Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? #23

adsense here WACE CE ITA..?? 23
Na BBA GANA
Cox a rana sai tayi brush Sau biyar ba'ayi
kwana sati day ba suka fara cire wannan lakar,
kuma tsatsar ta fara bacewa,
Ranar tana zaune tana charafke sai ga farhaan,
dama bata gaidashi idan yazo ya zauna yace
yau kuma TV ake kallo da charafke, ta juyo ta
kalleshi tayi dariya, tace eh so nake in zama yar
gayu irin na matan Tv ya kalleta sosai sai yau
ya kula tana da wushirya,idan ba idonsa suke
masa gixo ba yaga haqoranta sun cire wannan
laka lakar na da,.
Yace gashi kuwa su Umma zasu dawo anan
zasuyi azumi, Dan murna batasan lokacinda ta
tashi tsayeba Ashe nayi kusa tafiya gida,? Naga
su dije da rukayya da goggo, tanata dariya, lallai
gaskiya ya hango, haqoranta sunyi haske, kinga
idan kin tafi kin huta dani ko, ta kyalktale da
dariya saida kumatunta ya lotsa, ai zama da
mugu irinka sai An shirya kamfaci arzikin ina
tausayinka, shi yasa duk matanka suke guduwa
duk matar daka aura sai ta gudu, kalli fa cikin
wata biyar saida kayi Aure 8 lallai yarinyar nan
batada wayo,! ita ta dauka duk matanane kena,
hahaha nine mugu iffaat?? babba ma kuwa. Ta
fada ba tareda shakkar komaiba bakya kunyar
fadamin haka a gabana? lallai kin girma, ta
kalleshi ta tabe baki, ai gaskiya na fada, nima
yanzu zan shirya suna dawowa sai in tafi
gidako? Taci gaba to yanxu kai zaka mini
dunkin sallah ko hajiya??
Yagyara zama ni xan miki ai ni kike yiwa aiki ko?
Eh Kaine maigiana, ta juyo tana fuskantarshi
kasan wani abu,?? Saikin fada, naga aminar
baba sule idan ta dawo aikibirnib sai ta dawo da
kayan gayu, tufafi sabbi qanzon shinkafa sabulai,
abubuwa dai da yawa na birni, ni ina zan
samu?? yayi murmushi dama tanada surutu
haka? Yace kema da kina min aiki da kyau da
duk zan siya miki abubuwan da kika lissafa
hadda qari ma zan miki, amma ke bayan tsiwa
da rashin kunya da zubar min da mutunci ba
abinda kika iya LA ilaha illallahu, yanzu duk
aikinda na maka haka zakace? kallifa baka taba
dukana na ramaba, au da ramawa kikeyi?
Taaaab wallahi a qauyen mu komi girman qato
idan ya dakemu sai mun rama, kai hadda
shugaban yan sandan garinmu ya dakemu
mukaje gidan sa da dare muka fasa mai mota,
ya fito da I do da gaske kikeye??
Ta qara gyalgyalewa da dariya sai tamai kyau,
wallahi da gaske nakeyi, kicemi ke yar
ta'addace...! adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *