Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 25

adsense here WACE CE ITA..?? 25
Na ABBA GANA
Tashiga dakinta ta zauna ta tsefe amma saida
tayi kuka dan zafi kuma gashi ba kibiya duk ya
harhade ko gida kullum sai tayi kuka idan ana
mata tsifa, yauma saida tayi taje ta wanke da
man da taga anyi hoton qashi jiki haka datti ta
riqa zuba kamar an kwaba qasa, haka tayi ta
xubarda daddi har yayi fess dashi kamar bana
iffaat ba, matsalar daya ba tada mataji kuma ba
tasan yanda zatayi irin na yar baqaba, sai ta fito
Palo tana goge gashin farhaan ya kalli gashinta
aransa dama tanada gashi haka, ya zauna yace
dama kinada gashi shine baki kyarawa, tace
wallahi parhuun zafi yake min.! Ya kalleta tanata
kiciniya da gashi yace ya sunana? Tace Parhuun
mana haka naji kowa yana fada, ya kwashe da
dariya saida yayi kwalla wai PURHUUN yarinya
katki bata min suna sai nanatawa yake
PURHUUN lallai wato kusan shima bata iyaba
gaskiya anyi baqauya anan yace to ba haka
bane farhaan ne, ta dago kai tace Parhan, yace
aah farhaan, parha, ke kalli bakina, kice far, tace,
par, kalli ki haqoranki akan lebenki zaki Dora sai
kice far, takuwa yi tace far yayi dariya yauwa
kinyi daidai, sunana farhaan,ta fada daidai tace
Dan gayu ko sunan ka sai ka koyamin. Ta bashi
dariya wai Dan gayu, so funny, tace to yanxu
gayamin yanda ake wannan abin a saman kai
yayi sama sosai, yace ni ban iyabafa banmasan
mi kike nufina, LA ilaha illallahu, ta to saki
gashin ta toshe baki babba na qarya, wallahi ko
wasu a matanka kamin ka sakesu nagansu dashi
kace baka sanshiba, yayi dariya lallai yarinyar
nan case ce, ni nake qarya?? Waima waya gaya
miki matanane?? Ta zunburo ta kama gashinta
ita burinta a mata irin na yar baqa ta hanya,tace
to miye naka? Abokainane ko ban fada miki
inada abokai mataba, ta saki gashin kanta ta
qara rufe baki da hannu, shine kake tabasu?
Hmmm!! Ta tabe baki Mudai garinmu duk namiji
mai taba mata Dan iskane, ko wasa bamayi da
maza duk iskancine garinmu, kaga da garinmu
kake da nace maka Dan iska, keeeee, nine dan
iska,?? ta zaro ido ai ban fadaba. nace da garin
mu kake.. aranshi yace ko inane wannan
iskancine, yace to a birni wayewace ba
iskancineba, ya fuske ya miqe zai fita, baka
gayamin yanda akeyiba, sai na dawo zan gaya
miki...
A hanyarshi ta dawowa yayi karo da wata tayi
acucu maza sai ya tuna da alqawarin da yayi,ya
siyo mata ribbon manya da mataji da man kai
ya kawo mata.. Tanatajin dadi zata yi irin na Yar
baqa, ba'anan kizo ke saqarba bata iya
sakawaba ta kuwa fara hadashi da Allah, ya
koya mata shi ba iyawa yayiba, yana mamakin
yanda take mai kamar wani sa'arta yanaga ta
mance WACE CE ITA.!! Yayi tsaki ke kada ki
dameni kinji, na siyo miki kuma ni zan saka
miki? duk ma yan matanshi basuda gashi irin
nata duk qarine sukeyi, ya zauna yaci gaba da
kallon ball dinsa, dama iffaat akwai naci akan
abinda takeso. tazo tana hadashi da Allah tana
mai shagwaba abin ya burgeshi.. Yayi tsaki
aranshi yace yarinyar ta fara rainani, ta kuwa
miqamai gashi ta zauna ya rasa yanda zaiyi to
ki taje mana ta fara tajewa tana gwalla Dan duk
ya sarqe tanayi yana shafa mata mai har ya
taju yayi kyau gashin yana gyalli abinka da
gashin fulwni sai Wanda ya gani,ya karbi gashin
ya kasa tattarshi yace ta tattara da kanta ya
nuna mata yanda zatayi ta tattara, to aike basai
kin saka irin nasuba tunda gashinki yana da
tsayi sosai, Allah ko? eh mana, haka ya
taimaka mata tayi parking dinsa kuma yayi irin
yanda take so, yanxu kasan mi nakeso? Yace
Aah, akwai wasu kaya da ake sakawa sai ayi
wannan abin sai ayi kyau a zama yan gayu idan
xantafi gida zaka siyomin? nama taba ganin
abokiyarka da irin su! Ke ni ban ganesuba, kuma
ki sani duk suna cikin kayan sallanki, eh na
yaddda ta amsa tana zagwadii.... adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *