zuwa ya fita ya
tafi dakin Fadila. A takure ya ganta akan gado
taci kuka ta koshi. Itama bata cire kayan jikinta
ba ya soma mata fada. Yana yi tana yan wake
waken rashin mutumci. Ba abinda yafi bashi
haushi irin kallon da yaga yaransa suna yi gashi
an barsu a falo cikin dare. Dama mai aiki ke
dawainiya dasu gashi ta tafi gida neman
saurayi. Gajiya yayi da fadan ya koma dakin
yaran ya taso su ya basu tea sai ya tarar sunyi
bacci. Tare dasu ya kwanta a dan gadon Aliyu.
Bayan asuba ya shiga kitchen da kansa ya dafa
zuwan zafi ya soya kwai ya hada ma yaransa da
bread. Shiru Fadila bata fito ba har yayi musu
wanka ya shirya su suka ci abinci. Babu wanda
yayi cigiyarta ma. Dakin ya leqa tana baccinta
hankali kwance. Yayi tsaki suka fita. Gidansu ya
kai yaran suna ta murna Umma tace gandoki ai
ka riga duk masu zuwa getson zuwa. Sai karfe
goma aka gama taruwa suka dunguma zuwa
Getso. Shabiyu da rabi na rana aka daura auren
Dr Huzaifa Muhammad Rano da Aishatu Sa'id.
Fahad yana jin an daura auren hawaye ya sauko
masa. Yana kallo Huzaifa bakinsa har kunne
yana ta gaisawa da mutane. Aishatu tasa ce shi
kadai ko zata yi aure goma sai yasan yadda
zaiyi ya sake aurenta.
Gidansu Aishatu anyi yini su Anti Sauda aka
zauna sake bitar karatun zama da mijin Fadila.
Wanka Aishatu tayi aka kawo mata garwashi ta
sake turara jikinta. Idan bata fada ba yanzu
babu mai sanin bata da lafiya. Jikinta duk ya
ciko ga kamshi duk karni da warin discharge
babu. Pad take sakawa yanzu saboda discharge
kuma tana canjawa akai akai. Atampa tasa
wadda tasha dinki mai kyau sai katon mayafi.
Baba ya dade yana mata nasiha ita kuwa Mama
sai kuka. Anti maryam ma matar khalid tazo da
ita aka kai amarya gidanta. Tun daga waje ake
yaba kyan gidan, side dinta aka wuce da ita
mata suna ta guda. Yaya Kubra tasa key zata
bude kofa yaki shiga. Tayi tayi abu ya gagara
yan kawo amarya suka zauna ana kallon kallo.
Waya ta kira Huzaifa ko yayi mistake din key
yace ya tabbatar shi ya bata. Fadila bata
gayyaci kowa ba sai Wasila suka wuce su Anti
lawisa suna dariya har Wasila na cewa idan
kofar taki sai ku mayar da ita gida. Yaya Zainab
ta shigo kira Huzaifa tana ta fada don cikinsu
akwai tsofaffi harda kakar Aishatu G Juma.
Kuka kam Aishatu tayi Yaya Shukriya ta bawa
mutane hakuri daga baya suzo suga dakin
amarya. Da daidai aka tafi mata an sami na
surutu. Daukar Aishatu suka yi zuwa gidan
Umma. Tayi ta bata hakuri itama don sun gano
Fadila ce tasa aka canja key din kofar gaba
daya. Waya suka yi masa yazo gidan ya dauki
matarsa. Sai bayan isha ya sami zuwa lokacin
tana zaune kan abin sallah tana addua. Sai da
ya jira ta idar umma ta sake musu nasiha suka
tafi. Yau ma kin kula shi tayi don abin na fadila
ya fara yawa. shima baiyi attempting jan ta da
zance ba. Grand square ya shiga yayi yar
siyayya ya fito. Wani irin kamshi take mai dadi
da kwantar da zuciya. Ya kalleta yayi murmushi
Allah kadai Yasan me zata yiwa Fadila ra rama.
Sai ya sami kansa da son ganin abinda zata yi.
Fadila na jin shigowar motarsa ta fito da gudu.
Rigar bacci ce wadda da ita da babu duk ta
rungume shi tana kuka. Haba Abban Aliya yau
ka ja min zagi ka bada wrong key aka kasa
budewa amarya. Yanzu dole ta kwana a gidansu
ko gidan Umma ko. Zuwa gobe sai a canja
wani. Tureta Huzaifa yayi a hankali yana kallon
kofa suka hada ido da Aishatu. Ranta ya gama
baci ta daure sai ta shigo da sallamarta murya
kasa kasa. Katon mayafin jikinta ta cire, rigar
jikinta fitted ce ta kamata tsam da skirt din. Ta
kwance dankwali gashinta ya zubo har baya.
Kukan shagwaba ta saka tun kafin ta gama
shigowa Huzaifa yayi murmushi yasan ramuwar
ce ta tashi. yau da wata ya aura kila sai ya
zane fadila amma Aishatu ma ta isheta. Yace
Aish me ya faru ne? Miko masa mayafin tayi da
dankwali...ba kaine ka barni da kaya ba. Kuma
duk sunyi min nauyi. Ni dakin ma bazan iya
karasawa ba. Karbar kayan yayi tana ta
kwarkwasa....tana kara shiga zuciyarsa. Fadila
ta soma zage zage shegiya karuwa. Don bakin
naci da kika biyo shi ina zaki kwana. Huzaifa
zaiyi magana Aishatu ta girgiza masa
kai...babyna mu tafi daki ni na gaji. Ya rike mata
hannu suka wuce dakinsa wanda Fadila ta gama
gyarawa sosai ya sha turaren wuta. Suna tafiya
fadila ta fizgo mata riga ta baya wallahi baki isa
ki shiga ba. Huzaifa bafa zan yarda da wannan
rashin mutum....tas taji ya dauke ta da mari.
Fadila ki kiyayeni wallahi. Kin fara kai hakurina
karshe.ke dai ki kuntata min shine jindadin
rayuwarki. Akan Aish zan miki abinda baki taba
tunani ba. Tunda suke bai taba daga murya yana
mata fada kamar yau ba. Wannan munafukar
yarinyar bazata zo ta hanata zaman lafiya ba.
Tana kallo suka shiga dakinsa harda sawa kofar
key.
 RASHIN GODIYA ✂ 31
Juye yuye Huzaifa ya rinka yi bacci ya
kauracewa idanunsa, ya cire rigarsa don ya
ragewa kansa nauyi amma duk a banza. Bai
taba tunanin zai kara aure ba saboda Fadila dai
gashi yau saboda itan dai yana kwance gado
daya da wata a matsayin matarsa. Ya rasa
dalilin da yasa ya kasa bacci. Aishatu kuwa
tsabar gajiya ce tasa ta baccin dole. Idan ya
tuna yadda yaji lokacin da ya rungumeta sai yaji
kamar ya janyota jikinsa yanzu ma. To amma ya
Aish zata dauke shi? Yayi dan tsaki indai yayi
sharing gado da ita bazai jure nisanta daga
gareta ba. Shi kadai yake ta saka da warwara,
karshe dai filo ya jefa kasa ya kwanta.
Kiran farko na asuba ne ya tasheta. Kanta yaso
ya juye har ta manta inda take. Ta duba gadon
da kyau ta tabbatar ita kadai ta kwana a kai.
Zuciyarta taji tayi mata nauyi da tayi tunanin ko
kyamarta tasa yaki kwana akan gadonsa. Kawai
sai bata ji dadi ba.
Tana sauke kafarta daga kan gadon ya fito daga
toilet. Ganinsa ba riga yasa taji kunya sosai tayi
saurin dauke idonta. Gani tayi ya kara mata
girma da kwarjini. Ya kawar da shirun dake
tsakaninsu kin tashi lafiya Aish. Ta gyada masa
kai ba tare da tayi magana ba. Yanayinta ya
canza idan ya dawo daga masallaci zai
tambayrta abinda ke damunta.
Yana bude kofar dakin yayi karo da abu a
dunkule a kasa a cikin falonsa. Ya dan ja da
baya sannan ya shuri abin da kafa. Muryar
Fadila yaji tana cewa wallahi Huzaifa baka isa
ba. Ya kara shurinta ta tashi a firgice. Tsabar
masifa na cinta mafarki take wai Huzaifa ya
kara auro wasu matan. Yace me kike yi a kofar
dakina ko a nan kika kwana? Ban sani ba ta
amsa tare da tashi tayi hanyar fita. Ya dan riko
mata hannu sannan yayi magana daidai saitin
kunnenta ki dena labe saboda kada kijiyo wa
kanki sirrin boye. Yadda yake maganar yana
lumshe ido yasa ta ture shi ta fice.
Wurin karfe tara ya fito ya shiga wurin Fadila.
Akan doguwar kujera ya tarar da ita a falonta
tana zaune. Ko da ta ganshi kawar da kai tayi.
Ya karewa falon kallo Allah kadai yasan
rabonshi da shara. Kila tunda mai aikinta ta tafi.
Ga dukkan alamu ma akwai wani abu mai tsami
a dust bin din falon don ana shigowa zai daki
hancin mutum.. kusa da ita ya zauna kinci
abinci kuwa? Tace cikin tsiwa bana son gulma
don nasan cin nawa ba damunka zaiyi ba. Yaji
zafin abinda ta fada sai ya share. Ki tashi ki zo
falo an kawo abinci daga gidan umma. Idan kin
gama kizo dakina ina son magana dake. Bai jira
amsarta ba ya tashi.
Ya rasa wannan tura baki na Aishatu tun asuba
da ta tashi. Tayi wanka babu kayan sawa
saboda nata suna kulle a side dinta. Ya zauna a
kusa da ita a kan gado sai yaga ta dan matsa.
Yayi dan murmushi A haka zamuyi kawancen
kina zumbura min baki Aish, Ko dai nayi laifi ne
ban sani ba? Eh .....subhanallah me nayi miki.
Ta sake turo baki, hakan yana bashi shaawa
game da ita. Tace kana kyamata ko? Tambayar
yaji ta wani iri yace me kika gani? Sai ta dukar
da kanta saboda ya kafe ta da ido...gani nayi ka
kwanta a kasa. Sai tayi tunanin kada ya
fassarata kuma da wata manufa. Uhmm ina
nufin da ka barni a kasan ko...ba komai dai abar
zancen. Hancinta ya ja har ta danyi kara. Ki
dena irin wannan tunanin Aish. Ko har kin manta
maganarmu ta jiya? naga duk kin ruda kanki
,tambayar ma kin kasa yinta sosai. Kina son
sanin ko ina kyamarki ne ko amma kina tsoron
kada nace kina son kwana kusa da mijinki.
Murmushi ne ya kufce mata ta kasa dago kanta.
Bana son takura miki shiyasa amma da ina
kyamarki ai bazan aureki ba. Amma yau haka
zamu kwana ya nuna mata yatsunsa guda biyu
a hade. Ba shiri ta tashi ni ba nufina kenan ba.
Ni kuma nufina kenan my dear best friend.
Amma seriously ya kike jin jikinki yanzu? Babu
kurajen sai kaikayi wani lokacin. Yace discharge
fa? Akwai amma bai kai na da ba. To
Alhamdulillah sauki ya fara samuwa. Irin
wannan infection din naci gare shi ki cigaba da
shan magani. Kuma tsaftar nan kada ki
sassauta mata. Anjima zan siyo miki wani ma.
Godiya sosai tayi masa yana dariya yace kinga
fa bana son godiya malama kawai ki kawo kudin
consultation. An fada miki ana ganin Dr kyauta
ne? Aishatu tace to da me zan biya Dr Rano?
Bugo kofar dakinsa kamar zaa balleta yasa ya
fasa magana. Fadila ce ta shigo da alama har
yanzu batayi wanka ba. Ganinsu da tayi zaune
kusa da juna yasa ta harari tace Aishatu to
jarababbu da sanyin safiyar ma. Huzaifa ya
daka mata tsawa kina hauka ne zaki shigo min
ba sallama..kuma ki kiyaye abinda ke fita
bakinki kada ranki ya baci. Samu wuri ki zauna
mana kin tsaya min a ka. Aishatu tace ina
kwana? Fadila ta yatsina fuska a hankali tace
yana wurin uwarki. Sarai tasan sunji. Huzaifa ya
yunkura zai tashi cikin fushi Aishatu ta rike
masa hannu. Baby dan karasa shafa min man a
bayana mana. Dama wata jallabiyarsa ta saka
Fadila tana ganin ya mika hannu ta tashi
wannan karuwancin ba dai a gabana ba. Dama
kiran na wulakanci ne? Ya ce ga wanda ya
wulakanta kansa ba.
Bayan yan mintuna dakin yayi shiru Huzaifa yayi
musu nasihar zaman lafiya sannan yace idan
Aishatu ta gama kwana ukunta a matsayinta na
bazawara zasu raba kwana two-two days.
Sannan ya gargadi Fadila akan rufe kofar side
din aishatu. Zansa a saka sabun handle yanzu
amma Allah kika sake a gidanku zaki kwana.
Itama tayi dana sanin yin hakan don gashi dakin
da take jimawa bata gyara ba ta zage ta gyara
wata daban ta kwana a kai.
RASHIN GODIYA ✂ 30
Huzaifa na rufe kofar gaban Aishatu ya fadi.
Wani tsoro ya saukar mata ta kasa karasa shiga
dakin. Irin kallon da Huzaifa ke yi mata yasa taji
kunyar kayan jikinta ta mika hannu zata karbi
mayafinta da ta bashi. Boye shi yayi a bayansa
tace don Allah ka bani...kwaikwayonta yayi yace
don Allah naki. A hankali ya matso kusa da ita...
har suna jin sautin numfashin juna yace ba don
ni kika yi wannan kwalliyar ba. Tayi dan
murmushi tare da sunkuyar da kanta kasa.
Hannunta ya rike ya ja ta har bakin gado sannan
ya zaunar da ita. Ya zauna a daidai saitin
kafafunta daga kasa. Ya kallonta yace Aish you
always amaze me. Nayi mamakin yadda mijinki
na fari ya kasa fahimtar ki har ya rabu dake.
Maganar Huzaifa tasa hawaye ya cika mata
ido....muryarta tana rawa ta soma magana.
Shekarata 17 aka yi min aure. Kuma kamar
yadda na fada maka Fahad mugun mutum ne.
Bazaka fahimce shi ba sai zama ya hadaku. Sau
tari mutum baya gane ni'imar da Allah Yayi
masa sai ya rasa ta. Duk musulmin kwarai yana
da kyau yayi godiya ga Allah a halin samu ko
rashi domin duk abinda Ya bamu yana tafe da
alkhairi. Rashin godiya ga Allah akan kyautarSa
garemu yana jawo mana asara mai yawa. Kaga
dai yadda Fadila ta gigice akan auren nan
wanda ita ta jawowa kanta. Shima Fahad har
yau bai fidda ran sake aurena ba. Kaga a da
basu nuna damuwarsu yadda ya kamata ba sai
yanzu da suka ga zasu rasa abinda da basa
bashi mahimmanci. A shekaru ashirin da hudu
nayi aure uku, ina fata ka zama mijina na
karshe...ta dan numfasa, nasan cewa ours is
not a love marriage amma ina fata zaka rikeni
amana ka zama mijina na karshe.
Maganganun Aishatu sun shige shi sosai amma
kalmarta ta karshe ta dan daga masa hankali
har yayi saurin rufe mata baki da hannunsa.
Murmushi ta sake yi masa....Dr nasan kana
matukar son Fadila kuma kana son ku zauna
lafiya da ita. Nima ina so maka hakan shiyasa
zan taimaka maka har ta gane rashin dacewar
abinda take yi. Amma ina rokonka alfarma
daya....ya kura mata ido yana jiran yaji abinda
zata ce. Nasan ina tare da ciwo don Allah kada
ka bari kowa ya sani. Sirrina ne wanda bana son
ya zama sanadin da za'ayi min gori watarana. I
just want a home to call my own.
Zuciyar Huzaifa ba karamin karyewa tayi ba. Sai
yau ya kara yadda Aishatu mace ce mai
hankalin. Hawayen da yaga tana shirin yi ne
yasa ya janyota jikinsa ya rungume. Sun jima a
haka yana shafar gashin kanta wanda yasha
gyara. Kanta a kasa ta fara kokarin tashi ya ce
tsaya mana ai nima ina da abin fada. daga yau
you are my best friend, my sister and.......shiru
tana jiran taji me zai ce har ta gaji ta dago
kanta. Kissing dinta yayi a baki kafin yace my
wife yana mata murmushi. Har ya tashi ya shiga
wanka bata iya tashi ba saboda yanayin da ta
sami kanta. Anya Aish ko dai son Dr H.M Rano
kike yi?
wasu riga da wando na bacci ya bata ta dauka
ta shiga toilet. Wanka tayi da alwala ta fito suka
yi nafila. Ya fita samo plate da zai zuba musu
naman da Saddiqa ta gasa masa. Yana dawowa
ya tarar ta jingina da gado tana bacci.
Tausayinta yaji ya kara kamashi ya dauketa a
dora ta akan gado. Sai da ya gama abinda yake
yi ya kashe fitila ya kwanta shima.
Fadila dake zaune a kofar dakin tun bayan ya
fita dauko plate tana ganin duhu ta karkashin
kofar taji kamar zuciyarta zata buga saboda
kishi. Tana kuka tace na shiga uku. Nan ta
zauna tana ta rusa kukanta har asuba babu
wanda yasan tana yi.
RASHIN GODIYA ✂ 32
Huzaifa ya kira mai gyaran kofa kamar yadda ya
fada an gyarawa Aishatu kofarta. Bangarenta
akwai kitchen, parlour da dakuna biyu. Daya an
saka mata gado mai tsada irin na zamani har
kuka sai da tayi. Iyayenta suna iya kokarinsu
wurin kyautata mata. Daya dakin kuwa kayan
turare ne da hadadden kafet da pillows. Ga shi
akwai wadatar iska a wurin. Sai ta mayar dashi
wurin shan iska kawai. Falonta ma ya hadu ga
kitchen wanda Huzaifa ya wadata store din
cikinsa da dukkan kayan abinci. Ya kuma sanar
dasu kowa zatayi nata abincin ne wadda take da
girki ranar ta hada dashi. Hakan yayiwa Aishatu
dadi don tana gudun abinda zai hadata da
Fadila.
A kwanaki ukun da Aishatu tayi sun kara
sabawa da Huzaifa. Banda masallaci babu inda
yake zuwa. Idan ya dawo kuwa hira suke yi da
bawa juna labarai akan rayuwarsu. Lokacin
bacci kuwa a kasa yake kwanciyarsa tana daga
kan gado. Haka zasu cigaba da hira har suyi
bacci. Abinci kuwa kullum zaa kawo safe ,rana
da dare daga gidan umma. Aishatu tace wannan
wahala ce zata rinka dafawa da kanta. Yaya
kubra da ta ji sakonta ta kira ta a waya...ke dan
kwana ukun nan ai lokaci na baki ki kara sace
zuciyar mijinki. Duk abinda nake dafawa irin
wanda yake so ne so kada ki damu. Kullum aka
kawo sai Aishatu ta buga waya tayi godiya. Ita
kuwa Fadila an ga bulus itama dena girkin tayi.
Wani lokacin ma kafin Aishatu ta debarwa
Huzaifa ita zata fara diba duk ta tsince naman
ta bar musu kada. Ana gobe Aishatu zata fita
girki Huzaifa yana aiki akan computer a dakinta
tana zaune daga gefensa tace yaushe zamu je
gidan Umma ne da Rano? Wani murmushi yayi
wanda ya nuna yaji dadin abinda ta fada sosai.
Aish harda Rano zaki je? Tace eh mana. Ba
garinku bane kuma akwai yan uwanka a can. Ni
kazo ka fada min su waye closest to you ma a
can tun wuri. yace mai yasa? Murmushi tayi
tace sirri ne. Lumshe idanunsa yayi cike da
nishadi. Yan kwanakin da suka yi tare
damuwarsa da yawa ta ragu sosai. Ya dan jima
a haka yana jindadin kamshin falon nata sannan
yace ki bari sai kin sake karbar girki. Ta bata
fuska har gidan Umman? Kinga yanzu aiki nake
dan dubawa kuma gobe ba ke ce da girki ba.
Kema bazaki so ranar girkinki na fita da Fadila
ba. Aishatu tayi dariya bazan hana ba amma ka
tabbatar idan kuka dawo sai dai ka koma
dakinta don ban san abinda zan maka ba. Dariya
sosai yayi ya kura mata ido har sai da ta kawar
da nata tana murmushi. Aish kina kishina???
Muryarsa can kasa yayi maganar ta tashi da
sauri uhmm bari naje na gyara maka daki.
Amsar da bata bashi ba kenan.
Sai da ya dawo daga masallaci da magriba yace
ta shirya su je gidan Umma da gwammaja.
Murna a wajen Aishatu baa cewa komai. Yau
zata je taga su mama, dama kullum sai sunyi
waya har da baba ma. Huzaifa yana kallon
yadda take ta shiri cike da doki har yar waka ta
rinka yi a gaban madubi. Wani turare ta dauko
mai matukar tsada. Anti Sauda ce ta bata
kyauta tun kafin tayi aure, tsaraba da mijinta ya
dawo daga Dubai. A ledarsa ma yake ta saka a
jakarta. Lace tasa mara nauyi riga da zani sai
mayafinta babba wanda ta dora a kanta bayan
ta kashe dauri. Kallonta kawai yake tana saka
takalmi yace Aish kinyi kyau kamar amarya. Ta
dan tura baki me kake nufi, ni ba amarya bace?
Kinfi kama da.....ta koma gaban mirror tana
sake kallon kanta. Da me nayi kama please? Ko
dai kayan basuyi ba na canja. To sarkin rikicewa
wasa nake. Komai yayi banda abu daya. Ta
dago idanuwanta menene baiyi ba? Baki fesa
min turare ba. Kinsan idan mutum baby ne babu
wanda ya kaishi shagwaba. Ta rasa me yasa
Huzaifa yake son sata jin kunya.
Tare suka fito duk sunyi kyau kana ganinsu kaga
masoya masu kaunar juna. Ya shiga dakin Fadila
yace mata sun fita. Naman gabanta ta cigaba
da ci hankali kwance. Suna fita ta shiga kitchen
ta dauko tabarya sai kofar bangaren Aishatu.
Gwammaja suka fara zuwa suka tarar da Baba
da abin sallah a waje zai tafi masallaci sallar
isha. Huzaifa ya bishi ta shiga ita kadai. Mama
da kannenta sunyi murnar ganinta sosai har
Huzaifa suka dawo suna ta hira. Baba yayi
musu nasihar da ya saba akan rikon amana da
kula da addini. Ga mamakinta kaya ya debo
daga booth dinsa masu yawa ya basu. Suka yi
ta godiya. A mota suna hanyar zuwa gidan
umma yace Aish ina son Baba. Yana da kirki ga
saukin kai, sai yake tuna min da nawa mahaifin.
Tace Allah Yayi masa Rahma ni na hakura ya
zama babanka daga yau. Shan miya amma.
Meye kuma shan miya Aish? Tace dama ranar
da na fara ganinka nasan kai dan kauye ne, ta
rike haba ace dan kano bai san shan miya ba.
To me ka sani? Ya kashe mata ido nasan yadda
ake...in fada? Fadi mana nasan bazai wuce kace
ka iya lomar tuwo ba. Sai da maigadi ya rufe
gate din gidan yace mata nasan yadda ake
kissing bakin Aish. Duk da sau daya hakan ta
taba faruwa tsakaninsu ranar da aka kaita amma
babu ranar da bata tunawa. Kafin ya gama
kashe motar ta fice ta shiga gidan da
gudunta..wannan kunya ta Aish. Ya shafi
sumarsa yabi bayanta. Umma tayi murnar
ganinsu sosai, tace autan umma har ka fara
kiba. Aishatu tace dama sunanka kenan? To
daga yau na samu. Yace haba umma meyasa
kika fada a gabanta salon ta raina ni. Yaya
kubra tace sai kai dai ka fiye son girma. Aishatu
zo muje kici abinci. Aishatu tace ni dai daga yau
umma nice autarki kinga ai girmeni. Duk suka yi
dariya, ta tambayi su Aliya akace Shukriya ta
tafi gidanta dasu. Sunyi hira sosai da zasu tafi
ta bawa umma turaren da taho dashi. Tana son
kamshinsa duk da yana kwali ana ji. Umma tayi
ta sa mata albarka. Yaya Kubra kuwa sai washe
baki kanninta ya auro yar arziki irin albarka. Sai
goman dare suka koma gida. Sai dai tun daga
kofar falo suka ga wurinta a bude. Kusan komai
na falon an fasa shi babu wani abin mora hatta
kafet da kujeru an tsaga su da wuka.
RASHIN GODIYA ✂ 34
Ranar har dare Aishatu bata ga fara'ar Huzaifa
ba. Gaba daya hankalinsa ya koma kan gyaran
dakin ta. Samarin unguwar ya samu su biyu
suka share dakin aka fitar da duk abinda bazai
moro ba. Ganin shima ya zage ana aikin dashi
Aishatu ta gaji da zaman dakin ta shigo wurinsu
harda dan murmushinta. Da me zan tayaku ko in
kawo muku ruwan sanyi? Hannu kawai ya nuna
mata alamar ta tafi. Haushinsa ya kara kamata,
wai meye laifinta ne da zai tsiri sha mata kunu.
Daki ta koma ta kunna tv tana kallo sai gashi ya
shigo. Dauke kanta ma tayi don kada su hada
ido. Ya dawo gefenta zai zauna ta matsa tare
da kawar da kai daya gefen. Sai ya koma gaban
tv ya tsaya ita kuwa ta runtse ido a dole bazata
kalle shi ba. Yayi murmushi ya shiga toilet yayi
wanka. Kafin ya fito ta tashi ta tafi dakinta.
Kayan da ya debo ta duba babu undies a ciki
shine ta tafi nema. Yana ganin bai ganta ba ya
fita daga shi sai dogon wando. Bazai wuce ta
koma dakinta ba, sai taje wani abin ya ji mata
ciwo. Kawai sai yabi bayanta.
A durkushe ya ganta tana kuka sosai. Jikinsa a
sanyaye ya karasa inda take. Ji tayi ya
rungumeta ta baya, duk yadda taso ta kwace ta
kasa. Shima kansa haushinsa take ji. Allah kadai
Yasan da yadda Baba ya siya mata wannan
kayan. Huzaifa ya juyo ta ita lokacin ta dena
fizge fizgen don tasan yafi karfinta ko motsi ya
hanata yi. Sake rungumeta yayi yana shafa
mata baya..a hankali taji yana cewa Aish ki kara
hakuri. Tun haduwarmu dake kike fuskantar
matsaloli amma you always find a way to make
things better. Wannan karon fadila ta wuce gona
da iri amma i promise you bazan barta haka ba.
Aishatu ta dago kanta a hankali suka hada
ido....wani irin abu da bazata iya fasaltawa ba
taji a wannan lokacin. Ga dukkan alamu Huzaifa
ma yaji don wani irin murmushi ya sakar mata
da ya kara narkar mata da zuciya. Hannunta ya
rike suka koma dakinsa. Aishatu tace
Dr...harararta yayi wai sai kinga fadila zaki
kirani baby, ni nayi fushi. Ya bata dariya tace to
yi hakuri baby. Amma seriosly magana zamuyi.
Banga dalilinka na cewa fadila bata da girki ba
har sai an gama gyaran dakina. Zaiyi magana
tayi saurin cigaba Wallahi hakan daukar hakki
ne. Abinda ya faru zargi ne muke tunda ido bai
gani ba. Huzaifa yace Aish ya wuce zargi fa. Ke
kinsan babu wanda zai miki haka sai ita.
Aishatu tace ni dai ka je ka fada mata zata karbi
girki ni bazan yi ba. Huzaifa ya ce Aish har zaki
fara musu dani? Ta zauna bakin gado ba haka
bane...lahirarmu nake dubawa. Me zamu ce idan
Allah Ya tambayemu hujjar mu ta hukunta bisa
zargi? Nasan kana mata uzuri amma please ka
kara. Haka tayi ta bashi baki ko kadan bai so ba
amma yasan gaskiya take fada masa. Rai a
bace yaje ya sanar da Fadila ta shirya karbar
girki da daddare.
Shawarar Wasila ta karba ta bashi hakuri sosai
tana kuka. Ya dai ji amma bai sakar mata fuska
ba. Kafin ya fita ya dawo ta gyara dakinta da
falo. Yau harda wankin toilet. Sai da yayiwa
Aishatu sai da safe ya fita...abin haushi hawaye
taji ya sauko mata. Meye na kuka Aish ta
tambayi kanta. Its not like kuna soyayya da
angon naki. Sauran abincin da Yaya Kubra ta
aiko mata taci. Shi kuwa Huzaifa yana ta cika
da batsewa ya shiga falon Fadila. Ba yabo ba
fallasa ta gyara dakin. Rigar jikinta kuwa
iyakarta cinya. Tayi kyau sosai don ta iya
kwalliya. Indomie ta dafa masa ya kalli abincin a
wulakance amma dole yaci don yunwa yake ji. A
hankali Fadila ta rinka jan hankalinsa har ya
sakar mata jiki. Ranar zuciyarta fes ta kara
tabbatarwa tana son mijinta kuma shima yana
sonta. Dole ta yi gaba da Aishatu don bata ga
matar da ta isa suyi sharing miji ba.
Fahad yana zaune gaban likita yana kara
karanta report din test din da aka yi masa. Ya
dago kai yanzu dr ka tabbatar ni da yahanasu
duk bamu da problem? Dr ya gyara zaman glass
dinsa yace kwarai kuwa Fahad. Komai lafiya
hakuri kawai zaku kara. Kasan haihuwa lokaci
ne. Amma na rubuta maka magani da zakuyi
trying. Fahad ya daki table din dr din ya mike
cikin fushi. Magani! Magani ! Magani! Na gaji.
Ka bar maganinka kawai ba yau na fara zuwa
test ba akan fertility ana bani. Ransa a bace ya
fita....ya gaji da trying result yake son gani. Ba
abinda yake so kamar haihuwa yanzu ido rufe.
Idanunsa yaji suna masa zafi alamun hawaye na
shirin zuba. A hankali yace Aisha I miss you.
RASHIN GODIYA ✂ 33
Saboda tsabar tashin hankali Aishatu ta kasa
cewa komai. Kofar dakinta ta kalla an rotsa ta
duk da katakon mai kwari ne. Da sanyin jiki ta
karasa ciki abin mamaki baa taba komai ba.
Karamin falonta kuwa cike yake da kamshi
saboda komai na show glass dinta ya fashe
rugu rugu. Bakinta ta toshe saboda kukan da
yake neman fin karfinta. Sai hawaye kamar
famfo. Huzaifa kuwa jingina yayi da abinda yayi
saura na kofar falon ya runtse idonsa. bazai iya
kwatanta yadda ransa ya baci ba. A hankali ya
bude idonsa yana kallon Aishatu...mayafin da
tasa ta toshe bakinta ne ya hana kukanta yayi
karfi. Tausayinta yaji sosai kukanta yana kara
daga masa hankali. Zuciyarsa kamar ta fashe
don tsananin bakinciki. Fita yayi yana kwalawa
Fadila kira cikin daga murya. Ko ita Aishatu da
take daki sai da ta tsorata. Tare ya sun shigo da
Habu maigadi. Mal Habu yace yallabai kaga
barnar da ta faru ko? Fadila ta ruga da gudu ta
rungume Huzaifa tana shesshekar kuka. Abban
Aliya kaga girman mutumin kuwa? Allah ne ya
rufa min asiri da kila ma yanka ni zaiyi. Iyakar
karfinsa ya tureta don bai shirya jin karyar da
zata yi masa ba. Mal Habu yace na zaga bayi
kenan na rinka jin kamar ana buga wani abu. Ina
zuwa naga Hajiya tana ihu tana kuka tace wani
ne ya hauro yake fasa kayan hajiya amarya.
Rainin hankali Huzaifa ya fada a zuci. Da kyar
ya iya cewa to kai ka ganshi ne Mal
Habu....ehhh, to na dai ga kamar giftawar inuwa
dana leqa ta taga. Ba don girmansa ba da babu
abinda zai hana Huzaifa dauke shi da mari.
Amma sai yace runda baka da tabbas ina ganin
gara a hakura da aikin nan naka idanunka sun
fara samun matsala. Mal Habu yace a'a yallabai
banga komai ba. Amma ita Haj a gabanta abin
ya faru. Huzaifa bai tsaya sauraronta ba ya
koma dakin Aishatu. Tana nan inda ya barta a
tsaye tana zubar da hawaye. Dakinta ya shiga
ya rinka fito da akwatunanta yana kwashe kayan
wardrobe din yana zubawa a ciki. Sai da ya
kwashi wanda zai iya sannan ya fara kaisu
dakinsa daya bayan daya. Fadila tana falo tana
dariyar mugunta. Ba don shigowar habu maigadi
ba har dakin sai ta lalata. Ganin Huzaifa da
akwatuna ta ce lafiya ina kuma zaka kai kayan?
Shiru ma magana ce. Sai da ya gama kwashesu
tsaf Aishatu dai bata iya cewa komai. Ya koma
ya rufe kofar gidan sannan ya sake shiga dakin
Aishatu. Ji tayi Huzaifa ya daga ta cak kamar
jaririya yazo ya wuce Fadila dake matsar kwallar
karya a falo. Bai ajiyeta ko ina ba sai akan
gadonsa. Ruwa mai zafi sosai ya tara mata a
toilet ya sake daukarta ya kaita sannan ya rufo
mata kofa. Kofar dakinsa kowa key yasa ta
waje ya rufeta sannan ya tafi dakin Fadila.
Waya ya tarar da ita tana yi. Jin alamun da
mutum a bayanta yasa ta koma muryar kuka. Ai
wasila na auna arziki da yau kunji mummunan
labari. Wani kato ne.....wayar ya fizge kafin ta
tashi ya fara zabga mata belt dinsa. Sai da yayi
mata lilis ya kyaleta tana ta kwarma ihu. Mal
Habu har ya gaji da buga kofar gidan. Itama
Aishatu ihun Fadila yasa tayi saurin fitowa daga
toilet taji kofar dakin kam a rufe. Bugu take iya
karfinta ta kasa budewa.
Huzaifa ya kalli Fadila da jikinta yayi rudu rudu.
Cikin fushi yace baki fi karfina ba Fadila, kina
cin darajar aure ne kawai nake raga miki. Amma
tunda kin zabi haka mu zuba ni da ke shege ka
fasa. Kuma wallahi baki da girki har sai na
gama gyarawa Aishatu dakinta. Idan zaki gyara
halinki ki gyara otherwise ki kama hanyar
gidanku. Haba na gaji da masifarki. Tun kafin
nayi aure kike hura min wuta. Nayi auren ma
ban tsira ba. Ki guji ranar da zaki kaini bango
sai na miki fiye da wannan. Wai ni zaki rainawa
hankali. Ki yi min barna a gida kice wani ne. Da
gaske ne ai so zanyi ya hada dake a fashe
fashen. Fadila cikin kuka take masa Allah Ya
isa. Yayi gaba abinsa zuciyarsa ba dadi.
Yana bude kofar dakin ya tarar da Aishatu zaune
a bakin kofa tana rusa kuka. Tana ganinsa tace
me yasa ka dake ta? Yace kinga ki sami wuri ki
kwanta raina a bace yake i dont want to talk
now. Bata sake tanka masa ba ganin ya dau
zafi sosai kamar ba yanzu suka shigo gidan
cikin nishadi ba. A haka ya kwanta wurin da ya
saba a kasa yana ta adduar neman sassauci a
zuciyarsa har bacci ya dauke shi. Washegari da
sassafe ya kira Yaya Zainab yace suzo gidansa
ita da sauran yan uwansa. Aishatu tunda ta
tashi take rakube a gefe. Fushin Huzaifa yana
neman shafarta duk da ita aka yiwa laifi. Kafin
tara na safe dukkan ninsu sun iso harda Yaya
kubra da tayiwa umma karya ta fito. A gigice
suke saboda kiran yayi wuri. Basu kara gigicewa
ba sai da suka ga dakin Aishatu. Saddiqa tace
ko baka fada ba auta nasan Fadila ce da
wannan aikin. Wallahi sai naci ubanta a gidan
nan. Yaya zainab dama halin umma suka yo ita
da Huzaifa wurin hakuri tace ba haka zaayi ba
saddiqa. Ina Fadilan take? Yaya kubra tace
Allah Yaya indai zata fito babu abinda zai
hanani dukanta. Ya take so ayi mata ne....fadila
na jin muryarsu ta kama kofar dakinta ta rufe da
key. Wurin Aishatu ya kaisu wadda tunda ta
tashi take kuka. Tana ganinsu ta fada jikin Yaya
kubra tana ta kuka. Gaba dayansu ta basu
tausayi. Yaya Zainab tace to yan uwa lokacin
zumunci yayi. Ya kamata duk mu hadu mu
gyarawa Aishatu daki ba tare da sanin Umma ko
su Mama ba. Itama Fadilan ka barni da ita zan
bata last warning. Ta koma ga Aishatu kiyi
hakuri kanwata don Allah kada ki daga
maganar nan. Kai kuma na yarda ka hukunta ta
duk yadda kake so amma banda saki please. Da
fadila taki bude kofa daga waje tayi mata fada
da nasiha. Huzaifa duk haushi ya ishe shi har
wani lallaba ta ake. Ai bata ga komai ba a
gashin kumar da zai mata. Aishatu kuwa ta rasa
bakin yi musu godiya. Yaya shukriya tace ai yiwa
kai ne.
Yaya Zainab na tafiya gida ta fadawa mijinta.
Managing director ne a wani travel agency ya ce
gaskiya yarinyar nan bata kyauta ba. Amma
nasan maganinta....ya kira waya yayi wa wani
magana sannan yace da Yaya zainab ki fada ma
Huzaifa yayi wa amarya passport next week
zasu tafi Umra. Yaya zainab ta washe baki
lallai Aishatu yar gata ce.
RASHIN GODIYA ✂ 34
Ranar har dare Aishatu bata ga fara'ar Huzaifa
ba. Gaba daya hankalinsa ya koma kan gyaran
dakin ta. Samarin unguwar ya samu su biyu
suka share dakin aka fitar da duk abinda bazai
moro ba. Ganin shima ya zage ana aikin dashi
Aishatu ta gaji da zaman dakin ta shigo wurinsu
harda dan murmushinta. Da me zan tayaku ko in
kawo muku ruwan sanyi? Hannu kawai ya nuna
mata alamar ta tafi. Haushinsa ya kara kamata,
wai meye laifinta ne da zai tsiri sha mata kunu.
Daki ta koma ta kunna tv tana kallo sai gashi ya
shigo. Dauke kanta ma tayi don kada su hada
ido. Ya dawo gefenta zai zauna ta matsa tare
da kawar da kai daya gefen. Sai ya koma gaban
tv ya tsaya ita kuwa ta runtse ido a dole bazata
kalle shi ba. Yayi murmushi ya shiga toilet yayi
wanka. Kafin ya fito ta tashi ta tafi dakinta.
Kayan da ya debo ta duba babu undies a ciki
shine ta tafi nema. Yana ganin bai ganta ba ya
fita daga shi sai dogon wando. Bazai wuce ta
koma dakinta ba, sai taje wani abin ya ji mata
ciwo. Kawai sai yabi bayanta.
A durkushe ya ganta tana kuka sosai. Jikinsa a
sanyaye ya karasa inda take. Ji tayi ya
rungumeta ta baya, duk yadda taso ta kwace ta
kasa. Shima kansa haushinsa take ji. Allah kadai
Yasan da yadda Baba ya siya mata wannan
kayan. Huzaifa ya juyo ta ita lokacin ta dena
fizge fizgen don tasan yafi karfinta ko motsi ya
hanata yi. Sake rungumeta yayi yana shafa
mata baya..a hankali taji yana cewa Aish ki kara
hakuri. Tun haduwarmu dake kike fuskantar
matsaloli amma you always find a way to make
things better. Wannan karon fadila ta wuce gona
da iri amma i promise you bazan barta haka ba.
Aishatu ta dago kanta a hankali suka hada
ido....wani irin abu da bazata iya fasaltawa ba
taji a wannan lokacin. Ga dukkan alamu Huzaifa
ma yaji don wani irin murmushi ya sakar mata
da ya kara narkar mata da zuciya. Hannunta ya
rike suka koma dakinsa. Aishatu tace
Dr...harararta yayi wai sai kinga fadila zaki
kirani baby, ni nayi fushi. Ya bata dariya tace to
yi hakuri baby. Amma seriosly magana zamuyi.
Banga dalilinka na cewa fadila bata da girki ba
har sai an gama gyaran dakina. Zaiyi magana
tayi saurin cigaba Wallahi hakan daukar hakki
ne. Abinda ya faru zargi ne muke tunda ido bai
gani ba. Huzaifa yace Aish ya wuce zargi fa. Ke
kinsan babu wanda zai miki haka sai ita.
Aishatu tace ni dai ka je ka fada mata zata karbi
girki ni bazan yi ba. Huzaifa ya ce Aish har zaki
fara musu dani? Ta zauna bakin gado ba haka
bane...lahirarmu nake dubawa. Me zamu ce idan
Allah Ya tambayemu hujjar mu ta hukunta bisa
zargi? Nasan kana mata uzuri amma please ka
kara. Haka tayi ta bashi baki ko kadan bai so ba
amma yasan gaskiya take fada masa. Rai a
bace yaje ya sanar da Fadila ta shirya karbar
girki da daddare.
Shawarar Wasila ta karba ta bashi hakuri sosai
tana kuka. Ya dai ji amma bai sakar mata fuska
ba. Kafin ya fita ya dawo ta gyara dakinta da
falo. Yau harda wankin toilet. Sai da yayiwa
Aishatu sai da safe ya fita...abin haushi hawaye
taji ya sauko mata. Meye na kuka Aish ta
tambayi kanta. Its not like kuna soyayya da
angon naki. Sauran abincin da Yaya Kubra ta
aiko mata taci. Shi kuwa Huzaifa yana ta cika
da batsewa ya shiga falon Fadila. Ba yabo ba
fallasa ta gyara dakin. Rigar jikinta kuwa
iyakarta cinya. Tayi kyau sosai don ta iya
kwalliya. Indomie ta dafa masa ya kalli abincin a
wulakance amma dole yaci don yunwa yake ji. A
hankali Fadila ta rinka jan hankalinsa har ya
sakar mata jiki. Ranar zuciyarta fes ta kara
tabbatarwa tana son mijinta kuma shima yana
sonta. Dole ta yi gaba da Aishatu don bata ga
matar da ta isa suyi sharing miji ba.
Fahad yana zaune gaban likita yana kara
karanta report din test din da aka yi masa. Ya
dago kai yanzu dr ka tabbatar ni da yahanasu
duk bamu da problem? Dr ya gyara zaman glass
dinsa yace kwarai kuwa Fahad. Komai lafiya
hakuri kawai zaku kara. Kasan haihuwa lokaci
ne. Amma na rubuta maka magani da zakuyi
trying. Fahad ya daki table din dr din ya mike
cikin fushi. Magani! Magani ! Magani! Na gaji.
Ka bar maganinka kawai ba yau na fara zuwa
test ba akan fertility ana bani. Ransa a bace ya
fita....ya gaji da trying result yake son gani. Ba
abinda yake so kamar haihuwa yanzu ido rufe.
Idanunsa yaji suna masa zafi alamun hawaye na
shirin zuba. A hankali yace Aisha I miss you.
RASHIN GODIYA ✂ 35
Haka Aishatu ta cigaba da zaman hakuri da
Fadila don bata fasa halin neman tsokana ba.
Tsakaninta da Huzaifa suna hira sosai. Dakinsa
kuwa ya bar mata sai dai ya je daukar kaya.
Ranar da Aishatu zata karbi girki tun da ya
farka da safe ya sami kansa cikin nishadi.
Fadila tana kwance gefensa ya dan taba ta...a
hankali ta bude ido saboda baccin da take ji.
Yace fadila tara da rabi fa...kinsan dai daren
jiya cornflakes nasha. Please ki tashi ki bani
abinci. Ta juyar da kanta ni ka kyaleni na dan
kara kadan, goma ma bata yi ba.
Yace idan baki tashi ba zanje wurin Aishatu
nasan....kamar an tsikareta ta tashi naji naji bari
nayi brush. Ta fita yabi bayanta da dariya.
Fadila kishi.
Bayan laasar ya tafi dauko yaransa don sati
daya ya rage Aliya ta koma makaranta. Sunyi
murnar ganin Abbansu sosai suna ta bashi
labarai. Har yar kiba yaga sunyi...ba dole ba
tunda suna samun abinci ba kame kame ba.
Aishatu tun asuba ta hau gyaran daki. Har
mamakin kanta take irin wannan zumudi kada
ma Huzaifa ya gane. Ita dai tasan ta damu
sosai da shi...muryarsa kadai idan taji sai
gabanta ya fadi. Garin yaya ta soma sonsa ne?
tun a kan fahad ta sallama maza shima bazata
bari ya sani ba har sai ta tabbatar da
matsayinta a wurinshi. Kamar kullum ya shigo
su gaisa bayan ya dawo ya ganta tayi kwalliya
sosai kamar mai zuwa biki. Sai dai ya kula bata
rabo da mayafi. Tun zuwanta sau daya ya ganta
ba mayafi ranar da aka kawota. Toilet take
shiga ta shirya kullum ta shirya. Yana ta binta
da ido ta fada masa abinda take bukata na
cefane don girkin rana washegari. Yace ko in
samo miki yar aiki ne Aish? Hankalinsa yana ga
kyakkyawar fuskarta kamar bai taba ganinta ba.
Ta danyi murmushi bana bukata gaskiya. Ina su
Aliyun ne ina ta jiran ganinsu. Yaji dadi sosai ya
ce suna dakin Fadila bari na kira su. Tace ka
bari zani da kaina muje kayi introducing dina
dai. Zan fada musu ke ce maman kannensu 12
masu zuwa nan gaba. Zaro ido tayi tana dariya
sai kace wata bera? Yace to wa ya sani ne abu
a duhu? Filo ta dauko ta jefa masa sannan suka
fita suna dariya.
Fadila tana rungume da Aliyu tace kada ku
manta sunan da na fada muku dai kunji ko?
Aliya tace ai ni Abba zan fadawa ya koreta kada
ta sha min jini. Karaf maganarta a kunnen
Huzaifa yace wace zata sha jininki kuma
Aliya..kinje kin koyo zance a wurin su hidaya
ko? Aishatu na shigowa Aliya da Aliyu suka yo
kanta har ta fara murmushi sai suka cire
takalma suka fara jifanta. Huzaifa ya daka musu
tsawa meye haka Aliya? Ta kyabe baki ta soma
kuka Anti Mayya ce ta shigo zata shanye mana
jini. Huzaifa ya tsaya yana mamakin wannan
magana ta yaran shi. Aishatu ta dafe goshi inda
takalmin Aliya ya sameta ta juya zata fita su
Aliyu suna mata ihun Anti Mayya. Sai da ta fita
Huzaifa ya janyo Aliya yar shekara hudu da rabi
da Aliyu dan shekara uku. Wa ya fada muku
sunanta kenan. Aliyu yace Mummy tace mana
itama ta sha mata jini jiya da straw ko Yaya ya
tambayi yar uwarsa. Kuma da zafi kamar allura.
Fadila ta kwashe da dariyar mugunta. He should
have known mai hali baya canjawa. Yaran yayi
wa fada sosai yace da Fadila kin kyauta sannan
ya fita cikin fushi.
A kitchen dinta ya sameta tana kwashe tuwon
shinkafa. Yayi saurin zuwa zai karba ta hana
shi. Tana gama zuba tuwon a leda ta kulle ta
rufe flask din. Sai ta hau gyaran gas cooker din.
Yana magana taki kula shi sai aiki take kawai.
Miyar agushin da take yi ta zubawa ganyen ugu
ta cigaba da aiki. ya gaji da kallom yadda take
yi ita a dole bazata karaya ba. Riko ta yayi ta
karfi Aish listen to me please. Ta fizge hannunta
kaje daki na kusa gamawa kitchen din akwai
zafi. Janyo ta yayi ta karfi ya matseta a jikinsa.
Kuka mai tsuma zuciya ne ya kwace mata ta
rinka yi bai ko yi yunkurin bata hakuri ba. Gara
tayi kukan ko zuciyarta ta sassauta.
RASHIN GODIYA ✂ 36
Kusan minti biyar tana abu daya bai kosa da ita
ba har ta gaji ta dena don kanta. Tana dagowa
ta ga gaban farar shirt dinsa duk bakin kwallinta
ya bata masa. Idanunta yabi yaga abinda take
kallo...ya dan shafi fuskarta stop looking worried
indai akan wannan bakin ne za'a wanke. Ta
kirkiro murmushi ni kwallin da nayi asara ne ya
dameni. Duk ya kare a gaban rigarka. Har
zuciyarsa take burge shi, a wannan yanayin take
iya wasa dole ya jinjina mata. Sai Fadila tayi
dana sanin abinda tayi don bazai kyaleta ba.
Amma yanzu burinsa bai wuce yaga farincikin
Aish ba.
Da taimakonsa suka kai kwanukan abincin falo
tunda nasa dakin babu. Ta kawo masa fruit juice
wanda ta hada da kwakwa, kankana, dabino da
ayaba tayi blending ta tace. Sugar kadan ta kara
tasa a fridge yayi sanyi. Komai nata a nutse
take yinsa yaji ta kara shiga ransa sosai. Love
will find its way tabbas haka ya taba fada
mata...ko dai har ya iso ne bai sani ba? Shi
kadai yayi murmushi tare da lumshe idanunsa.
plate ta dauko zata yi serving dinsa abinci tana
kallonsa. Bata gajiya da kallonsa...sai ta tuna
abinda Fadila tayi mata....a sannu zan rama ta
fada a ranta. Fahad ma ta koya masa hankali
bare mace yar uwarta.
Yaji dadin abincin sosai yayi ta mata godiya
akan yadda ta iya bata lokaci tayi masa girki. Ya
so nuna mata godiyarsa fiye da haka don shi da
samun abincin kirki dai yaje gidan Umma. Sai
dai kuma yanayin da suke yasa bazai iya ba.
Fadila tayi nasarar bata musu mood dinsu. Kafin
ya gama cin abincin ma tayi tafiyarta daki.
Wanka ta sake yi ta tsaftace jikinta ta kwanta.
Kanta taji yana mata matsanancin ciwo. Ta
kasa tashi ma bare ta nemi Huzaifa ya bata
magani. Wasu hawayen ne suka fara
zuba...yanzu ita haka rayuwarta zata kare
kullum cikin bacin rai. Anti Mayya da 'ya'yan
mutumin da sonsa yayi mata mugun kamu suka
kirata yafi komai kona mata rai. Tun yanzu
kenan ina ga idan suka kara girma Fadila tana
musu hudubar tsiya. Huzaifa kuwa da ya gama
cin abinci dakin fadila yaje. Yaran sunyi bacci
Aliya tayi cuku cuku da rigar shaddar dake
jikinta wadda Fadila ta gagara cire mata. Shi
kuwa Aliyu duk sanyin AC da fanka daga shi sai
pant ta kwantar dashi. Fadila na ganinsa ta ce
yau ma dukan nawa kazo yi a gaban 'ya'yana?
Bai kulata ba ya saka musu kayan bacci ya
gyara musu kwanciya. Ya dubeta da kyau...ki
sani Fadila duk mai hankali yana gudun ranar
dana sani. Duk abinda kike shukawa da
hannunki ba na wani ba zaki girbe wata rana.
Auren mace sama da daya ba kaija farau ba so
duk wani haukanki bazai sa na saki Aish ba. Na
fada miki ina raga miki ne darajar aure to ki sani
duk wanda bai godewa ni'imar Allah ba wata
rana zai godewa azabarSa. Naso yi miki hukunci
mai tsanani sai gashi wadda kika cutar ta nuna
min komai a sannu ake binsa. Yanayin da na
ganta bayan ta fita dazu ya sa zan barki da
halinki. Yana juyawa zai fita ta yi shewa ta tafa
hannu Ahayye yaro
Ahayye ba yaro ba
Iyye nanaye
Duniya bata bar kowa ba hatta wanda baa auri
uwarsa ba ma jiransa take. Ki ji tsoron Allah
Fadila.. tace ina ji Huzaifa, dole kake ganin
laifina tunda ka hadu da annoba, ka auri karuwa
ragowar mazan titi. Itakar karfinsa yasa ya
mareta sai da taga haske ya fita cikin bacin rai.
Dakinsa ya shiga yaji zafi don babu abinda ke
kunne na sanyaya daki. Hatta windows duk an
saki labule. A tsakiyar gado ya ganta ta rufa da
bargo. Yayi saurin yaye bargon yana cewa lafiya
Aish? Rawar sanyi take yi sosai jikinta ke
karkarwa. Ga wani katon hijab ta saka, yana
kokarin cirewa tana kara rike abinta. Idanunta
sunyi ja sosai da gani ta dade tana kuka. Ba don
Umma ba yau Fadila sai dai ta kwana a gidansu
a yadda yake ji a ransa. Da kyar ya iya cire
hijab din tan masa wani kukan ita sanyi take ji.
doguwar rigar bacci ce a jikinta ta cotton. Ya
kai hannu kai da wuyanta. Jikinta yayi mugun
zafi, Oh my God ya fada yana tashi ya tsaya
yiwa wadda bazata dauka ba nasiha ga Aish
tana kwance. Ruwan famfo ya debo a wata roba
ya hado da karamin towel. Jikinta ya rinka bi
yana gogewa tun tana cewa ya bari har ta dena.
Shi har mamaki ta bashi a wannan yanayin wai
har tasan kunya don rufe jikinta ta rinka yi ita a
dole kada ya ga jikinta.sai da ya gama ya zubar
da ruwan ya dawo ya bude wata drawer ya
dauko first aid box. Idanunta duk sun mata nauyi
da kyar take bude su. Amma tana ganin ya fito
da syringe ta fara kokarin tashi. Kayi hakuri don
Allah Dr bana so...hawayen da ya tsani gani
take yi. Yace kema kiyi hakuri nayi miki don ki
sami lafiya. A hankali ta fara kokarin gudu yace
bazan miki da zafi ba kinji. Tace to tsaya na
shirya...a zaune nake ma ya fada. Ganin dai
shirin yaki karewa sai kawai ya rungumeta
yadda bazata motsa ba har yayi mata. Ai kuwa
wata kara ta saki tare da cigaba da kuka mai
sauti. Yana sakinta ta soma dukansa. Shima
yasan ruwan allurar akwai zafi. Ya tashi ya
kawo mata ruwa tasha magani. Sai dai tana sha
shima da kyar ta fara kakarin amai. da gudu taje
toilet ta amayar da maganin. Duk tausayinta ka
kamashi ya gyara mata jiki kuma ya gyara wurin
sannan ya sake kwantar da ita. Sai da yayi
nafila har ya jefa pillow kasa inda yake kwana
sai ya dawo dashi gadon. Gefe dai ya kwanta
yana kallonta cike da tausayi da tsantsar so. Ya
tabbatar bazai taba jindadin rayuwarsa ba idan
babu Aishatu a ciki. Ta soma bacci yaga tasa
kafa tana ture bargon. Gumi take sosai hakan
ya tabbatar masa zazzabin ya sauka. Haka yayi
ta kallonta har bacci ta dauke shi.
RASHIN GODIYA ✂ 38
Tuni Huzaifa ya tattaro dukkan nutsuwarsa.
Idanunsa sun kasa barin Aishatu. Ita kuwa ba
don kada Fadila tayi saurin gano ta ba da ko
kadan bazata iya jurar kallonsa ba. Ya juga ga
Fadila wadda kuka yaci karfinta sosai, bari na
gama na dawo zan kira Baban gandu na sanar
dashi abinda yake faruwa. Ko sakin da Huzaifa
yayi mata bai kada mata ciki kamar sunan
Baban gandu da huzaifa ya fada ba. Wan
mahaifinta ne wanda tun suna yara suke
tsoronsa. Mutum ne mai tsayar da gaskiya
amma yana da fada sosai. Idan laifin mutum ya
tsananta ba bakon abu bane a gareshi ya dake
shi.
Aishatu ta dauki mayafinta ta yafa tare da bin
bayan mijinta. Falon Huzaifa na waje wanda
yake tarbar baki suka shiga. Bata ma san dashi
ba sai ranar. Mal Habu yayi wa Baba da
Mahmoud kaninta jagora ya shiga. Murnar a
wurinta ta kasa buya, ta durkusa su gaisa sai
kuka. Baba yayi saurin yiwa Huzaifa kallon
tuhuma. Har abada bazai kara bari wani namiji
ya wulakanta masa 'ya ba. Yana son abarsa
sosai. Huzaifa ya wayance kinga dai Mahmoud
yana kallonki kina hawaye. Baba ya dubi dan
autansa kai fita waje kafin ka sami labarin
kaiwa gida. Duk suka yi dariya harda ita mai
kukan. Huzaifa yace Baba ai tunda aka ce kazo
ta fara kwallah wai bata taba tsammanin
ganinka ba a gidanta. Mal Said yayi yar dariya
yau ma hanya ce ta biyo dani kuma dai kaninki
dana aiko ya nace sai munzo. Huzaifa ma ya
durkusa Baba ya taro shi da hannu ya bashi
hannu suyi musabaha. Haba Huzaifa ai kai dana
ne. Dana da ya kira shi yasa yaji dadi. Wani
karamin buhun da Mahmoud ya ajiye Baba ya
nuna musu. Ga tsarabarku daga Getso. G Juma
ce tace ki raba har su Hajiya kwan zabi ne.
Bakar Ledar kuwa na yar uwarki ne. Aishatu
tace wacce Baba? Yace yayarki mana, ya dan
kalli Huzaifa sunan ne ya dan kwanta min.
Huzaifa da Aishatu suka yi shiru sai can tace
mungode Baba. Da ganinsu yasan akwai matsala
yace Aishatu kada kiyi kuskuren yi min karya
menene? Naga kuna yiwa juna kallon kallo ko
zuwan nawa ne bai kamata ba. Huzaifa yace
Subhanallah Baba ba haka bane. Sallamar Fadila
ce tasa hankalinsu ya koma ga kofar falon.
Bayan fitarsu ta kira wasila a firgice tana kuka
tana fada mata abinda ya faru. Wasila na shiga
uku Huzaifa ya sake ni. Tace ke kwantar da
hankalinki yar uwa. Kije ki bashi hakuri sosai a
gaban Aishatun. Itama ki bata ni kuma ki bar
sauran a hannuna zam nemo mana Fahad
dinnan duk inda yake. Nayi miki alqawari ta inda
ta shigo zata fita. Fadila taji dadin zancen
wasila tace bari su dawo baban shegiyar ne
yazo. Wasila tace to zama bai kamaki ki ba. Kije
ki bada hakurin a gabansa. Ki tabbatar yasa
baki Huzaifa ya mayar dake.
Fadila ta karaso cikin falon lullubinta har ka.
Gaban Aishatu ta fara durkusawa ki yafe ni
Aisha. Nabi son zuciya na cutar dake. Wallahi
ina son mijina bazan iya rayuwa babu shi ba. Ta
koma kan Huzaifa ka yafe min Abban Aliya nayi
maka alqawarin ganin sauyi a halayena. Huzaifa
duk kunya ta kamashi a gaban suriki. Ta tashi ta
koma gaban Baba. Ka yafe min abinda nayi
maka kwanaki kuma ka taimakeni ka sa baki ya
mayar dani. Saki daya yayi min dazu. Ta kuma
rushewa da kuka kamar wata zautacciya.
Huzaifa ya harzuka me ya hadaki da Baba
kuma? Duk suka yi shiru ya sake maimaita
tambayarsa da tsawa ga Fadila a tsorace tace
kwata na watsa masa kuma na gargade shi kada
ya bari ayi auren ku. Huzaifa ya yo kanta zai
doketa da kafa. Tashi ki fitar min daga gida.
Baba yace ashe zamana anan bai kara komai ba
dana? Ina gabanka kana korar mace. Wata rana
Aishatu zaka koro min kenan. Cike da kunya da
takaici Huzaifa ya labartawa baba irin cin kashin
da take yiwa Aishatu. Kwarai ran baba ya sosu
saidai yana tsoron Allah Ya kamashi da laifin kin
bada shawara tagari. Na yarda kaddara ce ta
kawo ni gidanka a yau. Indai ina da mutumci
komai kankantarsa a idonka ka mayar da ita
yanzu. Huzaifa yace haba baba kafi karfin haka
ma. Aishatu taji dadin yadda ta kasance. Bata
da burin zama sanadin fitar wata mace daga
gidan mijinta. Baba ya yi musu nasiha sosai
akan hakuri da juna. Shi da yazo ya da niyar su
gaisa sai gashi sun kusa awa daya. Huzaifa ya
harari Fadila bayan tafiyar baba kinci sa'a yau.
Amma next time you won't be so lucky. Ta tashi
a sanyaye kamar gaske...babu next time
Huzaifa. Aishatu duk da taji dadi amma a
tsorace take, ta tabbatar mutum baya canja hali
lokaci daya. Sai dai zata yi mata uzuri da
adduar su sami zaman lafiya mai dorewa.
RASHIN GODIYA ✂ 37
Ita ta fara tashi da asuba jikinta yayi mata nauyi
amma zazzabin da ciwon idon duk yayi sauki.
Sai idanunta da suka kankance ita da kanta taji
hakan. Tana juyawa ta ga Huzaifa yana
bacci....kasa dauke ido tayi daga kansa ta fara
tunanin me ya kawo shi gadon. A hankali ta
tuna abinda ya faru a daren sai kunya ta
kamata. Rufe ido tayi da hannuwanta kamar
yana kallonta. Sai kuma ta cigaba da kallon
fuskarsa....Huzaifa irin mutanen nan ne masu
kwarjini da daukar hankali. Kyakkyawan sajensa
ya zagaye habarsa zuwa saman bakinsa. Ji tayi
sonsa yana karuwa a zuciyarta sosai. Ta
shagala da kallonsa kamar daga sama taji yace
nayi miki kyau ne cikin sanyin murya. Dama
gadon ya tsage ta fada ciki haka taji don kunya.
Zata gudu yayi saurin riko ta. Zama yayi suna
fuskantar juna amma ta runtse idanunta yace ki
bude ido mana Aish. Ta girgiza kai da sauri.
Yayi murmushi to bari nima na kare miki kallo
yadda kika yi min. Kokarin noke kai yaga tana yi
sai ya tashi bari nayi alwala kada kisa mu
makara sallah.
Ko da ya dawo daga masallaci bata dakin. Ya
zauna karatu ita kuwa tana kitchen. Sauce tayi
da mince meat wanda yasha albasa, attaruhu,
koren tattasai, da caras. Sai ta kwaba flawa da
ruwa da kwai daya sai dan gishiri. Haka ta rinka
soyawa da mai. Yayi fari kuma yayi kyau sai ta
dama kunun gyada ta kai masa dining table.
takwas ta kusa lokacin da ta gama ta same shi
yana bacci. Bandaki ta shiga tayi wanka ta
shirya. Har ta gama yana bacci ta dan kwanta
itama don jikinta babu kwari sai. Basu tashi ba
sai shadaya da rabi. Ta rinka salati wai ta
makara. Yace to aikin me zaki yi? Tace to tashi
kayi wanka kazo kaci abinci. Wai yaushe rabon
duniya...tun Fadila na amarya ma sai ta gama
bacci take dora abinci. Yace ki kawo min daki
kawai I am feeling lazy. Tayi dariya ta fita main
falon gidan inda ta ajiye abincin. Aliya ta gani
akan kujera shi kuwa Aliyu akan dinning table
din suna cin abinci. Wurin kaca kaca sun zubar
da miya. Kuma abin takaicin ma ba'a plate suke
ci ba. Flask din suka bude suna tsoma
hannuwansu. Yau da ita ta haifesu kila sai tayi
musu duka. Hawayen ma sunki zuwa. A hankali
ta karasa gaban table kafin tayi magana Aliya ta
sauka da gudu tana kiran mummy. Shi kuwa
Aliyu akan table ya kasa sauka sai ihu yake
wayyo Abba ga Anti Mayya. A tsaye yake yana
ihu sauran kadan ya fado Aishatu tayi saurin
daukansa. Kafin ta ajiye shi sai dukanta yake da
hannuwansa. Fadila da Huzaifa kusan a tare
suka fito. Yaro kuwa ihu yake kamar ya shide.
Fadila ta karbe danta kaga ni ko Huzaifa ka
dauko matar da zata kashe min yara. Huzaifa
yayi mata tsawa shut up fadila! . Aishatu kujera
kawai ta dafe don kada ta fadi. Bazata iya
kwatanta bacin ranta ba. Huzaifa yace Aish me
ya faru Aish? Cikin rawar murya tace na fito
daukar abincinka na tarar suna ci. Wallahi banyi
musu magana ba ma. Aliyu naga yana ihu shine
na sauke shi fa. Fadila ta kalli wurin da suka
bata ta rinka dariya. Aliya tace Mummy ce ta
bude mana tace muci. waya Huzaifa ya kira
dreban Umma yace yazo gidansa yana jiransa.
Duk a falon suka zauna wurin shiru banda kukan
Aliyu. Kusan minti ashirin sai ga dreban ya iso.
Hannun Aliyu da Aliya ya kama ya kaisu
mota..ka kaisu wurin umma ka fada mata zanzo
anjima. Fadila tana ta masifa a bata yaranta ko
sauraronta baiyi ba. yana shigowa ya sami
takarda da biro ya zauna kan kujera ya fara
rubutu Aishatu tazo ta karbi biron. Gwiwarta a
kasa tace don Allah Dr kada kayi haka. Ya
dagota a hankali Aish mutuwa ce kawai zata
hanani abinda nayi niya. Fadila kije na sakeki
saki daya. Huzaifa me kace? Cikin fada da kuka
take maganar. Yace ki fice min daga gida
Fadila na gaji. Ta cigaba ni zaka saka saboda
wannan karuwar? Har dame ta fini? Matar da ta
gagara zaman gidan miji. Kaine mijinta na uku
fa.
Aishatu dama ta gama kulewa sosai tace Fadila
kinsan da me na fiki? Fadila ta jefa mata
harara. Aishatu ta rinka tafiya a hankali tana
juya jiki. Jikin da yake tada hankalin Huzaifa.
Yana ganin ta fara tafiya yace a ransa abin
yazo. Bata tsaya ko ina ba sai gabansa ta
kashe masa ido. A hankali take magana amma
yadda fadila zata ji. Da irin wannan karuwancin
na fiki sai ta hura masa iska a fuska, ya lumshe
ido har yaso ya manta a gaban Fadila suke ta
sake hura masa a kunne. A hankali tace I love
you baby...sai ta karasa rage tsazarar dake
tsakaninsu ta hanyar hada bakinta da nasa.
Wani shock yaji har kafarsa ya biye mata. Ita
kanta ta manta a inda take. shima kamar mai
rada yace I love you too Aish.
Kiris ya rage zuciyar Fadila ta buga ta dafe kirji
tsananin kishi na damunta. Kujera ta dauko zata
kwada musu sai suka ji sallamar mal Habu mai
gadi. Faduwar kujerar hannun Fadila yasa suka
kula da abinda tayi niyya ma. Da kyar Huzaifa
ya iya cewa Mal Habu ya akayi. Yace Yallabai
ana sallama da kai ne a waje. Ya ce sirikinka ne
Mal Sa'id.
RASHIN GODIYA ✂ 40
Yinin ranar har Huzaifa ya dawo ko kallon banza
Aishatu bata samu daga Fadila ba. Sai dai ta
kasa sakin jikinta da ita. Sai da ta gama
abincinta na dare ya dawo lokacin tana wanka.
Dakin yasha gyara da turaren wuta mai dadin
kamshi. Jikinta ma sai da ta dade tana turara
bayan tayi wanka. Ciwonta yayi sauki sosai don
babu kuraje ko kaikayi. Discharge ne ya rage
shima kuma bashi da yawa kamar da. Shiyasa
bata wasa da shan magani ko kadan. Sanin
baya gida yasa bata shiga toilet din da kayan da
zata chanja ba. Fitowarta tayi kai tsaye da
kaskon turaren wuta a hannu. Ai tana ganinsa ta
koma da gudu saboda towel ne kadai a jikinta.
Ta dan leqo da kai Dr...sai ya harareta tayi
saurin gyarawa baby don Allah ga hijab dina can
akan abin sallah. Yayi mata murmushi ni na gaji
hijab din nauyi kada na fadi garin dauka. Sai ta
koma ciki ta rufe kofar. Shiru shiru yaji bata fito
ba ya dauki hijab din ya mika mata. Haka ta fito
tana sunne sunnen kai ta kwashi kayan shafe
shafenta da kayan bacci zata koma toilet.
Huzaifa yayi saurin tashi kinga shirya abinki
kada kije ki kwaso mutanen bandaki ki rinka
dukana cikin dare....tasan tsokanarta yake
saboda labarin fahad da ta bashi. Tayi dariya
duk mijin da baya jin magana ake zanewa ai. Shi
dai Huzaifa sai ya fita ya barta ta shirya.
Yana cin abinci yana kara godewa Allah da Ya
hada shi da Aishatu. Komai nata tsaf sabanin
yadda ya saba gani a nasa gidan. Yau ba yadda
bata yi ba akan ya kwanta a kasa yaki. Tace to
ita zata koma kasan nan ma yaki. Suna ta
rigima da wasa ta sauke pillow kasa yace indai
zaki kwanta a kasa kizo na rama abinda kika yi
min. Kafin ya gama magana ta dawo dashi kan
gadon tayi kwanciyarta a can gefe. Kusan awa
daya da kwanciyarsu amma babu wanda yayi
bacci. Juye juye kawai yake tsakanin hannunsa
na hagu da dama baccin yaki zuwa. Duk da
duhun dakin ya san itama ba baccin take ba
shiru kawai tayi ta kasa juyawa ma kada su
fuskanci juna. Bargon da ya rufa dashi ya yaye
duk a banza yayi tsaki kawai yasa hannu ya
janyo Aishatu jikinsa. Ta fara kokarin zillewa
yayi mata rada a kunne lets stop pretending ko
Aish. This is what we want. Yayi ajiyar zuciya
sweetdreams my Aish. Amma kiyi addua kinji
ko. Daga haka bai sake magana ba sai
kankameta da yayi ta kwanta kan kirjin shi. A
haka suka yi bacci......
Daga ranar suka kara shakuwa da juna sosai.
Idan ya fita aiki sun rinka waya da text kenan.
Sabon jere su Yaya zainab suka yi mata wanda
dole yafi na da kyau da tsari saboda tsadar
kayan. Ana aikin jeren Fadila ta shigo suka
gaisa karshe ma dai da ita aka karasa aikin. Su
Saddiqa sunyu mamakinta sosai. Aka gama
Aishatu ta koma side dinta. Bayan kwana biyu
Anti Sauda tazo da su Islam suka yini a gidan.
Sunsha hira sosai don Aishatu da kyar ta bari
suka tafi. ita dai Anti Sauda shawar zaman
lafiya da rike gaskiya ta bawa Aishatu. Kuma ki
dage da yawan godiya ga Allah bisa niimar da
Yayi miki sai kiga Ya kara miki. Kuma ki
kasance harshenki baya rabo da azkar. Da zasu
tafi kayan kwalliya ta hadawa yaran suka tafi
cike da murna.
Tsakanin Fadila da Huzaifa ma zaman ya dan
daidaita tunda yaga ta dena abubuwan da take
masa. Hatta bangarenta ma tana gyara shi
sama sama. Main falon gidan kuwa Huzaifa ya
kafa dokar duk mai girki ita zata gyara shi. Ana
haka mai aikin Fadila ta dawo. Ba karamar
murna tayi ba don dan gyaran da take yi ji take
kamar ta shekara tana abu daya.
RASHIN GODIYA ✂ 39
Suna shiga gida Aishatu ta fara tattara
kwanunkanta da su Aliya suka bata. Huzaifa na
ganinta ya kwalawa Fadila kira ta fito a sanyaye
ita a dole ta shiryu. Ya sha kunu wa kike jira ya
gyara wurin nan? Kizo ki dauke ki wanke mata
kayanta. Fadila tace dama tsintsiya zan
dauko..Aishatu bari zan karasa. Itama Aishatu
tace haba ki bari kawai ta cigaba da tattare
kayanta. Sai da ta gama gyara wurin sannan ta
koma kitchen ta dumama sauran sauce din.
Ragowar wainar da ta ajiye saboda su Aliyun ta
hada masa a tray daban ta kai masa. A kwance
ta same shi ya rufe idanunsa. A bakin kofar ta
tsaya ta kasa shiga dakin. Wannan kunyar tasa
da take ji kada ace ta munafurci ce shine
tunaninta. Lokaci daya take ajiye ta a gefe sai
bukatarta ta biya kuma kunyar ta rufe ta. Anya
yau bata zake da yawa ba kuwa? Da wane ido
zan sake kallonsa ma. Zancen zuci ne ya fito fili
don bata san maganarta ta karshe ta fito ba. Ji
tayi yace da wadannan idanun masu rikitawa
Huzaifa lissafi mana. Yana maganar yana
tahowa gabanta. Tray din hannunta ne ya fara
rawa saboda yadda ta rude da irin kallon da
yake mata. Ba tare da ya dena kallonta ba yasa
hannu ya dauke mata tray din. Gaba daya ta
karasa rikicewa ta soma in'inar karfi da yaji.
Uhmm dama...dam...dama na..nace. Ya dan
kalleta kika ce me? Uhmm nace kayi..ko zakayi
hakuri akan dazu. Huzaifa ya jawo hannunta ya
zaunar da ita akan kujerar table din da yake
aiki. Ya zauna a gabanta amma ya juya mata
baya. Duk a takure take jin kanta sai ya kwantar
da kansa a cinyarta. You were saying nayi
hakuri. Hakuri akan me? Ta yaya ma zata iya
magana a yadda suke dinnan. Tayi shiru kamar
ruwa ya shanyeta. Daga kwancen yace na dauka
ma zaki bani hakuri ne for kissing me. A ranta
tace ashe yaji haushi...da saurinta ta daga kai
sama eh shine dama nace kayi hakuri ai.
Huzaifa yana lura da reaction din Aish dinsa.
Komai nata yana bashi shaawa yace kada ki
damu fa zan rama ne kawai. Tace zaka rama
kuma? Eh yanzu if you dont mind. Bata san
lokacin da ta ture masa kai ta rufe kanta a toilet
ba. Dariyarsa ta rinka ji daga ciki yace ki fito ki
bani abinci kafin na suma.
Sai da yayi laasar ya tafi gidan Umma. Ta
matsa masa da tambaya auta me ya faru ne,
jiya ka dauko yaran nan daga gidan Shukriya
yau ka turo su kafar Aliyu ko takalmi babu. A
takaice ya sanar da ita abinda fadila tayi amma
bai sanar da zancen saki ba. Umma duk
hakurinta tayi ta fada. Tace ni sai inje har gidan
naka wallahi. Haka kawai daga yin aure wannan
da iyayenta sunji ai rai zai matukar baci. Kuma
shine ka rufe min. Bansan an fasa mata kayan
daki ba sai yau. Yaya kubra tace Umma mun
kusa gama komai don gobe zamu karbo kayan
ayi jere. Fadan sai ya dawo kan kubra haka kika
iya ke kuma gyara gidan wani. Tun wuri ki
daidaita da mijinki ki koma. Kubra tayiwa
Huzaifa alama da ido.. mu bar wurin nan tun
wuri don ran umma ya baci.
Wasila bata sha wuyar samun number din Fahad
ba don akwai ta da shige shige. Yadda ta dau
zafi ko mijinta ne ya kara aure sai haka. Ana
turo number din ta kira shi. A lokacin sun gama
fada da yahanasu duk akan rashin haihuwa.
Kowa yana ganin laifin dan uwansa. Wasila ta
kira bai gane ko wace ba tace bazai gane ba
tana son su hadu ne akan maganar Aishatu ne.
Nan da nan ta samu attention dinsa yace zai zo
kano ranar asabar suka tsayar da wurin
haduwarsu. Da murna ta kira Fadila ta sanar da
ita tayi mata godiya sosai. Tana ajiye wayar tayi
dariya sai na nuna miki Fadila ba saar yinki
bace.
RASHIN GODIYA ✂ 40
Yinin ranar har Huzaifa ya dawo ko kallon banza
Aishatu bata samu daga Fadila ba. Sai dai ta
kasa sakin jikinta da ita. Sai da ta gama
abincinta na dare ya dawo lokacin tana wanka.
Dakin yasha gyara da turaren wuta mai dadin
kamshi. Jikinta ma sai da ta dade tana turara
bayan tayi wanka. Ciwonta yayi sauki sosai don
babu kuraje ko kaikayi. Discharge ne ya rage
shima kuma bashi da yawa kamar da. Shiyasa
bata wasa da shan magani ko kadan. Sanin
baya gida yasa bata shiga toilet din da kayan da
zata chanja ba. Fitowarta tayi kai tsaye da
kaskon turaren wuta a hannu. Ai tana ganinsa ta
koma da gudu saboda towel ne kadai a jikinta.
Ta dan leqo da kai Dr...sai ya harareta tayi
saurin gyarawa baby don Allah ga hijab dina can
akan abin sallah. Yayi mata murmushi ni na gaji
hijab din nauyi kada na fadi garin dauka. Sai ta
koma ciki ta rufe kofar. Shiru shiru yaji bata fito
ba ya dauki hijab din ya mika mata. Haka ta fito
tana sunne sunnen kai ta kwashi kayan shafe
shafenta da kayan bacci zata koma toilet.
Huzaifa yayi saurin tashi kinga shirya abinki
kada kije ki kwaso mutanen bandaki ki rinka
dukana cikin dare....tasan tsokanarta yake
saboda labarin fahad da ta bashi. Tayi dariya
duk mijin da baya jin magana ake zanewa ai. Shi
dai Huzaifa sai ya fita ya barta ta shirya.
Yana cin abinci yana kara godewa Allah da Ya
hada shi da Aishatu. Komai nata tsaf sabanin
yadda ya saba gani a nasa gidan. Yau ba yadda
bata yi ba akan ya kwanta a kasa yaki. Tace to
ita zata koma kasan nan ma yaki. Suna ta
rigima da wasa ta sauke pillow kasa yace indai
zaki kwanta a kasa kizo na rama abinda kika yi
min. Kafin ya gama magana ta dawo dashi kan
gadon tayi kwanciyarta a can gefe. Kusan awa
daya da kwanciyarsu amma babu wanda yayi
bacci. Juye juye kawai yake tsakanin hannunsa
na hagu da dama baccin yaki zuwa. Duk da
duhun dakin ya san itama ba baccin take ba
shiru kawai tayi ta kasa juyawa ma kada su
fuskanci juna. Bargon da ya rufa dashi ya yaye
duk a banza yayi tsaki kawai yasa hannu ya
janyo Aishatu jikinsa. Ta fara kokarin zillewa
yayi mata rada a kunne lets stop pretending ko
Aish. This is what we want. Yayi ajiyar zuciya
sweetdreams my Aish. Amma kiyi addua kinji
ko. Daga haka bai sake magana ba sai
kankameta da yayi ta kwanta kan kirjin shi. A
haka suka yi bacci......
Daga ranar suka kara shakuwa da juna sosai.
Idan ya fita aiki sun rinka waya da text kenan.
Sabon jere su Yaya zainab suka yi mata wanda
dole yafi na da kyau da tsari saboda tsadar
kayan. Ana aikin jeren Fadila ta shigo suka
gaisa karshe ma dai da ita aka karasa aikin. Su
Saddiqa sunyu mamakinta sosai. Aka gama
Aishatu ta koma side dinta. Bayan kwana biyu
Anti Sauda tazo da su Islam suka yini a gidan.
Sunsha hira sosai don Aishatu da kyar ta bari
suka tafi. ita dai Anti Sauda shawar zaman
lafiya da rike gaskiya ta bawa Aishatu. Kuma ki
dage da yawan godiya ga Allah bisa niimar da
Yayi miki sai kiga Ya kara miki. Kuma ki
kasance harshenki baya rabo da azkar. Da zasu
tafi kayan kwalliya ta hadawa yaran suka tafi
cike da murna.
Tsakanin Fadila da Huzaifa ma zaman ya dan
daidaita tunda yaga ta dena abubuwan da take
masa. Hatta bangarenta ma tana gyara shi
sama sama. Main falon gidan kuwa Huzaifa ya
kafa dokar duk mai girki ita zata gyara shi. Ana
haka mai aikin Fadila ta dawo. Ba karamar
murna tayi ba don dan gyaran da take yi ji take
kamar ta shekara tana abu daya.
RASHIN GODIYA ✂ 41
Aliya da Aliyu sun dawo gida Huzaifa ya kaisu
dakin Aishatu da kansa. Aliya sai rabe rabe take
a jikin bango don tafi Aliyu wayo. Huzaifa yace
musu wannan itama mamanku ce kunji ko. Daga
yau nan ne gidanta kada na sake jin kun kirata
da wani suna mara dadi sai na zane ku. Aishatu
tayi murmushi ta mika musu hannu ku zo mu
gaisa. A dan tsorace suka karasa gabanta suka
mika mata hannu. Ta basu sweets harda ice
cream.. daga nan suka saki jiki har da cin
abinci. Tana ta musu wasa Aliya tace mummy
tace mu rinka kiranki Maama. Abin yayi wa
Aishatu da Huzaifa dadi suna cin abincin Aliyu
yace maama abincinki yafi na mummy dadi, zaki
dawo dani nan dakin? Huzaifa yace kana son
dawowa ko. Yace eh Abba ita Aliya sai ta zama
yar mummy ni kuma ga maama na. Ya koma
cinyarta ya zauna. Huzaifa ya rada mata
maaman Aliyu yaushe zaki masa kani ne? Kai ta
sunkuyar tace ba rana bare wata. Yayi dariya kin
kusa gama shan magani dai. Saboda haka ku
fara saka rana.
Fadila ke ta kai kawo a daki tun rana da taji
labarin tafiyar Aishatu da Huzaifa Umra ta nuna
bacin ranta a fili. Ba Umrar bace ta dameta
kamar tafiyar da zasuyi tare. Duk inda Huzaifa
zaije tare suke zuwa ko bayan ta fara haihuwa
baya yarda ya tafi ya barsu a gida. Yau ga
tafiyar tana ji tana gani zaiyi da Aishatu.
Hawaye mai zafi ya sauko mata ba karamin
daurewa take ba da tana gani Aishatu ke shigar
mata dakin miji.
Huzaifa na daki shiru har shabiyu saura na dare
Fadila bata shigo ba. Ya kira wayarta yaji shiru
bata dauka ba har sau uku sai ya tafi dakin
nata. Bata cikin falo ya duba dakinta har da
nasu Aliya bata nan. Hankalinsa ya dan tashi ya
tafi dakin Aishatu. Da sallama ya shiga ya ganta
tsakiyar yara suna bacci. Dadi da son Aishatu ya
karu a zuciyarsa. Cikin kankanin lokaci ta siye
zukatan yaran. Rufe musu kofa yayi ya koma.
A tsakar falo ya ganta ta bude baki ganin daga
ina ya fito ta fara halin. Kuka take yanzu
Huzaifa ranar girkina ma sai ka shiga dakin
Aishatu? Ya ce Fadila kenan, dakinki na duba
ban ganki ba. Suma yaran basa nan shiyasa
nazo dubawa. Tayi gaba kawai ta shiga dakinsa
yabi bayanta wai meye yake damunki ne Fadila.
Dole kace meye yake damuna mana. Don cin
amana sai ka biya muku zuwa Umra ku kadai.
Idan adalcin zaka yi ai dani zaka fara zuwa
sannan wani lokacin kaje da ita. Huzaifa yayi
ajiyar zuciya Fadila rigima to ai bani na biya ba.
Alh Sabiu ne ya biya mijin Yaya Zainab. Kuma
idan baki manta ba munje hajji da umra dake.
Wace kasa na taba zuwa batare dake ba ma.
Harararsa tayi kafin tace karyar banza yanzu ka
fara aure da bai taba biya maka ba sai yanzu.
Kunje kun gama kulla munafurcinku shine zaka
fada min son ranka. To dole kasan yadda zaka
yi dani wallahi don bazan zauna gadi ba.
Zancenta ya fara kular dashi ya dai daure yaki
magana. Wuri ya samu ya kwanta ta fita tare da
bugu kofa. Bata jima ba ta dawo da sauri
Huzaifa ina 'ya'yana? Na duba basa dakinsu.
Yana daga kwance yace suna dakin Aishatu.
Fita tayi da gudu wallahi bazasu kwana a can
ba. Haka kawai kai din na hakura kuma yaran
ma namu ne yanzu mu biyu? ta haifi nata mana
tunda ta ita zuwa dakin miji. Huzaifa yace na
rantse miki idan kika fita daga dakin nan sai
ranki ya baci. Sai ki rinka abu kamar wata jahila.
Ki fitan na gani. Dole ta hakura ta kwanta tana
bambami. Can yaji ta dan matso kusa dashi
Abban Aliya kayi bacci ne? Uhmm Abban Aliya
kayi hakuri da abinda nayi. Ji yayi ta rike masa
hannu yayi dan murmushi ya sake rintse ido.
Shiru yayi mata yar rainin hankali kawai...ta iya
shafawa idonta toka sai tata ta kawota ta shiga
kwantar da kai.
Kafin ya dawo daga massalaci da asuba Fadila
ta bude wata drawer zata dauki dan kudi yadda
Wasila ta bata shawara. Wai idan bata dauka ba
Aishatu zata kwashe. Tana cikin nema ne tayi
karo da kwalayen magungunan Aishatu. Ta
dauka tana jujjuya su a hankali ta rasa gane ko
na meye. A iya saninta Huzaifa baya shan wani
magani wadannan kuma an sha da yawa a ciki.
Tana ta juyayin abin a ranta sai ta bude
takardar cikin daya tana karantawa taga ance
kada mai ciki tasha. Sannan an ce idan an dena
ganin dischage sai mace ta dena sha. Hannunta
har yana rawa ta kwafe sunan maganin a
wayarta don ta tabbatar na Aishatu ne tunda
mace ake ta ambata.
Haka Huzaifa ya dawo ya sameta akan gado
tana browsing. Bakinta bude ciki da mamaki da
fargaba. Yanzu Aishatu na fama da mugun ciwo
irin wannan shine ya aurota. Kuma dole yasan
da ciwon tunda haka kawai Aishatu bazata bar
magani a dakinsa ba. Huzaifa na dawowa tayi
saurin jifa da wayar ta mike da sauri. Yace ina
zaki tace alwala. Yanzu bakiyi sallah ba kika
zauna duba waya da asuba. Allah Ya shiryeki.
Tace amin amin dai, a ranta kuwa murna tayi
don wannan sirrin kamar ta baza shi ta gama.
Kai anya kuwa Huzaifa zai kusanci Aishatu da
ciwo........no wonder ta taba shigowa taga
pillow da abin rufa a kasa. Kai wannan abu yayi
dadi wasila zata sha labari.
RASHIN GODIYA ✂ 42
Wasila a kashingide kan gadon Fadila tace ai ko
kadan kada ki tona mata asiri ta hanyar baza
zancen nan. Komai a hankali ake binsa. Ni
yanzu kirawo min ita mu gaisa kiga yadda zanyi
sai ki dau course. Koda yake gara naje da kaina
sai taga kamar an bata mahimmanci. Wasila tayi
sallama a kofar falon Aishatu Aliyu ya amsa.
Fadila tace kinga yadda ta raba ni yarana ko.
Wasila tace su Aliyu manya har ka iya amsa
sallama haka kamar babban mutum. Ya durkusa
Anti ina wuni, maama na ce ta koya min. Su ka
sake hada ido lallai da sake. Aisha ce ta fito
daga daki sanye da dogon skirt baki sai wata
farar sleeveless riga. Gashinta ta daushe shi da
ribbon daga gefe sai kamshi take, hannunta duk
kumfa. Tace bismillah ku zauna mana baki ne
damu. Daga ciki suka ji muryar Aliya tana cewa
Maama in goge jikina kafin kizo. Aishatu tace eh
ga towel nan ki dauka. Fadila ta dan wayance
wanka tace kiyi mata ko? Tsifa na turata wurin
Laure fa. Aishatu tace lauren ce ta yanke a
hannu shine na karasa mata tsifar aka wanke
kan. Nan da nan Fadila ta hade rai har sai da
wasila ta dan take mata yatsa alamun ta saki
fuska. Aishatu ta mayar da hankalinta ga wasila
sannu da zuwa ina wuni. Wasila ciki da faraa
tace lafiya kalau amarya ya gida da kiriniyar
yara? Ai basu da kiriniya Aishatu ta amsa tana
shafa kan Aliyu yaran albarka ne. Wasila tace
sannu Aishatu kin sha aiki ga jiki kina fama
dashi. Cak Aishatu ta tsaya a jikin fridge da take
shirin daukowa wasila lemo. A sanyaye ta waigo
jiki kuma? Wasila tace kinsan masu lalura irin
taku suna bukatar hutu sosai. Kuma dai a rinka
hankali kada wasu su dauka. Cup din hannun
Aishatu a take ya fado bakinta har yana rawa
tace wane ciwo? Sai Fadila tace rabu da ita kinji
kanwata wai ta dauka ciki gareki kada nima na
samu. Na fada mata ai ke da ciki ba yanzu ba
sai nan gaba. Aishatu zancensu yana kara
kidimata ta danyi yake ta zauna. Fadila tayi
murmushi ina nufin sai kin gama cin amarci.
Aure wata biyu ai baki fara komai ba a
amarcinki. daga nan suka tashi suka fita har
tana jin dariyarsu. Gaba daya sai ta rasa
nutsuwa. Ta kasa gane hasashe suke na cikin
ko kuwa dai zancen lalurarta ne ya fito fili. Haka
ta gaji da tunani ta hakura.
A daki wasila tace to kawata kinga yadda ake yi
dai. Daga mata hankali zakiyi ta yi daga baya
sai ki fasa kwan kowa yaji. Haka kuwa akayi
Fadila sai tayi ta shagube idan taga Aishatu.
Abin ya rinka damunta sosai, dan sakin jikin da
take tare da Huzaifa ya fara ja baya. Ana haka
wata jumaa Huzaifa ya sanar dasu zasu je Rano
gaba dayansu. Fadila har tace bazata ba sai ta
tuno maganar wasila tace zata bisu. Ranar
asabar kafin karfe tara sun kama hanya. A mota
suna ta hira Aishatu da Fadila kamar wasu yan
uwa. Hirar ma Fadila ke kawo ta.
Gidan kowa murna anga iyalin Huzaifa. Fadila
dai ta kasa sakin jiki sosai dasu. Ita kuwa
Aishatu da yaran kamar wadanda suka saba. A
falon wan baban Huzaifa duk yawancin matan
yan uwa da 'ya'yansu suka taru ana ta tsokanar
juna. Wata abokiyar wasan Huzaifa ta dubi
Aishatu...anti amarya ina fata mun kusa zuwa
suna ko. Murmushi tayi cike da kunya don akwai
manya a wurin Huzaifa yace kin tanadi shanun
suna ko, baki ji an hana yanka rago ba sai
shanu. Duk aka yi dariya Fadila tace rabu dasu
kanwata ke ina kika ga lafiyar yin cikin yanzu.
Duk kuyi ku gama sai nan gaba. Aishatu da
Huzaifa suka yi saurin kallon Fadila ita kuwa ta
basar. Matan wurin sai suka mayar da maganar
wasa. Har suka dawo gida Aishatu bata da
nutsuwa.
Ba jimawa da faruwar haka kuma Nurain yazo
gidan kanin Aishatu na biyu. Tayi murnar
ganinsa sosai, da yake yana da saukin kai har
kasa ya gaishe da Fadila. Da taimakon Habu
maigadi ya kinkinmo kwandon tumatir masu
kyau ya shigo dashi main falo. yace baba ne ya
dawo daga getso jiya gonarsa tayi albarka.
Aishatu ta kira babanta tayi masa godiya. Da ta
gama tana durkushe da ledoji a hannunta tana
rabon tumatir din har da yan uwan Huzaifa
saboda manya ne sosai masu kyau. Tace Baba
yasan ina son tumatir shiyasa yayi min wannan
babbar kyautar. Fadila ta yatsina fuska sai ta ce
ai da yake ance ana son irinku su rinka shan
tumatir sosai yana da sinadarin kariya daga
kamuwa da cancer. Aishatu da Nurain suka
kalleta cikin rashin fahimta. Aishatu tace ban
fahimci maganarki ba. Fadila ta dafa mata
kafada ba wani abu nake nufi ba. Kinsan shi
tumatir yana da sirruka masu tarin yawa. Zai
miki amfani sosai lokacin da kika warke. Ta
tashi ta shige daki. Nurain yace anya Yaya
matar nan kalau take kuwa. Ni duk zancen nata
na kasa ganewa. Aishatu bata ma jinsa sosai
hankalinta ya tafi ga tunanin da take. Wai yan
kwanakin nan meye yake damun Fadila take
mata irin maganganun nan. Banda iyayenta da
Anti Sauda, Huzaifa ne kadai yasan lalurarta.
Gabanta ya fadi....Allah Yasa ba fadawa Fadila
yayi ba. Sai tayi saurin kwabar kanta. Dr Rano is
a good man bazai taba tozarta rayuwarki ba.
RASHIN GODIYA ✂ 43
Aishatu ta tambayi Huzaifa zuwa gidan Anti
Sauda ta yini ya amince. Tace nagode Allah Ya
saka da alkairi. Cikin mamaki ya kalleta don na
baki izinin fita kawai kike min wannan godiyar?
Ta na bude masa maballan rigarsa tace ai ya
wuce kawai. Ya rike hannuwanta biyu yanzu
idan nace bazaki ba zaki hanu? Sosai ma kuwa.
Haram ne mace ta fita ba tare da izinin mijinta
ba. Huzaifa ya rungume ta sosai na sani Aish
amma banyi tsammanin akwai macen da fitarta
ta dogara da izinin mijinta ba. Allah na gode
maKa da Ka bani Aishatu a matsayin mata. A
hankali itama tace Alhamdulillah. Yace kinsan
kin kusa dena shan magani ko. Idan kika shanye
dose din da na siyo jiya zamuje ayi miki pap
smear. Yana dakina idan kin shigo anjima zan
baki. Ya daga gira... Hopefully zuwa time din kin
gama warkewa sai ki zama amaryar gaske.
Murmushi suka yiwa juna Ya saita bakinsa a
kunnenta did I tell you how much I love you?
Tana dariya tace noooo. Wani irin kallo yake
mata tana ja da baya yace zo na fada
miki....suka ji an bude kofar dakin. Fadila ta yi
saurin ja da baya kuyi hakuri wallahi ban san
kuna ciki ba. Huzaifa ya daka mata tsawa wane
irin iskanci ne wannan Fadila. Ta dan nuna
alamun rikicewa to ai bansan ka dawo ba ne.
Kuma naga nan dakinta ne. Yace shi dakin nata
bazaki iya yin sallama ba. Fadila tana bashi
hakuri Aishatu na bashi. Yayi tsaki ya cewa
Aishatu idan kun gama ki sameni a daki. Kuma
kiyi sauri. Har ya rufo kofar Aishatu tana
murmushi....tana son mijinta fiye da tunaninta.
Ta dubi Fadila da ta tsaya jikin kofa ki zauna
mana ko mu koma falo ne. Fadila ta sunkuyar
da kai kasa sai ga hawaye yana zuba. Aishatu
na gani ta dawo kusa da ita. Subhanallah me ya
faru? Fadila ta shaki hanci nasan Huzaifa ba
karamin fushi yake dani ba akan abubuwan da
nayi masa a baya shiyasa baya min uzuri yanzu.
Haba ki dena kuka tunda mune a karkashinsa
hakuri zaki sake bashi. Fadila ta goge ido to
nagode sosai Aishatu Allah Ya barmu tare.
Dama jiya ne da ya dawo lokacin kin kwanta ya
bani wadannan maganin na kawo miki sai bacci
ya dauke ni. Zuciyar Aishatu sai harbawa take
da sauri da sauri don bakincikin da ke cin ranta.
Fadila tana kallon yanayin Aishatu tace ga
maganin ki taimake ni kisha yanzu kuma don
Allah ki rufa min asiri kice tun a jiya na baki.
Kinsan lalurar shan magani kullum babu dadi.
Amma yace daga wannan kin gama ai. Shiru
Aishatu bakin magana. Fadila tayi alamun
tausayi da fuskarta baki ga yadda ya damu da
lalurar nan taki ba. Nima duk na damu bayan ya
fada min. Ta tashi tsaye bari naje daki...af! Ai
kuwa ina da kawa mai gyaran jiki idan kin warke
sai muje. Tana fita Aishatu ta fashe da kuka ita
kuwa Fadila ta kwashe da dariya. Kadan kika
soma gani yarinya.
Huzaifa har ya gaji da jiran Aishatu yace ko dai
Fadila ta ja ta da zance ko kuma bacci ya
dauke ta. Yayi ta kiran wayarta a kashe. Yaje
dakin kuma tana sallah. Haka ya zauna yana
jiran ta idar har kusan minti talatin taki idarwa.
Ta sallame raka'a ta takwas a kirgensa yayi
saurin tsayawa gabanta. Muryarta har rawa
take ta daga hannuwa sama zata yi kabbara ya
rike su. Haba Aish tun dazu nake jiranki. Ki
duba time har daya saura baki bani abinci ba.
Kukan da take rikewa ya kwace mata. Ya
rungume ta yana rarrashi me aka yi miki. Fadila
ce ko? Cikin kuka tace bani da lafiya ne. Sai
tauyinta ya kara kamashi kuma shine zaki yi
shiru tun dazu. Ita dai kukanta take yi. Sai da
tayi shiru yace Aish yaushe kika koyi karya ne.
Ki fada min gaskiya me aka yi miki. Tace
tausayin kaina nake ji. Huzaifa ya riketa sosai
Aish this is so unlike you. Ki fada min gaskiya.
Sai ya fita kawai yana kiran Fadila. Aishatu ta
na riko shi yaki sauraronta. Duk da dare ne
Fadila ta jima tana kasa kunne taji lokacin
tashin bomb.
RASHIN GODIYA ✂ 44
Kafin ya shiga dakinta Fadila ta shige cikin
bargo tana baccin karya. Da karfi ya buga kofar
ya bude. Ta tashi tana murza ido ita ga mai
bacci me ya faru Abban Aliya? Yace ki taso ki
biyoni daki yanzun nan sannan ya koma. Da bin
bango ta shiga a dan tsorace ta ga Aishatu ta
takure a kasa tana kuka. Tayi kwafa a ranta
lallai tarkonta yayi kamu. Huzaifa sai kai kawo
yake a dakin yace kinga samu wuri ki zauna zaki
wani tsayawa mutane a ka. Sai da ta zauna
shima ya zauna akan kujera Fadila ki fada min
gaskiya me ya hadaki da Aishatu. Ai itama sai
kukan Aishatu ba dai kin masa zancen maganin
ba, ke da na rokeki ki rufa min asiri kada yasan
yau na baki. Tuni Aishatu ta karasa yarda da
cewa Huzaifa ne ya fadawa Fadila tunda gashi
bata ji tsoron maimaita zancen a gabansa ba.
Dan zaman da tayi daga gefensa a kasa ta tashi
ta canja wuri gaba daya. Shi kuwa ya kasa gane
inda su biyun suka dosa yace Fadila wane
maganin. Ta kalli Aishatu ina ledar? Aishatu ta
nuna mata tana kan bedside drawer. Fadila ta
dauko ta durkusa a gabanshi ta mika masa.
Yana gani yayi saurin tashi Fadila a ina kika
dauko ledar nan? Dan kukanta ta cigaba kayi
hakuri Abban Aliya nasan tun daren jiya kace na
bata shine na manta sai dazu da na shiga
dakinta. Dama ni nace ta sha na yau yadda
bazaka gane ba. Ta kalli Aishatu nasan ba fada
masa kika yi ba, ganewa yayi na kwana daya ne
ko. Huzaifa yace ke ni ban fahimce ki ba. Aish
yi min bayanin abinda ya faru. Fadila tace ni dai
na fuskanci kamar baki so ya sanar dani ba ko?
Shima ai ba son ransa bane. Shimfida na gani a
kasa na tambayeshi shine yayi min bayanin
infection dinki. Yace saboda karnin discharge
ma shiyasa ba kya rabo da turaren wuta da air
freshner. Nasan ba dadi miji ya nuna kyamar
matarsa shiyasa na bashi shawarar ya daure ya
kwana tare dake. Ta dan masa kallon tuhuma
dont tell me baka dauki shawara ba.
A lokaci Huzaifa ya tabbatar Fadila makira ce
ajin farko. Yana kallo ta tashi ta rungume
Aishatu kiyi hakuri kinji kanwata. Nasan da ciwo
amma kamar yau ne komai zai daidaita
tsakaninki da mijinki. Duk mace ai tana son
ganin danta bayan aure. Burina ki warke yadda
zaki iya samun ciki ki cika gidan nan da yara.
Aishatu fuskar Huzaifa take kallo yadda ya
saduda cewa ta gama dashi. Har gumi yake
saboda yadda hankalinsa ya tashi. Aishatu duk
fushinta a take ya sauka. Idan Huzaifa yana son
tona mata asiri ko kyamarta bazai aureta ba.
Kuma tun yaushe suka fara kwana wuri daya
ma. Tuntuni baiji kyamar ba sai yanzu? Ta yaba
da kyaun halin Huzaifa da na yan gidansu.
Hakika kullin Fadila ne wanda ta jefa mata
shakku a zuciyarta game da mijinta.
Tana tunaninta taji yace Fadila abin har ya kai
ga ki yi min sharri haka. Aish wallahi karya take
min. Yadda yayi maganar ya kara bata tausayi
sosai. Hawaye ya zubo mata ta share da bayan
hannunta, gabanta yazo ya tsaya a sanyaye zai
sake magana tasa hannu ta rufe masa baki.
Cike da tsantsar so tace Babyna did I tell you
how much I love you? Yayi murmushi mai cike
da takaici saboda Fadila ta masa wulakanci
sosai. Yace No. Ta rungume shi ta baya to muje
muyi wanka sai na fada maka. Huzaifa da Fadila
gaba dayansu sunyi matukar mamakin abinda
Aishatu tayi. Tamkar Fadila bata dakin ta dawo
gabansa ta tsaya tana masa shagwaba ni ka
zuge min zip din na kasa. Bai iya cewa komai
ba ya zuge zip din doguwar rigar atamfar dake
jikinta. Ta ja hannunsa suka shige toilet suka
bar Fadila a tsaya baki bude.
Bata san lokacin da tace kan uba anya yarinyar
nan mutum ce kuwa? Ta fita ta bugu musu kofa
da karfi. Bata kula da lokaci ba ta kira wasila
tana kuka, dama itama jiran feedback take bata
kwanta ba..tsam ta tashi daga daki ta koma
wani dakin ta amsa wayar. Ni na rasa yadda
zanyi da yarinyar nan. Ta bata labarin duk yadda
suka yi Wasila tace kwantar da hankakinki next
week Fahad zai zo. Su Aishatu kuwa suna jin ta
fita suka fito. Huzaifa zaiyi magana ta ce kada
kace komai. I trust you. Kissing dinta yayi tare
da godiya ga Allah.
RASHIN GODIYA ✂ 46
Fadila ta aikawa Fahad text tana son su hadu
ranar litinin da safe a kofar makarantar su Aliya.
kamar yadda ta sani wannan litinin Huzaifa yana
da call wato aikin kwana a asibiti. Da wuri ta
tashi ta shirya Aliya harda yi mata girki ita da
duk ranar girkinta sai dai ta bata biscuit da
lemo.
Ta shiga dakin Aishatu ga yarki zata tafi school
tace bata ga Maama ba. Aishatu ta gyarawa
Aliyu kwanciya ta dauko homework din Aliya ta
saka mata a jaka. Sai kun dawo Aliya Allah Ya
bada saa. Fadila tace amin maaman yara.
Lokacin sati uku kenan da faruwar rikicin da ya
jawowa Fadila saki na biyu. Tun lokacin take
neman shiri da Aishatu. Tana dai kokari su
zauna lafiyan amma ta gagara sake mata.
Mutum kamar Fadila ba haka kawai ake sakewa
dashi ba. Kamar maciji take mai jiran sara da ya
sami dama.
Aliya na fita daga motar ta fara neman numbar
Fahad zata kira shi. Seat din gaba taji an bude
sai ta ga mutum ya zauna a gefenta. Bude baki
tayi zata yi ihu yace shut up and drive. Kamar
tasan muryar amma bata tantance ba jiki na bari
tace tare muke da mijina. Yayi yar dariya irin
wadda ta taba ji a waya. Sai yanzu ta gane
shi...Fahad? Yace eh. Bata sake magana ba ta
rinka bin hanyar da ya nuna mata sai da suka je
gate din central hotel yace ta shiga. Jikinta ya
danyi sanyi kana hauka ne? Hotel ne fa sai wani
ya gan mu. Fahad ya bata rai sosai idan kin
fasa ne shikenan. Aikin banza kai, ki neme ni
sannan ki nuna tsoro. Ai na zata mijin naki dan
gwal ne zaki iya komai dominsa. A harzuke tace
kada ka gaya min magana mana. Mijina yafi
karfin ka zage shi. Fahad yace eyye kaga mai
miji...yana magana yana tafa hannu. Fadila a
tsorace take da shi tace muje amma kayi sauri
kada ya koma gida bana nan. Har dakin da yayi
masauki ya kaita duk da ta san hakan bai dace
ba amma tana ji a ranta babu abinda bazata yi
ba akan raba Huzaifa da Aishatu. Mijinta ne ita
kadai. Sun hada plan din duk yadda zasu
bullowa lamarin yace to sai naji daga gareki.
Fadila tace shikenan.
Tana fita ya koma kan gadonsa ya zauna.
Yahanasu ya kira a waya tace ya aikin kayi
breakfast kuwa? Ya gyara kwanciya banyi ba na
dan soma abinda ya kawo ni ne. Tace to Allah
Ya dubi niyya my dear. Yace amin Yaha....yana
jin ihunta tana cewa Allah bana so, wane irin
Yaha kamar a kauye. To ba yar kauyen bace ya
amsa yana dariya.
Huzaifa daga wurin aiki gidan Umma ya wuce.
Yaya kubra tace to meye kuma kayi mana
sammako yau kamar wani gwauro? Yayi
murmushi yau a waliyinki nazo. Ta jefa mishi
dankali Umma kinga autanki zai min rashin
kunya ko? Umma tace rashin kunya ko gaskiya
kaga shigo daga ciki autan umma muyi magana.
Yaya kubra ta tsaya daga jikin kofa tana jin
bayanin Huzaifa akan yadda suka yi da mijinta.
Yayi alqawarin raba musu gida da mahaifiyarsa
tunda ya tabbatar zaman tare ne yasa Hajiyar ta
koyi sa wa iyalinsa ido. Gobe zasu je Rano tare
ya biya sadaki. Yaya kubra ta ce duk yaushe
aka gama wannan shawarar ina cikin gidan nan.
Nifa ba cewa nayi ya rabu da Haj ba. Kawai
abinda take yi ne bana so. Umma tace ya rage
naku ni dai wannan zaman naki ya isheni a
koma ayi bautar aure. Daga nan Huzaifa ya
wuce gida. Sai da ya shiga dakin Aish suka
gaisa sannan ya tafi dakinsa. Fadila yanzu
kwantar da kai take sosai shi dai yana zaune da
ita ne kawai saboda Allah amma duk ta fice
masa a rai.
Aishatu kuwa gyaran jiki suke zuwa da Anti
Sauda sauki ya samu. Anti Sauda har tsokanarta
take wai tana sheki saboda zata fara amarci.
Tace kai antiña ni kunya nake ji. Ta kai mata
duka a baya kyaji da gulmarki bayan nasan
kwana bakwai dinnan sunyi miki nisa. Aishatu ta
sake dariya. Wayarta ce tayi ringing gashi duk
jikinta an shafe shi da wani abu an rufeta da
bargo ga garwashi da turaren wuta mai matukar
kamshi. Ta kalli wayar da kalar tausayi alamun
anti sauda ta saka mata. Anti Sauda tace kaji
min yarinya fa. Tun dazu yake bugowa ku gaisa
kamar na sato ki. Aishatu tace na karshe ne
Anti daga wannan zan fada masa yayi hakuri sai
an goge min yadda zan dauka da kaina. Anti
Sauda da mai gyaran jikin suna ta dariya. Daga
lokacin da suka fara Huzaifa ya kira sau hudu
duk Antin ke saka mata wayar a kunne. Wannan
karon tana dora mata tace baby kaji Anti Sauda
ko.....muryarta da yaji tayi masa dadi. Yaushe
rabon da yaji wannan muryar mai taba masa
zuciya. Shiru taji tace baby ko baka ji na ne.
Yace ina jinki Aisha....Inna lillahi wa inna ilaihi
rajiun. Da karfi tace FAHAD? Anti Sauda ta yar
da wayar ba shiri.
RASHIN GODIYA ✂ 45
Kasa bacci Huzaifa yayi a daren saboda bacin
rai. Hakika ba don Allah Ya taimake shi Aishatu
mace ce mai fahimta da yin uzuri ba bai san da
yadda zai fitar da kansa ba. Zama da Fadila
bala'i ne, sai yanzu ma ya kara tabbatar da
hakan. In Allah Ya yarda sai ya toshe duk wata
kofa da zata sake kawo musu matsala.
Yana dawowa daga sallar asuba ya tafi dakinta.
kwance tace hankali kwance tana bacci. Lallai
bata da kunya duk abinda tayi har ta iya bacci
haka. Takardar da ya rubuto tun kafin ya shigo
gida ya ajiye a karkashin wayarta ya fita. sai
yanzu yaji wani dadi kamar an sauke masa
katon dutse. Yaransa yasan ko bashi da rai
Aishatu zata rike su amana. Ya koma daki suka
koma bacci bayan sunyi karatu don bacci bai
ishesu ba a gidan. Wurin karfe takwas suka ji
wani gigitaccen kuka. Aishatu ta farka a tsorace
baby waye wannan? Kaji wani irin ihu kuwa. shi
kuwa ko yunkurin tashi baiyi ba tunda yasan mai
kukan da dalilin kukan. Aishatu ta dan jijjiga shi
don Allah ka tashi ka duba. Yayi murmushi na
duba wato idan dodo ne ya cinyeni ni kadai ko?
To anki wayon. Tace to ni bari naje ya cinyeni
tunda haka kake so. Ya janyo hannunta dawo ki
kwanta kinji Aish. Fadila ce take yi. Ai tuni ta
mike shine kake kwance bayan kasan mai yi.
Idan wani abin ne ya faru a gidan fa. Huzaifa ya
juya baya ya gyara kwanciya sai ya cinyeta ita
kadai. Ganin da gaske bazai fita ba sai ta tashi
ta tafi dakin fadilan. Kuka take sosai tana fizge
fizge. Aishatu dai sai taki karasawa ciki don
tsoro ta bata. Fadila me ya sameki? Da katon
zaginta ta juyo zata fara sai ta tuna yadda suka
yi da uwarta wasila. Ta rarrafa ta rike kafar
Aishatu ki min rai Aishatu kingani. Abban Aliya
ya sakeni, na biyu kenan. Duk abinda nayi jiya
sharri ne da karya. Ni kadai nayi bincike na
batare da ya sani ba. Daga yau na dena na
hakura na tabbatar aurenku babu mai iya raba
shi. Wannan masifaffen kishi ta fada tana dafe
kirji ki tayani addua Allah Ya yaye min. Dama
tsoro nake kada ki rabani da mijina to gashi da
kaina nake sawa ya nisance ni saboda halaye
na. Kayya na cuci kaina na biyewa kishin banza.
Tausayi sosai ta bawa Aishatu tace nawa yayi
miki. Fadila a ranta tace ji kamar ba ita ta zuga
shi ba. Daya ne ta fada tana ta matsar kwalla.
Ki rufa min asiri yadda Allah Ya rufa miki. Tare
suka juya zasu dakinsa suka ganshi a tsaye.
Yace Aish zo ki wuce daki. Kin zauna tana fada
miki karya da gaskiya kina ji. Zuwa yanzu ya
kamata kisan halin Fadila. Tafiyarta ita ce
alkhairi garemu. Fadila ta fara bashi hakuri
kawai sai ta fadi kasa. Huzaifa yayi dariya yana
kallonta. Yace kin gani ko Aish, idan bata yi abin
kallo ba bata jindadi. Idan kin farfado ki kira
mutanen gidanku suzo daukarki don wallahi
bazaki min idda a nan ba. Zan baki ci da sha
duk inda zaki. Aishatu ta sake kallon Fadila
wadda taki motsi duk da yadda kanta ya soma
kaikayi kamar mai kwarkwata. Tace babyna kayi
mata afuwa for the last time. Nasan dacin saki
da rayuwar da ke biyo bayansa ga wanda ya
zalumci dan uwansa. Ta dan shafa mata ruwa a
fuska sai gashi ta farfado huzaifa yace ai na
zata kin tafi kenan. Fadila cikin kuka tace ku
taimake ni ko albarkacin cikin dake jikina. Duk
sunyi mamaki sai dai Huzaifa yasan bazata
masa karyar ciki ba. Don tasan zai iya dubawa
ya tabbatar. Aishatu tace Fadila nasan zan dade
ban kara yarda dake ba don na biyu kenan
abinda kika yi min. Amma darajar abinda ke
cikinki muna rokonka ka taimaka maganar sakin
ka janye. Idan ta sake yi maka laifi nayi
alqawari bazan shiga ba. Fadila ta rungumeta ta
tana ta godiya. Shi kuwa fita yayi.
A sanyaye ta bishi daki yana zaune bakin gado
ya dafe kai. Aishatu ta zauna a kusa dashi ta
dafa masa kafada. Baby ka gode Allah
sharrinta baiyi tasiri a kanmu ba da yanzu
zuciya ta debe ni kila nice zan nemi sakin. Yayi
saurin rufe mata baki. Allah Ya kiyaye
Aish...tace to tunda hakan bai faru ba ya
kamata mu nuna godiyar ga Allah ta hanyar
yafe mata. Ka kara hakuri ko don darajar yara.
Yace yanzu kin yarda na dawo da ita. Ta gyada
kai don tsakani da Allah tana tsoron Fadila.
Amma tana kwadayin ladan da ake bawa mai
yawan afuwa idan an cutar dashi. Ya kankameta
yana mata magana a kunne Aish it seems kina
so sonki yayi min yawa a raina. Ke wace irin
mace ce? Ya shafi fuskarta...you are too nice,
too good. And Dr Rano loves you so much for
that. Ita ma tace and I love you too. Ban taba
tunanin zanyi aure namiji yaga darajata ba sai
gashi ka zama sanadin gushewar duk bacin ran
da na kwaso a baya. Duk da halin da nake ciki
baka guje ni ba baby ta yaya zanyi sanadiyar
raba maka iyali? Yace Alhamdulillah itama ta
maimaita suka manta da Fadila da ke daki tana
waya da Fahad.
Wasila ce ta turo mata numbarsa ta kira. Cikin
isa da gadara tace masa sunana Fadila matar
mijin tsohuwar matarka. Idan har kana sonta har
yanzu ka zo mu hadu. Fahad yace ke kinsan da
wa kike magana kuwa kike nema ki rinka bani
order kamar yaronki? Ta tabe baki ba Fahad
bane. Yayi wata yar dariya shine, ya kamata ki
san ba'a yiwa fahad magana a haka. Idan kin
shirya ki sanar dani wurin da zamu hadu. Sai
kawai ya kashe wayar. Ta tsaya tana kallon
wayar a hannunta tana juyata. Shi kuma wannan
waye ta fada a zuciyarta.
RASHIN GODIYA ✂ 47
Aishatu ta rude jikinta na rawa tace Anti Sauda
me zai sa ya kira ni haka kawai. Anti Sauda
tace kinga kwantar da hankalinki in Allah Ya
yarda ba komai. Ita dai Aishatu hankalinta bai
kwanta ba sai da aka goge mata jiki ta tashi
jikinta duk ba kwari. Anti sauda tace kina zuwa
gida ki sanar da Dr don daga labarinsa ni ko
kadan ban yarda dashi ba. Aishatu tace ai dole
anti. Ni sam ban yarda da rufa rufa ba. Fahad
mugun makiri ne ga iya hada sharri. Suna
magana suka fito waje, dama gidan babu nisa
da na Anti sauda a kasa suka je.
Fadila tana zaune gaban motar Huzaifa ya
daukota daga gidansu tace Abban Aliya mu biya
mu dauko Aishatu naga jiya irin lokacin nan ta
dawo. Huzaifa yayi tsaki bana son iyayi, ta
sanar dake inda zata ne da kike cewa a
daukota. Ko kuwa son jin kwaf ne ya motsa kike
neman bugun cikina. Fadila ta sunkuyar da kai,
nasan duk abinda nayi ne a baya yasa komai
nayi yanzu sai ka fassara shi da wata manufa.
Shareta yayi don yasan son jan zancen take. Ya
dauki wayarsa ya kira Aishatu dama niyarsa
kenan su biya a daukota tunda yamma tayi. Ta
fada masa ta gama zata jira ta koma gidan anti
Sauda. Fadila na jin haka ta dauko wayarta ta
tura text.
(Tana gidan nan da na kwatanta maka a yan
kaba. Kayi sauri muna hanya)
Baiyi mata reply ba ya cigaba da kallon gate din
gidan da Aishatu ta shiga daga cikin mota. Ta
kara kyau da haske...sai yanzu ya kara ganin
wautarsa akan yadda yayi treating dinta a
gidansa. Yaro ya gani zai wuce yayi saurin fita
daga mota ya tsayar dashi. Don Allah kace
Aisha tazo inji Huzaifa. Ka fada mata tayi sauri
wayata ce ta mutu. Yaron ya shiga ya fadawa
Sajida sakon ta shiga dakin mamanta ta fada
musu. Aishatu ta tayi saurin gyara fuska Anti
Sauda sai dariya take...na dai fada miki amarcin
nan sai an gama gyaraki. Na fuskanci Huzaifa
ya gama koya miki rashin kunya idan ban kaiki
ba zaki kai kanki. Aishatu ta rinka dariya suka
fito tare. Anti Sauda tace gori zan masa har yau
bai taba shiga gidana ba.
Basu ga motarsa a bakin gate ba har Anti Sauda
na cewa ko dai tafiya yayi wani wurin kila yanzu
zai dawo. Sam bata kula da yadda Aishatu ta
sandare a tsaye ba. Hannunta taji ta damka har
ta danyi ihu ke lafiya zaki karya ni. Kamar me
rada ta nuna mata mutumin da yake tahowa
wurinsu. Anti Sauda tace waye wannan? Ko
Fahad ne? Aishatu ta gyada kai alamar eh.
Assalam alaikum wa rahmatullahi wa
barakatuhu. Anti Sauda ta sha kunu ta amsa da
kyar sannan ta rike Aishatu shige muje ciki.
Fahad yace don Allah Haj ki daure ku saurare ni.
Abinda ya kawoni yana da matukar
mahimmanci. Aishatu ta juya a fusace yayi
saurin cewa don girman Allah ki tsaya. Ba tare
da ta juyo ba ta tsaya. Kan gwiwoyinsa biyu ya
durkusa ki yafe ni Aisha. Ni mai dumbin laifi ne
a gareki kuma wallahi ban taba jin son mace ba
sai da na rabu dake. Nayi nadama mara iyaka
kuma tun a duniya naga sakayyar abinda nayi
miki tana faruwa a kaina. Sai hawaye suka fara
zuba a idanunsa. Ya kalli Anti Sauda ki taimaka
ki bata hakuri ko zanga sassauci a rayuwata.
Bani da wani burin da ya wuce ki furta da
bakinki kin yafe min. Duk maganar da yake kin
juyowa tayi. Tana tuna irin wahalar da ya rinka
bata ciki harda zubar mata da ciki sau biyu. Anti
Sauda tace ni abinda ya bani mamaki ya akayi
kasan tana gidan nan. Yayi murmushi ki roketa
ta yafe min sai kuji abinda ya kawo ni. Wallahi
Aishatu bazan kara cutar dake ba. Ina tsoron
lahirata, ina tsoron wutar Allah, ina kunyar
haduwa da Mahaliccina. Ta dan juyo na yafe
maka amma don Allah ka dena bibiyata haka.
Ya tashi yana kade rigarsa nagode sosai Aisha.
Sai kuma mu koma ga abu na biyu da ya kawo
ni....kafin yayi magana suka ji wani mahaukacin
horn. Dukkansu basu tun san lokacin da Huzaifa
yayi parking mota yana kallonsu ba. Ransa ya
gama baci ji yake kamar ya shake fahad don ya
tabbatar shine saboda haduwar da sukayi a
kofar gidan su Aishatu. Zuciyar Aishatu kuwa
don tsoro da fargaba kamar ta fito waje
RASHIN GODIYA ✂ 48
Gaba daya Aishatu ta rikice ta ma kasa
motsawa. Huzaifa ya fito daga motarsa a
fusace ya janyo hannun Aishatu. Anti Sauda
tace Dr kayi mata a hankali bamu san yana
wurin nan ba. Tamkar ba da shi take magana ba
haka yayi gaba abinsa. Fahad bai ce masa
komai ba har ya tada kura suka wuce. Anti
Sauda ta yiwa fahad kallon banza. Ince ko kaji
dadi ka hada rigima. Aishatu tana fada min
sharrinka sai yau na tabbatar. Mai yasa baka yi
masa bayanin abinda ya kawoka ba. Fahad yayi
murmushi tare da dan tabe baki saboda kishi
mana. Anti Sauda ta yu hanyar gate din gidanta
a fusace Allah wadaran halinka. Fahad yace
please ki saurareni. Maybe na iya fitar da
kawarki daga zargi. Na tsaya sauraronka nima
nawa mijin ya dawo ko. Sannu mugu to ta Allah
ba taka ba. Ta shige tare da bugo gate din da
karfi.
Kana ganin yanayi Huzaifa kasan bashi da
kwanciyar hankali. Babu abinda shaidan bai kitsa
masa ba a zuciyarsa. Wai garin yaya ma Fahad
yasan gidan Sauda? Kuma ya akayi yasan inda
Aish take a wannan lokacin? Fadila ta dan juya
baya inda take jin sautin kukan Aishatu a
hankali. Aishatu wai me ya faru ni kun sani a
duhu. Kaima Abban Aliya meye na fushi bayan
baka kirata ko kayi mata horn ba tunda muka
zo. Ai kaga ba laifinta bane don bata taho da
wuri ba. Mtsw kuma maza da rigimarku. Shiru
babu wanda ya kula ta. Ta sake cewa Aishatu
waye mutumin nan ko dan uwanku ne. Na tuna
shi a wurin walimarki yana ta miki liki. A fusace
Huzaifa yace to uwar jaraba kina mota har kin
kare masa kallo...tayi saurin daga hannuwa
sama yi hakuri na yi tunanin ko dan uwanta ne
ko mijin wannan matar. Daidai lokacin da ya
shiga gidan mal habu na rufe gate Fadila tace
kai amma fa Aisha jininku mai karfi ne don kuna
dibar kama da mutumin nan. Hancinku
yayi....wani irin burki Huzaifa ya taka saboda
yadda ya harzuka. Yace Fadila idan bakiyi min
shiru ba zan tattaka ki wallahi. Tayi dariya
Aishatu yau angonki sai a hankali bari na barku.
Ta fice abinta ta shiga ciki. Aishatu ta dago kai
suka hada ido ta mirror din gaba yace kema ki
fita. Ta soma magana baby ka saurare ni
wallahi...katse ta yayi da tsawa Aishatu ki fita
nace, am not in the mood. Bai taba fadar
sunanta ba sai yau. Yau ma cikin bacin rai. Ba
musu ta fita yayi ribas da motar ya rinka danna
horn har mal habu ya fito da gudu daga bandaki
ya bude masa gate ya fice.
Aishatu ta shiga ciki tana kuka. Komai yayi
mata zafi. Ta tabbatar plan Fahad ya hada
tunda cewa yayi tazo inji Huzaifa. Komai yayi
mata zafi ta shiga daki ta takure akan gado tana
kuka a hankali. Ba ita ta tashi ba sai da taji
kiran magriba.
Fadila tana kallon yadda Huzaifa ya fita ta tafa
hannuwa. Wannan karon ko kinfi kuda naci
Aishatu sai kin koma inda kika fito. Ta kira
wasila suka sha hira hankali kwance.
Masallaci daya suka yi sallah. Sai da ya jira ya
gama gaisawa da mutane ya fito sannan ya biyo
shi waje. Sallama yayi masa mutum ya amsa
cike da nutsuwa. Sai yace kamar Dr Rano ko
mijin Aishan Sauda? Eh nine ya dan saki fuska.
Don Allah magana nake son muyi. Gefe suka
koma Huzaifa yace kaine mijin Haj Sauda ko?
Babban su Islam yace eh nine lafiya dai?
Huzaifa yayi masa bayanin abinda ya gani. Yace
to ni bana son aiki da zargi, nasan halin
mutuminan amma ina neman izini muyi magana
da Saudan ta fada min gaskiyar abinda ya faru.
Alh Adam yace kayi tunani mai kyau Dr. Allah
Ya tsare mana iyali daga sharrin shaidan. Muje
gidan..Huzaifa yayi masa godiya yace haba har
daurin aurenka fa nazo. Rashin zamana yasa
bama haduwa sosai.
RASHIN GODIYA ✂ 49
A falon gidan suka zauna Anti Sauda tayi musu
gamsasshen bayani game da zuwan Fahad. Ta
kare da cewa wallahi Dr matarka tana sonka
kuma tana da rikon amana. Bai kamata zargi ya
shiga tsakaninku akan abinda ka gani kawai
baka bincika ba. Idan da tana son komawa
gareshi ai bazata aureka ba. Huzaifa ya dafe kai
ya kasa magana. Garin yaya ya nuna bacin rai
sosai ga matarsa wadda take yiwa mai lafi
uzuri. Alh Adam yace Sauda kibar kishi, babu
abinda baya sawa. Tace hakane kaga ko ba
komai nasan kanwata tana da babban gurbi a
zuciyar Dr. Murmushi Huzaifa yayi yace nagode
sosai da yadda kike kula da Aish, Allah Ya saka
da alkhairi. Ya tashi zan tafi don Allah idan ya
sake contacting dinku sai ki sanar dani tunda
kince ya fada muku akwai abinda ya kawo shi.
Har bakin motarsa Alh Adam ya rako shi. Sai da
ya fita sannan maigadin ya biyo Alh Adam.
Uhmm Alh ga wannan takardar. Wani mutum ne
dazu ya bani yace na bawa Hajiya sai na manta
yanzu na tuna da na sake gani bako. Alh Adam
yace kuma bai fadi suna ba? Maigadi yace na
tambaya yace idan na bata zata gane. Alh Adam
ya bude takarda ya karanta.
(Nasan ba lallai ku yarda dani amma akwai
bayanin da nake son yi Aisha ko mijinta. Ga
numbar wayata pls contact me.
Fahad)
Alh Adam yayi tsaki kuma shine sai yanzu zaka
bani? Gashi wanda abin ya shafa yanzu ya tafi.
Gida ya shiga ya nunawa Anti Sauda tayi ta
salati ta kira Aishatu wayarta a kashe, ita kuma
bata da numbar Dr Rano. Dole suka hakura sai
washegari.
Huzaifa bai koma gida ba sai da ya nemo wata
kaza da Aish ke so. Duk ranar da rigimarta ta
tashi ta rinka nacin sai ya siyo mata ga layi da
akeyi a wurin. Haka ya zauna yana ta tunanin
halin da take ciki. Fatansa daya ba kuka take yi
ba. Gashi ta kashe waya ya kasa samunta.
Hudu ya siya ya wuce gida. A falonta ya ajiye
nata ya wuce dakin Fadila ya kai mata biyu.
Nata daya na yara daya, ta karba cike da murna,
ita dai ta ga kayan kwadayi kawai. Har zai fita
tace Abban Aliya ina na kanwata? Yana jin
yadda tayi maganar yasan gulma ce kawai.
Yace ban siyo ba ki kyale ta kawai. Ta ce
gaskiya irin haka ba dadi ai sai ya zama rashin
adalci. Ya dan kalleta to ko zaki dibar mata ne.
Tuni ta hade rai kai ne hakkin ciyar da ita ke
wuyanka ai. Kuma nasan idan ka koma kila ya
tashi mai naman ko? Ba komai amma dai ka
rinka adalci. Yace naji kije ki kwanta ki kular
min da baby. Ta sake jindadi ta rufe kofa tana
tsalle da murna. Aiki ya fara kyau saura na gobe
ma.
Huzaifa yana mamakin hali irin na Fadila, ya
tabbatar da ita ce a wannan yanayin Aish
bazata nuna farinciki haka ba. Da sallama ya
shiga dakinta ya tarar bata ciki. Allah sarki Aish
yasan dakinsa ta tafi duk don kada ta nunawa
mutan gidan halin da suke ciki. Can gefen gado
ya hangota tana bacci akan abin sallah.
Zuciyarsa tayi masa zafi ya kara jin tausayinta.
Shiyasa Annabi SAW ya hanemu da daukar
mataki cikin fushi. Ya ajiye ledar naman ya
zauna a gefenta tare da dora kanta a cinyarsa.
Motsinsa ne ya tasheta tayi saurin mikewa tana
murza ido. Tana ganinsa ta soma kuka wallahi
ban san shine yazo ba. Cewa akayi nazo kana
jirana wayarka ba chaji kuma. Kamshin turaren
da take yini ana yi mata ya doki
hancinsa....bakinsa yasa ya hanata magana.
Sun jima a haka hawayenta bai dena zubowa
ba. Ya dago habarta da hannu biyu yana
kallonta...kiyi hakuri nayi kuskure da ban tsaya
sauraron hanzarinki ba. Kishi ne ya rufe min ido
tare da mamakin abinda ya kawo shi har nan.
Wani kukan yaga zata fara yayi saurin
rungumeta, gaba daya ya zaunar da ita akan
cinyarsa yace Aish I love you so much, bana
son tuna kin taba auren Fahad bare na ganshi.
Ya cutar min da ke sosai kokari nake na mantar
dake duk wannan mugun experience din. Tana
kukan tace kai kadai na taba so a rayuwata
baby. Idan ka kasa amincewa dani bansan
yadda zanyi ba. Duk wani farincikina ya
danganta da kai. Haka suka yi ta kara
jaddadawa juna so. Can yace wai kinyi wanka
yau kuwa? Tsami nake ji. Dundu tayi masa a
baya ba kaine ka sani kuka ba. Kuma wallahi
bana tsami duk turaren nan da nake yini a ciki.
Yayi dariya to kauri kike yi no wonder naji dakin
kamar ana girki da itace. Hawaye ta soma tana
kukan shagwaba ta tashi tana tura baki haka ma
zaka ce ko? Duk gyaran nan da nakeyi saboda
kai, to na dena kuma wankan ma na dena gaba
daya. Yana mata dariya yace ashe haka kike da
nauyi cinyata kamar ba a jikina take ba. Yana
murza wurin da ta zauna daga yanzu idan zan
rarrasheki daga nesa nesa zanyi. Kara shan
kunu tayi tana masa mita nima bazan kara zuwa
kusa da kai ba. Ta dauki mayafinta sai da safe
na dena zuwa dakin nan. Ya dago ledar kaza ga
wannan bari na cinye sai kisa a shara. Yadda
tayi murmushi ya burge shi ta dawo da sauri
wasa fa nake yi. Ai duk macen kirki a dakin
mijinta take kwana. Yayi dariya sosai sannan
suka zauna suka ci abinsu. Bayan sun gama
suka yi wanka ya janyota jikinsa suka kwanta.
Aish taji ya kirata a hankali. Naam babyn Aish
ta amsa masa. Wai sai yaushe za'a gama gyara
jikin nan? Naga ya gyaru sosai tun yanzu. Tayi
murmushi sai nan da sati uku. Dan murmushin
fuskarsa ya dauke ki manta da wani sati uku
don bazan bari ba. Wai baki san medically bai
kamata a rinka yawan shakar hayaki ba. Shi
kanshi turaren da kuke yi ba'a so yayi yawa
saboda kada yayi wa jiki illa. Aishatu ta gane
abinda yake nufi tace to ai kaga ba laifina bane.
Wato shi irin wannan gyaran idan ba'a jira an
gama ba to baci zaiyi. Jinsa kawai tayi ya kara
matseta cikin kunnenta taji yace wannan dai yau
zai baci gobe sai a sake wani. Tace to ai Anti
Sauda tace........maganar da bata sami damar
karasawa ba kenan sai da asuba.
Washegari tana kitchen wayarta ta rinka ringing.
Huzaifa da ke shirin fita asibiti ya dauka yaga
ko waye. Sunan Anti Sauda ya gani ya duba
time bakwai da yan mintuna. Sai kawai ya
dauka. Tana jin muryarsa ta gaishe shi sannan
tayi masa bayanin sakon Fahad. Yayi mata
godiya sosai ya fita kitchen wurin Aish ya sanar
da ita. Suna maganar text ya shigo da numbar
da ya rubuta musu. Huzaifa ya kwafa a tasa
wayar ya kira.
RASHIN GODIYA ✂ 50
Yanayin canjin fuskar mijinta yasa ta fara
tsorata ta kagu ya gama ya sanar da ita abinda
ya fada masa. Bayan sun gama yace mata ta
zai je wurin Fahad a hotel din da yayi masauki.
Aishatu ta ce kada ka je idan don nasan karshe
ranmu ne zai baci. Huzaifa ya shafi fuskarta
kada ki damu duk wanda ransa ya baci shi yaso.
Tace ban gane ba. Zaki gane bari nayi sauri.
Kafin ya fita ya kira wani abokin aikinsa ya nemi
alfarmar ya kama masa aiki kafin ya zo.
Fuskarsa a hade ya bi bayan Fahad ya shiga
dakin. A jikin kofa ya tsaya ya rungume
hannuwansa a kirji. Fahad tace don Allah ka
zauna Dr. Magana nake so muyi ta hankali.
Huzaifa yace nan ma ya isa. Fahad yace suit
yourself.
Fahad yace nasan ka sanni ka san wasu
abubuwa da dama akaina. Bayan rabuwata da
Aisha na so ta kamar inyi hauka. Kuma har
yanzu ina sonta. Huzaifa ya daure fuska abinda
ka kirani ka sanar dani kenan? No bashi bane
amma ka sani son da nake mata ne yasa zan
sanar da kai. A shekaru uku da nayi da matata
ta yanzu naso haihuwa sosai. Duk lokacin da
naje asibiti sai likitoci suce lafiyarmu kalau
lokaci ne kawai baiyi ba. A lokacin na rinka
tunanin yadda zanyi na rabaka da Aisha. Sai
watarana naji waazi da ya tayar min da hankali.
Ga tsananin mamakin Huzaifa hawaye ya gani a
idon Fahad. Nayi nadamar zama sanadin
zubewar cikin Aisha har sau biyu. Nayi roki
iyalina, iyayena da sauran yan uwana gafara
game da irin zamanmu da su. Aisha kadai ta
rage min da hakkin rai biyu. Huzaifa abin ya
fara isarsa. Kaga malam ni fa ba tarihin
rayuwarka nazo ji ba. Fahad yayi murmushi ni
kuma sai kaji tarihin zaka fahimci inda na sa
gaba. A halin yanzu dai na shiryu daga munanan
halaye na. Sai dai kwatsam wata rana wata
mata mai suna wasila ta kirani a waya. Suna
neman hadin kaina ne a rabaka da Aisha ni na
aura tunda sun sami labarin ina sonta. Sai a
lokacin Huzaifa ya zauna. Fahad ya cigaba tun
lokacin na amsa mata amma banyi niyar yin
komai ba sai da matarka Fadila ta kirani a waya
da wannan bukatar dai. Naji tsoron idan ban
amsa ba zata iya neman wata watar ko wani
mutumin shiyasa nazo. Tare da sannin matata
don ita ta bani shawarar yadda zanyi. Huzaifa
ya tashi tsaye kana son kace min fadila ta
sanka ne,wato sharri kake son kulla mata. Dama
nasan zuwa wurinka will be a complete waste of
time. Hotuna Fahad ya baza masa akan table
din gabansu. Wasu shi da fadila ne a wajen
makarantarsu Aliya. Sai wasu a gate din hotel
din,wasu kuma a kofar dakin. Jikin Huzaifa ya
soma rawa a sanyaye yace Fahad ka nemi
matata ne? Fahad yace ka kwantar da
hankalinka ko a da ni ba mazinaci bane. Magana
tazo muyi akan yadda zamu bata tsakaninka da
matarka. Ta yaya nasan gidan da Aisha take
jiya?
Huzaifa gumi ne ya jika shi lokaci guda. Wane
irin tashin hankali ne wannan. Ina Fadila zata
kai mugun halinta. Bata laakari da kullum tayi
sai asirinta ya tonu. Wannan yafi komai kure shi
tunda har zata iya kebewa a dakin hotel da
mutumin da ba muharraminta ba. Ya ce da
Fahad to meye next plan dinku. Fahad ya dauko
waya a gabansa ya kira Fadila yasa a speaker.
Tana dauka tace ,yauwa tun dazu nake jiran
wayarka, ya fita itan ma dreban gidan uwarsa
yazo ya dauketa. Huzaifa ya rike baki wai
uwarsa.
Fahad yace to yanzu ya zaayi?
Ta cigaba na gano gyaran jiki take zuwa. Na
riga na yanki key din dakin nata. Fahad da
Huzaifa suka hada ido. Jin anyi shiru yace
Fahad kana ji na?
Eh ina jinki yanzu ya zaayi na shiga dakin yadda
wannan mijin naku zai ganni.
Fadila tayi dariya kada ka damu. Kazo bayan
laasar sai na bude maka dakin. Zan tabbatar
yau ni na daukota ba shi ba. Daga nan sai ka
buya kada ka kuskura ka fito sai kaji muryarsa.
Idan da hali ka rungumeta ma komai ihunta.
Tana dariya fahad ya biye mata suka yi tare.
Huzaifa kirjinsa ya dafe zuciyarsa kamar ana
hura wuta. Fadila ta fi karfinsa yanzu mace me
irin halinta zaman aure ba nata bane sai dai
idan hali ya dace da na mijin. Huzaifa yace
Fahad meyasa ka zabi ka fada min gaskiya?
Fahad yace baka ji lokacin da na ce maka nayi
nadama ba? Da ban amince ba Fadila zata iya
neman wani. Dukkansu suka ajiye kishinsu a
gefe suka tsara plan din yadda zasu bullowa
Fadila. Ita wadda ake yi dominta bata san me
sukeyi ba. Tana can cike da farinciki tana
karasa gyara jikinta domin neman yardar Allah
da ta mijinta.
RASHIN GODIYA ✂ 51
Huzaifa ko aiki ya kasa zuwa saboda yanayin da
yake ciki. Duk cikin 'yan uwansa babu wadda
zai iya fadawa tayi shiru ba tare da ta sanar da
umma ba. Shi kuwa yafi son sai ya kashe
gobarar ma sannan za ta san abinda yake
faruwa. irin wannan sirrin kuwa ba abu bane da
zai iya fadawa aboki. Ciki ba don abinci kawai
aka yi shi ba, wani idan ya sani ma dariya zai
masa ace ya kasa rike mace. Daga karshe dai
office ya wuce amma ya sanar yau bazai iya
ganin marasa lafiya ba. Maaikatan asibitin sunyi
mamaki domin hakan ba halinsa bane. Bai dade
da zama ba sai ga wayar Fadila. Gabansa har
faduwa yayi ya dauka ya kuma yi kokarin nuna
mata komai lafiya yake. Sai da ta gama yi masa
hira tace Abban Aliya kaga wasila ce tazo nan
aka bugo waya yayarta ta karye a kafa. Na fita
rakata muka ga tayarta daya tayi paci. Naga
hankalinta duk ya tashi shine nake son in kaita.
Hmmm kawai ya ce, yanzu ba don yasan
gaskiya ba haka zata raina masa hankali. A fili
kuwa cewa yayi mal Habu ya cire ya daura
mata spare mana. Kukan wasilar yaji fadila ni na
tafi kawai don bansan halin da take ciki ba.
Fadila tace kaji ta ko duk a rude take. Huzaifa
yace to ba komai ki kaita. Allah Ya kiyaye gaba.
Fadila ta ajiye wayar suka tafa da Wasila. Tace
kai amma fadila mijin nan naki akwai matsi
sosai. Ni Kamilu bai isa na tambayeshi fita ba.
Fadila ta ce uhmm nima da bana tambaya,
zuwan shegiyar nan ne naga tanayi shiyasa na
fara. Sake tafawa suka yi sannan ta kira Fahad
tace yazo yanzu.
Basu dade ba kuwa sai gashi kamar yadda ta
fada masa kada yazo da mota bai zo da ita ba.
Ya kira ya sanar da ita yana bakin gate. Sai ta
fito ta ce Mal Habu ya duba mata baya tana jin
kamar motsi, kafin ya dawo ta shige da Fahad.
Wasila ta kare masa kallo tace gaskiya Fadila
na kyasa. Ko kadan bata ji kunyar yana jin
abinda ta fada ba. Fadila ta ce ke duk namijin
duniya ai yayi miki. Fahad yana jinsu dai bai
kula ba. Wasila ta sake cewa ita kuma Aishatu
duk mazan da ke sonta haka suke kyawawa in
dai bazaka damu ba Fahad ina son zama friend
dinka. Yadda take masa kwarkwasa ya bata
masa rai. Wasu matan basu san darajar da Allah
Yayi musu ba. Fadila dai ta dauki key din mota
ta rike mayafi a hannu. To zamu tafi zan
tabbatar ni na dauko ta. Ga dakin ka shiga na
hada maka da keys din falo da na daki. Yace to
nagode amma kuyi sauri. Wasila dai kamar kada
ta fita. Ta dade tana son Huzaifa ma amma
saboda Fadila take hadiye wa.
Ana yin laasar ta sake kiran Huzaifa ta sanar
dashi zata koma gida amma taga wurin yayi
kusa da inda Aishatu take zuwa za ta biya ta
dauko ta. Yace ai yau da wuri ta gama ta tafi.
Ina jin ta isa gidan ma. Amma dai nagode da
kike wannan kokarin na ganin kun daidaita.
Fadila dadi ya isheta dama bukatarta Aishatu ta
riga Huzaifa zuwa gida.
Huzaifa ya ajiye wayar ya kalli Aishatu da ke
zaune a gabansa tana sharbar hawaye. Idanunta
sunyi ja sun kumbura sai ajiyar zuciya take yi.
Yau bata gama gyaran jikin ba yaje ya daukota.
Ya gama yi mata bayanin yadda suka yi da
Fahad kenan Fadila ta kira. Kallonta kawai
Huzaifa yake yi yace Aish menene abin kuka
kuma? Bayan Allah SWT Ya fitar dake ba tareda
anyi nasara akanki ba. Tace hakane amma me
na tsarewa Fadila haka? Idan da Allah bai
kaddari zamanmu ba da tuni mun rabu. Tashi
yayi ya rungumeta yana ta rarrashi ni bana son
zancen rabuwa kinji ko. Duk bawan da ya
dogara da Allah kuma yake gode Masa a
kowane hali bazai tabe ba. Allah bazai dora
mana jarabawar da tafi karfin imaninmu ba.
Shiryuwar Fahad ai ba kokarinmu bane. Ina so ki
kara inganta imaninki ki kasance mai hakuri da
juriya sai kiga rahmar Allah tana bibiyarki.
Aishatu ta kalli Huzaifa tana murmushi tace
Alhamdulillah. Ya rike hannunta ko ke fa. Tashi
mu tafi gida.
RASHIN GODIYA ✂ 53
Kowa na binsu da ido ya kaita gaban
mahaifiyarsa ya zaunar da ita sannan yace mata
Aish bani key din dakinki. Ba musu ta dauko ta
mika masa, yace guda nawa ne mukullan? Ta ce
hudu ne biyu suna jakata biyu kuma suna
wurinka. Huzaifa ya shiga daki ya fito da su. Ya
hada ya ce da Baban gandu ai sun cika hudu
ko? Yace hudu ne zahiri. Wai ni kadai ne kaina
ya kulle a wurin nan? Umma tace nima jira nake
su yi min bayani. Idanun fadila kamar zasu fado
kasa. Ta riga ta gama tsurewa tunda taga ya
shigo da Aishatu tasan abinda zai biyo baya
bazai mata kyau ba.
Huzaifa ya tashi yaje ya bude dakin Aishatu sai
ga Fahad ya fito. Nan fa kowa ya tashi tsaye
ana kallon kallo. Umma tace auta don girman
Allah me yake faruwa? Huzaifa yace su zauna
yanzu zaiyi musu bayani. Suna zama yace
Fahad bismillah. Nan da nan fahad ya fara
bayanin abinda ya faru tun daga wayar Wasila
ta farko. Kowa da abinda yake fada game da
Fadila da kawarta. Aishatu kuwa sai kuka take
yi. A wurin Huzaifa ya fadi wasu daga
abubuwan da fadila tayi masa a baya tun kafin
aurensa da Aishatu. Fadila ta soma kuka
Huzaifa sharri zaka yi min ko har ka iya hada
baki da tsohon mijin matarka don kawai baka so
na. Baban fadila ya tashi ya hau dukanta. Fadila
ke wace irin yarinya ce yanzu da ke zaa hada
baki a kawo namiji dakin wata don miji ya
saketa. Kuma da yake baki da tsoron Allah har
ki kirawo dangin mijinki su zo kallo ko. To gashi
ramin da kika gina kin fada ciki. Tana kuka tace
Abba wallahi sharri ne. Tunda yarinyar nan tazo
take kulla min sharri. Huzaifa kawai sai ya jefa
mata hotunansu ita da Fahad a mota da hotel.
Wannan karon Baban gandu ne ya kai mata
duka. Kin cucemu kin cuci kanki Fadila. Umma
ta ce Aishatu iyayenki sun san abinda ke
faruwa...ta girgiza kai a'a Umma. Tace Allah
Yayi miki albarka da kika rufa sirrin gidanki.
Fahad ya tashi zai tafi suka yi masa godiya da
bai biyewa son zuciya ya fada ga halaka ba.
Ana ta yiwa Fadila fada tana rusa kuka wasila
ta sabi jakarta zata gudu Huzaifa yace dawo
nan. Ki jira mijinki zai zo daukarki. Wasila ta
soma matsar kwalla tana bada hakuri. Babu
wanda ya saurareta har Kamilu ya iso bai tsaya
gama jin bayani ba ya ce ta tafi ya saketa saki
uku. Nan kuma manya suka soma yi masa fada
yayi aika aika. Shi dai murna yake yau ya sami
kwarin gwiwar rabuwa da matar da ta zame
masa karfen kafa. Dama iyayensa basa son
auren. Haka wasilq tabi bayansa tana ta kuka
har waje ana jin muryarta. Hankali ya dawo ga
Fadila, Huzaifa yace Baba dama na kiraku ne
don ku zama shaida saboda kada magana ta fito
ta karyata. Ku gafarceni amma bazan iya sake
zama da Fadila ba. Fadila ta taso tana ihu don
Allah kada ka karasa sakina Huzaifa. Igiya daya
ce ta rage min. Wayyo na shiga uku Aishatu kice
kin yafe kada ya karasa sakina. Huzaifa ya
dauko takarda ta tashi ta fizge wallahi baka isa
ka sakeni ba. Kayi kadan Huzaifa dama nasan
duk bakwa sona ta nuna su Yaya Zainab.
Wallahi zama daram a gidan nan babu inda zani.
Baban gandu ya kwada mata wani mari ba shiri
ta nutsu. Yace bazan hanaka sakinta ba
Huzaifa. Fadila kin zalunci kanki don
Ubangijinmu sarki ne mai adalci. Kin zama daga
cikin mutanen da basa iya godewa Allah. Godiya
ga Allah fa ba ta tsaya a cewa
ALHAMDULILLAH bane. Idan kika yi abinda ya
dace ma kin nuna godiyarki. Fadila kina sabawa
mijinki yana hakuri baki gode ba, kin kullawa
matar abubuwa da dama wanda ya kai a saki a
tsakaninku har sau biyu tana sawa ya yafe miki
baki gode ba, Allah Ya baki rai da lafiya, gidan
aure da zuria nan ma baki gode ba. Mijinki da
abokiyar zamanki basu taba tunanin tona miki
asiri ba sai gashi rashin godiyarki ya janyo naki
asirin ne ya tonu. Me kike nema ne a rayuwa
Fadila? Babanta cikin kunan rai yace me take
nema kuwa Yaya banda ta jawo mana zagi da
bacin suna. Babu abinda Allah bai baki ba na
jindadin rayuwa Fadila sai dai zuciyarki bata da
godiyar Allah. Duk macen da zata kasa sauke
nauyin mijinta kuma ta nuna kishin banza don
zaiyi aure bata da maraba da jaka. Fadila tayi
saurin kallon mahaifinta yace kwarai kuwa. Baki
da maraba da jaka mana. Kina zaune wata can
tana koya miki yadda zaki zauna da mijinki. Ke
kuma kamar mara hankali duk abinda ta fada ya
zauna miki a ka. har ki fasa kayan dakin kishiya
dangin miji su biya ba tareda an neme mu ba.
Haba Fadila! Indai hakan riba ne yau idonki ya
gane miki ai.
Umma ta ce Fadila yau kinga sabanin abinda
kika so ya faru. Da yanzu wannan baiwar Allah
zamu saka a gaba da fada da zagi. Ki sani
zaman gidan miji iyawa ne. Kissa da kike ji ana
fada ba hauka bace. A yadda kika iya kulla
abubuwa haka da kinyi amfani da basirarki wurin
kyautatawa miji da tuni bamu zo ga yau ba. Ni
shaida ce auta ya so ki sosai sai gashi abin
mamaki aure bai rufa shekara biyar ba ya kara
wata. Zamanin daga ni sai mijina ya wuce.
Yanzu fatanmu kawai idan tazo a zauna lafiya
idan kuma ita muka tarar ma dai a zauna lafiya.
Rayuwar har nawa take da zamu batawa kanmu
lokaci da neman ganin bayan wasu. Shawarata
ta karshe gareki shine kiji tsoron Allah ki gyara
halinki. Su Yaya shukriya duk suna da abin fada
a bakinsu amma tarbiyar umma ta hanasu
magana idan manya nayi. Dole dukkaninsu suka
yi shiru. Huzaifa ya dubi iyayen fadila...Baba ku
yi hakuri ku yafe min amma bazan kara iya
zama da ita ba. Ina tsoron abinda zaije ya dawo
nan gaba ne. Baban gandu yayi ajiyar zuciya
Huzaifa kayi hakuri gaskiya kuma bazan goyi
bayan ka zauna da ita a wannan yanayin ba.
Duk macen da zata iya shiga hotel da mutumin
da ba muharraminta ba har daki dole aji tsoron
zama da ita. Huzaifa ya kalli Aishatu wadda tun
zamansu bata yi magana ba. Kawar da kai tayi
gefe alamun yau babu ruwanta sai kawai ya
tashi ya dora wa Fadila takardar da tun bayan
da ya baro wurin fahad ya rubuta.
Kukan da take yi ya bawa mutanen wurin
tausayi sai dai duk bawan da bai godewa rahmar
Allah ba,wata rana bazai ki godewa azabarSa
ba. Haka iyayenta suka saka ta a gaba tana
hawaye suka tafi gida. Umma ta sake yiwa su
Aishatu nasiha suka tafi.
RASHIN GODIYA ✂ 52
Kafin Fadila ta karasa gida Fahad ya tura mata
text akan cewa kada tayi masa text ko waya
saboda Aishatu tana dakin. Hankalinta kwance
ta yi masa reply akan za ta kiyaye. Sai bayan
rabin awa da komawar Fadila gida sannan
Huzaifa ya dauko Aishatu suka taho. Da ya iso a
waje yayi parking din motar suka shigo ciki sai
Aishatu ta tsaya a falonsa na waje. Shi kuma
yayi sallama ya shiga ciki.
Ciki da nishadi ya shiga gidan yana ta faraa. ba
shiri ya tsaya da yaga Fadila da Wasila a tsakar
falo suna ta kai kawo. Ya sake maimaita
sallama Fadila ta amsa da kyar, muryarta har
rawa take yi. Huzaifa ya kallesu kamar mai
mamaki yace lafiyarku kuwa ko yayar taki ta
mutu ne wasila? Ta ja dogon numfashi jikinta da
sauki. Gidanka ne dai a cikin matsala. Fadila ta
share hawayen munafurci kinga ki iya bakinki
kawai idonsa ya gane masa.
A can waje kuma motoci biyu ne suke horn a
bakin gate. Mal Habu ya bude musu suka shigo.
Daya Yaya Kubra ce tare da Umma. Dayar kuma
dreban yaya zainab ne ya daukosu ita da Yaya
shukriya da Saddiqa. Aishatu ta leka ta window
ta gansu hankalinta ya kara tashi me ya kawosu
gidan a lokaci daya ta tambayi kanta. Su dinma
a cikin tashin hankali suka shiga gidan. Huzaifa
da yake tsaye a falo yana jiran amsar su Fadila
ya juyo a tsorace yana tambayarsu ko lafiya.
Saddiqa tace kai zamuyi wa wannan tambayar
auta. Fadila ta kira dukkanmu tace muzo gidan
nan akwai matsala. Yace nima shigowata kenan
bata fada min komai ba. Umma ta kalleta ke
Fadila ko dai yaran ne? Wasila tace yara Laure
ta rakasu islamiya. Za ta sake magana sai ga
sallamar baban Fadila da yayansa Baban
Gandu. A take cikin Fadila ya bada wani mugun
sauti tace Baba daga ina kuke haka? Baban
gandu yace kaniyarki, ba amsa sallama ba
gaisuwa sai daga ina muke? To daga inda kika
aikemu muke mara kunya. Huzaifa da sauran
suka gaisa dasu. Umma tace ni ku fada min
abinda ke faruwa fadila ce ta kira mu. Baban
gandu yace mu kuma Huzaifan ne ya kiramu da
kansa. Yace lallai yana bukatarmu a gidan nan
saboda wani abu mai matukar mahimmanci.
Yaya Zainab tace wai ni ina Aishatu ne. Fadila
ta durkusa gabansu dama dalilin nawa kiran
kenan. Nasan duk abinda zan fada zaku ga
kamar kishi ne yasa na fada shiyasa na kiraku
ku zama shaida. Ban dade da dawowa gida ba
munje duba yar wasila sai nake jin kamar
maganar mutum sama da daya a dakin Aishatu.
Da nayi zaton baki ne da ita sai kuma naji
muryar ta namiji ce. Duk da haka nace ko
kannenta ne. Ta kalli Huzaifa nasan dai ka hana
maza wuce falon nan amma sai nace kila wani
abin ne daban. Baban gandu yace ke kuma uwar
shisshigi sai kika dorawa kanki damuwar da ba
taki ba ko? Umma tace haba Alh kyaleta ta
gama bayaninta. Fadila ta sake sauke murya
tace to daga nan nace da wasila tazo muje mu
gaisa sai naji kofar a kulle ta ciki. kuma na
tabbatar da mutane a ciki. Na buga baa bude ba
shine hankalina ya tashi na zaga tagarta ta
baya. Wayyo Allah sai kuka ya kwace mata
Abban Aliya ha'intarka Aishatu take yi. Ta
window din tagar na hangota ita da wani
suna.....Baban Fadila ya daka mata tsawa bana
son zancen banza. Su Umma kuwa sai salati
suke. Wannan wane irin tashin hankali ne. Jinkin
kowa a mace suna kallon Huzaifa wanda ya
dafe kai yana hawaye. Kowa ya tausaya masa
basu san kukan tsabar bacin rai bane na irin
halayyar Fadila. Falon yayi tsit can Huzaifa ya
ce Fadila kin tabbata kin gansu tare. Tace
wallahi na gansu a mugun yanayi. Ai wasila ma
na wurin, ban bari sun ganni ba dai. Kasan yau
baka dawowa da wuri kuma na mata waya cewa
na fita. Kila shiyasa ta kirawo shi. Yayyan
Huzaifa suna ta juyayin zancen. Kawai suka ga
ya tashi. Waje ya fita har umma na cewa a bishi
kada yayi wani wurin. Bai dade ba sai gashi ya
dawo rike da hannun Aishatu. Fadila ta tashi da
sauri jikinta na bari.
RASHIN GODIYA ✂ 53
Kowa na binsu da ido ya kaita gaban
mahaifiyarsa ya zaunar da ita sannan yace mata
Aish bani key din dakinki. Ba musu ta dauko ta
mika masa, yace guda nawa ne mukullan? Ta ce
hudu ne biyu suna jakata biyu kuma suna
wurinka. Huzaifa ya shiga daki ya fito da su. Ya
hada ya ce da Baban gandu ai sun cika hudu
ko? Yace hudu ne zahiri. Wai ni kadai ne kaina
ya kulle a wurin nan? Umma tace nima jira nake
su yi min bayani. Idanun fadila kamar zasu fado
kasa. Ta riga ta gama tsurewa tunda taga ya
shigo da Aishatu tasan abinda zai biyo baya
bazai mata kyau ba.
Huzaifa ya tashi yaje ya bude dakin Aishatu sai
ga Fahad ya fito. Nan fa kowa ya tashi tsaye
ana kallon kallo. Umma tace auta don girman
Allah me yake faruwa? Huzaifa yace su zauna
yanzu zaiyi musu bayani. Suna zama yace
Fahad bismillah. Nan da nan fahad ya fara
bayanin abinda ya faru tun daga wayar Wasila
ta farko. Kowa da abinda yake fada game da
Fadila da kawarta. Aishatu kuwa sai kuka take
yi. A wurin Huzaifa ya fadi wasu daga
abubuwan da fadila tayi masa a baya tun kafin
aurensa da Aishatu. Fadila ta soma kuka
Huzaifa sharri zaka yi min ko har ka iya hada
baki da tsohon mijin matarka don kawai baka so
na. Baban fadila ya tashi ya hau dukanta. Fadila
ke wace irin yarinya ce yanzu da ke zaa hada
baki a kawo namiji dakin wata don miji ya
saketa. Kuma da yake baki da tsoron Allah har
ki kirawo dangin mijinki su zo kallo ko. To gashi
ramin da kika gina kin fada ciki. Tana kuka tace
Abba wallahi sharri ne. Tunda yarinyar nan tazo
take kulla min sharri. Huzaifa kawai sai ya jefa
mata hotunansu ita da Fahad a mota da hotel.
Wannan karon Baban gandu ne ya kai mata
duka. Kin cucemu kin cuci kanki Fadila. Umma
ta ce Aishatu iyayenki sun san abinda ke
faruwa...ta girgiza kai a'a Umma. Tace Allah
Yayi miki albarka da kika rufa sirrin gidanki.
Fahad ya tashi zai tafi suka yi masa godiya da
bai biyewa son zuciya ya fada ga halaka ba.
Ana ta yiwa Fadila fada tana rusa kuka wasila
ta sabi jakarta zata gudu Huzaifa yace dawo
nan. Ki jira mijinki zai zo daukarki. Wasila ta
soma matsar kwalla tana bada hakuri. Babu
wanda ya saurareta har Kamilu ya iso bai tsaya
gama jin bayani ba ya ce ta tafi ya saketa saki
uku. Nan kuma manya suka soma yi masa fada
yayi aika aika. Shi dai murna yake yau ya sami
kwarin gwiwar rabuwa da matar da ta zame
masa karfen kafa. Dama iyayensa basa son
auren. Haka wasilq tabi bayansa tana ta kuka
har waje ana jin muryarta. Hankali ya dawo ga
Fadila, Huzaifa yace Baba dama na kiraku ne
don ku zama shaida saboda kada magana ta fito
ta karyata. Ku gafarceni amma bazan iya sake
zama da Fadila ba. Fadila ta taso tana ihu don
Allah kada ka karasa sakina Huzaifa. Igiya daya
ce ta rage min. Wayyo na shiga uku Aishatu kice
kin yafe kada ya karasa sakina. Huzaifa ya
dauko takarda ta tashi ta fizge wallahi baka isa
ka sakeni ba. Kayi kadan Huzaifa dama nasan
duk bakwa sona ta nuna su Yaya Zainab.
Wallahi zama daram a gidan nan babu inda zani.
Baban gandu ya kwada mata wani mari ba shiri
ta nutsu. Yace bazan hanaka sakinta ba
Huzaifa. Fadila kin zalunci kanki don
Ubangijinmu sarki ne mai adalci. Kin zama daga
cikin mutanen da basa iya godewa Allah. Godiya
ga Allah fa ba ta tsaya a cewa
ALHAMDULILLAH bane. Idan kika yi abinda ya
dace ma kin nuna godiyarki. Fadila kina sabawa
mijinki yana hakuri baki gode ba, kin kullawa
matar abubuwa da dama wanda ya kai a saki a
tsakaninku har sau biyu tana sawa ya yafe miki
baki gode ba, Allah Ya baki rai da lafiya, gidan
aure da zuria nan ma baki gode ba. Mijinki da
abokiyar zamanki basu taba tunanin tona miki
asiri ba sai gashi rashin godiyarki ya janyo naki
asirin ne ya tonu. Me kike nema ne a rayuwa
Fadila? Babanta cikin kunan rai yace me take
nema kuwa Yaya banda ta jawo mana zagi da
bacin suna. Babu abinda Allah bai baki ba na
jindadin rayuwa Fadila sai dai zuciyarki bata da
godiyar Allah. Duk macen da zata kasa sauke
nauyin mijinta kuma ta nuna kishin banza don
zaiyi aure bata da maraba da jaka. Fadila tayi
saurin kallon mahaifinta yace kwarai kuwa. Baki
da maraba da jaka mana. Kina zaune wata can
tana koya miki yadda zaki zauna da mijinki. Ke
kuma kamar mara hankali duk abinda ta fada ya
zauna miki a ka. har ki fasa kayan dakin kishiya
dangin miji su biya ba tareda an neme mu ba.
Haba Fadila! Indai hakan riba ne yau idonki ya
gane miki ai.
Umma ta ce Fadila yau kinga sabanin abinda
kika so ya faru. Da yanzu wannan baiwar Allah
zamu saka a gaba da fada da zagi. Ki sani
zaman gidan miji iyawa ne. Kissa da kike ji ana
fada ba hauka bace. A yadda kika iya kulla
abubuwa haka da kinyi amfani da basirarki wurin
kyautatawa miji da tuni bamu zo ga yau ba. Ni
shaida ce auta ya so ki sosai sai gashi abin
mamaki aure bai rufa shekara biyar ba ya kara
wata. Zamanin daga ni sai mijina ya wuce.
Yanzu fatanmu kawai idan tazo a zauna lafiya
idan kuma ita muka tarar ma dai a zauna lafiya.
Rayuwar har nawa take da zamu batawa kanmu
lokaci da neman ganin bayan wasu. Shawarata
ta karshe gareki shine kiji tsoron Allah ki gyara
halinki. Su Yaya shukriya duk suna da abin fada
a bakinsu amma tarbiyar umma ta hanasu
magana idan manya nayi. Dole dukkaninsu suka
yi shiru. Huzaifa ya dubi iyayen fadila...Baba ku
yi hakuri ku yafe min amma bazan kara iya
zama da ita ba. Ina tsoron abinda zaije ya dawo
nan gaba ne. Baban gandu yayi ajiyar zuciya
Huzaifa kayi hakuri gaskiya kuma bazan goyi
bayan ka zauna da ita a wannan yanayin ba.
Duk macen da zata iya shiga hotel da mutumin
da ba muharraminta ba har daki dole aji tsoron
zama da ita. Huzaifa ya kalli Aishatu wadda tun
zamansu bata yi magana ba. Kawar da kai tayi
gefe alamun yau babu ruwanta sai kawai ya
tashi ya dora wa Fadila takardar da tun bayan
da ya baro wurin fahad ya rubuta.
Kukan da take yi ya bawa mutanen wurin
tausayi sai dai duk bawan da bai godewa rahmar
Allah ba,wata rana bazai ki godewa azabarSa
ba. Haka iyayenta suka saka ta a gaba tana
hawaye suka tafi gida. Umma ta sake yiwa su
Aishatu nasiha suka tafi.
RASHIN GODIYA ✂ 54
Kwana biyu da faruwar wannan al'amari aka kira
Huzaifa daga gidansu Fadila kan cewa tayi bari
cikin dare. Ko da ta fice masa a rai yaso kwarai
ta haihu don yana son yara. Ranar da yaje
dubata ta bashi tausayi sosai kuma ta bashi
hakuri. Har ta roki ya tayata bawa Aishatu ma
hakuri.
Bayan sati biyu Aishatu da Huzaifa suka tafi
Umra. Bakinta ya kasa rufuwa lokacin da ta ga
Ka'abar Allah. Daga inda ta ganta ta durkusa
tayi sujjada ta kara godewa ALLAH SWT bisa ga
niimoninsa gareta. Sunyi sati biyu banda ibada
babu suke yi. Sai soyayyarsu da shakuwa da
suke karuwa kullum. Basu da burin da ya wuce
kyautatawa juna. Nan suka yi azuminsu har
sallah. Ranar da zasu dawo tun safe Aishatu
tace jikinta ba dadi tana ta narkewa. Huzaifa ya
ce nasan ciwon bakya son komawa gida ne.
Tayi murmushi wa yake son yin nisa da kasa
mai tsarki? Ya ja hancinta babu.
Suna jirgi ta dan kwanta jikinsa ta tashi ba shiri
saboda amai da yake damunta. Kafin jirginsu ya
sauka tayi sau biyar. Duk ta bashi tausayi haka
suka tafi gida jikinta ba kwari. Su Aliya sun sha
tsaraba ta dame shi sai an dauko mata su a
daren yaki amincewa. Ke kin fiye rigima Aish.
Kina fama da kanki kina kiran yara. Ki bari gobe
na dauko su. Yau naga alama kwanan jinya
zanyi. Ta dan turo baki please baby. Nayi
missing din su sosai. Ya janyota jikinsa ni bakiyi
missing dina ba ko. Ta gyara kwanciya ba ina
ganinka ba kullum. Yace su ma yaran ai kullum
kina waya dasu. Gobe zanyi musu albishir mai
dadi. Tayi kara riko shi don Allah ka fara yi min
kaji. Ya noke kafada haba babyn Aish. Huzaifa
ya kura mata ido yana kare mata kallo....shi dai
yana sonta. Ta hura masa isa a fuska me kake
kallo ne baby? Yadda kika ciko mana 'yan
kwanakin nan. Gobe zanyi miki pregnancy test.
Naga alama yarinyar nan ciki gareki. Kunya tasa
ta kara shigewa jikinsa taki yarda su hada ido.
Yayi yayi taki dagowa haba Aish meye na jin
kunya kuma. Ko kunyar karyar ce ta motsa. Ta
na dariya tace ta gasken ce baby.....shima
dariyar yake yace indai ita ce to bari nayi
maganinta.
Bayan wata hudu kowa yasan Aishatu tana da
ciki don ya fito ya fi watanninsa girma ma.
Kulawa take samu sosai daga iyayenta da
umma. Su Yaya Zainab ma duk sun gama
yankewa yan biyu ne a cikin yadda yayi girma
shiyasa suke kara shagwabata. Duk da haka ita
ke yiwa mijinta girki kullum. Tun yana hanawa
har ya hakura, yace da kanta zata dena idan
jikin ya kara nauyi. Rayuwarsu abin shaawa
suna kula da su Aliyu sosai. Yaya Kubra ma ta
koma gidanta sun dena fada da uwar mijinta.
Wata talata Huzaifa na asibiti ya gama duba
patient an kira next one sai yaga Fahad tare da
wata mata ta sha katon mayafi. Tun ranar da
aka tona Fadila basu sake haduwa ba. Huzaifa
ya yi murnar ganinsa don kuwa yayi ta kiran
wayarsa baya samu. So yake suyi zumunci
saboda taimakon da yayi masa. Shima Fahad din
da faraa ya shigo suka gaisa. Fahad yace Dr ga
madam fa Yahanasu. Ta sake gaishe shi Fahad
yace duk abinda ya faru kwanaki da taimakonta
ne. Huzaifa yana ta murmushi yace kawai kace
kanwata ce. I hope ba problem dai. Fahad yace
akan matsalar haihuwa ne Dr. Ya nuna masa
medical reports dinsu na wasu asibitocin. Bayan
dogon nazari ya tura su yin wasu gwaje gwajen
tare da basu wasu magungunan. Suka rabu cikin
mutunta juna.
Daren ranar suna kwance da Aish yake bata
labarin zuwan Fahad. Tace ikon Allah kenan da
yana gudu yanzu yana nema. Huzaifa yace haka
rayuwa take. Allah Yayi mana jagora. Wai kinsan
labarin da na ji yau kuwa? Fadila ta auri mijin
Wasila suna ta rigima da wasilan don itama har
tayi auren kashe wuta. Aishatu tayi mamaki to
Allah Ya kyauta. Ya sake cewa ai akwai wani
labarin...Aishatu ta ce yaushe ka zama mai
labarai ne. Tun da na auri Indo Aisha mana...my
one and only Aish. Ta rungume shi sosai ai
kuwa Aish tana da labari mai dadi da zata baka.
Suka ja bargo suna dariya.
Ko da Huzaifa yayi mata scanning yan biyu ya
gani amma basu fadawa kowa ba. Cikin na da
wata bakwai ta dena fita ko'ina saboda
girmansa. Mama bata zance sai na tausayin
Aishatu har Baba yana mata tsiyar bata jin
kunyar yar fari.
Wata rana Huzaifa ya dawo daga gidan Umma
ya tarar da Aishatu tana ta kai kawo a cikin
gida. Dama ya barta da safe tana complain din
mararta ta rike. Yana ganinta yasan haihuwa ce
ya dauko akwaitin da ya hada mata suka tafi
asibiti. An shiga da ita labour room suka hanashi
shiga. Ya zauna a waje sai ga su Yaya Kubra
dukkanninsu. Mama ma tazo tare da kanwarta
lawisa sai Anti Sauda. Wurin awa uku suna ciki
kana kallon Huzaufa sai ya baka tausayi. Da an
fito ya rinka tambayar ko lafiya kenan. Karshe
har wani fada fada ya koma yi musu. Dr Abida
ita ta hana ya shigo ganin yadda Aishatu ke
wahala. Da fargaba ta ishe shi a waje ya shiga
kawai ana ta kiransa yaki sauraronsu. Aishatu
na ganinsa ta soma kuka don ta sha wahala. Dr
Abida tace Dr Rano ina jin ko CS zamuyi mata
ne cibiya ta nade baby daya. Safar hannu ya
saka ya tsaya gaban matarsa. Yana yi yana
karfafa mata gwiwa ya yi dabararsu da likitoci
ya warware cibin. Kusan rabin awa yana kanta
kukan ma ta dena sai ga kan da ya fito. Dr
Abida tana gefe tana kallon yadda Dr Rano ke
lallaba matarsa. A hankali ya taimaka dan ya
fito ya mikawa nurse, sai ga na biyun shima ya
fito da taimakon Allah. Yana yi mata sannu ta
sake wani nishin sai ga na uku. Bakinsa yaki
rufowa cewa yake ku sa musu shaida. Aish har
uku kika haifa. Ya koma ya rungumeta...i love
you. Sannu yanzu ki rufe idonki a hankali zanyi
miki dinki kinji ko. Ihunta yasa Dr Abida da
nurse din fita.
Gidan Mama a cike da yan uwa da abokan arziki
yan barka don taki yarda Aishatu ta koma
gidanta. Huzaifa yayi ta mita har ya hakura.
Ranar suna kuwa a gidan Mama akayi saboda
yafi fili. Jamaa sun taru sosai harda su
Yahanasun Fahad da Anti Maryam matar wansa.
Itama Yahanasu da karamin cikinta. Yara sunci
sunan Abdulrahman, Abdulrahim da Abdulrashid.
Anyi taro lafiya an tashi lafiya. Bayan wata
shida Yahanasu ta haifi yarta mace. Bakin fahad
kamar gonar auduga. Ya fidda rai da samun
haihuwa a da. Aisha ya sawa babyn bisa
shawarar Yahanasu. Suna ta zumuncinsu. Itama
sunje suna Aliyu ya kankame baby Aisha har
yana cewa Maama wannan ce baby Aish dina ko
irin yadda Abba yake fada miki. Aka yi dariya
ita kuwa sai kunya.
A gida tana bawa Huzaifa labari yace ai kyan da
ya gaji babansa. Amma dai tun wuri ya sake
sunan nan. Huzaifa ne kadai mai Aish. Suka
rungume juna tace Babyn Aish....a hankali yace
naam. Tace yau na fada maka ina sonka kuwa?
Yace eh amma yana da kyau a yawaita
maimaitawa. Allah Yasa mu dace.
ALHAMDULILLAH
Godiya ta musamman gareku yan uwana
wadanda suka bani kwarin gwiwar rubutun nan.
💞 Zainab, Shukriya, Rumanatu, Sadiya and
Ibtihal.
Nagode sosai Allah Yabar zumunci.
Sai kuma yan uwana dukkan masu karanta
books dina. Wadanda na sani da wanda ban sani
ba. Fatan alkhairi garemu baki daya. Kamar su
Rufaida Omar's fans, Matan Albarka, Mu kula da
addininmu mata, Classic Ladies Novel, home of
novels, modern hausa writters da sauran yan
uwa da abokan arziki. Allah Ya bamu rayuwa
mai albarka.
Batul Mamman💖
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
        (admin
   Arewa hausa novels
       Novels villa
     Duniyan novels
   Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
          And
Cool novel, makeup and cooking)

      WHATSAPP NO:
    +2347039625239

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *