Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Sunday, 19 July 2015

WACE CE***ITA? 47

adsense here computerimages1.jpg

WACE CE ITA..??47
Na ABBA-GANA
Yan matan gaba daya suka miqe tsaye, dayar ta
gefe ta kwasheta da mari itama dayar taci
kwalarta suka mata lilis,duk sun buge mata
fuska, suna tsaka da dukanta saiga baba sajeen
yana kora kamin yazo sun gudu bai tsaya duba
halinda iffaat take cikiba kawai yaganta kamar
tsugune yahau zuba mata bulala tun tana kuka
har tayi shiru. Ke wace irin mai taurin kaice?
Maza ki tashi ki wuce class bai tsaya kulataba
ya hango wasu yara biyu ya bisu a guje suka
tsere, iffaat dai an mata lilis baki sai jini yake
yaji duka gun yan mata gashi baba sajeen ya
qara mata wani, tana nan gurin taji ana cewa
still tanananfa, kixo mu dubata, nidai baxanjeba
ke kije , habadai sabida kefa na daketa kuma
kice bazakijeba, please kixo muje, sukazo gurin
iffaat sai kuka ganta tana xubar da jinin baki da
hanci duk hijabinta ya lalace, nidai abba abin har
mamaki ya bani wai iffaat ce take daukar xilla
yau!! Rayuwa juyi juyi....!!!
Suka dagota suka tallabota hannu biyu dayar ta
ruga ta siyo pure water Leda daya sukaxo iffaat
bata iya koda magana, suka wanke mata jikinta
suka qaro ruwa suka wanke mata hijabinta da
duk gun da jini ya bata, dayar take gulma a
hankali tace kalli gashinta! Dayar tace ummm
nagani, suka kalli iffaat wacce ta bige mata
bakince ta fara bata haquri, sai dayar ma tac ci
gaba da bata haquri batace dasu komai ba,
hasali ita batajin zafin dukanda aka mata illa
xafin Cewar da akayi Yy farhaaan takeso.!
Sunata bata haquri ita kuwa tanata tunaninta.!
Wai yaza'ayi taso saurayin yayaryta?
Yaza'ayi taso Wanda nake kallo a matsayin
yayantaa?
Lokaci daya ta tuna da rashin kamun kansa
shegen Neman mata, ta tuna duk wani iskanci
nata yasanshi, shine yafi kowa sanin WACE CE
ITA, har abada baxai karbi soyayyar taba, idan
ma zai karba yazatayi da yayarta Suhaila, anya
ma gaskiya suka gaya mata da sukace sonshi
takeyi,???
www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *