Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 40

adsense here .: WACE CE ITA..?? 40
Na ABBA-GANA
Abba Ku taimakamin ku mayar dani gidan mu,
jikin kowa yayi sanyi yanda take kuka kamar
ranta zai fita ta basu tausayi koni Jabo ta
matuqar bani tausayi Dan saida nayimata qwalla,
tabbas So bala'eeee ne, yana zautar da mutum
ya rasa mi yake masa dadi yama rasa gane
kansa,! zaiyi loosing din control dinsa ne gaba
daya, ko manya ya suke fafatawa da soyayya
bare yarinya Yar shekara 15 irin iffaat da har
Yanxu batada wani wayo bare har ta gane wane
hali take ciki....
Abba yace To ki daina kuka iffaat za'akaiki gida
dama Dan kada ya zama mune muke shiga
haqqinki ba tare da mun saniba amma tunda
kince bakomai kin zabi hakan shikenan, dukansu
basu ji dadin tafiyar da iffaat zatayiba, amma ba
yanda suka iya dole su saka mata ido, farahnax
ma ta sameta a dakinta tana kwance bayan ta
hada kayan ta, yanxu iffo tafiya zakiyi ki
barmu?? Muka miki dan Allah da har bakya iya
zama damu?? Ta kalleta tace sister wallahi ba
haka bane bakumin komaiba, kawai rainane baya
min dadi kuma bansan dalilin hakanba, kuyi
haquri Dan Allah, anan dai sukayi hirar qarshe,
koda iffo taqi sakin jikinta...
sun mata goma na arziki suka bata kudi masu
yawa sannan akasa driver yakaita har qofar
gidansu.
Shikenan iffaat ta baro gidansu farhaan.....
******
Iffaat a qauyen su,
Ashe yanzu bala'en yake bata saniba, yanzu
take qara shiga damuwa yanzu take gane cewa
ganin iyayen farhaaan rahamane gareta, amma
kuma still bata gano hakanba, ganin su da
takeyi yana raqe mata qunci matuqa, ta
sukukuce kamar ba itaba kai duk Wanda yaga
iffaat sai yayi mamakinta bata magana, Yar gayu
kam da take burin zama ta Riga ta zama, saidai
so silent yanzu take yanxu. goggo har tana tsoro
kardai ba abin kunya tayo aka korota birnin ba!!
*****
Watan iffat biyu a qauye ba walwala kullum
fuskar nan a turnuqe kamar ta dijee dama dijee
haka take ba sakin fuska su iffaat ne masu
dariya, yanzu kam iffaat ta zama Yar baqin rai
fiye da dijee..
Ranar iffaat ta tashi da ciwon cikinta har Yanxu
goggo batasan ta fara period ba tasha magani
ciwon ya fada mata tana zaune cikin runfar
qofar dakinta da Dan tsinke a hannunta tana
tsane a qasa taji sallama ta amsa batareda ta
dago kaiba tsul goggo ta fito daki tana washe
baki na dago kai na kalleshi, ke ihhatu bakiga
yayanki yaxoba, koda na Dade ban ganshiba
hakan bai hanani ganeshiba Yaya nane! Taje
gunsa na fada jikinsa tna kuka shima dai yayi
gwalla, suka zauna saman tabarma,
Yaya Ameen yake cewa goggo kinsan kuwa ba
nan nakeda niyyar zuwa ba sai naga na biyo ta
kusa danan nace bari na shigo qauyen namu in
gaisheki, Ashe rabon naga Yar mamane kullum
zancenki take mana, nayi murmushin jin dadi
Dan uwa Rabin jiki ciwon cikinta tuni ya ware sai
murna takeyi tana xubar da yan hawayen
murna..
Nan take Ya kira Mama ya gayamata ai gani ya
sameni yanxu mama murna kamar ta kasheta
yau taji autanta munyi magana ta ita inatajin
dadi,
Anan aka kitse akan gobe Yaya zaizo ya fafi dani
daidai nan na Dan shirya, goggo ranta baisoba
don iffaat ce rufin asirinta gata ba da bare
jika..... adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *