Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, 20 July 2015

WACE CE *******ITA? 60

adsense here computerimages1.jpg

WACE CE ITA.?? 60
Na ABBA-GANA
Iffaat miyasa kike min hakane? Koba komai ni
Dan uwankine tun kamin mu hadu da margayiya,
kuma naxo na auri yayarki, kina tunanin kodan
wannan ai bai dace ki riqa min wani gani ganiba,
ki tuna kin min laifinda ya dace na hukuntaki
amma na gyaleke na yafee miki..!
Anti masifa madam iffaat ta watsa mai kallon
banza hadi da wata uwar harara! Laifin me na
maka oga? Wato ma ni na maka laifi ko?? Ka
manta chin mutuncin da kake yiwa Yar uwata?
Kamanta wulaqancin da kake mata?? Ka manta
yaudarar da kake mata?? Sannan duk ka shuresu
kaxo kana cewa ni na maka laifi?? Ta daga kai
tayi karo da hotonta ita da Suhaila sun rungume
juna suna dariya. Hawaye ne suka wanke mata
fuska tayi missing din Yar uwarta abar sonta,
farhaan ya kamo hannun iffaat yana zaune iffaat
Dan Allah ki yafemin! Nasan ban kyautawa
Suhaila ba ko kadan, wallahi sai yanxu nake
ganin irin rashin kyautatawar Dana mata idan
kika yafemin tamkar itace ta yafemin ta kasa
kwace hannunta daya riqe batace komaiba.!
Tayi ajiyar zuciya ta karbe hannunta, ta zauna
har ya qare surutansa batace masa komaiba,
wallahi iffaat ina tsananin son Suhaila, ji tayi ya
daba mata wani gwaho a zuci har saida ya
gane. Nasan baxaki yardaba amma gaskiyane na
fada miki, ya gaji ya tashi Ya qara wuta..
***
Iffaat yan mata result ya fito ana kiciniyar
shigarta jami'a ta sami damar shiga cikin nasara
an bata course dinda takeso kuma.
Dai dai lokacin auren farahnax ya matso sai
shirye shirye suke qawayen amarya, komai itace
gaba itada Yar baqa sai iyayi suke, anyi auren
farahnax lafiya ankai amarya Gidan mijinta da ke
abuja, iffaat dai kam kullum sai tayi sabon
saurayi amma ko kallo Basu ishetaba karatun ta
ta saka gaba.!
Ranar umma tayi rashin lfy sunje dubata itada
mama da maman suhaila, umma ke tambaya ta
yaushe zatay aure? Ko sai ta samo mini mai
saida ruwa irin na dijee, akasa dariya kunya ta
kamani na tashi na shige lanbu don demo
abincina na da na barsu su nan.....
KU BIYOMU DON JIN ABINDA IYAYEN
WAYANNAN YARAN ZASU TATTAUNA AKAI. adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *