Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

ZAMAN MARINA COMPLETE HAUSA NOVELS

ZAMAN MARINA COMPLETE HAUSA NOVELS

[4/7, 13:46] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

   *4rm* Nabilancy luv
         
  Page.... 1-5
Kyawawan yn matane su hudu zaune akan kujerun dake ckn kayataccen falon dayaji kayan alatu kowacce fuskarta ba walwala balantana annuri dukkansu sun rafka tagumi tamkar masu jimamin mutuwa, alokaci daya suka kalli agogon bangon dake manne a dakin suka mike atare jin dirin motar wacce suke jira, dasaurinsu sukayo waje,daga can bakin gate kuma kyakykyawar matashiyar ce ckn mota ta danno da kan motar ta ckn gidan bayan megadin ya bude mata,  kai tsaye ta wuce parking space ta faka motar tata sannan ta manna bakin glass a fuskarta ta dauko turaren *five star* ta feshe motar kana ra futo ta rufeta, da saurinsu suka nufo gunta ganin yanayin fuskarta yasa suka sha jinin jikinsu cewar lallai ba ai nasaraba, babbar cknsu dasuke kira da Aunty Ruby takamo hannunta ta jata zuwa kayataccen gurin da suke zama dan shan iska a farfajiyar gidan gurin kewaye yk da fararen kujeru ga babbar rumfa da akaiwa gun kawanya da ita,dg can nesa kadan kuma dan karamin swimming pool  ne da gun hutawa  kamar gado agun, kowaccen su tasami guri ta zauna suna fuskantar sis Zuby wacce ta cire space din fuskar tata takallesu one by one kana tagirgixa kanta tagoge dan siririn hawayen dy taho mt a kuncinta, bataso ta karyar musu da zcy dan taga yanayinsu amma dole ba yanda ta iya kowacce tasan sirrin yr uwarta basa boyewa juna komai sbd kaunar d sukewa junansu, kowacce na dmw da dmwr yr uwarta,karamar cknsu ta dafata ckn sanyin murya tace mata"sis zuby baki dace ba kenan?daganin yanayinki bakiy nasaraba pls cool down ki gaya mana koma ya kukai insha Allah zamu samu wata hanyr bullewar,

  Dan murmushi rayi dabekai zcb, sannan tace"tabbas simoli banyi nasaraba amma nasamu ganin mahaifina saidai har yanzu yaki yai accept dani narasa ya zanyi da raina matar uba tai nasara akaina abu yk ci yaki cinyewa Aunty Ruby dazaki kyaleni walh da bazan koma gida ba zantayin yawon bariki nane har karshen dny tunda haka yk so shine silar sakani awannan hanyr amma yakiyin yafiya agareni ya yakeso inyi da raina?,  tafashe da kuka tareda kwantar da kanta ajikin Aunty Ruby wacce itama hawayen takeyi dama ita simoli tunkafin Zuby tai shiru dazancen taketa tsiyayar hawaye tanada raguwar zuciya gata da saurin kuka, hakama Laila Ukhty tausayi ne da ita sosai itama kukan takeyi,sai fiddausi Feedy yr dagwas batada saurin kuka amma manyan idanunta sunyi jajir ranta abace yk gata batada hkr ko kadan nan da nan taharzuko tace" a gaskiya mahaifinki mutunne me tsanani amma beyi miki adalci dukda akwai saka hannu a al amuran naku ni abinda nake gani  yakamata mui xuga muje hr can kanon walh musami matar mahaifinnan naki mui mata..... 

Hannu Aunty ruby ta daga mata da sauri tace"mui mata me? Kefa a,muranki sunada karancin nazari,inmukace zamuyi abinda kk nufi to zamu bata shirin mune, kunsan me zamui? Sukace a, a, zamuje ga dadyn zuby dukkanmu domin mutayata rokarsa tare da kai masa mgn me dd,  dasauri zuby ta dago kanta ta kalli Aunty Ruby tace"wace mgn ce aunty?  Murmushi Ruby tayi tace,maganar Auren khalid mana, akwai mahaifin daza aje masa da zancen aure ne yaki awannan marrar?

 Zuby tace"Aunty mahaifina daban yk ada can ma ya bujere wa aurena balle yanzu daya cire hannunsa akaina, alokacin yaki na auri wanda nakeso ma adalilin ya kasance talaka, "to idan da yaki yanzu zaiso insha Allah sbd saimunyi addu a zamu tunkareshi,  "aunty baxan Auri khalil bafa... For what?  Aunty ta watso mata tambaya, "khalil yana miki mugun so zuby zai iya komai akanki yaro da kudine khalil dan manyana ne shi mahaifinki bazai guji auranku ba mahaifinsa shine sanate a yanzu kullum khalil yana mk naci kina kinshi why?  Zuby tace"ina ganin kamar nagirmeshi aunty yaimin yarinta.. Dry laila tayi tace"hhhhh wadatar biki tsarki da romo lallai sis zuby ki godewa allah kada ki bujerewa ubangijinki yakamata kiy koyin ma aiki tunda shima ya auri nana khadija tafishi shekaru kuma ki sani wannan damar insha Allahu itace sanadiyar shiryuwarku da dady, Tace, to Allah yasa, tana yin shiru megadi yana bude gate wata arniyar mota ta kunno kai ckn gidan direct ya wuce prkng spc ya jera motarsa kusada tarin motocin nasu, murmushi aunty tayi. Tace :"dan halak na gidana.  Yakaraso da fara arsa dama yana da barkwanci saiyahau waka yana dry"yn matan gidanmu guda 4 ne sunki jinin wasa in aure kukeso kunsamu Auntyn mu kin yarda? 😁 dukansu suka kwashe da dry ya sami guri kusa da zubyn sa ya zauna *khalil ma' aji dala kenan*


*nabilancy luv*💘💘💘
[4/7, 13:46] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

    *4rm* ~NαβilancyLuv~®

    *page 10-15*
Gidan yn *marina* shine sunan da akaiwa gdn yn mata 5 dinnan lakabi sbd ynda mutane suka fuskanci zaman kansu suke zamane na kazo nazo amma nasu zaman me tsaftane suntab'a karuwanci wanda kuma Allah ya shiryesu a lokaci d'aya adalilin wani shehin malami daya nuna yana son Auren d'aya dg cknsu, k'erarren gidane nagani na fad'a wanda yk a ckn Abuja unguwar metama sule, wannnan gida sunyi h'adin guiwa ne wajen siyansa dmn kowaccensu me kudin kantace banda kudin da suke samu gurin maxa suna business agefe guda, saidai yakasance a samunma daya tafi d'aya samu, sunci wahala ta ryw kafin suxo wannan matsayin nazama guri guda, sunyi zaman gidan haya don anan suka had'u suka hade kawunansu gu guda.

  Babbar cikinsu itace  Aunty Ruby tanada shekara 38 sai mebi mata sister zuby wacce takeda shekara 32 sai kuma metake mata baya feedy "yar dagwas shekararta 27 sai Laila Ukhty me 25 years sai Autar cikinsu simoli tanada 22.

  Rayuwarsu zamansu gwanin ban sha,awa kansu ahad'e yake matuk'a ba'a jin kansu suna matuk'ar bin maganar Autynsu Ruby basa tsallake mgnrta itama tanaji dasu tarigasu tara arxik'i dan haka atun farko komai sukeso tana musu harkawo yanzu bata denaba itake ajiye kayan abinci agidan,Aunty Ruby macece me matukar tsafta, haka kuma tana tsawatr musu intaga sunyi ba dai daiba kfn su daina barikinsu bata tab'a bari sui kwanan gida,kwanan waje knn, bata so su kwana a hotel,duk abinda zasuyi to daga safe zuwa darene ko krfe nw zasukai bazatai fad'aba akan dai su kwanan tunda komin dare insuka dawo akwai megadinsu zai bude musu kowacce tanada motarta, su suke biyan megadin ckn asusun gida da suke zubawa haka me aikinsu yrnyace karama dg k'auye take suna biyanta kudi metsoka, basa barin gidan ba kowa,Ruby tana business dg dubai zuwa kano ana d'auko mata kyn funitures yn gaske akan farashi mesauki tana samun ciniki sosai tanada ma'aikata dasuke zaune a shagunan nata suna kula mata da kayan, Sister Zuby kyakyawace fara komai yaji tanada farin jini sosai akwaita da d'aukan hankln yn maza gata dason k'amshi turarirrikanta masu tsadane komai nata daban ne hatta motarta akwai turaririka sunkai 5 ciki wanda kowanne akwai tym din fesashi, hakama kuma d'akinta inka dubi kan mudubinta saika gaji d k'irga turare, itama business women  ce tanada babban shago dake dank'are da turarika da english wears wanda ta d'ora masu kula mata dasu, Alh sada shike shigo mata da turarika diseiner dg waje, Alh sada dan majalisane yana kashewa zuby kudi sosae domin shine yasa mata wannan jarin,

 Fiddausi feedy dasuke kira yr dagwas kyakykyawa ce chaculet kala gata da gashi har gadan baya ga hanci kmr biro, tanada wani hali na saurin fushi yanzun nan zaku hautsine amma batada rik'o ko kad'an tana girmama Aunty Ruby da sis zuby domin su suka jata jikinsu yakasance bata wulak'anta abarikiba, saidai tana drinking alcohol wanda dakyar Aunty Ruby ta rabata dashan giyar, infa tasha dakyar take kawo kanta gida daga mashaya, akwai saurayinta yusif sisco wanda shine ya koya mata shan giya tunkafin tasan su zuby, sisko shine silar hautsinewar komai nata arayuwa, Aunty Ruby ita tadage akanta hartaga ta rabata da zuwa mashaya domin intasha taringa kelaya musu amai knn har tsahon kwana 2 Aisha simoli itake gyarata sbd tanada tausai da jinkai, sukuma sukai burus da ita dataimakon Allah dai tayakice shan barasa, Laila ukhty kyakykyawa ce fara yr duma duma tamkar balarabiya take duk da ta tab'a zaman saudiyya wanda daga can tafara tab'arb'arewar ta silar wasu larabawa, tanajin larabci,hakama ayanxu hk ta dalilinta ne shiriyar Allah taxo musu domin wani bawan Allah ne magidancin shehin malami daya nuna yanason Auranta ya shiryar dasu wanda sun tab'a hdw a makka,

 Aisha Auta (simoli) yr fulanice fara beautiful tanada k'aramin jiki tanada girmama nagaba da ita, ita bata dad'e dashiga barikinba.....

 *Nabilancy Luv* 💘💘💘
[4/7, 13:46] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

    ~NαβilancyLuv~®

       *page 5-10*
Aunty Ruby tace da Kalil 'dan halak yanzun nanfa nake zancenka ashe kana tafe, kwana 2 ina kashiga?  Khalil ya juyo da kallonsa ga Aunty yana murmushi yace'sorry Auntyna nayi yr tafiya ne bansanar mukuba, bansan dani za, ai tafiyar nanba ne sai adaren Aunty Umma take sanar mini cewar ni zankaisu yola,

Aunty Ruby tace'dama ku yn Yolana ne? Haba _no wonder_ naga alamomi dayawa daga gareka....'hhhhh aikuwa dai Aunty na baki cankaba don mahaifina d'an maidugurine mahaifiyata kuma yr yobe state,  "to meya kaiku yola hr 2 days kuna can? "hhhhhh yan mata yaudai Auntyn mu tazama yr jarida,  yafada yana kallonsu, sudai sai Aikin murmushi suke,khalil yace"wato Aunty matar mahaifina mesuna Aunty Umma itace yr yola gidansu mukaje mahaifiyata ta rasu itace tazama tamkar ita ta haifen, tana da kirki sosai, a kullum ina mata zancen zuby ta aminta  da ita akullum dokinta taga ruby soyayyar da takemin ita takewa zuby tana ganin hotunan zuby  a awayata dan Allah Aunty kibamu dama inje inkai mata zubaida dan taganta hankalinta ya kwanta,  ya dawo da kallansa ga zuby data zuba uban tagumi tana kallonsa yana zuba, batai maganaba sai Aunty Ruby ce tace"wato khalil ka kwantar da hankalinka indai zuby ce ka kusa samunta dungurun gum domin na shirya mana tafiya gun mahaifinta inmunje za a tsaida maganar Auranku insha Allah kaidai katayamu da Addu, a domin samun nasara sbd mahaifinta yanada tsatstsauran ra, ayi, dan hk ka kwana da sanin zubaida takusa zama taka gaba daya, nandanan khalil yahau dry farin ck ya lillibeshi tamkar mahaifin nata nema ke ms wannan albishir din, tabbas dolene yaji ddi domin burinsa yakusa cika na mallakar wacce yk so, mafarkinsa zai tabbata, lallai daya zama me sa, a inhar yasami mallakar *zuby k'amshi2* 

Ya juyo ga zubaidar yai mata wani kallo me tsuma zcy tareda kanne mata ido guda yana murmusawa, yace"toya amaryata zaki je gidanmu tukunna  ki gaida Aunty Ummah me kaunarki ko kuwa saina fara zuwa gun dadyn naki?  Murmurshi itama ta mayar masa wani abu in khalil yayi kunya yake bata amma saita kanne tace"gaka ga Aunty nan duk yadda ta tsara haka za ai, 
   Aunty Ruby tai dry tace"khalil na amince zuby taje ta gaida Aunty umma tukunnan _latter_ saimuje gun dady da namu shirin koya kuka gani ladies?  Ukhty ta gyada kai tace'hakan yayi Aunty, Feedy yr d'agwas tace'hakan za ayi Aunty amma ina ganin kada mui jinkiri gara mugaggaguta tunda da zafi2 kan daki karfe,  Aunty takalli simoli tace'toke Auta bakice komaiba ko beyiba hakan kinada naki tsarin?  Da sauri simoli tace"haba Aunty yyi mana aiduk abunda kk tsara yy, saidai inason inmuki tuni da labarirrikan juna da kk ce zamu baiwa junanmu kafin mu rabu tunda kinga kowaccenmu nanda dan lokaci zamu koma gidajen iyayenmu.

  'wannan hk yake gara da kk tunamin wannan shiya kamata ma musaka agaba domin jin labarin junanmu yana da muhimmanci domin na bayan mu su dauki darasi agunmu, dan hk mutashi muje mui sallah anjima saimu had'u a _main falo_ domin mukoro _history_ dinmu _one_ _by_ _one_ tokai khalil saika zauna ckn shiri zan iya kiranka akoda yaushe inmunshirya tfyr dg gobe zw jibi, 

 Khalil yyi murmushi yace _ok_ my Aunty bari na tafi saina jiki.  Sukai sallama ya tafi sukuma suka mike suka d'unguma zw ckn gida dan gabatar da sallar magriba.

 *nabilancy luv* 💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

       *4rm* ~Nαβilancyluv~

  _wannan_  _page_ _din_  _nasadaukar_ _dashine_ _ga_ _Auntyna_ _*deejatu* _dorayi_  _maman_ _muhibbat_ _tareda_  _my_ _doghter_ _*pharty*_ *B*~*B*
_Alherin_ _Allah_ _yakai_ _muku_ _inda_ _kuke_

  *page 15-20*
Bayan sunyi sallar magriba da ishsha,i misalin ~8:05pm~ suka had'u a babban falonsu wanda yake d'auke da d'akunan kwanansu 5 ck d'akuna biyu suna kallon d'akuna biyu hud'u knn sai wani a tsakiyarsu na Aunty Ruby ne,tsayawa fad'a muku irin kayan alatun dake cikin d'akin b'ata bakine da _westing_ _tym_ domin kudi yai kuka wajen siyan kayan funture falon kuwa kamar agidan wani me baban matsayi a siyasar, suna zaune akan kujeru da babban table atsakiya wanda yk d'auke da kayan motsa baki,shugabar tasu bata isoba kowacce tana cin abinda takesone wanda kuma ko mara nauyi akaci shikenan saida safe kuma abinsu gwanin sha,awa, zuby _milk_ d'in kwali takesha sai _cake_ guda d'aya data gutsura ta ture, itako feedy yr dagwas danbun shinkafa takeci,sai lemon kwakwa datake korawa dashi Aisha simoli kuwa best food d'inta alale mekayan hade hade takeci dayake itake yawanyinsa tasaba cinsa ak'auyensu,  Ukhty kuwa shawarma ce agabanta tana ci ahankali tamkar anmata dole tacin, da sallama ta k'araso cknsu taja kujera ta zauna tareda yi musu sannu, suka amsa suna yi mata barka da fitowa, tace"kunjini shiru a d'aki walh waya nake me muhimmanci shiyasa,  zuby tace"aini Aunty nak'ara naji labarinki kawai shiyasa na matsu da fitowarki, Ruby tai dry tace"ai zakijine yanzunnan kuwa amma saiki shirya dan kece _second to d history_ sukai dry sannan taja ganganin malt ta bud'e ta kurb'a tai gyaran murya ta fara kamar haka:......

*****
Kamar yadda kuka sani sunana Rubayya hashim an haifeni agarin kaduna amma mahaiifiya ta yr k'asar Nijar ce acan mahaifina ya aurota, ni kadai suka haifa Allah yai mata rasuwa,sai rikona yadawo hannun kishiyarta da suka zauna tare duk da ba zaman ddi sukaiba dan dai mamana macece me hkr tana bin inna kulu sauda k'afa shiyasa basa fad'a sai tsananin haushinta da inna keji sbd baba yafi son mamana shatu sbd irin biyayyar d take masa, basu tab'a fad'a ba batai masa musuma, amma inna kam idan tana masa fada tamkar itace mijin shi matar har shayin ta yk sbd takan dan ci da gidan shiko baida sana a dayake itace uwar gida yaranta 2 duk mata sun girmemin zainab da Aisha me sunan mama na, zainab din talla take d'ora mata sai Aisha dayake sa, a tace bamu da wayo sosai, inna tana lelen Aisha yr primaryn da muka samu megari yasakamu nida Aisha saita cireta wai ana cin zalin yrta, nikuma haka a dan dakyar nasamu nakai aji 6. Inna bata saka Aisha ko zainabu aikin gida saidai ni nayi na horu da wahala komai ni nakeyinsa daga cefanen abincin siyarwar har kai nik'a da shara wanke wanke dana gama primary ma sai girki ya dawo kaina,baba bashida bakin mgn dayai mgn saitace yadaukeni yakaiwa dangina ni inyaso sai su aurarni haka yk zuban ido amma yana tsananin tausaina,ni kadai nake kwana a d'akin da mahaifiyata ta rasu ta bari, sukuma d'akinsu daya, inna tana samun kudi sosai banda kudin tallan harda nasamari inzainabu takawo karbewa take ga yn sana o in gida da take su kuka ,kubewa karkashi da sauran busassun kayan miya......

*Nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

  *4rm*~NabilancyLuv~®

   
  *Page 20-25*
Ranar dabaxan tab'a mantawa da itaba itace ranar da Muka fara had'uwa da wani kyakkyawan saurayi me suna munir akan hanyata ta kai nik'a abayana ya biyoni a motarsa mekyau yanata matsamin hon,harsaida najuyo Nad,an tsaya agefe Dan atunanina ko hanya yakeso nabashi zai wuce,saigani nayi yai fakin ya futo yanufoni da fara,arsa Wanda tak'arawa fuskarsa kwarjini da haiba,

kasa yin gaba nayi harsaida najira k'arasowarsa gareni yaimin sallama Na amsa masa,yagabatar da uxurinsa gareni ya bayyana min sonda yake min wai Ashe wannan shine gani Na 3 dayaimin akan hanyar saiyau Allah yabashi ikon saduwa dani,munnir yaburgeni kyansa yatafi dani Wanda nantake Na aminta dashi naimasa kwatancen gidanmu.

 Ashe Munnir dai kyan d'an macijine dashi asalin gidansu babu tarbiyya mahaifinsa mekud'ine sosai yashara yaransa maza hud'u mata uku ya Aurarsu,amma kaf cikin mazan kowanne da mugun halinsa Wanda suke aiwatarwa babu kwab'a balle harara,dukkansu a k'asar waje sukai karatu amma daga masu shaye2 sai masu bin mata da lalata yara alayi sai Wanda suka had'a duka mahaifiyarsu ma basa jin maganrta inma taso tsawatar musu to mahaifinsu kemata togaciya akan lamuransu dole itama tasaka ido akansu duk nima bangano hakanba sai bayan faruwar abubuwa da dama.

Aranar da muka had'u da munir saigashi bayan sallar magriba ina kan sallayata Na idar da sallah ina addu,a akan Allah yasa munir Mijin Aurena ne Allah yakawon domin Na matsu danaga nai Aure kina samu nutsuwa da "yancin kaina

Sannan nai addu,a akan Allah yasa munir yanada kyan hali domin tashi guda zuciyata takamu da sonsa, koda yaro yashigo yace ana kiran Rubayya awaje saida inna ta zabura danjin abinda bata tab'a jiba harcewa yaron tayi yajedai yatambayo Aisha akace ko zainabu? Nidai nai shiru agefe dannasan kwanan zancen itanma zainabu babu ko kare daya tab'a zuwa gunta saboda muninta,🙄😉

Yaro yadawo da k'arfin guiwarsa ya jaddada mata cewar Rubayya akace masa,aiko inna tahau raba ido ta tambayeshi waye yafad'a mata cewar wani ne a mota,aifa nan naga bak'in ciki ka'rara duk sukai tsit dama baba bayanan yana masallaci,natashi asanyaye nafuce,

Munsha hira da munir wayayyene sosai ga iya tsara kalaman soyayya nasace zuciya aifa nan da nan kafin murabu nasaki jiki dashi tamkar mun dad'e tare,banshiga motarsa Wanda shi naga hakan yaso Dan harda kwantar da sit wai naxauna Niko nak'i sbd rashin sabo,kuma ina tsoron baba yadawo yaganni a cikin motar namiji tunda kullun yakan nunamin innutsu inkame kaina kada zubda mutuncina Na "ya mace ganin yanda " yan uwana suke a sakaka ba kwab'a basajin maganarsa dama kodon suna ganin inna ta renashine kokuma ganin bashi dashine? Kokuma ganin in yana musu fad'an innar Na shigar musu kota hana,to nikam nasan marainiyace kamar yadda yake gayamin akullum inrik'e maraicina ko Allah ya yashigen gaba.

 Da munir yaxo tafiya wata bak'ar Leda yabani cike da kayan kwalam su biscuit da alawowi masu tsada da kuma kayan kwalliya harda kud'i ya k'aramin Wanda dak'ar nak'arba saida naga ya matsa min Na karb'a ckn jin nauyi,

Ina shiga gida inna nagani atsakar gdn tana zarya tamkar tana jirana,aiko ina shiga tai caraf ta karb'e ledar hannuna ta bud'e takwashe kayan kwalliyar tace zainabu xata baiwa ita yakamata tagyara baniba,

Ta wullon alawowin sannan tace dole nabata kudin daya bani domin tana zaure tana kallon lokacin daya bani,ban nuna damuwataba Na bata domin bansan zansamesuba balle Na damun,

To Ashe abinda bansani  bama harda zainabu ayimin "yar labe in munir yazo sbd zuciyarra takwadaitu da munir kullum inyazo saita mak'ale azaure tana kallonsa domin yana zuwan yamma inyasha wanka yaxo tamkar in lashe nima Dan had'uwar dayake yafi kyau da k'ananun kaya,

tabbas munnir d'an kwalisa ne gashi abin hannunsa berufe masa idoba,duk zuwa saiyabani kud'i amma danasan cewa inna nake karbarwa sai nadena karba duk nacinsa Na saida karb'a saida y hkr sai in kayan kwalam da mak'ulashe yakawon ne nake karb'a sbd inna 2 take rabawa tabani rabi kuma bana dmw Dan arxik'ine nima inbasu shaba sunmin yawa dole nakyautar, akwai ranar Dana gane lab'en da zainabu takemin munnir yakawon atamfofi guda 2 nakarb'a munrabu nayo gida kacibus mukai da zainabu a zaure aiko naxuba mata ido da mamaki afuskata itako bata damuba Dana gantan saima harara data bini dashi naiciki ina Allah wadai da ita araina dankam girma ya fad'i,

 intak'aice muku wad'annan atamfofi basu zama rabonaba dan inna karbesu tayi ta rabawa su zainabu da Aisha to nanma bataga nadamuba Niko nake gani 'yan uwanane in inadashi zan iya musu abinda yafi hakama tunda abin duniya ai fararrene k'ararre.

  *nabilancy luv* 💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

 *4rm*~NabilancyLuv~®

*page 25-30*
Tafi-Tafi soyayyarmu da munir ta mik'a munyi kusan wata 2 tare,Ashe abinda bansaniba Zainabu Yr Uwata Son munir yasakata awani hali hr rashin lfy ta kwanta

 baba yasata agaba yana tambayarta meke damunta tak'i gaya masa Dan tana ganin bazai iya mata mgnn matsalar ba tunda tasan baba yana sona bazai rabani da abinda nake so yaba taba,haka a dole ya hkr ya kyaleta don yaga kullum inya shigo gidan tana kwance a tabarma a tsakar gd kuma duk ta rame,shi tsoronsa ko ciki ta d'auko tunda yasanta da rashin kamun kai dama Aisha ce Yr nitsattsiyar

 to itama kullum tana hanyar tallar abinci bin shago2 da kasuwa da tasha shikam don dai ba yanda xaiyine daya hana amma bashida power

toshikansa shayin innar yk juyashi take sai abinda tace dashi saida yaga inna bata gurinma ya iya tuhumar zainabun Dan inna harzuk'o ms zatayi.

Dataga zata cutu bashiri tasami inna da zancen aifa dad'i kashe inna dama tasha kwad'aita hakan aranta dontasan in zainabu munnir ya Aura zatafi kowa hutawa amma inhar Rubayya ce matarsa bazatai ta itaba dangin mahaifiyarta zata nema.

Aranar inna taja zainabu gidan wani bokanta da take kai Babana can,

Da kudin dayake bani tana karb'ewa dashi akai mana mugun Abu domin tagayawa bokanta k'udirinsu akanmu tanason arabu kwata2 ya mance dani yakid'ime da zainabu yaji duk duniya ita kad'aice agabansa

Mak'udan kud'i ta direwa boka d'an tsulaye nan ya bata wani kwalli da turare kwallin yace inyaxo zatasaka aranar da zasu had'u kada ta had'a ido da kowa saishi,turaren kuma Na mallaka ne duk randa yaxo gunta zatasaka shi,

Hakan kuwa tayi tabi ka'ida don kuwa Ni aranar inna ta aikeni in kai mata kudin adashi da takeyi ranar juma,a ce hardacemin in me adashin batanan naxauna Na jirata,

Sai shida Na yamma munir yaxo dama tana zaure a lab'e tana ta lek'e tasan yana zuwa juma,a guna baya tsallake wannan ranar taringa Allah2 yaxo kafin nadawo dantaga yai jinkiri,saida taji dirin tsayiwar motarsa sannan taji ddi da sauri ta futo daga bayan kofar a zauren ta gyara d'aurin d'ankwalinta ta fesa turaren tareda zizara kwalli a idonta

Da yanga ta isa gareshi azatonsa sahibarsace ta futo haryana lakwasa kai yana murmushi saida ta matso kusa yaga akasin haka

Da sallama ckn siririyar muryarta tashiga gaban motar 🤔😮o,su zainabu ba kunya ko don tasan abinda ta takane ta d'ago da kanta ta kalleshi cikn kashe ido ta gaidashi,ya amsa a dabarbarce 

Wani shock ne yashige shi yakasa d'auke ido akanta ganin irin kallon da take masa,kasa mgn yyi don bakinsa da jikinsa sun mutu ji yake tamkar ya rungumeta bayama dayaga kirjinta ta turosu gaba,tabbas zainabu ta kware kan makirci da kissa,harda shafo hannunsa tana fad'in "ko bakai Na,am dani bane?inbakaso Na dena sai intafi,

Da Sauri a kidime yace" a,a a, in kika tafi kuma waxan kalla naji ddi?takanne ido tace"Rubayya mana, yai tsaki tare da girgixa kai yace "babu wata Rubayya a gabana ni saike

Ckn jin ddi ta shafa tafin hannunsa tana masa tfyr tsutsa tace" Allah moonyr d"ina? Ya lumshe ido ckn jin ddin sunan data kirashi

"Allah kuwa aidake Na dace baby' " ba baby suna naba sunana Zainab, yai murmushi yace"my zee kinfi ko wace mace iya kallo da mgn.

Tace"nagode da yabawa.

 Suna haka Na dawo daga tsinannan Aiken inna Na makirci Wanda tayine dantaga cikar burin zainabu Wanda yazame musu nadama daga k'arshe

Saida nakusa fad'uwa daganinsu a tare  nai dauriya sosai daban iya tunkararrsuba nakalli munir Wanda yakallen ya watsar nakalli zainabu wacce taketa hararata,

Kafata kasa d'aukata tayi da sauri nayi ckn gida aifaduw nayi ad'akn kfn ma Na k'arasa kan Yr katifata lallai namiji kudan zumane,narasa laifin waxan gani anan,

Nafijin haushin munir dahar zaiyi saurin amincewa aci amanata kuma dashi za a cuceni lallai Niko nabar munir har k'arshen rayuwata tunda aiyasan yanda muke da zainabu

*nabilancy luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 30-35*
Nasha kuka nagode Allah aranar har zazzab'ine ya rufeni, tabbas zuciyata tanason munir Amma dolene inkoyi juriya akansa nasan *SO* Wanda yakoyar dani wasu abubuwa da dama nadaga cikin sanin muhinmancin soyayya munir d'an luv ne gashi kyakykyawa son kowa,

Yatara abubuwan da mata keso Shin Amma meyasa Zainabu zata min haka? Ba komai akwai Allah sainasawa raina wannan itace babbar jarabawata arayuwa nai alk'awarin zanyi juriya Na d'auka,

naci burin inzanyi Aure inje ga dangin mahaifiyata a Nijar,to yanzu komai ya tarwatse shin wa zan Aura?  Ba kowa" naji zuciyata tabani amsa Na goge kwallar data zubomin nace araina"Allah kashigen gaba.

inajin shigowarta wajen taran dare tana fad'awa inna sunje shopping dashi yai mata siyayya, hhhhmmm lallai munir wato duk kyauna betab'a cewa muje ba sai zainabu danafi ta kyau,nafad'a zcyta a wauta knn, Na tashi dakyar Na lek'ata ta window nahangosu su uku a tsakar gidan

 Aisha Na bud'e ledar Inna kuma tana faman irga kudin daya bata tana washe baki tana fad'in "kinga ko ai da arxik'i a garin wani gara anaka,shiyasa nake sonki zainabu akwai bin aiki dalla2,

 na dawo da baya nakwanta kan katifa ina kuka Shikenan Na rabu da munir ina ganin ko abin bame yiwuwa bane Ashe hardasa hannun inna a ck Shikenan Na barwa Allah,

aranar tsakar dare natashi nafad'a Allah kukana Na rok'i Allah daya ciremin son Munir A raina
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *continue 30-35*

Washe gari ranar asabar saiga munir yadawo ya aiko zainabu taxo nasha mamaki domin baya zuwa guna kullum fashin kwana d'ai-d'ai yake min,da rawar jiki ta futa har najiyo inna tana fad'in "kin fesa turaren ko? Hartakai zaure ta dawo da sauri tana fad'in" namanta inna gara da kika tunamin,

Na tab'e baki ina tu,ajjibin wannan abin kunya natabbata yn unguwa ma saisun zagesu,koda ta dawo ina tsakar gida ina tuk'a tuwo inna ta tareta sukai d'aki Ashe waya ya kawo mata.

To tundaga nan dai Na tabbatar munnir ya zama Na zainabu ko bezoba suna tare a waya, wani abin ma da gayya take dannaji haushi amma bantab'a bari angano wani Abu a fuskataba Dan ina k'ok'arin shanyewa


 baba kuwa saida yaga munkeb'e yake tambayata dalilin dayasa munnir ya dawo gun zainabu ko Na masa laifine?nace ' babu wani dalili makirci suka kullamin yadena kulani,ina hawaye nake gaya ms aiko ya tausayamin shima kamar yai kuka ya girgixa kai yace'Rubayya kiyi hkr kid'auki hakan tamkar wata jarabawa ce Allah yasakko miki da ita kiyi kokarin cinyewa zakiga haske arayuwarki kuma zantayaki da addu,a Allah ys hakan ne mafi alkairinki,nace"amin baba,

Watansu d'aya da fara soyayya ya turo magabatansa gidanmu Neman Auren Zainabu,Baba da mak'ocinsa suka karb'i bak'i aka tsaida lokacin Aure wata biyu

 suka cake mak'udan kud'i akaita kuwa zuzuta zancen danhar nunata aka ringayi danma idonta ba kwalli.
Ammafa kfn a tsaida mgnr Auren yana yawan zuwa d'aukar ta su fita yawo ko siyayya shop-shop

Inko yad'auketa da dare basa dawowa da wuri saisukai goma koma fi tasan baba ba fad'a zai mata ba tunda bai isa komaiba agunta,

Inna bata bacci harsaitaga dawowarta sannan saita rufe gida inma sunkai dare sosai inbaccin ya d'auketa insun dawo takan buga taxo ta bud'e mata.

Yanda baba ya zuba ido akan lamarin haka nima Na zuba idon nakuma fawwalawa Allah domin Munir yaficen arai kwata2 mutuncinsa ya gama zubewa bansan haka yk ba dama. Dukda yasan takun shi da zainabu da nawa ba d'aya bane.

Innafa zama bekamata ba domin tana ganin kwanaki ya rage ayi bikin tahau shiga daficen siyayyar kayan Aure dantace saita fitar da yarta zainabu kunyar gidan masu kud'i.


Tana samun kud'i gun Aisha Wanda bata tambayrta ya akai tasamosu over akan tallar data d'auka

Haka ta tusa baba agaba wai lallai sai yyi wani abun a Auren d'iyarsa ta fari ko bashine yaje yaci be isa ya zuba mata ido tasha wuya ita kad'aiba.

Yace mata shikam bashida hanyar bashi tace tanada hanyar ita zata samo inyaso nan gaba ya bayar,haka ya amsa badan yasoba Dan yasan rigima ce babba take nmn ta d'ingimo masa.

Anyi haka da kwana 2 ta nemo masa bashin fili filoti guda aka saida akan tsububun kud'i tace Na wani tsohone akai mata hanyar samu nanda watanni inya buk'ata saiya bashi,

To dayake anyi masa rufin baki haka ya amince mata batareda yayi tunanin ina zaisamo ya biyaba.

   *nabilancy luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

 *4rm*~NabilancyLuv~®

*page 35-40*
Anyi biki Na kece raini munnir yakawo kayan lefe akwatuna shida cike da tsadaddun kaya da ita suka had'o lefensu,

party kuwa saida akai kala biyar nikam d'aya Na halakta Dan banida kayan zuwa partyn Wanda najema babane yaimin kala d'ayan bantambayeshi inda yasamo kud'inba haka ranar d'aurin Aure yinin iyaye Na inna kayan Na maimaita,

Inna ta fitar da zainabu kunya kamar yadda tace domin taimata kayan d'aki masu kyau da tsada yn kamfani haka ma munnir ya k'era gida Na gani nafad'a a ckn kd d'in Tabbas bikin yaja maganganun mutane Wanda sai bayan bikin ne magana ta futo mukasan munanan halayen munnir Wanda nagodewa Allah nariya araina cewar Alhakina ne Allah zai nuna musu shiyasa duk baasu sankomaiba saida akai Auran

Ban tab'a tunanin zuwa gidan zainabu ba to mema zaikaini inje inga takaici? Dama jininmu bai had'u da itaba koda ba munir maci amana ta Auraba ba inda zanje mata inna ma bata tab'a cewa najeba Aikema Aisha take Aika.

Tofa wata daban bayan bikin da wata uku Aisha ta d'ingimo abin kunya tayo ckn shege awajen tallan nata kuma abin takaici tace Wanda yaimata ya gudu asalima ba d'an kadunan bane akano yake lodin kaya suke zuwa a babbar mota ya gudu legos

Babanmu Dan bak'in ciki har hawaye ya zubda ya tusani agaba yanamin nasiha yanatuna sarni Dana rik'e maraicina kada nakalli abinda Aisha tayi dukda yasan ba halinmu d'aya ba sannan yace lallai2 nafito da miji yaimin Aure kfn yabar duniyar yanaso yaga nasami yncina kamar kowacce mace dake d'akin mijinta.

Nacewa baba nikam ba Wanda nake saurara asamarin dake zuwa guna banji Wanda ya kwantan araiba asalima ko zancen bana futa insunzo gara kawai inyanada Wanda yaga ya dace dani Na amince ya Aura masani kawai zanyi biyayya Na zauna

Yaji tausayina matuk'a yasan zan iya masa biyayyar shiyasa yace zaiyimin Addu,ar Allah ya futon Dana gari Inna kam Haushin shi takeji ganin yadda yake nunan kulawa ko shigowa yayi beganni ba hankalinsa baya kwanciya saiya ganni ko aikena inna tayi har hanya yake bina mudawo tare kokuma yazauna a k'ofar gida harsaiya ga dawowata mushiga tare tofa

 hakan kebak'antawa inna rai ganin Aisha ko kallonta bayayi saitake shan takaicinta ita kadai danma mutane basu fargaba tunda cikin befutoba bashiri ta tusa awakanta agaba ta tasaidasu takai Aisha Asibiti don azubda cikin Aiko dai Ashe zubda ciki shine hanyar rasuwar Aisha anan ajalin yake

Inna tasha kuka had'eda Dana sani kwananta 2 tana kukan rashin Aisha aidole taikuka domin Aisha tana nemar mata kud'i sosai in abincin dubu uku tad'auka zata kawo mata dubu shida ko bakwai takarb'e ba tambayar ba,asi

Ga zainabu bata taimaka mata da komai dan tunda akai Auren batazo gidaba
Nima nai kuka sosai Na rashin Yr Uwata Aisha sbd takan sakarmin fuska tajani ajiki bata yrda taga anhanani abinci tasha d'ebarmin ta b'oye adakinsu tace indare yyi inci Inba ai girkiba


Anyi zaman Jana,iza mutane suntaru sosai domin baba Na mutane ne yana xaman mutunci da yn unguwa haka kuma basusan meye ummul-aba,isin mutuwar Aishaba

Abin mamaki zainabu batazoba sai ranar sadakar ukun Aisha sai wani yatsina take tana jijji dakai wai ita ga matar me kud'i amotarta taxo fara mekyau Ashe yana Aurarta yafara koya mata mota suna dawowa dg honey moon yasai mata motar

Bataji kunyaba tafad'awa inna cewar mijntane baya gari yana India saijiya yadawo ba dama ta futo besaniba

Kuma bata dad'eba Tace zata koma gida tana da bak'i Inna dai bataji ddn abinda zainabu tayi matabà Dan dai kada mata yn zamaan makokin sugano suce wani abin shiyasa tayi gum

Jikin inna yafara sanyi akan Auran data had'a Na zainabu da munir tunda taga hr yanzu bata morar zainabun kuma tasan tana samu gunsa Yr tsako tazama dai samu kk dangi,

azuciyarta taringa nadama tana ayyanawa inama da Rubayya tahad'a tasan datuni tasamu abinda tasamu tunda tana tsoranta komai zata bata inta buka'ta  amma ga zainabu tajuya mata baya tamkar ba ita ta haifetaba,

Aidama Alhaki kuikuyone....😛😛😂😂
 

*nabilancy Luv*💘💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

  *page 40-45*
Cikin "yan Kwanaki kad'an innafa tashiga rashin kud'i yn jarin nata sunxama k'alilan ga ba kayan abinci datake ajiyewa dama itace gidan ba kullum VB baba yake samuba inya futa buga-bugarsa

Lamarin ya ta axxara befi muci abinci sau d'aya aranar ba haka zamu hak'ura saitace in anaso aci abinci saidai in zage inmata tallah

Abinda kuma baxan iyaba kenan ko baba yanaso baxanyiba ganin halin da Yr,Uwata ta shiga kafin rasuwarta adalilin tallah takuma rasa ranta to balle ma baba baya sona da yin tallah tun usuli, tunda naji tai shiru da zancen
nasan k'ila akwai wani mugun abun daxata k'ulla shiyasa tai gum ta xuba mana ido.

Akwai lokacin da taje gidan zainabu k'arfe goma nasafe ko tashi dg bacci bataiba taji zuwan innar aiko dai danhaushi bataiwa inna taron arxik'iba

K'irik'iri tace mata kada tasake mata sammako haka mijinta befutaba kada ta bada ita ko taja mata abin gori gun dangin miji inna taji haushi tahau mata fad'a itama ta k'ufula tayo kan innar da fad'a hardace mata taisauri tafuta kada yaji yafuto inwani abinne ita zatazo(kajifa kamar zuwan take)😉

 Inna rai ab'ace tafuto hartana tuntub'e aranar ta dad'ayin mugun Dana sani dawanann Aure Na zainabu

Danaga abincin danake samuma sau d'aya aranar yana nema ya gagareni samu saina samu Babana da zancen yanemomin kud'in motar zuwa gun dangin mahaifiyata intafi can, yabani hkr wai bayason nai nisa dashi yana ganina yana jin dad'i gara inbari in Allah yakawon miji innai Aure naje musu da xiyara kawai,haka Na hakura badan nasoba

******""""""""
Bayan kwana 2 inna taxo dawani tsoho a motarsa vectra sun samu baba yana gida dayake tasan shirin data shirya saida taga yananan dama tatsiri fitar,Ashe wai shine me filin data dauko masa bashin alokacin Auran zainabu,

*nabilancy Luv*💘💗
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *Continue 40-45*

~ayimin uxiri in anga naraba 2 nayi cigaban adalilin innafara typing ne kafin nai nisa sai cajina ya k'are to ina gudun kada tamutu yagoge shiyasa nake saurin katsewa  kunsan kuma type akwai wuya dakuma takaici kayi ka rasashi~ *tanks ol my pan's*

Hankalin baba yaso yatashi danganin bashida kud'in daxai biya bashin yabaiwa mutumin guri yazauna akan tabarma suka gaisa tsohone zaiyi Sa,an Babana amma daganinsa yana smoking gashi mummuna bak'i

Nidai ina daga d'aki nakasa kunne Inji abinda zai wakana

Saijinai mutumin yacewa Babana yaxo karb,ar kud'insa ne kokuma fili inba kud'in Aure yakeso yayi don matarsa tarasu tabar masa "Yaya yanaso yasami macen da xata rik'e masa su,

Baba yahau bashi hkr yace yanada wata gona a k'auye zaisaida intayi rabin kud'insa zai bashi...bebari baba yak'arasaba yace Sam bazai karb'i rabiba tunda shima bada Rabi yabashiba,wato shiya rufa masa asiri alokacin Auran yrsa shine shi kuma zaitona masa anasa Auran to tabbas kotuce xata rabasu, yanda Babana yashiga d'imuwar maganar haka nima nashiga daga d'akin kaina yahau sarawa jin za,akai ubana kotu duk akan tsinannan Auran zainabu

Inajiyo inna tad'an rage murya tace" to mallam mexaisa kabashi Auran Rubayya abacin kudin tunda ko matar dazai Aura besamu ba yana dai Neman tagarine tunda kuwa yarinyarnan akwai nutsuwa da biyayya ai za,a dace kokuwa? Baba yai shiru kansa ak'asa yana tunani takalli Alhajin takanne masa ido tace "ko kanada macen da xaka Aura ahak'ura da had'in Dana tsara Alhaji?

Dasauri ya girgixa kai yana dariya da gib'insa abaka yace" a,a inafa nasamu mahaifiyata CE ta matsamin dama amma tunda gata gidama ai Shikenan sai ayi hakan,(dagajin wannan batu ai kunsan akwai makirci cikinsa)

Baba idonsa ya kad'a yai ja yace,ba za,ai hakaba,baxaiwa Rubayya Auran doleba har inba ita kesoba sbd yana tausayinta batada uwa araye...nanfa inna tahau fad'a bai isaba tunda ta shirya hakan to dole ayi Dan ya tozarta ya nuna bata isaba,to walh saidai ayau ayau yamaida Ni nijar gun dangin mahaifiyata tagaji da rik'on wahala kuma k'ara ayau za,a shigarta

Tahau xuga Alhaji tana yatashi yaje yashigar da k'arar itakam ba ruwanta aima yayi mutunci tunda wata uku akayi xa,a bashi gashi ank'ara masa watanni akai.

Asukwane nafito daga d'akin na durk'usa gaban baba kaina ak'asa ina zubda hawaye nace'baba Na amince zan Auri Alhaji inhar za,a bar maganar kud'innan hr abada, inna tai murmushi tace,kaga Yr albarka, shiko baba dafa kaina yayi kawai yace"nagode Rubayya Allah yai mk albarka yabaki yaran dakema zasui miki biyayya kamar yadda kikaimin ayau kika fitarni kunya, Na mike nabar gun ko kallan Alhajin banyiba balle naga Kalarsa.

To tundaga nan fa zancen Aurena yatashi da Alh Namadi Wanda zuwansa guna zance sau d'aya nikuwa nak'i futa tome kuma zan masa yakawo kudinsa Na gaisuwar uwa da uba da sadaki duka dubu d'ari Wanda kuma yace kada akaini da koma yasaka kayan furniture's agidan har kayan kicin akwai lefene yace baxaiyiba sbd yana bin ubana kud'i inna tace aiba komai hakanma ai yaimana mutunci ansaka ranar Aure wata d'aya kacal sai baba yakwanta rashin lfy aiko dai hankalina ya tashi matuk'a gaya dama naga tunda aka fara mgnr Aurena da Alh namadi yake ckn damuwa duk ya rame,

Alh namadi shiyaita jigilar kaishi asibiti anan nasami damar k'arewa angon nawa kallo lallai badan nayi niyyar yiwa baba biyayyaba Dana fasa, aikoke mekaratu aka d'aura mikishi ak'afa saikin kunce kin gudu gashi k'ato gashi mummuna ga wasu muggan tsagu kwaya kwaya tundaga baka har wjn kunnensa

Allahu Akbar! Ana saura sati d'aya bikina Babana ya rasu aiko nasha kuka tamkar zanbishi Shikenan nazama marainiyar dole Na rasa mesona da tattalina zanyi Aure nashiga sabuwar rayuwa zan Auri mutum me budurwar zcy, rana zafi inuwa k'una.

Zanyi biyayya bayan rai Dan Auran Alh yafiyemin zaman gaban inna tunda babu Babana aduniyar tabbas gata tayi arayuwa.

Ranar sadakar uku inna tace baba yabar mata wasiyya cewa komutuwa tayi tokar ad'aga bikina da Alh namadi lallai ko aranar ya rasu tokar afasa ayishi ko ran ukunsa ko bakwai,haka ko akayi aka shaidawa 
Mutane cewa ranar sadakar bakwai ana gamawa yiwa baba addu,a to za,a d'aura Aurena da Alh Namadi..

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm* ~NabilancyLuv~®

*page 45-50*
Ranar sadakar bakwai d'in Babana aka d'aura Aurena da Alh Namadi Yayan Babana baba Umar shine wali Na Wanda shikad'ai dama yake dashi aduniya yana zaune gidan d'ansa sbd ya tsufa bayada abinyi matarsa kuma ta rasu
Ba ko dangin mahaifiyata a d'aurin Auren basu saniba zainabu taxo ranar da baba ya rasu bata dawoba sai ran bakwai duk ta rame tai duhu inna kallonta kawai take data gaishetama dakyar ta amsa mata nikuma naga tasaki jiki dani tasakarmin fuska asab'anin da, dasai kallon wulak'ancin da harara

Aranar da dare aka kaini gidansa dake tudun wada babban gidane ba laifi ya d'an had'u

Sai can dare wajen sha d'aya da rabi Ango ya shigomin ko d'an kayan siyan baki beshigo min dashiba kamar yadda ake zuwarwa da kowacce Amarya ran Daren farkonta nai mamakinsa ma daya xamo jahili a fannin addini domin ko Yr sallar da akeyi bece muyiba balle hira me dad'i atsakaninmu ya afkamin yarabani da budurcina ta k'arfin tsiya kuma yatashi ya koma d'akinsa babu rarrashi dayaga ina kuka,ai dole ne Na koka mekaratu kufa haska abin aranku akwai tausayi a ckn lamarin toshi sangamin baejiba ya tsallakeni yai nasa sashen

Da safe tashigomin da buredi da shayi a plask

Da rana kuma ya kawon abinci a take away,da dare kuma saiga tuwon masara miyar kuka a wata k'azamar langa wai Inji matarsa!😳

Nai mamaki sosai dayace matarsa domin muce mana yai matarsa ta rasu Ashe kenan k'arya ya sambad'awa babanmu,

Wannan k'aryar dayai ita tak'ara min tsanarsa araina mutincinsa kuma ya zube a idona Dan da alama akwai yaudara aharkarsa da munafurci

Da dare yayi ma hakan ya dad'a afkamin babu tarairaya balle yn Aike Na wasa haka ya jijjimin ciwo saini nai bikin kaina da ruwan zafi

Saida mukai sati 2 ahaka ba fashi ba d'agun k'afa innaganshi hr fargaba nk saida nashiga hutun sallah kana sannan nasami salama yakoma gun matarsa da kwana amma sainaji gidan tsit nayi tsuru dani

Saidai kwanan tsoron danake yafi min kwana da mugun nan domin nasan wataran zan saba, ya ajjemin kayan abinci dama ina girkina garin tuwon dawane wai yafi sonta sai shinkafa Yr Hausa amma med'an kyau (jamila) nihakan yafimin dadai  intacin k'asimun d'anyen tuwon matarsa kokuma ZAMAN gaban inna gara ace in share d'akina in zauna inyi biyayyar Aure Wanda nakeyi don Babana

Saida yai sati agidan matarsa sannan yadawomin

Tsarin dayai wai kowacce sati sati zai ringa mata kujifa banzan tsari saikace awata uwa duniya matar tasa take,bawani nisafa sosai

Wannan zuwan Na Alhaji ya tsoratani sosai domin da dare yayi zai kwanciyar Aure dani sai yaxomin akasin yanda yake zuwarmin ta baya yake kok'arin nemana nikuma nak'iya

Mukasha damben tsiya dashi duk k'ibarsa Allah bebashi ikon fin k'arfinaba,domin beci galaba akainaba amma nasha wahala haka ya Hakura ya kyaleni yana maida numfashi haka kullum nake kwatar kaina da cizo da naushi da yakushi har kwanakin dazaimin yak'are ya k'ara gaba,tabbas nasan wannan hanyar bame bullewa bace nasha ji anacewa babu kyau namiji yanemi matar sunnarsa ta baya Dan haka saina d'aura d'amarar yak'ar Alh

To koya matarsa take dashi?? Allah masani ina gefe bansaniba shi kuma dama behad'amu

Aikuwa aranar dayabar gidana nagudu gidan inna Dan baxan iyaba,tunda naga abin nasa da gaskene nayi hakan ko Allah zaisa inyazo aimasa fad'a ya gyara, Aiko ina zuwa natarar Zainabu taxo gida kwananta ma 2 duktai bak'i tarame ssosai batada lfy

Inna taxaci zuwan ziyara naxo saida taga dare yayi ne tace shizaixo yad'aukeni nacemata a,a nifa baxan komaba,aifa tayo kaina danme ban isaba,inma nadawo ne Dan in d'ora mata nauyi to baxata iyaba jegon jakar datai da ma Allah ya biyata,

Inkuma zan mata talla ga d'aki nan inxauna gaba takaita inko baxan yiba tunwuri kan dare ya tsula innemi gurin zuwa (kuji fa kodon ba ita tahaifen ba shiyasa baxata tsaya jin ba,asiba balle ta sharen kukana)

Nidai ban ce mata komaiba Na shige d'akina Dana bari akwai kud'i a k'uguna suna ringa b'atarwa Dan kwanana 5 agidan bata bani abinci insunyi Dan zainabu bata tafiba basa son Inji abinda suke ck sai k'us kus suke kawai,

Takaicina Alh bebiyo bayanaba to sainai tunanin kodon kwana Na bexagayo ba shiyasa besan ina gdnmuba,

Tunda shi bashida tsari mekyau balle kulawa

Aranar danai kwana 6 saijinai sundawo daga asibiti zainabu tana kuka wai munnir ya cuceta yashafa mata Alak'ak'ai, anan naji inna tana kyararta aidalefinta meyasa tun farko datasan yana Neman mata har ckn gida yake kawo matasu bata fad'a mata ankaishi gun malaminsuba yai aiki akanshi yahanashi saida Abu yakwabe to tasani wannan Alhakine data d'auka yadawo kanta

Nidai ina daga d'aki ina Al, ajabin abin ina kuma godewa Allah Dana ni ya k'addarowa Auran munir ba tabbas gaskiyar inna akwai hakk'ina ack dakuma nata domin duk Wanda ya wulak'anta iyaye to wataran shine wulak'antacce gashinan ai xata gani akwaryar Shanta....

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

 *4rm*~NabilancyLuv~®

*page 50-55*
Aranar Dana ck kwana bakwai agidan mu saiga Alh Namadi da daddare wai yazo yaji dalilin shin meyasa nataho gida batare daya saniba?,

Inna tace aiganinan ya tambayeni don tunda naxo ban gaya mata dalilinba,tahau dai zugashi matarnan ta yanda ya hark'uza tun agidan yahau min bala,i kamar ya cinyeni harda kumfar baki da kawon mangara inna tace lallai lallai Na d'auko mayafina nabi mijina

Haka nabishi ina kukan rashin gata da bani dashi,tunda mukaje gida ko zama bebari nayiba yahauni da duka yana faman cab'amin maganganu wai ubana mecin bashin tsiya yakasa biya ya biya da "ya,

Kuma dole ne konak'i ko naso inxauna dashi kokuma inbiyashi kudin daya biyo tsohona.

Nasha kuka aranar Dan bak'in ciki baxan tab'a mantawa da wannan ranar ba domin itace ranar da Alh ya cika burinsa akaina Na nemana ta baya aiko dai nasha bak'ar wahala tabbas Alh mak'etacine Mazalinci kuma saidai Allah ya sakamin kawai

Haka awashe garima yazomin da niyyar hakan Dan rashin tausai nikuma naga zai cimma burinsa bashiri Na rarumi wani k'arfen labulai Na kwad'a masa Na gudu toilet Na rufe

Haka har akai sati bansake ganin saba a " yan kwanakin saina hana idona bacci nake tashi ckn dare ina gayawa Allah daya kawo k'arshen wannan zaman ckn hanya me sauk'i

Tabbas Allah me karb'ar addu,ar bayinsa ne domin kuwa aranarmu dashi Na k'arshe ya dawo gidana benunan komai a fuskaba,kuma aranar be neme niba har kwana uku sai ana hud'un yazomin da sha,awarsa nikuma nak'iya mukaita artabu yaringa tumurmushe Ni harda duka ina kaucewa har Allah yabani Sa,a yakawon wani mugun k'arfi Na angaxashi kan table aiko saiga jini a hannunsa amma bawan Allahn nan mugu saida ya mik'e yashak'o Ni yaringa duka aciki ina ihu har nafuta ahaiyacina bana gani Ashe suma nayi yazo zai tsallakeni kenan yaga jini tak'asana yana malala atsorace ya tab'ani yaga kamar namutu ya rud'e ya kinkimeni sai asibiti private aka bani taimakon gaggawa bayan Na dawo hayyacina Ashe wai b'ari nayi,aiko nai hamdala da Allah dacikin tsohon najadu ya xube shi kuma yasha takaicin jin yaxubar da gudan jininsa da hannunsa Wanda yake nema ido rufe be tab'a haihuwaba shekara da shekaru Auransa Na goma kenan Aiko yau yai nadamar dukan mata.

Koda naga nasami sauki ansallamo Ni ban tsaya jiran zuwansaba Na wuce kai tsaye gun "yan hisba da kukana nace inaso su taimakeni su raba Aurena da mijina yana cutata mugune,

Aka aika kiransa yaxo,suka ce nakoro bayanin abinda yakemin nafetse komai ban boyeba, suka tambayeshi hakane? Yana wuri2da ido irinna marasa gsky yace musu hakane saidai yana Neman Alfarma ya daina zai gyara atayashi bani hakuri yana sona kada ingujeshi(kuji ja,iri yaji mace me kwayayen haihuwa)😛😂

D'an hisba yatambayeni me nake buk'ata suimin ? Nace susakashi yabani takardata inason saki uku,d'an hisba yace,saidai inyi hkr domin hisba bata tab'a Aure sai gyarawa,inyi hkr tunda yace zai gyara ya daina nabishi inhar bai dainaba zasu d'aukarmin mataki akansa,

Kafin mutafi saiga kwamandon yn hisba dakansa dama bayanan mukaxo yana ganin Alh yace meya faru aka fad'a masa komai saiyace atsaya yai binciken Al,amarin tunda Ance Auran bashine Dan yasan Alh sosai yasanshi da Auri saki dakuma dukan mata farin sani,aranar wannan babban Dan hisba yasa aka dank'o inna dayake taga harda yn sanda aciki saitai wura wura tana tsoron masu kaki sosai aka sakata agaba akace tafad'i gaskiyar lamari akan Auranmu domin naxo nace yana min abinda addini bayaso

Anan inna Kulu ciki ya duri ruwa jin ance inbata fad'i gaskiyarba har aka gano awani gurin tota tabbatar zata k'are rayuwartane a kurkuku

Bashiri tace niba Yr ckn tabace Yr mijintace kuma tatsaneni sbd yanda yake fifita Ni akan yaranta Dan haka tasha alwashin sainasha wuyar rayuwa duk wani hali Dana shiga itace sanadi domin babu wani bashin fili data karb'a gun Alh had'in bakine kawai Dan Allah inyafe mata ita yanzu ta tuba tagane halin rayuwa kunjifa makira

Nan nahau kuka ina cewa inna kincuceni nace lallai baxan koma gidan Alh namadiba saidai yasakeni shima jikinsa yana b'ari ganin yn sanda sunyo kansa da ankwa yace inje ya sakeni amma kada sui masa komai ya tuba.

To sudai yn sanda hkr suka bani sukace baxasui masu komaiba domin duniya zata koyar dasu darasi Alhaki nama kad'ai zai ishe su zai zame musu ixinah nan gaba

~wannan kenan~

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*

*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 55-60*
Ashe inna tasaida gidan mahaifina niban saniba saboda Neman magungunan zainabu datake faman siya Ashe harda ciwon sanyi take fama dashi kuma wani zafin kan zafinma Munnir ya aiko mata da takardar saki har 3 gida,

Aranar Dana sanda zancen saida gidan muna zaune atsakar gida ina tsifar kaina inna kuma tanaiwa zainabu wankin kayanta(Allah sarki uwa kudubi dai abinda zainabun taimata a lokacin tana gdn munnir amma ta manta lallai tsakanin d'a da uwa sai Allah)
Sallama mukaji afokar gida wai megidan ya aiko agaya mana notice d'in daya bayar nasati d'aya yak'are don haka yana so agobe mutashi mu bashi gdnsa zai gyara yasaka yn haya

Tabbas nashiga halin firgici meyasa inna taimin haka domin bansan inda zan kamaba inhar nabar gidannan don nasan duk inda zataje bazata yarda tazauna daniba tunda ba k'aunata takeba inkuwa Yayan Babana naje gunsa nauyi zan d'ora masa tunda shima da d'ansa ya dogara gashi k'auyene can abin gutsuri tsoma baya k'adan baya yawa

Nasha kukana ad'aki tabbas inna zata had'u da azabar Allah domin tunda akwai  hakk'ina ck banyafe

Baccima aranar bansan zan iya yinsaba danna raba dare ido biyu inata tunanin mafita gashi banida kud'in daxanyi na motar zuwa garin mahaifiyata Nijar.

Washe gari ana sallar Asuba su inna suka sulale suka gudu bantashi saniba saida gari ya gama wayewa Nafito da kofin dazanje siyan koko makwabta saimukai kicib'us da Wanda yasai gida a zaure yace"yazo ya gaya mana yabamu awa biyu anjima masu yi masa dab'en k'asa da fulasta da fenti zasuzo Dan haka kada yadawo yatarar damu ackn gidansa,

Jikina asanyaye nakoma ckn gidan domin nafad'awa inna Saina tarar da d'akin wayam bakomi wato sungudu sunbarni natagayyara kenan,to ai akwai Allah nawuce d'akina ina kwalla Na had'o yn kayana Na k'ullesu a leda nayo waje bansan inda zan nufaba ga yunwa ackn Dan tara tayi  dama banci abincin dareba Na kwanta.

Nasha tafiya a k'asa kafin Na isa tasha nahango wata me abinci ckn wata babbar Rumfa Na nufi gunta nagaidata ta amsamin da sakin fuska nasan ta arxik'ice tana da fara,a danhaka saina gaya mata ina nmn alfarmar Dan Allah tabani wani aikin inringayi mata taringa biyana ko wanke2n ne saitace akwai meyi mata wanke-wanke saidai inringa kular mata da girki dakuma mik'awa customers abinci.

Na amince nace zanyi tasa wata yarinyarta tazubo min wainar shinkafa da nama nasami guri naci nasha ruwa tanunan Aikin daxan fara.

To tun daganan nazauna agurin haj. Karima takaini gidanta datake ck me d'akuna hudu 2 nata nawa 1 Na yarinyarta Rufkatu d'aya

Rufkatu kusan Sa,atace amma ita ba bahaushiya bace tanada kirki zamanmu da ita nafahinci hakan munyi sabo a "yan kwanakin danai dasu take gaya min hajiya akwai mutunci gata abin hannunta berufe mata idoba saidai tanada son kud'i Dan haka inzage inringa kawo mata kud'i ko hanyar daxata samesu nace kamar Yaya? Saitace duk namijin dayace mata yana sona yanakuma son muje kwanan gida to in amince domin innak'i zata iya korata sbd suna cafe mata kud'i kuma nima zan samu agunsu

Maganar ta gigitani ashe itama rufkatu hanyar datake bi take samu kenan kuma shiyasa hajiyar keji da ita ga wasu d'amammun kaya datake sakawa dukda ba wata kyakkyawa bace amma akwai k'ira

Nida Rufkatu ke zubawa customers abinci ko mik'a musu lemo insuna buk'ata anan Allah ya d'oramin k'addarar had'uwa da wani Alhaji *wada* Wanda tundaya ganni yaketa shishshigemin har Haj tagane nanta shiga murna Dan tasan Alh wada mekud'in gaskene zata samu ajikinsa

Basai hajiya tace rufkatu tabani kwancen kayan taba waidon nayi kasuwa agun Niko nakasa sakawa da hajiya taga zanmata turjiya saita kwashe nawa danazo dasu tak'ona bashiri nadowa saka Na Rufkatu Wanda suka kamamin jiki nima tun bana sakewa hardai nasaba ba kuma nan da nan sai idanuwan customers suka dawo kainaba sbd ganin bakuwar fuska me matsu ba duk Wanda yaxo siyan abinci saiyace nixan mik'a masa ckn Runfaba wasu sunsha barmin canjin sainake Tara abina aboye sbd inaso intara Na motar zuwa Nijar

  Ranar dabazan mantaba itace ranar da Alh wada yanemi danai masa Rakiya masaukinsa nikuma nak'iya aiko saiya sanarwa hjy wai yanason ta ara masa Ni kwana d'aya kawai zan masa,aifa hajjaju ba musu bare dataga rafar "yan dubu saitace inma kwana 2 zan masa ba matsala

Tasameni tacemin ga hanyar samu yaxo min kada nabujire domin Alh zai iya saimin mota dataga ban aminceba saitahau lallashina namma taga ba halin yarda saita harxuk'a tace inhar ban bishiba to walh saidai innemi gidan kwana ayau..Na tsorata ba shiri Na amince amma nakuduri aniyar ckn zarafinsa

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

Koda Alh wada yaxo muka tafi baizarce dani ko inaba sai wani babban hotel Na masu hannu da shumi, banji ko d'arba nafito ina takun yauk'i nabi bayansa Riga da wandone ajikina fakistan sai d'an mayafinsu oh,! A yaune ranar farko tashiga ta hotel kuma da namiji! Haka naita zancen zuci harya kaini d'akin daya kama room 20 Na zauna a gefen gado ina kissima irin tagayyarar da zan masa inhar yanemi yaketan rigar mutuncina to ashe haukana nake nashi shirin yafi nawa,

Domin lemo da ruwa ajiyemin agabana ya matsa da lallai saina sha lemon nikuma nak'i sai ruwan nakurb'a to Ashe acikin ruwan ma ya zuba kwayar datake kad'ar da hankalin mutum

Aiko dai jikina ya mace Na ringa hamma ba sassautawa ga wata muguwar sha,awa dake min zarya ajikina dishi-dishi nafara gani amma da abin ya ciyoni dakaina Na tashi nayi kan Alh dake baje akan gado yana jirana don yasan za,a rina dagashi sai gajeran wando haka nahau kanshi ina masa wasu wasanni bashi yakarb'i tayi yahau sarrafani son ransa ahaka Alh wada yayi abinda zai dani ya gama sai ckn dare nadawo hayyacina Na farka naganni kwance kusa dashi breast d'ina d'aya a bakinsa d'aya kuma a hannunsa yana murzawa

Nai saurin tureshi Dan takaici gashi dare yatsala yatashi yana murmushi yana kallona yana fad'in"gud girl!sweet girl!!honey girl!!!
 "Gaskiya Ruby kinfi Zuma zak'i bantab'ajin macen data yimin dad'in sha,aniba irinki baxan iya rabuwa dakeba, me kikeso nabaki fad'i ko meye gida? Ko mota? Kokuma....nai saurin katseshi da fad'in banason komi naka kacuceni walh banyafeba domin kaika gusarmin da hankali Dan ba,a hayyacina akai komaiba,

Ban fargaba ya busamin wata hoda bashiri Na fad'o kansa da wata muguwar sha,awa datafi tafarko shagaltuwa,

Tokunji mafarin Tarawa ta da d'a namiji ta hanyar daba Aure Wanda kuma tun daga nan naxama oganniya wajen b'adala da maxa Ammafa Alh wada shine silar faruwar komai domin hartakai kobeniba Ni nakan nemeshi ta hanyar wannan masifaffiyar hodar dake kad'ar da hankali donta kamani sosae adalilin farko ina masa turjiya amma daga baya sainafishi kwarewa a harkar intakaice muku labari wannan rabuwa da hajiya karima nataho hotel shine k'arshen ganina da ita,

Domin saidanai wata a ckn hotel d'in ko futa banayi sai dare mud'an futa shan iska ko siyayya amma shi yana futa yaje yayi abinda ya kawoshi don d'an kanone wata kwangila ce ta kawoshi kd,

Da mukai wata a hotel d'in yace zai koma kano amma baxai dadeba zai dawo yasaimin d'an gida madaidaici a sabon gari ,ya bud'en Account be dai barni da damuwar babuba,ya tafi tabbas Alh wada ya lalatani domin bayan tafiyarsa sha,awa taita ciwoni dakyar nake iya jurewa hardai yai sati yadawo gareni haka yaringa gurxata kamar matarsa,aranar inyaso yayi 2 rawul nima bana gajiya inaji insuna waya da matarsa yana rage murya tamkar munafiki dai saidaga baya nagane tsoronta yake da alama hamshak'iyace me zaman kanta a gidansa

Tofa takai takawo nakasa jurewa saida nafara bin wasu mazan ina rage zafi kafin yadawo inya yafi amma bana yadda inkawo kowa gdn saboda b'acin rana kada wataran yaimin zwn baxata,

Hakan dayaga Ni shiyasa tak'ara yarda dani Dari bisa Dari betab'a ganina da kowaba,aifa saiya dad'a buden bakin aljihunsa gaskiya ya jik'ani da nera amma shege shed'an saiya mantar dani zancen zuwa nijar gun dangin mahaifiyata

Naxama dai karuwar k'arfi dayaji akwai wani zuwa da Alh yayi saina bujuro masa da zancen yakamata mui Aure...huuu

Aifa saiyahau min fad'a daxance mui Aure yaushe muka had'in ko fahimtar juna bamu gama yiba wannan ai toxarcine shifa in nagaji dashi ingaya masa sai a rabu.

Na tsorata da lamarinsa dama magana sai cibi yazaama k'ari sainai gum da bakina, anyi haka da sati biyu yaxo yatarar mu wani yasaukeni ak'ofara gidan Knn nashiga bankula da zuwansa bama

Aiko aranar naga kalar kishinsa masifa kwando kwando harda kumfar baki tunda halin Dana koma yi kenan gara kawai arabu zai kwace gidansa shi bazai lamunci cin amanaba shibaici tawaba


To!🙄 tunda naji haka sainayi dabara da wuri Na nemi dillali nabashi takardar gida aka saida nakarb'i kud'a Na had'a da Wanda yake taramin abanki Na sake wani new account d'in nak'ara gaba

Inaso inje ga dangin mahaifiyata  amma Ni a sona nafison inje musu da mijina ko Wanda zan Aura atawa dabarar kenan

Rabuwata da Alh wada saita k'ara sawa Na waye sbd tarayya danake da gogaggun yn bariki banyi gigin siyan matsuguni ba sai gidan haya Dana kama me dauke da d'auke da d'akunan mata "yan bariki Irina Wanda *ZAMAN MARINA*  Ya had'amu tare zaman kaxo naxo zamanhad'akar halayya mabambamta

Azamana daku nagoge Na waye sannan naji dad'in tarayyata daku tunda gashi ta dalilin d'ayarmu munsamu shiriya ta hanyar ya shehi Wanda kuma mukewa Allah godiya daya ganar damu gaskiya abinda muke ba abune mekyauba,saidai fatan zunubanmu Allah ya yafe mana

 Dukkansu suka amsa da Amin,

Zubaida tace" gaskiya Aunty Ruby kinga taskun rayuwa dukda nima naganta amma Ni ta dalilin mahaifina ne sab'anin matar ubace....Aysha simoli tace"sister Zuby nak'agara naji naki kema Dan Allah kifara muji

Murmushi zubaida tayi tace"yanzu kuwa Auta....

 ~muje zuwa~

*masu karatu mu Tara a page nagaba don jin labarin gwagwarmayar rayuwar zuby*

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

 *4rm*~NabilancyLuv~ ®

_wannan page din nasadaukar dashi ne gareku k'awayen Arxik'i da yayyena da duk wata masoyiyar wannan novel din nawa musamman_....
*Aunty Dj Mmn muhibba dorayi*
*Mmn twins*
*Ummu Affan*
*Ummi Hambali*
*Aisha uwar muminai*
*Larkin*
*sis Nafi Anka*
*Asea Fulanin daji*
*Pharty B.B*


 ~LABARIN ZUBAIDA~


*page 65-70*
Ni Zubaida haifaffiyar kano ce mahaifina Alhaji Alkassim Babban d'an kasuwane sannan d'an siyasa ne domin yana kan matsayin d'an takarar d'an majalisa ya Auri mahaifiyata Haj Umma ata biyu domin uwar gidansa Haj.Rakiya sun dad'e tare Allah be basu haihuwaba sai akan mahaifiyata ne watanta Tara daidai  tahaifo masa santalelen d'a mekama dashi aiko murna kamar me yaringa kyautar kujerar makka saniya ya turke ranar suna aka yanka ga raguna aka rad'a wa jariri sunansa Alkassim sai ummana tace aringa cemasa junior aiko duk inda ya zauna saiyai zancen magaji da rai junior dinsa me kama dashi wannan gigin daso da yake nunawa junior shiyaja akai silar rabashi da gidan ubansa

 Haj Rakiya ak'ule take kullum da wannan haihuwa Dan sau D'aya ta tab,a d'aukar sama  to bazama takeba kullum in dadyna ya fita itama tana hanyar waje itada shak'ikiyar kawarta hajiya Murja  wacce take sata a muguwar hanya

Aranar da abun ya faru bak'uwa Ummana tayi me hijab har k'asa tasa nik'ab da safa, ummana ta karb'eta hannu bibbiyu takawo mata kayan motsa baki sannan ta bata jariri dayake anyi suna da kwana ukune k'afa bata d'aukeba wad'anda basu sami damar xuwa sunaba suke taxuwar mata barka to haka wannan bak'uwa tace da ummana itace matar abokin dady Alh Salmanu todake Umma tana jinsa abakin dady kuma betab'a kaisu gidanba shiyasa bata santaba

Aiko sun d'an tab'a hira Umma ta mik'e tace mata tana zuwa tai ckn d'aki domin tasanarwa da dadyna zuwan matar abokinsa aiko dai mace naganin shigar Umma d'aki saita gudu da jariri kuma dama aranar me gadi yaje gida kwanansa 1 agarinsu an aiko matarsa ba lfy yatafi da niyyar zaiyi kwana 2 ya dawo

Haka ta zille ba Wanda ya ganta dayake da mota taxo wani yana driving d'inta ga layin tsit Na masu hannu da shuni GRA ba hayaniya

Umma tanacan tana bugawa dady waya har 2missed call be d'agaba suna meeting ta hkr dai takyale tasan zai kira after tana dawowa falo taga wayam ba baku'wa ba jaririnta jikinta yad'au rawa ta rafka salati tai waje ta ringa lek'a ko ina batagan taba itace har waje ba gyale ga hajiya Rakiya bata nan taje k'auyensu tun washe garin suna gaba me gadi balle tasami yn tayin jimami,aguje jikinta Na b'ari takoma d'akin tatarar dady yana kiranta da kuka ta daga wayarsa tasanar ms komai

Wai!ai dady yafita yafita diriricewa ya kid'ime harda fad'uwa dakyar ya iya fad'a musu abinda ke faruwa aiko direct sukai station wasu kuma sukai gidajen redio Dan bada sanarwar sukansu abokan nasa akid'ime suka

Aiko aranar yn sanda sunyi kamen mata masu nik'ab kamar me

Duk wacce Umma tagani saitaga ba itabace

Asalima dady yafad'a mata cewa shifa matar abokinsa bata k'asar domin tunkafin ayi sunan junior suka tafi k'asa metsarki itada mijinta Alh salmanun

Tabbas ummana tashiga tashin hankali Mara misaltuwa har a asibiti takwanta jinyar dole

Haj Rakiya data dawo harda kuka tamkar ita tahaifa mata (munafuka🙄)

Har addu,a aka ringayi a masallatai da makarantun islamiyyoyi anyi wata biyu shiru babu labarin dawowar junior haka dady yasa dangana aransa ummana kuwa saida aka had'a dayi mata rubutun danganar arai don ba uuhhm ba a,a kullum shiru da ita dama macece me hak'urin gaske batada magana watanta biyar tasami cikina Wanda yaxo mata da laulayi akasin Na Junior data sameshi a sadaka


Aiko dady yace wannan karan ba,a Nigeria zata haihuba ak'asa me tsarki zata haihu har renon ckn ma
 
Da Haj Rakiya taji bak'aramin haushin hakan tajiba don tasha alwashin sabauta cikin tunkafin ma yaxo duniya balle aimata giggiwa taji takaici

Saitacewa dady yakamata yai biza da ita tabi Yr uwarta ta kula da ita

Kamar dadyna yasan kudurinta saiyace a,a akwai  Wanda zasu kula da ita sosai ba matsala yanada kuma abokan arxiki kada ta damu ya gode

Tun cikin yana wata biyu akai tafiyar itada dady can yabarota yahad'ata da matar abokinsa Janan suna k'awance

Kafin ta haihu yakoma sau d'aya yaganota abubuwa suna tafiya dai dai yaji dad'in haka ya dire mata kud'ad'a yadawo gida Nigeria

Dady yanason ummana sbd irin biyayyar da take masa ko uwar gidansa Albarka

Gashi kuma marainiyace yayanta ne kad'ai ya rage mata a bauchi yke da Aure itama Yr can ce fulanine su

Da lokacin haihuwa yaxo kamar dady yasani ya dira a k'asa me tsarki aiko aranar da asuba tahaihu ta haifeni kwabo da kwabo nida ita kyakkyawace amma kyauna ya zarce nata Albarkacin ni ak'asa me tsarki aka haifoni 😂 itako agarin waina (masar bauchi 😛😉)

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 70-75*
Dady ya rad'amin suna Zubaida, sunan  yayar sane data rasu Aiko dai naga tsantsar *SO* da kulawa gun dadyna nasha kaya masu tsada kafin yabaro ummana ya dawo Nigeria domin yace baxata taho gida da jaririyar "yarsa azo adad'a sace masa ita ba ta ta zauna harsaina shekara ta dawo ba haka Umma tasoba don tayi kewar gida ba yanda ta iya dole ta hkr

Jaanan matar abokin dady tanasona ganin irin kyan da Allah yabani ko " yayanta dasuke larabawa Albarka jininmu ya had'u sun shak'u da Umma sosai gidansu Na kusa da gida

 Kafin Na ck shekara a k'asa me tsarki zuwan dadyna 2 ganina duk zuwa kuwa da tsarabar queen zubynsa haka yk gayamin Umma kuma tanacemin sister sbd kara haka inxai tafi tamkar ya tafi tani

Da shekara taxagayo dady yazo tafiya da Umma sunji ba dad'i itada jaanan saboda shakuwa dady yace kada su damu zai ringa kawo Umma tai ibada tai musu zumunci haka aka rabu badan ansoba

Dady yabaiwa Ummata mamaki domin kai tsaye ya wuce da ita gidan daya tamfatsa mata a kundila,

Aiko tayi murna taji dad'i domin gida yai kyau ga "yan aikinta dame gadi awashe garin da suka dawo aka had'amin partyn birthday Na one year Ashe dady yai gayya sosai harda buga kati ya raba kafin mudawo  umma sai ganin mutane taringayi kota ina ancika gida duk wani abin motsa baki kuwa yabada kwangila anyi ankawo kayan rabo kuwa gasunan lodi-lodi ga hotunan kalandu da memo da sitikar key holder dasu manyan robobi abin sai Wanda yaje gun yagano yakashe kud'i sosai tamkar haihuwar fari Umma taimasa

Zakusa mamakin irin halin da hajiy Rakiya tashiga domin bata b'oye masa bak'in cikin taba k'iri k'iri tanuna masa ita bazataje wani partyn birthday ba saboda be d'auketa da muhimmanciba ai baya shawara da ita in xaiyi Abu,

Saijin dawowar Umma tayi begaya mataba haka data haihu saidatai kwana 2 yagaya mata gashi yagina mata gidan dayafi Wanda take ciki kyau wannan duk ba adalci bane domin da ita gdn ya dace tunda itace uwar gida kodon yaga bata haihuwa shiyasa zai ringa wulak'antata

 Toshidai dady be biye mataba sbd yana ckn murnar dawowar abun sonsa amma zuciya yakai nesa sbd tasanshi yanada zafi akwai fad'a saidai yanada saurin sauka

Aranar party anci ansha anshoshali da matan dady da abokansa a farfajiyar gidan Wanda anan wani abokin dadyn yake ce masa gaskiya yana yiwa d'ansa kamu inhar Na girma yana Neman Alfarma da,a had'a Aurenmu domin su k'ara k'arfafa dank'on Zumunci

Dady ya amince masa babu ja,ganin yanda suke da Alh Tahir kuma matarsa hajiya Zeenah  k'awar hajiya Rakiya ce

Ranar daikam nasha kyau anyimin kwalliyar da kowa yakalleni tamkar alasheni Dan had'uwa gashi ina tafiyata ko ina inada gabb'an jiki Yr duma duma dani Umma tasami kyaututtukan kaya sosai da kud'ad'e  atamfofi da lesika da kayan babies tamkar a kasuwar kwari

Wannan abin arxik'i da akaiwa ummana saiya k'ara harxuk'ara Haj Rky suka baxama gun hatsabibin bokansu yai aiki akan Umma aka haukatar ta ba,a barta a gidaba saida aka tabbatar annemeta anrasa tashiga duniya da rashin lfy ta fara sai mafarkai da iho iho da buge buge dady yai zaton zafin zazzab'ine ko mutanen b'oye tosai daga baya yagano haukane tuburan yashiga damuwa kuwa har rama yayi bashida lokaci sai nata aka kaita asibitin mahaukata tafi wata biyu acan daga baya aka dawo da ita gida matar Wanda Yaya Nafi,u ta dad'e agunta tana lura da ita saida ta tafi adaren tabi daji ta sulale megadinta be fargaba aiko dady harda suma yashiga tashin tashin hankali sosai fiye da b'atan junior shima saida aka ringa masa addu,o,i kana ya dawo hankalinsa

Tofa sai rik'ona ya dawo hannun Haj.Rky wacce ta ringa azabtar dani amma in dady yana nan bata nunan komai sai kulawa da tattali saima inyai tafiya seminar wani garin kafin ya dawo har rama nake abinci bata bani Na arxik'i saidai in me aikinta ta faki idonta ma ta bani amma nida gidan ubana befi inci sau 1 ko biyuba

Inko ya dawo baya iya shiru saiya tambayeta ya yaga Na rame haka? Saitace ai kasanta da kwawar ka may be kai take tunawa intaga bakanan hr kuka take tana ambaton dadynta saifa nai aikin rarrashi take hkr ai wannan soyayyar taku sai Allah

Kunji makira haka ko yake yarda dady yana nunan soyayya k'iri2 zai shigo da abubuwa nawa naci kona kwalliya amma bana hajiya hakanne kuwa ya k'ara saka tsanata aranta har a kullum take mugun cin alwashi akaina...


*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 75-80*
"Yar Aikin Ummana tun Asali itace taxama Yr aikin Haj Rky shiyasa take tausayamin ko sch za,a kaini itake shiryani takan sakamin biscuits ajakata driver yakaini babbar makarnta dady yakasakani Nigerian Torkish Wanda Haj taso acireni amaidani ta gwamnati yace bazai yiwuba duk kudinsa ai sai a zageni cemasa take banida kokari data fad'i haka kuwa saiya kawo min memin lesson agida Dan kwakwalwa ta bud'e

Naxama Yr tsakar gida in huwaila me aiki batanan ko kukan jini zanyi hajiya naxaune baxata tankaba saima inna isheta zata kwadeni kota kaimin mangara duka duka ko shekara biyar ban rufaba nagane matsayina agidan  mu

In Hjy Murja taxo suka fuce sai dare kosu k'ule ad'aka ana k'ulla tsiya

Huwaila nabani duk wata kulawa baxab manta da itaba har goyani tasha yi agadon bayanta inyi bacci takwantarni

Hjy saita canza taku rana d'aya naga dadyna ya canxamin ko dawowa yai becika nemanaba bakin aljihunsa ya bud'ewa hajy sosai yake shak'a mata nera adalilin ganin yadda take min Na kashemin kudi da lelena agabansa komai takawo in yana nan saitace nawane amma fa bata bani kullum ckn yi mata godiya yk ta rik'e masa amanata

In yananan fa har jana take ajikinsa ta d'orani acinya ai tashafamin bayana ana lallab'ani inko bayanan taita hanb'arata kenan ana angaxani ina gwaruwa da kujerar falon

Kud'in datake samu gunsa shi ake shak'awa bokansu yanai musu aiki kan Alhajin don burin ta a kullum shine taga Na dauwama a bkn ciki tasha alwashin indai tana raye baxan kad'aita a frn ckiba domin tsanar da takewa Umma tane tun asali yadawo kaina

Motar da Hjy take ja harta kere ta dady yana d'an majalisa gidan da ummana ta zauna kafin ta b'ace shiya barmata kyauta (to kuma dagaji aikunsan ba hk akabar shiba)

Sannu sannu kwana nesa alokacin danakai munxalin budurwa nagama karatun sec sch d'ina a torkish nasami ilimi mekyau tundaga pre-nur nafarata harna gama inada k'okari sosai duk wata gasa da ake futa dani aka ringa futarta haka Dana gama nasamu kyaututtuka a sch d'in ta yara masu haxak'a naso inci gaba da karatuna sbd k'udirin dady Na kenan a kullum amma ada kenan kfn ya canzamin amma a lkcn Dana gama sai Hjy tace ita Sam bata yarda naci gaba da krt ba tagaji da ganina a ckn gidan muna had'a kafad'a gara yaimin Aure

Toni kuma saurayina d'aya ne Me suna Aliyu zuwansa d'aya guna najishi shiru besake zuwaba bansan daliliba amma naso aliyu alokacin d'an talakawane saidai kyakykyawane ajin k'arshe gashi da kyan k'ira majiyin k'arfi saidai bashida aikin yi sai noma yai karatun Aikin ya gagara samu dakyar ya kammala Yr diplomarsa a management

Mahaifina yasameni da mgnr lallai lallai yabani wata guda nafito da miji zaimin Aure

Narasa yadda zanyi bana saurarar kowa Aliyuma da nacinsa daya dameni inna futo islamiyya a hanya yaganni nai ms kwatance yaxo sau d'aya ya d'auke k'afa Dan haka narasa mafita gashi niba k'awar arxikiba balle tabani shawara bana kawaye Hjy ta hana nakawo mata kowa gida

Saikawai Na yanke shawar zanje insami Aliyu a gonarsu naji dalilin d'auke kafarsa dayai shin ko dama basona yakeba?

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

 *4rm*~NabilancyLuv~®

*page 80-85*
Tun dana kusan isa gonar naji gabana yana fad'uwa anya zan iya kuwa? Wai yau nice da biyo namiji bama shixai biniba


Tundaga nesa Na hango Aliyu aduke yana nomansa tuburan baya tsayawa sai sharce gumin fuskarsa yake Na nemi wata Yr darbejiya makusanciya dashi Na jingina INA kallonsa Tabbas Aliyu Haidar Namijine Wanda yaci ace office ne dashi Na zaman kansa tabbas talauci baiyiba Aliyu kyakkyawane daka ganshi kasan yana wahala ga wasu kwanji a hannayensa kamar ance ya d'ago yako d'ago ya sauke manyan sexy eyes d'insa akaina

Nan danan yai wulli da fatanyar ya taho guna saida ya iso kusa dani sannan ya dara yace"kai! wanake gani kamar Zubaida?

Nayi murmushi nace"nice Aliyu kayi mamaki ko?

Yace'sosaima kuwa dafatan lfy ?

Nace"to lfy ba lafiya ba

Yaxaro ido da sauri  yace"meya faru?
Nai k'asa da kaina hawaye ya taru a idona nace"Aliyu ban zaci zaka gujeni lokaci gudaba bansan mena makaba dg zuwa d'aya ka d'auke k'afarka gareni alokacin da Allah ya jarrabeni da k'aunarka ka gujemin asakamakon nikuma bana kula kowane saurayi mahaifina ya matsan tamin ahalin yanzu danake ck akan dole nafito da miji ya bani wata guda Aure zaimin... tagumi Aliyu yyi kana yace"hhhmmm Zubaida nasan bakisan abinda ya faruba domin dakin sani tabbas nasan da baxakice naguje kiba

Na d'ago dakaina Na kalleshi nace"meya faru dakai Aliyu?

Yace"aranar dana fara zuwa gidanku muka fuskanci juna dake bayan munrabu nafito daga ckn gidanku Knn saiga mahaifiyarki a mota ta dawo itada wata a ck ta tsaidani taimin tambaya gunwa naxo? Nafad'a mata gunki naxo kuma yauna fara zuwa kuma da Aure nake sonki anan taimin yn tambayoyi wace sana,ar nakeyi kuma wane k'usane ubana,?

Nagaya mata ubana ba kowa bane a kano sai manomi haka nima banda aiki sai noma amma ina Neman Aikinyi nayi karatu

Intak'aice mk Zubaida kaca-kaca hajiyarki taimin tace kada ta k'ara ganina a gidanta niba Sa,ar Auren Yr d'an majalisa bace inko nasake kawo k'afata gdn to xan kwashi kashina a hannu kotasa a d'aureni d'aurin dindin

Natsorata sosai nima kaina saidaga baya naiwa kaina fad'a Na zuwa gunki batareda yin naxarin ruwa ba Sa,an kwando bane,nasan kuma inhar naci gaba da zuwa gunki duk abinda akaimin Ni najawa kaina donko d'aurin akaimin bame belina

Ko mahaifana bansanarwa gudun kada sumin fad'a tunda kowa yaji ma dariya za,ai min aimin Allah y k'ara

Tokinji abinda yaimin tsaiko da zuwa gunki Zubaida Amma inbanda haka Allah yasani ina sonki *So* Na hak'ik'a Dan haka kinga hak'uri da juna yaxame mana dole

Nakalli Aliyu ido ckn ido nace dashi'Aliyu baxan iya hak'ura dakai ba tunda har mahaifina yace Na futo da miji toni kaina zab'a amatsayin Mijin daxan iya xaman Aure dashi Dan haka inhar kana sona da gaske hanya abud'e take daka dawo gareni domin ka gabatar dakanka ga dadyna...ya katseni da sauri "kina ganin zai amince ki Auri talaka Zubaida? Nace" haba Aliyu da talaka dame Arxik'i duk d'aya suke gun ubangijinmu kama dena wannan tunanin tunda dai yace nafito da miji ai matsala ta takau inyaganka amatsayin mijina Aliyu kuma wannan da kake maganr tai maka wulak'anci kada kasa abin aranka matar ubana ce ba ita ta haifenba komai me wucewane.

Ya gyad'a kansa yace"hakane Zubaida Na aminta insha Allahu zaki ganni gobe insha Allahu, Allah ya wuce mana gaba,nace masa amin, nai masa sallama nakoma gida.

Munyi haka da kwana 1 saiga Aliyu da yamma yasha wankan shadda yai kyau bame cewa dg gidan talakawa ya fito hargun dady nakaishi suka gaisa dady yai Na,am dashi yace masa ya saurareshi zai masa mgn

Hakama Hjy nai mamaki tasaki jiki sungaisa dashi da fara,arta (Ashe hajiya murjace tabata shawarar gara ta yarda Na Auri talaka tayanda zankasance ckn k'unci inko me kud'i Na Aura zan walwala son raina

Akwai ranar da Hjy murjar taxo gidan suka k'ule ad'aki suna yn maganganu nikuma naxo wucewa najisu suna shewa ana tafawa hajy Rky naji tana fad'in "hakan da kikace k'awata za,ayi shine mafuta gareni narasa yadda zanyi da wannan yrny walh natsani dana bud'i inganta a ckn gidan kinga tun farko nagayawa boka itama a hauka tarta kmr yadda aka haukatar da uwar ta amma boka yace innai hk za,a iya zargina saidai mucanza tsari..." Ai walh dakin sani da baki biye masaba saiki canza gurin zuwa yo bokaye da yawa bakiga jaririn Dana sace yadda akai dashiba d'an uwan nata aibokan Dana fara zuwa gunsa k'inyin aikin yayi wai za,a iya haukacewa daga baya koni koshi inhar aka yanda yaron aka had'a jinin da maganin aka bawa Alhaji yasha a sob'o to yanzu bagashiba tsit kakeji aikawai yanzu yanda nace miki haka za,ai

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 85-90*
Wannan zance danaji daga garesu ya kid'ima ni lallai hajiya shed'aniya ce ta k'arshe Ashe dama itace silar b'acewar d'an uwana da naji ana fad'a tun yana jariri? Kuma itace ta haukatar da ummana? Allah sarki ummata ko tana ina ko awane hali take Dan,uwana kuwa andad'e da rabashi da duniyar Ashe

Tabbas makomar wad'annan bayin Allah itace wuta zasu gamu da Allah aranar da basuda tsumi basuda dabara iyawarsu baxata musu komaiba

Asanyaye nawuce d'akina Dan banaso sugannima balle Susan cewar najisu

Aranar nakasa aiwatar da komai kukan zuci kawai nake narasa waxan fad'awa wannan magana da naji domin ban isa Na tunkari dady da wannan k'azamin zancenba Dan bazai tab'a yarda daniba tunda Hjy tai masa rufin baki sai yadda tai dashi ko danginsa baya iya tsinana musu komai hajy ta takan Kane koina da komai nasa baya iya zardar da komai saida ixininta ko gidan basa zuwa domin cin mutuncin su take intaga kafarsu agidan,dama iyayansa basa raye "yan uwansa mata uku suka rage aduniya da suke ck d'aya kowacce tana gidan miji kuma suna da rufin asiri sun had'e kansu basa tunkararsa duk basusan asiri tai masaba sun zaci baya ya juya musu ganin ya zama wani shiyasa suma sukai zuciya dashi da iyalansa

Inata nuk'u nuk'u da wannan zance harsaida naga Hjy batanan nakeb'e da huwaila Na zayyane mata komai danaji daga bakinsu Hjy aiko itama ta girgixa dukda tasan irin makircin da suke k'ullawa amma batai xatan Hjy ce ta haukatar da ummaba huwaila tabani shawara da kada nafad'awa kowa wannan zancen kawai Na ringa yiwa mahaifiyata addu,a a kullum shi yafi


Haka ko akai saina dage a duk sallata ina sakawa da ummana akan Allah yakareta aduk inda take yasa tana hannu nagari Allah kuma yabata lfy

Soyayya tsakanina da Aliyu Haidar ta kankama domin kullum muna tare kuma har sitting room nake shigar dashi munshak'u da Aliyu sosai kullum yana jiran yaji kira daga dadyna tunda yace ya saurareshi yabashi lokaci daya gama bincike akansa zaiyi masa mgn ya turo magabatansa ayi maganar Aure

Mun D'ebi sama da wata uku muna shek'e soyayyarmu me dad'i domin Aliyu gwanine wajen iya Luv dumu dumu mun jik'u da siyayyar juna saikawai dady ya kawo mana tsaiko tahanyar gayamin cewa ingayawa Aliyu yadakata da xuwa guna domin d'an Amininsa xaibawa Ni

Tabdijan! Walh nashiga tashin hankali mara misaltuwa domin kullum kuka nake yi hr rama nayi Aliyu kansa saida ya gane hkn amma nakasa gaya masa harsaida dadyn yasameshi da kansa ya gaya masa yaimin miji ya Dakata da zuwa guna ya dad'a jaddada masa cewar yauce rana ta k'arshe daya bashi ta zuwa guna kada ya sake ganin kafarsa ckn gdn

 Halin da Aliyu yashiga baxai fad'uba awannan ranar domin idonsama dayake fari tas saida ya rikid'e yakoma jajir sbd b'acin rai yacemin"tun farko abinda Na guda kenan Zuby amma sonki ya rufen idona k'aunarki ta toshen kunnena domin mutane sunsha cemin dama haukana nake akanki Yr manya sai d'an manya gashi kuwa nagani kiyi insha Allahu Zubaida daga yau nabarki kenan insha Allahu gara naje Na nemi Sa,ar Aurena dama tunda naga dadynki ya jamin lokaci gameda binciken da baifi yayi shi ckn sati gudaba nasan da wata ak'asa ba komai Allah ys hakan yaxame mana Alheri nagode da soyayyarki gareni nasan kinsoni banida komai haka nima baxan dena k'aunar kiba hr inkoma ga mahaliccina natafi sai wata rana...
Haka muka rabu da Aliyu awannan rana ina kuka ina kallonsa ya fita daga gidanmu haryar bamu sake had'uwa

Soyayyar Aliyu dake raina ita ta hana min naso Wanda dady suka lik'amin wato barista kamal yaro matashi metashen samun nera dukda iyayensa sunada kud'i baya dogara da nasu domin Aikinsa yake yana samu aturai yai karatu yai soyayya ta sheke aya da "yammata kala kala tun daga turai har a kano amma har a lokacin had'uwar yace bega matar dayake jin zai iya zai sota har azuciyarsaba koda ya fara zuwa guna ranar farko da muka kasance dashi a d'akin saukar bak'i raina ya b'aci dashi aranar domin duk zancensa 1 saiya shafamin gefen fuskata wai jikina laushi lallai xa,a huta,babu xancen wata k'aunata data futo abakinsa sai sha,awata dayake ko sakin fuska begani daga gareniba haka muka rabu dashi ya diren mak'udan kud'i yatafi nad'auka nakaiwa Hjy aiko harda murnarta tana 'fad'in kin gani ko me baka yafi me karb'a ai dadynki yai miki gata amma me ake da talaka Na xunbura baki nace" gaskiya Hjy tarbiyyarsa bataiminba duk maganarfa daxaimin saiya shafani nitalakan yafiyemin shi d'ari bisa d'ari Dan kud'insa basa gabana.

Takaimin duka"Dan ubanki saikije ki d'aurawa kanki Aure da talakan harxaki iya kallon idona ki fad'an haka, barista kamal nitsattsen yaro zakiyiwa sharri tokisani bakida miji saishi koma me yaimiki ai Dan yana sonkine Dan haka kema ki xage kinuna masa soyayya danki janyo akalarsa kanki sbd akwai "yammatan dasuka fiki komai dasuke sonsa ya tsallakesu yataho gunki Dan yai biyayya Dan haka kema dole kiyi.


(Kunjifa sbd ba Yr ckn ta bace)

_muje zuwa_

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm* ~NabilancyLuv~

*page 90-95*
Harga Allah maganar Hjy bata karb'u azuciyataba domin zan Auri barista ne kawai domin nayi biyayya ga mahaifina kuma nabar gaban Hjy Na huta tunda ko ba komai Aure yana da "yanci ga d'iya mace

Hajiya Zeenah mahaifiyar barista kamal hamshak'iyar macece ishashshiya agidan Alh Tahir Wanda sai abinda tace akeyi agidan _business woman_ce tana sare saren kaya a k'asasen Dubai irinsu Dubai da Cairo da igypt da dai sauran k'asashen k'etare tanada manyan shaguna a Dubai nantafi yawan zuwa dukda dukda mijinta me kud'i ne d'an siyasa amma ta kereshi a Arxik'i

D'an su d'aya tal a duniya *kamal* Wanda Allah yabasu ko b'ari bata sakeyiba abayansa sunbaiwa kamal kulawa da gata sosae kafin yakawo k'arfi domin kuwa duk abinda zaiyi Na ashsha basa kwab'arsa

kome zai jajibo Na d'aukar magana basa masa fad'a yasha yiwa yaran mata ciki a Unguwa amma basa goyan baya su yarda shiyayi saima suci xarafin dangin yarinya dole tasa kome zaiyi awaje Na bad'ala ba,a iya zuwa a tunkari iyayansa da mgnr don ansan cn xarafine zai biyo baya


Wannan hali nasa shiya kaishi hr girmansa koda yaje karatu wajema haka yaita aikata masha,a da ymmata saidai bayashan giya kuma Allah yataimaka musu ya tsaya yai karatu domin yanada kafin basira koda ya k'are karatun sunso rik'eshi yai Aiki dasu amma iyayansa sukak'i amince masa don sunfi son kasancewarsa a kusa dasu


Yana dawowa Nigeria yafara Aiki a wani babban kotu yana samun salary ma tsoka da mahaifinsa yaxo masa da xancen yai masa mata beyi ja dashiba domin yasan baxa aimasa xab"en tumun dareba don sunsan halinsa da son mace mekyau bashida niyyar yai Aure da wuri yafison saiya dad'a rik'a amma bemusa musuba sbd duk iskancinsa yabaiwa iyayensa biyayya dukda suna ji dashi d'in.

Akwai wani zuwa dayai guna yana sitting room yaimin waya yasanar cewa infito gashi yaxo

Sainai masa k'aryar banda lfy baxan iya fitowaba yatafi kawai ya sake dawowa

Ashe betafin ba yasanarwa Hjy yanda mukai saikawai tabashi umarni dayaxo hr d'akina yadubani ta nuna masa

Aiko ina kwance dagani sai "yar yaloluwar shima me shara-shara ko bra babu ajikina sai 3kwata danasa me kama jiki, Na baje agado idona arufe saijin shigowarsa kawai nayi kafin nai magana harya shigo tsakiyar d'akin ya d'aga masa hannu da sauri nace" Dakata anan mallam waya baka ixinin shigomin d'akin ba _nokin_ ba sallama aiko kai ba musulmi bane ka tsaya daga k'ofa Na gyara ko inbaka ixini ko?

 Murmushi Yy kana yace" nida matata sai Na tsaya anbani ixini mexaki b'oyemin alhalin nixan mallaki komai kada ki damu ninakine...kfn nai magana saijinsa nai akaina Yakama leb'ena yana tsotsa.

Da k'arfi Na angaxashi ya tashi ya dank'oni ya mannani a k'irjinsa hannunsa biyu a kan k'irjina yana matsawa da k'arfinsa aibansan lokacin da zuciya taciyoniba Na wanka masa mari bashiri ya sakeni ya rik'e kuncinsa yana kallona a k'ufule ya nuna niyana fad'in "Ni kika Mara akan Na tab'a jikinki?

Nace" anmareka d'in banxa d'an iska dabaisan mutuncin kansaba...'ke! _Don,t shouted me again_  tunda nake babu wani hannu daya tab'a marina aduniya sai naki sbd naxo taimakonki tokisani kisa wannan aranki saikinyi nadamar abinda kk yimin walh! Saikinyi kuka da idanunki


Yana kaiwa nan yafice axuciye Hjy bataga futar saba nikuma yabarni da tunanin shin meyake nufi da fad'in hakan? Wulakantani zaiyi kenan inya Aureni ? To inma zai sakoni bayan munyi Auren aini gaba ta kaini sai insamu in Auri masoyina daga baya,kuma dole su dady su amince


Anawa tunaninfa Knn, amma Ashe ba haka ne k'udirin kamal ba

A satin aka tsaida ranar Auranmu wata 2 shiru shiru Aliyu bexoba saiji nayi dady yazomin da wata babbar magana wai Aliyu zaije Dubai duba wasu kayan mahaifiyarsa yace yanaso inbishi domin muhad'o kayan lefena a can kuma zai d'auki satittika inmunje.

Tab! Ban b'oyewa dadyba nace "baxan bishiba yaje shikad'ai tunda addini beyarda da hakanba,aiko mari dady ya kwad'amin yace xan nuna masa sani sanin addini ne inhar nak'i binsa to innemi wani uban bashiba

Hajiya taringa xuga dady akan dole saina bishi badan raina yasoba kuwa aka shirya tafiya Dubai dani


Aranar da xamu tafin hajiyace ta tayani had'a kayana a d'an k'ara min akwati Ita harda min Rakiya bakin motar kamal dayaxo d'aukana zuwa filin jirgi da driver a gefe shikuma sai cika yake yana batsewa tamkar wani mijina


*Nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

_Assalamu_ _Alaikum_ _xan d'anyi_ _tsokaci akan page 90-95_ _asakamakon_  _matsalar typing Dana_ _samu guri 2_ _amaimakon_ _asa kamal_ _saikuga Aliyu to agarfarceni_ _kada aji ba dad'i domin nima_ _saida nakammala da type nayi send_ _nagani Dan haka_ _dafatan_ inkungani_zaku  _fahimta_ _nagode_

*sak'on gaisuwata gareku k'awayen arxik'i H. Mmn Aleesha da Takwarata Nabila Mmn Khalil*


*page 95-100*
Axatona tashar jirgin sama zamu nufa sainaga akasin haka drivern ya saukemu a wani babban hotel dafarko gabana ya fad'i jin yacewa drivern gobe 11:00am ya dawo ya d'aukemu yakaimu Air port d'in lallai kamal wato 24hours xamui acikin hotal d'in Knn domin alokacin sha d'ayan tayi

Abaya naringa binsa ahankali nake tfy tamkar wacce kwai yafashewa ack janye da d'an akwatina a hannu shikuma saitakun k'asaita yake shima travelling back ne a hannunsa ya tsaya a reception  ina gefe inata kalle kallena harya gama dasu yaxo ya wuce tagabana ba magana nabishi zagwai zagwai a room 10 ya tsaya yasa key ya bud'e yashiga nabishi ck

 d'akine room nd falo k'aton gadone sai three siter a gefe guda ga wani d'an k'aramin furji sai toilet k'arami da kayan kallon da A.C a d'akin

Ya shige Ckn d'akin nikuma naja tunga anan falon naxube akan kujerar tareda ajiye a kwatin a gefe

Ya futo ya fita jim kad'an ya dawo da lemuka Na kwalli da Leda ahannunsa ya saka ruwa afirjin ya diren lemon da k'unshin nama agaban beyi min mgn ba hakanima ko kallonsa banyiba ya kunna TV *Arewa 24* Allah yataimakeni suna yin film d'in danakeso *kyautata Rayuwa*fassarar hausane aiko nan nabada hankalina ina kallon

Yana daga d'akin shi abinsa har wajen biyu befutoba da alama bacci yk naji shi shiru,

Saida nai sallah kana naxo Na bud'e ledar k'unshin naman nahauci nagama nasha lemon

Nakwanta akan doguwar kujerar sai bacci bani natashiba sai la,asar natashi nai sallah naci gaba da kallona alokacin kuma suna maimaicin shirin *dad'in kowa* dukda nakalla amma tunda banida abinyi haka na d'an kishingid'a ina kallon amma kuma hankalina yana ckn d'akin ina tunanin shinko ya fito yai azahar ga La,asar tayi

Sai biyar da kwata najishi a toilet dake tsakiyar d'akin banluraba Ashe yafito yashige

Nai tsaki araina nace Allah ya wadaran naka ya lalace sallarma sai anyi mata African tym lallai sanin addini yai k'aranci agunsa

Bayan sallar ishsha,i yakawomin abinci a take away tuwon shinkasa miyar agusi

Shima anan falon yaci nashi yana kallon tashar namun dawa

Intak'aice muku awannan ranar ko maganar Arxik'i bata had'ani dashiba saida safe yake cemin inshirya driver zaizo d'aukarmu zuwa Airport jirgin 11:am zamu hau

Dama a ckn d'akin ya kwana nikuma a falon da asuba alarm nasa awayata lokacin sallar yanayi ya buga natashi nayita

Shima sai goma nasafe yafito yashige toilet ya d'auro alwala yashige d'akin Dan tada sallar k'ara,i don saidai ace k'ara,in ta wuce akirata sallar asuba

Yakawon kayan kari nakarya ina gamawa danaga yana ckn d'akin agurguje Na fad'a toilet nai wanka ack nashirya dama nasaka key sbd tsaro

Shad'aya saura mungama shirinmu drivern akwai gudu don shad'ayan a airport taimana

A cikin jirgi nai mamakinsa domin ya sakarmin fuska sosai kujerata Na kusada tasa hannunsa yasa yarik'e nawa gam yana zolayata wai yasan yauna fara hawa jirgin sama bari ya rige Ni kada nai k'auyanci

Nidai bance masako kanxil ba domin lamarinsa ya d'auren kai saida yaga zamu  bar gida shine zai sakarmin rai to lallai akwai wani k'udiri aransa dake kaina kuma Allah ya fishi tuni nahau karanto addu,o,in tsari ckn  zuciyata


_muje zuwa_

*Nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧
Koda muka isa Dubai ma nan nan yaringa yi dani tamkar xai maidani ck

Babban hotel Yakama mana Amma d'aki d'aya ne babba ya kama band'ago nufinsa nayin hakaba

Hardacewa nashiga nawatsa ruwa nazo nakwanta kona samu inhuta inkuma baxan iyaba shisaiyamin muguwar harara kawai Na watsa masa nandanan yaja bakinsa yai shiru

Gadone babba a d'akin dayasha lallausan zanin gado sai doguwar kujera a d'akin sai kayan kallo dafirjin kamar dai Wanda muka baro saidai yafi wancen girma

Awajen kwanciya da daddare saiyace Ni inhau gado shixaihau kujerar ya kwanta bankawo komaiba nabi abinda ya tsaran

Kwananmu 1 a hotel d'in yace mushirya muje ingano shagunan kayan mom d'insa aiko hakan akai Dan munje nagaggano nabaiwa idona abinci tabbas mahaifiyarsa takama k'asa

Da muka koma gida yasa aka kawo mana abinci a hotel d'in duk abinda aka dire mana shawarma kawai naci bankula sauranba shikam har pizza yaci  ina zaune ko kallo be isheniba nima sbd innace xan sakar masa fuska naga alamar saiya zak'e dayake ya kunna mana tashar bolly wood sainake ta kallo Na saidai nad'an saci kallonsa kad'an innaga yana latsa waya agabana sukai waya da budurwarsa naji yana ce mata yaxo amma shida k'anwar sane tayi hkr saidai kfn yakoma zai nemeta

Ko ajikina bandamuba naci gaba da kallona

Ckn dare ina kwance abin mamaki saijin mutum nayi ajikina ya kwak'ubeni yana shashshafani nayi iya yina ganin Na tureshi nakasa ga duhu dukda nasan shine tawajen k'amshin turarensa nace"walh koka kyaleni kokuma inmaka ihu,yace"Oya yisauri kiyi kada ki fasa, kome zakiyi bame zuwa kwatarki balle tare aka ganmu kowa yaganmu kuma yasan honey moon mukazoyi,walh koki tsaya muji dad'inmu anutse kokuma insha nawa dad'in tak'arfi da yaji tunda kinsan yau bame kwatarki bakuma bakin tsiwa balle hannun mari

Maganarsa batasa natsorataba saima wani k'arfi danasa danna tureshi amma nakasa ya ringa matsani yana shan bakina tak'arfi duk saida jikina ya mutu murus nakasa katab'us xigidir yamin saida yacinma burinsa akaina wai! Ai awannan ranar nasha kuka harda majina yasha zagi aguna da duka amma bekulaba dayasan yasami abinda yakeso ya juyan baya akan gadon yai baccinsa

Idan nace muku aranar nasami yin bacci nai k'arya axaune nakwana sai danaji agogon wayata yabugane lokacin sallar asuba sannan nasauko naje toilet natari ruwan dumi nashiga nagasa jikina nai wanka nad'auro alwala nafito natada sallah shiko bashi yatashiba sai goma nasafe yashige toilet inanan akan darduma Dana taho da ita inatajan carbi ina istigfari akan Allah ya yafemin Dan gani nake tamkar Na aikata babban kuskurene aranar dukda bada amincewata akai hakanba,

Inka kalli manyan idanuna da suka k'ankance sukai jajir saboda kuka saika tausayamin

INA kallonsa yafuto yaxo yai sallarsa yakoma gado yaci gaba da baccinsa d'an wulak'anci naji wata muguwar tsanarsa ta k'aru araina wai wannan Mara d'a,ar akeso Na Aura har wataran akirashi da uban "yayana,

Hawayene kawai naji suna kwarara a kuncina don takaici

Sai 12:00 pm ya farka yana saukowa akan gadon yaxo gabana yadurk'usa kamar me Neman yafiya yace" Zuby baby nasan fushi kk dani kiyi hkr kinji balaifina bane duk ke kk jawowa kanki hakan idan baki mantaba aina tab'a fad'a miki ackn gidanku a d'akin ki cwr indai nahaifu kuma Na amsa sunana nakamal sainasha romomki ckn sauki, banshirya wannan tafiyar don wani had'a lefeba saidon nashiryatane donkawai naxo dake inda bakida kowa kigane kurenki Na Marin fuskata, yanzu ina bakin tsiwar,?

Yai murmushi ya shafa gefen fuskata yace'Allah sarki ymmata nasan tun ayau kinfara nadama ko? To bakiyi komai bama domin tuni nakansile Auranki da xanyi kuma baxamu koma gida yanzuba harsai munyi wata anan ina gurxarki

Ckn kuku nace'Allah ya isa tsakanina dakai kamal walh inkana tunanin nika cuta tokasani kanka ka cuta Dan Allah zaimin sakaiya mugu kawai

Yasaki wata muguwar dariya tareda buga hannunsa ajikin gado tabbas kamal mak'etacine Yace"ai baki gama ganin komai nawa bama harsai munkoma gida zakiga abinda zai biyo baya kuma,

Yatashi yafice daga d'akin

Nakifa kaina a kan cinyoyina ina kukan takaici da bak'in ciki bakowa yaja min hakan ba sai dady Na

Banida gatan uwa tabbas nasan da Uwata tana gidan duk baxa ai min hakaba domin babu uwar daxata yrda "yar cknta tabi saurayi wata uwa duniya nikam Allah yagani nayi biyayya ne kawai

Barista kamal mugune nak'arshe domin tun yana saduwa dani tak'arfin tsiya har yadawo xubamin wata shegiyar kwaya mekashe jikin d'an Adam a ruwan daxansha ko lemo daxarar nasha kuwa asalin alin yake zuwarmin ba gardama tamkar mijina nake amince masa


Sai kawai rana guda Allah ya ganar dani naga kwalin kwalin kwayar bayanan akayansa nakaranta aiko nagirgixa sosai Dana fahimceta


Allah ya nunamin ya b'allo ya xuba axatonsa ban luraba to tundaga ranar nadena shan ruwa daga hannunsa ko lemon


Ashe mugun ya d'auke wayata ya b'oye sbd kada nasanar agidanmu

Watanmu guda cur a Dubai yazomin da zancen gobe zamu koma nig.hutun daya d'auka agun Aiki ya k'are aiko naji dad'i sosai araina domin domin nasha alwashin saiya gane kusansa inmun koma....


~Muje zuwa~

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

_dis page dedicated to my luvly sister_*Zainab Autar Hjy* _nd all my luvly pan's_


*page 105-110*
A Daren da barista yazomin da zancen xamu koma gida gobe zazzab'i ya rufeni Ckn daren b.kamal yaxomin da buk'artar sa wai nabankwana xaiyi tsabar yarenamin wayo saikace wata iyalinsa ya maisheni

Dayake an dad'e bekulaniba tunda yasan nagano yana samin kwaya a abinsha saiya tsiri fita baya dawowa sai cikin dare

To yau tsabar mugunta irin nasa yanajin jikina da zafi haka yai niyar yi

Ya dumurmusheni yana k'ok'arin ciremin kayan jikina naji wani amai yatasomin bansan lokacin Dana kwaroshi akansaba turarensane ya tsayen a mak'ogwarona yasani amai bansan dalili ba ada inajin dad'in turaren amma alokacin saiya sakani awani yanayi

Tsabar yakidime a wani hali yake Na jaraba bekula daya kyaleniba ganin Na b'atashi a,a shita abinda ba halalinsa bane yake

Allah ubangijina yabani wani k'arfi Na dage Na turashi k'asa aiko sai akan wani mirro da aka jingineshi ak'asa saijikake taratsatsatsa Ashe da ka ya fad'a nan da nan kuwa jini ya wanke masa fuska goshin ya fashe,

Ko d'ar banyiba yai k'arfin halin tashi ya dafe gurin yai toilet

Ashe gurin yasamu yad'aure zuwa da safe kamar wani Abu befaru tsakanin muba ko borin kunyace saicemin yai zaije asibiti adubashi abashi magani Dan kansa yana sarawa

Nima bashiri Na mik'e nace muje tare banda lfy nima inaso naga likita

Da mukaje asibitin gillawa likita k'arya Yy wai fad'uwa Yy akan glass,doctor ya duba gun yai treating d'insa yabashi magani  yamasa allura sainikuma yace meke damuna nai masa bayanin yanda nakeji Na tashin zcy da zazzab'i likta yai tunanin ko maleria ce tunda tanasawa har mutuwar jikin danake ji yaimin test har kala 2 don axatonsa inada Aure

Aiko test d'in cikin dayai ya nuna positive nan likita ya dubi b.kamal da murmushi kan fuskarsa yace" Ranka ya dad'e matarka tana d'auke da ciki,Dan haka xan rubuta mata magunguna Na k'arin lfy sannan saika kula da ita sosai banda Aikin wahala harsaiyai kwari....tun kafin likitan yagama wannan bayanin daya sakani a tashin hankali Na mik'e tsaye tamkar xan fad'i k'afafuna sai karkarwa suke idona ya kawo ruwa nace"wayyo Na shiga uku likita ka rufan asiri acireshi walh banida Aure kaganshinan mugu shiya ringamin ta k'arfin tsiya har aka sameshi

Na d'ora hannu aka nahau kuka tausayi nabaiwa doctor ya girgixa kansa yace"yi shiru daina kuka kada kitarawa kanki jama, a ki kwantar da hankalinki za,a iya zubarwa tunda Na "yan satittika ne baekai wataba _cool ur mind_ _OK?_ _Just relax_ komai xai xama _normal_

Yakalli b.kamal dayake karkad'a k'afafunsa fuskarsa d'auke da murmushi ko a jikinsa likitan yace"Ranka ya dad'e yakai shiru bakace komaiba,
     "" hhhmmm to mekakeso ince doctor bayan naji kayi kid'anka kai rawarka kana faman rarrashinta kana fad'in za,a zubarmin da ciki alhalin Ni inaso nayi murna da samuwarsa Dan haka banga Wanda zai zubarmin da gudan jini naba inkuma kundage xaku fitarshi ai gaka gata nan nabarku lfy.

Ya mik'e ya fuce a sukwane da sauri nabi bayansa ina goge hawayena zuciyata tamkar ta buga yashiga mota yatada ta nima nashiga ya figa da gudu yabar asibitin ko kallona beyiba saima k'ure kid'a dayai yana bi

Da muka isa masaukinmu yace inhad"'a kayana zamu wuce haka nasashi gaba INA kuka yace gara inyi shiru Dan banyi kuka ba tukun yana gaba


*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

_ina mik'a_ _d'unbin godiyata me tarin yawa ga wad'annan manyan grps d'in masu Albarka_

*COOKS YUMMY n NVL* _grp admin_ ~khadijatul kubra~
*MAR,ATUSSALIHA NVL* _grp_ _admin_~Ummu Affan~
*HIKIMA WRITER'S  ASSOCIATION* _grp admin_ ~Nafee Anka~
*RUMBUN ASEA BASHIR NVL* _grp admin_ ~asea fulanin daji~
*KHADEEJA CANDY NVL*
*PHARTY B.B. NVL*
*DANDALIN AUTAR HJY NVL*
*CRAZY BUDDIES NVL*
*SAHAFS NVL*
*MACEN GABAN GOSHI NVL*
*FABULOUS LADIES GANG NVL*
*NOVELLAS LODGE*

*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 110-115*
Ban fahimci manufar b.kamal ba saida muka dira a gida Nigeria muna Sauka a Airport yakira wayar dadyna yasanar masa cewar gamu mundira ba b'ata lokaci dadyna ya turo da mota a d'aukemu amma sai b.kamal yak'i shiga wai inje yakaini gidanmu shima drivern gidansu yataho d'aukarsa

Ban damu da hakanba Dan duk haushinsa nkji ga jikina duk ba dad'i duk kasala nakeji nagaji kamar anmin duka gawata muguwar fad'uwar gaba dake damuna fargabata ma d'aya ta yadda xanyiwa dadyna bayanin ckn jikina koya zaiji aransa dady ga Aurena da b.kamal yace ya fasa

Koda Na dira agidanmu dady yaji dad'in ganina nai mamakinsa yasakarmin fuska sosai har yanacemin tunda nadawo inna huta zaitsaida ranar da zaikaini gun dangin mahaifiyata domin da bananan Yayan ummata uncle Nafi,u ya zozzo sau 2 ganina amma yai masa alkawarin zaikawoni da kansa,

Nai murna dajin wannan zance hr ckn raina danko inhar naje baxan dawoba tunda dama can uncle Nafi,u yaso yakarb'eni tunda aka yayeni dady ya hana tun rashin lfyr ummana ya rufe idonsa yace bazai iya bayarwaba Shikenan uncle yaji haushi ya d'auke k'afarsa agarin

Hjy Rakiya kuwa sai nan nan take dani waitaga nai kyau nak'ara k'iba Na cika me nakeci haka nabarta anan tanata tunanina (hhhmmm kaji makira mak'aryaciya)

Nikam dariya kawai nake don banida tacewa

Sati 2 da dawowata b.kamal yak'i biyo bayana gdnmu bandamuba ko araina don natsaneshi bayama inna tuno abinda ya wakana atsaninmu sai intsi tasntsar tsanarsa araina nakanji tamkar nasanrwa dady amma kuma sai xcyta tabani shawarar gara nabari har lokacin daxaixo yasamesu da xancen ya fasa Aure nikuma xan fad'i komai ai dole idonsa ya Rena fata kuma nasan dadyna zai d'aukar min mataki akan abin

Ashe kfn idon barista ya Rena fata nawa ne zai rena

Domin kuwa Hjy ce ta tusani agaba ranar wata lahadi da dare dady beshigo gidan ba alokacin tana tambayata kodai naiwa barista kamal laifi tajishi shiru baizoba baiyo wayaba ga biki yana gabatowa za,a shirya tsare tsare,nace mata niban masa laifin komaiba

Tad'au wayarta takira mahaifiyarsa suka gaisa take gaya mata dalilin kiran

Aifa sai momynsa tace"Au! Ja,irar yarinya b'oye muku tayi bata gaya muku abinda tai ba?

Hajy tace"meya faru bata fad'aba walh'

Momy tace'to ai Ni sai in fad'a miki don tsakaninmu babu b'oye b'oye Ashe tunda sukaje Zubaida take bin maxa itace kwanan wancen hotel d'in itace kwann bin k'ato gidansa intak'aice miki walh saida takwaso muku abin kunya don cikine da ita ahalin da ake ck,kamal yace min tunda batada kamun kai shikam yafasa,

Kuma nibaxan tursasa shiba hakama Abbansa begoyi bayan ayi wannan Auranba gara taje tasami daidai ita,shikuma Allah yabashi yarinya metarbiya irinsa,abinda yasa ma mukai shiru da zancen kobakwaso ad'agane kada mutane suji asirinku ya tonu...

Ai Hjy tana Ajiye wayar momy tayo kaina tana huci kamar kububuwa tana cewa yau saita kasheni suxan k'ullawa bak'in ciki indauko musu ck inyi shiru dan Na renasu ta shak'oni ta had'a da bango ta ringa dukana a cikin ina ihu

Bata tsaya jinta bakina bama saida ta jigatani ta kyaleni huwaila tanaji a kicin badamar taxo ceto bata isa saiya zama abakin aikinta

Waya Hjy taiwa Babana tagaya masa komai baxata jirama ya dawo gidanba

Ran dady a b'ace yashigo gidan yasameni a mak'ale a k'uryar kujerar ina kuka bakina yana fitar da jini ya zauna akujerar dake fuskanta ta yanuna kansa da yatsa yace"Zubaida Ni kika ciwa mutunci ko Ni xaki zubarwa da kima a idon duniya ko? Dama abinda nace kije kiyi kenan a Dubai shine zaki kawon sakamakon ackn gidana ko to baxan d'aukaba, domin ayau basai gobe be zaki barmin gida

Na d'ora hannu aka 'nashiga uku ina xan nufa,nace"dady kayi hkr ba laifina bane kuma sharri yamin,yataimaka yabarni inxauna inhar yakoreni banida inda zan nufa

Aiko dady ya rufe idonsa yace intashi tun kafin dare yaimin insan nayi in ma gurin samarin nawa zan koma ga hanyarnan ai duniyace tunda nasakashi kukan zuci to insha Allahu nima sai nawa "Yayan sunsakani intafi inma babbar karuwa nake so naxama sai inzama

Ya mik'e ya nunani da yatsa ckn d'aga murya yace" maxa ki tashi kisan inda dare yai miki Na baki minti 20 inhar nafito nafito natararki agidana saina kasheki da hannuna Zubaida,yana gama fad'in haka yahaura sama

Hjy datake gun tace"aikabata da yawa Alh minti 5 yakamata tak'ara acikin gidannan  inba hakaba duk abinda kk gani ke kikaja

Nashiga tashin hankali aranar nan Wanda bana mantawa haryau natashi jikina ba kwari nai hanyar d'akina da nufin Na had'o "yan kayan da xan tafi dasu

Amma sai Hjy ta tare min hanya " ina zaki aibaki isaba yanda kk zo duniya babu komai haka zaki koma yawon duniya ba komai

Haka da kayan jikina kawai  sai hijabi Na fito Ina kuka megadi namin mgn banbi takansaba nai waje zcy ta sai tafarfasa take bansan inda xan nufaba nad'anyi nisa da gidan dare yafara yi layin tsit naji taku abayana kafin injuyo naji anrik'en hijabina ta baya....

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm* ~NabilancyLuv~®

*page 115-120*
A tsorace najuya Dan ganin kowaye Allah sarki Ashe huwaila ce tagoge hawayen dake zarya a idanunta tace"tausayinkine yasa nabiyoki Zubaida kiyi hakuri da halin da kk tsinci kanki nasan sharri akai miki bakiyi cikiba tunda ba halin ki bane ashararanci

Nace mata,huwaila akwai ciki ajikina amma walh bada son raina aka same shiba domin tak'arfi da yaji kamal ya ringa Tarawa dani har aka sameshi amma kinga daga baya yaxo yaimin wannan sharrin amaimakon kuma dady yakarb'i wannan babbar k'addarar data sameni Wanda shine silar faruwarta a,a saiya sakamin da HK ba komi zantafi huwaila Allah y kaddara saduwarmu nagode da kulawarki akaina tundaga kuruciya Allah ya biyaki da gdn Aljannah


Huwailà tace"to yanzu ina zakije a tsohon Daren nan Zubaida Ni gashi banda kowa agarinnan sai a kauye indai ba can xan kwatanta miki kije ba....
Na katseta dafad'in"babu gurin Wanda zanje Huwaila tunda har yace inje inshiga duniya to xan shiga ai dama duniya fad'ine da ita Na tabbata Allah zai had'ani Dana gari

Huwaila ta mik'omin wata Leda da kud'i tace"ga wannan Zubaida ckn albashina Na gutsuro miki dubu 5 ne wannan kuma kayana ne masu kyau kala uku Na d'auko miki Dan Allah kada kik'i karb'a kema kinayimin shiyasa zan saka miki da alkairin da kika shamin kuma bayan bakyanan Aliyu saurayinki yaxo yabani wata leta in ajiye mk tanan ina saurin insameki shiyasa bantsaya nmn taba kuma yace insanar miki za,ai Auransa da Yr uwarsa.... Tun kafin tagama bayaninta naji wasu zafafan hawaye sun surnano mini

Allah sarki Aliyu Haidar nayi rashin mesona tsakani da Allah tabbas dady ya cuceni Allah ne kad'ai zaimin sakayya

Haka muka rabu da huwaila mutuniyar kirki

Taimakon dataimin baxan iya mantawa da itaba domin wannan kud'i data bani sunmin amfani sosai tunda banfito da ko sisiba dama

Tafiya kawai nake bansan inda nake jefa k'afa taba tun inabin lunguna lunguna da sak'o sak'o harna ganni a bakin titi ina tafe a gefen titin tamkar xan fad'i cikin sai murd'awa yake ga mak'ogwarona ya bushe dishi dishi nadawo gani kaina ya dawo juyamin harsaida nakai ga fad'uwa agurin

Adai dai lokacin Dana fad'i wata mota taxo giftawa kusa dani ta tsaya dasauri wasu ymmata uku suka fito daga cikin ta metuk'ansu befutoba

Sunci ado da dogayen wanduna d'amammu da body hug da yn mayafansu a kafad'a drivern nasu ya xuro da kansa yana ce musu "gaskiya fa zakusa mu makara gun xw partyn nan mexaku tsaya yi mata saikunje kunjawa kanku jangwan kuka sanima ko aljanace

Basu kulashiba babbarsu ta tattagoni ta mannani a jikinta inajin hayaniyarsu dayar  tana fad'in" tana numfashi Ashanty yi maxa d'auko ruwa a mota a yayyafa mata.

Da gudu ta d'auko ruwan faro ta mik'awa babbarsu ta shafamin a fuska naja wani gwauron numfashi sannan ahankali Na bud'e idanuna ina kallon su takafan ruwan abaki nakarba nasha naja ajiyar zuciya nace"nagode, babbar tace "bakomi miya futo dake keko awannan Daren kina d'iya mace kuma kina halin rashin lfy?.

Nace" labarin yanada tsayi mahaifina ne ya koreni daga gidansa Dan Allah kutaimakeni kutafi dani gidanku,

Babbar cikin su tace"to zamu taimakeki saidai yanzu zamu partyne Dan haka tashi mukaiki gidan saimu dawo mu wuce,ke karansi d'auko mata kayanta kekuma Ashanty tayani kamata mushigarta mota

Ackn motar direvern sai mita yake musu akan zasu koma gida bedaenaba saida babbarsu ta hayaiyak'o masa yai luf da,alama ma tsoronta yake

Sai kwarar gudu yake saida tai masa magana tace"Nurancy karage wuta kasan banason gudu a hanya ko don gudu Na wuce Sa,a gangancine ko ance maka muna saurine? Partyn nan fa ko k'arfe nawa zaka iya zuwansa tunda _till down_ ne ranta ab'ace take maganar aiko ya saisaita gudun yace"sorry Aunty *Zeenah* narage baxa,a k'araba tai tsaki tace"dafa kanajin magana ne,saunawa kanacewa ka daina kuma kadawo kaci gaban,shiyasa ai Alhaji baya yarda yayi doguwar tafiya dakai

A Wani d'an madai daicin gida yai faki muka futo suna rik'e da hannuna muka shiga

D'akuna ne reras a ckn gidan guda goma biyar Na kallon biyar sai toilet guda 2 ajere dasu da alamar gidan Na "yan *ZAMAN MARINA* ne....

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 120-125*
D'akin da aka saukeni shine d'akin babbarsu danaji suna kira da Aunty Zeenah mace me mutunci gata da faran faran,

D'akin babbane yana d'auke da babbar katifa me tudun gaske kamar gado yasha lallausan xanin gado gefe jikin bango doguwar kujerace sai k'aramin firij akusa da kayan kallo harda kayan kid'a sifikune gasunan

Daga kowacce kusurwa hotunan tane tayisu ta mammanna wasu da k'ananun kaya wasu kuma da dogayen riguna Na material photo d'ayane ya d'auken hankali Wanda naganta tareda wata kyakykyawar yarinya fara tamkar aljana Dan kyanta sun d'auka suna fara,a sunyi kyau ainun d'akin dai yai kyau ba laifi

Aunty Zeenah ta b'ude firij ta d'aukomin babbar Robar yoghurt ta diren agabana da d'an k'aramin Kofi tace"kisha wannan kamin mu dawo kada ki zauna da yunwa barima nakunna mk kallo danki d'ebe kewa donba yau zamu dawoba saida safe

Bayan takunnamin film d'in American film ta dawo kusa dani tace"ki kwantar da hankalinki akwai mutane ackn gidan kinji?

Nagyad'a kai nace"nagode saikun dawo"

Sukaimin sallama suka fice nabisu da kallo

Inanan ina kallona harsaida naji inajin bacci nakashe kyn kallon nakwanta akan doguwar kujerar nadad'e ina zuxxurfan tunani yanzu Shikenan nabar gida Knn? Zanshiga wata sbwr rayuwar ya Allah ka iya mini

Nashafa cikina dayake ad'akale nace"wai yanzu nan cikine gareni Na d'an mutum! Allah ya isa kamal.hawaye suka zubomin natuna ana bina salloli magriba da ishsha,i tuni nazabura Na mik'e da saurina nai waje Nagano toilet d'in guda biyu amanne da juna nazo shiga kenan naji motsi aciki da alama ma bana mutum d'aya bane

Inanan tsaye ckn "yan dak'iku naga sun fito mace da namiji ne da alama wanka sukai jikinsu d'aure da tawul sunrik'o hannun juna suka wuceni nabisu da kallon mamaki toko mata da mijine?

Nashiga toilet d'in da addu,a abakin nakama ruwa nai alwala Na futo Dan akwai ruwa a famfo gashi ba laifi dakwai tsafta aban d'akin

Da safe ban tashi da wuriba tunda nai sallar asuba Na koma sai goma Na tashi shima hayaniyar dawowar su Aunty Zeenah ne ya tasheni, bayan mungaisa ta had'a mana kayan kari muka karya daganan ta nemi jin labarina

Nagaya musu komai ban b'oyeba anan naga ranta ya b'ace tacemin" kwantar da hankalinki tunda har yakoroki saiyayi nadama wataran tunda duniyar da fad'i kibiyomu mushigeta domin Adama dake kema kisaki ranki ki bararraje kisamu kud'i kitara kud'i domin ki wuce raini

Sannan tak'ara da fad'in "kinganni nan nima Babana korata yai daga gidansa domin ciki nayi Na shege adalilin be d'auke mana komaiba mahaifiyarmu ta rasu nice babba sai k'annena guda uku komai Nike musu hatta kudin makaranta nike basu innasamu gun samari har abinci kafin ya dire Na dire dama Ni d'in me farin jinin samarice kuma masu kud'i k'arshe akwai Alhajin dayaimin ciki kuma yace kada insake inxubda yanaso don Allah be tab'a bashi haihuwaba da matarsa

Haka naita renon ckn yana kashen kud'i har account ya bud'en sbd inkula dakaina da cknsa

Ingaya miki da ck yafara fitowa Babana ya gane saiyace ba,a gidansa ba ya fitittike yaimin rashin Arxik'i walh saida ya koroni agidansa inaji ina gani nabar k'annena ckn wahala donbaya iya tsinana musu komai

Alhaji shiya kama wannan gidan d'akuna uku yake biyan hayarsu shine nabaiwa wad'annan aminan arxik'in nawa d'ai-d'ai su zauna kyauta Ashanty da Ramcy Karansi,

Ina gidannan nahaifi " yata kinganta can Nana Aysha kafin ta rasu mukai hotoncan alokacin shekararta biyu Alhaji yai kukan rashinta fiye dani adalilinta fa yake bada mota akaini duk inda zanje kuma koda ta mutu befasa min komaiba muna tare

Nakalli Aunty Zeenah jin tayi shiru nace"Allah yajik'anta"

Tace"amin, ki saki ranki zankula dake da komai naki harki haihu kema ki rik'e kayanki watakila nan gaba taxama mejink'anki

Nagyad'a kaina kurun Dan wani zancen nata ba fahimtarsa naiba sbd banajin xan iya zama karuwai irinsu

Tofa sabuwar Rayuwa dai nashigeta don zamana ya kankama awannnan gidan ina d'akin Aunty zeenan atare muke kwana kan katifarta tanaimin mutunci sosai abinda duk taci shinake ci

Ayanda nakaranci halayyar karansi tanada kishi da kyashi bata iya b'oye fushinta akan Abu

Koya taga Aunty Zeenah tabani wani abin saita nuna b'acin ranta koma ta furta itako  Ashanty ba ruwanta tanada kirki batada Sa ido akan abun wani


Aunty Zeenah bata fiye ZAMAN gidanba idan Alhaji zaiyi tafiya tana binsa saidai takan ajiye min kayan abinci nima kuma dake akwai kudin da huwaila tabani suna ringa b'atrwa ahankali


Ganin yanda Aunty Zeenah keji dani yasa "yan gidan kecemin " yar lelen Zeenah kokuma sucemin "yar lele...


*nabilancy Luv*💘💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 125-130*
Bani manta wani halin bak'in ciki daya tab'a riskata agidan Na rashin Auntyna Zeenah alokacin cikina yashiga wata Na 3,


Aranar wata juma,a Aunty Zeenah taxomin da xancen zasuje wata dinner inshirya muje tare kona d'ebe kewa aiko nai murna don dama tunda naxo gdn sau 1 natab'a fita waje lokacin dana raka Aunty Zeenah kasuwa mukai siyayyar cefane da kayan abinci

A ckn kayanta ta xab'omin wani dandatsetsen swiss less bak'i me stone Tabani mayafi golden da takalmi Golding colour dama kafarmu d'aya da ita Ni kaina nasan nai kyau haka itama tasani agaba tana yaba kyan danai hartana cewa kota mutu tabarmin kayan Dan sun karb'eni kusan jikinmu d'aya dama hatta _breast cafe_d'in da akai arigar yaimin dai-dai

K'arfe 5 nayamma Nurancy drivern ta yaxo d'aukarmu a ckn motar Ashanty tanata yaba kyan danai ita kuma karansi bata b'oyeba dama tanata shan k'amshi tanaimin wani kallo tace da Aunty"haba Aunty Zeenah less d'in danace dake inkin tashi badashi inaso kibani shine xaki baiwa Zuby?

Aunty dake gaban motar ta juyo tace da ita"Dan nabaiwa Zuby kayana shine zaki nuna halin naki ina ruwanki ina hanaki wannan halin wato kina ci gaba ko? Walh babu kyau kyashi, tokisani ko mutuwa nayi nabarwa Zubaida kayana duka ma abinda Na mallaka Na d'akina kinga ai bakida iko dasu kenan

Takalli narancy tace"kuxama sheda kaida Ashanty

Nurancy yakwashe da dariya yace"aikinki yana kyau Auntynmu Allah yabar manake...

Ashanty tace"inma bamu itama shedace ai, to tundaga nan taja bakinta tai gum

Koda muka isa hotel d'in tahir ancika mak'il kowa ka kalla kasan yakai don bikin Na manyane,duk inda Aunty zataje ackn hall d'in dani take tafiya ta nunani cewar k'anwar tace Ni

Tanunani ga ango da Amarya amatsayin k'anwar tata muka gaisa,ananfa wani abokin ango ya k'alloni ya mannemin saida ya nace Aunty tabashi nambata (dama ta saimin waya)har kwatancen gidan tai masa

Nikaina gayen yaimin black beauty ne handsome guy ga sajen dake fuskarsa yai masa kyau

Har taran dare ba,a tashiba saida Aunty taiwa Nurancy waya akan yaxo yad'aukemu yamayar damu gida wai bata jin dad'in jikinta

Haka muka tafi da Nurancy yaxo ba,a tashiba waisai goma

Akan hanyarmu ta zuwa gida Nurancy sai kwarara gudu yake aiko ya bugi wata mota dataxo yi mana over taking saijin motarmu mukai ta gangara gefen titi tafad'i tana kifawa damu tundaga nan bansake sanin halin da ake cikiba sai a gadon asibiti

Allahu Akbar!Auntyna Allah ya karb'i ransu itada Ashanty da Nurancy,itako karansi buguwa kawai tayi akanta sai ciwo ahannunta aka bata gado itama

Niko bandawo hayyacina ba ma saida akai kwana uku naji ciwuka a kafata kad'an sai targad'e ahannu saikuma cikin jikina daya zube

Ashe labarin yin hatsarinmu yakaiwa "yan gun dinner don bawani nisa mukai da baro hotel d'inba angano daga gun mukene ta hanyar ganin kalandun Auran da kayan rabon da aka bamu dayake angon fitaccene nandanan labarin yakai musu

Ashe wannan saurayi dayacewa Auntyna yana sona k'arshen tama shine yaringa jinyata harna farfad'o daga doguwar suman danai Na kwana uku

Al,amin shiyaita jigilar bani kulawa har aka sallamoni itako karansy ma anriga sallamota

Rasuwarsu Aunty ta tab'ani sosae dukna rame nafita hayyacina har akai kwana arba,in bandena kukan rashin Auntyna mesonaba


Kamar yadda Aunty tafad'a kafin ta rasu haka akai komai nata Na d'akin yadawo nawa ba yanda karansy ta iya duk bak'in cikinta domin tasan Auntyna tafisu da komai gashi kuma ya zama mallakina ankuma sami kud'i ad'akinta dubu d'ari biyu Wanda narabashi biyu nad'au d'ari Na sadakar da dubu d'arin

Al,amin yana nuna kulawarsa akaina yana gwadan soyayyarsa harna saki jikina dashi naji dad'in fitar ckn jikina domin bana fatan inbud'i ido inga d'an shege agabana

Mund'au kamar wata biyu da Al,amin saiya bujiromin da buk'atar yanason in bashi had'in kai mud'an hole kamar yadda yaga wasu masoyan nayi

Nasha mamakinsa don saida Na caccab'a masa bak'ak'en maganganu nace dama Ashe ba son tsakani da Allah yakeminba Toni baxan iyaba

Ransa yab'aci harda cemin shiko yake sona, nice dai bana sonsa inbanda haka aiso kejanyo hakan kuma Na amince da waninsa ma balle shi da zai Aureni gashinan harda samun ciki amma zance masa baxan amince ba shine dai banaso

Nan yai fushi Ya tafi bansake ganina ba tsahon watanni

Ammafa naji haushin kalamansa Na maganar cikin da yayi besan tayanda aka sameshiba ne dabai gaya min hakaba

Naxa Al,amin gwadani yake bazai iya jurewa ba dai dawo amma saigashi shiru-shiru ya shareni tsahon watanni

Ashe bansaniba Karansy ta saci nambarsa a wayata harsun fara soyayya....


*nabilancy luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 135-140*
Da futa ta nasami d'an sahu nace masa yakaini green place hotel yagayan kud'in nace muje kawai danba sanin gun naiba


Aikodai da isata nahango motarsa ackn hotel d'in yafakata a parking space yana ciki yana danna waya Gabana ya fad'i Allah yasa basuyi waya da karansy ba don sai kwab'ata ta rushe


Na bud'e murfin motar nashiga da sallama ai kasa amsamin yai Dan tsananin mamakin daya shiga Na ganina ganin irin shock d'in daya shiga one tym yasa nai murmushi Na kad'a manyan idanuna nace'nasan zakai  _surprising_ d'in ganina a atare dakai a ckn motar kama to kwantar da hankalinka me guri ne yaxo me tabarma saiya had'e yakama gabansa

Bakinsa bud'e yana kallona yakasa magana kwata2 nai murmushi akaro Na biyu nace dashi"Al,amin kabani mamaki Ashe son da kakemin bana tsakani da Allah baneba dahar xaka gujeni kaso k'awata wannan ai cin amana ne da tsagwaron yaudara

Ya zaro idonsa da mamaki k'arara afuskarsa kafin yai magana naci gaba da fad'in" kada kace komai domin yau asirinku ya tonu bakada tacewa aguna nayarda dakai wato waikai nan kana xaman jiran karansy domin kasauke sha awarka ajikinta saikaga kuma Zuby a madadinta

Shin dawane idon xaka kalli soyayyata? Shin me karansy tafini daxaka k'ini ka sota?

Yakama hannayena biyu ya damk'esu yace" sorry my Zuby bansan kinada alak'a da karansy ba domin bama tab'a had'uwa face to face ba asalima ita tafara kirana awaya tace tana sona

Danasan cewar karansy tasanki da banyarda Na amshi tayin soyayyar taba ki gafarceni baxan sake ba duk da laifin kine da kk yi wasa rairai dani nakawo mk k'okon barata kika k'i amincemin alhalin ina miki son Aure bakuma xan tab'a gudun kiba,amma yanzu tunda kin dawo gareni zaki kwantar min da hankali Shikenan zan manta da wata karansy

Wannan kalaman Na Al,amin su suka rudeni Na aminta dashi domin inna sake saidai inga anayi don tsaf karansy zataimin sinacin

Muna tare kfn murabu acikin hotel dinnan saida karansy ta kirasa yak'i d'auka saida Na karb'i wayar Na daga kiran nai maganinta nace"wacece haka take kiran Mijin Zuby,koma wace kada tak'ara kira inmuna tare domin ayanzu lokacina ke gareshi muna jippatu,

Nasan zata gane Ni Dan haka saina kashe kawai sbd shiru tayi batai mgn ba

Intak'aice muku dai tundaga wannan plan Dana d'ana Shikenan muka dawo normal nida Al,amin kusan koda yaushe muna tare dama bana kawoshi ckn gidan saidai mukebe a wani sirrintaccen guri kokuma Yakama mana hotel muje muhuta Al,amin yana samun yadda yakeso ajikina Dan hakanema yasakarmin bakin Aljihunsa nake abinda nakeso

Ganin haka yasa karansy ta dad'a k'ulewa da k'ullewar da mukai da Al,amin gashi duk kwashe kwashen samarinta bata samun abinda nake samu gun Al,amin ya bud'e min account yana d'uran kud'i bama saina tambayaba hatta abinci Na restaurant nakeci kullum ko inje dakaina ko yayomin take away kokuma Na dafa me kyau adakina inbanajin ganda, itako batada aiki saina Aiken siyan alala,dambu,shinkafa da wake a ckn unguwa

Al,amin ma,aikacin kostom ne  masu uwar kudin Knn

Ko mgn karansy bata min koduk borin kunyarne  oho nikuma saina watsar da Al amuranta

Ko mutanen gidan sun dawo daga rakiyarta suna mutuntani sosai inai musu alkairi musamman inna rage kilishi dasu dambun nama nakan basu su raba dukda kowacce fita take nema kokuma axo har gida asameta abata amma akwai masu kwad'ayi da son abin hannunsu baxasu iyacin dad'iba saidai abasu

Bani manta dalilin daya kawo k'arshen xamana awannan gida fad'a aka tab'a yi da karansy da wata mak'wabciyar d'akina adalilin hajjo "yar ficika tayi d'inki tasa abinta saiko ke karansy kk kushe mata tace aibatayi kyauba d'inkin bada irinsu tsilaye ya daceba

Aifa sai cacar baki daga k'arshe fad'a ya kaure Abu yak'ici yak'i cinyewa harda police ckn lamarin nasu gida ya cika dank'am aka Tisa k'eyarsu aka tafi dasu station


Aranar nasa anemomin gida haya gara natashi baxan iya da wannan zaman ba

Naso ace nasami gida Ni d'aya amma dayake da gaggawa nakeso aranar dillalin yace indai aranar nake son natashi saidai inkoma Wanda yake a hannunsa tukunna mutanen ciki basuda yawa


Haka Na amince Na koma wannan gida Ashe rabon had'uwa da Aunty Ruby ne...

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

_Assalamu Alaikum zuwaga "yan'uwana  makaranta wannan novel d'in nawa zan d'anyi tsokaci akan yanda wasu ke tambayata wai shin menene ma_ *ZAMAN MARINA*?
_to nasan masu Tambaya basu karantashi tun a farkoba domin nayi tak'aitaccen bayani a page Na biyu_
*ZAMAN MARINA* _zamane Na mabambanta halaye zamane Na masu zaman kansu zamane Na kaxo-nazo_ _akwai shirin da ake a redio freedom me taken wannan sunan kutara kuji yanda mawak'i Mahmud nagudu yake wak'a akan_ *ZAMAN MARINA*


*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 130-135*
Ranar Dana Ramfota nagane abun kuma nai maganinsu shine ranar dana karb'i wayarta ina Turin wata wak'ar m-shariff me taken Zahra

Ina d'akina ita kuma tashiga wanka misalin k'arfe bakwai Na dare kawai sainaga kiran nambar Al,amin ta wayar karansy naxaci gixo nambar taimin saida takatse Na nutsu Na dubata sosae naga itance dai domin special nambace narik'eta akaina

Bangama mamakiba saiga shigowar test ta ckn wayar tata kamar haka.          _Assalam Munyi_ _Alk'awarin had'uwa_  _yau kuma_ _nabugo naji a ina zamu_  _had'un kuma da k'arfe nawa_ naga baki _d'agaba dafatan lfy dai ko? Nak'agu naganki yau domin ina ckn matsananciyar sha,awa nasan duk da yaune farkon had'uwarmu zaki kwantar min da hankali_


Nasha mamakin wannan sak'o Na Al,amin lallai namiji k'udan xumane ko kuma ince wata macen shed'aniya ce don gashi Karansy ta nunamin shaid'ancinsu Na "yan bariki

Ni karansy zataiwa haka?tabbas saina nuna mata nima kwaruwa ce nafita ilimi awannan harkar tunda bariki alalan gero ne...

Naisauri natura masa sak'o ta wayar tata kamar haka: _Ganinan zanfito muhad'u a_ _green place hotel kasan_ _inasonka my lovely babu abinda zakace inmaka_ _ink'iyi aikasha kuruminka nawan yau zaka huta a jikina_
          _Taka Karansy_

Ina ganin sak'on yatafi sainai maxa Na goge su duka harda Wanda ya fara turowan har missed call d'in dayai mata don karta gano

Dama nai wankana tun yamma don haka saina tashi a gurguje Na bud'e akwatina Na Ciro wata doguwar b'akar riga me kama jiki tai min cas ajikina rigar tasha stone ahannu da wuya gaban k'irjin rigar anmata shatin k'ok'on brexiyya dama gani Dana shanun suka mik'e sukai cako-cako

Gyalen rigar d'an mitsitsine nayanashi akaina nai _simple make up_

Karansy tashigo tatarar ni ina fesa turarena Na *Firstly* tak'are min kallo sama da k'asa ta girgixa kai tace" sai ina haka wannan kwalliya kamar zakije gasar kyau?, nai dry nace" walh jippatu nake son naje zan siyo turare naji ance sunkawo designers gara inje kada ayi bamu mukaso kud'inmu mukwaso,

Tai d'an guntun murmishi tace"haka dai kekam bakya gajiya da siyan turare anya aljanunki basuda nasaba da k'amshinki kuwa? Nace" _may be_inxakije  dai kawai taho kiyi rakiya a siya miki ko d'an karami ne kema ladan rkyr

Ta tab'e baki tace"A,a ina naga ta rakiya zanyi bak'o yau"


Nace mata "bak'o kuma daga ina? Tace" _new catch_ ne walh a _network_muka had'u shine yau zai fara kawon ziyara

Nace"lallai Toni saina dawo kawai,nai mata sallama ta fito ta koma d'akinta Na rufo d'akina nai waje....


*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 140-145*
Naji ddin had'uwa da Aunty Ruby a wannan sabon gidan haya Dana kama domin munyi zaman mutunci da ita ta rik'eni amana sainake mata kallon Auntyna Zeenah data rasu kusan halayyarsu d'aya ta son mutane da faran faran itama abin hannunta berufe mata idoba ko zatai tafiya key d'in d'akinta a hannuna yake wuni koda Na awani ne munhad'e kanmu da ita tamkar Yaya da k'anwa ita taxamar min abokiyar shawarata duk da cknmu bawanda yasan labarin juna a lokacin

Su uku natarar a gidan biyun yarensu d'aya sun had'e Kansu ko fita zasui yawo tare suke tafy saidai in da saurayi za,a fita shine suke rabuwa

Alokacin da Al,amin ya nunan halin nasu Na maxa naikuka kamar raina zai futa sbd Na amince masa yaci amanata ya amanta alk'awuran dayaimin Na zai Aureni bazai tab'a gudunaba sai gashi yayi domin yaxomin da xancen iyayensa sun tursashi saiya Auri Yr uwarsa Dan haka inyi hkr zaiyi biyayya bazai iya bujirewaba kawai insami wani agaba

Aunty Ruby ta tayani jin takaici ita taringa tausata tana nuna min aidama ba,a amincewa maxa har a xcy a bariki

Da Allah yasama banyi sake ciki ya gifta atsakaninmu ba domin   planning yaita sawa nakeyi kokuma mui amfani da condom

Aunty Ruby jajirtacciyar mace tanada kaifin basira ita ta dage wajen binciken gaskiyar lamarin Al,amin don cewa tayi bata yadda da abinda yaceba

Ya xa,ayi yana Namiji kuma da girmansa da uwar kudin Sa ayi masa dole aiko mata awannan xamanin andena yi musu Auren dole

Ashe kuwa Al,amin k'arya ya sub'urbud'a mana domin saida ta gano Ashe "yar ubangidansa agun Aikinsu zai Aura kuma suna son juna

Nan taita bani shawarwari akan halin maxa konan gaba kada Na sk aminta domin kuwa itama anshata ta warke sannan xaman duniya iyawane

Da shawarwari Aunty Ruby nai amfani wajen iya taku da duk wani namiji dayaxo min da xummar zai Aureni bana yarda har araina sbd bakowane namiji ke Aurar macen dake barikiba

Nayiyyi samari kala kala amma ba bijari-bijariba manyan masu kud'i " yan siyasa da "yan kasuwa haka naringa samun kud'i ina Tarawa a banki Aunty Ruby tabani shawara damu fara Business tunda muna samun kudi.


 Alh Sammani shiya fara siyamin motar hawa " yar karama kafin daga baya nacanxa wacce tafita tsada.


 Aunty Ruby ta iya takunta itama,domin barikinta metsafta takeyi itama tai motar kanta kafin had'uwarmu musai wannan gidan

Tokunji Tarihin Rayuwata da abinda yai sanadin shigowata bariki....


*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 145-150*
Kowacce cknsu ta zabga uban tagumi suna sauraron Zubaida

 Ruby tace"tabbas Zuby labarin ki yafi nawa rikitarwa da tausayawa domin kinga ke a budurwarki aka kwareki aka keta miki "yancinki Na budurci nikuwa saida Na tab'a yin Aure sannan mahaifinki akwai asiri a ckn lamarinki dashi anshiga tsakaninku dolene yanzu musamo mafita baxamu zauna hakaba dole mui wani abin aciki addu,a zamu saka ayi domin Allah ya karya lagon Hjy Rakiya matarsa yakuma bayyana miki Ummanki

Ukhty tace" gaskiya ne Aunty, Ni walh mata masu asiri suna bani mamaki kwata2 suna manta akwai Allah agabansu kuma k'arshen tuka tiki dai tik!

 Feedy ta muskuta ranta a b'ace tace"walh sister Zuby da xaku  barni da saina shigar da k'arar abinda *b.kamal* yai miki sannan a dank'o Hjy atuhumeta akan b'atan junior da suka sace tun yana tsumma dakuma abinda taiwa ummanki...

Rubayya tai murmushi kana tace"Duk baxata kaimu ga hakaba domin abinda hkr bebakaba to rashinsa ma bazai tab'a bakashiba
Addu,ar dai danace zamu saka manyan malamai ayi akai shi xamui baxamu biye ta takiba sarkin "yan kato b'ara,feedy bakida hkr ga saurin fushi kekam walh zamuso muji naki labarin.

Aisha simoli tace'wai Aunty Ruby waya kamata ya fara a ckn sune nifa nak'ara aci gaba domin dare yanayi duk da namu labarin bazai kai naku tsayiba,

Ruby tace" aikomin dare sai kowa ya ida zamu tashi mubar gun nan ba Wanda nasa labarin zai zama kwantai koda zamu kai ukun dare anan duk saurin baccinki yau saidai kiyi hkr,Dan haka *ukhty* ke zaki fara,dagake sai feedy Auta ce a k'arshe.

Ukhty ta gyara zama tafara dacewa....

***********************
Kamar yadda kuka sani sunana Na Ainahi *laila* sunan ukhty nasame shine a k'asar saudiyya ta dalilin wasu k'awayena

Nataso agaban kakata gwaggo Attu mahaifiyar Babana

Mahaifiyata ta rasu tun daga haihuwata ba dad'ewa asakamakon jinya datasha haka mahaifina ma ya rasu ta dalilin ciwon sugar da k'oda

Gwaggo Attu masifaffiyar gaske ce Wanda intana fad'a bakinta harfidda  kumfa yake, hartakai a ckn k'auyen namu Na marke ana shayin tab'ota sbd jarabarta

Mijinta baba Musa bayada aikinyi kullum yana gida ko danya tsufa inkaga baya gida to yana gun "yan tsoffin abokansa a majalisarsu gwaggo Attu itace keyin komai n gidan tun tana takura baba da masifar daya futa ya nemo hardai tazuba ms ido kyaleshi tunda taga ba iyawa zaiyi ba



Da safe tana saida koko da k'asai a ckn gida Nike tayata suyar da bayarwa in anxo siya dayake ba,a sani a makarantaba

Da rana tana min wake da shinkafa natafi talla da yamma kuma ina mata sana,ar awara a k'ofar gida nake soyawa kafin ishha,i nasiyar natashi dayake Allah yana samin nasibi bana kwantai a sana,ata

Nikenan banida lokacin kaina sai dare dayake kuma ina mugun tsoronta bana kawo mata ciniki gib'i kokuma nai mata ragi nasan halinta batamin ta dad'i inna shiga hannunta
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 150-155*
Kamar yadda nasaba fitowa sana,ar awarata k'arfe shida nayi nafito nafara ko kaskon farko ban kwasheba sai gashi yaxo a motarsa ya faka a kofar gida ya k'araso guna da fara,arsa

Yaimin sallama Na amsa tareda gaidashi ya amsa yana fad'in"toke bakya d'an ajiye d'an benci ko kujera ta xaman costomer?

Nai murmushi nace"bana ajiyewa saidai in kanaso ka zauna ne sai in d'auko maka kujerar tsugunno ackn gida.

Yace"barta kawai ba zama xanyiba sauri nake zanje gun abokina yana jirana zamuje zance

Ai bansan lokacin Dana ware ido ina kallonsaba araina ina maimaita Kalmar zance? To gunwa kuma?

Yakatsen tunanin da fad'in "duka awarar taki takai ta  nawane?  Nace" ta d'ari takwas da hamsin ce, ya bud'e walet d'insa ya xaro sabuwar dubu d'aya kar tana shek'i ya mik'omin yana fad'in"gashi kisoyata duka kirabawa almajirai da mabuk'ata sadaka

Nasa hannu nakarb'a nace"to bari akarb'o maka canjinka a ckn gida' yace"a,a nabar maki indai canjine,

Nai murmushi nace"nagode,amma dai katsaya inkwashe wannan kaskon katafar mata.

Ya zaro ido yace"wa xan tafarwa, nace"ita mana,banaji kace zance zakaba,

Yai wata dry sannan yace "lallai yarinyarnan bakida mantuwa da alama kuma zakiyi kishi daga cewa zamu zance,har abin ya tsaye mk to sorry abokina hannafi zanje Na raka nasan baxaki gaxa saninsaba,

Nace" hannafi d'an bokon nan Yayan hansai?

Yace"kwarai shifa yanada k'anwa hansai ashema kinsanshi toki cire aranki ba gun budurwa xanjeba rakiya xanyi, ina da budurwa xanbartane naxo nayi wata ai sai akirani da d'an yaudara tunda nasameki kuma ai nagama budurwa kokuwa?

Nai dry kawai Dan tunda yafara koron bayani naji raina yai fari amma da harga Allah naji kishin araina

Mukai sallama yatafi wannan ranar dai ban dad'e awajenba kamar yadda yace haka Na rabarta naji dad'i nima da ban dad'e awajenba ita kanta gwaggo taji dad'in ganin haka

Haka zuwansa Na biyu guna ya dad'a bani dubu yace insoye duka in rabarta yana gun nasoye naringa rabawa almajirai shima yana tayani kafin yatafi kuwa saida mukasha hirarmu saina samu kaina da sakewa dashi haryake tambayata cewar ina zuwa makaranta

Nafad'a masa gaskiya cwr bana xw ba,a sakaniba beji dad'iba har a fuskarsa nagani

Yacemin"kina son kiyi karatu ? Nace"sosaima inaso walh" yace " to kwantar da hankalinki zansakaki inhar za,a bari a gidanku,

Nahau murna ina masa godiya,sai a ranar yake fad'amin sunanshi *Nasir* nima nafad'a masa nawa sunan


soyayya me k'arfi ce ta k'ullu tsakanina da Nasir Wanda kullum yana k'ofar gidanmu baefasa siye awarar yana rabawa sdk ba domin shi fitowa suyarne bayaso haka har gwaggo ta daina saidai taga dubu ita adad'inta ma tsuntsu daga sama gashashshe kunsan kunsan yn kauye da ganin yawan dubu basai Nasir yaxama d'an gidaba hatta baba yasan dashi

Daga bayama saiya kansile min tallar danake da rana Na shinkafa da wake yace zairinga baiwa gwaggo dubu uku kullum haka ko akai domin har kayan abinci yake siya mata duk wata gashi yasakani a makarantar boko a primary akasani wai nai girma a one kuma sungwadani sunga zanyi basira


Dayake Nasir ya kashe bakin tsanya ai gwaggo bata hana sakani a makarantar ba


Nasir ya sami karb'uwa gun gwaggo sosai, (Nasir malamine a makarantar danake zuwa yana koyarda b'angaren "yan sakandare )

A yanzu nasami Hutu ko ince nasami yncin kaina saboda wahalhalun da nake acikin gidan ya ragu saidai inna tashi sallar asuba bana komawa zanhau sharar tsakar gida zan gyarawa gwaggo waken k'osai inkai mata nik'a sannan ind'ora mata ruwan koko takwas tanayi nagama shiri nakarya sai makaranta tana bani kud'in break naira goma kullum....


*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *continue*.... *ZAMAN MARINA*.... *145-150*

Nassir shine saurayin danai munsha soyayya dashi had'uwata dashi ne Rayuwata ta haskaka


Baxan tab'a mantawa da ranar had'uwar mu da Nassir ba  Wanda nadawo daga tallana ina hanyar komawa gida yabiyoni abaya amotarsa bak'a yanata min hon alamar intsaya zai magana dani nai funfurus naki saurararsa bekyaleniba harsaida yaita bina abaya hrnaje gida yaga shigata ya juya

Bayan sallar magriba yadawo yasameni a k'ofar Gida nagama suyar awara nasiyar ina harhad'a kaya xan shiga gida akusa dani ya faka motarsa

Da sallamarsa ya iso gareni Na amsa ina kallonsa Dan baganeshi naiba,"yace" Ranki ya dad'e me ake siyarwane Naga kamar har an gama anci kasuwa ank'are bani,?'

Nai murmushi nace"walh awarace nake siyarwa kuma ta k'are don kfn magriba nake fara suya ba,a ishsha take k'arewa yauma dai natashi da wuri wanine ya siyewa Almajirai kusan rabinta.

Yace"yayi kyau gobe insha Allahu  nadawo nima insiya d'in amma ina Neman alfarmar abani ko minti 5 ne naxo da d'an batu gunki xamu tattauna

Nace"ba komi ai fad'i komiye ina sauraranka.

Ya gyara tsayuwa yace"nagode, nasan baki gane niba to nine Na d'axu da rana da naita binki abaya nai nai ki tsaya kk k'i tunda naganki alokacin Allah ya jarabceni da sonki,nikuma banida kwauron baki naga dana cutu gara naxo nakawo k'ok'on barata ko Allah xaisa nasami karb'uwa gunki

Nai murmushi wata kunyarsa ta rufeni naji kamar  k'asa tsage nashige don ba tab'a yin saurayi nayi bansan kuma amsar da ake bayarwa ba idan saurayi yace yana son budurwa

Na rufe fuskata da hannayena biyu ya dad'e atsaye yana jiran amsata yaga nakasa bashi sai nuk'u nuk'u nake dayaga dai banida niyyar in had'a ido dashima a wannan lokacin saikawai yaimin sallama yatafi kan cewa zai dawo gobe da wuri.

Aiko dai awannan rana bacci ya dad'e bed'aukeni sbd tunanin wannan saurayi dayace yana sona nima harga Allah nakamu domin da gari ya waye Allah Allah naringayi dare yayi koya dawo Na sake ganinsa....


*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 155-160*
Asalin Nasir d'an cikin unguwar Fagge ne dake ckn garin kano mahaifinsa Alhaji Nuhu meshadda d'an kasuwane dake harkar saida shaddoji da lasa lasai atamfofi,a kasuwar kwari shagunansa sunyi goma mahaifiyar Nasir hajiya Rabi bakatsiniya ce suna kiranta da Mamie Nasir ne d'anta Na fari sai k'annansa mata biyu Na gidan miji sai Autarsu dake karatun NCE a Sa,adatu Rimi

Nasir d'an bokone don digirinsa Na biyu yakammala bautar k'asa aka turashi a mkrntr  k'auyen mu shine daya gama suka rik'eshi a sch d'in  saidai yakoma Fagge duk juma,a yai weekend d'insa a can yadawo Monday

Dafarko k'in amincewa yyi saida Allahbya had'ashi dani sannan ya amince da k'udirin inhar naxama mallakinsa zai d'aukeni mukoma ckn birni

Nasir mutumne shi me rik'o da ibada Dan har tabon salla ne a goshinsa,wankan tarwad'a neshi yanada doguwar fuska gashin bakinsa ya mugun yi masa kyau shi ma,abocin saka glass ne mahaifinsa yanaji dashi domin shine magajinsa ko bayan ransa tunda bayada namiji saishi kadai don hakane ma yake sakar masa kud'i duk wata yake tura masa kud'ad'e a Account d'insa tun farko fara krtunsa har kawo lokacin daya gama be dainaba.

Ajinmu d'aya da hansai k'anwar hannafi abokin Nasir Kawata ce haka hannafi tunda yasan muna soyayya da Nasir Shikenan muke mutunci ko Nasir bayanan ya tafi gida a weekend yakanxo guna musha hira

Nasir yatsaya tsayin daka Dan ganin nasami ilimin zamani Dana addini, donshiya sakani a islamiyya ma 

Shekara uku muna zuba zazzak'ar soyayya nidashi alokacin nagama primary d'ina dama dg aji uku akasaka ni

Na d'ada zama budurwa sai baba yasami Nasir yace masa yaturo magabatansa don ayi mgnr Aure inhar da gaske yk

Asatin daxai tafi gida ranar wata Alhamis muna k'ofar gida muna hira yace dani" *lainas* kitayani da addu,a akan tunkarar iyayena da xanyi nabatun Auranki domin akwai yarinyar da take sona "yayar Mamie nace dake katsina amma yarinyar a gidanmu take da zama tana diplomarta a FCE

harga Allah Umaima tana sona amma nikam tun kafin nagamu dake babu soyayyarta araina abinda yasa ma tun farko ban gaya mikiba don karki tashi hankalinki ne akanta don Nagano kinada kishi banaso kuma kiyi zargin inna tafi gida soyayya nk da ita, idan ina tare dake walh mantawa nake da ita kuma tun farko da akaimin zancenta banyi amannaba

Amma yanzu nasan zata iya yiwuwa su taso da xancen ta nikuma inhar sundage Na Aureta to saidai su yarjemin Na had'a dake kixo ata farko sai ita taxo ata biyu kinga ai nayi adalci ko?

Kaina yana k'asa amma zuciyata kamar ta fashe Dan Allah yasani inada tsannin kishi

 Amma Dan ink'arfafa masa guiwa saina kanne nai murmushin yak'e nace"Ba komai *lainas* abinda Allah ya tsara akanmu dole mui hkr dashi mubi Allah dai ya shige mana gaba Allah kuma yasa Umaima ta hkr da *lainas* d'ina (sunan da muke fad'awa junanmu kenan shiya tsara hakan farkon sunansa da nawa)

Bak'aramin dad'in lafuxana yajiba yayi murmushi yace" Amin'

Saida ya shak'amin kud'i dubu goma wai inyi amfani dasu kfn ya dawo don zai kwana 2 tunda anbada hutun makaranta gashi nikuma munyi command entrance zamui shirin shiga secondary inta fito....

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧


*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 165-170*
Inaji suna kirana amma nai banxa dasu kuka nake sosai xcy ta Na tafarfasa nashiga gida gwaggo tana tsakar gida tana k'arasa Tatar Dana bari Na wuceta nai d'akina aituni ta dire a tsorace taxo tana Tambaya ta meya faru nake kuka?.

Saida nai kukana nagode Allah bata dakatar niba harna gama sannan daga bisani nake gaya mata duk abinda Nasir yazomin da shi

Itama ta kokonta abin acikin ranta bataji dad'iba ranta ya b'aci gashi taga samu taga rashi


Anan taita rarrashi Na tana bani baki da baba yaxo ta gaya masa komai,shima abin ya tsaye masa arai amma saiyace mana ba komai kada mu damu wannan jarabattace Allah ya d'oro mana mui hkr domin musamu cinye jarabawar Allah ya musanya min da mafi Alkairinsa yasa haka shiyafi min Alkairi arayuwa

Bamu dad'e da Rabuwar mu da Nasir ba baba ya kwanta ciwon kafa jinya sosae Ashe sugar ne harda cwn k'oda baba yaji jiki gashi danginsa basa kusa dashi haka haka gwaggo tai tayi masa hidimar jinya harya Amsa kiran mahaliccin Sa sarki Allah

Baba ya tafi ya barmu da kewarsa mutum ne Wanda ba ruwansa da tashin hankali ma,abocin rahane da farkwanci gashi yanada rik'o da addini

Bayan sadakar arba,in d'insa naceda gwaggo inaso inje gun dangin innata a yankatsari tunda ba makarantar nakeba gara inje can kawai

Aiko inna ta hana ta fututtuke idonta tace suda basa nemana kuma mesika tab'a tsinana min tun girmana sai yanzu zanje garesu su rik'eni kenan gudunta zanyi

Danaga aranar tanata masifa tun rana har dare akan zancen saina bata hkr nace nafasa zan zauna atare da ita

Anyi haka ba dad'ewa tazomin da zancen wai tasa gdn nan akasuwa xata had'a da filinta Rabin filoti ta biya mana kud'in zuwa makka mutafi can munemi kud'i don anan d'in bame taimakon ta a yn uwa ita kuma ba "yayaba.


Nace" haba gwaggo yaushe kudin gidan nan Dana filinki zai mana wani kudin kujerar maka harmu biyu alhali naji ance kudine tsububu yayi miliyoyi mu biyun

Tace"waya fad'a miki ta jirgin sama zamu tashi? To ta jirgin ruwane inmunje Sudan ta boyayyen hanya. Na xabura nace"gwaggo bantab'a jiba walh kinga kadafa muje a cinye miki kudin ki abanxa kizo kiyi b'atan b'akatantan

"Insha Allahu ma baxa ai hakaba da yardar Allah zamu samu hayewa lfy.

Hakan data tsara kuwa akayi munsami zuwa Sudan inda naga mata dayawa kowacce nason ta tsallake saudiyya, agent d'in gwaggo yace mata sainan da sati biyu zamu samu tfy,aina tsorata ganinmu a dokar daji ckn bukkoki gashi har ana kira mana sati biyu naxaci xaice kwana biyu

Aikodai saida mukai wata Allah yataimakemu mukai Sa,ar tfy muka baro wadanda sukai kusan wata biyu agun agent dinsu yanai musu hanya hanya

Munyi kwanaki ahanya kana muka sami isa k'asa me tsarki agigace guxurinmu bame yawa bane Dan haka ba bata lokaci gwaggo ta nemi gidan aiki tafara kfn nima nasamu sainake binta nake tayata wanke wanke ne agidan larabawan sai gyarae gyaren gida,sai renon yaransu

Hardai nima matar data samawa gwaggo tasamomin aikin agidan wata balarabiya datake futa aiki mijinta yana gida ba lfy mutuwar barin jiki Ni nake masa kusan komai kanta dawo wanka kawai take masa kafin ta futa nikuma nice kula da cin abincinsa sakawa da canza pampers d'insa ta manya inyai kashi ingoge masa da tissue Dan baxan iya masa tsarkiba🙄😉

Dan ma basuda yara har kayansa Nike wankewa amma tana biyana albashi me tsoka har Allah ya karb'i ransa asakamakon jinyar da yakeyi ta tashi don k'arshe asibiti ta maidashi a can ya rasu.

Saikuma nadawo zaman gida tunda dama agidan haya muke kafin wani aikin yasamu ammafa duk abinda zamui a d'arare muke Dan kar akamomu amaidamu k'asarmu tunda bamuda igama....


*nabilancy Luv*💘💘💘💘
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

_wannan page d'in nasadaukar dashine ga duk wata Zainab da Fatima dake fad'in duniyar nan_ *jinjina gareku "yayana* *ZAINAB*(  _Sayyada_) *FATIMA*(  _Shahida_) *Allah ya rayamin ku* _Amin_


*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 160-165*
 Inata xuba ido Inji dawowar Najir amma bulum buk'ui wai shaho yaci shirwa

Shine har aka koma hutun makaranta da sati uku banji duriyar Saba har jarabawarmu ta common ta fito naci makarantar kwana,amma saisu gwaggo da baba sukace ba inda xani kota jeka ka dawoce baxaniba harsai sunga dawowar Nasir sunji inda zance ya kwana

Bikin Kawata hansai da yayanta hannafi yanata gabatowa kullum naje nasami hannafi nagaya masa halin danake ciki Na rashin dawowar Nasir kwana kusa, toshikansa hannafin Ashe kullum ckn buga wayarsa yake sbd shine babban abokinsa  tun a B u k

Hakama dasuke koyarwa tare baida kamarsa a ckn mkrntr da ckn unguwar hannafi yacemin" walh laila da ace nasan gidansu Nasir tabbas danabi baya sbd baxanji dad'i ayi bikina bashiba

Amma kiyi hkr ki dena damuwa insha Allahu zai dawo da yardar Allah lfy ce ta b'oye shi

Wata biyu da tfyrsa duk Na rame sbd damuwa ko bikin hansai da akai ckn rashin kuxari Na aiwatar da komai

Ranar asabar aka k'are biki don tun laraba aka fara gabatarwa washe garin d'aurin Auran su hansai da yamma ina ckn gida inaiwa gwaggo Tatar k'ullin gasarar koko saijinai yaro yai sallama yace ana sallama da laila awaje inji Nasir

Aibansan lokacin Dana dakataba nace yace ganinan Na gyara jikina Na fice gwaggo tana band'aki

Har tuntub'e nai axaure Dan sauri daga nesa nak'ura masa ido yayi mugun kyau yasha boyel ske blue da yasha tsadadden Aiki a agaban rigar ya kafa hula zanna light blue da sassarfa Na isa garesu shida hannafi ne suka amsamin Na tsaya ina k'are masa kallon tsaf!

Ya rame sosai yai duhu daganinsa ackn damuwa yake idonsa ya canza kala ya rine zuwa ja

Ashe nikuma nawa idon hawaye yake shatatarwa bansaniba munacan muna kallon kallo

Saida hannafi yacemin"laila bekamata kiringa zubda hawayeba tunda gashi agabanki ya dawo duk da wannan dawowar tana d'auke da wasu damuwowi wanda ke kad'aice zaki fitar dashi ack

Sannan kuma inaso kixama me tawakkali da bashi kwarin guiwa domin kusamu gaci anan gaba don komai Na dny sai kayi hkr zaka sameshi..."hannafi me kakeso ka gayamin?kanaso kafahimtar dani cewar iyayan Nasir basu yadda da Aurenaba Knn?

Hannafi ya girgixa kansa fuskarsa da kalar tausayi yace'ki kwantar da hankalinki zakiji komai a gunsa

Idon Nasir a k'asa yakasa ci gaba da kallona yace'ki gafarceni laila nasan kin shiga wani hali Na rashin dawowata da wuri gareko walh ba ason rainaba,iyayena ne suka sakani agaba suka tirsasani akan dole saina Auri Yr Uwata Umaima

Koda naje musu da xancenki kwata2 basu saurareni da zancen ba suka k'i yarda futuk ssuka rufe idonsu akan baxan Auro musu Yr kauyeba kuma sukace ga gida bata koshiba nadawa bazai samuba

Damuwar Dana shiga Allah ne sheda domin dasuka saka ranar Aure wata d'aya da Auren yaxo ina kwance gadon asibiti akai Auren

Walh koda Na fito Amarya ta tare bana kulata cikakkiyar kulawa

Laila nid'in da kika ganni me biyayyane agun iyaye,bana yarda naga nasab'a musu balle Na tirje akan mgnrsu jini Na saida ya hau

Amma mahaifina duk son da yake min ya to she kunnansa kuma ya haneni da sake dawowa wannan k'auyen duk Dan karmu had'u tunda sunsan ina sonki

Mahaifina shago  ya bud'e min nawa nakaina a sbn gari market yasamin jarin kaina yahana aikinma don haka ma Ni yanzu nayanke shawarar komawa karatu zanyi masters d'ina amma ba a kasar nan ba

Laila ki....Na d'aga masa hannu idona Na xubar hawaye nace"kana nifin kacemin ayanxu umaima matarkace?kai kuma Mijin tane?

Yace" hakane laila amma...kafin yasake cewa komai nayi baya nai ckn gida aguje ina kuka...

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 170-175*
Ban rufa wata biyar a xaune ba aikiba nasamu a gidan wasu "yan biyu maxajensu ya da k'ani babban gidane amma kowa da part d'insa Mijin hassanar shine babba Sudais Mijin hussainar kuma Assadiq,

Inajin dad'in aiki atare dasu bawani aikin wahala nakeba domin goge gogen tayel d'in kasan gidan ne da kuma jikin bango sai wanke wanke da share share arana sau d'aya ina gamawa nake tafiya gd kowacce inai mata aiki maxajensu ke biyana matan kullum basa zama agida suna makaranta sukan barni ackn gidan suna riga maxajensu fita kullum

 Hakan ne yasa shed'an yafara baiwa babban dama yafara nemana munkai ruwa rana dashi ata dole k'arfi da yaji sudais ya sanni a " ya mace, yana shak'a min kud'i sosai duk randa ya kwanta dani yana bani kud'in dayafi albashina todayake matan suna gida week end basa fita suna Hutu bana zuwa aranar

 Muna ckn haka da sudais saiga assadiq da tashi sha,awar akaina ashe ya dad'e da auno kwad'ayinsa akaina shiru kawai yayi

Hhhhmmm banyi ja da tayinsa akainaba domin d'an uwansa ya gama b'atani haka shima ya ringa mu,amula dani tamkar matarsa ackn gidan kowanne idan Na gama yin aikina a part d'insa nake kasancewa
Dashi amma fa babu Wanda yagano cewar ina tare da d'an uwansa

Takai takawo asatin da bana zuwama ina tare da sudais domin yafi assadiq nuna jarabarsa akaina sannan yafi bani kud'i

Duk uban kudin danake baiwa gwaggo bata tab'a tuhumata ba akan tai yawa wayake bani su haka akai akai? 

Rashin lfyr gwaggo shiya kawomin tsaiko axuwana gidan wad'annan yn iskan larabawa nina ringa jinyar gwaggo Ashe cutar bata tashi bace donko sati biyu bataiba ta rasu tabarni Ni d'aya kwal a k'asa me tsarki

Matar sudais Nabeela da matar Assadiq Ni,imah matane da suke da kirki baruwansu da fitina irinta matan zamani insunga mijinsu Nada kud'i suita wulakanci ko shan k'amshi kodon suma nasu iyayan akwai abin hannu ba laifi

Bayan inna tai sati uku da rasuwa nakoma gidan aikina sbd xama bekama niba don burina danasa agaba shine inga nasami kudin komawa gida Nigeria

Aiko dai ganin banda mafad'i balle me kwabata ko harara sai abin nawa ya shahara nida wad'annan larabawa sudais da Assadiq takai takawo ma kullum ina tare dasu a hotel don aikinma dena yi nayi

Daga baya nai tunanin kada wataran su gano cewar dukansu suna mu,amula dani nashiga uku asirina ya tonu kuma Na had'a fad'a saikawai Na xille musu suka dena jina da ganina kwata kwata

To dama natara kudina ina ajiye dasu k'ari kawai nake nema Wanda zanyi guxuri dasu inna dawo

Asatin danake shirye shiryen dawowane muka had'u da wasu kyawawan "yammata a wani shago sunje siyayya su biyu anan muka saba jininmu ya had'u suke fad'a min sunansu d'ayar datafi haske itace *marwa* dayar kuma *safa*

Safa da marwa sun nunan kauna domin sun nuna suna sona da k'awance don 'karshema kacokan nadawo gunsu daxama acikin hotel suke

Sai da nad'an yi sabo dasu Na yan kwanaki Nagano Ashe k'asurgumayen karuwaine masu zaman Kansu kuma karuwanci Mara aji,kaxamin karuwanci domin da kowane Dan iska yin mu,amula suke.

Niko daban saba ba saina ringa mamakinsu ada kafin naxo kasar ana cewa ana wannan harkar k'in yarda nake domin k'asa me tsarki aita girmi haka to Ashe akwai yan iskan amma dai nagarin dole sunfi yawa suma Allah ke ara musu lokacinsu kafin suje gareshi su amsa quiry


Kullum burin su safa da marwa suga ina wannan harka irin tasu bayama kwankwararriyar marwa takancemin" *Ukhty* naga alama bakyason kiji dad'in rayuwa gaki kinada kyau kinada aji gara kawai ki saki jiki kibaiwa maxa dama asha minti abaki kud'i domin kune sune jin dad'in rayuwar duniya

Nakanyi dry ince'indai kudine Wanda nake dashima sun isheni jin dad'i kuwa nabaya danaji ya isa Ni yanzu hankalina ya karkata gida,Nigeria nakeson komawa,  safa tacemin"muma yn Nigeria ne amma muna nan ba ranar komawa anan aka haifemu amma babanmu ya rabu da mamanmu ta koma nigeriar yak'i batamu saidai taxo taganmu kawai ga nan da kk ganmu abinda muke shi namu uban yake ahaka kuma yaga uwarmu ya aura

Nakan jinjina abin araina tab lallai wad'annan sunfi karfina

Aiko dai akwai Wanda yace yana sona ta dalilin su shiya ringa ribata ta yadawo dani hanyar da suke dumu dumu

Nasami kud'i kuwa ta hanyar adnan Wanda shiya dawo dani Nigeria sbd Dan can ne ana yakamamin gidan haya ni nikad'ai yana biya yana zuwa muna holewa daga baya kuma nafi k'arfinsa sbd samun Alhazai da yn siyasa harna gujesa domin akarshe duk zuwan da zaiyi gidan baya samuna Na canza layi sbd shi Na nemi gidan haya natashi daga wanna nakama wanda na tararku da yawa aciki

Alokacin Dana tararku Ku biyu kanku ahad'e yake Aunty Ruby da Sis Zuby ganin nima bahaushiya ce musulma kamarsu sai suka sakarmin komai nima nashiga cknsu muka jone muka zama tsintsiya madaurinku d'aya amma fa bama yarsa mubi namiji mukwana dashi wannan umarnin Aunty Ruby ne domin itama batayi tace muxama masu aji shi yafi don kar arenamu

 To atakaice dai wannan shine k'arshen tarihin Rayuwata Ni laila.

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

*Page 180-185*
Tunda mukai haka da Babana sainaji jikina yai sanyi tunda banga alamar xaibi bayana ba da zancen donko dayace inyasami kawuna da zancen baxan iya tunkarar sa dashiba tunda nasan bazai aminceminba dama dafa Babana ne yaje masa da batun may be ya amince yabarni na k'arasa karatun nawa to dole naja bakina nai gam

Haka abin yaita nuk'urkusata arai har ammaa tagano ina ckn damuwa ta tusani agaba tana tambayata ban b'oye mataba Na gaya mata komai

Ammaa tace"Fiddausi da xaki dauki maganata Dana baki shawarar ki bar zancen karatun nan don baki d'auko wa kanki me bullewa domin kawunki bazai yardaba tunda yafara datse karatun yayarku to nakima dolene a datse kokin fara,kinsan  basa nuna bambanci atsakaninnku Dan haka kicire batun wani karatu aranki.

Tunda Ammaa tafadan  haka kuma naji raina ya dad'a jagulemin narasa inda xan tsoma raina Dan Inji dad'i nasan innajewa baba mallam da wannan batun shima bayan Kawu xaibi shiyasa kawai nak'i tunkararsa da zancen

Ranar wata laraba nadawo daga islamiyya da yamma lik'is nashigo gidan Knn naji munyi karo da mutum ckn xauren a k'ufule Na d'ago kaina Ashe Fatima ce rasai k'anwar ummie aiko ta makamin harara nikuma Na dankota nakai mata mari tahau xagina Na dad'a zuciya naringa kai mata duka amma bakinta be mutuba ana ckn haka saiga Ummie nan tashigo tana ganin abinda ke faruwa tashigarwa Yr uwarta saijinai ankaimin naushi ta baya aiko nasaki Fati najuyo afusace nakai mata wawura muka kacame da danbe nan suka rufarmin mukaita dambatawa innakaiwa wannan duka da k'afa sai inkaiwa wannan da hannu ana haka sai mukaji shigowar Yaya bashir ya buga mana wata tsawa ba shiri muka bari Ummie sai muxurai take da ido Fatima kuma tahau kuka jikinta narawa Dan tsoronsa take nikuwa nahau harare harare ina kad'a k'afa

Yakalleni yace"ke uwar yn rashin kunya meya hadaku dasu  kuke dambe kamar wasu jakuna? Nai masa banxa ina hararar k'asa ya dakan tsawa "ba dake nake ba kkike faman harare harare walh inhar baki ladabtar da wannan kwala kwaln idanun nakiba nixan ladabtar dasu, nakalleshi nace" gasunan kafara tambayar su mana saini Dana tsare maka gaba.

Yace'e kexan fara Tambaya din Dan kece babba amma tunda kin zama babbar banxa Shikenan ke Ummie meya faru?.

Itama Ummien kasa magana tayi Dan batada gaskiya tunda itama batasan ba,asin abinda ya hadamu da fatinba

Dayaga batada niyyar magana saiya tisamu agaba yace muje gurin malam a can zai hukun tamu.....


*nabilancy Luv*💘💘💘💘💘
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧


*4rm*~NabilancyLuv~®

*Page 175-180*
Kowacce cknsu tasaki nannauyar ajiyar zcy Ruby tajanye tagumin datai tace"Gaskiya laila labarinki ma akwai ban tausai domin banda ankawo muku tsaiko a soyayyarki da Nasir tabbas da tuni yanzu kina gdn Aure da kun more kedashi arayuwar Auranku to amma dake haka Allah ya kaddaro muku ba yanda zakui Dan haka ba tare da b'ata lokaci ba feedy mundawo gareki domin jin naki labarin rayuwar bissimillah.

Feedy tai ajiyar zcy ta d'anyi murmushi sannan ta muskuta ta fara da fad'in .....

***********************
Dafarko dai kamar yadda kuka sani sunana Na gaskiya  fiddausi, sunan feedy da ake gayamin kuma nasameshi agurin masoyina kabiru Sisco

Kabir Sisco yasoni sona hakika nima nai masa soyayya ta tsakani da Allah amma iyayena basa kaunata dashi sbd d'abiunsa ba masu kyau bane nikuma Yr babban gidace kakana babban malamine Wanda kowa ckn unguwar keganin mutuncinsa da girmansa haka kuma kakana shike limanci a masallacin ckn unguwar tamu ta "yan dodo.

Malam balarabe da muke kira da baba malam shine kakan nawa daya haifi ubana,haihuwarsa biyu kacal aduniya dasukai tareda matarsa inna larai

Kawu Adamu shine d'ansa Na fari sai kaninsa wato  mahaifina baba Ummaru

 Gidanmu babban gidane ginin zamani ne Na bulo da bulo bana k'asaba,saidai b'angaren baba mallam daban haka Na Babana daban Na kawu Adamu daban.

Kamar yadda Babana keda rufin asiri haka kawu Adamu kedashi ba laifi saidai samunsu ya bambanta da Babana shi kawu principal ne a makarantar maxa shikuma Babana be xirfafa a bokoba saiya tsinduma a harkar kasuwanci nan da nan Kuwa Allah yasaka masa nasibi yake samu

Mahaifina duk abinda zaiyi saiyai shawara da d'an uwansa kawu Adamu duk wasu filayensa dayake siya saida amincewar kawu hakama takardun agun kawu yake barinsu ajiya yanada kau dakai a abin hannunsa hakama baida fad'a sanyine dashi mgn ma bata dameshiba duk abinda zasuyi iyayansu suna saka musu Albarka baba mallam yanajin dad'in abinda suke yi Na had'in kai

Mahaifiyata macece me hkr inace mata *Ammaa* sunanta Na gaskiya halima nikadai ta Haifa aduniya amma ta yiyyi wabi, b'ari yayi sau 5 matar kawu Adamu tana nuna mata faccalanci sosae sbd ganin yanda Babana ke mata facaka bata nemi komai ta rasaba gunsa gashi dama iyayanta sunada Arxik'i Yr garin jigawace a dutse

Kawu Adamu mutum ne me xafi yanada fad'a kaf yaransa tsoronsa suke har matarsa Asiya da muke kira da mami, nikaina da nataso da fad'a da saurin fushi da xcy nasan shina gado ko ba,a fad'a ba ba a min lefi inkyale a aji kaf ckn sch dinmu bana tsoron seniors d'ina balle yn made dinmu

"Yayan kawu 5 maxa biyu mata uku babban d'ansa Yaya hamxa yanada kirki yanada ilimin addini hr gemu ya tsayar mutane suna cewa da alama shine zai gaji kakansa mallam Dan Abokansa ma da d'an uztaz suke kiransa

Yaya bashir kebi masa ba halinsu d'aya ba domin shi Yaya bashir akwai tsare gida baya kulamu kannansa balle yajamu da wasa kamar yadda Yaya hamxa ke mana

Gashi da shan k'amshi duk karatu suke a buk shi Yaya hamxa yana matakin k'arshe digri shikuma Yaya bashir matakin farko yake a digirin Aunty Atika ita kebin Yaya bashir tana gidan mijinta a karkasara ta Dade da Aure tana yin candy aka Aurarta Dan kawu yace bazai bar " ya mace ta gand'ame agabansaba da angama krt zai ringa Aurarwa gara in anje gdn miji inxai bari ayi acan karatun namiji zai fad'ad'a

Ummie itace Sa,ata wacce kanmu d'aya da ita sch d'aya muke amma ba aji dayaba tana B, ina A,  kanwarmu bata jik'uwa da ita sbd ita Yr jinkaice ga k'arya da d'agawa kuma bata k'aunar ta ganmu da kB shiyasa nima natsaneta da xarar munhad'u a hanya mun xanta saita fad'a agida anci mutuncina sbd anhanshi zuwa gidanmu

Ko tashi akai daga makaranta kowa hanyarsa daban kota rigani zw koni inrigata tun ana mana fad'a hardai aka zuba mana ido a gdn

Fatima itace Autarsu nagirme mata sosai fati tanada tsokana ga giggiwa da reni.

Alokacin Dana kammala karatun secondary dina sai kawu yace nida Ummie mufito da miji Aure zai mana

To nikuma Wanda nakeso din yace shi bazai Aure bashida aikinyiba kb yacemin yafi son naci gaba da karatu kafin nan shima yasami aikin yi yasandai akan hakane yn gidanmu basa sonsa atare dani


Dayake science class nayi sainake da burin Na karanci medicine ba fargaba na samu Babana da zancen amma saiyace inje ingayawa kawu abinda duk yace shi xa,ai...

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧
*continue page 180-185*

Saida mukaje gaban baba mallam sannan Yaya bashir yace"Fatima koro min jawabin abinda ya hadaku kuke fad'a "

Fati ckn in inarta tace"walh Yaya laifin Fiddausi ne... Ckn k'unar rai da zafin zcy nagalla mata harara nace"laifin uwarki'

Aiko Yaya ya kawon wani mugun duka a bakina,narige gun ina fadin'wayyo Allah walh saina fad'awa Babana wannan ai cin zaline cknsu babu Wanda ka daka saini sbd ka tsaneni,

"Maxa kije ki fad'awa baban kada k'uda ya rigaki banxa Mara kunya saina xubar mk d hakora wataran inhar baki canza haliba.

Na buga tsaki natashi da gudu nai cikin gida sashenmu ina gunguni harya mik'e danya biyoni amma baba mallam ya tsaidashi" Dakata basiru kaima bakada hakurin kuma baka iya sarrafa yara ba,aibata haka zaka Ni da itaba...."amma mallam Fiddausi batada kunya ko kad'an

Mallam yai murmushi yace"hhhhmmm  duk wannan halin nata kawunta ta gado saidai ita dayake macece shiyasa akafi ganin tsiwarta sai a hankali zata dena bari ta kara wayo dole xata rage yanzu akwai yarinta a ckn lamuranta kayi hkr..

Yaya yai kwafa yace"haba mallam yrnyr da take kula samari shine xa,ace da ita da yarinya ackn lamarinta bata da wayo ai walh daka barni yau saina koya mata hankali.

Inna larai da batai mgn ba sai yanzu tace"hkr xakai da wad'annan k'annan naka basiru yaran xamani ne sai ahankali inkace zaka ringa biye musu to zasu rainaka ne abanxa,

Yanda yabar gun a zuciye haka su Ummie suka bar gun sum sum

Da suka sami mahaifiyar su da mgnr fad'a tai tayi meyasa Yaya bashir beje har dakinmu ya tattakani ba shikam dayake  a k'ule yake baece uffanba.

Anyi haka da kwana 2 baba mallam ya Tara iyayanmu maxan da yayyena maxa yace yanason ya bayyana musu wani k'udiri dake ransa Na son ya had'a Auren bashir da Fiddausi

Aikodai iyayanmu sunyi murna sunyi Na,am da xancen Wanda shi gogan abin bai masa dad'iba domin baetaba jin son fiddausin aransaba gashi jininsu dama bae haduba Dan dai ba yanda xaiyine be isa kuma yai musu turjiyaba sunaiwa iyayansu biyayya sosae

Da zancen yaxo kunnan Ammaa duk saitaji ba dad'i donta san baxan amince inada Wanda nakeso, tasameni da xancen da daddare ina falonta ina kallon ta koromin bayanin yanda baba mallam yatsara Na had'in Auranmu da yya bashir aibansan lokacin Dana mik'e tsayeba ina fad'in"nashiga uku ni Fiddausi arasa dawa ma za,aimin Auran dolen saida babban makiyina Wanda baya k'aunata ko kad'an to walh ba,a isaba.hannu Ammaa tasa ta toshen baki da sauri"haba Fiddausi meyasa zaki fad'i haka a kullum ina gaya miki ki ringa koyawa zuciyarki hakuri akoda yaushe domin kici ribar zaman duniya kinsan dai tunda baba mallam ya tsara kuma iyayenki sunyi Na,am babu me wargaxa wannan had'in sai Allah kuma tunda shi yana namiji ya amince baeja dasuba toke baki isaba Dan haka kiyi hkr Fiddausi kisa dangana aranki xan miki addu,a wataran insha Allahu wataran zakiso shi shima zai soki,

Na rushe da kuka Dan tuno da masoyina kB Sisco tabbas sunyi hakannema Dan suga sun rabamu gabaki d'aya Ammaa ta janyoni jikinta tanata lallashina.

Itako Mamie mahaifiyar Yaya bashir taji dad'in wannan had'in don tasan gaba takaisu tunda Na kasance Ni d'aya kwal gun iyayena zansha gara kuma danta ya huta da wasu abubuwan duk da itanma ba wani qaunata takeba haka tasa Yaya bashir agaba da dabara tana rarrashinsa akan yai hkr ya amshi kyautar da aka masa Na Aurena"kaga inkai haka tamkar kayi jahadine sbd ita tafison wancen d'an iskan yaro da akace ko sallah ba duka biyar d'in yake arananba wasuma suna cewa kiristan ne,gashi kuma zaka gyarata ta daina rashin kunya kada ka damu ko daga baya saika Auro duk yarinyar da kakeso ka Aura baxamu hanaka ba

Washe Garin da akai haka natashi takanas naje nasami kB nake fad'a masa komai akan yanda xa,a rabamu "yakamata kayi wani abun kB walh ina sonka kuma baxan iya Aurar wanin kaba,.

KB ya k'uran ido yana kallona yace" yanzu feedy kina nufin Aure iyayanki ke shirin yi miki? Na gyada kai "kwarai kuwa kuma walh tunda kakana ya tsara hakan ba makawa za,ayin kuma da makiyina Yaya bashir suke shirin yimin Auran,

Kb yai murmushi yace" tun farko naso inbar garin nan da naga alamar hakan tunda aka hanani zw gidanku,to Amma yanzu dole kafin faruwar ganin hakan a idanuwana dole nabar garin nan.

Nace"ina xaka tafi kabarni kB? "Zanshiga duniya feedy kinsan Ni maraya ne dama ba wani gata gareniba shiyasa nake ganin bak'in ck iri iri arayuwa,


Nace" kb duk inda zaka xanbika ina tare dakai kB Abadan daiman har k'arshen rayuwata..yai murmushi yace "Allah zaki iya bina kibar iyayenki?

Nace " kwari kuwa sona hakika nake maka'

Yace"nasani feedy, nasan kina min sona gaskiya ba algus Alla yabarmu tare,"nace,Amin"


Mukai sallama dashi yarakoni har kusan layinmu anan asirina ya tonu Yaya bashir ya ganmu ya kallemu kawai ya d'auke idonsa nikuma Na maka masa harara Dan harga Allah tsanarsa ce ta k'aru araina....

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 185-190*
Ina shiga zauren gidanmu nai karo da mutum atsaye ya had'a rai yana kallona ido ckn ido Na d'auke kai zanwuce ta gabansa yasha gabana yana fad'in "Mara kunya kinsan ke nake jira ai dawa naganku a hanya?

Nace" Ni kuma ? Ni bani ka ganiba...kafin nai shiru saijinai yaja kunnena yai ckn gida dani ina ihu ina fad'in nika sakeni walh inkajimin ciwo baxan yardaba
B'angaren baba mallam yanufa dani zaune muka tararsa akan tabarma yana ganinmu ahaka yace"basiru kaida mutuniyar takane, mekuma tayi yau haka xa,a cire mata kunne,

Yaya bashir yasakeni yana fad'in "gatanan mallam walh batajin magana can naganota da wannan d'an iskan yaron can me saka sark'a awuya da yawo da matsatstsen d'an wando iya guiwa Wanda bashida tarbiyya,

Aifa saiya k'ara k'ularni da wannan mugayen kalaman dayake kiran masoyina dasu Na harareshi ina murgud'a masa baki ya kawo hannu zai mareni baba

 mallam ya dakatarshi"Barta basiru banda duka ai ba,a dukan mata inhar kasaba dukanta ko anyi Auranku ba dainawa zakaiba a kullum ina fad'a maka gara kayi fad'a ko nasiha shiyafi kuma kadaina aibanta shi haka gara ai masa addu,ar Allah yashiryeshi wai a ina yaron yakene? Ke Fiddausi ba anhanaki kula shiba ko bakisan da maganar Dana tsara atsakanin Ku da basiru ba?

Ckn b'acin rai nace" mallam inma mgnr Auran wannan mugunne walh banayi,Ni ba sonsa nakeba gara abarni in Auri Wanda nakeso shikuma in bashida wacce ke sonsa sai a nemo masa a hadasu...

A kufule da jin kalamaina Yaya bashir yace" da angaya mk Ni d'in sonki nake?walh banda darajar su mallam ke baki isa injera dakebama balle in xaman Aure,matan dake sona kuma sunfiki aji da kyau tunda inba rashin ajiba meye alfanun bin d'an iska kina sonsa shikuma yana yawon zuwa party da bin club club da "yam matan bariki

Baba mallam yace" ya isa haka basiru bekamata kana biye mataba kaifa namijine kadaina b'ata namiji d'an uwanka xato zunubi,inma yana yi to abishi da addu,a

Ke kuma Fiddausi inhar baki rabu da yaronba to zamu kai k'ararsa gun iyayansa suja masa kunne kuma bari kawunki yaxo tunda kunfi shayinsa akan kowa, naga alamar kin fitsare kafarki akansa Ni abinda yasa nahad'a ki da basiru sbd akarfafa zumunci a  tsakaninku ina tausayinki sbd bakida dn uwa ko Yr uwa a gaban iyayanki Amma ke bakya tausayin kanki Dan haka zan miki Addu,a akan Allah ya shirya mana ke.

Na buga k'afa ina gunguni nabar gurin baba mallam ya bini da kallo shikuma yaya bashir hararata kawai yake

Anyi haka da kwana 2 kwatsan saiga waya daga jigawa mahaifin Ammaa ya rasu dama babarta ta dad'e da rasuwa aiko anyiwa Ammaa kara agidan motoci uku akai aka tafi ta,aziyya jigawa gidansu

Aranar suka juyo suka baroni da Ammaa acan sai ranar uku suka dawo mana gaisuwar sadakar uku, daganan kuma Babana baedawoba sai ranar sadakar bakwai dayaxo yace mubishi mukoma Ammaa taso yabarta ta k'ara kwana amma bababbaba yace Sam tunda anyi addu,a kowa ai watsewa zaiyi tai hkr nan da kwanaki zai dawo da ita haka muka taho dama Ni aranar inatajin rashin lfy banda kuxari ajikina

To Ashe rabuwa da iyayene yasa domin aranar mukai wani mummunan hatsari ahanya atake Babana ya rasu Ammaa kuwa saida ta kwana a asibiti sannan tace ga garin kunan nikuwa kwana biyu a asibitin bana ckn hayyacina banji ciwo ko kwarxaneba sai buguwa danai a k'irjina da kaina

Nasha kuka kamar raina zai futa rashin iyaye akwai ciwo bayama inna tuno da ranar rabuwarmu munata hira ackn motar Ashe hirar k'arshe mukai dasu Shikenan gatana ya k'are aduniya.

Na dawo abin tausayi ranar sadakar bakwai din Amma tunda Babana ya rigata rasuwa Amma tare aka had'a addu,ar an cika damk'am anata koke koke yn jigawa sunxo sukam abin biyu ya hade musu aranar ina kwance akan cinyar kakata inna larai idanuwana sun xurma dukna rame ba doleba naxama marainiya ta k'arfi da yaji toko wace irin sabuwar rayuwa kuma xan shiga ta rashin iyaye acknta?


*nabilancy Luv*
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 190-195*
Aranar sadakar arba,in d'in iyayena kuma muka shiga wani tashin ckn dare ciwon ciki ya turnik'e baba mallam Wanda yaxamo ajalinsa Dan ko awa ba aiba yace ga garin kunan

Fadar irin halin da aka shiga agdn nan b'ata bakine don ba Wanda ya rintsa gida cika yai mak'il wasu nata koke koke shi dama Kawu Adamu fad'uwa yayi aka kwasheshi sai asibiti ba,a sallamo  shiba saida akai ukun baba mallam dama tunda Babana ya rasu Kawu ya rasa kuxarinsa kullum baida lfy alhinin bae sakeshiba ga kuma wannan datafi gigitashi

Inna larai takaba ta kamata dama Ni ina dakinta tun rasuwarsu Ammaa bankoma sashen mamieba kamar yadda ta buk'ata niko baxan iyaba Dan nasan babu me k'aunata a cknsu kuma baxan dauki raini ba banda hkr komai sukaimin xan rama babu bata lokaci

Duk wani nauyi nawa Dana inna ya dawo kan Kawu Adamu shike kula da komai namu, dama duk dukiyar Babana tana hannunsa wasu yana juyawa, haka kullum in zai fita xaishigo sashen inna ya gaidata ya dire mata kud'i ya fice daga gun mamie kullum ana aiko mata shayi a flask dinmu da kayan had'i haka da rana in an girka abinci hr dare ana aiko mana.wannan ixinine daga Kawu

Tun bayan rasuwar  baba mallam sai limancin masallaci ya dawo kan Yaya hamxa dama yakan d'anyi tun baba mallam Na nan

An sassaka ranar Aure a ckn gidanmu anasaka ranar Aurena da Yaya bashir wai wata biyar sai Ummie itada d'an abokin Kawu sai Yaya hamxa shida wata k'anwar abokinsa duk xa,a had'a ayi tare nanda wata biyar nidai duk jinsu nake don bawani Yy bashir da xan Aura tunda basonsa nk ba kuma baxan tsaya inaji ina gani aimin Auran dole ba

Har a lokacin inada k'udirin bin kB mutuwar da aka yiyyimin ce ta kawo mana tsaiko wani saka rana da akaimin baya gabana Dan kullum innaso zanje inga masoyina agun da muka sake Na had'uwa


Ko kallo Yaya bashir be isheniba babu wata mgnr Arxik'i a tsakaninmu inxai wuce in wuce babu me tankawa dan,uwansa cknmu nicema in yn tsokanar suna kaina nakanyi tsaki Dan yaji ya k'ulu dani to wani zubin shareni yake ya nuna tamkar baejiba Amma wani zubin in yn rashin hkrn Na kusa kufula yake dani ya kawon duka nikuma Na xille aguje.

Akwai ranar da muka keb'e nida kB yake cemin"anya feedy kuwa baki canza kudirinki Na bina ba kuwa? Lokaci nata tfy,kadafa nan gaba Inji ance andaura auranki ina ZAMAN jira, hhhmmm aiko walh inkika yarda kika Auri bashir kika xauna saina kasheshi...

Nai saurin kallon kb ina mamakin  furucinsa,ya gyad'a kansa tareda kallona ido ckn ido"ban fad'a donjin dad'in bakinaba nafad'a har ckn raina walh akanki babu abinda baxan iya aikatawaba, ina mk sonda bantab'aiwa Uwata shiba sbd ban sanma son uwarba tunda bantaso tare da itaba bata raye, feedy Ni maraya ne mahaifin nawama baxama yakeba kullum baya gari yana buga bugarsa nmn Na abinci

Ni yanzu ke kad'ai nake tsumayi agarin nan da tuni Na d'aware don haka ki fadamin ranar da zamu tafi kawai,

Nace"akwai abinda yasa kaga nai shiru da xancen lamfo nai musu kB so nake sai biki ya k'arato saimutafi  yanxufa yanxufa saura wata guda Dan haka ka jirani ckn satinnan inaso in sama mana kud'ad'e agun angon kaga dole saina sake Na nuna musu kamar inaso,Amma kuma wane gari zamu nufa?

Ya Sosa k'eya yana dariya "garin Kaduna zamuje akwai dangin Uwata a can zan nemi kwatance inmunje.kada ki damu nima zan d'an nemi nawa kudin sbd mui guxuri

Mukai sallama dashi nakoma gida ina tunanin wannan katob'ara da nake shirinyi

Saida biki ya rage saura sati 2 nasamu inna larai a d'akinta tana linkin kayanta Na zauna a gefen tabarmar nace" inna dama wani taimakone nakeso kiymin "

Tace"to Na meyefa?

Nace"Dan Allah kisamu Yy bashir ki karb'amin kudin da zanyi hidimar biki dasu kinsan ba wani hirar kirki muke dashiba.

Inna ta harareni "ke kinga banason guntun iskancinku Na yaran zamani inxaki zage ki karb'i kud'i ki xage ai duk laifinki nake gani kefa macece inshi yana shareki keba saikisan yadda zakiyi ya dainaba ya dawo kasanki macecefa ke,ko baki iya kissa ba?indai baxaki karb'a da kankiba to ba abinda xan iya miki akai.

Tana ckn wannan surutun saiga Kawu yashigo da sallamarsa muka amsa masa ya zauna gavan inna ya gaidata,

nagaidashi ya amsa yana fadin" inna meke faruwa keda k'awar taki?

Inna tace"kaganta nan tasani agaba wai adole Ni take so nakarb'a mata kudin da zasuyi partyn biki gun basiru ita baxata iya tambayaba nikuma nace nima baxan tambayar matan ba saidai kkada ayi partyn,inbanda iyayi mace da mijinta ta ringajin kunya ina dalili yana dn uwanki


Kawu yai murmushi yace"Fiddausi kamar nawane zai ishekin?  Nace"Kawu dubu hamsin ba wanima taro sosae zanyiba.

Ya xira hannu a aljihu ya xaro bandir d'in dubu dubu ya mikon yace"ga dubu d'ari asatin nan lefenki zaizo hannunki saiki zabi Na dinki kikai keda Ummi.

Naiwa Kawu godiya natashi da murnata Na fice Na nufi gun kB cancakas Na bashi kudin nan Dan ya ajiye agunsa muka tsaida ranar guduwa sati d'aya lokacin biki ya rage sati Knn.

A ckn satin nahau yn shirye shiryena a b'oye Amma saina dawo sakarwa Yaya fuska inmun had'u nakan gaidashi yakan amsamin shima ckn sakin fuskar nasan zaiyi mamaki Amma banda gaisuwa bana yarda wata mgnr tasake had'a mu....


*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

*Page 195-200*
Aranar da  zamu gudu aka bugo I.V d'in bikinmu wannan baisa Na karayaba,kona canxa kudirina saima Karin k'arfin guiwa Dana dad'a samu daga b'angaren zcy ta, aranar banyi bacciba inata fakon naga hankalin inna baya kaina, tun a Daren naso nagudu gun kB mukwana tare Amma bansamu wannan damarba sai da asuba natabbatar maxan gidan sunfita masallaci gidan a bud'e Na hado kayana inna tana band'aki Na silale sai inda mukai alqawarin had'uwa da kB yana ganina yahau jinjina min naganin yanda Na zama gwarxuwa jajirtacciya Mara tsoro yace lallai yakara yarda da son da nake masa insha Allahu zai rik'e Ni amana.

Muka rankaya zuwa tasha motar farko data tashi tamuce sai kd

Ban tab'a xuwa kadunaba sai a wannan rana gidan abokinsa muka dira Abdul abokinsa Na ashararanci saurayine shi kadaice ne agidan uwarsa ce tamutu tabar masa gadonsa tunkafin ubansa ya rasu Knn

Banda kowa a kd sai kB shine yaxama Uwata yaxama ubana saida nadau yn kwanaki Na iya sakin jikina tare muke kwana a d'aki daya haka kuma inya bukaci yatab'ani bana iya hanashi tunda shinakewa tanadin dama kuma nasan yana sona ina sonsa,

Mukan fita yawon shak'atawa Ni dashi wataranma harda Abdul d'an rakiya mukanje mashayarsu inta kallonsu suna tittilar abarsu bantaba sha,awar shantaba Amma saida kB yasa nashata wai zatasa namance damuwa haka yasa nakoyi shan giya ta k'arfi da yaji kullum sainashata kud'ad'en da mukaxo dasu su mukeci musha ack abinmu

KB yanada d'an banxan kishi bae yadda Na futa nikadai ba ko yaga mutum yana kallona nantake zai taka maka burki yace matar saceni

Akwai ranar da baxan tab'a mancewa da ita ba ranar da wani babban Al,amari ya Auku Wanda ya girgixani mutuka gaya nashiga d'imuwa awannan rana

A gidan mashayar giyar da muke zuwa mukaje nikadai nasha tawa shikuma aranar yace baya sha,awar sha Amma bari ya futa yanemo sigari,nai mamaki Dan ya dad'e baeshataba da yace ma yadaina Shanta gaba d'aya

Ya d'au mintina da fitarsa saiga wani matashi yaxo guna muka gaisa yake cemin tunda naxo gun yaganni yaji duniya bawacce yakeso saini,giyarma dayazo sha yaji cknsa ya cika ba saiya shaba duk ganina dayai ya k'osar dashi,yana da barkwanci sosai yaringa bani dry ina darawa.

Muna haka saiga kB ya dawo aiko Ashe tundaga nesa ya d'auko kwalba yana zuwa ya rotsawa wannan gayen shiko wannan saurayi yana tashi ckn layin jini da k'arfin hali irin nashi shima ya d'au kwalba ya dab'awa kB a ciki kB ya rik'e gun yai k'arfin halin d'aukar wata Kwalbar ya cakawa gayen a wuya nanfa sukaita cake cake har sukai mutuwar kasko,

Wai?naga tashin hankali awannan ranar Ashe ba,a raba fad'a a mashaya ina ihu ina kururuwa nai waje saiga yn sanda sunshigo gun sainaga wasu suna darewa suna guduwa.

Nima saina ari kafar kare Na garxaya naje nasami Abdul a shagonsa yanata had'a kaya a akwati yana ganina a firgice yahau tambayata meya faru?

Nan Na zayyane masa komai Abdul yace"tabdijan gara kema da kika gudu Dan walh da "yan sandan nan sungano kece silar faruwar fad'an nan da kashinki ya bushe,Dan yan sandan kd ba mutunci ne dasuba yanxuma ba tsira kikayiba don suna tsaurara bincike zasu gano inda kk Dan haka zan taimakeki kibiyoni maxa muwuce abuja dama zantafi yanzu.

Ckn rawar jiki da murya nace" Na amince Abdul zan bika.

To tundaga wannan rana da muka taho Abuja bansake komawa jahar kanoba ina tare da Abdul a hotel daya kama mana Na tsahon wata biyu Amma fa yana fanshe kud'insa da yake kashemin ajikina,kullum ina tunanin kB Allah sarki Allah ya jikansa

Abdul shiya buden ido hartakai inabin wasu maxan a ckn hotel dinma dayake yasan ba soyayya muke dashiba baetab'a jin haushiba balle yasamin doka akan yahana kula maxa

Takai takawo nabar wannan hotel d'in nabi wani saurayi me suna Faruq Wanda ya kamamin haya nikadai abina yana kashemin kud'i ya buden account yana d'uramin kud'ad'e  soyayya muke dashi Amma bae b'oyeminba yace shiba da Aure yake sonaba yanada wacce zai Aura tun kafin muhad'u tobanji haushiba sbd be b'oyeminba balle gaba ince ya yaudareni

Aranar da ya gayyaceni wani party Na abokinsa anan naganku Ku uku kunci kwalliya ankon dayaimin Na wani gown din doguwar Riga ta farin yafi da kwalliyar light fink da gyale kalar kwalliyar shi kuma kuka saka anan naje nasameku muka gaysa Na zauna a kusa daku da aka tashi dg partyn Na sameku nace muku inason inyi k'awance daku niba "yar garin nan bace banda kowa toko tausayina kukaji nan naga kun amince min Aunty Ruby da sis Zuby da laila ukty kune kuka janyoni jikinku naxamo wata Wanda daga k'arshe gashi ta dalilinku zan koma gida gaban iyayena

Wannan shine k'arshen labarina Ni Feedy

*nabilancy Luv*💘💘💘💘
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 200-205*
Sukai ajiyar zuciya gabaki d'ayansu Zuby ce tafara magana"agaskiya feedy a ckn labarin ki naga abubuwan da kikayi Wanda baki kyautashiba totally laifinki yanada yawa domin bakiyi biyayyaba da ace keme biyayya ce ga mahaifa da baxaki guduba akan xa,ai miki Aure da Wanda bakyaso,ki dubeni mana kikuma tuna da nawa labarin nayiwa mahaifina biyayya nabi wani qato kasar Dubai duk Dan inkyautatawa dadyna kuma aka rabani da Wanda nakeso Aliyu akace dole saina Auri *b* *kamal* a bana sonsa akai wannan tfyr har ya aikatamin akuyanci....

Ruby tace"kwarai kuwa abinda Zuby tafad'i gaskiya ne feedy nikaina na Auri Wanda banaso kuma Na xauna dashi nayi biyayya bayan rai to Amma ke tunda ran iyayanki ma kince mahaifiyarki tasha yi miki nasiha akan kixama meyin hkr da juriya Amma baki d'au maganar tab'a haba feedy yanzu da muke da niyyar komawa ga gidajenmu inkin koma me zaki fad'awa Kawu ya yarda dake.?'

Feedy tashare hawayen daya gangaro mata tace"Aunty Ruby keda Sister Zuby kunyiwa mahaifanku biyayya ne ba wai Wanda basu suka haifekuba nifa asali ba Babana ne ya tsara zaimun wannan Auranba k'rfa k'arfa akai masa bae maganaba danba yadda zaiyine, Kawu ba shine ya haifeniba Amma zaimin dole "yarsa daya haifama Wanda take so za,abata kufa duba wannan lamarin Ku tausaya min nima,

Laila da kanta ke k'as tunda aka fara tattaunawar sai yanzu ta furta cewar" Ku tsaya Aunty idan har kince Kawu bashine yahaifekiba Amma tunda babu mahaifinki dole shine a matsayin madadinsa kuma shine bangwanki shiya wajaba kiywa biyayya,walh dama nice ke saboda kinganni nan bankaiki gataba,sbd mahaifina baida d'an,uwa da suke ciki d'aya banida kakanni Na gurin uba,saina uwa da ayanxu haka gunsu zan nifa su suka zamemin dole,niyanxu Ni nakema inama xan samu iyayan da zasumin dole aduniya da walh nayi musu biyayya kawai Dan naci ribar duniya,

Aysha Auta "ai gaskiya Aunty feedy kin tafka babbar katob'ara Wanda koni da bansami iliminki ba baxan yi abinda kikayiba,duk Wanda bashida gata a yanzu dai saiyayi kuka da ace Allah yasa kin hkr kin zauna zaman Aure da Yaya bashir watakil da tuni yanzu kun haihu Allah yasako muku son junanku,kuma banda Allah yasa kB Sisco me gajeran kwanaki ne aduniya da kinyi nadamar bin namiji uwa duniya domin Na tabbata da saiya nuna miki halin nasu da saiya yaudareki ya gudu yabarki, ki duba labarin Aunty Zuby yanda ta baiwa Al,amin amannar zuciyarta mana Amma daga k'arshe ji yarda yai mata kuma yaso yaci amanarta ta hanyar tarayya da kawarta Karansy Dan dai kawai Allah yasa ta ganosu da wurine tai musu ta yn bariki itama da tuni yasa mata cwn zcy.

Auta nayin shiru dukkansu suka hau tafa mata suna dry Ruby tace" yayi yayi simolin mu gaki k'arama Amma akwai hangen nesa,kinburge kinada fad'in gaskiya kindai ji feedy dafatan zaki gyara komai inkin koma gida.

Feedy tana murmushi ta gyada kai tace"insha Allahu'

Auta tace"Aunty Ku duba agogo fa d'aya tayi Na dare,tab! Bantab'a kaiwa haka banyi bacciba

Ruby tai dry tace"to sleeping sickness me cutar saurin bacci duk abinki a yau dai saimun gama zamu kwanta bissimillah fara bamu naki labarin musha.


***********************Sunana Aysha nafito daga k'auyen d'an dume mu Fulani ne gaba da baya asalinmu da a ruga muke duk dangin Babana da Mamana suna can Babana ne dai ya taho gari ta hanyar wani uban gidansa dayake siyan shanu gunsa yabiyoshi tareda iyalinsa mamana ce dani ina k'arama alokacin nikadai suka haifa Dan hakama suke kirana da Auta Amma dawowarmu d'an dume da zama sai yn k'auyen suke kirana da Indo,

D'an gidanmu k'arami ne da muke haya acikinsa Alh yaro shine ubangidan mahaifina yanada kirki sosai shine kebiyan kudin hayar da mukeyi awannan gida

Alokacin Dana kai shekara goma sha biyar sai Alhaji yaro yacewa mahaifina mexe hana yabashi Ni yakaiwa matarsa tarik'eni kotaji dad'i don bata tab'a haihuwa ba shekarunsu a shirin mahaifina baeja dashiba sbd banida nisa da gidansa inna wuro mahaifiyata itacema ta nuna damuwar abin aranta Amma dataga kyakkaywan rik'on da hajy maryam matar Alh yaro takemin saita saki ranta,

Nak'ara kyau dama gani fara ga gashi saidai banida jiki komai tasamo nitake kawowa dayake iyayanta a brni suke tana siyo kayan gyara ta gyarani Na fito fes dani,dataga ina k'ara zama budurwa saita shiga koyamin girkin zamani danni babu abinda Na iya alokacin sai dama futa da Dan wake da dambu da alala sai biski, aikodai nakoyi wasu abubuwan Wanda ko gurin kunya naje xanfutar da kaina wajen girke-girken yn burni Dan har had'a lemuka ta koya min gata da tsafta

Saidai kash! Bamu shekara da ita atareba Allah yaiwa Alh yaro rasuwa babana jauro yaji wannan mutuwa don sunyi sabo dashi tunda har kwastamomi yana kawo masa masu siyan shanunsa

Tunda Haj maryam ta gama takabarta saita koma birni gaban iyayanta nikuma Na dawo gaban iyayena

Tofa ana wata ga wata saida zaman wannan kauye yaiwa inna  wuro dadi tai sabo da mutane sosai ana mutunci da makwabta da yn unguwa sai Babana jauro ya fad'i ya mutu aiko munshiga tashin hankali da d'imuwa sosai....

*nabilancy Luv*💘💘💘💘
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧


*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 2005-2010*
Bayan shekara d'aya da rasuwar mahaifina sai inna wuro tayi niyyar ta koma ruga gun danginta, Amma fafur sai aminiyarta dasuke makwabtaka baba jummai tahanata tabata shawarar gara ta zauna anan tayi "yn sana,o,inta tasamu ta Aurar dani Amma inta koma gida ai nauyi xata d'orawa manyanta

Haka ko akayi domin inna wuro ta d'auki shawarar baba jummai saitake yn sana,o,inta tana kuma d'oramin tallar fura da nono a duk ranar laraba nake kaiwa kasuwar mu don aranar takeci ina ciniki sosai.

Akwai wata ranar kasuwa Dana kai tallar fura wani saurayi d'an gayu dashi yasani Na dama masa ta d'ari biyu, Na dama masa Na mik'a masa yashanye ta tas yana santi, ya mik'on Dari biyar yace " kai Amma Yr Fulani da alama kina hadawa da Zuma ckn furarki,?

Nai dry nace"aiko dai babu wata Zuma aciki banda kayan k'amshin da aka dakata dasu tosai sugar da nono Dana dama maka dasu

Yashafa k'eya yana kallona da murmushi kan fuskarsa yace"to Amma gaskiya furarku daban take da saura don ko a birni bantab'a shan wacce takaita dad'iba, zubomin ta sauran canjin Na kaiwa kakata itama tasha gangariyar fura.

Nai murmushi kawai Dan dama Ni magana bata dameniba.

To haka dai wannan saurayi ya zama kwastama Na duk ran kasuwa saiyasha furata yatafarwa da kakarsa itama,daganan kuma ba sai soyayya ta shiga tsakanin muba, shine harda biyoni gidanmu tad'i.

Jamil sunansa kyakykyawane dogo wankan tarwad'a Yanada dogon hanci da dara daran manyan idanunsa da d'an sajensa daya k'arawa fuskarsa kyau.yacemin a ckn unguwar tarauni yake gurin kakarsa yake zuwa k'auyanmu wacce ta haifi ubansace tana sonsa sosai Hutu yake zuwar mata d'an makaranta ne karatu yk a Buk yana matakin k'arshe digri

Munyi sabo sosae da jamil saidai mutum ne shi me surutu yana kuma da barkwanci.

Saida yai wata biyu yake gayamin xaikoma gida hutunsa ya k'are saida naji ba dad'i araina domin "yan iya magana sunce sabo' da dad'i rabuwa da wuya,yaita kwantarmin da hankalina,yace zai dawo gareni Amma zai dad'e don semester d'insu doguwace,hargun kakarsa inna binto ya kaini tsohuwar Arxik'i ta nunan kauna itama aranar da zai tafi mun dade tare a k'ofar gidanmu yana jaddada min cewa" Aysha ki rik'en Alqawari Dan Allah kada kiyarda ki Auri wani kfn nadawo walh ina sonki mahaifina bazai yarda nai Aure yanxuba harsaina gama krt,da xarar nakammala zanyiwa magabatana zancen Auran ki


Wad'annan kalamai haryanxu suna ckn k'okon raina sun kasa goguwa harna bar k'auyen jamil baedawoba

Babban dalilin daya baro dani dg k'auyen nan baba jummai ce Wanda kuma haryau bankoma shiba

Taxowa da inna wuro bayanin cewa tasamomin gidan da xan ringa aiki a birni za,a ringa biyana Albashi me tsoka,matar da xanwa aikin tanada kirki kuma yarinya take so me jini ajika.

Inna wuro bata yiwa baba jummai gardamaba domin ta aminta da ita tasan baxata t'aba cutartaba.

Jin inna wuro ta amince yasa nima Na aminta nahau shirin tfy birni sbd k'aunar da nake akullum naganni a birnin.

Aranar da muka dira a birnin ckn Unguwar sokkoto road gidane tangameme sunan megidan Alh iliyasu kantoma matarsa d'aya Haj Azzumi.

Aljannar duniya wannan falo Na hajiya Dan nasha k'auyanci Na ringa lallatsa luntsumemen kafet d'in tsakar d'akin axatona bargon rufa ne ga wata k'atuwar TVn  bango data d'auke hankalina daban tab'a ganin irintaba har Hajiya tashigo falon bansan tashigoba saijinai baba jummai Na gaidata,figigit nadawo nutsuwata Na durk'usa hr k'asa nagaidata ta amsa min bayabo ba fallasa fuskarsa dai ba fara,a gata k'atuwa lesin jikinta kawai abin kallone ga sarkar gwal data cika kirjinta tana shek'i. Ga zobuna nan reras a yatsinta

Haj tasake kallona shek'ek'e tace"jummai wannan itace yarinyar da kk ce zaki kawomin?

Baba jummai tace"eh itace ranki ya dad'e dafatan tayi?

Hajiya ta gyada kai tace'tayi ba laifi Allah yasa dai ba kaxama bace kamar waccan data gudu dafatan kuma ta iya girkinmu
Na burni ?

Da sauri Na gyada kai nace"Na iya wasu sosai harda had'in lemuka Na iya akwai wacce Na koya agunta,

Ta gyada kai "to Yy banda girki sai share share da goge goge Na d'akina da falukan gidannan da kuma dakunan maxan gidan zaki ringa gyara musu da kula da abinda zasuci safe dare rana dafatan zaki iya duka? 

Nagyada kai nace" eh"

Tace "to ina zuwa" tamike ta haura sama jim kadan sai gata da kud'i ahannunta ta mikawa baba jummai tace"dubu d'ari ne kidau hamsin kikaiwa uwarta hamsin wannan kyau tace nabaku albashinta sai k'arshen wata zan ringa bata dubu hamsin itama


Baba jummai da murnarta ta hau godiya hajiya ta mike tace"muje innuna  miki dakin kwananki,

Namike nabi bayanta baba jummai kuma tai mana sallama ta koma...

*nabilancy Luv*💘💘💘
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*👩‍👩‍👧‍👧

*4rm*~NabilancyLuv~®

*page 2010 -2015*
A ckn sati d'aya nagane kan aiyukan da xan ringayi balaifi inajin dad'in zaman gidan don hajiya batada hantara ko kyara barta dai inhar ka tabota akwai fad'a ta iya masifa kwando kwando don haka komai a hankalce nakeyi bana yarda nasab'a mata.

Babu takura duk abinda Na girka zanci son raina komai akwaishi a kicin d'in hajiya inai mata girkin datace tanaso saini da maigadi sai kuma wani saurayi dake gidan d'an k'anwar tane shima duk abinda yakeso nake girka masa.

Dak'ina babbane ciki d'aya da babbar katifa da kuma tvn bango sai dorawata tasa kaya katuwa manne a bango da harda A.C dakuma d'an bandakina duk aciki.

Haj.Azzumi hamshakiyar macece meji dakanta domin sai abinda tacewa mijinta Alh ilyas yake aikatawa baya aiwatar da komai saida ixininta ba maxauni bane dukda d'an siyasa ne yana tab'a kasuwanci a kasashen k'etare

"Yayansu biyar da suka haifa mata hudu namiji d'aya, a matan daga wacce ta Auri senator,sai wacce ta Auri d'an majalisa,sai wacce ta Auri d'an kwamna d'ayace ma ta Auri babban d'an kasuwa,

*prince* *m.m* shine d'an lelen hajiya Autanta datake ji dashi muhd mahfuz yaro d'an kwalisa abokansa ke kiransa da prince,duk abinda mahfuz yakeso shi ake masa shekararsa ta uku Knn a egypt, yana kan gab'ar dawowa gida Nigeria karatu yakeyi a can Amma yana had'awa da Neman mata duk macen da yace yana so nan take' take bashi had'in kai wasuma kfn ya nuna yana sonsun suke kai Kansu gareshi sbd yanda yake jik'a mata da nera tabbas yana bazazawa,ga muggan abokai masu saka shi a hanyar tab'ara saidai baya shaye shaye ko kad'an Babban amininsa Arfat shi yake dad'a saka shi a hanyar lalata da iskanci har kawo masa wata Muguwar hoda yake wai idan yaga mace tai masa inya taya intaki amincewa dashi to da zarar ya busa mata hodar zata bada kai bori yahau.

Tabbas mahfuz yana tsula tsiyarsa a Abroad Wanda mahaifansa basusan halin da yake cikiba a ckn sati dayafa saiya nemi mata sunkai biyar kafin wani satin kuma ya canxasu ya samo wasu.

D'an k'anwar hajiya mesuna mubashshir shima yanada rawar kai karatu yake a BUK shiyasa ya dawo gidan hajiya Azzumi da zama iyayansa suna zariya hajiya tana nuna masa kauna komai yakeso tana masa tamkar Dan cikinta.

Mubashshir shine yafara bani matsala azamana ckn gidan hajiya a kullum da safe zan shiga inkai masa breakfast d'insa dake d'an wulakancine ma inna kawo masa indomie daya d'and'ana zaice gishiri yai wost ko yace baya ra,ayinta inje insoyo masa hankali ko yace kwai ko agada fi,ili kala kala ga hantara da kyarata da yake,inya tafi sch zanshiga nagyare masa d'aki tas,weekend ne nake masa abincin rana sbd yana gida inya sakani aiki nai delay kuwa yaitamin haushi Knn tamkar kare yanaimin fad'a kamar shiya d'aukeni aikin gidan.....


*to be continue*.....

*nabilancy Luv*💘💘💘

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *