Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Sunday, July 19, 2015

LABARIN WANI MAZINA CI

adsense here thankyougraphics13.gif

ZINA BASHI CE!
'Yan uwana Maza da Mata akwai wata Qissa da
zan bamu, mai matu'kar amfani acikin wannan
zamanin namu, ma'abocin Qissar, wanda abin
yafaru dashi, shine yake bayar da Labarin yadda
al'amarin ya kansace dashi.
Labarin yana cikin wata Mujallah (Magazine News
paper) ta 'kasashen Larabawa, kuma cikin
harshen Larabcine, amma
zanyi 'kokari wajen fassarawa gwargwadon yadda
na fahimta, saboda nima din ba gwani bane a
harshen Larabci.
gata kamar haka.......
Mutumin yana cewa:
A lokacin da ina saurayina nasami Admission a
Jami'a, bayan nafara karatunne sai na had'u da
wata Budurwa (Girl-friend) acikin Jami'ar tamu
muka 'kulla soyayya da ita tamkar ma'aurata,
hardai tasami juna biyu, (yai mata ciki kenan).
Da iyayenta suka gane sai suka tambayeta wanda
yayi mata ciki sai tace nine nayi mata.
Sai yayanta yataho nema na a fusace yana nufin
d'aukar mataki a kaina, yana zuwa saiya
tambayeni kaine kayima qanwata ciki ko ???
Sai na amsa masa da cewa:
Wace ce, ni banma ta6a ganinta ba a Rayuwata,
ban santa ba.
Sakamakon rashin hujjar da zasu kamani da ita
dole suka 'kyaleni.
Bayan tsawon zamani, wata rana nadawo gida
saina tarar da Mahaifiyata a dur'kushe tana tana
kuka.
Saina dur Qusa na daga ta sai tasake yanke jiki
tafad'i 'kasa har sau uku saina tambayeta a karo
na qarshe:
"Ya Ummi Man ladzhi haddath (me ya faru
mama)?
Sai tace:
Qanwarkace gata can wani yayi mata ciki!
Yace sai naji kamar an sokeni da mashi,
hankalina yatashi na tasa 'keyarta muka tafi
wurin wanda tace yai mata cikin.
Da mukaje sai yafada min maganar data tayarmin
da hankali.
Bawata magana bace face wadda na fadama
yayan yarinyar da nayi
ma ciki a baya.
(Ban santa ba, banma ta6a ganinta ba)!
Bayan zamani yaqara yin nisa sai nayi nufin yin
aure nafara neman aure nasamu matar da nake
so kuma akasa lokaci akayi biki, ranar farko dana
tare da ita saina sameta ba a matsayin budurwa
ba.
Ma'ana tariga tayi zina, tuni hankalina yatashi.
Saita fadamin wata magana mai shiga rai.
"Don Allah karufa min asiri, ka suturta al'amarina
kaima Allah sai ya suturta al'amarinka."
Yace sai nace acikin zuciyata:
Ya Rabby yakfy, yakfy.
(Ma-ana Ya Mahalliccina ya isa haka ya isa
haka).
•Ya cigaba da cewa:
Bayan mun kwashe shekaru da matata sai muka
haifi 'ya mace kyakkyawa gata da haske kamar
wata.
A lokacin da tacika shekaru 6 a duniya sai gata
wata rana tashigo gida tana kuka.
Me yafaru ?
Ai me gadine yayi mata fyad'e!
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN
Aljazaa'u min jinsil amal!
Wallahi duk tsiyar da kake sheqewa idan Allah
ta'ala yaga
dama sai ya hada maka zafi kan zafi irin wannan!
Yanzu kunga shi ya lalata 'yar mutane guda daya
tak shi kuma an lalata masa guda uku!
Yaa Allah ka Qara karemu daga zina, masuyi
kuma Allah ka shiryasu.

favicon.ico adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *