Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 26

adsense here WACE CE ITA..?? 26
Na ABBA GANA
Bayan ya dawo, ita duk wautarta yau zai siyo
mata kayan taga wayam hannunsa ba komai,
laaa farhaaah Yaushe zaka siyomin kayan
gayuna? irin na abokanka,? Ya harereta bakida
kunyako kina kiran sunana. Ko bangirmekiba. yi
haquri Mixance makato? ta fada irin ta matsu
dinnan taji zancen kayan gayu, look ki bari zan
siyo miki kawai kamin ki tafi gida, yayi niyar yaje
da ita a aunata gun mai dinki amma ina yana
tsoron ta kwafsa mai wannan hargitsatsaiyar
wataqilama taje ta nemo magana, to kawai tace
mai amma ranta baiyi dadiba ta wuce daki ta
zauna, ta fara tunaninta na zama gayu irin na
Yar baqa iffaat yanxu batada buri irin taga ta
zama Yar gayu, Niko inason ganin iffaat da gayu,
aranta tace gayufa dole saida wanka, taaaab
yanxu kullum sai tayi wanka kenan.?? idan ba
wanka ba gayu, ta tashi ranar farko data ji tayi
wanka Dan ra'ayin kanta, ta fada wanka tayi
wanka da ruwan zafi ta wanke dattin
wafafuwanta sabida bata yawo da takalmi ko
lanmu haka take tafiya ba takalmi tana wankewa
ta tuna da qafafun hafsa lokacinda tasata gashi,
sumul sumul qafar yan gayu ba kaushi, ta
wanke iya yanda zata iya, ta fito ta saka yan
tsumma karonta.. Tayi bacci anan tayi mafarkin
ta zama Yar gayu, tayi qawance da Yar baqarta,
ta farka ta fito Palo cin abinci bata dadeba sai
gashi ya kawo mata kaya English Wear ne, ya
nuna mata wayannan kayan kike nufi?? Sauran
nakai dinki duk na sallah ne amma, Ta kallesu a
tsorace ita a qauyensu idan mace ta saka wando
za'ace mata yar iskane so bazata sakaba, data
fada mai yayi dariya sosai wato qauye bala'ee
ne, qauyanci masifa, yace ki riqa saka wannan a
gida idan zaki fita saiki saka wayanda bana yan
iskaba. OK bari in saka ka gani, anan yaga zata
cire kayan jikinta no ki shiga daga ciki mana, ta
kwashi kayan ta shiga daki da gudu ta saka
wandon yafito da ita ainihin ita sai Wanda ya
gani mazaunan suka fito hips din ma ya fito, da
yake dukiyar fulanin yanxu take fitowa yayi dan
tudu kadan sai head dinsa ake gani ya fito
saman rigar, ta fito da gudu tana dariya na fara
xama yar gayuko? farhaaah ya kalleta tashin
hankali, Ashe babyn nan ta hadu a ransa ya
fada, dukda cewa ba daidai ta saka kayan ba
amma sun mata kyau, kalli nayi kyau, sosai kin
ganki kuwa, tace kamar ba yar aikiba ko, yace
sosai kuwa, tana ta dariya ta janyo gashinta da
yake ta cire riboon garin saka tufafi wai dole sai
yayi mata yanda akeyi dinnan, no ki bari in miki
hoton tarihi kuma na turawa umma taga
yarinyarta ta fara zama gayu, nan ya sa tayi
wannan tayi wannan idan tayi wani style sai
yakai zauna Dan dariya, qarshe yace to tazo ya
dauketa ita dashi ba tare da damuwaba ta
kwanta a qirjinsa ya daukesu photo tana dariya
duka dimple dinta sun lotsa gwanin ban sh'awa,
kawai daga kan da zasuyi sukaga hafsa kamar
daga sama, ta kalli kayan jikin iffaat ta watsa
mata harara, ta riqe kunkumi wai farhan na
tambayeka waye wannan yarinyar?? kawai fada
min gaskiya, ya kalleta kallon bangane mi kike
nufiba, sau nawa ina fata miki WACE CE ITA!
Amma kina min magana wai iri, hafsa ranta ya
gama baci iffaat kuwa dama batayi ta kantaba,
murnar kayanta takeyi batama gane hafsarba
yana juyowa tace Yaya farhaaah yaushe zaka
kawo min kayan sallah? Ya kalleta ita ba abinda
ya dameta sai su umma sun dawo,
Kamin ya juyo hafsa ta fita Yabi bayan hafsa,
itakam ta dauki kayanta ta je dakinta,
Kamin ta tada mota yasha gabanta yace mai
gadi ya kulle gate, hafsa kuwa anriga anyi fushi,
ya bude motar ya janyota jikinsa, ya rungumeta
yana shafata a hankali, miye na fushi, hafsa??
Ni kawai ka fada min WACE CE ITA please!! adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *