Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, July 18, 2015

WACE CE ITA? 35

adsense here WACE E ITA..?? 35 Na ABBA GANA A cikin kayan da Yaya Farhaan ya siyomin hadda waya wai mu riqa gaisawa, ranar da aka bata kayan Dan murna ko bacci takasa yi, kuma wannan abinda takeyi bata gane komai, * wayar ni ban iya komaiba hasalima nidai saidai na gaisa dashii in miqa musu, tawa wayar kullum tana qasan pillow karatu ya sakata gaba, ga abinda ta daukarwa kanta tunene tunanene... farahnax ta koya min yanda ake amfani da waya, ta kira min yaya farhaaah munyi waya dashi, Wanda tunda ya tafi saudaya muka gaisa shima ina fara magana ta tsinke, Mun gaisa sosai yanayi yana jefomin English ina ganewa amma bana iya bashi amsa, har yan kudin dake cikin suka qare abinka da international call.. Bayan kaman kwana hudu ranar na dawo lesson ina danne danne a wayar kawai tayi karo da maganar da sukayi da Yaya farhaan, zan iya CE muku duk yinin ranar abinda ta saurara kenan, ta rasa mi yasa komai nashi burgeta yakeyi, bama kamar idan taji dariyarshiba, itama saita dara haka take zama ta miqe gafafu tayita saurare tana dariya, wannan voice yasata walwala ranar farahnax taso ta gane sai kawai ta daina saurare dan bata iya delete ba, Sai yanzu ta gane mi wannan takardar da goggo ta bata tace yayyenta sunce ta kira take nufi, Ta nemota a cikin kayanta ta saka amma wayar tata ba kudi, ta je gun farahnax tace ta kira mata wannan number, farahnax kuwa chatting takeyi bazata iya bata wayantaba sai ta saka mata recharge card na 1,500 ta saka mata number tace ta kira, ta koma dakinta haka tayi ta kira ba tareda tasan kiran yana shigaba saida ta bar miss call 47... Ameen bayan ya dawo yaga miss call da yawa sai ya kira, Tayi sallama, ya amsa yadauka mamarshi ne Dan kusan muryarsu iri dayane, mama lafiya kira haka ?? sai tace ba Maman shi bane ya tabbatar da wrong number ne sai kawai yace wrong number ya kashe, bai tsaya yaji abinda zataceba, Itama dataga haka sai bata qara kiran number ba, ************** Kwanaki sun tafi iffaah ta waye iya wayewa kamar ba Yar aikiba, wani lokaci Idan sunfita tareda farahnax bazaka ganetaba cox tafi farahnax kyau nesa ba kusa ba, saidai har yanxu qauyancinta da yake nuturally ne sai bai saketaba tana taba abinta, gata bakinta baya shiru duk abinda ta gani saita tambaya gata a waye a dressing amma a aikace har yanxu da saura... shekara ta zagayo iffat zata koma qauyensu Dan sallah da azumi achan kamar yanda sukayi alqawari run farko,ta rasa gane dalilin da yasa ranta bayason komawa qauye kodan zancen goggo ne da take cewa za'a saka mata ido a qauye tayi zamanta birni! ko kuwa rabuwa da iyayen farhaan da, ko mahaifiyarsa ta kalla sai taji sanyi sabida tsabar kamarsu da farhaaah..... adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *