Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, July 18, 2015

WACE CE ITA? 36

adsense here .: WACE CE ITA..?? 36 Na ABBA GANA ************ Iffaah ta isa qauyensu cike da tunanin rabuwa da da iyayen farhaaan.. Goggo tayi mamakin yanda ihhatu ta chanza tayi kyau duk wani Abu da ake buqata a gurin mace ihhatunta tana dashi saidai tunda iffaat taje bata zuwa ko ina daga gida sai gida, ta natsu matuqar natsuwa, ga yawan shiru shiru da takeyi. Ranar goggo ke tambayarta bata sami miji a birniba, goggo ni har yanxu ba Wanda yakesona,! Ta dafe qirji kardai birnin ma kin musu halinsu kin kashe kasuwarki, zancen goggo ya bata dariya, goggo Allah ne bai kawoba, hakane kuma Dan yanxu naga kin tsama yan mata, wallahi sai mai mota zaki aura kikaini makka ko? Ta amsa da sosai kuwa ta fada tana miqewa tashige daki, zan iya CE muku tunda iffaah ta dawo qauye kullum sai tayi kuka, wani Abu takeji ya tsaya mata a zuci ya tokareta ya hanata sakat, bata iya aikin komai Idan wannan abin ya motsa mata.. abinka da yarinta Sam bata gane cewa soyayyah bace, bata gane kanta Sam. sau tari takanje bayan gari ta sami bishiya ta zauna taci kukanta har ta godewa Allah, sannan ta dawo gida ba abinda yafi damunta illa rashin gane takamammen abinda yake damunta. Wayartace tayi qara, ta dauka farahnax ce. Hello Ta amsa tanajin dadi Farahnax chikin dariya take maganar bayan sun qare qaisawa, kee iffaat Yaya ya dawo dazu sai tambayar ki yakeyi, qirjintane yayi bala'en bugawa sai ta tsinci kanta da zubar da hawaye, na rashin dalili ta yi shiru. Hello hello iffo kinajina? Tanata magana amma iffaah ta kasa bata amsa, qarshe ta tsinke wayar, iffaat ta shige dan dakinta ta zauna ta rasa mi yake damunta yan watannanin Miyasa duk lokacinda take tunanin yaya farhan take shiga wani hali?? Miyasa duk taji sunanshi sai taji faduwar gaba?? Miyasa taji tanason ta Ganinshi yanxu ?? Miyasa duk ta zauna labarin sa take sonyi?? Kai tambayoyinta sunyi yawa, batada amsar ko daya. Tayi wani tsaki Ba abinda yake daga mata hankali irin son ganin farhaan da takesonyi, Wanda ji take kamar tayi fiffike taje ta Ganshi, Amma ba halin yin haka, Su iffaat an fada tarkon soyayyah amma batada labari har yanxu ba tasan miye soba.. adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *